Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ƙwalla ta tare gaban shi tana bashi haƙuri...

Kallon Rainin Wayo yayi mata ya raɓa Gefen ta ya wuce Batareda yace da ita komai ba, a ransa yana ayyana rashin zuciya da rashin Aji irin nata,shi koda ace batada aure bazai iya aurenta ba Saboda sam batayi tsari da irin matan da yake so Ba, ba kuma zai iya auren Macen da tabar Tarihin bin Zuwa gidan namiji bada haƙuri ba a rayuwar shi.

Yana Shigewa ya rufo ƙofa, Bash ya leƙo ta window yace

"Inma zaki tafi ki tafi tun wuri, Don A halin yanzu Arrow bashida Appointment dake"

"Don Allah Bashir kace masa ya ara Min Koda Minti ɗaya ne, I'll value it no matter how please..."

Basheer yaja Tsaki

"You're Not serious"

ya rufe Window yana jan tsaki.

Bubbuga kofar ta shiga yi tana Kuka tana bashi haƙuri yayi haƙuri ya dawo Rayuwarta, kar ya rabu da ita, Amma yanda kasan ba Mutane ne a Ɗakin ba, babu wanda yabi takanta.

Da ta gaji ta samu wuri ta zauna tana maida Numfashi, a hankali Cikin ta ke murɗawa irin Murɗawan da bai taɓa yi ba, Zuciyar ta taji yana tashi, a hankali ta zame ta nufi wani waje da babu mutane kanta na wani irin juya mata ga wani Juyawan da cikinta keyi at the same time, duƙawa tayi a wurin Amma aman yaƙi Zuwa.

zama tayi tana jan numfashi Idanunta yayi jaa sosai da ƙyar take buɗewa, zamanta ke nan taji aman, kakarin aman ta fara amma yaƙi fita sai wahala take sha, gashi babu kowa a Wajan da ƙyar ta miƙe tsaye tana ƙoƙarin tafiya Jiri najan ta, ta Koma bakin Ƙofan ɗakin shi ta duƙunƙune ta cure Guri guda, Batareda ta damu da tafiyan Daren ba, Burin ta kawai Tayi ido huɗu dashi ta bashi haƙuri yace ya yafe Mata bakuma taso ya kwana da ɓacin rai, Hakan kadai shi zai sa ta iya rintsawa a yau dinnan.

Jikinta yayi Nauyi,bata Iya ɗaga koda dan yatsanta ne, Numfashi take saki sama Sama ga wani irin Yunwa dake gallabar yan hanjinta, tana nan Zaune banda Kakkarwa babu Abinda takeyi.

3:35Am. ↩️🔙 *PG1*

Dare yayi Nisa sosai, Baka jin sautin komai Sai Na tsuntaye, The sky was aglow with bright city lights, wata da Taurari Sai Walqiya Suke Kaman azurfa a sararin samaniya Jefi Jefi haushin karnuka Na Ratsa Ni'imtaccen Shurun Daren Hasken street light ne Mamaye da ko Ina na fadin Anguwar.

Unguwar kaman an share babu kowa, babu abin hawa babu ko tsuntsu,ita kadaice tana nan Zaune ita ɗaya ta kasa Ɗaga koda yar yatsanta ne saboda wani irin Nauyi da yayi mata, tsoro ne Cike a Cikinta,Amma ko kadan zuciyarta ta gaza Sarewa da lamarin ,har yanzu Bata fidda ran Fitowan shi ba, gani take zai iya fitowa a kowane lokaci ya kumace ya yafe mata.

kofar ɗakin Kamal data ji an bude ya sa ta kamewa daga inda take durkushe lkci daya ta xaro ido tsoro ya kamata a tunanin ta babu Kowa a ɗakin.

Motsin da yaji ne yasa ya kai dubansa kanta yana haskata da Yar touch light dinshi.

"Subhanallah Aeesh me kike yi anan Cikin daren Nan to 4aM fa."

