Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ganin reaction dinshi Amma he's expressionless.

Waving hannunsa dad yayi Kan Fuskar Sa yace

"Hello.."

Sai alokacin ya kifta ido, ahankali ya motsa baki yace

"I don't get you uncle, kaina ya kulle ,What did u mean"

Murmushin Mugunta yayi sannan  yace

"I mean so an Saka Ranar Aurenka Da Khadijah, nan Da watanni Biyar Za'a Daura Aurenku, Har Sadaki munkai she's All yours Now , *Congratulations* "

Zaro idanu ya ɗan yi sannan ga mammakinsu ya Chanza da Murmushi, murmushin da ba a koda yaushe yake yin irinshi ba, Yafi yin Murmushin a duk inda yaga Mugunta.

"Lol.. Amma dad Danginsu Matsiyata ne ko?, Ko kuma Sun Gaji da ita ne halan?, ko suma Irin Cutar d Uncle ɗina Ke fama dashi ne taresu"

Aikam Ba karamin  fusata kawu Shiru yayi ba amma Sai ya Shaye,Dad Kou yayi yana kallon yadda ya maida abun Shirme.

"Hey boy Dawo Hankalinka da ga Yanzu har zuwa nan da 6months Alhakin Kula da ita ya Rataya ne akanka...!,She's Now Your Wife *To be* "

Dad ya Ƙarashe maganar Da daka Masa Tsawa, sam Ko kaɗan Tsawarsa Bai razanashi ba Kalamansa Sunfi Gigita tunaninshi.

"Wife...? Wife to be fa kace Dad? Meye Amfanin hakan? don Na gabatar muku da ita ba hakan ke nuna Aurenta Zanyi ba Ba ko wace soyayya ke kaiga Aure  ba, Ni inada wacce na shirya rayuwa da ita ,Dan ina Soyayya da Dija hakan bai isa ya baku damar zuwa nema Mn Aurenta a duk Lokacin da Kuka ga dama ba"

Tafada Shima cikin son danne 6acin Ransa but deep down he's frying.

"Ashman Bazaka maida mu kananun Mutane ba?, What did you mean?, Baiko ne anriga anyi maka kuma mun kai Sadaki Dubu ɗari Ko kaƙi ko kaso Sai ka Aureta Baka da yanda Zakayi"

"Wait Dad.., come again, Banida me? Banida za6i fa kace? Don't tell me You have done everything Illiteratly"

Ya katseshi tana kallonshi unbelievable.

"Ashman... Wannan ba jahilci bane, Kaine kake Kokarin Introducing Jahilci into this matter Taya zaka ɓatawa Yarinya Kamaila'yar Gidan Mutunci Lokacinta alhalin ba Aurenta Zakayi ba?"

Shiru yayi don she's speechless ma, kallon shi kawai yake cikeda kunar zuci

"Gobe ka Shirya Ka koma kd Kaje Gidansu kayiwa babanta Godiya"

Cewar Baffa a tausashe, Murmushin Mugunta manne a Fuskar Sa.

"Dad baffa Kun kasheni da raini, nakasa yarda da abinda nakeji Daga gareku, Bansan Tsanar da kuka mn Har ya kaiga hakan ba"

"Ashman aure jigon ɗa namiji Rayuwar ka babu Aure babban Barazana ce ga 'yan mata"

'dago Jajayen Idanunsa yayi ya watsawa Baffa dake Mgn Wanda hakan ya sashi yin  shuru ba shiri.

"Dad! Are you kidding me? Auren dole zaku mn? Ni? Dad kafi kowa Sanin yanda na tsani Auren dole, atunaninka  haɗani da ita da kayi Shi zai sa ka Auri Aeesha? No Never...!, idan Ina Raye Bazaka taɓa Aurenta Ba koda nayi Aure a gidana zata cigaba da Rayuwa"

Katseshi a firgice dad yayi

"sanin hakan yasa nace A sa Ranar nan da Watanni biyar kafin Lokacin na Gama Kimtsawa..."

"Ni kuma ina Mai tabbatar Maka da cewa Kafin Watanni Biyar Su Cika ,Sai na Aura Mata Saurayi wanda yafika kuruciya da komai"

"Let's Seee!"

