Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a gareta, Abinda ya bambanta shi da Ash Kenan shi Ashman Baya taɓa Nuna Takurawan da akayi masa Akan Abu koda Bayaso ya fiso ya bar wa Ransa komai .

Kaman Abin Arziki haka sukayi ta acting har aka yanka cake babu wanda ya bukaci Ganin Fuskar Amaryar Saleem, inama sukaga Fuskar 😅?, abokansa Sai Tsokanansa Suke da wai ya cika Kishi.

Saleem yabi doka da oda Yanda ya kamata Sai da akazo Wurin daukar hoto, Duk abinda ake Ashraf be ko kalli gefenta ba, haka itama Amma jefi Jefi yakan Leko ya dubeta har Ta Kamashi sai ya maze yayi kaman ba ita yake kallo ba .

Da akazo daukar Hoto aka Bukaci ganin Fuskar Amare, Ashraff dakansa Ya budewa Deejah suka Dingi daukar Hoto, Kawayenta sai Iyayi suke....

Gaban Maryam babu Abinda Yakeyi in Banda Dukan Uku ,uku, koda Aka bukaci Ganin Fuskar tasa Amaryar Cewa yayi ya riga da ya siye Fuskar babu Mai ganin masa mata, idan Zasu Dau hoton a haka su dauka,idan kuma bazasuyi ba abarshi.

Daya daga cikin Kawayen Aeesh ce tayi tsalle ta Fizgo Mayafin dake rufe a fuskar Maryam, cikin Daburcewa ta juya fuska, bata saukeshi ko ina ba sai a ƙirjin Saleem.

Hannu yasa yayi tapping bayanta ya Rungumota Gabaki daya Ta dawo Jikinshi.

Shewa hall din ya dauka masu Hoto kam Abin nema ya samu Sai dauke dauke suke.

Hannu ya mika ya karɓi Mayafin da aka Cire mata,Sannan cikin Dabara ya mayar mata.

Kunya, haushi da takaici Duk sun gama Rufe Maryam ,Haka ta kasance har aka gama Taron.

*ASH Aeesh*

Itama Barci mai nauyi ya D'auketa bayan Ya yi barci, a ƙasa Ta kwanta yayinda shi kuma yake kan Doguwar Kujera.

4:00pm
Shi ya fara Farkawa ,a lokacin yajishi garau zazzaɓin Jikinshi ya sauka babu inda ke Masa Ciwo

Miƙewa yayi ya shige Banɗaki yayi alwala sannan yazo ya gudanar da sallah

Yana dawowa ya isketa zaune kan Cussion tana rarraba Idanu.

Bin dakin take yi da kallo daga zaune cikin mammakin uban kudin daya kashe wajen yin Kawata gidan ,Tasan ko ba'a tambaya ba an karkar da kudade sosai.

Saida tagama kalle kallenta sannan ta maido kallonta kanshi

Hada ido sukayi hakan yasata sunkuyar dakai tana murmushi

"Tashi Kije kiyi sallah"

Sake Sunkuyar dakanta tayi tana Murmushi, an jan hancinta yayi sannan yace

"Awww na Manta yau 23rd bakiyi"

Ɗagowa tayi ta harareshi,  miqe tsaye yace yana zuwa

Binshi tayi da kallo harya fita sannan ta maida hankalinta akan kalle kallen datake

Ba'a jimaba ya dawo hannayenshi riqe da kuloli manya manya.

Tana kallonshi ya ajiyesu saman carpet dake gaban Kujerar sannan yaqara fita can saigashi yadawo da tray mai daukeda plate da spoons, forks da Mugs.

Ajiyesu yayi qasa suma sannan ya Tuɓe Yar Cikin Sa dama tuni ya cire Babban Rigar ya rage daga shi Sai Yar Vest.

Tashi yayi ya Kulle windows, Ya kashe Wutan dakin, take Ko ina ya mamaye da duhu.

Kallon sa takeyi Gabanta na faɗuwa, Sai Zare ido takeyi kaman Mara Gaskiya.

Zama yayi Kan carpet din, yasa hannu ya dauko Remote ya kunna Msu Television sai Yanzu taji Hankalinta ya kwanta,Yana daga Cikin Best moment dinta yin Kallo Cikin Duhu Especially idan Horror movie ne.

