Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Office din Inspector suka iske Ashman da Barr Junayd, Hannu barrister yaba ma Inspector suka gaisa .

Barr Junayd ya miƙa Masa takarda , takarda ce daga Sama an Sallami Aeesh kuma za'a Sa mata ido Tareda Jami'an tsaro,kuma za'a cigaba da bincike har ransa za'a Shiga kotu.


wani irin kallo Ya Ashman yama Inspector ,ya kamo hannun Aeesh suka tafi .

*Maryam*

4:59 ta shigo ɗakin tayi mamaki da taga Babu Shi, Taɓe baki tayi ,jikinta ba daɗi, mood ɗinta duk ya sauya, toilet ta shige ta sakarwa kanta shower, kana tayi alwala ta ɗaura towel ta fito.

She's thinking ina Saleem ya tafi?, jikinsa babu kwarin da zai iya driving dakansa ba ,Ko yana wajan su mama? Ko kuma Driver ya tafi dashi?, da wannan tunanin ta shirya cikin wata tattausan blue yadi mai kyau simple ɗinki akayi mata amma ba karamin kyau yayi mata ba,

Zata fita Idanunta suka hasko mata wata farar takarda akan Mirror, da har zatayi ignoring sai Ta dauka, ta buɗe ta fara karantawa.

Tsararren handwriting ɗin Saleem ta Gani

"You can't start the new chapter of your life if you keep re-reading the last one *FZ20* , I know About it may be I can help."

I love you💋

Your Husband Forever.

S.Shettima


Tsaki taja tayi wulli da Takardar.

"Husband my foot....!, Who need ur help?😒, Help ur self first"


*Barr Hamza*

sanye yake da baqar suit mai light blue din shirt daga ciki, necktie dinshi ma blue ya sai takalmi cover shoes baqaqe sai shining Sukeyi.

Ya jima tsaye jikin mirror yana kallon kansa, yau zai fara zuwa aiki, tun bayan Aikin Kidney da akayi masa.

A hankali yayo ɓalle Bottoms din rigarsa, ya kare ma kansa kallo ta Mudubi, daidai inda akayi rubutu a ƙirjinsa ya kafe da Kallo zuciyar sa na boiling.

A fusace Ya maida buttons din, ya fito

yayi gaba hannunshi riqeda briefcase ma'aikatansa biyu na mara masa baya.



*Ashman*

Suna isa gida sukaga Ammie da Inna Yathai Suma sunji labarin Abinda ya faru, Sadeeq ne yayi masu bayanin Komai, harda Rashin mutumcin da Ashman yayi ma Inspector.


Cikin Fushi inna Yathai tace

"Har Yanada zuciyar da Zai nuna Fushin shi akan Yan Sanda?, Duk ba Laifin shi bane?"

A mamakince Ashman ya dubata, with Supprise, confident dinta ya bashi mamaki.

Cikeda tsawa tace

"Ka sake kallo na Sai na tsole Idon"

Ya duƙar dakai

"Kai wane irin ragon namiji ne?, Kai ba namiji bane!, da ka nuna mata kai Mijinta ne tun farko da bata cigaba da Sauraron wannan jahilin ba"

Inna Yathai ta fada cikin Matsanancin fushin da ya gaza ɓoyuwa a Fuskan ta.

Ammie tace

" Yathai, ai itama shashan da Laifin ta, kullum sai nayi mata nasiha akan Nauyin dake kanta, ashe wahalar da kaina nake ,tana chan tana Shashanci da Wannan yaron, ai maganin ta kenan..."


Aeesh na zaune ta ɗora kanta a kafadarsa, Ya sunkuyar dakai yana wasa da yan yatsun ta, kukan Zuci Takeyi don hawayen Idanunta Sun riga sun Kafe Idanunta Sun bushe.

