Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsiya ta tusa masa shi "oya tauna ka haɗiye!"

Hakanan Ya Shiga tauna yana Runtse idanu,Fuska a Dame .

Dariya Security dinsa Kwashe dashi yace

"Lallai Oga yau ka gamu da Mace daidai dakai da Alama Tasan ka a Wani waje ka shuka mata rashin Mutunci ne,Don Haka bazan shiga tsakani ba, tayi yanda ta ga dama dakai"

Haka Maryam tayi ta Cusa masa Kazar yana haɗiyewa Cikin Azaba, Harshen sa kaman Zasu tsage saboda zafin Yaji, Bata saurara masa Ba saida ta tabbata ya Cinyeshi tassss.

Numfashi yayita saukewa Sama Saman kaman Mai shirin Shiɗewa Cikin Fitar hayyaci.


Waiwayawa tayi Taga babu Kowa , sannan ta dau wayanta da ta Saita yana Video coverage tayi saving sannan ta hau Babur din ta tada har zata wuce ta hango shi kwance yana Sauke numfashin wahala, saukowa tayi ,ya kamata ta taimaka masa badon Halinshi Ba.

Aljihunsa ta laluba ta fiddo wayarshi tayi sliding, Taganshi a lock ɗagowa Tayi don ta tambaye shi Pin din kafin ta kaida buɗe baki taji yana Jero mata su
"1948 ki buɗe Min wayar Muyi Sel..fy"

Tana Kyautata zaton Pin din ne ya gaya mata don Haka babu bata lokaci ta saka wayar ta buɗu, Abin mamaki Ganin Aeesh tayi a fuskar wayar, Mamaki ta shigayi don a iya saninta dashi wani abu Bai taɓa hadasu ba Wasu lokutan har mamaki take ace su Cousins ne amma basu shiri!, Latse latse ta farayi a wayan, ta shiga Gallery Hotunan Aeesh tayi arba dasu Bila adad Da alama duk bata san yana dauka ba, Wani Folder ta gani yayi Naming da *_Targets_* hannu na rawa ta Latsa.

Ji tayi an kwace wayar a hannunta, Saurin Ɗagowa tayi, Security dinda ya biyoshi ne Sanye da Uniform dinsu ta gadi.

"Meye hadinki dashi"

Ya jefo Mata tambaya

"Colleague Dina ne a wajen Aiki"

ID card dinsa ya nuna mata

"Ni securityn Gidan sa ne"

Gyada masa kai tayi,ta bar wurin Da sauri, hular kwanonta da Ta dora kan Bike dinta da dauka ta saka , ta murɗa Key din Bike din Taja Shi da gudu ta bar wajen, har tayi nisa Ta tuna bata karɓi Kudin kazarta ba.

Cije Lips dinta tayi tace

_"Ba komai, kaci bashi Zaka biyani Gobe In mun hadu"_










Thofa


🙆🏻‍♀️

Shin saleem zai biya bashin kazar?

Ya zata kasance in sun hadu gobe?


Shin Ashman zai hadu da Bamalli a Chan Lagos?

Ina Aareef?,Ya reaction dinsa zai kasance idan yaji labarin Aeesh Zatayi aure?


Comment
And.
Share


Bintou ✍🏼
16th July 😌

Nayi Gabas 🚶🏻‍♀️
[7/18, 9:30 PM] chubby number: 🫀🗡️ *_WUƘA A ZUCIYA_* 🫀🗡️


*020*



Koda ta isa Gida, asual mutanen Gidan Duk sunyi barci, kudaden kajin da ta siyar ta haɗa  a leda Ta ajiyesu a inda Ta  saba ajiyesu in ta tarar Duk sunyi  barci.

Washegari Tunda Bakwai na safe ta fita ,har a lokacin Mutan gidan Basu farka ba, ta riga ta saba da hakan basu samun lokacin juna sai ta dawo da Rana , In Kuma Afternoon Shift takeyi Sai dai Su hadu da safe...

Yau kam ta Rigashi Zuwa,babu ɓata lokaci Ta sauya shiga zuwa kayan aiki sannan ta shige Ward ɗin ta ,ta karɓi Shift a hannun Masu Night.....

