Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Sosai tare da ranƙwafowa bakinsa saitin kunnenta.

“ada har na Sadakar na Rasaki kenan, Har na hakura na bar ma Bamalli, Ashe ke din rabona ce "

Fuskarta ta sake kaudawa gefe ta lumshe ido da son ƙwace kanta. Matso da fuskarsa yayi gab da nata, saukar numfashinsa akan tata fuskar ya sata ɗan buɗe idanunta dake rufe.

Da gudu Sureey ta shige ciki tana dariya, Mama ta fito daga Dakinta Jin Shurun yayi yawa , Charab Suka hada Ido da Saleem Yayi saurin sakinta ya sunkuyar dakai Yana Sosa keya.


Itama A kunyace ta shige daki kanta a 'kasa, Mama tabi bayansu da Salati, yaran zamani sai Addu'a😅.

Duban Ayyan Tayi, wannan Yaron Kuma fa

" _'Dan wani Dan uwana ne, Ita tace in taho taredashi ya muku kwana Biyu_ "

Saleem ya Fada kansa a sunkuye don bazai iya cewa Dan Maryam bane, kuma ya maido mata dashi.....


*ASH AEESH*

Ashman na Fita kai tsaye Gidan Aareef ya nufa,

"Idan da gaske kana Sonta ka fada min Gobe Goben nan zan Aura maka ita, Zan baka Gida da Mota, Zan baka jarin da zaka Dogara dakanka ka riketa..."


"Dakata Ashman kake kowa?, bakayi arzikinda zaka Biyani na auri kwantan Matar nan taka ba, zuciyarta tayi sanyi da yawa Ban aureta ba na buga mata zafi inaga na aureta, idan Na aureta a daren farko Kasheta zanyi"

Yayi maganar babu wata fargaba a taredashi idanunsa Na Nuna tsantsar gaskiyan Kalamansa, zai iya kasheta idan aka Biyashi ya aureta, hankalin Ashman a tashe ya maidata Gidansa, tausayinta Yakeji Sosai har Cikin ranta, baya jin zai iya Komawa da ita gidan su , a yanda yake ganin yanda Sadeeq ya fusata zai iya babballata.

A Ranan yadda sukaga rana haka haka sukaga dare, damuwan duniya tayi mata yawa tayi kuka Tayi Kuka sosai, kukan da ta dade batayi irin shi ba idonta ya kumbura sosai, ga kaikayi ya addabi rayuwanta, ta rasa Ya zatayi da ranta, Ashman baiji Haushinta ba Ko kadan , Lallabata yakeyi throughout the day, anan ta tabbatar Ashman Shine masoyinta Na asali Wanda bazai gujeta ba duk rintsi.

Ganin Addiction dinta na neman sama mata neuro problem yasa hankalinsa ya tashi, Psychiatrist ya kira nan take aka fara nema mata magani, na adsini Dana zamani.

Kullum tana rufe adaki shike mata girki ya kawo mata ya bata a baki, bata iya yin komai dakanta har wanka shi ya koma yana yi mata, Abin yayi girmanda Bata iya komai banda Kuka da surutai babu Abinda takeyi,Treatment akeyi amma kaman Ana manna mata ciwon Hauka, Kullum Cikin Rokonsa take akan ya taimaka yayi mata Allura Koda Na P.C.M ne, haka zaiyita rarrashinta yanaji kaman Yayi mata Kuka, sai ya fita yake samu yayi kukan Shi daya hankalinsa a tashe.

Tayi Wata data bata zuwa ko Ina Tana Gidansa, anan ake Mata psyciatric Treatment, Ammie bata nemeta ba, haka Yan uwanta ma haka, sannan ba'a kira Ashman an tambayeshi ya take ba, don bai bada damar hakan ba.

A halin yanzu watanta daya cuff da Fara karbar Magani, Alhamdulillah ta fara dawowa hayyacinta, ta daina Soshesohen da takeyi da sumbatu saidai har yanzu bata daina Rokonsa akan Yayi mata Allura ba, tayi sa'a cikinta ba mai sa Laulayi bane kuma baya wahalar da Ita.

