Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

buɗe idanunta ganin Saleem yasa ta kwaɓe fuska sai kuma ta sakar masa kuka, ya zaro ido yana Binta da kallon Mamaki kukan da ta kwana tanayi bai isheta ba?, cikin wata kalar shagwaɓɓiyar murya tace

"Ni ka buɗe Min ƙofa zan koma gida"
Ya ɗage girar sa ɗaya yana Murmushi

"Kowace Amarya Kwana take tana kuka,kema ranar ki ta zagayo, ki tashi kiyi sallah, In kin idar ki daɗa daga inda kika tsaya kar ki fasa, In na dawo zanzo na rarrashe ki"

Daga haka ya fice yana dariya, tabi bayansa da harara sai yanzu tuna abinda tayi, take taji haushin Kanta ya kamata.

Sama ta Haye inda taga ya fito, ta faɗa bathroom tayi Alwala ya dawo Sitting Room ta dau mayafinta tayi rolling sannan tayi sallah.

Tana idarwa ta shiga wanka kafin ya dawo don Jin kanta take kaman Tayi shekara batayi wanka ba.

Tana ciki ya dawo, bai taddata a Sitting room ba,Haurawa sama yayi yayi knocking a kofar ɗakin da ya gani a buɗe, batareda ya jira tayi masa isoba ya bude yashiga bakinshi dauke da sallama


Maryam da Shigan ta kenan taji Alaman sahun mutum ta tsure, tsoro ya higeta.

Hankalin sa a tashe yake ambaton sunanta, amma taƙi amsawa a hankali ya murɗa ƙofar bayin ya zuro kansa ciki,Gabanta ne yafadi ganin mutum tsaye a bakin kofa ya tsareta da idanu.

Kallon ta yake daga ita sai Farar towel da Blue net cap.

Kallon ta yake a hankali yafara takowa gareta, ganin yana takowa yasata dubanshi a tsorace.

Tsaye yayi gabanta yana cigaba da tsareta da idanu, tayi saurin kauda kanta don Kasa jure kallon da yake mata tayi , a hankali jikinta ya fara rawa

Ya zagayo ta bayanta ya tsaya, tareda zura Hannu ya rungumo waist dinta.

Ta ɗago ahankali idanunta suka sarƙe da nasa,ji tayi ta kasa ɗauke nata idanun daga gareshi yayinda wasu abubuwa from no where suke tahowa daga cikin idanunsa suna shiga cikin nata wanda hakan ya haddasa mata mutuwar jiki na daukewan tunani a lokaci guda,take ilahirin jikinta yashiga rawa.

Sake riƙe waist ɗinta yayi sosai da sunkuyowa yana sinshinan wuyarta a hankali,

A hankali ta lumshe idanunta tanajinta tana tanajinta a sama tana yawo

A hankali ya kusanto hancinsa hancinsu na ta6a najuna, tana shaƙar Numfashin da yake saukewa.

Yana kallon idanunta dake lumshe yafara kusanto bakinshi yana a nata,lips ɗinsa na sauka kan nata ta kauda kai a hanzarce tana sauke numfashi.......








Nayi Gabas🦶🏿🦶
Bintou ✍️

7th jan
[1/14, 17:43] Bintou Abdul: Ta ɗago ahankali idanunta suka sarƙe da nasa,ji tayi ta kasa ɗauke nata idanun daga gareshi yayinda wasu abubuwa from no where suke tahowa daga cikin idanunsa suna shiga cikin nata wanda hakan ya haddasa mata mutuwar jiki na daukewan tunani a lokaci guda,take ilahirin jikinta yashiga rawa.

Sake riƙe waist ɗinta yayi sosai da sunkuyowa yana sinshinan wuyarta a hankali,

A hankali ta lumshe idanunta tanajinta tana tanajinta a sama tana yawo

Slowly ya kusanto hancinsa hancinsu na ta6a najuna, tana shaƙar Numfashin da yake saukewa.

