Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bai tsaya ba,tafiya Yakeyi a gajiye cikeda takama.

"Saleem wa ya baka Case file Din Mutanen nan?, A Ina Ka samosu?"

Baffa ya fada cikin ɗaga murya, yawwa Anzo daidai wurin da nake so Kazo.
Wani irin juyowa yyi ya Zura hannayen sa Dukka cikin Aljihu ya Nufoshi, a gabansa Yaja Burki yana Kallon Cikin Gajiyayyun kwayan idanun Baffa
"A dakinka na Bincikosu "
Ya fada in whisper
A ruɗe Baffa ke kallonsa cikin Tsananin firgici
"Waya baka izinin Shiga dakina?, Wa ya baka izinin taɓa min Sirrina?"

"Babu Wanda Ya bani Izini, Amma nayi hakan ne don kare mutuncin kaida Dana mahaifina har da na mahaifiyar matatah Maryam ,wacce Kayi mata fyade Ka ya'da tsiraicinta a social media Ka Kuma yi blackmailing dinta ka Karbi 20M Daga gareta, She sold her kidney for her dignity amma daga bisani u planned to kill her sai Mijinta ya rigaka, Inaso Ka Sani kaine Ka Faro wasan ,matata da yayanta Sukayi Playing wasan Ni Kuma karewa nayi"

Saleem ya faɗi Hakan Yana sake matsowa gab da baffa, babu tsoro Ko kaɗan a idanunsa yace

"Acct Password dinka Shine FZ20"

Tsananin Firgici da tsoro hadida razana sun bayyana a fuskar Baffa ,haka yake so dama cikin izza da isa ya cigaba

" na Shiga account dinka Nayi hacking folders dinka na goge video Ɗin Da kayiwa mahaiyar Su Zeeyk, na maye gurbin Shi da wani, Wanda Kake Dukan Wani client naka akan yaki bada hadin kai a cuci Watah, na Kuma siyarda Gidanka na Kano, na Cire 20M a ciki zan Damkawa Matatah, Sannan ni Na Kwashe Kudaden da kake tarawa a akwatin Sirrinka na Cikin Gidan nan, don Nasan Shi Kadai ne Halal A Dukiyarka, Zan hada masu a matsayin Diyyan yaranta da ka kashe har su Biyu"

wata zabura Baffa yyi zufa na yanko masa yace

"A... Ina ka Samu Takardun gida na?"

"Sai kace ba'a gida ɗaya muke zanne ba? ,Tunda ga Hawaye a idanun Matata na dau Alwashin Sai na share mata su koda hakan Shine zai Zama ajalina"

Wani Irin Shaka baffa y kaimasa Duk ilahirin Jikinsa rawa yakeyi

"Saleem Me Ka Sani A kaina?, Taya akayi kasan duk abubuwan Nan?, Wannan Sirrina ne"

Saleem Da yasha Shaka ya ture hannun Baffa Da ƙarfi, yaja da baya yana sauke numfashi

"Tun Sanda Ka lalata min Rayuwa kasa Aaash ya zargeni da kashe mahaifiyarsa, tun a Lokacin na fara bibiyar Rayuwarka"

Dai dai Nan Motar su Nafeesah ya shigo Gidan, Dawowan su kenan Daga Dinnern wata Ƙawarsu , kallonsu Saleem yayi yana Huci baice komai ba, ya maida dubansa Ga Baffa ya kada masa Yar yatsarsa ɗaya

"My last will is to end ur life"

A fusace ya juya zuwa sashen Abba yana tafe jiri na neman ɗaukan sa, a bakin ƙofa ya tsaya, hayaniyan da yaji yasa yja burki, jin Muryar Inna Saude yayi kaman tana Kuka, hakan Ysa ya sake kara kunnensa don Tabbatar da Abinda suke jiyo masa

"Ka Gaya Min wacece, Giathah wacece Ita, Alhaji dama Yaudara ta kake Yi?, Da girmanka Da darajar ka kake neman Matan banza?, Innalillahi winnailayhirrajiun"

"Dakata Saudat niba kwarto bane, Ban taɓa aikata Abinda kike zargin na aikata ba Kuma Allah Y tsareni da Aikata alfasha har na koma gareshi"
Cikin Tsawa da hargagi ta dakatar dashi

"Macuci ,fasiƙi..."