Dubanta yayi Ta wani takure waje Guda sai zazzare Idanu takeyi Alamar tsoro.

""Feel free , let's Enjoy this Moment together a matsayin Last haduwar da zamuyi, Cheer up Kinji!"

Gyada masa kai tayi, Amma  dukda haka bata saki Jiki ba.

"Yaya kasan Yanzu Ni matar Aure ce, Kuma Mutane na chan Suna Jirana don Allah ka kaini Gida"

Murmushi mai sauti yayi, yasa hannu yana Shafa Kanta dake daukeda kananun Kitso masu daukar Hankali

"Ki kwantar da hankalin ki Babu Abinda zai Faru, muna gama Cin Abinci zan Maidaki"

Hannu yasa Yajawo Coolarn da ya shigo dashi

Farfesun Naman kaza ne, Ya Zuba a Plate

sannan ya dauki  fruits dake saman Tray, ya yayyanka.

Duk abinda yake Aeesh na zaune kan Cussion tana wasa da zoben tanayi tana Satan kallonshi ta qasan ido tana mammakin yadda yake abu Cikin Kwanciyar hankali kaman ba Ruwa suka jawo ba, ita kanta tanason kasancewa dashi For the whole day Amma tana tsoro, tana tsoron Abinda Zaije ya dawo

Saida yagama sannan ya zuba musu fresh milk a mugs ya jejjera komai ya kwashe abubbuwan da ya bata amfani dasu yafita

Babu jimawa yasake dawowa baiyi wata wata ba ya dauketa Chak ya maidota kan carpet gaban abubbuwan daya gama shiryawa.

Sunkuyar dakai tayi tana mammakin yadda ya dauke ta Kaman yar tsana bai maji nauyinta ba.

"Now Zaki Rage Kayan Jikinki ne ko in Rage miki?"

Yafada yana kallon Hidding face dinta.

Dan dagowa tayi ta harareshi sannan tayi saurin sunkuyar dakai

Dan Zaro idanunsa Yayyi

"Aww in Rage Miki Kenan?"

Ya fada yana yunƙurin Zuge Zip din rigarta ta baya.

Saurin Riƙe hannunsa tayi hawaye na taruwa a idanunta

“ihty zafi fa Akeyi Gashi Na kashe AC, na kulle windows"

"Am Ok like this ,banida Matsala da hakan"

Dage kafaɗarsa Yayi tana Dan Taɓe baki  _Asif i care_

"Zanyi maganin wannan ne very soon"

yafada a bayyane yana kada kai

Itadai bata dagoba bare ta tanka mashi

Volume Din TV ya Kara,Hakan yasa hankalinta ya koma kan TVn.

Tsoka ya dauko Cikin Farfesun yakai bakinta, tayi saurin Kauda kai tana yatsine fuska.

Binta yayi dashi nanma ta kauda kai

"Kinsan Allah? Zanmiki dure"

yafada yana sake tunkararta da naman.

Sake kauda kai tayi tana cewa
"Allah am full" adan shagwa6e

"You're not" yafada yana qara nufarta dashi

Yunqurawa tayi zata Mike yayi saurin kamo ta ta kugunta.

Luu tafada a qirjinshi tana rintse idanu sanaddiyar Abu mai sanyi dayabi ya ratsa ilahirin jikinta asanaddiyar Kugunta dinta daya taɓa

Juya hannunsa  yayi a kwarin hips dinta hakan yasata zabura ba shiri tana riqeshi gam.

"Yaya Pls ka daina"

Murmushin gefen baki yayi yana sake juya hannunsa a gurin.

"Zakici Ko In cigaba?"

Saurin kada mashi Kai tayi alamun ta zataci.

Zaunar da ita yayi kan Cinyarsa,sannan ya Kaimata  abaki, babu Shiri ta buɗe baki ta hau tauna a hankali.