Dad katseshi da karfi yana Buga dinning Table a fusace

Miqewa Ashman yayi bashiri jijiyoyin kansa na Mimmiƙewa yana huci kamar matunwacin zaki idanunsa na sauya Launi.

"I said No! Bazai yiwuba! Impossible!, bazaka Taɓa Aurenta ba, Allah Dakansa Ya Haramta Maka Ita Bazaka Aureta ba"

Saiya juya da Sauri Cikin Takunsa Mai cikeda Jarumta ya Fita kansa na Sara masa .

Binsa duk Sukayi Da kallo ko wannensu Zuciyarsa Kamar Garwashi

Naushin iska Baffa yayi yana fadin "shit! Shit!!

Ba haka Yaso wasar ta ƙare ba, Yaso Rayukan Kowanne su Yafi haka Ɓaci.

Mistake yayi instead yabi ta inda Ya Shigo sai Ya fita ta kofar Gaba,Dama Sunji Muryarsa a Ɗakin Abba Jiran Fitowarsa Kawai Sukeyi.

Ya fito kenan yajiyo Saukar Tafasasshen Ruwan Zafi a jikinsa.

Dan Tsananin Bacinrai Da Zafin da Zuciyarsa Ke masa Ko Gizau baiyi ba Haka Ya Karasa Ciki tiririna Tashi a Jikinshi , gani yake Tiririn dake Tashi a jikinsa yafi wanda ke Tashi a Zuciyarsa.

_taya Mahaifinsa Zai so Wacce yake Gani a matsayin Duniyar sa?, Taya mahaifinsa zai So Ɗiyarsa Da Aure?, taya Mahaifinsa Zaiyi Sha'awar Auren Yarinyar da ƙanwarsa Ta Haifa?_

*_Inaaa Bazai yiwu ba..!_*

Ya faɗa Da Karfi yana Kaiwa Bangon dakin naushi da iya Ƙarfinsa ,Hakan Yasa Hannunsa Ya fashe Take ya Fara zubar Jini haka bangon Dakin Shima ya Tsaye..............


Nayi gabas🚶🏾‍♀️🚶🏾‍♀️


14th may🗝️

BINTOU 💙💚❤️

Please Comment 🤲
Share😙💛              🔪 *_WUƘA A ZUCIYA 🔪
                  ❤️   _(Bleeding hearts)_ ❤️
                 

                            *005*

          _taya Mahaifinsa Zai so Wacce yake Gani a matsayin Rayuwar sa?, Taya mahaifinsa zai So Ɗiyarsa Da Aure?, taya Mahaifinsa Zaiyi Sha'awar Auren Yarinyar da ƙanwarsa Ta Haifa?_

*_Inaaa Bazai yiwu ba..!_*

Ya faɗa Da Karfi yana Kaiwa Bangon dakin naushi da iya Ƙarfinsa ,Hakan Yasa Hannunsa Ya fashe Take ya Fara zubar Jini haka bangon Dakin Shima ya Tsaye..............

Safa da marwa yai tayi a tsakar dakin, hannuwanshi goye a bayanshi.

Kallo daya zaka yimashi kasan yana cikin tsananin damuwa da Tsananin Tashin Hankali .

Tsaki yasake ja a karo na ba adadi Yana Sake Kaiwa Kusurwar Ɗakin Naushi , jijiyoyin kansa Na Miƙewa.

"Kai impossible wlh!" Yafada cikin qaraji.

"Wlh bazai ta6a yiwuwaba... Ni za'awa Auren Dole ? Ni? Ni? The whole me? No, bazai yiwuba, dole insamu mafita, dolene!, Dadddy Bazan Taɓa baka Chance ɗinda kake nema Ba ,Aeesh ba taka bace"

Ya kai zancen yana sake kaiwa bango naushi.

Ƙarar Buɗe Kofar da Akayi Ne yasashi Juyowa a Fusace Zainab Da nafeesah ne Ƙannensa (wa'enda suka zuba Masa Ruwan zafi Recently) ,Mahaifiyarsu Ce ta Turosu tace su dubo mata me ya faru?,Don ta hango shigowarsa a fusace.

Da hannu ɗaya ya damƙosu Tun kafin Su Gama Yunƙurin Shigowa Yasa Makulli ya Kulle kofar.