Shima a tsorace ya faɗi hakan don Zuciyarshi bata tabbatar masa da ita dince ba.

Cije Lips dinta Tayi cikin azaba, Hawaye suka gangaro mata, ta miƙe da ƙyar kanta na sara mata ta nufoshi.

"Uncle Kamal please Tell him ya fito Muyi magana bazan iya Komawa Gida yayinda yake fushi dani ba "

Ta qarashe cikin breaking Voice haƙoran ta na hardewa.

Sosai Aeesh xata baka tausayi Sbd gaba ɗaya Yanayin ta ya koma Gwanin ban tausayi.

sakin baki Kamal yayi cikin Mamakin Da ya gaza ɓoyuwa a Allon fuskarsa, Taya zai yarda ita dince Ma?, Kodai Aljannu Ne suke Neman Suyi masa Siddabaru ba?.

Da touch din Hannunsa Ya haska ƙafafun ta yayi don ya tabbatar da ita din ce, tabbas itace, ya haska fuskar ta, tasa hannu tana share hawayen dake bin fuskarta...

Girgiza kai kamal yayi yace

"Karkice Min tun bayan isha''i Dana jiki dashi baki koma gida ba"

Numfashi Aeesh taja ta kasa ce wa komai sai hawaye da sukafi 'karfin ta.

Kamal jiyayi tamkar yamata kuka, tausayi take bashi ainun, wannan wace irin Masiface? Akan soyayyar 'da Namiji Mace ta kasance a waje har wannan lkcn? ,In Ka bibiya ma Abinda ya hadasu bai taka kara ya karya ba.

Tabbas Aareef yana bata wahala sosai akan soyayyar Shi, Don yaga tana Sonshi sosai, ta nuna masa Soyayyar *kaine rayuwata* shi ko a labari bai taba ganin Irin soyayyar da Aeesh take nuna ma Aareef ba bata iya sarrafa kanta akan shi ba at least even For once ta nuna masa ita mace ce ko zaiga girman ta.

Aareef bai cancanci Soyayyar gaskiya irin haka ba, kodan Fasiƙancin da yake aikatawa da yaran Mutane.

Aeesh duk tagama canja kamanni, tarame sosai, Ga uban haske datayi sai kace Ba Aeesh ba, a halin yanzu ko mak'iyinta ya ganta dole ya tausaya mata

Kamal hawaye na Cika masa idanu yace

"A haka Arrow ya shige ciki Ya bar ki a waje?, Kuma yasan kina nan? "

Kai tsaye tace

"Yasani "

Duban Unguwar yayi, yana ayyana ƙarfin Zuciya irin nata, What if something Wrong happened to her?, Bata Tsoron a saceta?, Bata Tsoron wani Wani abu ya cutar da ita??, Bata Tsoron sharrin ɓata garin Maza su mata fyaɗe ?, A irin daren Nan da babu kowa a cikinta babu Abinda bazai iya faruwa ba, amma da alama duk bata tunanin Waennan Ƙwaƙwalwar ta ta riga ta cushe da soyayya.

Lumshe idanunsa yayi, ya dubeta itama shi take kallo

"Ya kamata ki koma gida, zamanki anan nada Had........"

"You're not helping Please You can Go"

Ta dakatar dashi hawaye na fita a Idanunta.

Dubanta yayi da mamaki ,ta kauda kai hawaye na zubo mata tace

"Idan bazaka iya Hada ganina da nashi ba, You can Go please"

Cikeda Jin tausayinta Ya shiga bubbuga ƙofar Batareda yayi la'akari da Amsa kowwar Yake yi cikin daren ba,amma yanda kasan matattu ne a ɗakin.

Duk bubbugar kofar din da'ake yanaji amma beda kuzarin motsawa, he's so weak har cikin zuciya, jinshi yake kamar marar lakka ga barcin dake jan shi.

