Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi Kin yi ƙiba ga Kuma wani ƙaton tumbi a ƙasa, Muje Gida in duba ki, In Zargi na Ya tabbata Maida mai ki zanyi "

Maryam ta saki baki tana duba cikinta

"Wai ƙaton tumbi, wlhy har Ka tsorata Ni😏 ,ina tumbi anan"

"You felt guilty kenan? ,Allah ban yarda daku ba mu shiga gida sai nasa Dr Isa ya duba Min Ke,nasan inda Babu Abinda ya faru A tsakanin Ku Bazaki rika tsarguwa ba haka nan"

Ya fada Daidai Lokacin da yayi Parking a Tangamemen sabon Gidan su MaMa, Maryam Da Zeeyk ne suka hada kuɗi suka gina musu, a halin Yanzu Su suke kallo a matsayin iyayen su, a cewar su Tunda mahaifiyar su ta riga ta bar duniya Batareda taci arzikin Haihuwa ba, Babbar ƙawar ta zataci Albarkacin Aminci ❤️.

Shiga gidan Sukayi, yana Tsokanarta

A babban Parlor Ya iske Saleemah Mama nayi Mata Assignment .

Taɓe Baki Maryam Tayi tace

"Mutum ba Boko ba, Amma sai karambani"

Mama ta mere maki

"Ke kuma daga ina?, Allah yasa ba baƙin hali kika masa ba ya koro ki"

"Zama nazoyi Allah yasa An share min daki, dan Iskan ya sake ni"

Mama ta zaro ido ta rike baki

"Mijin naki ne dan Iska?, Taya aure zaiyi Albarka bakya ganin Darajar shi Shima haka?"

Tsaki Maryam Taja ta dubi Zeeyk dake ta faman dariya tace

"Yaya Don Allah ba dan Iska bane?

Sai yanzu mama ta lura da Zeeyk tayi saurin katseta da fadin

"Yo yau naga gantalalle ma da nake zancen nan da ke ashe yar aiken dan Iskan ce ke ma, Allah wadaran naka ya lalace, kai Tsabar Asara dakai za'a Haɗa baki a fiddo yar Uwarka a gidan miji?, ba damuwa ni da ya zame ma dole zan zauna da ita, Ga ɗaki chan a Bayan Gida Dakin mai gadi ne, har yanzu Ban samu Me gadin da yayi daidai da zamani na ba, nan dakin zaki zauna kuma kada wani shege ya shigo min Gida ya min maganan banza, kuma shegen Ya tashi ya bar min Gida tunda Burin shi ya cika, Allah kuma ya tsine ma auren me kudi"

Maryam dake tsaye bakin kofar shiga dakin Su Saleema ta tabe baki tace

"Kar ma ki ban haushi na bar miki gidan Ki yanzun nan"

a fusace mama tace

"Tafi nono fari, Saleemah Tayata daukan kaya kuyi waje, Ni kam bazan iya ba ina kallonki kina kallona don wllh yanzu an daina auren bazawara Gara tun wuri ki koma gidan Dan iskan ,dan Zaman ki anan ba alheri bane, koda Kin samu wani da kaina zan gaya masa gaskiya ince ke bazawara ce, raguwar dan Boko, ni yar gaskiya ce, Ga kaji nan indai su kika dawo mawa suna miki maraba"

murmushi Zeeyk yayi ya mike ya fita don yin Alwalar Zuhur, Maryam ta mata wani kallo bata son magana Saleemah na dariya ta miƙe ta tayata daukan yar ledar Hannun ta.



*CANADA*

Dole tasa Ashman ya koma ɗakin Aeesh da zama, saboda yawan tashin Daren da yunwa ke mata.

Zasu jima Suna hira da daddare , Da zarar tayi barci , karfe biyu take farkawa Ta addabi rayuwar sa, babu yanda ya iya shi ya kar zomon dole yayi haƙuri da ita a kowane hali.

Idan Kuma a ɗakinsa ya kwana har ɗakinsa take zuwa ta tasheshi, baya Musawa kome tace tana so shi yake mata.