Take Ya fara sauke Fushinsa Akansu, Aikam Sun Daku Sai ihu suke babu Mai jinsu, saidai ya tabbata ya saɓa Masu kamanni Sun kumayi laushi Basua iya Daya koda ƴar yatsar su ne Sannan ya jasu ya watsa A Ban ɗaki ya buɗe Musu Ruwan zafi,  ya sa Makulli ya Kulle Su ta baya bayan ya fita.

Yana Fitowa yaji ƙarar wayarsa Alamun kiransa Akeyi ,Hannu na kyarma ya dauki wayar dake kan  table , har zufa yake don bala'i.

Saida takusan tsinkewa sannan ya Daga, Batareda yayi la'akari da Wanda ke kiransa ba ya hau zazzage buhun masifa.

"Honey🍯 Are You ok?"

muryar Deejah ta doki kunnenshi.

"Honey my Ass,Get the Hell out of My Phon....."

"Sorry Sir, don't Cut the Call,Any ways  I called to congratulate Us 5Mouths Remainin...."

"Really?!.. Oh am grateful, thank you thank you okay...?" yafada yana katseta.

"It ok Sir, sai ranar Monday kuma ko? Please 8 dot inaso in ganka kuma We need to star........"

Kittttt ya katse wayar Yana Jar tsaki

Zubewa yayi kan cushion din bayanshi yana sauke ajiyar zuciya

"Wuhh! Allah na godema, Why can't She Understand How much I hate her"

Haka yayi ta  'yan sabbatunshi Hankalinsa a tashe, Yayi missing Calls Ɗin Aeesh Ya kai 20, ko kaɗan bazai iya Picking calls ɗinta a irin wannan lokacin ba , ya kasa samu kwanciyar hankalin yin magana da kowa,  bashi ya Fito ba sai Da Magriba ta Baya yabi Batareda an ganshi ba Ya wuce masallaci Gabaki ɗaya ya mance da yaran da ya Kulle a ban ɗaki.

Yana dawowa ya Iske Saleh Saurayin Zainab Tsaye a ƙofar Gidan ya jingina da RobaRobar sa.

Tsaki yaja ya wuceshi Zai buɗe Kofar ya jiyo Muryar Sa

"Hey Likita jimana"

Juyowa Ashman yayi Yana masa kallon Sama da ƙasa.

"Eh ya ?, kira Mn 'ƴar Zazuuu Ɗin Ƙanwarka Mana"

_Bala'i_

Yaron nan har ya samu liver ɗin Saka masa Magana Son Ransa?, Yaron da ada yake Tsoron sa Da shakkar HADA hanya dashi?.

Juyowa yayi a hankali ya zuba masa Wani mugun kallo.

"Are You Insane....?, ba na hana ka Zuwa a Ƙofar Gidan mu ba?"

Machine ɗinsa ya Gungura ya bar ƙofar Gidan Ya parka tsakiyan Titi

"Tho Sannu masu Gida nan dai ba Kofar Gidan ku bane Titin Gwamnati ne koma Kayan Gwamnati ta kowa ce"

"Ba laifin ka bane laifin Yar iskan da Ta baka damar Binta ne"

Juyar dakai Saleh yayi

"Thank God , ƴar iska kace kaga bani cikin 'ya'yan da iska ta haifa, Dakai da ita Kune ƴaƴan iskan"

Huci Ashman ya Fitar yaci Sa'a he's not in the mood today da ya Ragargaxashi ya ganar dashi kurenshi ,daga nan Zai koyi Yanda ake magana da Elder Amma ya kyaleshi idan ya Sake maimaita kuskurenshi Zai gane bashida wayau.

Bai sake tanka shi ba Yayi Shigewarshi Ciki,Shafff ya manta ya kulle su Zee A Banɗaki ,Saida yaji Su Umma Sauderh Na nemansu sannan ya tuna ya buɗesu, Sunyi Laushi sosai , Watsosu Waje yayi Ya kulle Ƙofar.

Ƙarfe 10:42pm

Gang ɗinsu Saleem (Kannen Ashman) suka shigo yanayin driving dinsu da shigowarsu gidan daban ne.

