Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a cikin su?"

"Maryaaam, Ina Sonta, bansan ya zanyi da rayuwata ba...!, Idan na rasata Mutuwa Zanyi"

Yayi maganar idanunsa a rufe suna ɗigar hawaye hankalin Abba yayi matuƙar tashi bai taɓa ganin Saleem cikin wannan yanayin ba, wani irin tausayin shi ya rufe shi.

"Me ya sa ka saketa bayan kasan kana Sonta?"

Lumshe idanu kawai saleem yayi yana sauke ajiyar zuciya.

Cikeda Wani irin yanayi ya sake murza Hannayen Abba da ke saman Ƙirjin sa .

"Ban.....saketa ba"
Yay maganar cikin fizgar numfashi, jin zuciyar sa yake kaman Ana hura wuta .

Hankalin Abba yakai ƙololuwar tashi yayi saurin zare Hannun shi Daga ƙirjin shi

"Ka kwantar da hankalin ka inshaAllah Ni dakaina zan dawo maka da Matar ka, Ni Abbanka nayi maka Alƙawarin haka”

Abba ya faɗa Tashin Hankali Rubuce a fuskar sa, yana share masa hawaye.

Murmushi kawai Saleem ya saki don Shi kadai yasan abinda yakeji a zuciyarsa.


Ahankali ta Fito daga Motarta bayan tayi Parking, a sanyaye take tafe har isa bakin kofar shiga tasa hannu cikin sanyi ta murda yabude tashiga.

Maida kofar tayi ta rufe sannan ta jingina da kofar tana sakin jakkar hannunta a wajen tareda lumshe idanunta dasuke mata Nauyi, jin kanta take kaman Ba ita ba, zamewa Tayi ta saki hawaye.

Wannan wacce iriyar qaddarace?, Meyasa saleem shigo Rayuwar ta? Saleem ƙaddarartace tasani, tun shigowarshi arayuwarta yayi Awon gaba da duk wani jindadi nata.

Sosai takejin wani irin baƙon yanayi Na shigar ta, ta rasa meke damunta, abinda ya faru tsakanin su ɗazu shike dawo mata, ji tayi ta tsani kanta ta tsani Saleem, yau ce ranar da ya kamata ta zam ta Farinciki a gareta, Ranar da ta fara ɗaukar fansan mahaifiyar ta da hannunta, Amma Sam tunanin Abinda tayi ya kasa bata damar hakan.

Hankali mama ke taka stairs Hankalinta akan Maryam dake duƙe jikin ƙofa tana sauke Numfashi, cikin kulawa ta iso gareta

"Mero lafiyan ki Kuwa....?"

Kaman daga sama taji muryan mama a tsakiyan kanta, a hankali ta ware Rinannun Idanunta ta dubeta, cikin Dauriya ta miƙe ta dau jakarta Batareda ta amsa ma Mama ba,ta dau jakarta tayi ɗakinta.

Mama tabita da kallon tausayi, Dukda bata san Mai ya faru ba, in Ka kalli yanayinta dole ta baka tausayi.




Ɗaya daga cikin attendant na Renal theater ne ya shiga Don ya gyara wurin, sai yaga mutanen da Maryam ta Shaƙawa abu a sume da gudu ya Sanar wa Incharge abinda ya gani, cikin kankanin lokaci labari ya isa kunnen Abba.

Taimakon Gaggawa aka masu suka farfaɗo, nan suka bada labarin Abinda ya faru, Ajiyan Zuciya Abba ya saki yace za'a yi bincike.

Inda Aka kwantar da Baffa ya nufa don ya tabbata da akwai abinda sukayi masa, Surgical Gown dindake jikinshi ya yaye Don yaga aikin da akayi masa, nan take yayi Arba da Rubutun da Maryam tayi a jikin sa.

Murmushi yayi ya Maida masa Lulluɓin

_Jinin Fateemah Sun Taso da guguwar ɗaukan fansa_

Ya fada a fili, sannan ya fice daga ɗakin, Murmushi yayi ma ma'aikatan yace babu Abinda Ya sameshi sun duba CCTV footage ɓarayi ne kawai ,kuma ba wani abin kirki suka sata ba.