5:30pm na dare, Yana zaune saman sofa watching TV dawowarsa kenan daga Office, vest ce a jikinsa da 3Qauter hannunsa riƙe da Remote Yana kallon world cup.

Tana Kwance a kan cinyarsa tana masa dariya , anci Team dinshi sai Tsaki yakeja.


Ta kira sunanshi

"Ahky...."

"Na'am Ihty...."

Ya Fada hankalinsa akan T.V.

" Don Allah ka Maida min shi Zee world"

Ta Fada kaman zatayi kuka, sanyin hawayenta yaji akan Kafarsa da hanzari ya dago fuskar ta yaga hawayen takeyi

"Ihty Why are you crying...?"

"Nide ka sa Min Zee world"

Tsaki yaja, ya maida Duban sa kan T.V zufa na keto masa, don Anci team dinsu dayawa.
Aikou kaman ance ya maida kallonsa A cisu ,Yana Duban T.V aka ci team dinsu, ransa bace ya kashe TV din gaba daya Yana huci.

Dariya ta saki ,

_Golan Nasu mai idon biri ya kama ya Saki ya shiga raga_

Murmushi ya Saki ya shafo gashin kanta ake a hargitse a hankali ta kira sunanshi

"Ahky...."

Ya amsa
"na'am Ihty"

"Ahky...Saura wata biyu babyn mu ya fito duniya, Saura 2months in fara amsa Sunan Ammie "

Sai kuma Ta saki murmushi..

"Wayaga Aisha Ammie"

Murmushi ne ya sake suɓuce masa, yasa hannu yaja hancinta, hakan yasa ta dago ta sarƙe idanunta a cikin nasa suka kurama juna ido, kallon juna suna aikawa juna zafafan sakonni masu atsa jinin jiki da bargo, wani Abu yake Kallo cikin idanunta wadanda Suke barazanar rabashi da duk wani ƙwarin laka na jijiyoyinsa.

Ita ta fara kauda idonta daga gareshi da fadin

" Ahky.... ,baby nason Ayi masa Allura"

Banza yayi Mata, Yana kokarin Saita kansa don Ji yake kaman bashi ba ,jiyayi kaman Ta kwashe komai na ransa ta barshi da gangar jiki a zaune.

Kuka tasa mai Itafa a dole sai yayi mata Allura, Abu kaman wasa Sai gani yayi ta fara Kukan mai sauti, ta tashi tana bubbuga kafafunta a kasa ko nauyin cikin dake jikinta bataji tsawa ya daka mata.

"Keh natsu...babu allurar da zanyi miki zauna ki natsu kafin Ranki ya baci"

Kuka ta sake saki .

"Allah sai dai Raina ya baci, Amma Wallahi bazan Zauna ba Sai ka min Allura"

Tashi yayi ya nufota zaii kamata, ta arce a guje tana fadin

"Haka Kawai Mutum an rufeshi a gida baya Fita Kuma sai a hanashi abinda yake so?"

Sai Kuma maganarta makale sakamakon Daurewan Da marararta Tayi

"Wassh..."

Ta fada tana rike mara, da gudu ya Nufota zai kamata ta zille tana Salati.

Wani irin Ruwa mai Yauki ya fara bin Kafarta ihu Tayi

"Wayyo Ahky....labour yazo Innalillahi Wainnailaihirraji'un, Ahky haihuwa yazo....ahky Bakwaini zan Haifa"


Cikin tsananin rudewa take magana tana Kallon Ruwan dake bin kafarta, ga azabar da takeji a mararta.

Hankalinshi ya tashi, murya na rawa yace
"Ki kwantar da hankalinki Ihty....ina zuwa"

Da gudu ya shiga ciki sai gashi ya fito da Kayan karbar haihuwa, sai Ihu take tana Kuka.