Saida Kamal ya haɗa da Roko da magiya da dabara Sannan A fusace ya miqe yana jan tsaki tareda duba agogo qarfe 3:52am

Ransa a ɓace ya buɗe ƙofar, Kamal Najin Alamar ya fara bu'de 'kofar yayi azamar Shigewa Dakinsa da 'yar Butarsa don baya Son abinda zai Kai ya kawo, a ɗakinshi yayi Alwalar yatada sallah.

Aareef na hada ido da ita yaji Gabansa ya fa'di, Shi fa har ya mance da ita fa.

Girar sama da ta qasa ya hade ya Kauda fuska rai 6ac3 yace

"Bakida hankali ne?, Me kikeyi anan cikin Wannan daren?"

"Sadauki Please............. "

"Wait Tambayan ki nake Me ya kawoki nan Cikin Daren Nan?, wae ke wace irin Mayya ce? "

Hawaye na Zubowa tace

"Beer har yanzu Baka haquraba? "

Wani kallo ya watsamata sannan yaja dogon tsaki yana cewa

"Tambayanki nake Mey kikeyi a Nan at this time of night?, Wai ke wace irin Mahaukaciya ce?, a haka kike so Na Aureki?, in Na Aureki ince Na Aura me kenan? rashin Aji?, ko Rashin Kamun kai ko Kuma Yawon dare? "

Dago jajayen idanunta tayi Duk ilahirin jikinta rawa yake zuciyarta Na bada wani irin sauti Na bugawa kanta na sarawa. Ga hawayen dasukaqi Tsayawa dubanshi tayi da Watery eyes ɗinta.

"Sadauki don't you see that you are over reacting?Albeer Ni kk kira Mahaukaciya…?, Ni kake Alaqantawa da munanan kalamai haka?, Ni zaka tozarta Aarrow?, I have been waiting for u Since 8:30 just to hear the word of forgiveness from u, a ganina I don't deserve All these From you, All I need is forgiveness, pease... please Don Allah... Please forgive me on Reeyyer's Behalf 🙏... "

Ta Dan dakata don saisaita Numfashin ta dake siezing, fuskar ta cikeda ƙwalla tace

"I payed for happiness please Don't break our promise "

KO kadan bai ji digon tausayinta ya dirsu a ransa ba illa ma 'kara haushin ta da taji, kenan tazo wajenshi ne da yaƙinin Zai yafe mata saboda Kuɗaɗen da take bashi, kenan Gori zatayi Masa?.

Yayi mata Kyakkyawar kallo a wulaƙance

"Awww Gori zaki Min ?,akan kin bani wasu 'yan chanji for us to be happy❓, Amma Ina so ki tuna wani abu!, Ban taɓa roƙon Wani abu a Wajen ki ba don haka Bakida ikon da Zaki min karar tsaye akan wasu yan changi ,and let me Tell you Something Yes na ci kudin kine don Buƙatarr ki, and Right now Subscription Din ki ya qare baki da hurumin In yafe miki, bayan Cin mutuncin Da kika Turo ayi min"

"Wlhy bani na Turo ta ba..."

"Shut up bake Kika turota ba,Amma bake na Kira a waya ba kika bata wayan donta ci Min Mutunci?"

"Sadauki but i paid I don't deserve this"

"Wait are still talking about the money you gave me?"

Ya Fada cikin kafeta da sleepy eyes dinshi sannan yace

"Ina so ki san wani abu !,bakikai standard din zaki Siya haappiness Dina ba koda daidai da second dayane, taimaka miki nake yi Ina amsar Kudinki, amma Bakida wannan quality din, and also kudinki basu isa susani yafe Miki ba saboda I don't fucking care about your f**king money! Ke suka Dama ni ko ajikina, lastly kisan wanda zaki dinga bibiya dadaddare domin yayinda kike bin wasu kamar karya kina ikirarin kin zo bada haquri wasu a lokacin Suke sanin kin wanzu a duniyarnan , koda Wasa karki Sake Nuna kin Sanni, Ni Aareef nace na fasa Soyayyar in kinso ki kaini kotun duniya, nace bana sonki kiyi zuciya kema ki ƙyale ni, mutum da mijinta Amma sai bibiyan samarin Mutane, ....ki kyale Ni Na Huta nima dole ne?"