Saleem Shine Babban Ɗan Umma Sauderh, Kishiyar Maragayiya Umman Hafsah (mahaifiyar Ashman), Sannan Rabeel ,Naseer duk 'ya'yanta ne, Sannan Abduljaleel (Abdul) ɗan kawu wanda Abokan sa sukafi saninsa Da (Fee-Jayl) ɗan kawu Zaratan Mazagen Gidan kenan.

Saleem saurayine wanda akalla bazai wuce shekaru 27 ba, murd'ad'd'en mutum ne irin mutanen nan da  miskili yafisu dad'in zama, danshi ba miskili baneba irin Yayan sa Ashman, ta wani ɓangaren bashida daɗin zama ko kadan tsabar jin kai ne dashi, gashi Mugu Ne baya Son mata ƙannensa mata ma tsoron hada hanya dashi suke, Watanni Shidan da suka Gabata ya kallama karatunsa ta fannin matsalolin mata inda ya karanci Obstetric and gynecology a halin yanzu bai fara aiki ba.

Naseer kuma Shekarunsa 25 da Wasu'yan Watanni Mutum ne shi na Kowa,kowa nashine yanada yawan Dariya da son Mutane duk Cikinsu Shi kadai ya banbanta a cikinsu sabanin sauran da jijji dakansu yafi Karfinsu ,Masscom ya karanta a BUK a halin yanzu yana Final year ɗinshi ne final exams kadai yarage masa.

Rabeel kuma Halinsu sak da Ashman kama daga Kamannmin fuska zuwa na hali bai Bar komai ba daga halin Ashman ba, Haka kamar yanda Aeesh take Weakpoint ɗin Ashman haka Siddiƙa take Weakpoint dinshi Shima, Best friend ɗinsa ce tun Suna yara ko kaɗan Baya Kaunar Aeesh Haka yasa Basua Jituwa da Ashman Sosai, Accountant ne a Wani babban Companyn Safarar Manyan Kayansawa kama daga Shaddodi, Atamfofi, Lesuka, Kananun kaya Abayoyi takalma Eye Glasses da dai Sauransu, Ya Samu Aikin ne bayan ya kammala Karatun sa na Degree ta fannin kasuwanci ba don ya kasa samun aiki a ko ina ba, sai Don hakan shine passion ɗinsa.

Abdul Jaleel kuma Shekarunsa 28 akwai shi da son Shiga harkar manyan Mutane Da halin Girma  ba kowa ke iya gane halinshi Ba koda Zaman Shekara Kukayi taredashi, Wani irin murɗaɗɗen Hali gare shi, Hartta Iyayensa shakkar sa Suke Don Komai nasa Ba kai tsaye bane, Idan Yace Eh Zai iya Kasancewa A'a yake nufi karantansa Nada matuƙar wahala Lawyer ne a Wata babbar kotun Gwamnati dake nan Cikin garin Kano.

                *Kaduna*

Sai wuraren 7 na yamma Ya Aliyu (Yayan Reey wanda suke uba ɗaya)ya shigo lokacin Suna Zaune a parlor Suna hira da Umma yace

"Aeesh ki shirya will drop u off kafin na wuce"

gyadamai kai tayi Reey ta rakashi da harara Suna Hirarsu mai daɗi zaizo ya rabasu, tuni ta wuce daki wanka tasake yowa ta shirya cikin doguwar bakar riga mai hade da baby pink color ta Reey ce Ƴaƴanta Sadeeq ne yasiyo mata daga Canada, bakaramin kyau doguwar rigan yamata ba gashi anbishi da stones, gaban madubi taje ta shafa hoda ta shafa man baki akan pink lips dinta sanan tai rolling gyalen rigan baki tadau small mini side bag din Reey baby pink tasaka baby pink flat shoe sanan tadau wayarta tafito tana rera Waƙa,

      _Na gaza kara tunanina_
     _Na gaza Cimma hasashe na_
    _Na gaza nuna kawaicina_
      _Bare a gane Kwatance na_
     _idanuwa na_
     _yau suka hangi nufi na_
    _wanda nakewa kauna ne A gabana_

Amota tasami Reey da Ya Aleey hakan yasai tai motan ta bude Front Side ta shiga ta rufo, tace

"gani Yaya"

"Kam bala'i Kayana?"

