Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ihty,Sickness is not the show for sadness...."

Buɗe ƙofar da akayi ne yasa shi maida dubansa Ga mai shigowa.

Sadeeq ne ya shigo Da sallama a Bakinshi, Chak ya tsaya in shock Yana ware idonshi Akansu yana Kallon su unbelievably

"What..!, Ku kuma daga Ina?"

"Surprise"

Ashman ya Fada yana dan ware ido.

Cikin kuka Aeesh tace

"Yaya meke damun Ammie?, Bata motsi numfashi kawai Takeyi"

Sadeeq ya Girgiza kai cikin yanayi na rashin jin daɗi, yace

"Babu Abinda ke damun Ammie ,Kullum sai Likita ya bamu Tabbacin haka"

"Tho meyasa take kwance...?"

"You Kept quiet Kodai akwai abinda Kuke ɓoye min ne?, Ammie ta rasu ko...?"

Ya gizgirgiza kai Feeling sosad, sannan ya riko hannunta

"Aeesh...!, Nasan Kinada karfin Zuciya me zaisa na Ɓoye miki wani Abu?, Idan ma Wani abin ne ya sameta kece ta farko da zan fara sanar ma Trust me she's fine"

Duƙar dakai tayi, hawaye na dropping a Idanun ta, sadeeq ya saki hannunta ,Ashman ya Riƙo hannun , ya matse cikin nashi, yana rungumo kafaɗarta cikin sigar rarrashi.

Sadeeq ya dubesu yace

"Mu fita, yanzu lokacin Medication dinta ne, Nurses Zasu shigo su bata magani"

Fita sukayi banda kuka babu Abinda Aeesh keyi, dole Sadeeq yayi Musu jagora zuwa Masaukin su, Habeeb bayanan ya tafi makaranta , Haka Ashman da Sadeeq suka Taru suna rarrashinta da ƙyar suka samu tayi shuru barci yayi awon Gaba da ita.

*Nigeria*

8:56pm

Dawowan su kenan daga Masallaci Sunje sallah Isha'i

Tafe suke Ayyan Sai Zuba masa Surutu yake cikin harshen Turanci don Ko zo in kasheka Bai sani da Hausa ba, suna tafe hannun Ayyan Riƙe cikin hannunsa na dama, hannun hagun kuma zube cikin Aljihun sa.

sanye yake cikin royal blue Longsleeve jersy tank top, da Troser dinshi, All blue , Shima Ayyan Sanye yake cikin Jersey Amma Nashi sky blue.

Kai tsaye Part din Su Abba suka nufa A Parlo ya samesu hadda Inna saude, dasu Naseer suna Dinner.

Duban Rabeel da Naseer yayi a ransa yace

_kattin gaurayen banza_

Murmushi Abba yyi yace

"Son .."

Ssleem yace "Barka da dare"

Shima Ayyan Sai ya kwaikwayeshi, yace _baike dededede_

Duk sukayi dariya ,Abba ya jinjina kai , saude tace

"Wannan Yaron fa?" Ya ɗan shafa kansa yace

"Ɗan ƙanin Abokin maƙocin Cousin din Tsohon mijin neighbour Matana ne"

Dagowa sukayi Gaba dayansu suka dubi juna cikin Rashin Fahimta suka kuma maida dubansu gareshi Abba yace

"Ban gane ba, Allah dai yasa Ba karbo yaron Wadannan Yan iskan Abokanka na Turai kayi ba"

Cikin tafiyar nan tasa ta isa ya tako, ya samu Kujera daya ya zauna , ya dora Ayyan Bisa cinyarsa, fuskar nan tasa a hade kaman na wanda aka turowa sakon mutuwa

"Nifa sa ido ne bana so a rayuwata"

Yay maganar yana Lumshe idanu

tsareshi da Ido Rabeel yayo cikin Gargaɗi ,saleem Ya sinne kai yana Turo baki yace

"Mutum ba'a sa mai ido ba tun Kana yaro sai da ya girma Za'a fara shiga rayuwar ka fisabilillah sai kace Ni kadai ne?? ,Daga an ganni da ɗa sai a tambayeni dan waye?, Satoshi zanyi?, ko kuma adopting dinshi nayi?, Please dad Inaso ka gaya ma matarka Yanda ka bata shiga Sabgata ba sanda nake yaro yanzu ma ta daina don bazan iya jurewa ba, na riga saba da Rayuwar ƴanci"

Ya fada Yana zuba ma kansa abincin, ya Ƙwala ma Inna Yathai Kira da ƙarfi, inna Yathai dake Dakin Goggo ta taho jiki na ɓari .