Ta dube kayan da ya fito dashi Cikin tsananin Azaba tace

," Ahky ka maida kayan ban Shirya haihuwa yanzu ba"

Mararta ta sake kullewa da Karfi, ta saki kara

" wayyo Allah Na, Hazbunallahu was ni'imal wakeel , Ahky mutuwa zanyi".

Gaba daya Ashman Yarude, rirriketa yayi Yana fadin

"Bazaki Mutu ba Ihty ki Damke numfashin ki Sai kiyi Nishi mai mai karfi"

Ta rike bayanta da ya daure tana Harararsa, cikeda Son daurewa.

"Koya Min Haihuwa zakayi?"

Nishi takeyi tana Kuka Cikin Azaba, amma dukda haka Bakinta bai mutu ba, sai wasu surutai take marasa kan Gado.

"Ahky Ka duba Min, yaron kato ne....? bana so yaron ya karani..."

Sai kuma tace
"Wait Ahky... Kayi min Alkawari idan macece za'a sa mata Sunan Ammie Na _Noor_ idan kuma namiji ne zaici Sunan Kakanmu Shettimah "
Kuka takeyi sosai tana Maganar, muryarta ba wani fita takeyi Sosai ba Tsabar wahala da Azaba.


Nayi Gabas🚶

Bintou😘
*_WUKA A ZUCIYA_*
-(BLEEDING HEARTS)




*60*


"Wait Ahky... Kayi min Alkawari idan macece za'a sa mata Sunan Ammie Na _Noor_ idan kuma namiji ne zaici Sunan Kakanmu Shettimah "
Kuka takeyi sosai tana Maganar, muryarta ba wani fita takeyi Sosai ba Tsabar wahala da Azaba.

Shuru Ashman yayi trying to help her,tasa hannu ta tureshi
"ka Min Alkawari, if not wallahi bazan bari ya fito duniya ba, kanshi na fitowa zan zauneshi ya mutu kowa ma ya huta"
Ta fada new tears na fita daga idanunta,yasa hannu ya Fara goge Mata hawayen
"Stop crying...pls..." Ya fada ahankali Yana goge mata zufan face dinta,numfashi Take ja Tana Ambaton Sunan Allah,tana Maimata

"yayi mata alkawarin Za'ayima ammie takwara"

Shikou kasa amsata yake tsabar tashin hankali
Azaba ta ishi Aeesh ,sai nishi takeyi Ji take kaman zata mutu, duk addu'ar datazo bakinta yitake, tana kiran Ammie, Ahky..,Yaaa Sadeeq,Habeeb...ya Saleem, Reey suzo su taimaketa zata mutu.
"Wayyo Ammie zan mutu, Dan Allah Ahky ka min Alkawari, ya fito ,Jaririn nan zai kasheni wayyo Anty Ammie,ko ceci ratuwata."
"ki Daure Ihty kiyi nishi da k'arfi kinji, kinga kan yaro gashinan ya kusa fitowa, insha Allah,Nayi miki Alkawarin zanyi wa Kaka ko Ammie takwara,kinji...ki taimaka kinayin nishi zai fito ki huta, addu'an da kikeyi dazu ki cigaba bazaki mutuba insha ALLAH".

" to Daddyn.., inayin addu'ar aii, hazbinallahu wani'imal wakil, Allahunmaajurnifi musibaty ,lahaula walakuwwata illa billah,la'ila anta subhanaka inni kuntaminadhalimin, Alllah Sarki Ammie..."

Ashman ji yayi kaman ya maido nakudar ya dawo jikinshi, tausayinta yakeji sosai, dukda bayau ya fara ganin Haihuwa ba,Amma na Aeesh yasa jikinsa yayi sanyi matuka

yanzu nan haka Anty ammanshi tasha azabarnan don Tsabar muguntan Abba saiya ringa kaima wata su yana bata kyauta sai kace 'ya'yan faara?.

Abba ya cutar da Ammah Gaskiya, wannan alhakin kad'ai ya isa hanashi zaman lfiya da kwanciyan hankali a duniyan nan.....