*Asibiti*
★Female Medical Ward★
(Nurses Station)

Cards din dake zube a gabanta take kallo 'daya bayan Daya a mugun Mamakince.

Cikin Mamaki ta ɗago ta dubi Aeesh da ta zuba mata ido tace

"Aeesh Garin ya haka?, Ina kuka kai Printing aka Bugo muku Shirme?"

Zama Aeesh tayi bakin gado tana dafe kanta da hannu daya.

"Ba error bane da gaske ne, katin bikin mu ne, Kinsan Family dinmu basu sa Long time idan Za'ayi Aure "

Dafe kanta Reey tayi

"This is unbelievable, nakasa yarda da abinda ki ke gayamin Besty , me hakan Ke nufi?, bada Aareef aka saka ranar Aurenku ba?"

Rintse Idanu tayi,Jin sunan Aareef ya Taso mata da tsohon Jiɓin dake Zuciyarta, Tana son Aareef So na haƙika Shine zaɓin ta, dashi ta tsara Rayuwar ta, Amma Kaddarar Aurenta badashi Allah ya tsara Mata ba,  *so daban, Rayuwa ma daban*.

A hankali ta ɗago Manyan Idanun ta tadire su akan Reey , muryarta a matuƙar sanyaye tace

"Allah bai nufa shi zan Aura ba"

Kallon rashin Fahimta Reey tayi mata

"Ban gane ba?, kina Nufin Duk soyayyar da Kike masa Ta tashi a banza kenan?, kodai ya nuna miki Halinsa na mayaudara ne"

Girgiza Kai Aeesh tayi a sanyaye

"Nope ..ko kadan Hasalima ,Nice na chanza ra'ayina, na ba Yaya Saleem dama”

Guntun tsaki Reey taja tace

"Aikin banza!, Me saleem din ya taba miki da zaki sadaukar da soyayyarki akansa?, Kinada Hankali kuwa?"

Shuru Aesh tayi Na wasu Sakanni, Kana ta ɗago Rinnannun Idanunta da suka Fara tara ruwa , Cikin Raunanniyar Murya tace

"Reey Ya kamata ki fahimta, so daban Rayuwa ma daban, bai zama lallai sai ka rayu da wanda kakeso ba idan Allah bai ƙaddara hakan ba, Amma ita kaddarar Aure girmamata a garemu wajibi ne, Haƙika zuciyata Aareef take so ,Amma Ni nasan Bazan taɓa rayuwa dashi ba inba Ikon Allah ba,hakan ne yasa nace miki Allah bai nufa zan Aureshi ba, Amma dukda haka inajin Sonshi a Zuciyata Fiyeda da, na sani Aure baya hana zuciya son Abinda ta jima tana so , Amma na sani So Abu ne na Allah ,da zan iya da na goge soyayyarsa a raina''

ta qarashe maganar tareda Rintse Idanu,taba Hawayen ta daman Zubowa

Reey was totally shocked, kallonta kawai take tana son hango bakin gaskiyarta ta cikin idanuwanta.

"Besty..!"

Reey ta kirata a sanyaye Ganin Hawaye take Bilhakki, Hakan ya kara tabbatar mata da Ba Son Ranta bane auren Saleem ,Mai yiwuwa tilasta mata akayi.

Ahankali ta dago kanta daga kallon gefe, batareda ta damu da Goge Hawayen Idanunta ba.

Reey kau sai kallon kawar tata take tana karantarta, Mamaki Da takaici duk sun rufeta tabbas Ko rantsuwa tayi bazatayi kaffara ba idan tace bada son ran Aeesh za'a yi auren ba, fin karfi suka mata,ita shaida ce akan Tsoron Saleem da takeyi,ko kadan babu wata kyakkyawar Alaƙa a tsakanin su .

