Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a hannunshi yana sakin Murmushi, Aeesh yar rigima, Muryar Deejah yaji kaman Daga sama tana cewa

"Dawa Kake waya?"

Ɗago fuskarshi yayi ya dubeta baki sake

Saida yaja 10secs Sannan ya Kauda Dubansa daga Gareta Cikeda Salon cusa mata Takaici yace

"Da Ihty"

"Amma Dai Kasan baka kyauta ba ko, Kasan Hakan bai dace ba , A matsayin ka na Mijin Aure Furta wadannan Kalaman ga Ƙanwarka bai kamata ba ...."

"Na sani Amma ina Ruwan ki?, Kema fa Albarkacin ta kikeci?"

Take bakin Ciki ya kamata, a ranta tace
_Wai Wannan Albarkacin Aeessh din wata tsiya ce?, Da Anyi Magana Sai yace Albarkacinta nake ci, kuma Akanta yake Azabar dani!, ina Albarka a abinda babu Riba?_

"Amma Dai Kasan Ba mutuncin Ka bane , a matsayin ka na babba Bai kamata ajika kana Wadannan Maganganun da yarinya Ba"

"Na lura kaman Kishinta kike, Aikam Idan kishi zakiyi da ita ki shirya tun yanzu don ita din Kishiyar ki ce kuma uwarGida, Kibita a sannu...!, She own This house"

Deejah jitayi Tamkar ya watsa Mata Ruwan zafi, tace

"Nasan inshaAllahu A'isha Bazata taɓa zama Kishiyata ba, macen da ta *HARAMTA A GAREKA?, A GABAN DUKKA FAMILY KA FURTA WANNAN KALMAR, SO NASAN KO BAYAN RAINA BATA ISA TA ZAMA KISHIYATA BA* "

Yayi shiru maganar tana sinking a rashi, da Deejah tasan yanda yakeji idan An Taɓo masa Magana makamancin Wannan Da bata yi yunƙurin tadata ba.

Lokaci daya Yaji jikinshi yayi Weak, Ya sauko daga Kan Gadon , ya fice daga Dakin Gabaki daya, batareda ya ce da ita komai ba.

Ayau Yayi Niyyar bata Abinda Take nema Wata da watanni,ko don Darajan furfuran Tsohonta da Kuma Tsoron Halin da zata Iya Shiga ta sanadin Hakan.

Amma ta ɓata komai, tasashi jin kamar itace ta haramta a gareshi, koda ya koma dakinshi, Alwala Ya doro, ya fara Gudanar da Salloli yana yi Yana Sallamewa Tareda Rokon Allah ya kawo masa Sauƙi cikin Lamarin shi, Kuma ya Kwato Masa Hakkinshi akan Masu don madashi Mahaukacin Dole......

AEESH

Tana Jin ya katse wayar ta share Hawayenta ta koma ciki, ta maida wayar Inda Ta dauko, Ta zauna a ƙasa Gefen Side din Reey Sannan Ta kwantar da kanta a tafin Hannunta.

Ada tayi tunanin Reey ce matsalar ta, daga Ƙarshe kuma ta gano Itace maganin Matsalar ta,daga Lokacin da Ammie ta kwanta Rashin Lafiya ita kadai take Rayuwa ,babu yaya, babu ƙani babu Uwa , babu Uba Amma a kwanakin da sukayi a makaranta tare, Taji tanada Yaya At the same time Reey ta zame mata Uwa da kuma Ƙanwa, yanzu Kuma Da ta fahimce ta sai taji ta zame mata Family 💕

A hankali tayita share hawayenta Har bacci ya dauke ta, da Asuba ta tashi Domin Yin Sallah kaman Yanda ta saba.

Ganinta a zaune a ƙasa Yasata jin babu daɗi, Tashinta tayi tace ta Koma kan Gadonta Gudun karta kamu da ciwon Sanyi, Sanyin Ƙasa Yanada Illa sosai A jikin mace.

Kuka ta fashe mata dashi wai ita a dole Gadon ta zata kwana, Dukda a dokar makarantar ba'a kwana a gado mutum Biyu, in Kuma an kama Mutum Hukuncin Korace a gareshi.