Reey dake zaune a Backseat ta faɗa tana Ɗan Jan Mayafinta ta baya

"Yau na fara sa Kayanki ne?”

"Amma Kunsa Illar Sharing Kaya ko?"

"Whatever Inma Cuta Gareki na yarda In kwasa, Nasan Matsayin Wanda Ya siya kayan a zuciyarki Ne yasaki jin Wani abu Dan na saka Kayan Abi''

tada motar ya Aleey yayi yana Murmushin Shirmensu batare daya kallesu ba yayi horn mai gadi yabude musu suka fita, tafiyar kusan 10minutes yakaisu Gidan su Aeesh, agaban gidansu yay parking baice masu komiba, hakan yasa Aeesh ta juyo ta kalleshi kaman zatai kuka tace

"Pls Yaya Laifi na Maka ne?,tun ɗazu sai Kallon mu kake baka ce komai ba"

Gajeren murmushi yayi ya Juya yana  Faɗin bari naje masallaci in na dawo gobe zamuyi magana

"Allah ya kiyayehanya Yayan mu, byeee"

gyada mata kai yayi sanan ya juyo ya Watsa mata Fararen Idanunsa Irin Kallon da ƴaƴanta  Ashman yake yawanyi  mata Saurin Kauda kai tayi Gabanta na faɗuwa me kallon nan ke nufi?

Kauda dubansa yayi daga Kallonta yace

"Juwairiyyah in Zaki dawo ba ki hau Napep don't stay long, I might be late"

Yaqe tamai tace "to, bye" tamai waving hannu tana yaƙe, shima dan murmushi yamata

yace "bye"

Bude kofa tayi ta sauka daga motan yayinda Ya Aleey dakansa ya Buɗe wa Aeesh.

Kauda kai Reey tayi Tana Taɓe baki, Ta lura da taketaken Yayan nan nata Son Aeesh Lallai in ma Barci Yake ya farka Aeesh tayi masa nisa Ehe.

  knocking gate Sukayi din aka bude suka shige, kallonta yay tayi har ta shige murmushi yayi yatada motar yay reverse yabar anguwan.

Sallama sukayi suka falonsu.

Umma ce zaune a parlourn tanacin fruits gefenta Kuma Deejah (fianceé) ɗin yaya Ashman)

kama baki Aeesh tayi tace

"wanake gani yau yar tselen uwan"

"yarinya bata zumunci ,ko a asibiti muka haɗu kallon banza Kike mana Shiyasa kikaga bamua Kulaki ma 'yar Air Duk tsiyar da kike Tsulawa muna sane dake Ƙiris ya rage Mu Fasa Yayan mu ya fasa Auren naki"

Cewar Reey

"Ku Dallah ku Rufewa Mutane baki kun shigo Ko sallama babu kun  kama Yarinya da faɗa sai kace Wacce ta Mku Laifi?"

dariya sukayi Reey tace

"kai mum Yarinyar nan Tunda ta Samu yaya Ashman ya fara Sonta ta Guje mu ko a Ward Students take Kiran mu ƴar iska wayaga Certified *J-CHEW* "

Dariya Duk Sukayi Umma tace

"Whatever ai ita Aikinta take ku kuma fa, school of nursing dinma ya taddaku da halin"

tai maganan tana dungure mata keya, dariya Reey tayi ashagwabe tace

"kai Umma nidai ina wuni, Ke kuma Ki wuni da baƙar halinki"

tai maganan tana karbe Plate din fruits din hanun Deejah tana dariya, dariya Umma da Deejah sukayi

Deejah tace "ai nasan tunda kika shigo bazan shashi ba"

" oya  duk ku tashi ku barmin falona kuyi sama kafin ku kusa kasheni da surutu"

dariya sukayi suka mike tsaye Aeesh na cewa

"Umma Ni Yunwa nakeji gashi Yaya Ashman Yaƙi daga Wayata, Wayyo Zuciyata zata buga"

Aeesh ta faɗa  a shagwaɓe

Harara Deejah ta galla Mata A fakaice a Zuciyarta tana cewa

_Shegiya Lokacin Rabuwar ku tayi 5months ya rage min sai na ɓata Rayuwarki sai kin zama Abar tausayi_