"Meyasa kika amince da Auren Saleem Alhalin Kinsan Halin da Umma take ciki na Rashin Lafiya!, har yanzu bata buɗe Idanu ba fa?, Kinada Hankali kuwa or lemme say Kunada Hankali?, cus ban Cire kowa ba daga kan Angon Naki zuwa Masu tsaida Ranar Dukkanku naga Alamar hankali bai isheku ba"

Tashi tayi Tana gyara Guntun Nurses hijab dinta

"Yau ba Dr Saleem ba Ko Naseer Shettiman ne dakanshi Sainaji Dalilin Da yasa Zasuyi miki aure bayan sun san da Alƙawarin wani Akanki!,Kuma don Mugunta Sunsan Inda Lafiyar Umma ƙalau bazata Amince ba Shiyasa Suke cukucuku don ayi Komai Kafin Ta farka"

Saurin Riko hannunta Aeesh tayi da karfin gaske ganin Tana shirin Fita a fusace , karamin Aikin Reey ne taje har Office din Saleem taci masa Mutuncin akan maganar Auren, In kuma tayi hakan ita tajawa bala'i.

Sake tamke idanunta tayi zuciyarta na bugu sosai tanajin kanta na juyamata ahankali.

Ganin kamar hannunta nadan 6ari yasa Reey zare  hannun ta Daga Riƙon da Aeesh tayi mata, Sai tayi saurin maida hannun cikin Aljihun Scrub dinta still Idanunta a rufe

Ware watery eyes dinta tayi ta Reey sannan ta saddasu tana saka bayan hannunta tana share hawayenta, cikin Raunanniyar Murya mai ban tausayi tace

"Please Reey Don't Go!, Ni kaina ina buƙatar aure a halin yanzu ,Buƙata tace tasa Nayi Saurin Amincewa Da buƙatarsa ta Aurena"

Ta ƙarashe maganar Mood dinta na dada Komawa  mai Ban tausayi.

"Ban Fahimceki ba?"

Reey ta faɗa tana kafeta da idanu

Ajiyan Zuciya ta saki taja Numfashi kana tace

"Ke Aminiya tace koda zan Ɓoye miki wasu Abubuwan Da ke damu na , I can't hide this from You"

Shuru tayi na 2secs Idanunta na cigaba da zubar da Ruwa

"Inada ƙarfin sha'awa akan Namiji , na gano Hakan ne Satin da ya gabata a ranar da na Kai karfe Goma a gidan Ya Ash, a ranar da ace yayi yunƙurin aikata wani abu a gareni ,Tho Babu shakka biye masa zanyi, Tundaga Lokacin Nakejin abin na karuwa Ta yanda ko Muryarsa naji Sai Abubuwa Sun Motsa a cikin Jikina ,a matuƙar Matse nake Nima mutun ce ba Dutse ba, Badole sai na auri Aareef burina zai cika ba, Akwai Hanyoyi da dama Na cimma buri Please Besty Ki fahimci halin da nake ciki, Cikin Kwanakin nan da ƙyar nake Rintsawa babu Wanda ya lura da yanayin da nake ciki, Besty....Ina tsoron abinda Zaije ya dawo , Wannan dalilin Shi yasa nayi Avoiding yaa Ash Nace ya fita rayuwata Domin Kuwa idan ina ganin shi akoda yaushe babu makawa wataran sainayi Mshi fyaɗ...."

Zaro ido Reey tayi tasa hannu tayi saurin toshemata baki don kar Kalmar tafito.

"Innalillahi Wainnailaihirraji'un!, Don Allah kiyi Shuru karki bata Min tarbiyyan Kunne"

Hannu Aeesh tasa ta cire hannun Reey ,harara Reey ta galla mata a kufule tace

" Da kin Fada Min ai da dakaina zanje In Gayama Ya Aash Nasan Bazai ki Aurenki ba,Kodan cetan Rayuwar Ƙanwarsa Daga Shiga Mugun Yanayi, Amma Still banso ki aure Ya Saleem ba kinfi kowa sanin halinshi Bashida Kirki Ko kadan, ki duba Kaf Nurses din Asibin nan babu wacce takai Sis Maryam Iyayi Da Kama Kai Akan Abinda Bai shafeta ba ,Amma ji daga zuwan shi ya maidata ƙarƙashin shi!”

"Kuttt Ya Aash din zaki Gaya Mawa?,Tho kice Mai Me?"