A hankali ta tuno old days Dinsu, Bata iya cin abinci batareda shi ba, Dakansa yake bata a baki, a lokacin da za'a Ce mata Rana irin ta yau na nan Gareta ,Ranar da cin abinci Tareda yayaanta zai zame mata makon Abu Karyatawa Zatayi

Saida taci sosai don qin kyaleta yayi saida ya tabbatarda ta qoshi sannan ya kyaleta ta sauka daga jikinshi tana sauke Ajiyar zuciya

Sai a sannan shima yasamu zarafin cin Farfesun, saida yayi ci ya koshi sannan ya kora da milk din mai sanyi da fruit

Duk abinda yake Aeesh na zaune tana kallonshi Kaman Ba Patient ɗinta na ɗazu ba, Har Yanzu bai cire Cannulation dinda tayi Masa ba.

Tattara kayan yayi , ya kai Kitchen sannan Dawo dauke da Katon Parkages Din Popcorn Har Guda Biyu, Miƙa mata daya yayi ya dau ɗaya , Sannnan ya Chanza Masu channel zuwa Horror Series.

Kallo Suka fara yi kowannensu Cikeda FarinCiki ,Cikin kankanin Lokaci Tayi Cheering suka manta da Damuwar su, ta zage Sai kallo sukeyi, idan nuno Fatalwai sai ta kakumeshi tana leƙe, idan Anzo wajen Dariya kuma ta zage tana Dariya.

Ashman Yayi Matuƙar taimakawa Wajen samar mata da FarinCiki Wanda Ta Fara Tunanin ta rasa kenan ta har Abada.

Wani Ha'dadden Box ya dauko wanda akayi wrapping Ɗinshi da Wrapping Sheet Mai tsananin Tsada da kyau.

Ya miƙa mata Yana Sakin Yar Murmushi

"This is for ur new beginning"

Karɓa Tayi tana Murmushi

"Zan iya kwancewa yanzu?"

Gyada mata kai yayi ,hannunta har rawa Yake Wajen bare Sheet din, ta buɗe box din.

Da Makullin Mota Idanunta suka farayi mata tozali followed by Rafan Yan dubu dubu kwara ɗaya da Alama Dubu 'dari ne,sannan Wata yar takarda da Akayi Sealing Ɗinshi da Pink Flower Haka Rubutun Gaban farar Envelope din pink Akayi shi.

Hannun ta har rawa yake ,ta dau Makullin Motar, ta jujjuya tana gani kamar ta wasa ce sai kawai ta rungume shi Cikeda Tsantsar Murna Hawayen Farin Ciki suka Gangaro mata

"Nagode yaya Nagode Nagode Nag....."

Sai Kuka, sake mannata yayi da jikinsa Yanajin Wani iri a ransa baya son Rabuwa da ita ko na second ɗaya ,Amma sai gashi cikin takardar da ya rubuta mata ya bayyana mata komai tare da cewar Idan Wani Abu ya shiga Tsakaninsu da Saleem Daga Lokacin ya datse Igiyar aurenta daya dake kansa, Idan Kuma babu Abinda Ya shiga tsakaninsu Ya bar Auren akanta har sai Allah ya bayyana gaskiya.

Dubu ɗarin kuma ya bata ne a matsayin sadakinta.

Karfe Shida na bugawa ya maidata gida Dakanshi, har lokacin yan Reception Basu dawoba.

Ganin Babu Kowa a gida yasata Kiran Reey a waya dama ta manta wayar ta a gida.

Hankalinta yayi matuƙar tashi da taji wai har anyi Reception bata sani Ba kuwa har wata ta Zauna a matsayin ita, Tsarawa sukayi motar Su Reey ce ta fara Kaiwa gida Cikin Kankanin Lokaci Maryam ta shiga wanka ta wanke Makeup dinta dukda ba wani fita yayi ba,amma yayi dama dama , yayinda Makeover ta sake tsara Aeesh ,bayan tayi wanka itama ta chanza Cikin Wata Ash Gown Mai ratsin Fari tayi kyau sosai.

Dawowan Sauran Yayi daidai da gama shirinta nan Suka fara mata mitan ta Shammace su ,wasu na tsokamanta akan Mijinta na da mugun Kishi Shine ya kasa barin su ganta a wurin Reception?.