Yana kallon idanunta dake lumshe yafara kusanto bakinshi slowly a nata,lips ɗinsa na sauka kan nata ta kauda kai a hanzarce tana sauke numfashi.......

Cont....

Saurin ɗagowa yayi ya ya dubeta still idanunta a lumshe suke, shima lumshe idanunsa yayi, slowly ya zagaye hannayenshi a flat tummy ɗinta yana kwantar da kanshi a wuyanta , yana cigaba da sauke numfashi, Jikinta na rawa ta daura hannunta a hannunsa dake dafe da cikinta yana shafawa a hankali.

Gently ya sauke wet lips ɗin sa a side lips yajasu kadan ahankali sannan ya sakesu, tayi saurin ware idonta a tsorace, ta sake damƙe hannunsa Gam jikinta na rawa.

Jin hannunta a hannunsa ya sake kwance masa Lissafi ji yayi ta janye gaba ki ɗaya karfin jikinsa, a hankali ta Cire hannun nasa daga Jikinta, ta juyo tana Kallon Lumsassun idanunsa, Slowly ta Hura iska a fuskansa ya waresu a hankali.

idanunsa ta kalla ƙirjinta ya buga sbd wani mugun jaa data ga idanunsa yayi bata taɓa ganin idanunsa sunyi irin Wannan jan ba, fuskarsa ma tayi jajurr, cikeda tsoro taja da baya, nufota yayi cikin fitan hayyaci, ta Rintse idanunta da karfi tana ƙoƙarin saita kanta tana girgiza masa kai don babu wani kuzari a tattare da ita.

Sake nufota yayi yana cigaba da sauke numfashi a Hankali, tayi saurin matsawa gefe, ita kadai Tasan Yanayin da yake ciki, kaman yanda Shima ya tsinci kansa a yanayi Mara misaltawa,da kyar ta iya tattaro ragowan karfinta ta ture shi, amma ko gezau baiyi ba, illa ma Sake Matsowa da yayi ya haɗe jikinsa da nata, tayi Saurin Rintse idanunta.

Kallonta yayi ta rufe idanunta gam! A hankali yace

"Please"

tayi masa shiru taƙimotsawa, yace

"Please wifey just once...!"

Still shiru tayi masa taƙi yarda ta kallesa, ta damƙe bakinta gamm yayi ƙasa da murya yana ɗago Fuskar ta yace

"Look at me Wifey.m.."
ƙwace fuskarta tayi ya ƙara kamo fuskarta kamar jira take ta fashe masa da kuka sosai harda Shessheka, kwantar da kanta yayi a kirjinsa yanajin yanda hawayenta ke jiƙa masa ƙirjinsa, shiru yayi Still holding onto her ,muryarsa a sarƙe yace yace

"I a..m sorry... Sorry Bazan sake ba"

kukan ta kawai take rera masa yana patting bayanta a hankali, yana jin yadda jikinta ke rawa, clamly yace

"Ki amince inyi sau ɗaya, sai In maidaki Gida" Ta girgiza kanta sai kuma ta fashewa da kuka tana Sake cusa kanta a ƙirjinsa .

_kaji Saleem Wai mu za'ayi ma Wayau🤔🙄😒_

Saida yaga tayi Shuru sannan ya fice, ta jima a Tsaye tana kuka kaman Wacce kwarto ya titseta, sannan Tayi wanka, ta fito bayan ta leko taga baya dakin, Wasu kaya ta gani ajiye akan Gadon ta, batabi ta kansu ba tana ganin baya nan ta rufe ƙofar sannan Ta dawo ta zauna gaban mirror tanaa mamakin ganin All body creams irin wanda take amfani dasu da turarukanta Kuma komai sabo, Murmushi tayi Sannan Tayi shafe shafenta har yanzu Jikinta bai daina mata wani iri ba.