Tunaninsa yakatse lokacinda ta saki Nishi kan Baby ya leko ,ya gyara kan sannan Ya jawo Gangan jikin a hankali, wni irin jini ya biyo baya, ya yanke cord, bakinsa dauke da Alhamdulillah,MashaAllah, Weldone ihty, masha Allah,welcome to the world Noory.......
Kuka baby ta tsala daidai lokacinda Aeesh tayi baya ta fadi sumammiya jini duk yabi ya jikata sharkaf.

A rude ya daura Babyn a kirjinta, yana Tattaba Gefen fuskarta da Ambaton Sunanta, amma baiga Alaamar numfashi ba,baby kam Sai kuka take tsalawa, Kanta yad'auka yad'ora bisa cinyarsa, a matukar razane yake tattabata yana ambaton sunanta amma nO response ,a gigice yasasu a mota mota ya kaisu asibiti, Nan take suka Shigar da ita Suka fara KokariN ceto rayuwarta.

Ta suma ne due to Postpartum drop in blood pressure, ga Bleeding dinda takeyi, gado aka bata, tareda wasu Allurori, sukayi Stopping jinin dake zuba a kasanta,Suka shiryababy Sukayi admitting dinta a Baby care Unit,Don babyn yayi kankanta dayawa kuma baiyi wani kwari ba.

Ashman yaki motsawa daga inda Aysha take kwantar Da Aeesh, tana maida numfashin wahala a hankali, fuskar nan tayi fayau,zama yayi a gefen gadon ya shafo Sumarta dake baje duk ya hargitse, tausayinta yakeji sosai addua yayi ta jero mata.

"Kinyi kokari Ihty... Sannu Mata tah, Allah yayi miki albarka, yasaka farinciki arayuwarki, kin faranta min, Kin dadada min, kema Allah ya faranta miki fiye da haka, ya ubangijina bazan daina godemakaba da wannan k'yauta dakamin, ya Allah ka karawa matata lafiya ka rabata da Sharrin cutar da take fama dashi".

Hawayen sa ya sauko ya dira a goshin ta, yana zaune anan har aka kira sallah isha'i bayan Ya dawo yaga ta farka sai kuka takeyi, Midwives Sun zagayeta sai rokonta Suke tayi shuru ta rufa musu asiri kada Ashman ya dawo yaga tana kuka.


Suna ganinshi suka tsure, Tun kamin ya tambayesu suka fara bada labari

"kayi hakuri ranka shi da'de bamu muka sata kuka ba, kuka takeyi akan Sai an kawo mata babynta ta shayar da ita..."

Murmushii yayi, yace a kawo Babyn ta bashi abincinshi, tunda aka kai baby Special Baby Unit babybatayi shuru ba ,kallon baby jikinta har rawa yake, tayi positioning babyn ta fara shayardash, idanun Ashman Kyar akansa yana kallon Ikon Allah.

Zama Yayi kusa da ita yana duban Fuskar babyn

"Ihty....babyn na Kama da..."

"Ammah" (mahaifiyar Ashman)

ta rigashi fada

" a'a yafi Kamada Ammah(mahaifin Aeesh)

Ya fada cikin Murmuahin Karfin Hali jin ta Ambaci Sunan Ammah

"Eh...Haka ne,Amma kasan Amma da Abie yan Biyu Kuma kamanninsu Daya..."