Dubanta yayi a natse yana Yatsine fuska

"Haɗo mana coffee nida Ayyan"

Ta ɗan russuna cikeda Girmamawa tace

"Ranka shi daɗe Coffee wane iri?"

Dagowa Abba yayi, ya dubeta itama dubanshi tayi a sace ta kanne masa ido ɗaya, yayi Murmushin gefen baki yana cigaba da cin abincinsa.

Saleem Kaman Bazai bata Amsa ba, saida Ya yagi naman kaza , ya saka ma Ayyan a baki sannan yace

"Normal Nigerian Coffee"

"Da Sugar Or Honey"

Tsawa ya daka mata, ya bugi dinning table da ƙarfi har saida Ayyan ya tsorata

"I said Nigerian Coffee "

Cak Abba ya tsaya da cin abincin yake, kafin ya ɗaga idanunsa suka haɗa idanu da inna Yathai, cikin sanyi ya kuma kallon Saleem , Shima Saleem Kallon sa yayi ganina idanun Abba ya cika da ƙwalla yasa ya ɗan zare ido yace

"Dad what again?"

Girziza Kai Abba yayi, Hawayen dake maƙale a gefen idonsa suka sauko, ya sa hannu ya ture abincin dake gabanshi ya miƙe tsaye haɗida ture Kujera ya nufi ɗakinsa.

Da mamaki sukabishi da kallo ,tunda Suke basu taba ganin Abba cikin wannan yanayin ba, yanayi mafi ban tausayi harda hawaye Sukagani a idon nashi.

Taɓe baki inna Yathai tayi, ta nufi kitchen ,babu wata damuwa a tattare da ita

Gabaki dayansu dubansu suka maida kan Saleem don Sunfi Alaƙanta Yanayin Abba da kalamanshi.

Rabeel yaja Yar ƙaramar tsaki shima ya miƙe yabi bayan Abba, Shima Naseer ciki Ciki yaja nashi Su nafeesah kam ko a jikinsu dama halin uwarsu garesu.

Naseer yace
"Gaskiya yaya baka kyautawa, Koma dai menene Uba Ubane, kuma matsayin uba ya zarce komai tunda ya kawoka duniya, Wlhy ka bar ganin Abba na raga maka irinsu daya da ya Ash kaji tsoron randa ransa zai ɓaci akanka, Ayau har takai mahaifinka ya zubda ƙwalla akanka kaji tsoron Fushin Allah akanka”

Harara ya watsa ma Naseer wanda hakan Yasa shi saurin jan Bakinshi yayi shiru, yaja yar karamar Tsaki

“ni dama tun a duniya nasan makomata, Shi yasa nakeyin duk Abinda nasan bazai kawo min matsala ba...."

Sai yayi shiru sakamako Abinda ya gifta Brain ɗinsa ya kai dubansa ga Nas

"Kai don Ubanka Kaine ma zaka Min wa'azi?"

Naseer ya Girgiza kai ransa ba daɗi, sam yanda Abba yabama saleem dama yake Gasa masa magana yanda yaga dama bai dace ba

"Gaskiya ce dai bazamu Daina fadinta ba, duk wanda ya gujeta, Shima Yasan Makomansa"

Saleem yasa hannu ya make ƙeyar Naseer

"Kai tashi ka bar nan"

"Kayi hakuri Saleem Ni babu inda zani?"