Kayan da ta gani a kan gado ta duba, abayoyi ne guda Uku different colors, Da Baƙi da brown da maroon, brown din ta dauka, ta yafa mayafin kayan sannan ta sauko kasa don sama ma cikinta abinci saboda yunwar da takeji , a dinning ta gansu shida shida Ayyan Suna karawa.

Kallo daya tayimashi ta dauke kai,saboda kunyar da Taji ya kamata daga shi sai Farar singlet da Nicker , almost half Of his broad chest a waje, suna haɗa ido ta sunkuyar dakai Sai ta Kasa Karasawa inda suke, tayi tsaye, ba yau ta fara ganinshi a haka ba, Amma yau sai taji kunyar haɗa ido dashi , ta juya kaman Munafuka, ta Nufi inda tayi Plugging wayarta a wajen TV ta Cire ta fara daddannawa a hankali.

Jin daddadar ƙamshin Turarenta ya matsota yasa ta ɗaga kai tana kallonsu da mamaki , Saleem da Ayyan ta gani ko wannensu ɗauke da Tray, suka dire a gabanta ɗagowa tayi suka haɗa ido, wani irin kunya ya rufeta da ta tuna yanda ya ganta ɗazu, Tayi saurin Kauda kai tana yaƙe,

"Mummy...Good morning"

Ayyan Ya gaishe ta Yana Dire Yar ƙaramar Tray din hannunsa.

"Morning..."

Ta Amsa a hankali kaman an tilasta mata

"Ni baza'a gaishe ni ba kenan"

Inji Saleem Yana Sauke nasa Tray a gabanta ta harareshi.

"Ki harareni Da kyau in na Tashi ramawa Yarinya bazata ji da dadi ba"..

Shuru tayi masa batareda ta sake kallonShi ba, ta maida Hankalinta akan wayarta, Saida ya Gama haɗa mata komai ta turo gabanta.

"Here is ur food ranki ya daɗe"..

Murmushi ta saki, jin yanda yayi Magana

"Thank You".

Ta furta ciki Ciki kanta a kan wayarta, ganin da gsk Kunyar sa na neman hanata cin abincin yasa ya tashi ya fita, Shikou Ayyan zama yayi yana shan Coffee ɗinsa, Yana gamawa ya Dire cup din Yana kallonta, hararar sa tayi..

"What...!"

" Aunty saleemah came ,she just left"

Da mamaki take kallonshi ya cigaba.

"She bought some stuffs in a bag"

Maryam ta taɓe Baki ,duk yanda akayi Salem Kawota amma ta rasa dalilan da zaisa tazo har ta koma bai gaya mata ba, gyara zama tayi taci abincin sosai ,saida ta ƙoshi sannan Ta tattara kwanonin ta shiga kitchen dasu ta wanke sannan Ta jejjerasu a ma'adanarsu.

Tanta ta ɗaga bayan ta fito suka haɗa idanu ,har yayi wanka ya fito yana sanye cikin wata Armless da wando dark blue iya gwiwa, hannunsu ɗaya cikin aljihunsa ɗaya kuma Wayarsa ce yana amsa Waya, sai ƙamshi yake ,zama yayi kan 3seater Fuskarsa a murtuƙe, Ayyan na zaune yana Game da wayarta.

"Wifey ki Shirya Zaki Rakani wani Wuri"

kallonShi kawai take da Alama wayar da yayi ne ya bata masa Rai, lamarin Saleem ya fara bata Tsoro , kwanakin Baya Ya zama trend a media sai yaɗawa akeyi ana nemanshi, Amma yau gashi gata ya daukota a kasuwa ,ita bata taba ganin inda aka dauko Amarya daga kasuwa ba.

Cikin kankanin lokaci suka shirya suka fita,Kai tsaye gidan Abba ya kaisu , Haka kawai ta tsinci kanta da jin Kunyar shiga gidan don haka kanta a ƙasa ta Shiga.