Cikin faɗa Inna Yathai Taja tsakk

"Ko kadan Banga Laifin ta ba, Dama tun farko bai so tasan da Auren ba, Inda ya nuna Wa Duniya auren ta yayi ta isa ta kula wani namijin bayan shi?, Inda na so ya tare da Matarsa Tun Farko da Babu wanda ya isa ya Musa, Amma Sai na ƙyale shi Inga hankalinshi, Amma da yike shine Shugaban Masu Zurfin Ciki na duniya sai ya nuna Min Bai damu ba"


Sauke kai inna Yathai tayi cikin takaici

" bansan wa ka Biyo a baƙin hali da zurfin ciki ba"


Ji yayi kaman anyi Ringing bell a brain ɗinshi, a Hankali yayi recapping Kalamanta, _Amma da yike shine Shugaban Masu Zurfin Ciki_

Kalmar sai maimaita kansa yake a ƙwaƙwalwar sa, da ƙarfi ya damƙe hannun Aeesh dake cikin nasa, take wani irin Zufa ya shiga keto Masa ,gabansa na faduwa, jikinsa na karkarwa, a hankali ya Zame hannunsa dake damƙe da na Aeesh, ya ɗaga kanta a kafadarsa, ya miƙe,zumbur bakinsa na rawa yace

"Ammma.....!"







Thoufa





Nayi Gabas
🚶🏼‍♀️


Bintou ✍🏼
[12/7, 8:26 PM] { Queen_Hernah }: *WUƘA A ZUCIYA*
( _BLEEDING HEARTS_ )

*056*



Ji yayi kaman anyi Ringing bell a brain ɗinshi, a Hankali yayi recapping Kalamanta, _Amma da yike shine Shugaban Masu Zurfin Ciki_

Kalmar sai maimaita kansa yake a ƙwaƙwalwar sa, da ƙarfi ya damƙe hannun Aeesh dake cikin nasa, take wani irin Zufa ya shiga keto Masa ,gabansa na faduwa, jikinsa na karkarwa, a hankali ya Zame hannunsa dake damƙe da na Aeesh, ya ɗaga kanta a kafadarsa, ya miƙe,zumbur bakinsa na rawa yace

"Ammma.....!"



Duk da a hankali sosai Ashman ya faɗi kalmar kaɗan ya rage zuciyar Inna Yathai ta wantsalo waje.

“A..am..ma...”

Da sauri Inna Yathai ta fice cikin sassarfa daga falon, wani irin zufa na tsatstsafowa ta illahirin ƙofofin jikinta har tana kifawa kamar zata faɗi, tana fita Driver ya buɗe mata cikin sauri tace yajasu suka bar gidan gaba ki daya.

Ji yayi kaman ta tafi da Numfashinsa, wani wahalallen yawu a haɗiye da ƙyar ya iya ɗago ido kaɗan ta kalla ƙofar da Mai gadi ke ƙoƙarin rufewa.

Ji yayi jininshi na gudu a cikin jijiyoyinsa kaman Zasu faso jijiyan yana kaima zuciyarsa da ƙwaƙwalwa.

Rintse idanunsa yayi da ƙarfi Fuskar Inna Yathai da Muryarta na Circulating a cikin jinin jikinsa, yana receiving rikitattun messages masu rikitarwa.

Gilin Gilin haka kararrawar kansa ta buga,da Gudu yayi Gate, Ba'a San Me ya faru ba sai ganin Mai gadi akayi yana yawo a sama Sannan Aka diro shi ƙasa.



Wani irin Ƙara ya saki wanda ya sanya Aeesh da Ammie fitowa a firgice



Daidai Lokacin da Ashman yasa hannu ya fisgoshi yakaishi baya yana wani irin haki, kasancewarta a halin yanzu ya fara fita Hayyacinsa, baya ji baya gani.


Da ƙarfi mai gadi ya kwace riƙon da yayi masa ya arta a guje Dukda yanajin Ƙashin bayansa kaman ya karye.

Yan sandan Da ke zagaye da gidan sai Kallonsu Suke sun kasa rabasu, da kyar Daya daga cikinsu yayi ƙarfin hali zai Riƙeshi ganin yana shirin faduwa ƙasa, Aikou yana isowa yaji Saukan Lafiyayyen mari a Saman Kuncinsa.