A fusace saleem ya kai dubansa ga Saude yace

"Mum talk to your Son ya tashi ya bar nan inba haka ba sai na babballashi"

Saida naseer ya debo Abinci ya kai bakinsa sannan yace

"Bazan Je ko ina ba in Ka ga dama ka yanka Ni!, Daga na Faɗi gaskiya?"

Sake make masa keya Salem yayi da ƙarfi

"Don Ubanka Ni kake gayama wannan Maganar?"

Dubansu saude tayi, ita da so samu ne ma ta barsu a haka suyita fadar burinta bai wuce taga ta raba kansu ba, rai ɓace tace

"Naseer Ka tashi ka tafi"

"Kiyi hakuri Mum Babu inda zani sai na ƙosh...."

Miƙewa Salem yayi ya kashe shi da mari, ai babu shiri yana jan Allah ya isa.

Shima Saleem barin wajen yayi yana jero tsaki.

"Ranka shi daɗe ga Coffee din"

Yaji muryan inna Yathai ta bayanshi, banza yayi mata ya nufi sashin su, Binshi tayi da Coffeen, yana Kaiwa bakin ƙofa zai bude yaga inuwar mutum abayanshi

Juyowa yayi a fusace ya daka mata tsawa

"What??, what again?"

"Sir the coffee "

A ƙyamace ya kare mata kallo kaman yaga Abin ƙyama, yana wani taɓe baki da hanci, baki a taɓe yace

"Kin Ketaro sashen Ku dashi a buɗe a haka kike Son Nasha?, After those Microorganisms da sukayi dropping a Ciki?"

Cikeda Girmamawa tafe

"Sorry Bari In hada muku wani"

Ya Lumshe ido kaman mai jin bacci, cikin sigar raɗa yace

"Good for you"

Ta juya zata koma sashen su Abba ya kirata

"Come here..!"

Ta dawo, yace

"Banida kitchen be a sashina?, Ko arziki na kika raina?"

"Yi hakuri ranka shi daɗe"

"Muje ki hada min anan?"

Yay maganar yana Ida bude kofar.

Da sallama ya shiga hannunshi Riƙeda na Ayyan dayan Hannun kuma zube cikin Aljihu, tabiyoshi a baya.

Maryam dake zaune a Parlo watching TV na kdrama ta ɗan saci Kallonsu ta mayar kan TV Batareda tace Dashi uffan ba, yayi shigewarsa ɗakinshi.

Zuwa inna Yathai tayi, ta russuna a gaban ta

"Ranki ya dade kema kina buƙatar a kawo miki Coffeen ?"

Maryam Ta girgiza kai Murmushi manne a fuskar ta

"No bana bukata, inna Coffee yace ki hada masa da daddaren nan?"

Inna ta Kauda kai a tausashe tace

"To ya zamuyi?"

“inna kije ki huta, Bari in haɗa masa tunda mijina ne"

Wani irin ɗagowa inna Tayi, fuskar ta ɗauke da farincikin da ita kanta ta mance rabon da taji makamancinshi a zuciyar ta wacce ta gaza ɓoyuwa a zuciyarta tafito fili, ta saki Murmushi tace

“Nagode diyata, Muje kitchen din tare don kar yagan bana komai hakan ta zama matsala"

Cikeda mamaki Maryam ta dinga Binta da kallo tana mamakin Dalilin da yasa Inna Farin ciki, ta saba yunkurin Tayata ayyuka idan Saleem ya sata, don a Ganin ta bai dace tsohuwar mace kaman wannan ya ringa sata aiki ba, Amma ko sau daya bata taɓa barin mata Aiki ba, sai gashi yau daga tace ta kawo sai ta kawo .

Taɓe baki tayi, ta mike suka nufi kitchen din, Tana Hana Coffee din Suna hira , Maryam tace

"Inna kin san wani abu?, Wlhy aduk sanda naga Saleem nayiwa mahaifinsa magana sai inji raina na ɓaci sam Babu ɗa'a a zamantakewarsu ko kadan, sai inji rinƙa tunanin Ko dai ba shine mahaifin nashi ba?"