Kallonshi take Jikinta ɓari da kakkarwa kawai yake idanunta na juyewa yana yin wani irin kalar launi, yayinda takejin kamar ana buga mata guduma a tsakiyar kanta ga cikin ta dake daɗa kaimi wajen Murɗawa, Jikinta na wani irin rawa haƙora ta har hardewa sukeyi wajen fadin

"... Ni...."

Batareda yaji tausayinta ba yace
"Eh din ke, ke uwata ce? , if u wish Ki kwana a nan don't go home I don't fucking care!, Ba laifinki bane laifin Iyayen ki ne da suka Gaza baki ingantaccen tarbiyya, basu damu susan ya Rayuwar ki take ba BASTARD! "

ya 'karashe maganar da shigewa ciki banging kofar da karfi yayi Shigewarsa.

Har tsakar kanta taji zagin da yayiwa iyayenta dakuma bugawar kofar ako da yaushe bata Ganin laifin sa koda Me yayi Mata Amma ayau ta6o Iyayen ta da yayi yasa taji zafin maganganun Sa sosai, take taji bugun zuciyarta na daɗuwa.

Bin inda yabi da Kallo tayi kamar zai dawo wajen.

Kalaman sa sai faman yawo suke Mata a qwaqwalwarta.

ji tayi Kafafunta sunyi sanyi, Wani irin yam, yam takeji yana yawo a jikin ta, tanaji kaman ana Ɗagata sama Izuwa wata duniyar Cikin takaitaccen lokaci Duhu ya Mamaye Mata ganin ta tayi baya ta fa'di ƙasa sumammiya.



A hankali ta fara dawowa haiyacinta, sanyin AC taji yana ratsata, tayi kokarin bude idonta taji yayi mata nauyi sosai, ta motsa hannayenta kadan tana son ta dawo da karfin jikinta, muryar Matar Baffa taji tace

" A'isha? Indo kina ji na?"

Ta dan bude idonta kadan ta kalleta, da sauri ta taho ta rike hannunta fuskarta tayi ja cikeda tausayinta, ta danyi kokarin yi mata murmushi amma ciwon da kanta yake mata yasa murmushin ya zama kamar kuka.

A hankali ta fara bin dakin da kallo, asibiti ne kuma da Alama asibitin Ashman, ga drip a hannunta, Matar Baffa tana zaune gefenta

Saleem yana daga can baya ya jingina da jikin bango, tsantsar tashin hankali ne a rubuce a fuskarsa, Lumshe idanunta tayi

_Ni Areef nace na fasa Soyayyar_ kalaman Aareef suka dawo mata.

A take hawaye ya fara kwaranyowa daga idonta, _innalillahi wa inna ilaihirrajiun hasbinallahu wani'mal wakeel_ , Allah kasa mafarki nake yi yanzu a tashe Ni ace min ba gaske bane ba.

Amma ganinta a asibiti shi ya tabbatar mata da gaske ne, Allah sarki Ni marainiyar ALLAH, But Aareef why? Menene kakeso daga gareni da banyi maka ba? Na baka kudina na baka zuciyata na baka rayuwata what else did you want?, Ko sai Na baka Raina zaka gane irin tsananin sonda nake maka...

"Ke Dalla Rufe ma mutane baki"

Saleem ya dakatar da ita cikin jin haushin kalamanta.