Aeesh tai saurin dafe kuncinta tana kallon Ashman da ya koma Tamkar mahaukaci hanyar fita.

Dansandan Mamaki, al'ajab da tsantsar ruɗanin daya haɗu da azabar zafin mari yake kallonshi ya koma Tamkar rikakken mahaukaci, da ka Ganshi zaka gane Ba shi kaɗai ba, hatta Ammie dake tsaye wutar kanta ta ɗauke dan mamakinta da Tausayin Halin da Ashman ya shiga, Kenan Dama bai rabu da wannnan Ciwon ba.


Kaman gunki haka Aeesh ta tsaya tana Tsiyayan hawaye, Har yanzu bata manta dukan da tasha a hannunsa Ba lokacin da ya birkice a makaranta.

Kallonshi take tana ganin yanda yake ja da baya yana Girgiza kansa da ƙarfi, sai kuma yayi wani irin Faɗuwa a ƙasa, ya miƙe yana Ƙoƙarin Kama kansa


Ji tayi yana


"Ammaa, Ammaa Ba Baffa Bane Abba ne,Abba ne, Saleem ya nuna min....
Kiyi haƙuri Bazan iya riƙe Alƙawarin ki ba, Ya Lalata ta, ya Lalata Amminta, y..y....ya kk..kiy"

A take idanun Ammie suka cika da ƙwalla, kalamansa suka tuno mata da wani mummunar Abinda ya faru a rayuwar ta, ta Rintse idonta tana karanto duk addu'ar da tazo mata a baki.

Da gudu tayi cikin gida tana share hawayen nata.


Jikin Aeesh sai rawa yakeyi, juyawa tayi zata bi bayan Ammie cikin tsoro,wannan Itace karo na biyu da taga Hawaye a idon Ammie, kaman Daga Sama ta Tsinkayi muryarsa kaman ba tasa ba Yana cewa

"A'a bazan Iya Aurenta ba, ta haramta a gareni bazan iya ba, ki kyale Ni , ba kin mutu ba?, Meyasa zaki dawo ?, So kike ki kashe Ni?"


Sai kuma yayi Shuru yana rirrike kanshi da ƙarfi, ji tayi Tausayin sa ya cika ta, a aguje t nufoshi tana Isa gabansa tayi saurin jabaya saboda yadda taganshi yazama kamar wani mahaukacin zaki idanunsa Sun juya, kirjinsa sai ɗagawa yake har tana iya hango Ƙwanjin jikinshi sumar kanshi dukta hargitse, da idanunshi da suka chanza launi yake mata wani irin kallo nufota Yana Huci.

rumtse idonta Aeesh tayi cikin zuciyarta tana Yin Duk addu'ar da Tazo bakinta shiru taji natsayin lokaci ahankali ta bud'e idon ta , wani damƙa yakai ma wuyanta ya ɗagata sama.


"Da gaske kece matata?"

Kasa magana tayi tana matse idanu sbd shaqarar da Ashman yayi mata.


"Ba an haramta Min ke ba?, Meyasa kika bari na raɓe ki?"

Nishi Sosai Aeesh keyi tana wuwwulla ƙafa a sama

" bana Sonki ,na tsaneki.... Kije Na sak..eki saki Uku, na sake Ki...!, Na sak..ke ....ki"

Ya faɗa yana Fidda Numfashi sama Sama, iya abinda Kunnen Aeesh ta iya Jiyo mata kenan Daga nan bata sake sanin Inda take ba, sai ana Gobe za'a Shiga kotu.

Sosai Kalmar sakin da Ashman ya furta mata ya Gigita ƙwaƙwalwar ta, gani take kaman a Hayyacinsa ya furta mata kalmar!, Gani take kaman da gaske ya sake ta, ta saku damuwa sun taru sunyi mata yawa, hakan Yasa bata iya yin magana da kowa Saidai tayi tabin su da ido, kaman Kurma idan Ta tuna Halin da take ciki a yanzu sai taji hawaye sun Sauko mata.

