Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

You thought I know nothing?"

Ta dakatar dashi a tsawace

"You Know nothing Aeesh ,Baki San Komai ba ,I'hv been worried About you that same night, I couldn't Even Sleep Duk Saboda ke I risked my life at that mare night Just to find out how u are feeling but All I got From you Was these?"

Cije Lips dinsa Yayi cikin Zafi ya cigaba da cewa

"Ba komai Is All my fault, I should Have stay Where God Leaves me , Nine nakeson Na kai kaina Inda Allah bai kauni ba, Zuciyata ta Yaudareni dayawa Da tayi Tunanin Yar Gidan Masu kudi irin ki zata so talaka irinna, I was Fooled..., Thank you Nagode "

Ya fada Yana ƙoƙarin shigewa Motar

"So Get off my car"

Duk Jikinta yabi yayi sanyi Sosai don kuwa Sai a yanzu taji rashin dadin Zargin da tayi masa , Aareef bai Chantanci hakan Daga gare ta ba,Atleast ya nuna mata so fiye da Kowa ,har Gashi yana Shirin Aurenta, ba kowane namiji zai iya Sadaukarwar nan ba.

"Sorry Sadauki na, I don't mean that to you,I was So nervous Pls kayi haƙuri"

Kauda kai yayi yana Furzar d Huci

"Kin bani mamaki Aeesh..."

"Pls ka daina Maganar Kayi haƙuri komai ya wuce , Kazo anjima in Jama'a Sun dan ragu zan baka kuɗin Naji ɗazu Umma saude na gayawa Ummana wai idan Baka kawo kudaden Kafin Yamma ba zasu Aura Mn Yaya Saleem"

Waro Ido Aareef yayi

"Waye kuma Saleem"

"Step brother din Yaya Aash ne, Bashida kirki ko kadan rayuwarsa Gabaki ɗaya a Turkish yayi shi Shiyasa bashida Tarbiyya baya ganin darajar kowa sai na Mahaifiyarsa da Abbansa ,Amma ko yaya Aash ba raga masa yake yi ba"

Jinjina Kai Aareef yy yana Saƙesaƙe a ransa Lallai Dole Yayi iya ƙoƙarin sa ya dage yayi wuff da Aeesh Yana hango Tarin Alherin dake tattare da Aurenta ,ya gayawa Dr Sabo da Nurses Ukun da Suka Bashi Kwarin gwiwan Auren Ta matsalar da Ake ciki Sun hada Hannu sun Turo masa 350k Ya fara Shirye Shirye, Burinsu a wannan Lokacin bai wuce Suga Matsiyaci yayi wuff da Aeesh ba don cika nasu Maradan.

Sosai Sukayi hira, hiran da rabonta da tayi Irinshi tun kan rasuwar Baffa ,har mamakin yanda Soyayyar Aareef ya mamaye ta lokaci guda take ko kadan Idan suna tare bata tuna Kowa bata tuna komai ,idan Basua tare kuma Shi kadai ke kasancewa a cikin tunaninta da mafarkinta.

A ranar kowa ya ganta zai san tana Cikin matsanancin FarinCiki mara misaltuwa Murmushin da ta daɗe batayi ba yau shi takeyi Ita ɗaya da zarar ta tuna kyakkyawar Fuskar Sa.

Da yamma bayan Ashman Yazo dubata Yajata Suka Nufi Gidansa ,tausayinsa takeji Sosai har yanzu Dingishi yakeyi Ƙafarsa bai Gama warkewaba ,Ya koma Amfani da Medicated glass don yanzu ba gani yakeyi sosai ba  ,baya iya driving hakan yasa Ya nemo personal driver ,Shi ne yayi driving Dinsu zuwa Gidan sa.

Gidan yayi kacakaca Sosai Babu kyan gani, tho me gyarashi babu Lafiya Saleem kuwa In ya fita tun safe ba'a Sake ganin fuskarsa Sai wata safiyar, Shigan dare yakeyi Bayan kowa ya kwanta, Rasuwar da akayi ne Yasashi Zaman gidan Dole don Yana Ganin ummansa Da Abba akoda yaushe.

Hijabi ta ta Cire ta Fara gyara gidan ,Cikin kankanin Lokaci Gidan yayi Tsab, Turaren wuta ta kunna Take Gidan ya Gauraye da Ƙamshin Turare Kaman Bashi ke Dan Doyi Doyi ba ɗazu .

Ashman Na zaune yana ganin Zuwa da dawowarta Sai Murmushi yake ,Bai taɓa ganin Ta tana Aiki ba ,Ko roba yace ta ɗauke narke masa take tace bazata iya ba , Sometimes ma Harda Kuka .