"Ina Ruwana ?,kinsani tsaff Zan Iya, in Gaya Mshi halin da kike shiga aduk lokacin da kk ganshi, Kinga da kin sanar dani Tuntuni da yanzu wani Maganar Mukeyi ba Wannan ba"

Tsaki Aeesh taja

"Amma ke banza ce Wlhy, Kina ganin Ko kin gaya mai zai Aureni ne?, ya Aureni yakai Deejah ina?”

“Sai ya haɗaku duka ya aura a lokaci Guda Ke UwarGida Ita Amarya”

“aikam Da na shiga Uku, Kishi da Deejah Ai Masifa ce,ina laifin Kice Ita UwarGida Ni Amarya?, Tunda da ita aka fara sa Rana"

Murmushi Reey tayi

"Ashe kina so?”

Itama Aeesh Murmushin tayi

"Naso yaya Saleem Ballantana Ahky ?Wanda yafi Kowa Nuna tattali da kulawa a gareni?"

"Ai duk ke kikaja, Bakida Lissafi ko kadan , Da farko Kinyima Mahaukacin nan Muzzammil Alƙawarin Aure, Kina Sha'awar Yaa Ash Gashi Aareef Kike so, yanzu Kuma Ya Saleem Zaki aura Da Kinada Lissafi da yanzu wanda Kike So zaki Aura!, Ina Amfanin Auren da babu Soyayya?"

Dafe Kafaɗar Reey Aeesh tayi a Natse tace

"Besty Ya kamata ki gane, Mutane da dama Sun Tagayyara a rayuwa sakamakon Maida hankali akan abinda Suka rasa ,Sannan suka kauda kai Daga Ni'imomin da Ubangiji yayi Masu, Allah kadai Yasan Abinda ya gani Shiyasa Ya Nesanta Aareef daga Rayuwata sannan Kuma ya musanya min shi da Saleem, Ya kamata in zama mai godiya akowane Lokaci"

"Haka baudaddiyar Tunanin Ki ya baki dai ,tashi Muje Ki tayani medication Shabiyu tayi”

A tare Suka Fice izuwa ward din don Serving Medication ga marasa Lafiya, Suna cigaba da tattauna Maganar Auren Aeessh.

*GYNECOLOGY Dpt*

Yau Allah Allah take Yi gudun Kar taci karo da Nasty Doctor dinta, Gashi Tana son Karɓar Kudin Kazarta da yaci Jiya, bataso ta koma Gida Tsohonta ya ga babu Kudin daya, kuma bata jin zata iya Cire kuɗinta ta biya masa Duk yanda za'a yi yau saidai ayi Sai Salem ya biya kudin kaza.

Tana Chan Labor Ward Amma hankalinta Gabaki daya ya karkata Izuwa kanshi, So take a Samu Complication Dinda zaisa A nemi taimakon Dr Oncall ace taje ta kirashi, wani SIDE na zuciyarta Kuma na Ankarar da Ita barnar da Ta Tafka masa Jiya, lallai idan Ya kamata tasan bazata ji da dadi ba.

Cikin Ikon Allah kuwa Aka samu Me Complication aka aika ta kirawo shi .

Shiru tayi kamar bazata jeba, saikuma tatuna da haduwarsu na Jiya Da Bashin Kazarta da ya ci, dan haka ta tashi tanufi office din, kwankwasawa tayi

"Yes? Come in"

inji Dr Hisham Abokin shi dake tareda Saleem suna Consulting Wata Patient dinda Hisham Ya duba lastweek aka samu Akasi File dinta ya Fado Office din Saleem.

Ajiyar zuciya tasaki sannan ta runtse idanunta ta murda kofar ahankali, tashigo.

Ganin Suna Aikine yasata Samun Kujera ta zauna, Ta ɗora kafa daya kan daya ta maida Dubanta kan Television ɗin dake kunne.

Kusan mintuna biyar Amma shiru basu Da niyyar Gama Duba Patient din,
Minti biyar...Goma...Sha biyar Amma still ba basu Gama ba, Dr Hisham Sai Jan Matan Yake da tambayoyi tana Biye masa Yayinda Saleem Ke Latse Latsensa a waya yana Sauraron su ,Badon Maryam da ta shigo ba da tuni ya kadasu waje, So yake ya ga Hankalin ta, zata Taso Ta fadi Abinda ya kawota Ko kuma sai ta jira Dr Hisham ya gama da Patient dinsa.