Tunda ya dawo Hayyacinsa ya gano barnar da yayi, yaji ta bashi Tausayi ji Bai taɓa tsanar ciwon Nan ba sai Yau ,Wani irin tattali da Kulawa yake bata ko a gaban waye, yanzu jinsa yake free, bashida damuwa ko kadan tunda tasan da Auren sa akanta, Wani irin Kunyar shi AMMIE Keji da zarar ya shigo gidan take shigewa ɗakinta, bata Fitowa sai ya tafi hakan ya tafi, hakan ba Ƙaramin faranta masa Yayi ba, Sai yazo gidan tun Da sassafe Bazai tafi ba Sai lokacin Azahar, Ammie ita kadai tasan Dalilin da Yasa take gudunshi, Amma Shi Gani yake kaman wani opportunity ne.


Inna Yathai Kou Tunda ta Fice ba'a Sake ganinta ba, an nemeta sama Ko ƙasa babu Alamar ta, Ashman yayi matukar kokari wajen yakice tunaninta a ranshi da kyar ya iya amince da cewa Gizo ne ba da gaske bane, Ko kadan baya so makamancin Abinda ya faru ya sake faruwa.

Hankalin Abba yayi matuƙar tashi sosai da yaji Baffa ya bar wasika wanda ya tabbatar Aeesh matar Aash ce, haka batar inna Yathai ba Karamin damunshi yayi ba, cikin ƙankanin lokaci ya rame sosai, damuwa ke cinshi amma babu wanda Zai iya fada mawa, Saleem Abokin Shawararsa a koda yaushe shima baya cikin Hayyacinsa balle ya fahimce shi, yana buƙatar Amintaccen da zai zanta matsalarsa dashi, ko zai samu Salaman Abinda ya Rike masa makogoro.

4:45pm

A Hankali yake Shafa Mata Gashin kanta da ya zubo har Gadon bayanta, Damuwa Sosai a Ransa, Tunda ta farka Batace Komai ba, Ta Koma Kaman Kurma ko Ka Mata magana a banza Bazata Amsa ka ba,a Koda Yaushe Idanunta a Jiƙe da Hawaye Da zarar ta tuna Aareef sai taji Hawaye Na gangarowa, gashi har yanzu ta Gaza yin nasarar Cusa ma Kanta tsanar sa , Duk yunƙurin da zatayi Sai taji wani Abu akansa, ga Sakin da Take ganin Ashman Yayi Mata,ta Ƙasa budar Baki Tayi magana Ballantana asan ya sake ta (🙄), hakan yasa ta Koma shuru shuru, ta rame ta Zama Kaman Mara lfy Kallo daya Zakayi Mata kaji ƙwalla ya Taru a idanunka.

Zaune take cikin sleeveless sun dress black,Kanta babu dankwali dan haka iska ta samu damar wasa da gashinta, tana Zaune bisa baby sofa


Yana tsaye a bayanta, ya dafe jikin sofan yana karewa siffar bayanta kallo yana jin wani irin abu yana taso masa , a Hankali yasa hannu ya tattaro Gashinta ya fara Wasa Dasu .

Lumshe Ido Tayi Hawayen da suka jiƙa idon Suka ɗigo, Hannu ya zura a Aljihun sa ya Ciro handkerchief ya Share Mata Hawayen Yana Tsaye ta bayanta, hakan yasa Tayi Saurin haɗiye kukan da ya taho Mata.

"Idan Kika Sake min Asarar Hawayen ki,sai na sa kin biya"

Yayi maganar a kausashe.

Sunkuyar dakai Tayi Gabanta na Faɗuwa.

Ba zato babu tsammani taji ya saka hannayensa ya zagayo cikin ta yana Shafa cikin a Hankali.


jikinta ya fara karkarwa ,Bakinta sai Rawa yake, tana so Tayi magana Amma intayi yunƙurin haka Zuciyarta Nauyi Takeyi sai Bakinta ya Hau Rawa, ya Lura da Haka shiyasa Bai takura Mata sai Tayi magana ba.