Duk wanda yasan Aeesh yasan tana cikin matsanancin Farin Ciki, gata ga Ummanta ga yayanta da Kuma Ƙaninta Ahalinta wadanda tafi so a duniyar nan sun dawo, sai kiran Yan Uwa da Abokan arziki take tana gaya musu Ammie ta dawo su kuma suna zuwa ana gaishe ta da jiki.

Tunda Ashman ya tafi bai sake waiwayan ta ba, Abubuwa sunyi masa yawa, a idon duniya ya zama Sak Rabeel (Ashraf) dan uwansa duk wata harkokinsa dama wani abin da ya dangance shi, shiyake tafiyar dasu, ya koma kwana gidan Abba a ɗakin Ashraf, a takaice dai ya koma sak Ashraf.

Rashin lafiyan Baffa shi yasa Hankalin shi ya rabu gida biyu, Ashman yasan Komai dangane da Binciken da su Zeeyk keyi Hasalima shi ya sama wa Maryam aiki a asibitin sa, tun yana yaro yaga Abinda ya faru tsakanin Baffa da Mahaifiyar su Maryam ,da kuma rashin Adalcin da Hukuma sukayi masu hakan yasa ya dage akan sai ya taimaka Masu, shike taimaka musu akan wasu abubuwa Dukda ba koma suke bari ya sani a lamarin ba, shine ya kawo shawarar Zeeyk ya aura wa Kanwarsa saleem, tunda yaga reaction dinshi sanda aka harbeta, yasan yana sonta, Kuma ya ƙuduri aniyar hada auren kota halin ƙaka, don yasan Soyayyar Maryam ita kadai ce zata iya Gyara Saleem.

Yasan bai iya son abuba kuma yana matuqar wahala idan yana neman abu bai baisamu ba, shysa ya kawo shawarar a hadasu kawai Dukda yanada tabbacin Hakan babu wani taimakawan da zai musu a tafiyar tasu, Amma da yake yasan Kan duniya baisha wahala ba wajen shawo kan Zeeyk ya Amince, shi kuma Zeeyk ya shawo kanta Har ta amince sukayi Auren.


Yanzu haka , Ashman ne ya saka ma Baffa strong Pill a Shayi har Yayi Affecting kidney dinshi, kuma shi ya bada Shawarar akaishi asibitin Abba, shine ya kashe CCTV ta Yanda ba za'a ga Shigowan wani ba, ya kuma cire Kidney ɗin baffa Mai Kyau, ya barsa da mara kyau akayi masa dashe da mara kyau, hakan yazo daidai da yanda suka tsara.

Abu daya ke damun Aeesh yanda yayi banza da ita kwanan nan ko kiranta bayayi, ya daina nemanta Gashi wani irin Tsoronsa takeji sosai tana tsoron ta kirashi hakan yasa ta zama wani iri.


Koda Reey tazo gaida Harara ce kadai ta shiga tsakaninsu, Har yanzu bata daina jin haushin ta ba, tana aminiyar ta Amma zuciyar ta na kwadaita mata masoyin ta😒, itama Reey Haushin ta takeji in ma Cin Amanar zatayi tama rasa Wanda Zata so sai Aareef wannan Soloɓiyon yaronnan?.

Tun daga ranar da Ammie ta faɗa mata Aash mijinta ne basu sake zancen ba, Haka itama Aeesh bata tabo batun ba, Infact wani irin Kunyan Ammie takeji, bata yarda ta hada ido da Ita, idan sun haɗa Kou sai ta sunkuyar da nata.

Yau saura Sati ɗaya Curr Tayi graduating, ran Monday Zasu fara final Exams kuma ran Wednesday Zasu Gama , Karatu suke babu kama Hannun yaro, Ya Sadeeq dakansa yaje har makarantar su ya kwaso kayanta, yanzu daga gida take zuwa, kuma har yanzu basu shirya da Reey ba.