"Kar ki sake aibantani da wadannan munanan Kalaman Ni ba macuci bane, Ban taɓa cutanki ba hasaleemah wacece kike zargin na aikata Abu da ita , ita na cuta ,Ba kowa bace Giathah Sai Matatah, Umman Hafsah Mahaifiyar ASHMAN dan ASHRAF Saleem ,Naseer da Hafsah wacce Kika sa na rabata da 'ya'yanta tun Suna jarirai, Wacce Kika aika Danta ya kasheta, Wacce tayi Zaman Yar aiki a gidan Nan For more than 18yrs just to save her kids Yathai Bata Mutu ba tana tareda Ni all these while ,itace mahaifiyar Saleem ,Rabeel ,da Naseer yaranda Kika maida naki Ta Karfi, Saleem Bai Kashe ta ba, saboda babu yanda zaa Yi ɗa ya Kashe mahaifiyarsa"

Saude ta rude iya ruɗewa, wani irin zufa na tsatstsafowa ta illahirin ƙofofin jikinta tsaye take ammma har tana kifawa kamar zata faɗi.

"Alhaji ka gaya Min gaskiya da gaske Giathah Bata Mutu ba?, Umman Hafsah Itace Yathai yar aikin Mu?, Coffee makern Saleem ?, Kaskantacciya Kucakar yar Kauyen nan?"

"Kwarai Kuwa, Kaskantacciya Kucakar yar Kauyen Da, kika rabata da ƴaƴanta tun suna tsumman goyo,kika gasa masu Aya a hannu itace Wannan Giyathar kuma bata rasu ba,bansan meye ribarki ba, Don kin kuntatawa ƴaƴan Kishiyar ki, Ni kaina Bannsan dalilin da yasa na goya miki baya na baki yaran Giathah da hannu na ba......."

Iya abinda kunnensa Suka iya jiyo masa kenan yyi baya jiri ba dibarsa, bazai iya jure Jin Irin wadannan Birkitattun kalaman ba don zasu iya zautar dashi, Da gaske Inna Yathai ce mahaifiyar Sa?, Saude ba ita ta haifeshi ba? ,how comes meyasa Abba zai ɗauke su daga hannun mahaifiyarsu ya damƙasu ga wata?.

ga wata irin zufa dake jiƙa duk sassan jikinsa sharkaf, sulalewa yayi ya Buɗe kofa ya fice, rawa lips ɗinsa suka addu'a yake sonyi amma saboda tashin hankali taƙi fita,dafe kansa yayi dan Karfi Yana Ambaton _Innalillahi wainnailauhirraji'un_ da kyar.

Sosai ƙirjinsa ke luguden duka, tunowa yayi dan wulakancin da yayitayi wa baiwar Allah, ya Zuba Mata Hot Coffee da tururinsa a Fuska yafi a kirga, ya wulakanta ta Irin Wulakancin da Kare bazai CI ba, Amma Banda Uwa Uwace Babu Wanda zai iya jure Irin Wulakancin da Yayi mata, Jikinsa na rawa ya koma cikin Motar sa.

"Innalillahi...” ta shiga ambata da kifewa kansa jikin stirring , wani al'amari mai girma na ratsa dukkan magudana da jijiya ta jikintsa, Bai cancanci Zama a duniyar Nan cikin Jin dadi ba, ya Wulakanta Mahaifiyar Sa da hannunshi, jikinsa na Rawa ya tada mota yabar harabar gidan.
Fitanshi kenan Tun daga ranar ba'a sake ganin Shi ba, Abba ya dauka aiki ne ya riƙe shi Don Yakanyi haka Ya kwana biyu bai Leƙo ba, tunda ya gama Ginin Gidansa ya Rage shigowa.