Itama lura da tayi Baya komai yasa taki Tashi a cewarta Tunda yasan Shi take jira Shi yakamata ya kirata ya TTambayeta abinda ya kawota.

Kowanne jira yake dan uwanshi yafara tankawa.

Maryam takaici kamar tayi kuka, shima hakan take a wajenshi, jiyake kamar ya tashi ya bar mata Office din don Takaici.

Ganin in ta cigaba da zama a haka takaicinsa ne Zaiyi Silar sheƙewarta yasata Miƙewa ahankali cikin jan Aji mai tattare da jin haushi ta tsaya a gaban kujerar dake Fuskantar sa.

Sai a lokacin Dr Hisham ya tunada Shigowarta Tun ɗazu.

Haƙuri yabata sannan Ya sallame Patient din ,Suka fice a tare, Dama ya gama , Surutansa ce ta Riƙeta.

"Sir Your Attention is needed”

Dago manyan sharp eyes dinshi yayi ya doramata su a karo na farko tunda tashigo.

Ko seconds daya beyiba ya dauke kai yacigaba da danne dannenshi a waya.

Kutt! Lallai ma, Mai hali baya taɓa barin Halinshi

"Your Attention is needed sir And it's Urgent”

Ta fada a ladabce Cikin danne takaicinta.

"Kije Gani nan zuwa" yafada still hankalinshi kan wayar hannunsa.

Ɗagowa tayi a mamakince ta dubeshi, she can't believe she's hearing These from Saleem  _*her nasty Doctor*_

"Kin kafeni Da Idanu Anything Else?"

Ya fada Still idanunshi Akan Wayarsa.

Girgiza Masa kai tayi kamar Wata Goluwa, Ta juya zata Fita, har yanzu mamakinshi bai ida sakinta ba.

Dakatar da ita yayi da kiran Sunanta, Sunan da ya saba kiranta dashi

"Miss Renal Nurse"

Chak ta tsaya batareda ta juyo ba, Bai damu ba tunda dama ba Kallonta yakeyi ba, ya cigaba da faɗin

"Apart From Nan Where Else did You work?"

Damm taji Gabanta ya Fadi, Saurin Juyowa tayi a razane, bata san Sanda Ta Iso Gabanshi ba,Cikin Firgici ta ce

“ai bani na Tare ka ba, Kaine ka shigo hanyata!"

Kallon mamaki ya bita dashi yana ƙoƙarin karyata Abinda Zuciyarsa Ke raya masa, ada yayi zaton mafarki ne, Saboda Farkawa yyi yau da safe ya ganshi akan Gadonshi, Kenan Duk Shirmen da yayitayi da gaske ne?.

Jiyayi kamar ƙasa Ta tsage ya shige kawai, he can't believe duk Shirme da Unknown Act dinda yayi cikin maye a gaban Idon ta yayi!, A lowly co-worker Dinshi kai Wiwi tagama dashi.

Muryarsa har rawa take wajen furta
"Kece na hadu da ita Jiya?..."

Karɓewa tayi da cewa

"Eh Har kaci bashin kazata lokacin kana Cikin Maye"

Wani malolo ya taso ya tokarewa saleem maqoshi, Ji yayi kaman ta watsa masa Garwashi!, Shi ne yaci bashi a Wajenta?, Bashin ma na kaza? ,kuma ta ganshi Cikin maye What a shamefull moment, Ji yayi Kaman Ya nutse Amma ance tabarmar kunya da Hauka ake nadeta cikin Hargagi ya hayayyaƙo ta

"How dare You!, ni nayi miki kama da Mashayi?, ke har kin Isa naci bashin Kaza a wajenki, har kin Isa?, Who the Hell did u think U are?, ki dubeni Sarai banyi Miki kamada Wanda yake Tareda Yunwa ba Hasalima Kudin da Nake dashi Zai iya feeding Din Whole family Ɗinku for their Whole Life,idan Kudi kike buƙata Roka Zakiyi Bawai kizo Kina Kirkiro Fake news ba, Ki kiyayeni ki kiyayi Kanki Akan Wannan Maganar Taki zan Iya sawa a koreki da ga Aiki Now Get Out Of my Office "

Dagowa tayi ta gallamashi harara batareda tasan sanda tayi hakan ba tace

"Sai me dan Ka koreni a aiki?, kafin Ka koreni Ni na riga na rubuta Resigning Letter so nake na karɓi kuɗina Kamin Na mika maka Sai Ka ci Asibin ka haɗa da Ruwa kasha, Bani Kudina"

Tayi maganar Tana Miko kasa Hannu daya, dayan hannun Kuma ta Riƙe Kugu kaman mai shirin Yin dambe.