A fili kuwa cewa tayi

"Muje Akwai labari, Mum ina habeeb catface ɗinki tunda nazo ban ganshi ba?"

tai maganan tana hawa sama sauran suka mara mata baya dariya Mum tayi sosai tace

"Ai Yaron ya girma ya je Tutorial"

dariya sukayi suka karasa sama  Reey nashan fruit din sukai dakin

Tura kofar sukayi, Dakin yayi duhu sosai kafa Reey ta buga kofan da ƙarfi tace

"Innalillahi mutum A ɗakin ki Aeesh"

ihu Aeesh tayi sabida tsoro zata Ruga a Guje Deejah ta riƙota

"Ke dalla karya ne"

Tay Maganar tana Kunna Switch haske ya mamaye ko ina, tsaki taja ta dafe kirji tace

"me haka zakija Zuciyata Ta buga"

"ya buga mana saime matsoraciya kawai"

tai maganan tareda bangajeta da kafaɗarta ta shige Ciki, ihu Aeesh tayi ta tureta hakan yasa takoma gefe ta faɗi, Deejah kuwa tuni ta Samu Gurin Zama ta hakimce tana kallonsu.

da sauri Aeesh ta taso tana Duban hannun Reey

"dan Allah Besty ki ban fruit dinnan nasha Wlh Yunwa nakeji"

Tsaki taja

"Kije Umma ta baki nima Kwata nayi"

" wlhy hanani zatayi"

make mata kafada Deejah tayi tace

"Kyaleta Abege je akwai fruit a freezern Side dinsu Ya Sadeeq ki dauka ki yanka naki kema"

Turo baki tayi ta zauna kusa da Reey tace

"please Besty wlh Bazan iya yankawa Ni ɗaya ba dama Yaya na nan ne 💔😔,da ban Wulaƙanta ba, I missed him I wish He won't stay long"

"aiko zakiyi bindi yarinya Dawowan yaya Ashman ba yanzu Ba ,Gara tun Yanzu ki koyi yin komai babu shi don nan da watanni Biyar zai Angwance"

Dumm.. Gabansu yafadi gabadaya yayinda Reey yayi mutuwar zaune awajen tana kallonta baki buɗe, A hankali Aeesh ta ɗago ta dubeta don Bata ma Fahimci ina zancen nata ya dosa ba

"What did u mean Deejah?"

"An saka Ranar Auren mu nan da 5months Abbana yace In Sunyi saurin kammala nasu Shirye Shiryen ma za'a rage Ranar Zuwa nan da 2 or 3 months"

Deejah tayi maganar Cikin isa.

"Innalillahi Wainnnailayhirraji'un...."

Aeesh ta faɗa a kasalance Tana dafe Saitin Zuciyar ta,jin Bugun Zuciyar ta na neman Sauya Salon bugawa.

"Deejah Pls ki MN bayani tayanda Zan fahimceki U Must be joking"

"Ke Wlh da gaske ne Har Sadaki an bada"

"What!"

Aeesh tayi exclaiming tana miqewa tsaye ilahirin jikinta duk cira yake.

"No......"  Girgiza kai hawaye na taruwa a idanunta.

"Yayana bazaiyi Aure yanzu ba!"

Tafada muryarta na cracking.

Wani kallo Deejah ta watsamata sannan yaja yar gajeren tsaki tana cewa

"Dalla mallama Mey haka?, Keda ya kamata kiyi murna Baƙin cikin me kike mana"

Kuka Ta fashe dashi sosai Ta faɗa jikin Reey tana Shessheƙa ita kanta Ko kasheta za'ayi ace ta faɗi dalilin kukan da takeyi Bazata ce gashi ba She just feels unhappy da Auren.

Sosai Hankalin Reey ya tashi, ta shiga Rarrashinta yayinda Deejah ta dau waya ta turawa Aareef Saƙo.


Fitowarsa Kenan Daga Ban ɗaki Sai Zabga Murmushi yk yi bayan ya karanta text ɗin Deejah.