Amma babu Yanda ta iya,ganin She's Weak Dole ta bari Ta kwana a Gadonta....

*Dr Umar*

Safa da marwa yayi tayi a tsakar falon bayan Fitan Ashman, hannuwanshi goye a bayanshi.

Kallo daya zaka yimashi kasan yana cikin Tsananin damuwa.

Da yasan Ashman ba son diyarshi yake ba, da Bazai bashi Aurenta ba, da yasan Irin Cin Mutuncin nan ya Shirya Mata da Baiyi kwadayin Hadasu ba.

Deejah ita kadai ce Ɗiyarsa Mace, Shiyasa Ya Dora Mata Son Duniyar nan akanta, Bata taɓa neman Wani abu ta rasa ba, idan ta nuna tana Son Abu ,duk Wahalar da zaisha wajen nemo wannan Abin sai yabi ya samo Mata shi,ko Duk duniyar nan zasu haɗu su Tsine masa bayan ya sama mata abin bazai damu na indai zata yi FarinCiki to fa Shikenan ran kowa ma ya ɓaci, he don't care ,akanta ya saki mahaifiyar ta saboda Yawan Mitan da Takeyi Akan Ɓata tan da yakeyi.

Kwanciyar hankalinta shine nashi, haka Tashin hankalinta rashin Nutsuwanshi, da kanta ta Tunkareshi da batun Auren Ashman ,Kasantuwar Abba Abokinsa Ne yasa baisha wahalar Sama mata Ashman Cikin Sauƙi ba.

Kalaman da Ashman Yayi masa Lokacin Da yazo masa da gargadin ya kula masa da ita sai fado Masa a rai Yake, Sai yanzu ya fahimci inda kalaman nasa suka nufa.

*_Insha allahu zan kokarta, domin Mahimmanci Wacce ta Hadani Da ita a gareni, kasan Da Wayau ake farauto mara wayau, a rayuwa, insha allahu tunda Kunyi Naku nima zan Kokarta inyi nawa , badan komaiba sai dan farauto Nasara ta gaske na dawo da ita Hanya, Kuma babu Abinda nake bukata daga Gareku, babu Abinda Kudin ku zai Amfanar Min,Idan da gaske mutuncin Diyarku shi yasa Kuka Matso da Auren Me zaisa Ku haɗa Da kudi?, A cewar Ku Kuɗi shine Matsayi ko mutunci?_*

Tabbas yayi kuskure da bai fahimci maganar tun farko ba, tabbas kalaman na nufin tunda Sunyi son ransu, Shima Zaiyi nasa son Ran bayan An aura masa ita, Gashi kuwa ya fara Gani.

Washegari Ya kira Abba ya sanar dashi Abinda ke faruwa , ya kara da cewa Idan Bazai iya riƙeta ba Ya sako Masa Ita, Shi ba gagara Riƙeta yayi ba, Sonda take masa ne Yasashi damƙa masa ita.

Ko kadan Abba baya Son Wata tangarɗar da zata billo a wannan Auren, yafiso Ashman Yayi ta zama da ita haka har ƙarshen Rayuwar su.

Don Haka da Kansa Yaje har Gidanshi ya ciccimasa mutunci, ta inda yake shiga ba tanan Yake fita ba, kan Ashman na Ƙasa baice dashi Uffan ba har ya ƙare masifarsa ya fice, anan Inda akayi masa faɗar anan Ya watsar da batun ,ya cigaba da sabgogin Gabanshi hankali Kwance .

_Illar Auren Dole kenan , Gara ma mace tanada Rauni koda an aura mata wanda bata so ana nan idan ta haihu Kiyayyar zata iya jurewa ta zama soyayya ko dan Ɗan da ta haifa mai, Amma Namiji Tankwara ra'ayinshi akan Mace wannan ba ƙaramin Aiki bane, idan anyi Auren ma Ita Zatayi tashan Wahala barin Ma in ita ke Sonshi shi baya Sonta_

*Pollokshields*
_GLASGOW United kingdom_

Tilon ƙanwar ZEEYK Babu Lafiya busy yake, Sai tattara kayanshi yake zai Koma NIGERIA.