Amma yanzu Abinda ke damunta, da zarar safiya tayi da wani irin zazzaɓi yake tashi, Duk juriya irin na Ashman da zarar ya fara zazzaɓin Kwantawa yake ,idan dare yayi har fargaba yake Gari ya waye.

Yau ma dai haka ne,Da ƙyar ya Samu yayi Break fast, kadan Ya tsikara ya Tashi ya bar Gurin.

8:30 Habeeb ya tafi makaranta dama Tuni Sadeeq ya sama masa Admission a makarantar da yayi ,Shima Sadeeq ya tafi Pharmacy ɗinsa.

Suna Fita ta ta shige ɗakinsa da sallama , Ganinshi a kwance yayi matuƙar tsorata ta, Yanayin da ta Ganshi a ciki yau yafi na kullum, hankalin ta tashe ta nufi Inda taga yayanta na ajiye Drugs for reference purpose, ta dauko

kwance ta sameshi , fuskar sa tayi fayau, tayi wani irin fari ta kumbura sosai kamar bashi ba, kamar bashi ne yayi mata girki biyun daren Jiya ba, kaman ba dashi suka kwana jiya lafiyan sa lau ba.

sharrr hawaye ya silalo mata, kasa ƙara sawa wajan tayi ta zube a inda take tare da sakin kuka maganin na rike a hannunta, duk kukan da take a cikin kunnuwansa daman yyi tunanin hakan shiyasa bai fito Ba.

Kasa motsawa yayi, yana so ya rarrasheta Amma babu yanda ya iya, dole yana kwance yake sauraron ta.

Ta jima tana kuka kafin ta ɗaga kanta zuwa garesa, ya daga mata kai alamar tazo garesa, Miƙewa tayi jikinta duk rawa yake ta nufi wajansa.

Ta rungume shi tana jin Zafin jikinshi na gasata cikin Kuka tace

"Ba Jiya Mun kwana Lafiyar ka lau ba?,meyasa Zazzabin nan zai mana haka?, Meyasa sai da safe?"

Ta girgiza kai hawaye na Diga

" Ahky...ka gaya ma zazzaɓin nan ya daina Dawowa da safe, ya daina Dawowa gaba daya, bana so ina ganinka cikin wannan yanayin"

Ta faɗa tana ƙara saka kuka, take Ashman zuciyarsa yaji ta tsinke shi kadai Yasan abinda ke damunsa, Allah ne ya sauwaƙe mata ciwon da ya kamata tayi, Ya Maido Shi akansa , ya gano Kwallon sa ya shiga raga, Amma yau kimanin watanni uku kenan Ko ciwon kai Baiji tayi complain ba, Amma Shi Kullum Cikin ciwo sai kace a jikin shi abin yake.

idanuna ya buɗe da ƙyar wanda sukai masa nauyi idanun sun kada Sunyi jazur har wani lumshewa sukeyi da kansu, idanu suka haɗa daidai lokacin hawayen idanunta ya sauka akan fuskarta, tasa hannu ta ɗagoshi da iya ƙarfin ta ya zauna .

"Tashi Kasha magani"

Ta fada tana ɓare masa Magungunan.

kasa cewa komai yayi saboda yanda yake jin jikinshi kamar ana hura masa wuta.

Ta dubeshi bayan ta baro maganin, ta dauko Gorar ruwa tace

"Bude bakin ka"

Kaman wani ƙaramin yaro haka ya buɗe bakin sa ta saka mishi Maganin ,hannunta na rawa ta kara Masa Gorar Ruwa a baki.

Hannunsa na kyarma ya kamo nata hannunta dake riƙe da Gorar ruwa, Hawayen ta masu ɗumi suka sauko a hannayen nasa, Kallon ta yake yanajin ko wane digar hawayen ta a cikin zuciyarsa, da tasan yanda Hawayen nata ke ƙara masa zafi da batayi ba.