Murmushi Inna Tayi tace

"Shine mahaifinsa kawai dai haka tasu zamantakewar take"

Maryam tace

"Sai naga kaman Abba baya Son Saleem"

"Subhanallah Kin Taba ganin Inda uba yace baya Son dan da ya haifa? ,Ko kuma inda kikaga Namiji ya auri mace har ta haifa masa ɗa yace baya so?, Kawai de kinsan Rayuwace bata rabata da ƙalu bale da matsaloli ,da kuma Akasin tunani Sai kin dage matuka wajen Roƙa ma Saleem Lafiya ,a halin yanzu kece kadai yake da wacce zata iya mai wannan taimakon"

Da mamaki Maryam ke dubanta

"Inna ban gane ba ,Dama saleem din bashida lafiya ne?"

"Eh he's once a psychiatric Patient "

Da Mamaki Maryam ta rinka kallonta kafin tace

"Psychiatric patient kuma"

Inna ta kyada kai

"Kwarai kuwa,bai cika hankali ba, baya ganin Kowa da mutuncin da abin ya dame Mahaifinshi har Asibitin asibiti ya kaishi Lokacin yana yaro, amma sai sukace lafiyarsa kalau kuruciya ce,Amma dukda haka sun bashi magunguna amma gashi har yanzu ƙuruciyar taƙi barinshi"

Maryam ta kauda duban ta daga gareta tana taɓe baki a ranta tace

_no wonder mutum kullum a buge babu fasali, ashe duk jin kansa na Rainon gidan mahaukata ne_

A fili kuwa cewa tayi
"Kenan inna kin fi 20yrs kina aiki a gidan nan?"

Inna tace

"A'a amma na kai sha shida"

Tayi magana a hankali tana bin fuskarta da kallo tana ƙara ganin zallar kamannin ta da fuskar Maragayiya yar aikin gidan Fatimah , kasa hakuri inna tayi tace

"Ni kam in tambaye ki?"

Maryam tace" ina jinki inna"

Inna tace "kin san wata Fatima?, Ana kiranta maman Yan biyu"

Gabata taji ya fadi, tayi saurin kyada mata kai

"Eh na santa, ta rasu ai...."

Inna tace

"Kin santa?!"

Sunkuyar dakai Maryam tayi, hawaye na taruwa a Idanunta murya chan kasa tace

"Eh na sani..mahaifiyata ce"

Jikin Inna ne yayi sanyi , _Aikam in da gaske Maryam Matar saleem itace Ɗiyar Binta Tabbas Akwai matsala, matsala gagaruma_

Saleem ne ya Turo ƙofar, ya shigo Ayyan na biye dashi kaman bindi

"Where is my coffee ?"

Duban Maryam Yayi yace

"Keh kuma me ya kawoki kitchen?"

Ko kallonshi batayi ba ,balle yasa ran samun amsa daga gareta.

Cikeda Girmamawa Inna Yathai ya Mika mashi coffee dinsa bayan ta zuba masa shi mug, Shima Ayyan bashi nashi tayi, ta fita.

da sauri Maryam ta bar kitchen din idanunta cike da hawaye ko gabanta bata iya gani sosai, ta fada kan gado tana kuka, ji tayi mutuwar mahaifiyar ta ta dawo mata sabuwa.

Taɓe baki saleem yayi, ya kamo hannun Ayyan suka fito suna sipping coffee .

Fita Inna Yathai tayi tana ta murmushi.

Maryam ɗiyar Binta tsohuwar matar Sa'eed ,Budurwar Abba, her arrival in saleem's life will bring light to his darkness ,Tabbas Tana hango hanken dake biyeda Yarinyar Amma Fa akwai gagarumin Matsala nan Gaba in ta gano Sanadin Mutuwar mahaifiyarta,Kamata yayi ta fara sanin Tarihin Saleem ta yanda koda tasan Wanda ya kashe mata Mahaifiya bazata gujeshi Ba, da wannan tunanin Ta nufi ɗakin ta.

Turo ƙofar Ayyan da ya biyota yayi, yana
"Mummy..."