Shiri yake yi sosai Sureey na zaune a gefe tana Kallonshi ta Zabga Uban Tagumi Idanunta sun Kawo Ruwa kaman Zatayi kuka.

Juyowa yayi ya dubeta , Ganinta a Raunane yasa yaji jikinsa yayi Sanyi, tahowa yayi Gareta Ya zauna Kusa da ita yana Fuskantarta ,kawai sai ta Rungume shi ta fashe da kuka

A hankali ya Rabata da Jikinsa yasa hannu ya share mata hawaye

“meyasa Kike kuka”

Turo baki tayi, hawaye suka sake Zubo mata

"Ina sonka da yawa"

Dif duka nepar jikinshi ta dauke ya tsaya sororo yana Kallonta, Tabbas Idanunta kadai ya isa Ya bayyana soyayyar gaskiya da take Masa.

"I'm mad at you , Zaka tafi ka Barni"

Muryarta Ta saki Dokan Dodon Kunnensa.

Lumshe Idanu yayi ya sauke ajiyar zuciya yace

"Kina fushi dani ,to Ki bini mu tafi tare mana!"

"No Bazan iya ba, idan Dad ya gano Kasheni Zaiyi, Please idan ka tafi ka rinƙa tunawa Dani Every Beat of your heart kasa cewa Ni kadai ce a cikinta"

Ta kasa riƙe Hawayen ta ta rintse Idanu hawaye suka wanke mata fuska, Murmushin yaƙe yayi shima yaji kamar yayi kukan ko zai samu sassaucin Abinda ke damunshi, cikin zolaya yace

"Madam Kowa nada nashi Zuciyar Ae, ki ɓuya a naki nima zan ɓoye kaina a nawa"

"Haka ma zaka ce ko?,Bana cikin zuciyarka sai kace baka sona?"

"Ina Sonki Mana ,Amma I don't feel comfortable keeping u in my Heart, Gani Nayi kaman zuciya Batada ma'adani mai kyau, idan abin baƙin ciki ya sameni sai ya soki Zuciyata sannnan Raina Ya ɓaci, Amma idan na Ajiyeki a raina kinga babu Mai ɓata Min rai, ya taɓaki idan Kuma an taɓa raina Mutuwa zanyi ✨, i'll keep u in my soul, daga Yanzu Zuwa Last Breath ɗina I promise to be your soul mate"

Yayi Murmushi ya shafa fuskarta

"ni da ke soul din mu daya, gangar jiki ce kawai daban, so the hidden fact is u were born the day I was born, jikin ne dai sai daga baya aka haifi naki. There is a strong Cardiac Connection between us spiritually"

Sureey tace "what kind of Cardiac Connection?, Endo cardium, Myocardial Or epicardium?"

Ya dan bata fuska yana kallonta Cikin zolaya yace

"Wanne ne yake Pumping Blood dinda Ke yawo a cikin Jikin Mutum?"

Dariya tayi sosai tace "muda muke rai daya ai Kamata yayi Jinin jikin mu da Zuciyoyin Duk a haɗe suke"

Tsokanarta ya cigaba dayi har ya Samu ya haɗa Kayan, Saida Ya dau jakarsa Zai fita ta farga, Nan fa hawaye Suka kasa Tsayawa nan ma Da kyar ya lallasheta ta rakashi Airport, Nan fa Akeyinshi Rungume shi tayi tana kuka kamar bazasu sake haɗuwa ba, Daƙyar ya samu ta sakeshi ,kalamanta na Ƙarshe a gare shi sune

"Baby Don Allah Karka manta da Maguninka,samun Lafiyar ka shine namu”

Yana Shiga Jirgi ya kira ta video call, sun Jima sosai Suna hira kamar bazasu rabu ba, Har barci ya daukeshi ,itama a haka bacci ya D'auketa kiran sallah ne ya farkar da ita, Bayan ta dawo suka Dasa daga inda Suka tsaya, lOKACIN shan Maganinshi nayi ta tuna masa , a Gabanshi tasha, Sai a lokacin hankalinta ya kwanta.