Ta dafe baki tana zazzare ido

Tsaki saleem yaja yace

" Your mum is back"

Yayi mata Albishir yana bin fuskar ta da Kallo, yana Gida aka Turo Ambulance daga asibiti a dauko shi ya sami Emergency call, Suna gabda isa asibiti ya hangota tana roƙon Aareef , a gaban Idonsa Ta faɗi ta suma, Shine ya taimaka ya kawota asibitin, kafin nan yayi iya ƙoƙarin sa wajen ganin ya samo Numfashin ta amma abin ya faskara dole tasa aka bata gado.

Tun jiyan take kwance bata san inda Kanta yake ba, ɗazu Su Ammie Suka dawo daga Canada , dawowan bazata don babu Wanda yasan da dawowan su da samun Saukinta.

Haɗiye Maganar ta tayi tana cigaba da zazzare ido, don bata masan a fili tayi maganar Ba.

Ta waro ido cikin zaƙuwa tace

"Ammie na?"

Ya Lumshe ido, ya kuma budewa alamar Eh hakan da yayi ya tuna mata da Aash, take ta tuna cewa akwai Ciki a Jikinta, ta tuno Ammie zata iya Ganewa da kallon farko, duban Matar Baffa tayi taga Fuskar ta normal.

Shuru Tayi

_Allah yasa basu gano da cikin ba_

Muryar ta na rawa tace

"Ina Ammin nawa take?"

Dafata matar Baffa tayi,

"ki kwantar da hankalin ki, Ammin ki ta samu lafiya tana Gida, yanzun nan ta dawo tana bukatar hutu ne kaman yanda kema kike buƙata"

Daga inda saleem ke tsaye banda Harara babu Abinda yake auna mata, babu Shiri ta sunkuyar dakai tana wasa da yan yatsunta, ta haɗiye zumuɗin ta.

Koda saleem yawota Asibiti saida ya koma gidan Aareef Ya haɗa masa Jini da Majina a halin Yanzu Yana nan Kwance shima a asibitin a EClinic.

Tunda Su Ashman suka sauka a ƙasar Mexico ya Dire Deejah a Masaukin ta Bai sake waiwayan ta ba, Koda ta Kira wayanshi cewa yayi aiki ne yayi masa yawa kuma idan ta sake ta taka kafarta ta fita daga gidan da ya Sauke ta a bakin auren ta tunda babu abin da zata buƙata, akwai komai a gidan abinci ma kullum kawo mata ake .

Zaman ta ita kadai ba karamin damun ta yake ba ,rayuwa take ita kadai kaman mayya, Da ta tashi Saidai ta kalli TV tayi video calls da Kawaye da Abbanta sai ta koma bacci daga nan in ta farka taga dama tayi sallah, in kuma taga dama bayi zatayi ba haka nan zata koma ta kwanta.

Ita da tazo Mexico Don Yawon buɗe ido da masoyin ta, Amma sai ta ɓige da zaman kadaici a gida ita ɗaya?, Gashi Sharadinshi yayi mata tsauri da yawa tana Fita ko taƙi ko taso auren su ya rabu kenan ,ba abin ta gaya ma Daddy ba daddy ya Dau matakin da bazaiyi daɗi ba.

Abba na chan ya saki Baki a cewan sa wannan itace mafitan da zata hada kan Ashman da Deejah, kullum sai ya kira Ashman yaji ya suke, idan ya nemi ya hadashi da Deejah sai yace ai Tana hutawa ne, Abba bai taba Damuwa da hakan ba.

Yanda Deejah take a takure haka Shima Ashman ,yanda yayi isolating Deejah Shima haka ya ɓoye kanshi Baya jin dadin Jikinshi ko kadan ,ciwo yakeyi a tsaitsaye, kewan Aeesh yakeyi sosai yana Son jin ya take yana Son Yasan ya ɗan sa na cikinta yake!, Amma Abba bai bashi damar kiranta ba.

Ya kuduri aniyar komawa Nigeria kota halin yaya, kuma baya so Abba Ya gane hakan, ya Rasa ya zaiyi .