Kuka kawai Maryam keyi tanajin zuciyarta na mata zafi, hayewa yayi kan gadon , hannunsa riƙeda Tea mug

"Mummy are you hungry ?, Stand up let's Drink coffee "

Bata kulashi ba kukanta take , abubuwa da dama na rayuwarta suna daɗa dawo mata.

Ayyan ya dafata da hannu ɗaya yana dan jijjiga ta kadan

"Mummy why are you crying?."

Nan ma Shuru ta mashi

"Mum Please Stop crying...."

Ganin bata Amsa shi ba yashi dakatawa yana dubanta jikinsa a sanyaye.

“Mum is your stomach paining you?, Are you hungry ?, Did dad Yell At you....?, Are you feverish ?, Let's go to the hospital "

Nan ma Shuru, kwanciya yayi a bayanta yana shesseƙa shima kaman mai shirin yin kuka,Ta ɗago a fusace ta daka masa Tsawa

"Get out of my head"

Jada baya yayi a tsorace , coffeen hannunsa ya zube akan gadon, cikeda tsanar yaron ta daukeshi da mari ,ta ja kunnenshi jashi kaman zata tsinka, sai ihu yake , ta ja hannunshi waje kaman kayan wanki ta dire a ƙofar Dakin saleem

Saleem najin Kukanshi ya fito hankalinsa a tashe yabi bayanta, amma kafin ya Isko ta har ta shige cikin bedroom dinta ta rufe ƙofa ta kwanta tana jin temperature dina tana kara hawa.

10:00 nayi ta runtse idonta tana karanto duk adduoin kwanciya, amma sam bacci yaki zuwa

gaba daya ta ƙagara gobe tayi, taji labarin Ummanta a bakin Inna Yathai Nan take hawaye ya balle mata.

Kuka take yi sosai amma ita kanta bata dalilin kukan nata ba. Shin na samun Tabbacin wacce tasan Mahaifiyarta ne ko kuma na menene oho. Tasan kila Karshen zamanta a gidan ne ya kusa shi yasa Allah ya hankado Mata Inna Yathai cikin sauki.

*Canada*

Aeesh was great, Babu Abinda zatayi ma Ashman da ya wuce Addu'a,ya tsamo ta cikin rayuwar kadaici ya jinginata da bangon ta da tagama cire rai da sake jingina dasu nan kusa, Yanzu ta fahimci family is everything, babu abinda yafi dadi irin ka ganka a cikin 'yan'uwanka, yanzu a Canada in ta kalla hagu da dama taga Habeeb da ya Sadeeq kuma 'yan'uwanta ne ,Sai taji like the whole world was Empty su kadai ne a cikin ta, ga Kuma Yayanta da tafi so fiye da komai wato Ashman Duk yanda tayi ta daina kulashi ta kasa, Ashman yayi mata Abinda ko da tanada uba Iyakacin Abinda zaiyi mata kenan, baiyi deserving shariya daga gareta ba, after all Shariyar ta a Gareshi ba shi kadai yake Affecting ba, yau kwanan su Uku kenan da Zuwa Canada Kullum sai sun je asibiti amma duk in Sunje Aeesh Bata dawowa da dadin rai ,kwana Takeyi tana kuka, shi yasa yau da zasu tafi suka barta a gida, itada Habeeb hira Sukeyi tana tsokanarsa ta dubeshi tace

"Habeeb Yanzu idan idan kuna jin yunwa sosai ya kuke yi?, Nifa tun da nazo ban taba koshi ba, daure wa kawai nakeyi, abincin restaurant baya isana"

Habeeb yayi dariya sosai yana kallon tarin Chocolates din dake zube a gabanta, ci take tana Ƙorafin yunwa yace

"Mu kam ai mun saba, Idan Kinga an dora abu akan wuta to ruwan sha yi ne ko kuma in soya kwai zamuyi"

Ta yamutse Fuska tana kai Chocolate baki

"Tabdi yaseen akwai Jarfa, anya zan iya rayuwar nan kuwa?"