Part din Abba Suka nufa,A parlorn Abba yaja ya tsaya yana Ƙwala masa kira.

Da fara'a Abba Ya fito ya tarbesu da Murna nan take a ka fara jera masu abinci akan Dinning Kaman An San d zuwansu, zama Sukayi Suna hira Maryam Ta cika da Mamakin yanda Abba da Saleem ke hira cikin wasa da dariya kaman abokai, duban Abba Saleem yayi now looking serious yace

"Dad where is inna Yattai?, Where is my mom?, Meyasa ka raba mu ?, Meyasa Ka bari nake wulakanta ta bayan kasan Ita ta haifeni?"

Jikin Abba a sanyaye yayi tapping kafadar sa

"Kayi haƙuri son.....It's not my fault, ni kaina bansan dalilin da yasa na amince da haka ba, i just found myself doing it”

Saleem yace

"Now Where's my Mom "

"Zaka ganta But, until I Complete the missing puzzle"

Abba ya faɗa yana Zaro wayansa, ya dannawa family emergency meeting.


*Ashman*

Kasa gane kan Aeeesh yayi, ya dauka abin nata wasa ne, Har Barci ya ɗauke ta ya tasheta ya Bita a hankali Amma sam taƙi amincewa dashi, abin har tsoro ya bashi dayaga ta sa masa Kuka, dole ya ƙyaleta ada yayi mata Uzuri ne Saboda Jegon da takeyi amma yanzu ta Kammala Bazai ya kamata ya gano inda matsalar take don Bazai yiwu su cigaba da zama a haka ba, zai cutu dayawa, zai komawa Deejah dukda bayajin zai iya Bata kulawan da ya Dace, Amma bayajin zai Iya cigaba da zama a haka yana shan lemon Tea akoda yaushe Bayan ga matan sa har biyu kowacce da lafiyarta.

Sosai Yaji bacci ya ɗauke a idonsa, ya tashi yayi Alwala ya dawo ya shimfida Sallaya yana kai kukansa ga Allah yana nan kan darduma har huɗu, kukan Aerah ya tashi Aeesh, ta daukota tana shayar da ita, Tana kallonShi yana Sallah yana Sallamewa, jikinta yayi sanyi, sai taji bata kyauta ba, Tana zaune for more than 30mis kafin Aeerah tayi Barci, ta kwantar da ita, haka nan Taji baccin ya ƙaurace ma Idonta, ta Shiga Bathroom ta dauro Alwala sannan Tazo bayanshi ta shinfiɗa Sallaya ta fara Binshi yanayi yana Sallamewa har karfe Biyar lokacin har an fara kiran asslatu, tuni Aeesh ta ɓingire a darduma, chak ya ɗauke ta Kaman yar tsana ya maidata Kan Gadon, ya zare mata Hijabin dake Jikinta, ya mike zai tafi ta riƙo hannunsa, ya dawo ya zauna da fadin..

"Ihty kin farka?"

Ta murmusa tana Kallon Fuskarsa,

"Ki kwanta bari nayi wanka..."

Ya faɗa yana ƙoƙarin zame hannunsa dake cikin nata amma ta riƙe gam.

"فقط ابقى هنا" _faqat aibqaa huna _(kawai ka zauna anan)_

Tayi maganar a shagwabe

Yayi shuru yana Kallon ta, ita ma shi take kallo da kwantattun hawaye a idanunta, ta sake damƙe hannunsa Sosai

"Let's Go with me falling asleep as I hold ur My hand like this"