Yau sati ɗaya daidai Rabonda Ya ganshi, hankalin Abba ya fara Tashi, yaje asibiti ance Rabon da yazo tun last week Yaje gidansa masu Gadi sukace tun last week Rabon da yazo, nan Fa ake yin shi , hankalin Abba yayi mugun tashi, duk cikin ya'ƴansa yafi Son Saleem akan sauran ƴaƴan nasa, cikin kankanin Lokaci yasanar da Jami'an Tsaro suka fara neman Saleem , Sannan ya baza a media, ya bada Cigiyar Saleem har a gidan TV ,Radio da Ma Internet ,duk inda ka Duba labarin Batan Saleem Zaka gani.

Gabaki ɗaya Abba y ruɗe, ya koma wani iri, ynzu ma dawowan Kenan daga Offishin yan Sanda Sunce har Yanzu babu labari.

Videon baffa da Saleem ya saki kuwa tuni ya bawa mutanen da Baffa ya cuta kwarin gwiwan kawo kokensu ga hukuma, wanda Hakan Yasa aka Karbe license din Baffa, hukuma ta shiga lamarin, an fara Bincike akan case ɗin Kisan Kannen Maryam .

*Abba*

Tunda shiga ɗakin bai sake fitowaba,damuwan duniyar nan sun masa yawa, kwance yake a gado ko takalmi bai cireba balle maganar wanka har aka kira Asri,Tashi yayi ya nufi Bathroom yayi wankan a kasalance da alwala,ya Tafi yayi sallah, yna cikin sallah Wayansa tayi Kara Alamar Sako ya shigo, don Haka yana idarwa ya duba,Numbern Saleem ne,Zunbur ya Mike hannunsa na rawa

_Dad...Naga Sanarwa a TV kasa Ana nemana, ba ɓata nayi ba, Ka daina Wahalar da Kudadenka Please am not a kid_

Hannun Abba na rawa yayi dialling Numbern But switched Off,

Hasbunallahuwani'imal wakeel

Y faɗa tana rumtse ido da cije lip ɗinta kamar zata fasa ihu, meyasa Saleem Zaiyi Masa haka?


★★★

Tun last week Aeesh ta Cika Arbain Sunyi Ɓulɓul Ita da Baby, In Ka ganta sai Ka rantse bata taɓa haihuwa ba, Ta Yi fresh ta maida Jiki, a halin Yanzu Babu Abinda ke damunta , so take taje gida Amma ya hanata Yace sai tayi Lafiya,har Yanzu ƙwaƙwalwanta sai ahankali.
Fita yayi ya mance da wayarsa, Ta ɗauka ta Kira Reey Suka sha hira,sai a Lokacin ta samu Labarin Surrey na Wajen Ammie Anan zatayi takaba, ta Lura Akwai Magana a Bakin Reey Kuma Bata son Fada mata tawaya, shiyasa tace zataje Gida Gobe, sai Reey tace zatazo Akwai Maganar da take so su tattauna.
Suna Gama wayan Ta goge recent call, tana Gogewa Zuciya ta dibeta Ta fara dudduba Messages Message tagani daga *Khadija Umar* tasan Deejah ce shiyasa ta taɓe Baki ta wuce, Nan Kasanshi Kuma Sai taga Message again Daga *Second wife* shesaid to her self dama Ahky nada wata matar ne bayan ni?🤔 .
Hannunta Har rawa Yake Wajen bude Sakon jerin sakonnin Hakuri ne sun kusa Hamsin a jejjere ko budesu bayayi, Anan Ta Tabbatar Wannan Layin Ma na Deejah ne, nan kasa taga new message.

_Na Gama Shiri, please Ka Turo driver yazo ya daukeni_

Kuttt Dama da gaske dawowan zatayi? 🤔😭

Batareda tayi dogon Tunani ba tayi Mata Typing kaman haka.