Ita dai Murmushi kawai takeyi Don batayi zaton Abubuwa zasu zo mata cikin Sauki haka ba, Lallai Maryam ta cika yar Halak Kawa ta gari ta ceci Rayuwarta

(Nikam nace Hmm, nida Masu karatu munsan komai)😂

Ana dabda Kiran Magrib motocin Kai amarya suka diro bayan Anyi masu fada, sosai suka sha Kuka Sai wulwulga Idanu take Tana neman ta inda zataga Habeeb ko yayanta SADEEQ da Su Goggo Amma duk taron Babu Su babu labarin su ,hakan yasa hankalinta rankatakaf ya koma kan Ammi dake Asibiti .

Tasha Kuka sosai sanda Za'a kaita har ta godewa Allah , Zuwa wannan Lokacin kuwa Wa'enda suka kawo Deejah Har Ashman Ya sallame Su sun tafi....

*Ashman*

Bude kofar dakin ta yayi yatura suka shiga hannunsa Manne a cikin nata fuskar ta Rufe cikin Farar mayafi kamar yanda kayan Jikinta yake Farare kall, Shima sanye yake cikin Farar suit da baƙar trouser, Aljihun Suit dinsa Anyi pinning Ɗinshi da Jar Rose.

A bedroom din Bedroom Din ya dinga bi da kallo shi kansa baisan Haka aka chanza Mshi fasali Ba, ya dai bada Kudi ayi komai Kuma ya manta rabon da ya shiga Bedroom Din.

Komai sabone ga makeken gadonta wanda yasha shimfida ta alfarma.

Daga bakin Kofa wasu tiny tiny red flowers ne a jere har zuwa kan Gadonta dake Shinfide da farar BedSheet Anyi Zanen Heart da flowers din abin gwanin ban sha'awa, Ko ina Da kananun Dwarf candle a kunne.

A kan gadon ya zaunar daita sannan yasa Hannu ya Buɗe lulluɓin da aka Rufe mata Fuskar ta dashi.

Ƙayataccen Murmushi tayi masa,Shima na gefen baki yayi yana Karewa Fuskarta da tasha Makeup kallo, Tunowa yayi da Beautiful Face din Aeesh Ɗazu da yaganta da Makeup, Bai taba Ganinta Da Makeup ba sai yau Amma ba karamin kyau Makeup yayi Mata ba, Ita kou Kusan koda yaushe tana cikin Makeup Shiyasa Bai maga kyan da tayi da Makeup Ba.

Bin dakin tashiga yi da kallo daga zaune cikin mammakin uban kudin daya kashe wajen yin wadannan abubbuwan don tasan ko ba'a tambaya ba an narkar da kudi sosai.

Saida tagama kalle kallenta sannan ta maido kallonta kanshi

Shima ita yake kallo, Hada ido sukayi hakan yasata sakin Murmushi, Shima Murmushin yayi Yace ta tashi Suyi Sallah , babu Musu suka gudanar da Sallah, Deejah sai faman Zabga Uban Murmushi take ,yau Allah ya karbi adduar ta ya mallaka mata Burin Ranta.

Miƙewa yayi ya fice batareda yace komai ba, binshi tayi da kallo harya fita sannan ta maida hankalinta akan kalle kallen datake, Duk Yawon Buɗe idon ta bata taɓa ganin Tsaruwa da Haduwan Bridal Room irin nata ba

Bai wani jimaba ya dawo hannayenshi riqe da ledoji manya manya , diresu yayi ya dauko Tray Mai dauke da Plate cups and knives.

Tana kallonshi ya ajiyesu saman yar ƙaramar table Dindake dakin, Sannan ya zauna a kan Daya daga cikin Kujeru biyu dake Zagaye da Table din.

Coat dinsa ya Cire ya rage dashi sai Yar Farar shirt din Ciki,kafin ya bata Umurni har ta Miƙe tsaye ta zauna kan dayan Kujerar dake kallon nasa, jawo wata Leda yayi ya fiddo banqarrarun kaji dasuka Gashi sai Maiƙo suke.

A hankali ya zuba Musu Fresh milk Cikin Glass Cups Ya miƙa mata 'daya.

"Cheers To a new beginning"

Deejah ta fada tana hada Cups dinsu Fuskar ta fal da Murmushi.