Tunda Aareef yaji labarin Ammie ta dawo ya sauko ya fara kiranta, har gidan yana zuwa su gaisa da Ammie ,amma baya samu yayi hira da ita sai a waya don Sosai Aeesh ke tsoron Abinda zaisa Ammie ta gayawa Aareef tanada Miji, tana Son Auren ta da Ashman Kuma tana Ƙaunar Aareef shiyasa ta kasa sanar ma kowa Cewa tana da miji kuma take kula Aareef.


A cewanta tunda mijinta ya gujeta ,ya banzatar da ita hakan bazai hanata kula Saurayinta ba.

Abba dakanshi ya turawa Ashman Mail yave ya dawo, ji yayi kaman Ya tsunduma shi a aljanna, nan take ya kira Waya yace Deejah ta dawo, washe garin ranar Ya shirya a matsayin Ashraf yace zaije UK zaije Saro Kaya....

Koda Deejah ta dawo saida ya sake jan Kunnenta akan kada ta saki yaji Wani maganan da bai dace ba ya fito daga bakinta, a ranar sukaje gidan Abba bayan ya maida kamanninsa Ya dawo normal Ashman ɗinsa, yanda Deejah ta rame ya tsorata Abba, Amma da yayi tunanin Ko ciki ne sai ya koma yana Murmushi yana sanya Musu Albarka.

Daga nan Kai tsaye Gidan Ammie ya nufa, bai tarar da Aeesh ba, tana school yau ne ranar graduation Dinsu, ya Sani don Ya gani a status ɗinta, Amma sai ya ja baya don kada Abba ya tsargu dashi.

Kai tsaye a gida ya Dire Deejah sannan ya nufi makarantar ,ya iske tuni Duk sun fito har an fara sign outs.

Dube Dube ya farayi ko zai ganta, chan ya hango Reey sanye cikin Navy Blue Scrub irin na wasu daga cikin su, Ya Sadeeq na jami'ar jingine da motarsa suna hira.

Karasawa yayi, yaba Sadeeq hannu suka gaisa ya dubi Reey ya tambaye ta ina Aeesh gangs din yan Ajinsu ta nuna mai, tana daga nesa tana ma wasu maza signing Akan Farar Shirt ɗin su, Wani abu yaji ya taso masa ya tokare Masa maƙoshi, da ƙyar yaja ƙafarsa ya nufi inda take, ya wani finciko Hannun ta da ƙarfi suka bar wurin.

Murmushi Reey tayi, ta kauda dubanta daga garesu, ta dubi Sadeeq tace

"Yaa Aash Akwai Kishi da yasan abinda sukayi tayi ɗazu da Aareef yazo inaga Sai dai wata ba ita ba"

Sadeeq yayi Murmushi yace

"Shida Baya Sonta kishin me yakeyi tho?"

Hararar sa Reey tayi

"Waya gaya maka baya Sonta?, Ai ko makaho yagansu Dole a kallo ɗaya zai gane tsananin Soyayyar dake tsakanin su"


Kai tsaye inda ya parka motarsa suka nufa, ya buɗe motar ta shiga , shima ya zagaya ya shiga sam ta kasa hada ido da ashman wani irin Tsoronsa takeji Jikinta babu inda baya Rawa, hannunta biyu tasa ta Dafe kuncin ta don har yanzu bata manta zafin marin da tasha ba.


Shuru yayi yana Huci, ji yake kaman ya huce Fushin sa akanta, da Auren ta take kula wasu maza hardayin rubutu a jikinsu?.

Duban ta yayi da Idanunsa da suka kaɗa sukayi ja, ganin yanda ta rikice ya sashi haɗiye fushin da ƙarfin hali ya saki Murmushi.

"Congratulations Ihty....”


Dagowa Tayi ta dubeshi da mamaki a fuskar ganin Murmushi a Fuskarta yasa ta saki Murmushi a tsorace, ta Dire Hannunta dake kwance a kuncinta tana cigaba da Murmushin.