Ƙarfe 6:30 na yamma Girginsu yayi landing a Nigeria .

Kai tsaye Gidansu ya nufa , Bayan ya gama Kimtsawa Abbansa Ya hadashi da Jami'ai suka Rakashi asibiti.

Maryam na Ganinshi tahau murnar Ganinshi, Rabon da ta ganshi Tun shekaru Biyar da suka gabata.

Rungumeshi tayi sosai, har da kwallar murna a idonta.

Sai da suka gama murnar ganin juna sannan suka Fara maganar Main Abinda Ya kawoshi ƙasar wato Hujjojin da tace ta tarkato masa, juya harshe sukayi zuwa fulatanci saboda Su mama da wasu tsirarun Yan uwa na ɗakin kuma wannan sirri ne da ya danganci rayuwarsu, gaskiya ta gaya masa cewa Hujjojin na cikin wayarta, Amma tunda aka harbeta aka ƙwace bata sake Ganin Mai kamarshi ba.

Ji yayi haushi kamar ya kashe shi,kuma wai Shekara Daya kenan Da bata aikin maimakon Tayi Saving Komai a system ɗinta sai ta barsu Cikin wayar ta, ji yayi kaman Ya kikkifeta da mari cikin Fushi yace

"Then Ya zama Dole ki Shiga Family ɗin Don Nemo mana Kwararan Evidence"

"What did You Mean?"
Ta Fada da Yaren nasara

"Ina nufin Dole Ki zama Part of Them,ta Yanda Zaki n....."

"Wait Yaya har yanzu fa baka Fahimtar dani yanda zan gane ba"

Ta dakatar dashi da Harshen Fullatanci

Ɗago Jajayen idanunsa yayi ya saukeshi Akanta

"Ina Nufin Ya zama Dole ki ƙulla wata Alaƙar da zata Kasance kinada Wani matsayi a gidan ,don Haka ya zama Dole ki Auri daya daga cikin 'ya'yan Dr Khamees Shettima ko Kuma barr Hamza Shettima"


Cikin Fushi tace

"AM sorry Yaya Bazan iya ba"

Shima Cikin Nashi fushin yace

"Then go....!, go to hell Ni Zanje Inyi dakaina...!, I'll look for a way to be their driver , bazan Taɓa bari Jinin mahaifiyata da Kannena su salwanta a banza ba, Bazan Taɓa mari Wadanda Suka kashe Ni da raina Su tafi a banza ba, Dole kowa ya karɓi Hukuncinshi daidai da Abinda ya aikata, don Haka, kije Ni zanyi Komai da kaina"

Jikinta yayi sanyi Sosai, zuciyarta ta karye ,tabbas bai Kamata a bar Wadanda Suka tarwatsa FarinCikin rayuwarsu cikin Farin ciki ba, Bai kamata Tayi saurin karaya akan Wannan dan Buƙatar tasa ba, zata iya bada Ranta domin kamo wadanda Sukayi Silar gantalewar FarinCikin Ahalinsu, kuma A halin Yanzu ta sanadiyyar Muguntar da Sukayi ma yayanta yana barazanar tafiya ya barta cikin Duniyar.

tayi ajjiyar zuciya tace

"AM sorry yaya Nasan kayi fushi sosai, and i deserves to be punished, na tarwatsa komai, akan Yar Buƙatar nan taka na Yarda na sadaukar da FarinCiki na gaba ki ɗaya Zan yi komai domin Kwato mana hakkin mu,I pray ba wannan bane last will Ɗinka a gareni domin Kuwa ina matuƙar buƙatar Commands Ɗinka a kowane lokaci "

Da sauri ZEEYK ya Rungume ta shima Yana hawaye , saitin Kunnnenta ya raɗa mata

"Sorry mi Angel, daga dawowa na Na hauki da faɗa, hankali na kullum a tashe yake idan na tuna cewar na kusa MUTUWA sai inji Raina ya ɓaci, bana so in Mutu ban cika burin Mami ba"

Ta runtse idonta hawayena sauka akan kuncinta, ya cigaba da cewa

"Please koda wasa Karki bari Abbi ya sani"

Rintse Idanunta tayi hawaye suka samu damar zubo mata, Ta gyaɗa mishi Kai.