Yayi dariya

"Eh kam Bazaki iya ba, Kin saba da cika ciki, kici 15plates a rana"

Hararar sa tayi, ta jefeshi da Pillow ta cafke yana dariya,

ita kadai tasan yanda takeji daga safiya zuwa yanzu taci abinci yafi sau Shida ,banda Yoghurts da chocolates dinda tayita ci Amma yunwa takeji again.

Kawda zancen tayi don Gani take idan suka cigaba da tattaunawa akan Abinci Yau yunwa sai ya Kaita lahira, dubanshi tayi har yanzu tana mamakin girman da yayi, sai kace ba Kaninta ba cikin tsokana tace

"Tho habeeb Da bana nan wake maka Wanka?"

Waro ido yayi, ya zuba mata Harara

"Kaiiii Lallai Ma yarinyar nan Kin Raina Ni"

Taɓe baki tayi , sai kuma ta saki dariya

"Aah ba batun Wani raini, Na taba yi maka wanka Faa"

Ta ida maganar tana kanne masa ido ɗaya.

Ya Harare ta yana dan murguda mata baki

"Yo Dan Kin taba min wanka ai so daya ne, kuma lokacin banida Hankali ne, amma ki dubeni yanzu kice zaki min wanka ai Sai kin Makance''

Chocolate din hannunta ta ɓare, ta gutsura Tana dariya sosai tace

"Babu makancewar da zanyi!!, Wani dare ne dawisu bai gani ba?"

"Kaji fa cewa ake Wani dare ne jemage bai gani ba?, Just Imagine Wacce bata san banbancin Jemage da dawisu ba itace take batun zata min wanka, Abege shift..."

Dariya sosai ta kumayi tana kare masa kallo, ta rungumo Pillow tana maida dubanta kan TV

" yo ai gani nayi koda kabar 9ja ko yayeka ba'a yi ba, yanzu Ka waniyi bulele ga Gemun da ka ajiye kaman wani babba, a haka in mun jera da kai Fa za'a iya cewa kai mijina ne, ko kuma babana"

Hararar ta yayi

" na lura tunda kikazo kike Bakin ciki akan wannan Gemun nawa, Hh Mage sai dai kiji kamshina Gemuna sai hange ko taɓashi bakiyi, zan de tayaki da addu'a Har sadaka zanyi Miki Allah Ya dubi lamarin ki ya baki handsome Man Kaman Ni, mai Gemu koda tsini biyu ne"

"Allah shi kyauta, koni inada Gemu sunfi sittin ,don Mugunta Ka rasa Addu'ar da zaka Min sai mai silin Gemu biyu?, Kaima nasan sirrin naka Gemun..!, Alcohol Kuke sawa Babu Abinda ban sani ba"

Wani murmushin yasaki mai sauti yana daukar filon kusada shi tareda rungume shi aqirji

"Eh din whatever wata ma tasa mu gani in xata ganu"

Har After 2:00 su Ashman basu dawo ba.
Yau kam tsokanarshi tayi tayi kaman yanda suka saba, har saida suka raba hali, 2:30 ta shige bathroom tayi wanka tai brush, tare da wanke sumar kanta, jikinta sai ƙamshin Canada shower gel yake, ko'ina na fatarta ruwa yake ɗigarwa ga body hair sun kwanta saman skin ɗinta, wajen mirror ta nufa, ta zauna tare da zabga uban tagumi tana Turo baki

"Ina su Akhy suka je?"

Ita harga Allah yunwa ta keji sosai, body cream ta ɗauka ta shafa a skin ɗinta, tana gamawa ta yi spraying jikinta da body spray, ta taje kanta gaskiya tana buƙatar zuwa a wanke mata, Rabonta da tayi Wankin kai tun kamin suyi Exams Sosai Gashin ya sauka har bayanta.
Miƙewa tayi zuwa inda kayanta ke ajiye,ta duba side dinda ta jera Gowns dinta ta ɗaga wani peach Italian gown sai kuma ta maida tana Taɓe baki saboda Ƙamshin turaren dake jinkin kayan baiyi mata ba.