_Ki Bari sai Next week sai ki dawo Lokacin Matata ta samu natsuwa, har Yanzu Tsorata take in Taji na Kira Sunan ki, Kinga bazaki dawo kina Tsorata min mata ba_

Tana Gama sending Saiga Reply

_Okay...Babu Matsala Zan Sake jira in Allah ya yarda_

Aeesh Taja Tsaki bayan ta gama karanta Message din, a Zahiri Ta furta *_Jaaka_*
Cikeda haushin Aash da Deejan ta Goge message dinda ta tura, da reply dinda tayi mata, ta maida Messages din unread messages.
Sannan Ta Koma Tayi shuru tana tunanin Yanda Zamanta da Deejah zata Kaya, A bayyane tace
"Bazan sa Ma kaina Kishin Hauka ba ,Amma zanci uban Yar iska....Amma Taya zan fara"

Sai ta kumayin shuru
"Yawwa Dakai zan fara Ahky, Kafin nan da Next week sai Na maidaka Abin tausayi"

tayi saurin dafe bakinta tana zazzaro ido

"Anya Zaki iya Kuwa?🤔"

"Eh zan iya mana, Saina birkita kwakwalwar bawan Allah nasa hankalinsa gba daya ya dawo kaina, kinga Koda Yar ithkan ta dawo bazai samu Lokacin ta ba"

Ta Fada to her self ta karashe Maganar da Waiwayawa baya don saida Ta Gama ta Tuna Ashe ita Kadai ce a dakin.

Miƙewa tsaye tayi tana jin jikinta babu daɗi, mood ɗinta duk ya sauya bata Son Kishiya bata kaunar Hada hanya da ita, toilet ta shige ta sakarwa kanta shower, kana ta dauro alwala ta ɗaura towel ta fito, She's thinking taya zamansu zai Kare da wacce tayi niyyar Kashe ta?, shiryawa Tayi cikin doguwar riga kaman yadda ta Saba, Kayan Baby ta kwashe tasss, Sannan Ta fara hada nata, duk ya hada Zufa ta gaji Tsabar Karfin Hali sai zazzago kayan take ki ninke su batayi take sakasu cikin Akwati, Har Ashman Ya Shigo bata Sani Ba sai Jin muryarsa Tayi Yana cewa

"Ihty.....wadannan Kayan Fa?, ina Zaki kai su?"

Juyowa tayi Tana sakin numfashi

"Yawwa Ahky ka dawo, tayani jawo karamin Akwatin Baby Ka Shirya min Kayan nan A Ciki kayi sauri Don Allah"

Dubanta Yayi da mamaki

"Ihty Me kike shirin Yi?"

"Kasan dai Bazan Gudu ba, ka Tayani Don Allah"

Jiki a saɓule kaman Wawa haka ya kama akwati ya sakko dashi, Ya shirya kayan a ciki cikeda tausayinta a tunaninsa Kan ne ya motsa.,

Suna Gama Shirya kayan ta ja Akwati ta Kai waje, ta bude mota ta sa a bakin Booth Din Motarsa, sai Kallon ta yake takaici ma ya hana shi cewa Komai , Psychiatrist dake dubata ya kira Yace akwia Matsala fa, yazo it's emergency, cikin Takaitaccen lokaci saiga Psychiatrist da Ambulance a tunaninsa the case was Serious tunda ya ce it's emergency, _Kunsan some Psychiatrist are Psychiatric patients 🤣🤣_ (Sorry Hurairah pardon my grammar I said some...)🤣


Nutsuwa tayi, tayi controlling kanta Sosai kaman da gaske , Tambayoyi yayi mata ta Amsashi Cikin Natsuwa ,Murmushi yayi Yayi congratulating Maan Yace Ta samu Lafiya.

Tsalle ta Buga Bayan tafiyanshi tace Wlhy Gobe Babu Mai hanata tafiya gida Haka kou Akayi Da sassafe ta Sa Masa Kuka taki yin breakfast Dole ya kaita Wajen Ammie, Ammie taji daɗin Ganin yarta cikin walwala, Farin Cikin Ta Gaza Boyuwa yayi Saida Ta zubda Hawaye, Albarka tayi ta Sa Musu tana yaba kokarin ASHMAN.

A daki ta iske Surry tana Kwance tayi ruf da Ciki tana Danna laptop ɗinta, da Alama Novel dinta take typing, Itama Kwanciya tayi kusada Ita idanunta akan Typing dinda Take Yi , BLEEDING HEARTS ta karanta tittle din a bayyane.