SALEEM bai tashi Farga da Kamun da Soyayyar Maryam tayi masa ba saida ya dau Kwanaki uku bai ganta ba, a lokacin ne ya tabbatar ma kansa Ya fada Soyayya mai Zurfi.

Baisan Soyayyaba, Baisan ya yake ba, Amma ya fasalta yanda yakeji akanta da Soyayyar Zahiri ba irin wanda Yakeyi ma Aeesh ba, Shi kansa yasan ba Soyayyar Gaskiya yake mata ba, Sha'awarta yakeji Shiyasa yayi Rufa Rufa yasan Yanda Akayi aka Aura masa Ita don Ya fanshe abinda yakeji a ransa dangane da ita , sai kuma Allah ya nufa ba rabon shi bane.

Gabaki ɗaya Cikin kwanakin nan Ya susuce, Ya zama Tamkar Mara lafiya, bayaci kullum Sai shan Ruwan Shayi, tunaninta ya zame masa tamkar abinci , idan baiyi ba bayajin daɗi idan Yayi sai yaji shi cikin Farin Ciki, ya koma tamkar zautacce, Wayarta Da ya karɓo hannun Victim dinda ya harbeta Shi ya zame masa Madadin ta, haka kawai yake tasa Wayar a gaba Da kallo yana zuba Surutai, baya Son Zuwa Asibin don yasan Zuwan sa zai Zamo Silar baƙin cikin ta ,shi kuma Bacin ranta ne Bayaso, ya Gummace yayita zama a haka har Lokacin da zuciyarsa Zata sanar dashi ta daina Fushi dashi, Sannan yace.

Yana Zaune a Dakinsu yana Kallon Wani Indian Love movie *Amrutharamam* , Yana Jin Shima zai iya yin kwatankwacin yanda Amrutha tayi Sadaukar wa ga Masoyinta, ta bada Zuciyarta tasa Aka dasa masa, a yanda yakeji zai iya bayar da komai nasa Domin Ya mallaketa.

Ya maimaita kallon movie din Ayau ya fi a ƙirga, Duk wai A haka Salon Soyayya yake son Koya 😒

Sai Jujjuya tea spoon yake cikin yar ƙaramar Mug din Hannunshi,Idanunshi na Kallon TV, Awa daya kenan da Kawo masa Shayin Amma Ko Kurɓa baiyi ba, Naseer dake ta faman Share share A dakin Ne ya dawo ya dubeshi da Mamaki ya kira sunanshi

"Yaa saleem"

Ɗagowa yayi ya dubeshi da Swelling eyes Ɗinshi batareda yace komai ba

Zama Naseer yayi kusadashi ya dafashi cikin Tausayawa yace

"Yaya what's wrong with you?"

Shuru Saleem Yayi Yana Dubanshi, Murmushi manne a Fuskar shi

"Dude Tell me Meke damun ka?, Na lura Tun shekaran Jiya ka sauya, you're Not the one you Used to be ,bakacin abinci sai ruwan Shayi, ka daina Zuwa wurin Aiki yauma Ko wanka bakayi Ba, tun da ka farka ka zuba ma TV Ido kana Kallo ko gajiya bakayi?"

Murmushi saleem ya Saki a karo na ba adadi, ya dire cup din hannunshi, Ya Dauki side Pillow ya Rungume

"Am..in..love" yafada in a whisper yana qara rungumar pillon.

Waro idanu Naseer yayi cikin mammaki, dukda yaga alamun Soyayyace ta maida Salem haka, Amma da yaji tabbaci daga Bakinshi sai Abin ya bashi mamaki.

Tsalle yayi yadawo kusada shi, Shima ya rungume Pillow Yana Washe haƙora

"Ahh Ashe haka akayi ,finally wata mai Sa'a tayi Nasarar Sace Zuciyar zinare"

Duƙar dakai Saleem yayi yanayin shi na sauyawa, Dubansa Naseer yayi a sanyaye

"Bro is anything Wrong?"