Batareda ya Cire Hannunta a Cikinta ba, ya kwanto Kanshi a wuyanta, hakan yasa ta ɗago a Mugun tsorace Daidai Lokacin Shima ya ɗago Kansa, like magnet Lips Dinsu Yayi jaming.

Aeesh ji tayi kamar ta narke akan sofa, babu abinda yake motsi a jikinta sai zuciyarta da take bugawa da karfi, a hankali intensity din kiss din ya fara circulating All over them har takai Aeesh ta fara responding, jikinta yana amsa duk sakonnin shi,he feels how her lips and Tongue were shaking , batada lafiya, she's just pretending, and her sickness isn't acute, it can cause problem To both her and the Baby.

Baya so ta Cigaba da Saka Damuwa a Ranta, dole abin ya dameta Amma zai Kasance da ita Akoda Yaushe, Bazai Bata Daman da zaisa ta Saka Damuwa aranta ba.

Cikin Ƙankanin lokaci suka fara Fita a Hayyacinsa, har ya fara kokarin cire rigar Ya manta a general parlorn Ammie Suke zata iya Shigowa Akoda Yaushe.


Kusan a tare Aeesh da Aaash Suka Ɗago suna Duban ƙofa, ganin Ana shirin Shigowa.

Wani mugun tumble Ashman yayi daga bayan sofa sai jinshi yayi Gabanta ya tankwashe ƙafafu.

Zazzare idanu yashigayi don gaba ki daya ya mance a ina suke, taya ya bari hakan ta faru?, Ya manta sunyi waya da Lawyern da zata kare Aeesh tace tana Ƙofar Gidan.

Saurin miqewa yayi tsaye yana Zazzare idanu Alamun Mara gaskiya Sun bayyana a kanshi, Aeesh Kou ko Motsawa batayi ba, Idanunta na kallon Direction na entrance tana Jiran Shigowan Mai buɗe ƙofa.

Ƙarar takalman ƙafanta ne ya fara masu Sallama kafin ta bayyana , A hankali Aeesh ke ƙare mata kallo Daga Head to toe, Kyakkyawa ce class 1, Doguwa ce sosai, Slowly Takai dubanta kan structure dinta, Amazonian figure dinta ya Zauna Sosai on her wafer-thin body, fuskar ta ta ƙare ma kallo baƙa ce Amma ba Sosai ba, tanada pencil-thin eyebrows Wanda ya sauko gently to her black, beetle’s-leg eyelashes.

Tana Sanye cikin Maroon Abaya, Hannunta rataye da advocate gown na Lawyers.

Murmushi ta Saki Wanda ya bayyanar da oyster-white teeth dinta wanda ya haska ɗakin gaba ɗaya ,Murmushin ta kadan ma ya isa ka bata full attention ko da ba wajenka tazoba .

Cikeda natuwa ta zauna kan 3seater da Aash ke zaune ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, Sunkuyar dakai Aeesh tayi tana wasa da yan yatsunta gaba ɗaya Jikinta a mace yake.


Duban Aeesh tayi na tsawon lokaci sannan ta gyara zama tana sake Daidaita nutsuwarta akanta, tunda ta Shigo Aash Ya zuba mata ido yana Kallon Tsantsan Sakarci awajen ta, taya Mutum zai fado gidan mutane babu Sallama , sannan Kuma ta samu Guri ta zauna tana Nuna isa!.