Side din da ta jera Kananun kayanta ta duba ta dauko farar logoless Shirt, long sleeve, ta saka , Black Slim jeans Troser ta saka, sannan ta dauko small black cap na Sanyi tasa, wanda bai ida rufe mata Gashinta b, gaba ɗaya Gashinta ya zubo ta gefen fuskar ta da bayanta.
Miƙewa tayi tana Yatsine fuska ta nufi Parlo harta shige ta dawo ta leƙa bedroom ɗin su taga ko sun dawo amma babu su babu Alamar su, infact ƙofarsu a kulle take.

Zama tayi kan cussion ranta a jagule, _Haka kawai za'a gana mata azaba da yunwa?, Sai kace wacce tayi kisa?_

Habeeb na kallon ta yasan kwanan zancen don Yasan mutumiyar tasa bata wasa da yunwa, bai ce komai ba.
Ringing na door bell da taji ne yasa ta miƙe a hankali take tafiya cikeda zumudi, ƙofar ta nufa ta buɗe ƙofar, wani matashin saurayi ne tsaya, taja tsaki cikin takaici, yana tsaye hannunsa riƙe da leder Restaurant, yace

"Evening Ma" kai kawai Aeesh ta jinjina, don ji take kaman ta wankeshi da mari, ta sa hannu ta amsa ledojin

Saida ta Galla Masa harara, sannan da ƙyar ta buɗe baki tace
"Thanks."
Mutumin yace "Its from Sir Deeq"

Aeesh ta kuma jan tsaki, duk takaici ya kuma rufeta bata ce komai ba ta juya Bayan ta rufe ƙofar, parlon ta dawo ta zauna bayan ta ajjiye ledojin, habeeb ya taso yana bubbuɗe ledojin

wajan deep frizeer ta nufa ta ɗauki Yoghurt da cup ta dawo ta zauna, a cup ɗin ta tsiyaya idanunta akan television tana Movie dinda Suke haskawa.

juyawa tayi suka haɗa ido da habeeb, tace

"Meye a ledar?"

Kauda Dubansa yayi da buɗe takeaway ɗin, wani lafiyayyan gashasshen kaji ne, sai kuma wani gassasshen flour Kaman Gurasa Amma wannan ba irin gasuwar ta kanawa bace 😂, Don harda wani ƙamshi kamshin nama take Alama anyi masa haɗaddiyar hadi, Kuma gashin na'ura ce.

Ba irin tasu gashin Gawayi ba🤤, Dayan Takeaway ɗin ya buɗe yaga fried Irish da fried egg sai kuma Another brand of Youghurt katon gora kwara daya, ko ba'a fada ba tasan wannan nata ne ita kadai, abincin tabi da kallo a hankali ta taɓe baki Abincin kenan Kullum babu sauyi daga kaji Sai Kifi da Soyayyun Abubuwa , Itafa tafiso taci su Shinkafa tuwo ko tasha fate in tana jin yunwa Shike Riƙeta amma wadannan banda Yunwa da kwadayi ma babu Abinda zai ƙara mata goran Yoghurt din ta dauka ta tsiyaya a cup ta haɗa da wanda ta fara daukowa .

Shi kuma ya shige kitchen ya dauko wuka da fork bankare kazar nan take ya gama da ita.

Ita kou sai satar kallonshi take, chan taji cikinta ya murɗe yana mata zafi Alamar Yunwa takai makura, ta ajjiye Cup din Youghurt.

Ga kajin sai tashin Kamshi yakeyi ,zama tayi ta tankwashe kafa Tayita tura abincin tana haɗawa da sassanyan Yoghurt dinta, a haka har Suka cinye.

Yau gani tayi gidan yayi mata fadi, Babu su Sadeeq da Ashman Babu labarin su, da zarar sunyi surutun su sun gaji itada Habeeb sai Suyi kallo Lokacin Sallah nayi su tashi suyi ,A haka har bacci ya dauke su .