Daga gira daya yayi kafin yace

"Da Alama Kinaso Ki bar aiki da Tabo a jikin Ki...!"

"Dukana zakayi ko kuma me?, Akan Na tambayi Hakkina?, tsaya Kaga inada Hujjata ko kotu nakai dole a zartar maka da hukunci"

"Ina hujjar taki"

Ya fada yana Balancing Akan Kujerarsa.

Hannu ta saka Cikin Aljihun Uniform dinta ta fiddo Wayarta, ta latso Video dinda tayi Masa Jiya, Kai tsaye tayi Forwarding Ɗinshi Izuwa Daidai inda ta bashi Kazar Yake cewa

_"Anty Maryam kazar da da'di?”_

Zumbur ya miƙe yana  rarraba Idanu, Yana Sake Kallon Fuskar wayar , Tabbas Sune Amma taya ya bari hakan Ta faru?

Saurin ja baya maryam tayi Ganin yana Ƙoƙarin Kwace wayar a hannunta.

Shan gabanta yayi saurin yi a matuƙar razane yana cewa

"What did u want?"

Rabawa Gefenshi Tayi tanajin Zuciyarta wasai Ganin Ruɗewarsa ba Ƙaramin Daɗi  taji ba, Lokaci Guda Kwarjinin sa da Tsoronsa da take ji duk ta nemesu ta rasa, Ba dole ba ?, Yau ta Tsorata Mai Tsorata ta

"Where did you tink you're going With My Video on ur Phone?"

"Look mallam wai what's wrong with you ne? Kaci Min Kaza ka hanani Hakkina, kuma kana Neman Hanani fita? What exactly did you want from me?"

Tafada atsakankanin haqoranta cikin fushi.

"I want you to delete That Video, Zan Baki Any Amount you want, Zan Ninka Miki Amount din Kazarki, I promise"

Ya ƙarashe magana Cikin Sigar Ra'da.

Tsayawa tayi tana kallonshi tunda yafara harya kai aya, Gabaki daya fusakarsa ya Chanza Zuwa Pleading Face ,Kaman  Bashine Nasty Doctor dinta Mara Imanin Nan ba, Harara ta sake watsa masa sannan tayi Ajiyar zuciya tace

"Idan naƙi fa?"

Cize le6ensa naqasa dasukayi jaa saboda Bacin rai yayi, yana lumshe idanu.

Zafi yakeji a zuciyarsa marar misaltuwa , he can't believe yau shi mace ta maida abin wasa, Yau shi za'a nunama isa da iko? Yau Shi mace ke Kallo cikin Ido gaba gadi tana gaya masa Maganganu?, Duk akan Me? Akan yasha Giya!, Da baisha Ba, bazai Fita ba har ya hadu da ita ba, balle Ya aikata abinda zaisa tayi masa Cin Mutuncin da taga dama.

"Sir Idan Ka shirya biyana ga Account Number!, 10k ne Babu Tsada, Na baka Daga nan Zuwa Nan da hour daya idan banga Alert ba zanyi Posting a Staff Platform”

Tana Gama Fadar haka ta fiddo wata yar takarda a aljihunta, ta ta jefa Masa .

Duƙawa yayi zai dau Takardar, Sai ta dauka Kamata Zaiyi ta Fice a guje tana dariya ƙasa ƙasa Binta da Kallo Yayi yana ayyana abubuwa da dama a ransa, Tunda yake ba'a taba Wulaƙanta shi irin na yau ba,Kunya kuma yajishi Maryam tasashi Ganin kansa as a lowly Mutum yau ,Kuma duk shi yaja da baisha Giya ba da bai kai kansa ba .