Murmushii ya saki
"Kinyi kokari Ihty...., Sannu kinji"

Ta turo baki,

"Na dana Sha Wahala, Wallahi na dauka mutuwa zanyi, har na Fara hango Mala'ikun Rahama,ai da marana ya wani Murda sai gani na nayi cikin fararen kaya INA bankwana da Duniya, Chan na Hango Ahky yana Share hawaye, Ga baby a ciki na yaki fitowa"

Girgiza kai yayi yana murmushi

"Ihty bazaki Mutu yanzu ba ,In Allah ya yarda Sai mun haifi yara da yawa mun Tsufa tare"

"Ta6di kana Nufin Zan sake haihuwa ne bayan wannann?, a'a wallahi Baka San wahalan Da nasha ba, Daukan ciki for 7months ga Nakuda na 37minutes suman 7hours g uban jinin da na zubar, Haba Ahky ka tausaya min Mana,kuma da kake maganar zamu Tsufa tare Sai Kace an Baka List din wadanda zasuga Gobe, harda cewa zan Haifa masa yara Sai Kace bai sakeni ba"

ta karashe maganar a shagwabe tana turo baki

"Idan kika sake cewa na Sakeki Saina fasa bakin nan"

Baki ta turo ta dora knta a kafadarshi ,ta narke masa a jiki.

"Allah ya Sani Ni yanzu bazawara ce"

Ta fada a shagwa6e tana gyara kan Baby dke hannunta tanabashi Abinci.

Ya lumshe ido sanyi na Shigarsa ta ko ina batareda ya tanka ta ba, ya Lura har yanzu bata gama warkewa daga psycho disorder ba.

Kaman An mintsineta ta dago kanta daga kafadarsa

"Ahky nasan Baka snarwa kowa ba ko?"

Guntun murmuahi yana lumshe idanunsa dake cikeda bacci

Taja guntun tsaki

"Mtsww , A haihuwar ma Sai kayi zurfin ciki?,haba zaujee ai ko Ammie ne ka kirata kayimata Barka Koh...?, bani wayata in kirata..."

Ta kasa ƙarasawa saboda kallon daya wulla mata cikin tsakkiyar Idanunta ta kauda kai tana lumshesu tsigar jikinta na tashi, dole ta buɗe bakin tayi Shuru tana turo baki.

Cikin mintunan dabasufi 30 ba aka tagyara maijego da jaririya tsaf, d'akinta na gida aka gyarashi, kaikace ba'a haihu a gidan ba, musamman ya turama'aikatasu gyara gidandukda dare ya fara nisa, Amma a bakin aikinsu ya daukosu sun saba aikin dare ,cikin kankanin Lokaci Gidan ya baje da kamshin turaren kamshi

Har yanzu bai sanarwa kowa ba, kuma ya hana Ta sanardasu sai turo baki take tana Mita, Haka kawai mutumya aihu an hana ya sanarda yanuwa da abokan arziki, ta karfi yake son ya manna matairin halinshi na zurfin ciki

Sai tsaki takeja Ranta a bace, in ka ganta bazakace itace ta haihuba ,bakin nan yaki rufuwa sai surutu takeyi tana Jagwalgwala babyn da zarar yayi kuka sai ta bashi abinci ko gajiya batayi dukda zafin da takeji sosai in tana zuka amma ta Danne, ta jure ita a dole tana so tayi keeping record a haihuwar fari batayi Raki ba ,taki bari a maida baby ,Baby unit a cewarta babynta lafiyanta kalau, Shi kou Ashman Biye mata yayitayi don Shima ya duba yaga Babu abinda ke damun yaron, A ranar haka Suka kusa kwanan zaune Suna jujjuya baby kaman ranar Suka fara ganin Baby, Ashman sai share hawaye yake yana maimaita Kalmar Alhamdulillah.

WasheGari
Dakanshi ya shirya Baby cikin fararen kayan sanyi, sunmasa k'yau sosai sai kamannnin babyn ya ha'de a kallon Farko zakaga yana Kama da maaan Amma idan ka sake kallonshi sai kaga Suna Kama da Aeeah , baby sai barcinta take zubawa hankali kwance, batada wata damuwar data wuce hakan.

Tana ganin Ya shiga ban daki zaiyi wanka ta dauko wayarta, har zata kira Ammie kawai sai taji Kunya a fili ta furta -Ai bai kamata ta faraji a bakina ba ko?-

"Baridai na rafkawa Mara kunyar nan kira"

Nan take ta dannwa Reey kira, bugu daya ta dauka

"Besty kece...?, INA kika shiga?, Sai nemanki mukeyi, Ammie na nemanki tace ki dawo ta yafe mik.."