"Everything is Wrong brother"

"Am not her type , Bazata so Ni ba"
Ya fada cikin murya mai ban tausayi, ya Lumshe Idanunshi cikin wani yanayi.

"No Babu wata macen da zata Ganka tace bata sonka ƙarya ne ,na farko dai bakada baƙin hali, halayenka duka masu kyau ne ga kyan Sura ga kudi ga ilimin Islamiyya da na boko, You're dream Husband indeed, Mata Burin su su Auri namiji Irin ka"

yafada cikin kwantar da murya yana kallon Saleem da har lokacin idanunshi ke a lumshe

Cikin Mamaki Saleem ya ɗago ya zubamasa Idanunshi yace

"Lallai Nasss baka Gama sani na ba, Ita tun Tuni Tasan Waye Ni, halayyana na ɓoye da bayyane duk ta sani"

Yay maganar Cikin Rauni ,dafashi Naseer yayi cikin kwantar da murya yace

"Don Allah ka gaya min Exactly what's Wrong May be I can help you"

"You can't help Buddy"

Saleem ya Fada a hankali kaman Mai koyon Magana.

"meyasa? just tell me, we can't say" inji Naseer

"you can't Naseer, bazaka iya taimakamin ahalin danake ciki ba, I am weak and...broken" yay maganar cikin raunin murya

Hakan yasa Hankalin Naseer ya tashi matuƙa ,tausayin Dan uwan nashi ya lulluɓeshi, tunda yake bai taba ganin Saleem cikin makamancin wannan yanayin ba.

Cikeda tashin Hankali Saleem ya cigaba da cewa

"Ban san Mafari ba, Bansan Ya akayi ba, The lady I hate , Wacce na Raina itace Allah ya jarabceni da Matsanancin soyayyarta "

Ta runtse idonta, sannan for the first time a rayuwarsa,Hot tears suka gangaro kan kuncinshi, akan Mace, ganin Hawayen Saleem yasa Jikin Nasss ya daɗa yin sanyi

Batareda ya damu da share hawayen b ya cigaba da cewa

"Inajin zafi a Zuciyata, I know I didn't deserve her but this is my destiny "

Hawaye suka sake Gangaro masa.

"Please Yaya Saleem stop this tears"

Naseer ya Fada shima kaman Zaiyi kuka share hawayen yayi, Amma basu daina zuba ba,saima ƙara ƙarfin gudu da sukayi,ya cigaba da cewa

"Ada Women and Love duk Shirme na daukesu, a Gani na ina Amfanin waɗanda zasu taso under man ,su rayu cikin bauta na namiji ,su kuma mutu suna karkashin Namiji, a tunanina mace bata da gata, Banga Abin burgewa a mace ba, Kaman yanda na dauki soyayya ba komai ba, na daukeshi ƙarya da ɓata lokaci , but Now Look at me crying over blind love while wacce nakeyi domin ta ma batasan inayi ba, bata San Ina Sonta ba"

Yana Kaiwa nan zuciyarsa Tayi wani irin rauni, ya kuma fashewa da wani Kukan yana Shessheƙa sosai

" what did i do to deserve this , Laifin Me Nayi da na cancanci wannan Hukuncin? Am even Afraid of telling her, Ina Tsoron In bayyana Mata abin dake raina, Nasan Kashe Ni Zatayi , i Have been like a monster to her all these while"

Kuka yake sosai kaman ƙaramin yaron goye ,You won't believe it in Kunga Yanda ya koma cikin ƙanƙanin lokaci ya zama abin tausayi.