Shuru yayi yana Jujjuya cup din Kaman yau ya fara ganin Fresh milk.

"Khadijah....!"

Ya ambaci Sunata Murya chan kasan maƙoshi.

"Yes Baby"

Ta Amsa tana Sakin Mutumushi.

Shuru yayi na wasu Seconds Yana Cigaba da kallon Kawatattun Flowers din dake zube akan Table din

"Did you know I LIKE YOU Alot!"

"I know you LOVE ME so much"

Ta fada tanayin fari da Idanu.

"Ok"
Ya fada yana ɗago kansa, Dubanta yayi sosai yace

"And Did you ever notice that I have never used the word I LOVE YOU to Express the feelings I have for you Since we started dating?"

A hankali Fara'ar Fuskanta ya dan Ragu ,Ta ɗan Dubeshi a duba na rashin Fahimta tace

"Ohhh yeah I noticed, but I know u love me so much so I won't bother"

Tayi maganar tana Daga kafada

"I know ...but I don't love you"

Ɓat Fara'ar Fuskanta ta ɓace

Bai damu ba ya cigaba da faɗin

" I know it sounds Shocking but I like you Alot, I mean a whole Lot! because My babe Aees Suggest you to be my wife (Saboda Aeesh ce ta zaba min ke don ki zama mata ta)"

Kallonshi take da dukka Idanunta a waje In an extreme Shock

Yaji dadin Ganin tashin hankalin ta ƙarara cigaba yayi Da cewa

"And I think So kike in Aureki and Na Aureki and offcourse u re caring, You're Beautiful and indeed Some men Material ,I mean I'hv Gone too far"

Wasu zafafan hawaye ne suka zubo mata tasa bayan hannu ta share.

"I don't mean to Spoil mood, I don't Mean To spoil your big day I just want you to have a happy Ending, and that's it ,am sorry ok"

Ya fada Yana Miƙa Tsaye

"And Don't You Ever think Akwai Abinda zai shiga tsakanin mu, banida Burin mika kaina ga kowa face wacce Zuciyata Take so da gaskiya!, so ki dauka Ni bana Haihuwa Ok?"

Ya ƙarashe maganar da Cire Necktie Ɗinshi Ya fada Kan gado yana sauke Ajiyan Zuciya.

Kame kanta tayi tana Fidda wani irin Numfashi mai sauti cikin matsanancin Shock dinda yasata tace

"Dr Aash ,Baby Please if this is the prank stop!"

Banza yayi mata ya maida idanunsa Sama.

"Innalillahi Wainnailaihirraji'un Da gaske ne, its true Bai taba furta min kalmar so ba"

Tasowa tayi zata zauna gefen Gadon ,yasa kafa ya shuri Flowers Dinda Aka zana Heart dashi Duk suka Tarwatse lokaci Guda.

Kuka takeyi Sosai tana faɗin

"Pls Ashman idan laifi nayi maka ka yafe min, Na tuba Zan kasance ta gari akanka!"


BanzA yayi mata ya juyar dakai hadi da Rufe idanunsa

"my joy You're Scaring me, pls talk To me"

Ko motsawa baiyi ba, ya Bama banza Ajiyan ta....



*Saleem*

Kulle Daki Kawayen Amarya sukayi Suka ce bazasu bari ya shigo ba sai ya biyasu 2.5m , nacewa saleem yayi akan babu abinda zai bayar Shifa ya tsani duk wata harkar da zata hadashi da mace, kaf duniyar nan babu macen da ta taɓa cin Kudinsa.

Maryam ce ta farko sannan Aeesh ,daga su kuma ya dau Alwashin bazai sake narkar da dukiyarsa akan Mace ba,inba matarsa Ba ita dinma don ya zame masa dole ne.

Da kyar abokansa da suka rakoshi suka hada 500k amma fa firrr Sukaki buɗe Ƙofar Sun kafe sun Tsare babu inda zasu in ba'a biyasu miliyan Biyu ba.

Ango fa ya fusata iya fusata, Dama Abinka da wanda Ransa ke a bace tun dama, yau ne ya kamata ya kasance Ranar Murna a gareshi sai gashi tun da aka daura auren har yanzu bai samu Farinciki ba sai bakin ciki.