Sai maganar Ta makale sakamakon jin kukan babyn da taji.

"What Besty...!, ba dai kin haihu ba"

"Ina naga cikin bare na haihuwa, ki kira Ammie ki sanar da ita an samu karuwa, nayi mata takwara....na Shiga uku ga shinan ya fito, kashe wayan, zan kiraki anjima..."

Ta fada jintakunsa yana fitowa Daga ban dakin

Cikeda mamaki Reey tace"karya ne Aeesh ban Yarda ba"

"Tsaya NaN yarinya,wlhy nayi Kashin Baby"


Sai a lokacin Reey takai labari cikin gida.

Aifa kowa yarud'e da murna,Nan danan suka cikaGidan Aash, Ashmn baisan komai ba sai gani yayi suna shigowa,, baby yar dangi, harfad'an wazai d'auka akeyi, Aeesh kou ganin haka Ta hana, tace baza'a jagwalgwla mata diya ba.


Suna tsaka da murnarsu ya Saleem yashigo kaman daga sama babuma Wanda yalura dashi, sai dake zaune hannunta rikeda baby ,taki kwantar dashi.

Zama yayi a gefen gado tabishi da kallo ,babu tsoro ko wani 'darr a Ranta ada in don yana shaye shaye take tsoronshi yanzu itama ta ta6a, idan kuma Dan Ya Taba zama a psychiatric ne, itama psychiatric patient CE babu abinda zai nuna mata, yana Wani yunkuri zata nuna masa nata haukan ba irin tashi bace
.

"My wife...sannu da k'ok'ari kinji? babudai inda kemiki ciwo ko?, Hope baki samu tear ba".

" Wacece your wife din?"

Ta fada cikin zaro ido.

Gyara zamanshi yayi kusada ita, Yasa hannu zai karbi babyn

"Kece mana,my first wife har yanzu kina nan a matsayin matata...."

Kokarin karbar babyn yakeyi ta hanashi, Kalamansa na rannan Suka dawo mata

*_"Ni saleem ba'a kasani a gasa, da ace na bar mashi ke na Gommace na Aureki na ajiyeki a matsayin Hoto, Koda Bazaki Min Amfanin komai ba, na gummace na Sakaki a bola Kodan na ƙuntatawa Maan"_*


*_"Ina ƙaunarki koda baki yarda ba, kuma har yanzu akwai Igiyoyin Auren mu akanki,ba barazana zan miki ba, Na miki tanadin Rayuwa bayan Kin haihu sannan nayiwa Dan Cikin ki tanadin Akasin haka a matsayin hukuncin Aikata fasadi da Aurena"_*

"Yaya Saleem ba sai ka dau babyn ba, don Allah ka tafi ... Ka tafi kafin na Tara maka jamaa"

Ta fada babu tsoro ko shakkarsa a fuskarta,Dubanta yake da mamaki

"Bazan Fita ba, bani babyn"

"ai kou ya zma dole ka fita"

Inji Ashman D shigowarsa kenan, yasa hannu yayi shifting saleem dake zaune kusa da ita har kafadarsu na gogan juna, ya zauna yana Duban fuskar babyn

"Baby...bani babyn, in ya saba da hannu zaiyi kiwiya"

Turo baki Tayi,
"Eh...din yayita Kiwiyan Ai nafi son haka.."

Aunty mami(Kawar Ammie ) CE ta shigo, wani irin kunya CE ta rufe Aeesh, Akunyace ta saukar dakai, Saleem ya mike yana Murmuahin takaici

"Maan kayi nasara, first time in my life da akacini a gasa"

"Ihty tafi karfin ayi competiton da ita ,she's like a gold"

Saleem ya jinjina kai yasa kai ya fice, Anty mami ta girgiza kai tabi bayan Saleem da kallo.