Kallonta yakeyi , physical appearance ɗinta ya koma na asalin Aeesh ɗin da ya sani a baya mai tsoron nisantansa da ita, wacce take like dashi a koda yaushe, Sai yaji kaman Ba ita bace Aeesh dinda aka kawo masa ɗazu ba, kaman Ba ita ke gudun sa ba, A haka bacci ya ɗauke ta, hannunta cikin nasa, Ko Minti goma ba'ayi ba aka fara Kiraye kirayen Sallahr Asbh, Ya zare hannunsa a hankali ya faɗa Ban daki Yayi wanka sannan Ya sake Alwala, ya nufi masallaci bayan Ya sake tashin ta sannan Ya nufi masallaci, yana dawowa kai tsaye ɗakin Goggo ya nufa, ya gaishe ta sannan Ya leka dakin Deejah tana zaune Tsakiyan Gado da Alama ko Sallah batayi ba, idanun nan nata Sun Kumbura sunyi jazur kaman garwashi a karo na farko da yaji tausayinta har cikin ransa , ya tabbata tanajin kwatankwacin abinda yakeji akan Aeesh, Zama yayi a kan gadon Ya shiga rarrashinta cikeda tausayinta, mamaki ya kamata Yau Ashman Da kansa yake rarrashinta? ,Don haka bai sha wahala ba ta daina fushin ta faɗa toilet tayi Alwala, Yana zaune har tayi Sallah ta idar yana zaune bai motsa ba, har tayi wanka still bai motsa Daga inda yake ba, ta buɗe wardrobe ta ciro Kaya Zata saka , ta juyo ta dubeshi Idanunsa kyar akanta

"Zan saka kaya"

"Okay.... "

Ya furta a hankali Yana gyad'a kai tare da lunshe idanunsa, girgiza kai tayi kawai aranta tace

_kaje chan ta motso jarabar kenan_ , ilai kuwa sai taji ya riƙota tare da kawo bakinsa bisa labbanta , ta ture shi da sauri tana ƙoƙarin Rike towel ɗin ta da yake shirin zamewa, idanun Ashman sun rufe ya manta da wa yake tare da Ƙarfi yake son ya biya buƙatar sa, ita kou ta hana, sai kuka takeyi, ringing din wayarsa ya dawo dashi Cikin hayyacinsa,ya koma gefe yana Sauke numfashi, wani kiran ya sake shigowa, dubawa yayi yaga Abba ne, kaman bazai ɗaga ba, saida ya kusan Katsewa sannan Ya ɗauka ya kara A kunne yana fidda numfashi kaman mai Athma.

Shuru yayi ya kasa cewa komai, cikin 15secs ya Tattaro nutsuwansa, ya gaida Abba da dishasshen Muryarsa wanda ta koma tamkar na mai mura

"Assalamu Alaikum Sir"

Banji me abban ya faɗa ba, amma da alama amsa sallamar yayi,

"Ina kwana"

"Dad yanzu yanzun nan Kuma?...."


"Okay Gamu nan Zuwa....sai munzo"

Daga nan Ya sauke wayan, ko kallon Deejah da ta kife Kanta a katifa tana kuka baiyi ba, ya fice abinsa yana mai jin Haushin Kansa .

Zaune ya iske Aeesh a Sitting Room,ta kunna System ɗin sa tana Kallo, hannunta riƙe da Tea mug tana sipping a hankali, tana sanyeda blue skinny jean da Maroon loose top sai gashinta dake dunƙule cikin blue cap , Kallo ɗaya yayi mata ya kauda kai yana haɗiyan dunƙulallen yawun da ya tokare Masa Maƙoshi ,batareda ya sake kallon inda take ba yace

"Ki Shirya Abba na neman Mu"


"Ahky Ga Breakfast Nan a dinning fa"

Bai tanka ta ba yayi Shigewan sa, yana mamakin yaushe tayi hankalin shirya karin Kumallo da Sanyin Sassafe?.

Cikin 20mins ta shirya cikin Lifaya Royal Blue Wanda Ashraf ya siyo masu itada Sureey ya kawo msu lastweek, jikin kayan Sai walƙiyan Diamond Stones yakeyi Wanda hakan Ya isa ya tabbatar da Tsadar sa ,ɗakin Goggo ta nufa har tayi ma Aeerah wanka , ta zauna tayi tana Kallon yanda Goggo ke Shirya ta har ta Gama, suka Fito, suka jira shi a Motar sa ya fito daga Part din Deejah, sanye cikin English Jampa Navy Blue A jikin ƙofar inner pocket ɗinsa wani silver chain ne, sai walƙiya yake.