"Thank You zaujee"

Ta fada tana washe haƙora don Shekara can't hide it, she miss him Alot ji take kaman Ta Rungumeshi.


Zaujee

Kalmar yayi ta maimatawa a ransa, da mamaki ya furta

"Zaujee?"

Waro Idanunta tayi da mamaki ta dubeshi tana mamakin ,mamakin da yayi don ta kirashi da zaujee sai kace ba mijin ta ba?.


Ganin irin kallon da take mishi yasa ya sauke Ajiyan zuciya, yaja Motar suka bar harabar makarantar.


*Maryam*


Biki sukaje, ƙawarta ke aure Muzzammil ne ya rakata dama jiya ya dawo ƙasar.


Dawowanta kenan taga motar sa parke a harabar Gidan , kallon motar take da mamaki tana Tunanin Me zai kawo Saleem gidansu bayan wulaƙancin da tayi masa Last zuwan da yayi?.


A hankali aka bude Back Seat Ayyan Ya Fito sanye cikin Milk yadi an Masa ɗinkin jampa, ɗinkin yayi kyau sosai kuma ya hau jikinshi, kallon yaron tayi take taji gabanta ya fadi, ya rame sosai.


Da Gudu ya rugo ya rungume ta, wani abu mai kaman Shocking Taji ya yi circulating a cikin veins ɗinta.

A hankali ta Lumshe ido tana Sauraron Bugun Zuciyarta.

Kallon Mamaki muzzammil yabita dashi

"Maryam Wannan dan Kuma daga ina?"


A hankali ta ware idon ta dake Lumshe, kai tsaye ta Dire su cikin na Saleem Dake tsaye jikin Motar, take abinda ya faru a haduwansu ta ƙarshe ya faɗo mata.

Saurin kauda kanta tayi haɗi da janye Aayyan daga Jikinta ta juya zata tafi, yayi sauri yasha Gabanta.



Ta kauce zata wuce ya Damƙo hannunta da ƙarfi kaman zai cire mata hannun.

"Maryam Please wait..."

Kiciniyar kwace hannunta take hawayena ƙoƙarin gangarowa a Fuskarta, bata ƙaunar ganinsa ko kadan

"Ka cikani you punk!"

Tafada cikin tsawa

"Bana Son Tsawa don Dare try that to me again!"

Yafada still damke da hannunshi, zuciyar sa na masa zafi

"Leave me alone!" Tafada tana ƙoƙarin kwace riƙon da yayi mata da iya ƙarfinta.

"Kai Malam lafiya?"

Muzzammil ya fada yana kokarin raba hannunsa da nata, wani irin bangaza saleem ya kai masa, sai ganin kansa yayi chan Gefe .

Fashewa tayi da kuka tana kiciniyar kwacewa , hannunsa yasa ya dago fuskarta data jiqe sharkaf da hawaye yace

"Please Come back....I need You back again ..., I promise to be good this time"

yafada yana nishi sama sama kaman Wanda ake janye Numfashin sa.

Cizo takai masa a hannu ,yayi saurin Sakin ta saboda zafin da ya ratsa shi

"I hate you! Na tsane ka bana Sonka, bana Sonka"

Tafada cikin kuka sosai Jikinta na rawa sosai

Tsayawa yayi yana kallon yadda take kukan yana kallon yadda hawayen ta ke gangarowa, ji yayi kaman tana watsa masa Wuta a zuciya, Ganinshi ne bata so ko kalaman sa ne suka sa ta kuka?.

"I..hate..you... Na ...tsane ka..... bana Son Sake ganinka a rayuwata....!, go away"

tafada cikin rawar muryar kuka.

Sosai Kalmar ta dakeshi,ji yayi kaman ta soka masa wuƙa a zuciya, zuciyar sa wani irin racing Takeyi Kaman zata faɗo daga mafakan ta.

Nuna kansa yayi da yar yatsa bakinsa har rawa yake wajen furta

"You hated me Maryam....?"