Ganin yanda Jikinsa ke kyarma ne yasa ta dubeshi cikin hawaye

"Ahky sanyi kakeji ko"

Ya Lumshe ido ya sake buɗe su akanta Alamar Eh, tashi tayi ta kashe A.C sannan ta rufe window,ta kunna warmer.

Sannan a hankali ta dawo ta yaye bargon da yake Lulluɓe kamar me tsoran taɓa bargon ta haye Gadon gabanta na faɗuwa, daga shi sai men vest Wanda ya bayyana Komai more than Half Of his chest.

Lumshe Ido Tayi da sauri, jin Wani abu na ratsa ko ina na Jikinta,Kallon ta yake Babu ko ƙyaftawa, a ransa yana fatan Allah yasa Abinda yake tunani shi take shirin yi, ƙoƙari take ta sama masa Heat by skin To skin method.

a hankali ya Lumshe idon sa take ya fara jin Zazzaɓinsa na gushewa tun bata haɗa Jikinta da nashi ba, Lumshe ido ya sakeyi hadi da Sauke wani Lafiyayyen ajiyar Zuciya daidai lokacin da yaji ta Rungume shi, ta ja musu bargo ta lulluɓe su har kai.

tana jin yanda yake sauke ajiyar Zuciya ahankali alamar ya ji daɗin abinda take masa ɗin, a hankali ya ware idanun nasa ya kafeta dasu.

Aeesh ganin yanda yake kallon ta ya sanya ta janye idanunta daga kansa tare da tura yatsun hannunta a ƙirjin sa.

Da sauri Ashman ya rufe idanunsa yana fidda huci, ya ruƙo hannayenta da ƙarfi

Tsoro taji ta fara ƙoƙarin Zamewa daga kusa dashi, ya sanya duka ƙarfinsa ya jawota kai tsaye kuma gaba ɗayanta ta samu masauki a ƙirjinsa hannunta ɗaya a ƙirjinsa ɗayan kuma da riƙe kafadar sa ,sai zazzare ido take saboda tsoro, da iya ƙarfin da yake dashi ya Sake mannata gaba ɗaya ta kwanta a jikin shi, yana Jin sanyin da yake ji na rayuwa.

Ajjiyar zuciya Aeesh ta sauke tare da faɗin

"Don Allah Ahky ka Daina fidda hucin nan, you're scaring me....."

Ta fada cikin kuka sosai

Hannu yasa Ya shafo kanta cikeda karfin hali ya buɗi baki yace

"Sorry ....uhky...Am fyn stop crying , am ok"

Ya kare maganar cikin fizgar numfashi yana shafa kanta, a hankali yake jin ɗigar hawayen ta a ƙirjin sa har ta daina, ta shiga sauke ajjiyar zuciya daga haka kuma bacci ya ɗauke ta, idanunsa ya buɗe ya kalleta kafin shima ya Lumshe su, a haka Wani barci mai dadi yayi awon gaba dashi.

12:38
Kusan a tare suka farka , ita ta fara farkawa ta farka da wani irin Yunwa.

Ta kure Shi da kallo bayan Ta buɗe ido, kallon face din shi take tana kallon yanda fuskar tayi fayau, ya rame kaman wanda yayi shekara yana ciwo.

Idanun sa dake Lumshe sunyi wani irin tudu, Alamar sun ƙara girma hancinsa ma ya Ƙara tsayi Lips ɗinsa sun Bushe sai Suka ƙara ja, Gashin Gemun sa kuwa Sunyi tsaitsaye sai suka ƙara ƙawata fuskar tashi.

A hankali tasa hannu ta shafo Lips ɗinsa, Inda yafi burgeta a fuskar tasa, Sannan slowly ta janye ta ja Gemun sa a hankali.

Buɗe Idanunsa yayi a hankali ya dubeta , yasa hannunsa ɗaya ya Ya yaye bargon da ta rufe su dashi , fuskar su ta Bayyana tangaran.

Murmushi ya sakar mata, ya ɗage mata Gira ɗaya

"You're Hungry Right..."