Fitowan sa kenan daga Kitchen Hannunsa riƙe da Plate ya Nufi Dinning, Kaman daga sama sai wata dabara ta fado masa.

Wayarsa ya dauko ya kira layin Ashaff a bugu na uku ya ɗauka da sallama, Amsa sallamar Ashman yayi, Rabeel Najin Muryar ya gane shine.

"Sufyaan ya Akayi"

Murmushi kawai Ashman ya dauki spoon ya debi abinci yakai baki.

"Twin Kana Ina ne?"

Ashraff yace

"Ina Nigeria off course da wata matsala ne?, Ya naji muryarka wani iri bakada lafiya ne?"

"Lafiya kalau, Please yaushe zaka bar ƙasar?"

Ashman ya faɗa yana sake kai wani Abincin bakinsa.

Dan Jim Ashraff yayi kana yace
"Akwai wasu kaya da nake Son In duba a UK inshallah Zuwa Next week, me ya faru?"

Ashman yayi saurin Dire spoon din hannunshi Yace

"Woww Kasan yanda za'a yi?, Kada ka gaya ma Abba zaka bar ƙasar, idan ka tafi Sai Ni in taho na zama a madadin ka!"

"Ban gane ba"

"Zanyi maka Bayani later...!"

Kit ya datse Wayar ,ya buga Tsalle

"YES...! ,Yes!!Wayyo dadi kasheni!"

Yafada cikin farin ciki sosai.

Saida ya Gama Murnar shi sannan ya sake kiran Ashraff ya shaida mishi shirin shi, nan suka shirya yanda za'a yi Ashman ya koma Nigeria bayan Ashraff ya baro NIGERIA ,Amma fa da ƙyar Ashaff y Amince don Ashman dan Rashin Mutunci ne, bashida mutunci ko kadan.

Bayan Sun tsara komai ,Ashman ya kira Abba yace zasuje UK shida Matarsa yawon shakatawa ya fadi hakan ne don kar Abban yace zai kawo musu Ziyarar bazata, ran Abba yayi fari Murna yake yana Sa masa Albarka.

Ashraf bai gayawa Kowa zai bar kasar ba, jirgin su Ashman na sauka a Nigeria jirgin Ashraff ya ɗaga.


Tunda Maryam ta fita daga gidan Mama, bata sake dawowa Ba a tunanin Mama ta koma gidan Mijinta ne.

Amma har yanzu tana Zaria , masarauta wajen Kakaninta.

Tuni Matan Yayyin mahaifinta dake zaune a masarauta suka Fara shawarar yanda zasuyi Su cusa mata ra'ayin Auren Muzzammil don yaron Ya addabi 'ya'yansu Kuma baya kula wata mace har su zauna suyi hira sai ita, in kaga yana dariya da mace Tho mahaifiyarsa ce ko Ita Maryam din.

Fitowa hajiya Fa'iza tayi daga part d'inta ta tanufi part d'in mama (Mahaifiyar Abban Maryam)

zaune tasameta tanata gaisawa da baƙi da suka sauka Jiya

zama hajiya Fa'iza tayi daga gefan Mama murya ƙasa tace

" mama dama wani tunani nayi nace yakamata asamu Wanda zai zauna da gimbiya ɗiyar Ɗanki da ɗan yarima Wato muzzammil sabida a samu zuri'a daga garesu "

shiru Mama tayi nawani lokaci don ta fahimci inda zancen nata ya dosa sannan tace

" to ai Fa'iza akwai hadimai dayawa a gaban mu, kinsanfa halin Bamalli bayason takura kwata kwata "

murmushin takaici hajiya Fa'iza tayi tace

" haba mama ai baza'a biye ma yara ba, Kamata yayi a hada hidimar nan da wanchan Ayi kawai"

jinjina Kai mama tayi tace " kuma hakane to amma gani nayi Shi Muzzammil din bai isa aure ba"

ajiyar zuciya hjy Fa'iza tayi tasake cewa

" haba mama ai Muzzammil ba yaro bane "

duban ta Mama tayi tace

"Ina nufin Banga Alamar soyayya a tattare da su ba shiyasa"

had'e fuska hjy Fa'iza tayi tace

" to mama soyayya kam ai a bayyane take, sai dai in akwai wata Dalilin da yasa bazaki aura masa ita ba, nasan duk hukuncin dakika yanke yazartu idan har ba kema bakison Auren bane "

ajiyar zuciya Mama tasauke tace " shi kenan zan zaunar da yaran inji ta bakinsu Tukunna....!"