Lallai AeeSh Anyi Hankali.

Kitchen ta shiga ta girka msu taliya Tunkan Ta sauke Gidan ya Gauraye Da wani sabon Ƙamshin Girki mai dadi ta hada Msu da Fresh milk Mai sanyi ,tuni yawunsa ya Tsinke ya kosa ta kawo masa Kamar Tasan rabonda ya samu abinci a cikinsa Tun jiya da suka ci tare da daddare itama Haka.

Kawo masa Abincin tayi har inda yake zaune Ta sa musu Forks Biyu ,shi ya fara daukan fork din ya Fara ci bayaji baya gani ko kallonta bayayi.

Sosai yaci abincin yanaci yana shan Milk Sosai ,hakan yasa Aeesh jin dadi ganin hakan yasa itama cin Abincin sosai.

Bayan ya Gama ya ɗan Dubeta yace

"A yau naci girkinki a karo na farko ,Waya koya Miki girki?, Ni a iya Sanina ban taba ganin kin shiga kitchen da niyyar Girki ba"

Murmushi ta sakar mshi tace

"Ai yanzu dole na Farayin girki tunda na Kusa Shigewa Gidan Sadaukina Aareef"

Wani abu yaji ya Tokare masa Maƙoshi,Ya rintse Idanu sannan ya waresu a kanta cikin basarwa yayi mata wani irin kallo

'' Shiyasa naji Abincin Babu daɗi"

Miƙewa yayi ya dauko Ledar maganinsa Ya Sha, Kallon Sa Kawai Take Tana Murmushi Tasan duk basarwar nan na menene Don ta Ambaci Sadaukinta.

Tunowa tayi da Kudaden da zata ba Aareef, bata son taɓa kudin account ɗinta , a ɗarare Cikin tsoro ta dubeshi, Ɗagowa yayi ya dubeta shima ,Kallon da tayi masa Yasa Ya gane Akwai alfarmar da zata nema daga gareshi ,Don haka gyara zama yayi Yana Sake dubanta a halin yanzu Ya najin zai iya mata Komai duk abinda take buƙata Tunda bata da kowa sai shi.

"Yaya Pls...."

Sai Kuma tayi Shiru tana wasa da yan yatsun hannunta.

"Uhum..!, comeon what did you want?"

Ya fada cikin bata kwarin gwiwa.

"Kasan An saka ranar Aurena Da Aareef ko?"

Kyada mata kai yayi tare da lumshe Idanu.

Cigaba tayi da fadin

"Ina so in Fara Gyaran Jiki kafin Lokacin kuma Ina buƙatar kudade"

Kallonta yakeyi tana Kokarin hango wani abu

Ko kadan karya baya mata Kyau,ya gane karya tayi masa Amma ya basar,tunda kudi take Buƙata bazaiki bata ba yasan ba mugun Abu Zatayi dashi ba.

Ajiyar zuciya ya sauke ya furzar da Iska mai sanyi Muryarsa chan ƙasa yace

"Shikenan Abinda kike Bukata"

"Eh Amma kila zan Bukaci wasu kudaden Nan Gaba kasan Yanzu banida me bani, umma bazata bani ba"

Murmushi kawai yayi ya zura hannu cikin Aljihu ya ciro business card dinsa ya mika mata

"You know the Pin You can withdraw any amount Anytime, Daga Yanzu feel free ki tambayeni Komai Kinji?"

Kai ta gyaɗa masa Tana jujjuya business card din a hannunta Murmushi manne a fuskar ta.

Godiya Sosai tayi masa ,Mamaki sosai ya kamashi Ganin yanda take murna Rabonshi da ya ganta cikin Makamancin FarinCikin nan har ya manta.

Ruwan zafin da tasa a flask ta juye Cikin Tsaftataccen Bowl sannan ta Dauko Sponge da soft Cloth.

Binta da Kallo Yayi tayi har ta dawo ta Zauna kan Rug.

Kafarsa Mai Rauni Ta daga ta Dan tattare Kafar Wandonsa Sama.

Sosai Kumburin kafar ta tsorata ta, batayi zaton Yaji ciwo haka ba, dole ya kasa tafiya ,tausayinsa ne ya kamata Sosai da ta tuna yanda Motar tasu ta bige da gini a ranar In ba kiyayewan Allah ba Tasan da babu mai sake rayuwa a cikinsu .

Hannunta har Rawa yake ta tsoma softtowel din A cikin Ruwan dumin ta fara gasa masa Ƙafar tana Runtse ido don Tausayi.