"Hmm story dinnan Must be very interesting"

"Labarin Soyayyar Daddy da Ammie ne, Naki da Sadauki, Anty Maryam da Yaa Saleem ,Deejah da Yya Sufyan Sannan Nida Baby"

Aeesh Taja Tsaki ya harareta, "harda Deejah da Ahky taya akayi kika san labarin Soyayyar Su? A Ina ma kika san Sadauki?🤔🤔"

"Baby ne ya bani Labari, Kuma naga Ya kamata na sakaki a matsayin jigon labarin!, "

Kallon ta Aeesh keyi cikin rashin Fahinta, Sureey ta Kauda Kai dga System ɗinta ta na Duban Aeesh Sosai

"Kin Tuna a baya Baby ya taɓa Cewa Yana Sonki?, Idan ban Manta ba Yace a ranar sadaukinki bayida Lafiya, Kinje Kinyi Masa Allura yayi Reaction, Har Suma Kinyi a tunaninki Mutuwa yayi"

Wannan Karon Abinda Aeesh taji ya zarce mamaki ya Koma tsoro, taya duk tasan wadannan Abubuwan?aikou Kaman Surrey tasan tambayan Dake Ranta tace

"Allah Ya jiƙan Baby...."

Sai Kuma Tayi shuru tana Jimamin abin A Ranta, mutuwarsa So yake ya dawo mata Sabo,

"Tunda yazo Nigeria Yake bibiyar Rayuwarki, a Wajen maragayi Kamal yakejin Komai, Yaso ki Amince da Soyayyar sa, ya Sama Maki Nutsuwa ya dawo dake Cikin hayyacinki sabida Yasan baki cikin hayyacinki a Lokacin Amma sai ya Lura kinyi nisa bakijin kira, Ammie Ma Haka ta haukace wa daddy daga bisani Daddyn ki yayi Masa shigar Sauri Zan baki labarin rayuwarsu anjima da daddare hope dai Anan zaki kwana"

Aeesh ta gyada Mata Kai tana Mamakin Sureey tana Chan,UK Amma tsab tasan Komai na Rayuwarta, Marubuci Kenan, kaji Tsoron Marubuci koya Yake Kana Rayuwar Ka a tunaninka Babu Wanda Ya damu Dakai , Shi Kuma Yana Chan Yayi scanning Kaff Rayuwar da Kayi har ya tsara yanda Karshenka Zai kasance 😉.

Zuciyarta cikeda tausayin Sureey, bata nuna damuwanta sosai, kodai don ta riga tasan Zeeyk zai rasu ne dama?, Muryarta a kasalance tace

"Uhkty kinada dauriya sosai, Allah Ka maidani danshen ki, I can't imagine myself in ur shoe Kila ko ruwa Bazan Sake sha Ba, Ya Allah Ka Tsawaita Min ran Mijina Kasa Mu tsufa tare, Bana so na rasashi...."

Ta karashe Maganar cikin rauni Hawaye na taruwa a idanunta, Sureey ta Amsa da Ameen Hawaye suka Wanke mata Fuska, Duk Lokacin da ta Tuna da Zeeyk neman kwaringwiwanta take ta rasa.

Turo kofar akayi da Karfi, duk suka dago Suna Dubanta, Reey ce Kaman an jefota, Rarraba Idanunta ta shigayi

"Nikam Ina Kawata?, Wacce Zan dauka a Ciki?"

Ta Kasa Ganesu tayi, sun rikide mata ta kasa banbance Su.

"Kenan Ni ba Kawarki bace ko?"

Sureey ta Fada Tana Goge hawayen Idonta duk Sukayi Dariya, Reey ta shigo Nan Take Hira ta barke a tsakaninsu, dama yaushe Gamo !, Tunda Aashman Y karbe wayanta bai Sake bari ta rike waya ba, Don Haka Basu Wani Haduwa sai in ta faki idonsa take dauke wayarsa ta kirata susha Hira.


"Besty Akwai Wani Magana Da nake Son na Gaya Miki"

Aeesh ta tattaro dukka Attention dinta ta bama Reey

"Wannan Shashashan saurayin Naki Aareef kike kiranshi Kowa Inaga Sai na Hadashi da Jami'an tsaro sunyi mana Iyaka dashi, kulllun sai yazo gidan Mu sau uku a rana dukda bana kulashi Amma ya nace sai Zuwa Yakeyi ,Aini Ina Cikin Tashin hankali a halin da ake Ciki Yanzu"

"Besty Kenan Kinada yayana Wane tashin Hankali zaki shiga Don Wannan Ya Shiga Rayuwarki?, Menene Abin damuwa Anan?"