Ashman sai tsokanansa takeyi ta sunkjyar da kai ko tankashi batayi Yasan sarai kunya takeji amma shi ko a jikinsa yak'i fita.


Goggo data shigo da ruwan zafi a flask ta balla masa harara, shima hararar ta yayi yana kauda kai.

" yau na ga taga takaina, iya hararar da kayi ta isheka ko in kawo tsumagiya ka Zane ni?"

Banza yayi mata, yacigaba damun mai jego.

"Ihty idan Wadannan Tarkacen masu zuwa ganin babyn sun lafa zan kaiki wani wuri kinji"

Dubanshitayi da mamaki cikin kunyar da bai gama barinta ba.

"Jego fa nakeyi"

"Eh Haramun ne mai jego ta raka Mijinta wani wuri?"

Girgiza kai tayi ,Goggo da takaicin duniyan ta isheta tace

"Yo karka tankamin d'in mana, ke kuma ja'ira ki bishi, ba Rakiya ba kuje bangon duniya ya sake Dura miki wani cikin , koda yake na nawa kuma?, bayan Wannan ma tun kan kisan da auren ya dura miki, kaiii Amma zamani baiyi ba, don Kunga kuna iskancinku ana maku shuru ko?, Wallahi a namu lokacin ko kinsan da auren namiji akanki sai yayi shekara Baku hadu a gado daya ba"

Murmushii yayi ya Dan langwabar da Kansa kaman mai ciwon wuya

"Ai a Zamanin Ku Lemun tsami yanada Arha ,kyauta ma za'a Baka amma a wannan zamanin Ganin lemun tsami sai rich kid"

dariya ya bama ANTY baby, cikin dariyan take cewa

"Kai Ashman a haka kaman baka maganaAshe kaima A Ne ,zama dakai ne ba'ayi ba?"

"Anty mami haka kawai Tsohuwa zatazo ta zuga min mata?, irinsu ne fa suke kashe aure, yanzu da ace da farkon Auren mu na kawo mata Aeesh ta mata nasiha iron hudubar da zatayi mata kenan?, cewa a lokacin su namiji baya shiga dakin matarsa, haka kawai inaji INA gani yarinya ya kama tsoro na, ina kudi na biya aka bani ita don hak...."

Mintsilinshi Aeesh tayi ganin ya fara sakin layi, ya rike wurin

"Wassh Ta gama dani..."

Murmushii aunty many tayi ta tamik'o hannu zata karbi jaririn tana fad'in

"Kawoshi a masa wanka"

Idanunta suka cicciko da kwalla

"Nidai Wallahi wannan wankan yayi yawa, An mai da asuba fa, Kuma kunsan illar yawan wanka yana tsofar da jariri da wuri"

Tsaki Anty mami taja, ganin babu kara ko kunyar Dan fari a tartare da ita, ta lura bata bari Ashman ya dau yaron ba tunda tazo.

Da kyar ta karbi babyn ahannunta ,tayi mata wanka ta shirya ta, sannan ta mikawa Ashman

Cikin mamai suke kallonyanda Ashman ya rungume da baby yana hawaye, bakinsa dauke da addua, jinnina kai mamy tayi lallai Ashman. Na son Yara,Ashe hanashi 'dansatayi shi kuma bai damu ba Ganin tafi son hakan.

Duk surutun Goggo shuru tayi ta saki baki tana kallonsa.


*MARYAM*

Daga biki akayiaka kara wata daya akan ranar da aka sa ada ,ta rasa ya zatayi da rayuwata, bata son Bamally ga Kuma auren dake kanta da ba'a sani ba, ita ya zatayi da rayuwarta.