Hannayenta biyu tasa ta ture ƙirjin sa,sai kuma ta fashe da kuka

"Ba kai bane baka Da lafiya?"

Yayi saurin cewa
"Ai yanzu na warke, Me zaki ci?"

ta Turo baki
"Ni bazan ci komai ba, kaima ai yunwa kake ji"

Ya Lumshe ido
"Banajin yunwa na ƙoshi"

Ta kuma fashewa da kuka

"Karya ne babu Abinda kaci"

Ya Kafeta da idanunshi masu rikitarwa yace

“Tho yanzu me kike so in ci?"

Ta kauda kai

"Iyye ni zan zaɓan maka abinda zaka ci?, Ni kai ne?"

Ya dafe kanshi a ranshi yace

_Ya Allah have mercy on Me,Allah na tuba_

A fili kuma yace

"Ni na ƙoshi babu Abinda zanci"

Tashi tayi daga Kusa dashi ta koma chan Gefe

"Nima bazanci Komai ba, Kuma....kuma "

Sai kuka

"Kuma Nidai wallahi Yunwa nake Ji"

Kwantar dakai yayi, ya jingina da Gadon yana jan karamin tsaki.

Cikin kuka tace

"Allah Sarki ,don Kaga banida Uwa bani da Uba shine kake Son Kaga baya na ko!"

Ta ƙare maganar da murya mai ban tausayi.

"Ihty.....!"

Yaja sunan chan kasan Maƙoshi.

"Na'am ....."

"Wa ya hanaki cin abinci?"

Ta Turo baki

"Ba gaka ba?"

ya juyo ya ware idonsa akanta

"Ni....?, Saboda nace banajin yunwa...?, Tho Tashi Muje "

Ya faɗa yana tashi daga kan Gadon, ta juyar dakai ranta a ɓace.

"Ni babu inda zani, Ni kaje ka samo mana Abinda Zamuci"

Fita yayi yana sosa kanshi, Aeesh Rigima so yake ya tambaye ta wani kalar Abinci zai kawo mata, Amma yana tsoron Ƙorafi.

Direct kitchen ya nufa, ya dafa Mata Doya da Stew ,Sannan yayi steaming Taliyar da taci jiya da daddare ya bude fridge ya dauko mata Youghurt mai sanyi da Cups Guda biyu.

Ya kawo mata, Tana zaune kan gado tana game da wayarsa ya shigo ya ajiye komai a kan Rug, Saurin tasowa tayi kaman Abin arziki ta zauna harda tankwashe ƙafa.

Murmushi ya saki ganin batayi ƙorafi ba, Saida ta bi Abincin da Kallo sannan Ta taɓe baki, Tasa Wuƙa ta yanko Doya Sannan tayi deeping dinshi a miya, takai Bakinshi tana Murmushi Baiyi musu ba ya buɗe bakin Ya tauna cikeda mamaki.

Ta dauko na biyu ta sa masa a baki, nan ma bai Musa ba ya buɗe baki ya karba.

Ta yanko na uku kenan zata kai bakinshi ya riƙo Hannun ta ya kai bakin ta,ta rufe bakin Gam tasa masa Kuka, ita a dole bazata ci Doya ba maƙogaron ta yayi kaɗan, Doya bazai iya wucewa ba, yace taci Taliyar tace Taliya da miya ƙauyenci ne, ita ba yar ƙauye bace kuma Allah shi taci jiya daddare yace ya za'a yi kenan

Tace tunda shi ya dafa Doyar, yaci Abinshi Sai ya tashi Su fita suje kasuwa Su siyo Garin Tuwo da busashen ƙuɓewa yau shi take jin ci.

Kunji fa karambani irin na Aeesh😏, ta ina take son ya fara neman Garin tuwo a Canada ?