"Ban Gane in kwantar da hankalina Ba?mekike nufi"


"Dawowan Aareef cikin Rayuwarki Shi zai bani damar rama abinda yayi min"

Reey Taja Tsaki Ganin ta fara Maida abin Shirme

"Be serious babe, A halin da ake Ciki Abbana Yana gabda gane Fuskarshi don Jiya saida na fito nayi masa Korar kare, a Lokacin ya dawo ya iske Mu Yake tambayana Wayeshi nace ban sanshi Ba"


"Manta da Abba, Ki taimaka min, Ki tuna Irin wahalar da Nasha Akanshi"

Aeesh ta Fada cikin wata murya mai ban tausai

Reey tayi Murmushin jin dadi ta dade tana jiran irin wanna Ranar da zata samu license dinda zata ci mutuncin Aareef

"Inda dan Gaske kike da na ji dadi, Yanzu za'a Fara yakin zakice na gaya Miki"

Aeesh ta sauke ajiyan zuciya

"Har kinsa naji daɗi besty inaso mu Hada Karfi da karfe domin Mu kawo karshen Al'amarin"

Reey tace

" Wlhy ni kaina banaso ya tafi a banza inaso in kwatar miki hakkinki Kawai banaso kiga kaman Na zake ne cikin lamarin"

Aeesh tayi Murmushin Yaƙe

"Tunda Ya Fara bibiyar Ki, Lokaci yayi da zakiyi Wasa da nasa Zuciyar,Ki fara kulashi karki Karbi soyayyar SA, Ki nuna mishi bakya sonshi Ta yanda bazaiga laifinki ba koda aure kikayi, Besty Ki tabbata Kin daidaita zuciyrsa ta yanda Bazata sake moruwa ba"

"Aisha Kin bani mamaki, Da bakinki kike cewa a Ɗaiɗaita rayuwar Sadaukinki?, lallai yariya kinyi Lafiya"


"Bayan Lafiya, na sake kaifin kwakwalwa, Aareef yayi kuskuren Tabo jaririyar Zuciyar da babu Komai a cikinta sai shirme da rashin Sanin ciwon kai, yayi kuskuren rainon zuciyata da Heart break,Yanzu Lokaci yayi da Zan nuna masa Ni macece, Mace Bata cika mace har sai ta baza kaidinta na 'ya mace kana Kuma tayi Amfani dashi, Ahky ma Ina gabda Gasa Masa Nasa sai yayi dana sanin dawo da Deejah cikin Rayuwata bayan Sharrin da tayi mn...."


Haka suka Cigaba da tattauna yanda zasu Hukunta Aareef har yamma sannnan ,Reey ta Tafi ,Bayan An idar da sallar Magrib Ashman Ya Shigo Yace Ta shirya in ya dawo zasu Tafi.

Baccinta Tasha batareda Ta shirya ba,Saida ya dawo Habeeb Yace Ta fayi bacci, Kiran Surrey yayi a waya yace ta tashe ta su tafi, Tashinta tayi Amma fa bata shirya ba.

Chan Sai ya sake Kiran Surrey yace tace Aeesh tazo, Aiko tana gaya mata ta Mike harda saka dogon hijabi Har kasa ya nufi part din Yaa Sadeeq Don tasan Yana chan.

Tana Isa ta shiga yin knocking tana kwala Masa kira Ahky....Ahky gani Ka fito .

Yana jinta yayi banza da ita ta kai kusan mintuna goma tana tsaye sannan Sadeeq ya buɗe har ta gama yanke shawarar juyawa ta koma Shine ya buɗe ƙofar Aeesh na Ganin yayan nata Ta turo Baki

"Ina Ahky?"

Shiga yayi batareda ya bata Amsa ba Ta bi bayanshi tana Turo Baki , Zaune ta iske shi a gefen Gado ya sunkuyar da kai hannunsa dafe da Kai.