Bazai iya jurewa Mata na wulaƙantashi ba, ji yayi bazai iya cigaba da jure Cin mutuncin su ba.

Cikin matsanancin Fushi ya zaro wayarsa,babu bata lokaci Yayi mata typing ya saketa saki 'daya....


Salati
Reey da wayar ke hannunta ta saki ,a razane sauran Suka juyo suka dubeta Cikin Tsananin mamaki.....✍🏼











Nima Dai salati na saki nayi Gabas 🚶🏻‍♀️

Ya?

A cigaba?

Sai naga Comments manya manya inba haka ba sai kun ganni ehen 😴


6000words😁✍🏼

Bintou ✍🏼

Kar a manta a yi comment fa🤫

23jul
[7/26, 6:42 PM] Bintou: 🫀🗡️ *_WUƘA A ZUCIYA_* 🫀🗡️
_(Bleeding Hearts)_

*023*


Cikin matsanancin Fushi ya zaro wayarsa,babu bata lokaci Yayi mata typing ya saketa saki 'daya....

Salati
Reey da wayar ke hannunta ta saki ,a razane sauran Suka juyo suka dubeta Cikin Tsananin mamaki.

"Me ya faru?"

Hafsah Jibo itace wacce ta kafe ta tsare tace baza'a bude ba inbai bada adadin abinda suka bida ba tace

"Juwairiyyah me ya faru?"

"Innalillahi Wainnailaihirraji'un"

Kadai take iya Maimaitawa ta kasa Daga kai ta dubesu.

Kwace wayar Hafsah tayi ta duba  a fili take karantawa

"Message ne daga Yaya Saleem , Wato Ango”

"Na lura friends Kinki sunfini Bukatar ki, So kije Suji dake ni  SALEEM NASEER SHETTIMA na sake ki AISHA HASSAN saki ɗaya"

Duk tsit mutanen dakin sukayi Suna Sauraron Hafsah Jibo.

Duk salati suka shiga yi cikin tsantsar mammaki da alhini

"innallilahi waina ilaihi rajiun,Ango ya saketa"

Kafin kace kwabo kawayen sun Buɗe Kofa sun Watse, kowa Ya gudu Gidan su Ya rage babu Kowa a Dakin Sai Aeesh da Reey .

Ajiyar zuciya kawai Aeesh take ta saukewa don ta kasa Yarda Da Abinda Kunnenta ya jiyo mata, ta kasa Yarda da cewan ya Saketa ƙawayenta sun sa Angonta Ya sake ta,

ita kadai tasan yanda take ji a Zuciyarta Tun bayan Fitan Su Sakon sakin Saleem Yazo mata a ba zata , Bata Son saleem Amma mutuwar Aure Nada Ciwo Ballantana Irin Nata da Ko Shiga Ɗakinta baiyi ba.

"Besty Ki tashi Mu bar masa Gida Bazamu Kwana Anan Gidan Ba"

Reey Ta fada a Sanyaye tana ƙoƙarin Kamo Hannun Aeesh .

Ɗago busassun Idanunta Aeesh tayi ta kalli Reey da idanun Nata Suka fara Tara hawaye,sai Kuma Ta Maidasu ta rufe .

"Besty.." taji tender voice din Reey ta ambaci sunan ta .

Ahankali ta bude lumssasun idanun nata ta dagasu ta zubama Reey din

Wani irin tausayinta ya tsirgama Reey ganin irin kallon datake mata, a very painful look

Itama Aeesh ita take kallo babu ko kyaftawa

Ahankali Reey ta jawota jikinta, Suka Rungume juna ,Reey ta saki Wani Irin Kuka Mai ban tausayi, Gaba ki ɗaya Ta ma rasa me zata ce?, tausayin Aeesh Takeji Sosai Sosai.

Wani nannauyan Ajiyar zuciya Aeesh ta sauke tana qara cusa kanta a wuyan Reey tana sauraron Sautin Kukanta.