Kauda kai yayi yana taɓe baki a Zuciyar sa yace _Gaskiya bintou batayi Sa'a ba, Jaruman littafan ta a koda yaushe Sakarkaru ne_


_bintou_ :👊🏽👊🏿👊🏿😰🧟💣💥📌✂️📍🔨⛏️⚒️🗡️🗡️⚔️🔫🔫🔫🔫


Gyaran murya Maƙuwa tayi cikeda izza ta fara magana

"Ss ....s.... Sunana Bb...barr Bintou from Zz...zaria, Ca..se dd..din..kine ya Kawoni KD,Nn...nice ja..jjja..Jaruman Bintou a Novel ɗinta nn...na gab (Zz..Zane) Ina fata zz..Zaki bani haɗin kai"

Duban Juna Aeesh Da Aaash sukayi , Sai kuma suka kauda kai , Ashman ya taɓe baki a ranshi yace

_iyayin banza ,After All in'ina take_

Kaman Bada Mutans tayi ba, haka sukayi banza da ita, Sosai haka ya sosa mata rai amma bata nuna ba ta cigaba da cewa

"N..nNa karɓi case dinnan a hh..hannnnnnun Barr Ju..ju..nayd"

Ta fada tana Duban Aeesh da har yanzu bata dawo daidai ba, kallo ɗaya zaka mata kasan bata cikin hayyacinta.

barr bintou tace

"Mrs Ashman kinga Gobe zamu shiga kotu amatsayina name kareki ki inaso kinatsu Kuma kiyi tunani sosai kisanar dani wa ya tayaki Girki a ranar sannan da zakiyi girkin babu Wanda ya shigo cikin gidan ki sannan a wane shago kikayi siyayya? , Sannan ina list dinda kika fita dashi?"

Shuru Aeesh tayi tausayin matar ya Kamata ita haka nata ƙaddarar take kenan, Sometimes Tayi magana Normal Sometimes in'ina ya riƙe ta, Aeesh, ta Sunkuyar dakai hawaye suka gangaro mata _why is she calling her Mrs Ashman Bata San ya saketa bane?_ , nan take sai hawaye


" karki damu ki kwantar da hankalin ki, naje Hostel ɗinku Nayi bincike na musamman na gano inda wannan kullin yake Kuma nayi inada tabbacin bakece kika kashe kamal ba, babe calm down and speak up"

Abu Kaman Wasa ,Aeesh taƙi cewa komai, babu irin rarrashi da banbakin da bintou batayi ba akan Ta furta mata ko kalma ɗaya ne amma taƙi, haka yasa ta baro Gidan Batareda ta samu information daga Gareta ba.

Washegari 10:12 suka Isa kotu ,yan gidan Abba Gabaki ɗayan su sun hallara cikin kotu harda inna Saude da Goggo da Banda Saleem donshi irin wannan abin bai cika damunsa ba.

Fitowan su kenan Sukaga Dirar wata dalleliyar sabuwar mota, a Gabansu Barr Hamza da ɗansa Abdool cikin shigan Lawyer.

Cikin sigar Gulma habeeb ya taɓo yaya Sadeeq , yace

"Yaya da Alama sharia'ar nan Akwai ƙura, kasan Wa ya karɓi case dinnan Kuwa?, Baffa da ya Abdul ne..."

Daidai lokacin Barr Bintou ce ta ratso gabansu Zata wuce, Abdul ya kirata ta dawo tana Masa Kallon 3saura ⅓

" Barrister Bintou,so you have made up for mind!, Zakiyi aiki, barka dazuwa wannan kotu mai Albarka, tun muna law school nake muradin Allah yahad'a ni dake cikin shari'a Koda sau ɗaya ne a rayuwa, na kashe Wannan Jijjida kan naki, na wargaza duk wani qwarin gyuwar ki, a wannan Shari'ar saina ki tsani doka wlhy"


Tunda ya fara Maganar take Kallonshi Murmushi kwance a fuskar ta, saida ta Dire sannan ta gyara tsayuwar ta



" Bbb...Baa..rrister Abdul, kkk...karka cc...cik..a zaƙewa dayawa,don Mahh...aifinka sshh...shine Judge Bashi zai bb...aka ƙwarin Gwiwan Faɗar zaka kadani ba, Kkk....ka sani ,nn...Ni bana dauko wa kaina abinda zzz...ai Faɗar dani"

Daga haka Bintou tajuya tashiga kotu kotu, kotu tayi tsit Alƙali Judge Hamza aka miƙe bayan yazauna kowa yazauna akayi tsit, Aeesh tana tsaye wajan tsayuwar masu lefi.