A Hankali ya Dago idanunsa da Sukayi masa nauyi ya dubeta

"Ihty dauko Baby mu tafi"

Turo bakinta tayi cike da shagwaɓa, sai ga Hawaye

"Ba na samu Sauki ba, Kuma na Gama Idda me Zan Yi a Gidanka?”.

Hannunta ya riko ya zaunar da ita kusa dashi yana share mata hawaye,da rufe idonsa daya nuna alamar a barci ya keji yana buɗewa,Ya matsa hannayenta a Hankali ,maida dubansa yayi ga Sadeeq da yayi tsaye yana kallonsu, ya kauda Kai ya maida dubansa kan Aeesh

Kusan minti ɗaya yana kallonta ko ƙyaftawa babu sannan yayi magana.
“idda Kuma?, mijinki ya rasu ne?”.

Baki ta taɓe tana ƙara tsuke fuska,Batare da tace komai ba ta Kwantar da kanta a kafadarsa,har Yanzu idonsa na kanta,Ɗagowa tayi suka haɗa ido, tai saurin janyewa da daga kanta a kafadarsa tana murguɗa baki.
Mikewa tayi

"Saida safe Ahky"

Ta faɗa batare data yarda ta kallesa ba, Bai amsata ba, sai hankalinsa daya maida ga Sadeeq dake faman danne dariyarsa, Haushi ya ƙara kume zuciyarsa, gashi ya sa ran Tarewa da Amarya ga Amarya ta Danna Masa Hauka.

Kallonta yake ta nufi kofa sai ƙunƙuni takeyi amma bazaka iya sanin me take faɗa ba, Juyowa tai tana jan tsaki ganin bai dakatar da ita ba, da sauri taja baya har tna taka doguwar hijabinta,Duk ta daburce dan sam bata san ya biyo bayanta ba, ga idanunsa masu kaifi daya kafeta da su, A hankali ya tako gabanta duk hannayensa zube cikin aljihun sa, ya tsaya dab da ita har tana iya jin hucin numfashinsa,Sai taji gaba ɗaya kwarjininsa ya cika wajen har bata shaƙar numfashi a wadace...

"Jeki shirya"

Yay maganar cikin tsare gida , muryarsa babu Wasa,muryar da bata taɓa ji daga garesa ba Kasa jurewa tayi sai da ta ɗago ta kallesa da idanunta da suka fara tara ruwa,Har yanzu idanunsa a kanta suke, tayi saurin janye nata tana girgiza kanta. Muryarta da ɗan rawa tace


"Tho....to..."

Daga Nan Ta fice da gudu har Tana tuntube, koda ta koma daki kulle kofa tayi a Lokacin Har Sureey tayi bacci, ta dau wayan tasata a flight mode Don Ma kada ya kira ya dameta, Aikam tana saka wayar a flight mode tji ammie na kwala Mata kira, Cikeda Jin Haushi Ta Tashi taje, Ammie tace ta dau Baby tabi mijinta, Kuka tasa ita wallahi babu inda zata, ya saketa Ya riga yyi mata Sakin da baa dawowa.

Ashman Bai ɗauka da gaske take ba, Ya dauka shirme ne irin nata don taga Ammie da Yar Uwarta tana so ya barta tayi kwana biyu a gidan, Shi yasa Ya kyale ta,

Ya koma gida koda ya Koma gida Ya kasa zama Gani yayi Gidan yayi masa Girma dayawa Goggo ce kadai a gidan itama ta jima da Kwanciya, haka yasa Ya dawo gidan Ammie, kai tsaye ya nufi part din Sadeeq Yna Kwance yana Waya da reey yaganshi ya Fado kaman Maraya kallonshi yayi da mamaki yace

"Maan Lafiya?, Na dauka ka Tafi ne?”

Tsaki Ashman yaja tareda Kwanciya akan Gadon Yana Sauke numfashi.

“nan Zan kwana"

Ya faɗa kaman an Tilasta Shi.