Su Ashman basu dawo ba sai after magrib, Jikin Ammie ne ya tsananta, kuma likitan dake dubata baya gari Shine suka jirashi yazo, dalilin da yasa basu dawo ba, basu son su gaya ma Su Aeesh Hankalinsu ya tashi.

Koda suka dawo duk sun kwanta, tashinsu Sukayi sai a lokacin suke sanar dashi abinda ya faru .

9:30

Habeeb yayi barci ,Sadeeq na dakinshi yana waya da Reey Reeyn shi.

Fitowa Ashman yayi ya nufi dakin matar sa, kwance ya ganta kaman tana bacci sosai ta rungome pillow a jikinta, she looks so sick and learn.

Jin tsayuwar mutum kanta yasa ta ɗaga suka haɗa idanu yana sanye cikin wata Armless da wando navy blue iya gwiwa, hannunsu zube ɗaya cikin aljihunsa ɗaya kuma Wayarsa ce, sai ƙamshi yake, Ƙamshin turarensa da take mugun So, a hankali ta Lumshe idanu tanajin Zuciyarta na Tsalle tsabar shaukin da tajata.

A hankali yake tafiya cike da nutsuwa ya shigo dakin, yana danna Ma Hafsah video call

Bugu daya ta dauka dama datan ta a bude yake

"Laahh yaya kaine?"

A hankali ya samu wuri ya zauna yana duban Aeesh da ta zuba masa ido.

"Eh nine..."
Tana kwance da wata pink Doguwar Rigar bacci mai kyau wacce tasha Hotunan teddies, ga wata pink hula a kanta.

wani ƙawataccen Murmushi Ya saki yace

"Ya school?"

Tace "Alhamdulillah yaya ina kaje Abba nata nemanka?, saura Ƙiris ya kai cigiyan ka gidan Radio"

Cikin e Sauri ya sa hannu ya dafe Bakinshi

"Really?"

Tashi tayi zaune tace

"Na rantse , bakaga yanda ransa ya ɓaci ba, In fesa maka wata Gulma ma?, ya kwace asibitin ka zai Bama yaa Saleem, Amma tukunna babu wanda ya sani kaima satan Amsa na baka"

Ya waro fararen idanunsa kaman zai fiddo su yace

"Da gaske?"

Gyara zama tayi tace

"Wallahi, ya kuma ce sai yasa ka saki Aunty Deejah, don Allah Yaya Ina kake dad yayi fushi dakai sosai fa"

Ta ƙarashe maganar cikin marairacewa

Ajiyan zuciya ya saki , yayi shiru kaman bazai sake magana ba, Sai kuma chan yace

"Tho naji kanwata, zan Tura Miki Kudi cikin account dinki, ki siya food Stuff"

"Nagode yaya Allah y..."

Dakatar da ita yayi

"Bye...!"

Kit Yayi Disconnecting call din.ya ajiye wayar, duban Aeesh yayi yaga har yanzu shi take kallo, ya kauda dubansa daga gareta yana Sauke ajiyar zuciya

Zame wa yayi ya zauna a ƙasa, ya dau novel din da ya gani a ƙasa

Duban Cover page na littafin yayi

*Dominantly yours*

Murmushi ya saki, a ransa yace _She too much likes love_


Zama tayi a ƙasa itama, ta ɗora kanta a kafadarsa.

Muryarta chan ƙasa tace

"Ahky...."

Lumshe Ido yayi, jin sunan yayi har cikin jinin jikinshi, ya Buɗe baki kaman mai ciwon Haƙori ya amsa

"Ihty....!"


"Akhy..."

Wannan karon Muryarta bai tsaya a jinin jikinta ba ,saida ta Ratsa ko ina na ɓargon sa.

Ya Lumshe ido Yana jin Abubuwa na sauya mazauni a cikin jikinsa, da kyar ya buɗe baki muryarsa kaman Na mai jin bacci ya amsa

"Na'am ihty..."


"A page 58 na tsaya, ka karanta mana"

Hannunsa na rawa ya fara bude littafin Har ya buɗo page

Please Login or Register in order to submit comment