"Goo and don't come back again"

Ta fada cikin Muryar da kuka taci ƙarfin ta.

Ahankali ya dinga ja baya still idanunshi akanta, Ba ƙafarsa ke janshi ba zuciyarsa ke jansa.

Da kallon Mamaki Muzzammil yake binsu dashi, Ayyan Kou banda kuka babu abinda yakeyi.

Da gudu ta shige cikin gida tana sharar hawaye.

Ji yayi kaman ta cire zuciyarsa ta tafi dashi gaba ɗaya, kansa ne yayi wani irin sarawa da ƙarfi Yasa hannu bibbiyu ya rike kan, Zuciyarsa ta buga da ƙarfi, jiri mai ƙarfi ya jashi yayi baya ya faɗi a sume.....✍🏼



Nayi Gabas 🚶🏻‍♀️

Bintou ✍🏼


19nov
[12/7, 8:26 PM] { Queen_Hernah }: *WUƘA A ZUCIYA*
_(BLEEDING HEARTS)_


*054*



Bintou ✍🏼






Da Gudu Maryam ta shigo, ta Wuce Mama da Baba dake zaune a Parlor Suna hira, ta shige ɗakin ta.

A tsorace Mama ta bi bayan ta tana ambaton sunan ta,amma ina? Ko sauraronta batayi ba ta haye ta bude dakinta tashige sannan ta maido kofar ta rufe ta saka key sannan ta sulale wajen ta cusa kanta tsakankanin cinyoyinta tana cigaba da kukanta mara sauti.

Ta tsani Saleem, ta tsaneshi bata Son Ganinshi, me yasa bazai bar bibiyar rayuwanta ba?.

Saleemah na Zaune a ɗakin tun Shigowan ta ta zuba mata ido tana kallon ikon Allah, ta lura cikin kwanakin nan Kuka baya mata wahala, yanzu ko me ya sameta take wannan kukan oho?, Bata ce da ita komai ba, Sai ta mayi kaman bata ɗakin.

Jin ana bubbuga ƙofa yasa Saleemah miƙewa zata bude, Sai a lokacin Maryam ta ɗago ta watsa mata wani kallon da yasa ta koma da baya.

Duk bugun kofa da magiyar da Bamalli yake mata akan ta bude bata motsa daga inda take ba, kukanta kawai take yayinda kanta ke saramata kamar zai rabe gida biyu.

"Maryam Buɗe min ƙofa nine"

Muryan Zeeyk taji, da gudu Saleemah ta tashi ta buɗe ƙofar abin da ta gani ne yasata komawa ciki da gudu tana Ƙwala ƙara.

Zeeyk ne da Bamalli Sun ɗauko saleem kaman gawa, mamace tace su kai mata shi ɗakin ta, tunda Ita Nurse ce tasan Yanda zatayi dashi, Amma cikin su babu wanda zai kaishi Asibiti in ma mutuwa zaiyi Gara ya mutu a ɗakinta, it's normal dama anfiso Namiji ya mutu a ɗakin matansa.




Zumbur ta Mike tana rarraba Idanunta akansu, ga Ayyan dake biye dasu yana share ƙwalla , kuka yakeyi Amma babu hayaniya ,Sosai zai baka tausayi idan ka Ganshi.

A tsorace Taja dabaya, Nan take tafashe da kuka tana toshe bakinta ita kuma saleemah tadago tana kallon Saleem Wanda A Halin yanzu Zeeyk da Bamalli suka direshi akan Gadon Maryam kaman Gawa.


Muryar Maryam na rawa tace

"Wh...at... Happened to him?"

" Suma yayi, da naba Mama labarin Abinda ya faru tace mu kawo Miki shi kiji dashi, in ma ƙarasa shi zakiyi duk ɗaya"

Inji Bamalli, wani irin kallo Zeeyk ya watsa mata wanda yasata shan jinin Jikinta, Yaja hannun Bamalli suka bar ɗakin.