Har Aka gama Morning Shift, Babu Kuɗi babu Alamar Su, taso ta sake zuwa tayi masa barazana Amma tana Tsoro ,Saleem Murdadden Murtum ne mai Ƙirar manyan Jaruman Wrestling, Ko ina na Jikinshi a cike yake  Irin na karfafan maza , Tanada Tabbacin Da idan Ya kamata Mai Rabasu sai Allah,Gata Babu auki ,Wanann ai ya kamaata Ballan rake Zaiyi Mata a wuce wajen .

Tana Saka Ƙafa a Layinsu taji alert din 10k, saura kadan Ta buga tsalle don Murna ,Cikin sauri ta karasa Gida.

Da kafa ta shuri kofar Ta buɗe, tana Shiga ta saki wani irin Ihun murna tana Tsalle Tsalle.

Mama dake Madafa tana Girki ta ɗago a mugun Mamakince tana Kallonta

"Ke lafiya ,kika shigo Gida Ko sallama babu?"

Ko Amsata batayi ba, ta fara waƙa tana rawa

*_Ashe Daga zaune ma ana🥁🥁🥁_*
*Ashe daga kwance ma ana🥁🥁🥁*
*Tafiya nake ina🥁🥁🥁*
*Zama nake ina🥁🥁🥁*

Baki Mama Ta saki Tana Kallonta,Rawa takeyi Bilhakki tana rera Waka, Saleema Kanwarta jin Muryarta da tayi yasata fitowa Ganin Tana Rawa yasa ta taso Itama Suka shiga yin rawar tare Batare da Tasan Dalili ba dama ita din mayyar Rawa ce ,ko ba kida Tiƙar Abinda Takeyi.

Saida Suka Gaji don Kansu sannan Suka Dakata suna Maida Numfashi, Bajewa Maryam Tayi Bisa tabarma tana Haki.

"Mero Lafiyarki Kuwa"

"MamanSu a fara zuba Min abinci Tukunna da Guntun Yunwa ta nake"

" Ja'ira gaki ga Abincin Sai ingani ko Danye zakici"

Turo baki Tayi kaman Zatayi kuka, Ta tsani Ta dawo Wajen Aiki ba'a sauke Girki ba.

"Anty Mero Share the Gist Mana Me kika Tsinto mana yau?, Da Alama babban Rabo Muka samu"

Inji Saleema tana Kanne mata Idanu

"Kaji Min Yarinya Kuka samu ku nawa?, zan Gaya Miki Amma sai Kin Min wanki"

Da Sauri tace

"Eh na Amince"

"Hahaha Yarinya Kinsan Halina , Alƙawari Kika dauka"

"Eh na yarda"

"Ina Tsohon Uban nan Naki?, Kira Min shi”

Maryam Tayi maganar Tana gyara zama, Kallonta Mama tayi Ta girgiza kai da Alama Bashukan Da Baba kebinta zata Kira.

"Aikam Baban Yarinya ya tafi masallaci"

Murmushi Maryam tayi tana gyara zama, ta fuskanci Saleema, Mama dake Madafa Kuwa Murmushi kawai take saki.

"Yawwa Little din Tsoho!, Kinsan Jiya da na kai Kaji Shurash Eatery na hadu da Mugun Dr Dinnan?"

Waro ido Saleema tayi

"Dr Takwara Na?"

"Eh Nameskirt ɗinki , har Yaci bashin Kazar 5k, Amma Na ƙara masa Da yaji da Albasa na 5k making 10k"

"Kai Anty ba kince bayason Albasa da yaji ba?, kuma ai ko Za'a cika Kit ɗinki da yaji da Albasa bazai kai na 2k ba ,Taya Mutum mai lafiya zai ci Yaji da Albasa ta dubu biyar haba Easy mana"

"Ke wlh da  gaske nake , Kuma Nice Nan na bashi a baki”

Dariya Salima ta kwashe dashi

"Lallai Anty naji wannan To Ya biyaki 10k din?"