Kai tsaye Gaban Mirror ya Tsaya yaita zabga murmushi shi kadai kamar wani shabiyu sha uku , shiryawa yayi Cikin yadin Kaftan Dinkin Simple  ne  ba wani  Kwalliya yasha Guga sosai kayan Ya karbe shi kuma yayi masa kyau sosai.

Hannu yasa ya shafo kanshi yana furzar da huci

Haduwar su ta dazu yafado mashi arai

Tunowa yayi da yadda yake Bayyana Mata Tausasan Kalamansa masu sanya zuciyoyi Cikin Shauki.

Murmushin gefen baki yayi yana cizon lips qasa in an arrogant Way.

Irin kallon da tayta masa ,Kallo mai cikeda Shaukin so ta tsakani da Allah.

Fararen idanunta data ware sanda ya maida mata martanin Murmushin ta ne ya tuna

Wani murmushin yasaki yanzu mai sauti ya Karya hularsa irin wanda akewa Laƙabi da zanna Bukar, Ba ƙarya Aareef First class handsome Guy ne , Kyakkyawa Ne sosai Ajin farko na bugawa a jarida.

Fitowa yayi Ya iske Abokansa Biyu Kamal (Sky Kay) da Bash suna Sana'ar su ta koda yaushe wato Latse Latse a System.

Kodashi suka Shigayi Suna rera Masa Waƙar

_who be this Guy_
_fresh Guy_
_Fly guy_
_Bad guy_
_kaftaan_
_They wan Compare_
_Allow them_
_they wan try You_
_iwo Bar man_
_wole guy can never guy another Guy man_

"Ehh what?, Abege stop I gatta Date" Yafada yana kanne msu idanu fuskarshi fall murmushin jindadi.

"Ehh...man Gist us"

Bash ya faɗa Yana ture laptop ɗinsa Cikin salon jin gulma, ya Nufoshi.

Tureshi Aareef yayi yana faɗin

"Abege shift...."

Yasa Kafa yayi ficewarsa.

Kai tsaye Gidan su Aeesh ya nufa, yana isa bakin gate ya kira wayarta har a lokacin Hankalin ta bai Ida kwanciya ba sosai taji Zuciyarta yayi mata nauyi taji ta tsane Deejah Dukda itace ta haɗata da yayan nata ,Bata taɓa Tunanin za'a saka ranar Auren Ƴayanta Batareda ya Sanar da ita ba.

Aeesh kou kuka take hurjanjan tana tunanin makomarta ya Rayuwar ta zata kasance idan yayanta yayi aure, Sosai Reey ta shiga damuwa sai Faman Rarrashinta yake ringing din wayarta yasata dan tsagaitawa ta kalli wayar, ganin mai kiranta yasata Jan tsaki tayi cilli daita.

Ganin bata dagaba harta tsinke yasshi sake bugawa nan ma ba'a daga ba.

Leƙa face ɗin wayar Deejah tayi _*My ENDOCARDIAC*_ tagani rubuce a Fuskar wayar

" Tofah? Your ENDOCARDIAC dey call oh Halan kunyarmu kikeji"

Deejah tafada tana ta6e baki.

Waro ido Aeesh tayi ta fizge wayar a hannun Reey tayi sliding ta kara a kunne, Kusan a tare duk Suka sauke ajiyar zuciya.

Sallama yayi ta bangaren sa,Amsawa tayi a sanyaye

"Your voice sounds Some how..."

Shuru tayi tana cigaba da sauke ajiyar zuciya.

"What did u mean?"

"Kina cikin damuwa I guess....!"

Shuru ta sakeyi, bai damu ba ya cigaba da cewa

"Idan da zaki bani Dama da na Musanya baƙin cikin da kike ciki da Farin Ciki mara misaltuwa"

Nan ma Shuru ta sakeyi

"Kinada Lokaci....?"

"Nope da tsada"

Ta furta a kasalance.

"Amma kai kam Gareka kyauta ce"

Dungurinta Reey tayi ta zuba mata harara, Turo baki Tayi daidai lokacin da tajiyo Muryarsa yana cewa.

"Zan iya samun Lokacin ki a wannan daren....?"

Wasu siraren hawaye ne suka zubo mata tasa bayan hannu ta share

"Ko zan iya sanin me lokacin nan ya ƙunsa?"