A matuƙar tsorace Take kallon Saleemah da ke tsaye tana Kallonta, ta kasa juya kai ta kalli inda Saleem ya ke kwance, meyasa mama zatayi mata Haka?😭.

Shi kuma Akan tace ya rabu da ita yake neman Kashe kanshi?, Yaushe ya zama rago?, Yaushe ya zama Mai raunin Zuciya haka?, Yaushe mace ta fara tasiri a zuciyarsa?.


"Aunty Ko in Fita ne nima?"

Muryar Saleemah ta dawo da ita hayyacinta, Hawayen da suka maƙale a Gefen idonta suka gangaro.

Tayi saurin sharewa,ta buɗe baki zatayi magana Da ƙyar gabaki ɗaya Jikin ta ɓari yakeyi tace

"No.. karki Tafi dauko min Ruwa a fridge"

Da sauri Saleemah ta ɗauko ta mika mata, don Ita kanta hankalinta a tashe yake bata Son Ya mutu gashi a yanda yake kwance kaman matacce.

Duban Ayyan Maryam tayi, yana zaune ta gefen gadon inda saleem ke kwance kaman matacce, ya sunkuyar dakansa yana hawaye, ta kauda kai idan yaron Yana wani abin Kaman Ita.

Hannunta sai rawa yake ta kasa riƙe Gorar ruwar, ta miƙawa Saleemah , karɓa Tayi tana Kallonta cikin rashin Fahimta.

Maryam ta Share Kwallan da Suka zubo mata tace

"Salima suma yayi, Please ki yayyafa masa ruwan nan zai tashin"

Saleemah tace

"Aunty badani za'a yi wannan ba, mijinki ne In ma ruwan ne zai farfadar dashi Meyasa Bazaki yayyafa a wuce wajen ba"



Tana kaiwa nan ta Dire Mata Gorar ruwar a ƙasa, ta fice da gudu, Maryam ta bita da idanu hawaye na zubo mata.


Kaman wance akeja da Magnet haka ta haye Kan Gadon, Ta miƙar da ƙafarta sannan ta ɗago kansa tayi masa masauki akan Cinyar ta.

Idanu ayyan ya ɗaga wanda ya cika da hawaye ya shiga kallonsu kaman Daga sama taji yace

"Mummy....why did you hate us?"

Dukda cewa Tausayin sa ya kamata, amma ta kauda kai tana Hade rai, Ruwan hannunta ta bude ta Yayyafa Masa Amma Shuru ko Gezau baiyi ba, sake ɗiga masa tayi ta shafo fuskar sa dashi,nan ma Shuru ne.




Wani kalar sanyi jikin Maryam yayi,ta dafe ƙirjin sa da hannayenta biyu da iya ƙarfinta ta danna Daidai zuciyarshi, Amma kaman ta danna dutse

kanta ta ɗaura saman Ƙirjin sa ta kafa kunne, bataji bugawan zuciyarsa ba, Zuciyarta ce ta fara rawa kodai mutuwa yayi?

Cikeda tashin Hankali ta taɓa hannun sa, Pulse dinshi Yayi ƙasa Sosai and no breathing response.

Nan tak hawaye suka Cika mata ido, tayi saurin maidasu,Dukda bata Son Saleem Amma Bata son Ya rasa ranshi, yayi mata abin da A rayuwa zata so ta cigaba da Ganinshi a raye, hannunta na rawa ta ɓalle Bottom ɗin rigarsa nan Take Fafffaɗar ƙirjinsa ya bayyana,zuwa wannan lokacin kuwa Ayyan Ya fara Kukan a Bayyane.

Hannu tasa taja Vest ɗinsa Gefe kadan Da iya ƙarfin ta ta sake daddagewa ta danna Ƙirjinsa da ƙarfi, nan ma Shuru ko motsi baiyi ba.


Saukar da kai tayi, duk iya ƙoƙarin ta na hana Hawayen ta ɗigowa saida suka sauko mata, basu sauka Ko ina ba Sai saitin Zuciyar sa dake buɗe.