Alert dinda ta gani yanzu ta Nuna Mata ,salima zaro ido

"Lallai Anty Dole muyi rawa, yau Akwai Cin kazar tsoho”

"Banza ban Gama Baki labari ba, Jiya ba a Hayyacinsa Yake ba, sai da Yasha Ya bugu sannan Allah ya jefo Min Shi, Dalilin da yasa kenan na Rama Muguntar da yake min, kuma na karɓe Masa 5k, Karkiso Kiga Face din bawan Allahn na yau Kaman Zai duƙa min, Mutumin da ko Kallo ban isheshi ba ?, Ada Duk Shirmen Da ya kwaso Kaina yake Saukewa fa, Saigashi Yau ido Zuru Zuru a gabana Yana Rokon na Rufa masa Asiri, ada nayi niyyar idan Ya biyani Kudina in Goge Videon da nayi mana ne, Amma na fasa tunda ya sake yasa naga Weakness Ɗinshi wlh ya Shiga Uku wajena”

"Wai Anty har Video kika masa?, amma bakida Mutunci Wlhy, ba cewa kikayi Yau In Kinje Zaki Ajiye aiki ba"

"Tho na Fasa ,na fara jin dadin Aikina , Nasan Daga yau bazai sake Gigin Aikena Ba, Ballantana Akaiga Wulaƙanci, Its Now my Turn!, sai na Rama Cin Mutuncin da yayi ta min a baya”

Tun daga Wannan Ranar saleem Bai sake saka Maryam Wani Aiki ba, Hasalima Kunyarta yakeji, baya kaunar Duk abinda zai hadasu koda Hanya ce baya Kaunar ta hadasu.

Hakan Kuwa Yaba kowa mamaki kama daga ma'aikatan har Izuwa Kan Attendants din Asibin kaf Sunsan Irin Cin Mutuncin da yake ma Maryam Amma Lokaci Guda ya Chanza yayi wani Irin laushi, Amma sunfi Alaƙanta Sauyawan nasa Da auren da Zaiyi.

Ashman Duk inda yake tunanin Zaiga Bamalli a Lagos yaje, Amma babu Shi,sai dai ace Yanzun nan ya bar Gurin daga Karshe ya samu Wani Abokin Shashancin Shi ya bashi Address din mahaifiyar Sa dake nan Cikin Garin Kaduna, yaji daɗi Sosai Don Yaji labarin Duk duniyar nan babu wanda ya isa Ya lankwasashi sai mahaifiyar sa.

Kwanan Ashman Huɗu a Lagos sannan Ya dawo Kaduna, Izuwa wannan Lokacin kuwa an fara Cigiyanshi don A zaton kowa Guduwa Yayi don a bayyane yake bayason Auren da za'ayi masa ,Sosai yasha fada Gun Abba Wai taya zai Bar Gari bai gayawa kowa ba kuma Ya kashe waya, Duk Yabi ya tada hankalin Mutane, Taɓe baki Kawai yayi Ya bada Haƙuri.

Shirye Shiryen biki fa ya kankama babu Kama hannun yaro , Hausawa Sunce Kuturu da Kudinsa Alkaki sai na kasan kwano, Gabaki daya Komai na Gidan Ashman an chanza shi Izuwa Sabo, hatta Flowers Dinda ke Kawata gidan An fige an jona wani Kai hatta Ruwan Dake Cikin Pool Saida aka Tsiyayar aka sake wani, Inaga Kayan daki da Sauran Su?, Ai nan ba'a magana Komai Order Su akayi daga Finland Babu Delay Cikin kwanaki biyu Aka sauke kaya, Lefe Kuwa Umma Saude Da Matar Kawu su suka hada Komai, Komai iri daya akayi musu Aeesh da Deejah kaman yanda Tsarin Cikin gida yake iri daya da Part din Ashman dana Saleem.

Tun Daga Ranar da Aeesh ta furta tana son Ashman ,Bata sake Ganinshi ba, Bai sake Kiran ta ba duk Sun fita harkar juna ,babu mai neman wani ,kaman Basu ba.

Yau Thursday jibi ne daurin Aure, Tun da Safe Saleem yasa aka Kaita akayi msu Lalle da Kitso itada Reey, Ada Reey bataso zuwa ba, sai da

Please Login or Register in order to submit comment