Cikin Rauni nass ya ce
"SALEEM please... kabar kukan nan haba Please stop it,Be strong"

"Nass Am Strong ,Tears are not sign of weakness, but of courage. hiding your emotions is self destructive , Hawaye suke fitarda dattin dake cikin Zuciya"

Yay maganar cikin kuka sosai

"Gaya min wacece ita?, Waye Ubanta a garin nan?, Ita din ba Mutun ce kamar kowa ba?, Tashi Muje ka gaya mata kana Sonta, ƙila kayi Sa'a Itama tana sonka tashi muje"

"No Bazata Soni ba, she hates me"

"That risk you're afraid to take could change your life, bakasan Sirrin dake cikin Zuciyarta ba,ka tashi Muje"

Da haka Naseer ya tasa Saleem gaba yayi wanka, Ya shirya cikin irin Shigan da bai sabayi ba, ya Chanza shigarsa zuwa milk color d'in janfa da wando Na lallausan yadi, Wanda aka k'awatashi da ɗinkin surfani Na ainahi, takalmansa cover masu lankwasa daga gaba irinna sarauta, su kuma Brown, Hulansa brown Mai ratsin Milk sai Maiƙo yake wanda hakan Kadai ma ya isa ya bayyana tsananin Tsadarsa.

Tho MashAllah yanzu kam fuskarsa ɗauke take da ƙasaitaccen murmushi he feels free at least ya Fitar da abinda ke zuciyarsa an Kuma samo masa mafita cikin Sauƙi 🔔

Nan take Asibiti Suka nufa ,inda aka kwantar da Maryam.

Da sallama Suka shiga bayan An basu Izinin Shigowa.

ZEEYK ya tasa ta gaba yana bata magani Sai Shagwaɓa take zuba masa.

Wani irin abu yaji ya dakar masa zuciya da yaga yanayin zamansu.

Suna zaune a bisa Sofa, ta Dora kanta a kafaɗarsa, Idanunta na kallon Hannunsa dake ɓare Magani.

Kamar daga sama taji Muryansu suna sallama ,hakan Yasata Kasa Ɗagowa kuma bata Amsa Sallamar ba.

ZEEYK ne ya ɗago ya dubesu cikin sakin fuska suka ƙaraso wajenshi sukayi bashi hannu Suka gaisa, kallon Mamaki ya bi Maryam dashi yace

"Angel bakiji Anyi sallama ba?"

Ga mamakinsa Sai gani yayi ta Lumshe Idanunta a dole ita bacci Takeyi.

Sunkuyar dakai Saleem yayi ,ko daga nan Ya riga ya sare ma Lamarin,ya sani Maryam bazata taɓa Sonshi ba

ZEEYK na ganinsu ya gane wadannan Jinin Dr Khamis Shettima ne, hannu yasa ya ɗago kanta dake kafaɗarsa ,ta bude ido tana Kallonshi Cikin turo baki ,ya sakar mata Murmushi ya mike yana cewa

''Ohhh i thought kina bacci ne"

Harararsa tayi, yace

"Bari In fita in Baku Wuri, Idan Dad ya dawo Kice na je KASU"

Langwaɓewar da kai tayi a shagwaɓe, hawaye na taruwa a Idanun ta, Tasan Dalilin fitar shi, a kuma yanda ta Tsani Family ɗin batajin zata iya Amincewa Da buƙatarsa nan Kusa.

Fita yayi ya barsu a ciki daga su sai Ita, itama Miƙewa Tayi ta haye gado tace

"Kuma sai Ku tashi Ku tafi ko?"

Haushi ya kama Naseer dama haka Halinta yake?, Batada kunya ashe?, Da zaibi ta zuciyarsa da ya fita ya barsu, amma da ya tuna halin Da yayan nashi ke ciki sai ya Sauke Numfashi yayi gyaran murya

"Ehmm Malama Maryam ,Ni sunana Naseer Khamis Naseer Shettima Ƙanen Saleem"

"Uhum!, Sai Akayi ya?"

Ta Fada tana kafeshi da Idanu, ya cigaba da cewa.

"Please Look at Saleem, he's slowly loosing hiself”

Kallon Saleem Tayi a Karo na farko, haka kawai sai taji Gabanta ya faɗi, ya Rame sosai kaman Wanda ya kwashe watanni yana Ciwo, Take Idanunta suka sake Hasko mata Shigan da yayi, ta Sunkuyar dakai ta saki Murmushin da bata san Tayi ba, a ranta tace

_Ba saban ba yau Su Nasty Doctor Anyi Shigan Mutane, ko daga ina suke Oho 😁_

Dagowa saleem yayi ya kalleta saidai kuma yakasa cewa komai sai hawayen da ke qoqarin taruwa a idanunsa.