"Ohh ga Wuri dama Ka Saba, ga kayanka a Closet in Ka tashi tafiya Gobe Ka dau Abinka Ka Tafi dasu na gaji da Ajiye Tarkace a Daki "

Bai kulashi ba, don haushi Ko Takalmin sa Bai Cire ba, Haka ya Kwanta Kaman a mafarki Yaji muryar Reey ta Cikin Wayan tana Cewa

"Hala mutumiyar ce ta buga Masa Hauka, yazo Zai huce akanka?"

Sadeeq yayi Daria Yace

"Kede Bari ,Zanso Kiga Fuskarshi ,Cewa tayi bazata Koma Gidan sa ba, Ya saketa Shi Kuma ya Dage Cewa Bai saketa ba"

Tsaki Ashman yaja Ya Rufe kanshi da bargo, Reey ta ce

"Tho Kuma Ammie tace me?"🤔

"Cewa tayi ya dawo Gobe zata zauna Dasu Taji inda matsalar take, Tunda ynzu daré yayi Shine mutumin kifa Hankali Ya tashi Ko gida ya Kasa Zuwa "





Nayi Gabas🖤🖤📯

Bintou 🖤

29th December.

*WUƘA A ZUCIYA*
_(BLEEDING HEARTS)_


_*Bintou*_

*064*

Cikin Dare Aeesh ta farka sakamakon kukan da Aeerah (Noor) da ya karade ko ina, ta zauna ta shayar da ita na Wani Lokaci Har bacci ya dauketa, Itama ta kishingida don tayi bacci Amma bacci ya gaza ɗaukan ta ,Ta nemeshi ta rasa tunowa tayi da Alkawarin da Sureey tayi mata cewa in Dare yayi zata Bata labarin Soyayyar Daddy da Ammie, a Hankali ta fara Tashinta, Cikin Takurarren baccin da ya fara ɗaukanta Taji Ana Tashinta, Ya bude idanunta a Hankali tana Duban Aeesh da ta Kureta da Idanu tana Kallonta

"Menene" Surrey ta Fada cike da jin Haushin Tashinta da tayi.

"Ki tashi Ki bani labarin da Kika min Alkawarin Zaki bani"

"Haba Uhty Shine Zaki Tasheni cikin daren nan?, Please Ki Bari sai gobe"

"Ni don Allah Ki tashi , Banason haka please wake up "

Tsaki Surrey Taja, ya dau bargo Ta Rufe kanta dashi cikeda jin Haushin Aeesh, tanaji tana gani Haka Sureey Ta shige bargo, Alkawarin da tayi Mata Yana Shirin Shan ruwa, Aeesh bata Bari Ta kwanta cikin salama ba, sai Mintsilinta take tana Jera Gajerun Tsaki, ita a dole an Bata Mata Rai.


WasheGari Suna idar da sallah Subh Surrey zata Koma bacci Aeesh ta zauna gefenta, ta kwanto jikinta bisa kafadanta.

Kallonta tayi cikin kulawa tace

"Ihty baki da lafiya ne?"

"Eh, cikina ke mintsilina kuma banjin kuzari ajikina "

"sannu ihty shiyasa naji jikinki da zafi"

Aeesh ta amsa da

"yawwa" tana gyara kwanciyar ta a kafadarta

"Waye Faisal?, Ya Alakarsu da Ammie?, Ina alkawarina?"

"Na Rantse da nasan Haka Kike da Shegen nacin Tsiya da tun farko ban nuna Miki nasan Komai ba"

"Oho dai nidai ban Labari"

Sureey ta gyara zama, Aeesh ta dago kanta tana Kallonta,gabaki daya ta mika mata attention ɗinta

"Da farko kafin Na fara baki Labarin kinsan Asalin Sunan Ammie?"


Da Mamaki Aeesh ke Kallon ta

" Mahaifiyata ce fa?, Taya zakiyi tunanin Bansan Sunanta ba?

"Alright ya sunanta?"

"Noor A Shettimah"

Sureey ta girgiza Kai
"Ba haka bane Asalin Sunan Ammie Noor Salman kurah, iyayenta Asalin Yan kurah ne, Daddy na yace Ammie cousin ɗinshi ce, ya Nuna min family pic na parents ɗinsu They both

Please Login or Register in order to submit comment