"So nake na Share Hawayen ki, Na maye miki Gurbin Wanda kike kewa a Halin yanzu"

"Bazaka iya ba”

"Ga proof Ina Ƙofar Gidan ku, Ki nema Mn Izinin Shigowa Gun Mumcy”






Tho pha 💔😔

Am speechless

Just comment

Thank😍😘

May20th
BINTOU 💘💕💛💚💙❤️
[7/18, 9:22 PM] chubby number: 🔪 *WUƘA A ZUCIYA*🔪
_(bleeding hearts)_💔


*006*

Wasu siraren hawaye ne suka zubo mata tasa bayan hannu ta share

"Ko zan iya sanin me lokacin ya ƙunsa?"

"So nake na Share Hawayen ki, Na maye miki Gurbin Wanda kike kewa a Halin yanzu"

"Bazaka iya ba"

"Ga proof Ina Ƙofar Gidan ku, Ki nema Mn Izinin Shigowa Gun Mumcy"

"Karya ne"

Ta faɗa Unbelievably.

"Serious "

Zumbur ta Miƙe farin ciki ya mamayeta ta ma rasa me zata Ce masa.

Fizge Wayar Reey tayi ta Katseta

"Wai ke wace irin Mara hankali ce?, Me kike shirin yi?"

" tarboshi zanyi mana"

Aeesh Ta faɗa Fuska a washe.

"Babu inda zaki ,Yay ta zama a waje in Ya Gaji Dakansa zai ware"

Cewar Reey tana Huci.

"Wlhy in kin isa Shegiya nake, ke da kanki kikace in so na yake da gaske shi da kanshi zai nemo Inda nake,and he do...!, what else did u want him to do.....?"

Shuru Reey tayi jiki a sanyaye ita kanta a halin yanzu bazata ce ga Dalilin da yasa ta Tsane shi ba..

"AM sorry Besty yau ko kin ƙi ko kin so You can't stop me from Confessing My love to Him......!"

"What's Going up?, Wai meke faruwa ne?"

Dijah ta faɗa as if she don't know what is goingon.

Murmushi Aeesh tayi Tasa tafin hannu ta Share Ragowan Ruwan Hawayen dake Manne a Gefen Fuskarta

"Dee..! I finally met him,yeah the man I wanna Spend the rest of my life with,but I guess Reey hates him because he's Such a celebrity to me, She's Afraid may be he might Snatch me away From her"

Tsaki Reey taja Cikeda jin haushi,hakan Ya sake ba Aeesh damar cigaba da faɗin.

"Turns Out,I wish you could meet him shi din rayuwata ne, he's tall cute And Handsome, gashi da iya Tsara Kalamai he's just perfect I can't wait to make him the LOML"

Ta faɗa sounding so silly ,duk dan ta kunsawa Reey takaici tsaki Reey Taja Cikin takaici tace.

"Like Seriously.....!"

daɗi ne ya cika Deejah ji tayi kamar ta zuba ruwa a Ƙasa tayi tasha don daɗi, ada Zarginta Aeesh Son Ashman take Shiyasa take Avoiding Ko wane Namijin da yazo mata da zancen Soyayya, Tsananin farin cikin da take ciki ya gaxa Ɓoyuwa a Zuciyarta har sai da ya fito zahiri, harara ta Galla wa Reey ta juya Kai cikin Kisisina

"Ohhh wow, Masha Allah Finally, We both 're getting marriage, kema Reey kiyi Ki Fitoda Tsayayye karki mutu gauruwa"

"Banja In Allah ya bani miji Ki Hana ni aure"

"Owh yar banxa Ashe Kinason Auren ,Shine kike mata Bakinciki?"

"Bakinciki fa Kikace?, nikam in Dan bana Goyon bayan tarayyarsu ne Kin da'de  Ki Siffanta ni da Abinda yafi haka ma I don't care"

"What...?,Juwairiyyah Are you Jealous or what?"

Cewar Dijerh

"Good Forbid"

"And then Why are You not Supporting her. ..."

"Ba mutumin Arziki bane, Bata Dace dashi ba"

"Ba mutumin Arziki bane Taya kika San Haka?, allow her To Find Out her self...."

"Dijah Understand what

Please Login or Register in order to submit comment