Alhamdulillah......


SINCE GOBE BABU UPDATE,
PAGE QUESTIONS AND ANSWERS NE.

ZAKU TAMBAYI CHARACTERS DIN TAMBAYOYI A COMMENT SECTION SAI IN ANSWER MUKU A NEXT UPDATE HOPE KUN GANE ABINDA NAKE NUFI? SANNAN ZAKU IYA TAMBAYANSU KOME KUKESO.
ZAKU IYA BA KO WANENSU SHAWARA AMMA QUESTION FIRST

CHARACTERS DA ZAKU TAMBAYA SUNE KAMAR HAKA:
1. Ashman
2. Aeesh
3.Saleem
4.maryam
5.Abba
6.inna Yathai
7.inna saude
8.deejah
9.Reey
10.Aareef
11. Zeeyk
12.Sureey
13. Alhaji Faisal
14.Ammie
15.BarrHamza
16.Matar kawu

Da fatan zaku tambayesu ?

Ku tambaye su ina nan At any moment zan baku amsohin ku inshaAllah 😘


Nayi Kano 🚶


Alhamdulillah End Of part2


Bintou ✍🏽



10th Nov

*WUƘA A ZUCIYA*
_Bleeding Hearts_




Part 3


*051*

Suna Asibitin har Bayan Azahar, saleem na dakin Har yanzu ko fita baiyi ba, zaune yake hankalinsa na kan wayarsa.

Aeesh ji tayi gaba daya ya takura mata, sai jan tsaki take ƙasa ƙasa, Yunwa takeji Matar Baffa ta bata abincin Amma ta kasaci saboda Kwarjinin da yayi Mata , ga wani mugun Tsoron sa da takeji ji take Kaman a ƙaya take,Ta rasa me ya hanashi fita, gashi Sai kiraye kirayen sallah Akeyi amma ko motsawa baiyi ba.

"Mtswww "

Ta sake jan Ƙaramin Tsaki

Dubanshi Matar Baffa tayi Bayan ta idar da nata Sallar, tana Zaune kan sallaya

"Kai bazaka yi sallar bane?"

yayi mata banza Kaman Baiji ta ba, itama sai bata sake tanka Masa ba, tana mamakin hali Irin na Saleem .

Taɓe Baki Aeesh tayi, a ranta tace

_kema dai Allah ya ƙara! ce miki Akayi bashida Hankali?, Sallan ma sai an Tuna mishi sai kace yaro?_

Saida yaja 2 mins sannnan Ya Tashi ya fice Batareda ya dubesu ba.

Yana fita tayi saurin sakkowa daga Saman Gadon, ta zauna gefen Matar Baffa dake zaune kan Darduma

"Yawwa Ummy, Ina Abincin da kika ban dazu?"

Matar Baffa ta dubeta cikin nazari tace

"Ba kince kin ƙoshi ba?"

wani irin marairaicewa Aeesh ta yi tare da ɗan kwaɓe fuska a shagwaɓe tace

"Ni dai yunwa nakeji Sosai"

Matar Baffa dakanta ta jawo Flask ta zuba mata abincin ta miƙa mata, karɓa tayi Murmushi fall a Fuskarta kaman Abin Arziki.

Duban Abincin take tana jujjuyawa tana taɓe baki, take Murmushin Fuskar ta ya ɓace.

Matar Baffa dake lura da yanayinta tace

"Ya akayi?"