Kallon Agogon Hannunshi yayi, 1:50, yace ,lokacin sallah yayi Muyi sallah sai muje, Sallar Sukayi sannan Suka shirya tana Sanye cikin Baƙar Arabian Gown, Tayi Rolling da mayafinta , Shi kuma yana Sanye Cikin Farar Inner shirt da Baƙar Open shirt a sama ,Shigar All black Yayi Inner shirt dinsa ce kawai fara ,sumar kansa yasha gyara sai ƙyallin Oily hair yake.

Tunda suka Fito sai Faman jan tsaki take, a taxi ma da ta juya ta kalleshi sai ta kauda kai Ta buga tsaki.

Da fari Banza yayi mata Gudun kada ya tanka a samu matsala, chan dai ya kasa jurewa ya dubeta Yace "ya Akayi? Tace "Baka san Har yanzu akwai Corona a Ƙasar nan ba?"

Dubanta yayi cikin Rashin Fahimta yace

"Ban Gane ba"

"Taya Zaka gane mun fito babu facemask a fuskokin Mu"

Dariya yayi daga nan bai sake cewa komai ba, ita ma bata daina Jan tsakin ba .
A wani kayataccen Shopping mall Mai taxi ya Sauke su , Gate din wurin suka siya face mask baƙaƙe suka kwama daga nan bata sake jan Tsakin ba ,Suka dudduba ta ko ina babu garin Masara, har sun Fito zasu tafi tace su koma ta hango Corn flacks Komawa sukayi Tajidosu dayawa kaman Mai shirin buɗe kanti guda baice mata komai ba ya biya suka fito.

Sunje wurare fin biyar amma babu Garin Masara,hakan yasa hankalin ta ya fara tashi ji take kaman yau idan bataci Tuwo ba mutuwa zatayi, Shima ganin yanda hankalinta ya tashi yasa ya dubeta cikeda tausayawa Yace

"Ko mu siya Sabon shinkafa ne muyi Tuwon shinkafa?"


Ta gyada masa kai da sauri tana Murmushi Ice cream ne a Hannunta Amma sam bata jin dadinshi, Kasuwa suka nufa, suka siyo Shinkafar sannan Suka siyo Danyen ƙuɓewa shima da ƙyar suka samu, Suka siyo kifi da kayan Miya da kayan Kwalama don Duk abin zaƙin da ta ganisai tace ya siya.


Haka suka jido kaya kanti guda suka dawo gida, lokacin Habeeb ya dawo Shi ya taya su Kwaso kayan.

Aeesh na ganin Ya shiga kitchen Murna Kaman ya kasheta yau zataci tuwo, har wani tsalle take tana Murmushi shima Murmushin yakeyi.

Ta dauko Frying pan bayan Ta daura Apron tace "Ahky In Soya Kifin Ko...?"

Ya girgiza mata kai, "ke me kika iya banda Haɗama?, ajiye min Pan...jeki zauna chan Karki Wahala"

Ajiye Pan din Tayi, ta samu wuri ta zauna tayi Shuru .

Jefi jefi ABDUL na dan Leƙowa shima ya ƙosa a gama tuwo yawunshi har ya gama tsinkewa.

Kafin Wani lokaci har Tuwo ya sauka, ko ina ya gauraye da ƙamshin girki ita ya fara sa mawa, ta karba Jikinta har wani rawa yakeyi Ta cinye Malmala Biyu, ya sake sako mata wani ta cinye ,Abdul na ganin haka Yayi saurin Dauke biyu Kar ta cinye ta sake neman Wani, Aikou haka akayi tana gama ci ta nemi wani, Ashman Ko ɗandanon Tuwon Baiyi ba, ita ta cinye shi duka.

Tana gama cinyewa tayi gyatsa _Alhamdulillah_

Murmushi yayi Yace "a ƙaro ne?"

Tayi Saurin Gyada masa kai Eh ,Kafin ta ida sauke kai Wani irin Amai ya taho mata da sauri ta tashi Amma kafin Ta fita Ya gama zuwan Mata, daidai lokacin da Sadeeq ya shigo .