Duban Ashman tayi, Shima Kallonta yakeyi, ya saki Murmushi , wasu hawaye taji Sun sauko mata, a hankali ta juya ta kallo Bintou itama kallonta tayi tasaki murmushi hakan yasa tasakejin natsuwa cikin zuciyarta.

miƙama Judge case file akayi

Bayan anyi Introducing Case din yau 28th November zamu fara sauraran shiri'a a tsakanin Muhammad Aareef da A'isha Muhammad kabeer abisa zargin ta da kashe Kamal wato Abokin Saurayinta.

Daga haka yamiƙa files ɗin sannan yazauna dubawa Judge yayi sannan yad'ago kanshi ya buƙaci gabatarwa daga kowane Lawyer.

Barrister Abdool ne yafara miƙewa

"Sunana Barrister Abdul jalil Hamza Shettima lawyern gwamnati nine lawyer mai jagorantar masu qara "

yakoma yazauna sannan Bintou ta mi'ke

"Sunana Barrister Bintou Abdullah, Pro- bono lawyer lauya mai zaman kanta, nice lawyer maikare wacce ake tuhuma "

jinjina kai Alƙali yayi cikin zuciyar shi yace _Nagode wa Allah da ya bani damar da zan Cikawa ɗana burinsa,Sai na tabbatar na faɗar dake ɗana ya zama Zakara a wannan Shari'ar_

Bayan wasu 'yan rubuce rubuce barrister Abdul yamiqe yace

"Ina son nayima Aisha wasu tambayoyi idan kotu tabani dama "

Alƙali yace kotu tabaka dama, fitowa Barrister Abdul yayi cikin takun sa na Ƙasaita, ya'isa inda Aeesh ke tsaye

Dubanta yayi Sosai, tsananin Firgicin da ya gani a Idanunta ya sake bashi Kwarin Gwiwan Tsoratata, ta hanyar zazzare mata ido, tana tsoron sa Sosai Ko a gida tsoron haɗa hanya dashi Takeyi yanayinsa na tsorata ta dayawa.

" Miss Aeesh Zan so in San Asalin Sunanki da kuma alaƙarki da Aareef "

A tsorace take kallonshi , sai zare mata ido yake, take Jikinta ya hau rawa ,ta fashe da kuka, ka saka cewa komai.


Jikin Ashman ne yayi Sanyi ya sunkuyar da kai, ji yayi kaman Abdul na watsa masa Ruwan zafi, jikinsa har wani boiling yake


jinjina Kai Abdul yayi ya taɓe baki sannan ya dubi Alƙali yace

"Ya mai girma mai Shari'a, tunda Aka kama A'isha, bata Bama kowa damar sanin Wani abu daga gareta ba, da anyi mata magana Sai kuka,Saboda haka ina son Ƙawarta Juwairiyyah Wacce tafi kowa kusanci da ita ta taso don haka Idan kotu ta bani dama ina so Ƙawarta Juwairiyyah ta fito Don Amsa tambayoyi "

"An baka dama"

"Ana Buƙatar ganin Juwairiyyah a Taburin bada shaida"

A hankali ta fito, ta Tsaya Duban Aeesh tayi, Jikinta yayi sanyi Ayau da zataga Aareef da babu Abinda Zai hana Ta Kasheshi shima ,a yanda yakejin Zuciyarta na tafarfasa tanajin Koda ta Kasheshi Bazata bari a iya tattaro gawan sa ba ,ballantana ayi masa sutura, bata San Ana rama Soyayya da kiyayya ba sai Yau akan Aareef ta tabbatar da Maganar manya da sukace soyayya duk kankancinta guba ce, ballantana Wannan da tasha shi Overdoes.