"Abincin yayi Sanyi"

"Da duminsa ci kiji, Nima ban daɗe da cinshi da zafinsa ba"

Kwafa Aeesh tayi kaman Zatayi kuka, ta Dire plate ɗin tana Turo baki

" Na ma manta,Ashe bana cin Shinkafa "

Ummy ta girgiza kai cikeda tausayin Aeesh

Aeesh ta ɗan yatsine Fuska

"Whly Tuwon Masara nake Son ci, bakina babu dadi"

Matar Baffa tace

"Ko bari saleem ya dawo sai na koma gida, inna tuƙa nadare sai in kawo miki"

Aeesh ta gyara zama Murmushi manne da fuskar ta ,tace

"Yawwa Ummy wai da gaske Ammie ne ta dawo?"

Cikin Murmushi itama ta bata amsa
,
"Eh ta dawo mana, dazu ma yayanki Sadeeq yazo amma sun Fita da Kawarki Juwairiyyah"

Aeesh ta waro ido

"Reey ma tazo? , Kai Amma anyi manafuka, shine bata jira na farka ba?, Nide banyi dacen Ƙawa ba"

Murmushi kawai Matar Baffa tayi, tana cigaba da jan Charbinta.

Dafe ciki Aeesh tayi jin hancinta na wani kaɗawa, so take tayi wanka tayi sallah Amma yunwan da takeji ya kasa bari ta tashi, Muryar ta Kaman zatayi kuka tace

"Wlhy wani Mugun yunwa nakeji"

Tayi magana Tana Kauda dubanta akan Matar Baffa, ta sunkuyar dakai hawaye suka sauko mata.

" kila na kusa mutuwa ne ban sani ba, Allah idan na jinkirta ban Ci Abinci ba Mutuwa zanyi"

Tayi maganar Muryarta na rawa sosai


Tashi ummy tayi tana Gyara mayafinta, tadau sandarta

" bari inje bazan Jima ba kinji ki kula da kanki"

Dubanta Aeesh takai kan Ƙafarta dake jone dana Na Roba,tausayin matan ya kamata.

Take Rasuwar Baffa ya dawo mata Sabo, abubuwan da suka faru a ranar da zai rasu ya dawo mata.

Wasu zafafan hawaye taji sun Sauko mata, gani take kaman itace musabbabin komai , gani take kaman itace tayi Silar Rasuwar Baffa da ma 'ya'yansa ta kumasa ummy ta zama mai kafa ɗaya, gani take ciwon Idon da Ashman ke fama dashi, wanda ya samu a ranar da Abin ya faru duk itace Sila, da batayi ma Bamalli alƙawarin zata aureshi ba da duk Abubuwan nan Basu faru ba, ji tayi ta tsane Kanta duk tayi hakan ne don ta kare mutuncin ta, gashi Mutumcin da take ƙoƙarin Karewa Ashman ya ɗauke shi a karon banza.

Komawa tayi tayi locking kofar tana Share hawaye, kayan jikinta ta cire ta shige wanka, ta fito ta shirya cikin Doguwar Riga, ɗaya daga cikin kayan da Ummy taso mata dashi, ta gyara gashinta tayi packing ya sauko mata har tsakiyan bayanta har a lokacin jin cikinta take kaman ɗan cikin nata nashirin Fitowa don Yunwa,tana yatsine fuska ta saka hijab ta fara ramuwar sallolin da ake binta.

Ta na idarwa taji anyi knocking nace "am coming" kafin ta karasa kawai taga an bude kofa an shigo, ta tsaya tana bin shi da Kallo.

Harara ya zuba mata, Wani kallar kallo yake binta dashi baice komai ba

Ganin leda a hannunshi yasa ta saki Murmushi

"Sannu da dawowa"

Taɓe baki yayi

"Ke zanyi ma sannu..."

Daga nan ya wuce,

Please Login or Register in order to submit comment