Wani irin zabura taga yayi da ƙarfi, yaja dogon Numfashi, saukar Numfashinsa yasa Maryam buɗe jikakkun idanunta akan fuskarta, tare da zuba masa idanu tausayinsa ya kamata.

A hankali ya fara motsawa tare da dafe kansa dake sara masa sosai, kafin slowly ya shiga buɗe gajiyayyun idanunsa wanda sukai masa nauyi, bai Dire su ko ina ba sai cikin nata ,Da sauri ya sake Lumshe su ya buɗe su still cikin nata.

Hannu tasa Ta share hawayen ta,Ta galla masa Harara wanda yasashi saurin kauda idonsa daga Gareta

Bin dakin yake yi da kallo, Hawayen dake maƙale a idonsa ya ɗigo, Muryarta yaji tana faɗin

"Jarumi baya kuka a soyayya, Barin rayuwar Mutum yakeyi🥺"

Sai yanzu ya Fahimci a inda yake, a dakin ta Kuma akan Cinyar ta, Lumshe idanunsa yayi a hankali ya farajin Ciwon da yakeji yana tafiya, bayan ganin Tsantsan tausayin sa da ya gani a Idanunta wannan kaɗai ya wadatar dashi.

Sake mirgina kansa yayi akan Cinyarta yana Sauke Ajiyan Zuciya, ta ture shi kadan

"Ɗaga Ni"

Bai tashi ba, Sai ma sake Kwantar dakai da yayi yana sakin Murmushi, tasa hannu ta tureshi da iya ƙarfinta.

hakan ya sanya ya ɗaga kansa a hankali suka haɗa ido, ta haɗe rai, ta miƙe ta nufi wajen Drawer dinta ta Buɗe, ta ɗauko Ampoule Analgesic da Syringe

Yana dagowa yaga injection,ya ɓata fuska sosai.

Maryaaam ta taɓe baki a ranta tace

_ji yadda yake muzurai,sai an shiga cikin mutane a dinga jijji dakai amma ana tsoran allura_

Saleem ya Hade Rai, ganin da gaske Maryam take Allurar zata Masa, babu shiri ya miƙe tsaye jiri na janshi zai fita ta jawoshi Ta dawo dashi ya koma ya zauna.

tasan yanda Saleem ke Tsoron Allura sosai don ko sanda Suke Turkish ya taɓa yin dambe da Dr akan Yaƙi Tsayawa ayi masa Allura.



A Hankali takai allurar zata tsira masa, Cak ta tsaya jin an riqomata hannu.

Tsayawa tayi daga yunkurin tsira masa baterada ta ɗago ba gabanta na faduwa.

"Please....., A ha...nkali"

Ya fada Muryarsa na breaking

Shiru tayi bugun zuciyarta na qaruwa sosai, she's feeling somehow, tanajin wani iri sosai.


Dubanshi tayi,yanda ya rufe ido sai taji Ya bata Tausayi.

Jikinshi har wani rawa yake yi,a hankali ta kai Allurar ta tsira masa.

Wani irin zabura da yayi har sai da yasa syringe din hannunta ya fadi, tayi saurin Liliya masa wurin da swab.

Idanunsa a Lumshe sai Cije Lips ɗinsa take,Ji tayi ya bata tausayi , ya ware idanunsa akanta.

Gani tayi ya kafeta da idanu wanda yasata jin wani iri cikin jikinta hakan yasata janye idanu ta sannan ahankali tace

"Kwanta ka huta anjima ka kama hanya ka tafi"


Kaman zaiyi magana kuma ya haɗiye abunsa ganin tayi kicin-kicin da fuska.

Ya bita da kallo ta ƙasan ido harta fice, ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da lumshe ido ya buɗe yana furzar da ɗan huci, a hankali Ayyan ya Hau gadon ya kwanta haɗida dora kansa a ƙirjin Abban nasa.