Yana fitowa yajasu suka bar gidan, sun tarar da Family Gaba ɗaya suna hira cikin raha da dariya banda Saleem da kanshi ke ƙasa ya kagara a Gama haduwa Abba ya amsa masa tambayansa ,ga abubuwan motsa baki baje ta ko ina sai tauna ake ana fira cikin raha da dariya, Maryam Kou jin ta tayi not comfortable ,ganin Ita kadaice bare a cikinsu, Naseer sai Tsokanar ta yake tana Murmushi.

Da zarar tayi Murmushi ta ɗago sai Su haɗa ido da Saleem sai ta Harareshi ta cigaba da biyema Naseer ,Ayyan Yana wajen Hafsah tana mai wasa Duk ya bi ya bata mata jiki da milka.

Shigowanta Maaan da Aeesh ne yasa Duk suka maida hankalinsu akansu, Saleem Ji yayi gabansa yayi Mummunar faduwa da yayi Ido biyu da Aeesh yaga yanda ta koma kyawun da ya hango a ranar da ya fara ganinta ya sake fitowa Sosai, Ga wani kwarjini da tayi masa ta cika masa ido Kaman ba A'ishan Da ya sani mara wayau ba, yanzu da yayi hakuri bai sake ta ba da har yanzu tana nan a matsayin matarsa fa🤔.

Tunawa yayi da Rigimatu Matarsa Maryam, ya juyo ya kalleta Itama shi take kallo, ta taɓe baki ya sosa keyarsa yana Ɗage mata Gira ɗaya.

Shima Abbba Binta da kallo yake yana kallon yanda take wani liƙema Ashman kaman hand bag ,yanajin yanda Zuciyarsa ke tafarfasa kaman zata fashe bazai iya ayyana iya adadin kaunar Da Yake yi wa Aeesh ba, yana mata Sonda zai iyayin komai akanta.

Ammie ma ta shigo itada Sureey ,jiya kwanan zaune sukayi, surayya babu lafiya , yanzu ma daga asibiti suke an Mata gwaji an Gano tanada juna biyu😌, a hanyarsu ta dawowa Abba Ya kira ta ya sanar da ita neman Da yake mata a gaggauce, shiyasa Suka garzayo kansu tsaye.


Batareda bata lokaci ba,Aka fara gabatar da abinda ya tarasu, Ashman ya buɗe taro da Addu'a, Ashraf ya ɗora da nasa.

Abba ya dube Saleem da Idanunsa ke kansa baya ko kyaftawa, sannan Ya juya ya dube Baffa, da inna Saude Suma shi suke kallo, Ya kuma kallon Maryam Wacce kanta ke duke ya maida Dubansa kan Ammie wacce ta matsu taji me ya tarasu?.


Abba yayi gyaran murya cikin Jimami yafara bada labarin asalin Ammie ,da alaƙar dake tsakanin Su Saleem da Inna Yathai wanda shi kansa baisan Dalilin da yasa ya biyewa Inna Saude Suka ɓata Rayuwar ya'yan sa ba, bai 6oyemasu komaiba har aikin da Inna Yathai tayi a gidan domin kare martabar ƴaƴan ta"