Lumshe soyayyun idanunta tayi tasake budewa

Da ada ne da yanzu tafara hawaye ko kuka amma yanzu ta rasa Me hana Su Zuwa A lokacin da tafi Buƙatar su, sotake tayi amma ya gagara, idanunta sun bushe, zuciyarta ta soye, kukan is now here to be found .

Ɗagowa Reey Tayi ta dubeta da Rinannun Idanunta tace

"Don't Cry dear!, every Thing is Gonna be Alright inshallah kinji karkiyi Kuka"
inji Reey cikin Hawaye .

Kallonta  Kawai Aeesh take Wani murmushi ya kufce mata wanda kallo daya zakamashi kasan murmushi na Mai huji a zuciya ne, kallon  Reey Dake kuka take Ji tayi dama Allah ya bata dama Itama ta danyi kukan ko ba komai hawayen zai wanko kadan daga cikin raunin dake zuciyarta.

Hannu tasa ta karɓe Wayarta dake Hannun Reey Cikin Muryarta da ta koma mai ban tausayi tace

"Bari In Kira Yaya Aash Ya zo ya kaimu Gida "

Saurin Kama Hannunta Reey tayi

"No !, Bai kamata ba this's Their First night!, Bai Kamata muyi Distracting dinsu ba”

Dubanta Aeesh tayi

"Tho ya zanyi?, Banaso Ya dawo ya iskeni a Dakinsa Kin sanshi Bashida Imani Zai iya aikata Min komai”

"Haka ne Tashi Mu tafi”

Reey Ta faɗa Tana Miƙewa .....

*ASHMAN*

Tunda yaga yan Kawo Amaryan Salem sun Fito hankalinsa ya tashi, Ya kasa Tsaye Ya kasa zaune sai Safa da marwa yakeyi a tsakar daki.

_Shikenan fa Yanzu Aeesh na chan da Saleem Suna Gudanar da Sunnar Aure_

Abinda ransa Ke ta kawo masa Kenan .

Fadin Irin Tashin Hankalin da yake ciki Ma ɓata Lokaci ne, gabaki daya ya rasa Nutsuwansa ji yayi ya tsani Kansa ya tsani Halinshi, da baiyi Nauyin Baki ba Da yanzu suna tare Da Ita a halin yanzu!,  Da yanzu ba'a daura Auren Saleem Akan nasa Ba.

_yanzu Fa Shikenan da ya shiga ɗakin ta auren Mu ya rabu kenan!_

Ya furta a fili

Gabansa Yaji ya fadi Zuciyarsa Tana neman Fashewa.

Tunowa Yayida Tsantsar Shaƙuwar dake Tsakaninsu Gabaki daya Rayuwan ta bata san Kowa ba sai Shi, komai Zatayi sai Dashi , Tunowa Yyi da Yanayin da Ta shiga daga Haɗuwarsu Da Saleem Zuwa Yanzu, Tunowa yayi da Rama da lalacewar Da tayi a sati biyu da aka sa Ranar Aure Zuwa yanzu, Idan Saleem Ya Auri A'isha Ba ƙaramin Rashi yayi Ba, tabbas Zaiyi Babban Rashi , Akoda yaushe Burinsa Bai wuce Su kasance Cikin Inuwa daya ba ,Sai gashi Allah ya kawo masa ita cikin sauƙi batareda Yasha Wata wahala Ba, Kuma yayi sakacin da zaisa Su rabu na har Abada.

Sai yanzu yake Ganin tarin Baiwar Da Allah yayi masa na Damƙa masa Aeesh da yayi, Sai yanzu ya lura da gatan da Allah yayi Mshi, ya sawwaƙe masa Wahala Ya bashi mata batareda yayi wahalar Nema Ba, idan ya yarda Auren Su ya Rabe Ba ƙaramin asara Yayi ba, Hakika da ya tafka babbar Asara.

Idanunsa ya kai kan Deejah Da ke duƙe a ƙasa Ta haɗa kai da Gwiwa tana Kuka.

Tsaki Yaja a fili da ya tuna da wai Ashe Shi Angon wata ne.

Wayar sa ya zaro daga Aljihun Wandonsa Cikin Yar gajeren nazari yayi dialing Numbern Aeesh ga mamakinsa Yana Fara Ringing aka ɗaga.