*Aash Aeesh*

hankali yake driving ɗin tamkar baya so ko kuma shi kaɗaine a titin, motoci da yawa sai sun masa horn yake ɗan kaucewa ya basu hanya su wuce, ga Aeesh sai faman Surutu take masa. Sai dai ko amsata bayayi, cikin Surutan nata take bashi Labarin yau tayi girki kuma Aareef tayi mawa, cikin Surutan ta Abinda yafi daukan Hankalin sa kenan Don yasan Aeesh bata girki , bata Kuma taɓa kwatantawa ba.

Yawu ya haɗiye da ƙoƙarin saisaita kansa sai a lokacin ya tanka Mata yace

“me kika dafa masa?”.


“fried rice”.

Ajiyan Zuciya yayi yana shafa kansa da lanƙwasa kan motar ya shiga layin gidansa.

“wow kenan kin iya Girki...?"

"Ohhw daukan ka ban Iya ba?"


Shuru yayi tace

" Hmmm ban baka Labari ba, in Gaya maka saida na gama Girkin na kai masa Yace bazai ci ba, Babu Sipili akai Kaji fa, Shi ya aike Ni?, Ni Kou nace in Bazai ci ba ya ban Abina na maida Shi kenan wai yayi Fushi...."

A hankali ya tsaida motar a ƙofar gate, sai dai baiyi horn ba, don labarin da take bashi Sound somehow interesting

“he don't know What I went through before Providing The food , yau inada Exams Amma Jiyan nan Ni kadai naje kasuwa Na siyo kayan Abincin babu wanda ya min Rakiya, na kashe more than 10k akan Abincin amma maimakon Na samu Yabawa daga gareshi saidai Akasin Haka!”.


Tamkar wanda aka zarema lakar jiki haka yayi baya luuu jikin sit ya kwanta,ya Lumshe idanunsa da suka canja launi .

Daidai lokacin da wayarta tayi Ringing, Duban Ashman Tayi kafin ta dubi wayan tace


"Ahky kaga Ɗan halal shine, bari in ɗauka inji Ƙila haƙuri zai bani"


Ta fada tana kara wayan a kunne bayan ta daga

“hel.."


"Ke wace irin Jaka ce?, Ke wace irin jahila ce?, Dakilancin ki har ya kai ki ari wayan namiji ki kirani dashi "


Saukar da murya tayi Dukda taji zafin Maganganun sa tace

"Kayi haƙuri Sadauki Wayana babu Credit ne, shiyasa Na Ari Wayar Yaa Sadeeq na Kiraka dashi, da naga baka ɗaga ba Sai na haƙura nayi maka beep da wayana....amma kayi haƙuri"


Maganar Takeyi kanta a ƙasa Muryarta har wani rawa yakeyi, Ahankali Ashman ya ware lumsassun Idanun sa da suka kaɗa sukayi ja ya zuba mata, sai hakuri take bashi shi kuma Aareef daga chan ɓangaren yana mata fada kaman Uban ta , Yaƙi ya haƙura sai Kumfar baki yakeyi, idan ta cigaba da bashi haƙuri tabbas zuciya zata iya kaita Inda zatayi nadama ,hakan Yasa tayi Shuru Ta sunkuyar dakai Tana jinsa, shurun da tayi ne ya sake hanzuƙa shi Ya zagi Ammie, ya kuma ce batada Tarbiyya.

Ya tabo Daidai Wurin da bazara iya jurewa ba, a fusace ta katse shi ranta a ɓace

"Dakata Aareef, I can't continue Arguing with you every day,kana Cin Mutuncin iyayena, this relationship is no longer Healthy, it's either we break up and be friends or you Erase me from your Life, bazan iya jure cin mutuncin iyaye na daga gareka ba"

Ran Ashman a ɓace ya ɗan Lumshe Idanunsa ya ya buɗe akanta, sai yanzu ya lura da wayan hannunta, ba wanda ya siya mata kwanaki bane.

Maganganun Aeesh ba ƙaramin kada Aareef yayi ba,Ko kadan baya Son su rabu a yanda yake gwabzar banza

Please Login or Register in order to submit comment