Ya gyara zama yace

"A shekarun baya, Ashman Da Saleem sun kasance yan uwanda ba'ajin kansu, dukda rabasun da akayi but blood is thicker than water, kwatsam lokaci ɗaya gaba mai Tsanani ya shiga tsakaninsu wanda a duk iya binciken mu a lokacin muka kasa gano Silar hakan, abinda ya faru shine A ranar 11 da watan January 2005 munyi wani babban Rashi wanda ya Girgiza dangi gaba ɗaya , a ranar da Hassan ya rasa rayuwarsa kuma duniya ta shaida mutuwar matata hussaina, ta dalilin Gobarar da akayi a gidana, A ranar da suka dawo daga aikin Hajji na sauke su a gidana, na shiga sashen Hamza domin na shaida masa Isowarsu kafin na dawo naga Wuta ya ci sashena gaba daya, da kyar aka iya banbaro gawar Hassan yayinda gawar Yathai ta Zamo Toka da kyar aka iya Banbance Kasusuwan ta, Akayi mata sutura Aka Kaita makwancinta, Amma ba haka lamarin yake ba, Yathai ta kuɓuta, a lokacin da wuta ya fara cin gidan ta gudu, tana fita mota ya kaɓeta, wanda ya kaɓeta ya Kaita asibiti"

Shiru falon ya dauka, mammaki ne sosai yacika mutane suna al'ajabin wannan lamarin mai Kanada almara, Ammie da nata labarin yafi girgiza ta kasa motsi tayi

Abba ya cigaba da cewa

"Ashe asibitina aka Kawota, nine na dauki nauyin Aikin da aka yi mata, kasancewar Kanta ya bugu sosai kuma zata iya missing memory ɗinta idan ba'a yi mata aikin Gaggawa ba ,akayi reffering ɗinta zuwa Egypt inda akayi mata aiki,Bayan anyi aikin ta kamu da Amnesia Amma temporary Memory loss, ban gayawa kowa ba har ta samu Sauki , ta fara gane Ni, amma sai ta nuna bata son dawowa ƙasar don bazata Jure ganin Yaranta suna amsa Wata a matsayin uwa ba, Ni kaina bana Son ta koma gidan don Tausayinta nake ji, idan Suna tareda matata Saudat bana iya kwatanta adalci a tsakanin su"

Ashman dayaji kalaman abban nasa kaman shafa labari yace

"Abba Saleem ne ya Kashe Amma, da kunne na Naji ana bashi Umurni"

Ya karashe maganar da Rike kansa dake barazanar Tarwatsewa,

"Sufyaan....!, Saleem bai Kasheta ba, abinda ka gani daban Abinda Ya faru daban...."

Dubansa yakai Kan Maryam, ya kirata a hankali, Ahankali tad'an dago idanu ta saci kallon Saleem taga kanshi na akasa don tunda akafara maganar yaji Jikinsa yayi sanyi, a hankali ta amsa da Na'am ya cigaba da cewa.

"Kiyi hakuri akan Abinda Hamza yasa Akayiwa mahaifiyar ki, Dukda Nasan Haƙuri bazai Wadatar ba"

Sauke idanunta tayi ahankali Hawaye suka sauko saman Fuskarta, Meye hadin Ummanta da Wannan Maganar?"

Dubansa ya kai Kan Ashman

"A ranar da akayi Sadakan uku , Kaga Wani video a dakina..., asalin videon Bani bane, Hamza ne, Asalin Videon da ya dora a media, Wanda na fyaden da yayiwa fatee (umman Su Maryam) ne , shine ya Sauya Fuskarsa Ya maye gurbin shi da nawa, Ya kuma maida fuskar fatee Da na Ammie, ta yanda babu wanda zai Gane editing akayi, Wanda ya kalli Videon zai ɗauka nine nayiwa Ammie fyaden Amma Sam banida alaƙa da hakan, da wannan Ya rinƙa amfani da wannan Videon Yana min barazana Ina bashi dama Yana debo ma'aikatansa Yayita jibgasu a Renar clinic din asibitina Suna satar kidney din patient, su maye masu gurbin shi da mara kyau, ina ganin komai amma na kasa cewa komai saboda an rufe min baki, Videon Ne Ashman ya gani ya ke haramtawa kansa Aeesh, Nima saboda Ina sonta sai nayita amfani da wannan damar wajen cusa masa takaici don Yaji tsaneta yabarni na aureta"