Aman Takeyi Sosai tana ƙarawa kaman zata amayo Kayan cikinta, hankalin Sadeeq a tashe yace ta tashi Su tafi Asibiti ,Ashman ya murmusa yace Ba wani Ciwo ne ba Kawai Overload dinda Tayi wa abinci ne yaso yayi Affecting dinta, ganin Aman yaƙi tsayawa Yasa Ashman yayi mata allurar tsayar da Amai, daga nan Sai barci ya dauketa.

Dakinsa ya koma Sai yanzu hankalinshi ya kwanta ,ya dauko System dinshi Yana dudduba New messages.

Wani message ne ya dau hankalinshi daga _Khameeth Nasss_ (Abba kenan)

Jikinshi na rawa ya duba tun kafin ya ida karanta Saƙon Zufa ya gama Jikashi, Dole ya koma Nigeria cikin Satin Nan, bazai iya juren Zaman Ƙasar ba Alhalin Mahaifinshi na Fushi dashi.

Yana Cikin Wannan Yanayin Yaa Sadeeq ya shigo Da waya a hannunshi, yace yanzu suka gama waya da Reey wata daya kenan Da komawan su makaranta, har wasu malaman Sun fara Test Kasancewar Final semester Dinsu ce Project supervisor Dinta yace idan batazo ba nan da next week Zaiyi canceling Project dinta, Kuma sai ta jira Next year kamin tayi Wani ,don Haka komawa Nigeria ya kamasu dole.


A satin Suka Gama Shirin komai suka dawo Nigeria ,a gidansa ta sauka ta ajiye kayanta a dakin da ya nuna mata a matsayin nata, sannan ya Kaita makaranta dakanshi.

Idanunta Sun kukkumbura saboda kukan da tasha, bataso ta bar Canada Batareda Ammie ta bude ido sun zanta ba.

Cikin Sanyin jiki ya juya motar ya nufi gidan Abba,cikeda fargabar abinda zai tarar.


Cikin yan daqiqu ya isa gidan.

Ahankali yasanyo kafa hafito daga motarsa gabansa na bugun uku uku.

Allah yasani dauriya kawai yake don zuciyarshi fall take da fargaba.

Kamar kullum dai, mai gadi da ma'aikatan waje nanan mazauninsu sai kallonshi suke suna kama baki, don Sun san yau dinnan Akwai kallo.

Fuska a daure ya qarasa ciki, har ɗakin Abba duk inda Yabi sai ya bar Ƙamshin Turarensa.

Gaban Umma saude ne yafadi datayi tozali dashi, Wanda a halin Yanzu take masa kallon Boss dinta.

"Is your husband around?" Inji Ashman cikin tsare gida.

"Ehmm...eh yana nan"

"Ok? Tell him yayi Baƙo"

Tafada tana zama kan daya Daga kujerun da Abba ke zama ya Dora kafa daya bisa daya, gabansa na cigaba da Faɗuwa.







Thoufa Yau ake yinta🏄🏾‍♀️

Nikam nayi Gabas🏄🏾‍♀️🏄🏾‍♀️


Bintou ✍🏽

31th OCT
[11/9, 9:33 AM] Bintou abdool: *_WUƘA A ZUCIYA_*

_BLEEDING HEARTS_

*048*



Shiru ta yi kamar bazata tafiba, saikuma tatuna da rashin M irin Ashman.

Tana shiga babu jimawa ta fito ranta a ɓace

"Yace ka shigo"

Ko a jikin shi, ya tashi cikin nutsuwa ya gyara zaman baƙar shade ɗinsa sannan yanufi dakin Abba Gabansa na faduwa.


Ajiyar zuciya yasaki sannan ya runtse idanunsa ya murda kofar ahankali, yashige bakinsa dauke da ADDU'A.

"Hasbinallahu wani'mal wakeel"

Inji Ashman a cikin zuciya dayayi tozali da Abba Fuskar nan a haɗe kaman hadari.

Batareda Ya iya Buɗe lumsassun Idanun sa ba Yayi kneeling Akan Gwiwowinsa Jikinsa na ɓaci.