Tashi Naseer yayi ya fice , gani yayi kaman zamansa a tsakiyarsu shi ya hanasu Sakewa.

Yana Fita Saleem ya tashi ya dawo Gefenta, ya zauna akan gadon, har suna iya jin Hucin Fitan Numfashin juna

Ta sadda kai gabanta na faɗuwa

"M....Mary..a "

Sai Kuma ya Kasa ƙarasa Kiran sunanta, a Ganinshi tafi Ƙarfin Ya kirata da Asalin Sunanta

Bata kalleshi ba sai amsa masa datayi asanyaye

"Na'am"

Mamaki ya Kamashi, baiyi Zaton Zata amsa Ba, yayi zaton ihu Zatayi masa Ta koreshi a dakin Kamar yanda ya saba

Kamo hannunta duka saleem yayi yana matsowa kusada ita sosai, wanda hakan Yasa tajin Emotional shock ya ratsa Nerves ɗinta.

Batayi Yunƙurin Kwace hannun ta ba, illa Dada Sunkuyar dakai da Tayi gabanta na faɗuwa

"Please look into my eyes" yafada yana kallonta

Kasa dagowan tayi sai hawayen dasuka cika mata ido.

"Please ki bani Dama na baki saƙon Zuciyata"

Shiru tayi bugun zuciyarta na qaruwa sosai, she's feeling somehow, tanajin wani iri sosai, hannunta dake Cikin nashi ya fara rawa.

Jin hannunta na Rawa Yasashi riƙe hannun Sosai ,Wanda hakan Yasata dabo ya zuba masa Wet eyes ɗinta da suka Kusa rikitashi ......

Lumshe idanu Maryam tayi tana qoqarin saita muryarta

"Please free my hand And Go...., I don't wanto see you near Me again"





sainaga ruwan comments tukunna zan Cigaba😒, naga alamun kwana biyu kun danyi sanyi ...



Nayi Gabas 🚶🏽‍♀️

Bintou ✍🏼

29th Aug
[10/3, 9:56 PM] Solace: 🗡

_(Bleeding Hearts)_


_Sarƙaƙiyar Soyayya Mai Wahalar wa_



_BINTOU_✍🏼


*034*

A haka saleem Ya koma gida batareda ta bashi Damar Furta mata Abinda ke cikin zuciyarsa ba.

WasheGarin ranar aka Sallameta,ta koma Asalin sabon Gidansu inda Dad ɗinta ke zaune da sabuwar Amaryarsa a Chan Lagos.

Tuni Matar Daddy tasa akafara shirin tarbar Maryam da Yayanta, Wadanda Suka shafe shekaru da dama Rabonsu da gida ,,Zuciyar dad cikeda FarinCiki haka sauran kannensu farinciki sukeyi .

MaMy karama da ita aketa shirya komi bayansu babu wanda yasan da dawowar Su Maryam kafin wani lokaci ansa an'kara gyara part d'in ZEEYK dukda cewa kullum cikin gyranshi akeyi.

yanda akaga motoci sunata shigowa kowa yasan wasu Manyan baƙine masu mihimmanci akaje ɗaukowa

Suna Shigowa parking security suka firfito har rigerige sukeyi wajan buɗe musu ƙofa ganin fitowar ZEEYK yasa kowa mamaki, mamakin ganin ZEEYK bai gama sakinsu ba aka sake Buɗe dayan Side din, Maryam Ta Fito hannunta daya Zagaye da Plaster

tuni Ma'aikata suka Fara Zuba Musu kirari

" barka da dawowa Ƙaramin Alhaji da likita Bokan Turai, zakunan fama sawun giwa kuke takena ragumi tafiya daku dole idan anason samun aminci a Gidan Babban Likita, dan Likita Jikan Likitoci shugaban Likitocin Nigeria ,ɗa ɗaya tall agun Bamallen jikan Sarkin Zazzau, Sa'eedu Aliyu isufu Bamalli 😒, sadauki yake baya tsoro jarumi yake baya gudu cikin dubban

Please Login or Register in order to submit comment