"Yaya na!"

Jin Muryarta Garas Yasashi Sakin Wani Ɓoyayyen Ajiyan Zuciya.

"Kanwata Baku yi bacci bane?"

"Ya Sake ni”

Ta fada In a lower voice.

Murmushi Yayi cikin Basar da Zancen Zaiyi Magana Yaji Muryar Reey tana faɗin

"Yaya Kayiwa Security Ɗinku Magana Su Buɗe mana Ƙofa, mu tafi!"

Mamaki ya kuma cika zuciyarsa, duk yanda nake tunanin Rashin Mutuncin Saleem Ashe ya wuce nan.

Cikeda Tsananin Mamaki yace
"Ban Fahimce ku ba Me kukeyi A Bakin Gate?"

"Saleem Ya Riga ya Sake ta, Gida Zamu Koma"

"What....!"

Bai sake Cewa Komai ba Ya kashe wayar, ya fito yanaji Deejah na Tambayan sa Ina zashi ko Kallonta baiyi ba ,ya fice .

A bakin Gate ya iske su ,masu Gadi Sun zagaye su sun ƙi yarda su Buɗe ƙofar,Saleem ya rigada Ya gargade su akan Duk wanda Ya Buɗe ƙofar A bakin Aikinshi .

Ƙarasowa yayi, Cikin Alhini Reey take Sanar dashi sakin Wulaƙancin da Saleem yayi Masu ya Saketa tun kafin Ya shiga Dakin.

Daɗi ne ya kama Ashman Ji yayi kamann Ya zuba Ruwa a kasa Yasha don Murna.

Murnarshi Har kasa Ɓoyuwa yayi Ya saki Murmushi yace

"Tho Malama Juwairiyyah Muje na Sauke ki a gida "

Kallon mamaki Reey tayi masa Ganin Tsantsar Farin cikin da ya gaza Ɓoyuwa a fuskar sa

"Muje ka sauke Mu dai..."

Katseta yayi da cewa

"Nan Ihty zata kwana"

"A ina Zata kwana?"

Reey ta fada tana Zato ido waje

"A side Dina!"

Ya fada kai tsaye

Bata son tayi Masa Musu Shiyasa Taja bakinta tayi Shuru.

Aeesh dai tana tsaye Ta kasa Cewa Komai Hankalinta Gabaki daya ma Baya kansu ,tunaninta ya koma kan Amminta,tana Kewanta Sosai Allah Sarki Ammie ,a kullum burinta Shine ta ga ranar Auren tilon Diyarta, burinta a kullum Aeesh Ta samu Miji na Gari TAYI zaman aurenta da Mijinta Mutuwa ta raba su, Gefe Guda kuwa Tausayin kanta dakanta take ji Tasan cewa a halin yanzu labarin Sakinta ya baje Ko'ina, Ko kadan Su Hafsah basu iya boye Gulma ba.

Komawa Ciki yayi ya dauko car key dinsa yaja Motar Suka Fice ya sauke Reey a gida Sannan Ya dawo ya shigar da Aeesh Part dinsa , a dakinsa ya Sauketa yace ta zauna anan Kafin Gobe da safe.....

*Saleem*

Raka abokan sa yayi bayan Ga tura Mata Saƙon, suna tsaye a parking lot Suka fara ganin Ƙawayen Amarya na fitowa daga bayan ɗaya, Sai a yanzu ya farga da gagarumin Kuskuren da ya tafka,Sai a yanzu Ya farga da gangancin Da ya tafka.

Wayar sa ya ciro jiki na rawa Ya goge Message din!, A fili yake Faɗin Baki Saku ba Aisha!, Ban sakeki ba!, No Baki Saku ba!, Har yanzu kina nan a matsayin matata.

Tashi yayi ya nufi dakin ta,Amma wayam babu Ita babu Labarin ta, hankalinsa a matuƙar tashe ya fara neman ta yana Kwala mata kira amma shuru.

Fitowa yayi ya tambayi masu Gadi dama Ya gargadesu kan Kada Su barta ta fita duk rantsi ,Ce masa Sukayi Sun Fita

Please Login or Register in order to submit comment