Rai ɓaci Abba ya taso kaman zai Wanke shi da mari,ko me ya Tuna oho sai yaja baya yana huci.

"Ni zaka tozarta Sufyan ?, Ni?, Ni mahifinka?"

Abba ya fada cikin huci, Shima Ashman din huci yake ciki ciki, muryarsa chan ƙasa yace

"Am sorry d...."

"Sorryn Ubanka...!"

Abba ya katse shi rai bace

"Naji labarin Barin Ƙasar Kukayi da Aeesha,Hope ka dawo min da takardar ta?"

Dagowa yayi ya dubi Abba Da idanun Sa da suka sauya launi zuwa Pure red, sannan ya ciji Lips ɗinsa da Ƙarfi, murya chan ƙasa yace

"Ihty nada Ciki bazan Iya sakinta yanzu ba!"

With so much shock Abba y dubi Ashman

"What.....!, Tanada me?"

Sake Sunkuyar dakai Ashman yayi

"You heard me, Cewa nayi she's pregnant ”

Sauke numfashi Abba Keyi, Zufa na yanko masa, ga wani Azababben bugawan da Zuciyar sa ke yi, ya sauke wani wahalallen Ajiyar Zuciya, ya goye hannunsa a bayan sa, yana zagaye Ɗakin Without Knowing What to say, don he's totally speechless ma chan ya juyo gare shi

"Kayi naka Son ran, nima nayi nawa"

Yaja Numfashi Saboda yanda Muryarsa ke rawa, Cikin Cracky voice dinsa ya cigaba

"Next week inada meeting Wanda zanyi attending a Mexico, you'll represent me, And also Tare zaku je da Matar ka Deejah baka isa ka dawo ba sai nan da 6months, ina so yanda ka sanar da Ni Aeesha nada Juna biyu ya kasance haka zaka sanar dani Deejah nada Juna biyu itama ,In ba haka ba babu kai babu dawowa 9ja har abada"

Saurin Ɗagowa Ashman yayi, Sai kuma ya sunkuyar dakai ganin Babu imani a fuskar Abban ,yasan a halin yanzu babu wata kalma da Zai ara ya gudanar Abba ya saurareshi, Sai yayi Smirking Wanda akace yafi kuka ciwo yace

"Na gode Abba, Amma ina tsoron Saɓa Alƙawarin ka"

"Saɓa alƙawari na nawa kuma?, And one more thing kada Ka sake Nufar Asibitin ka da niyyar aiki, tuni na damƙa ma Saleem Komai"

"Nagode Sir....."

maganarshi ta tsaya da wani abu yazo mashi a brain.

Saurin dagowa ya sake cikin Mamaki

"What dad...!, Saleem kuma...?, Ka manta he's just an ordinary Gynecologist?, me yasani? How can he handle a medical Hospital ?"

Murmushi Abba Yayi Ganin Rashin jin dadin Hukuncin sa ƙarara a idon Ashman,yace

"He has the idea Ka manta a ƙasar da yayi karatu?, he wasn't specialized on Gynecology only But also on medical and surgical courses, yanzu He can Even Handle it More than you can’’

Murmushin yaƙe Ashman yayi yana Miƙewa daga duƙen da yake , ya kakkaɓe jikinshi Cikin Turo baki yace

"Allah na gani"

Abba yace
"Allah ya isa Ya kamata kace, ka fito Fili ka faɗa Tsoron me kake ji?"

"Ba tsoro Bane, Amma ina takaicin girman da nake bawa Mutumin da yayi Kyauta ya Kuma kwace abinsa akan Yar karamar dalili"


"Whatever Yanzu dai since ka gane you're Now jobless sai Ka kwashi Takardunka Kaje bara wasu Asibitocin Maybe su tausaya maka su Karɓe ka"

"Abba kai kanka shaida ne ,babu wani asibiti a Nigeria Walau babba Ko karami da zan Iya Zuwa maulan Aiki a wajen su dakaina, i have Plenty offers but I rejected them just for you, and ya kamata Kasan Cewa am not jobless I even own a company of my own"


"Tashi ka Fita"

Gyara tsayuwar sa Ashman yayi, ya zura hannayensa cikin Aljihu, ya fuskanci Abban nasa sosai

"Dad yaushe ne tafiyar?"