Yana kaiwa nan ya sauke ajiyan zuciya yana kallon Ashman Da kansa ke sunkuye

"Son...Am sorry for maltreating you, sorry for putting you through pain nasan Na cuceku gaba ɗaya na rabaku da Mahaifiyar ku,a. Yanzu a gaban kowa ina mai tabbatar maku da cewa Ashman Da Ashraf yan biyu ne , haka Saleem da Naseer duk uwarsu ɗaya , ku gafarceni da na zama silar da hakan Ya zama labari a wajen ku"

Kusan a tare Ashman Da Ashraf suka ɗago suka dubi juna, Sun san Saleem da Naseer ba ya ƴan inna Saude bane ,Amma they were shock dajin Su yan biyu ne, dukda sun jima suna zargin Hakan duba da kamanninsu da kuma halayyan su da yazo daya! ,Kenan Inna Saude batada Ɗa namiji ko daya?.

Baffa da Inna Saude ciki sunyi zuru zuru sun hada zufa sun Gama jikewa da zufa, kowannen su baiyi Makircinsa da Ido buɗe ba Saida yaje wajen Malam aka Rufe bakin kowa suna Gani Amma babu wanda ya isa yayi magana,a halin yanzu da Abba ya fidda Abinda ke Cikin sa,sun tabbata kashin su ya bushe don da Alama akwai abinda shirya kafin ya tarasu m.

Godiya Sosai Abba yayi ma Maryam Don ta sanadin Shigowar ta rayuwarsu Abubuwan dake rufe suka fara budewa, a lokacin da tayi aiki a asibitin Saleem Ta Gano Abinda Baffa ke aikatawa a Renal Unit, ta tattara Hujjoji akansa, Amma Rashin Samun Hadinkan Hukuma yasa maganar taso tasha Ruwa, Sannan Auren Saleem da tayi a watanni ukun farko ta Gano kwantaccen Asirin da saude keyi ta karyasu batareda Tasan na meye bane.

"Abba yanzu ina Amma take?, Tana raye har yanzu?"

Hafsah ta tambaya tana share ƙwallah

"Kwarai Kuwa ,bata buƙaci nasan inda take ba , amma kuma babu yanda banyi da ita tazo ba amma Taƙi zuwa tace ta bar......"


"Assalamu Alaikum....."


Shigowar Wata kyakkyawar Dattijuwar mace ce, ya katse shi tana sanye Cikin shiga ta alfarma,kallo ɗaya zaka mata ka hango kamannin Saleem da Aash a tattare da ita.

Zumbur Suka miƙe a tare suna kallonta, duk Wanda yasanta 18yrs back babu Abinda zai hanashi Ganeta a yanzu bata chanza a komai ba,illa wani fresh and young da tayi alamar hutu da kwanciyar Hankali.

Kallonta Saleem yakeyi duk ilahirin Jikinsa Rawa yake ,Matar nan ce Mahaifiyar sa?, Matarda yasha Kallonta ido da Ido yace ya tsaneta?, Matarda tasa ya Tsani mata ta dalilin Haƙuri da wahalar da takeyi akan Mahaifinsu?, Itace ta chanza fuska ta sadaukar da Rayuwar ta ,ta zama yar aikinsa Don ta kare Shi daga sharrin Maƙiya?

Sake yin ƙasa yayi dakai yana jin wani matsanancin kunya da Haushin Kansa, Tsana da takaicin kansa Suka tarun masa, jiyake kamar ya ruga aguje yabar gidan don Kunya

Abba ya karya kai yana duban sa

"Saleem....!, Ga Mahaifiyar ka...!, Hope I have solve the missing Puzzle?"

Kasa dagowa Saleem yayi

A hankali inna Yattai ta karaso Cikin Dakin tana binsu da kallo daya bayan ɗaya, ta samu wuri ta zauna kusa da

Please Login or Register in order to submit comment