"Malama Juwairiyyah anbamu cikakkiyar sheda akan cewa Kawarki Aisha Bata taɓa Girki da kanta ba amma wannan ranar sai tayi da kanta kenan a wannan ranar tayi niyyar kashe Saurayinta Aareef sai tsautsayi ya fada kan Abokinshi "

"Objection my Lord, yakamata Barrister Abdul yadaina jinginama Wanda Ake tuhuma laifin kisan kai tsaye don har yanzu zargine babu tabbaci"

Inji Barr Bintou a fusace.

duban Abdool, Baffa yayi yace

"Objection sustain, barrister Abdul akiyaye "

Murmushin Gefen baki Ashman yayi, a ranshi yace _Nagode wa Allah da yasa Barr Junayd ya bar ma mace wannan Case din_

Dan russunar dakai Abdul yayi ransa a ɓace

" Thank you my Lord !, Malama Juwairiyyah zaki iya sanar kutu shekarun ku nawa kuna tare a matsayin Ƙawaye? "

"Tun Yarinta "

"Zaki iya gayama Kotu ya dangantakansu yake da Saurayinta Aareef?, Da kuma dangantakanta da samarinta na baya?"

"Tabbas Aeesh bata taɓa Soyayya ba sai akan Aareef ,wanda ta ɗorawa Son duniyar nan, Irin Soyayyar da ta nuna mishi , kwatankwacin Soyayyar da uwa Take nuna ma ɗanta, ta zame masa uwa ta zame masa Uba, itace cinshi itace Shanshi ,Aeesh har siyar da kayan Sawanta take yi don ta bashi Kuɗi yaji daɗin Rayuwa, Aareef Mashayi ne Amma ta ɓoyewa kowa gudun kada a rabata dashi, ta bashi kuɗin Auren su ya danne su don ba Auren ta zaiyi ba,daga Ƙarshe Kuwa don tace Zata rabu dashi, ya kashe Abokin Shi ya Manna Mata, don ya huce takaicinshi akanta, baya so ya rabu da ita don Kudin da take bashi...!"


"Ya isa"

jinjina Kai Barrister Abdool yayi sannan yace


" My Lord, inaso wannan kotu Mai Adalci tayi duba da wannan lamarin Sosai,a baya Aeesh ta kasance mara manemi koda Sun zo nemanta ruwan ido ya hanata tsaida Tsayayye, haka yasa da Aareef yazo ta riƙe shi sabida ya rufa mata asiri, Aareef kyakkyawan Saurayi ne Wanda babu Macen da zata samu irinshi ta ƙyale , so take ta zama ita kadaice a zuciyar sa, sannan Aareef baya Sonta ya kuma fada mata bata Gabanshi Ƙawarta Juwairiyyah yake so, itace Ta nace tace saishi ta ce Duk wanda zai mallaki hannunka wajen baka kyauta ka Ƙarɓa wataran zaka mallaki Zuciyar ka, sannan munsa anyi cikakken bincike sosai an tabbatar mana cewa Kamal Yaci Guba ne wanda aka Sa a cikin Abincin da ta dafa masa bayan sunyi faɗa yace su rabu, Aeesh bata girki Amma Abin mamaki sai Gashi akan Aareef ta fara ,ta kashe Fiyeda Dubu Tara wajen Girka masa wannan Lafiyayyen Abincin, mai dauke daguba, shi kuma yaƙici saboda yace babu nama a ciki, ya Bama Abokinshi Kamal Wanda Ƙaddara ta afka a kanshi , ya mai girma Mai Shari'a Akwai ciwo Rabuwa da Mutumin da ka kashema Almost All ur life savings ba Kowa zai iya resisting pain dinba, my Lord da wannan ƙwakkwaran hujjar nake roqon wannan kotu mai Albarka data gaggauta yankema Aisha hukunci cikin gaggawa, tunda kwararan shaidu sunfito zahiri cewa itace tayi wannan kisan ga takardar gwajin doctor "

miƙawa yayi akabama Judge ,amsa yayi yaduba sannan yayi rubutu yad'ago yace

" kotu tana buqatar Lawyer mai kare wanda ake zargi tafito tagabatar danata hujjojin "

Tashi Barr Bintou Tayi tace

" Nn..nagode

Please Login or Register in order to submit comment