"Jibi ne, kuma ka dawo da matarka ɗakin ta yau dinnan"

“ok Sir"

Kawai yace ya fice daga ɗakin gaba ɗaya ,yana jin kansa na Sarawa, baya jin zai Iya dawo da Deejah yanzu Tayita zaman ta achan in yaso Ranar tafiya Sai ta taho Su tafi.

★★
Tunda Ta dawo Reey ke Mamakin Wannan Mugun ci da Aeesh ta ƙaro, ga wani irin Ƙiba na musamman da tayi, a Rayuwarta Ko a mafarki aka fada mata Aeesh zatayi Ƙibi tuni zata farka ta ƙaryata zanyen Amma sai gashi a zahiri, Ga wani irin kyau da tayi, Asalin Color nata ya fito Tarr natural Chocolate Color, Amma yawan ciye ciyen ta ya fara tsorata ta, Ita da ta dawo Yau kamata yy ta kasance a gado tana huce gajiya, amma Sai gashi kaman ba da ita aka Ƙetaro wata Ƙasar ba ko a jikin ta, sabgogin gabanTa take yi.

Da fargaban Kada zargin da Takeyi akanta ya zam gaske ta kwanta, itama Aeesh saida ta Tabbatar ta take Girkin da Reey ta Girka musu da daddare wanda take sa ran Sasu ci da safe, su hada Da Tea sannan Ta kwanta.

2:00am
Cikin dare ta farka da Wani mugun Yunwa,Ta jiƙa Corn flacks ɗin da ta dawo dashi, tana sha tana hawaye don tasan koda ta tashi Reey babu Abinda zata mata cikin daren nan, haka nan tayi ta cusa Shi ba don Tana jin Daɗin shi ba.
Sai taji tayi kewar Ahky Sosai Allah Sarki bawan Allah da suna Tare Da hankalinshi Ya tashi ya shiga kitchen ya dafo Mata abinda takeso, tunda ta fara tashin Dare bai taɓa bata Ɗumame ba, komin date haka nan Yake zagewa ya Girka mata sabon Abinci mai zafi, sau tari bata iya Jure Jira, Sometyms akan Wuta take Deba tafara ci Sometyms kuma Sai tayi bacci yayi ta tashin ta taƙi farkawa sai Safiya tayi Take daukan Abinta taci.

Wayar Reey ta dauko ta cire pin sannan ta lalubo number Shi Tayi mashi short text

_ihty miss You_

Daidai lokacin da ya farka zaiyi Sallah,yaga Wayar sa tayi haske, ganin Text ɗin daga Reey ne yasa Ya saki Murmushi yasan daga Mutumiyar ne ba tare da jinkirtawa ba ya Tura mata

_Ahky miss You too_

Ya kuma daurawa da

_you're hungry Right?_

Sai ta tura Masa crying Emojis

😭😭😭😭😭😭😭

Shi kuma ya maida mata da Emojin dariya

🤣😂🤣🤣🤣


Aeesh :- I know Am not normal kai shaida ne da ba haka nake ba, You can laugh as u can But I know Am not normal.

Aaash:- yeah Off course you may be sick Buh I dunno!🤨

Aeesh :- may be am Pregnant ko🤔

Aash:- 🤣🤣🤣
_Who knows?_

Aeesh :- if that happens I will kill you 😠😠😡😡😡

Aaash:- your kid's Father will be Gone, and The world will identify them as Orphans


Aeesh :- please stop this joke, har Ƙasa na fara tsarguwa, Allah yasa ba ciki ne dani ba 😭😭😭😭

Aaashman:- ki daina Tsarguwa Sau ɗaya ne fa?, just once and

Please Login or Register in order to submit comment