Gashi Saleem ya bar zuwa gidansu tun sanda yagano Tana sonshi ya daina wahalar da kansa, yasan dakanta zata zo gareshi ko bajima ko ba Dade, ita kou ta dau ma kanta alkawarin bazata zubar da kanta wajen kiranshi ba, idan yaj za'a daura mata aure nan da sati daya dakanshi zai tako har inda take, ya sanar da daddy akwai aurensa akanta.
_(Thofa 🤔,Zamu gani tsakanin *Quack nurse🐓* da *Nasty doctor* Waza saukar da Girman kai yayi abinda ya kamata?)_ , ta dau damuwan duniyan nan ta dorawa kanta har wani rama tayi kashin wuya ya fito mata.

Ayyan Kou dadi kasheshi An maidoshi wajen Mommy, wani irin kula yake samu Daga gareta dama yan gidan gaba ki daya ya zama Dan gata dukda basu San ya aka samoshi ba, Amma gidan babu yara suna son yara sosai

Sury kuwa hankalinta kwnce buri ya cika, Wani irin soyayya suke shimfidawa da Zeeyk dama chan Suna yi yanzu da buri ya cika sai abin ya karu, dukd yana kan wheelchair ne amma idan kaga yanda yake tarairayanta Abin sai ya baka mamaki, sosai yake samun sauki don Sury bata yarda kuda ya rabeshi ba ballantana ya Shiga damuwa.

Ammie bata Zo ba, kuma bai yarda taje gida jego ba, babu Wanda ya hanashi Don Ammie ma tafi son haka, ana Gobe suna ya dauketa yace aibiti zasu suyiwa baby BCG, Daga nan Zai kaita wani wuri .

9:51 suka FIta,akayiwa baby allura ,suna fitowa instead ya kaisu gida sai ya karya kwana y saukesu a wani wuri,shi ya shiga ya bar ta a mota, gajiya tayi da jira ta fito tana duban mutanen dake kaiwa da dawowa.

"Aisha Muhammad"

Muryar bamalli ya sauka a kunnenta.

A matukar tsorace ta dubeshi, nan take jikinta ya dau rawa.

"Na jima ina jiran wannan Rana da idanu na zasu sakeyin tozali dake, abbana yace ya aura miki wani, da gaske ne?"

Shuru tayi duk ilahirin Jikinta rawa yake

Tsawa ya daka mata

"Answer me and don't dare say Yes"

Idanunsa sun kada sunyi jazur, huci yake fiddawa kaman Wanda ya hadiye transformer, wni irin shaka ya kai Mata yana huci.

Bai ida kai hannunsa wuyanta ba yaji saukan mari a kuncinsa, ji kake tassss.

"How dareyou?, me kake takama dashi?, me ka daukeni?, ni ba yar iska bace ni matar wni ce, House wife inada daraja"

Wasu hawaye masu zafi suka wanke mata fuska

"Kowane Abu mai daraja yana nan a killace ko kuma a rufe ,kudade Nada daraja Duk Wanda ya sameasu baya wulakanta su ,suna banki a killace, idan kou basua cikin bank suna aljihu a boye kuma ba kowa ke iya tabasu ba sai mai su, zinare suna cikin akwati a kulle Mai shi kadai keda ikon tabasu , motoci suna cikin gareji a kulle idan kou basua gareji suna nan an fakasu a inda babu mai tabasu sai mamallakinta ,credentials suna nan a killace maishi kadai keda ikon sarrafata, sai jikina ne zai zamana a bu'de ga Wanda ba muharramina ba? ,Ni matar aure CE mai daraja wacce darajarta ta kere na Dukiya kudi ,zinare ko mota ,na fi karfin na zama mallakinka har abada ,nayi maka Nisan da ko ka hau tsauni bazaka taddani ba......."




Manage please

Not edited


Nayi Gabas🐓🐓🐓
Bintou🚶🚶🚶🚶
*WUƘA A ZUCIYA*
( _BLEEDING HEARTS_ )


*061*


Bai ida kai hannunsa wuyanta ba yaji saukan mari a kuncinsa, ji kake tassss.

"How dareyou?, me kake takama dashi?, me ka daukeni?, ni ba yar iska bace ni matar wni ce, House wife inada

Please Login or Register in order to submit comment