Shikam kaman ba a Jikinshi Ciwon yake ba sai Kallonta yake cikin Burgewa.

Tausassan hannayenta Da yakeji Yana Shafar Kafar sa, shi ke taimaka masa Wajen Rage raɗaɗin .

Kafin Ta ida Goge kafar kuwa Hawaye Sun Wanke mata Idanu.

Ɗagota yayi Ya kalli Cikin Idanunta dake Fitar da hawaye ya sakar mata Murmushi mai narkar da zuciya.

"Ihkty kukan me kike yi?, Babu zafi fa?"

Kara matso Hawayen tayi ta ɗan Turo baki

"Jifa yanda ƙafarta ta Kumbura, ga fatar Gurin ya dau zafi, I can't imagine the pain u re going through"

Hannu yasa ya share mata hawaye,Cikin sigar rarrashi yace

"Haba Amaryata, Nurses basua kuka Idan suna Treating patients ɗinsu, am ur Patient U are my Nurse ,Ni na kamata nayi Kuka bayan Ciwon Kafa ga na ido Ga na zuciya,Pls ki daina kuka idan Kina kuka zaki ƙara ƙara min Wani ciwon ne akan nada"

Sosai magangganunshi suka ta6a Aeesh, Yanda yake magana Ma kadai ya isa Ya bayyana damuwar da yake ciki.

Kallon tausayi tayi masa

"Yaya is Something bothering you?"

Lumshe idanunsa yayi Batareda ya iya furta komai ba.

"Akan Rasuwar Baffa ko"

"A'a akan Deejah ne"

Saurin Ɗagowa tayi ta dubeshi, Cigaba yayi da cewa

"Bana Sonta, gashi Saura 5months ,Bazan iya aurenta ba, ban taɓa Sonta ba ,na yarda Da Soyayyarta ne saboda Kece kika Mn tayinta"

"Yaya dama Baka  Sonta ka yarda Aka sa muku  rana?"

"Ban san an sa ba Sai daga baya"

Dukar dakai tayi cikin Sanyi, Wannan wace irin qaddarace? Tausayi ya bata sosai, tasan he must be having tough time meyasa Zaiyiwa kansa haka bayan yasan Baya Sonta?, Meyasa zai amince da Soyayyarta bayan yasan bazai iya Sonta ba?.

Shiru dakin yayi sai Saukar Numfashinsu akeji qasa qasa,tana kallonshi tanajin wani abu na ta6amata zuciya.

Kallon fuskarshi take datayi fayau tana hango dan fadawar dayayi.

Ahankali tasa hannu tashafi lallausan gashin kanshi cikin tausayi ,ita kanta bazata Iya fasalta yanda takeji Cikin zuciyarta a halin yanzu ba  it's her fault Saida Ya Gaya mata Deejah ta taɓa samunshi da batun Soyayya yaƙi amincewa sbd baya ƙaunarta Amma ta dage Akan Kawartace zata iya rasa Rayuwanta idan Bata sameshi ba dole ya Amince ba don yaso ba.

Ahankali Aeesh ta ta dora kanta bisa kafaɗarsa ta rungumeshi tacigaba da rera kukanta, nan take taji kanta nadan sarawa zazza6inda begama sakinta ba na neman sake tasomata.

Shima tapping kafaɗarta  yayi Cikin rauni, yana  Tunanin yanda Zai iya sauke Amanar da Baffa yabashi  da Auren Deejah ,Dole yasan Yanda za ya hana Auren yiwuwar Aurensa da Deejah.

dago fuskarta tayi datayi ja saboda kuka tayi Shima ya ɗago nasa na suka Rine zuwa Ja saboda Tashin Hankali.

Shiru yayi yana kallonta na wasu mintuna sannan ahankali taji yana dago hannunta dake cikin nashi.

Saurin runtse idanu tayi don gudanar Wasu Abubuwan da taji cikin Jikinta.

"Muah!"

Yaba hannun light kiss a lips djnta wanda saida tajishi har cikin ranta.

Hasken Flash Suka gani from No where, Saurin Juyowa Duk sukayi a dan Tsorace.

Saleem Suka gani Riƙe da waya......



Nayi Gabas🧘🏾‍♀️

Share
And
Comment

Bintou ✍🏼

18th june
[7/18, 9:27 PM] chubby number: *_🫀🗡️WUƘA A ZUCIYA🫀🗡️_*
[B l e e d i n g_H e a r t s]



*014*



Saurin runtse idanu tayi don gudanar Wasu Abubuwan da taji cikin Jikinta.

"Muah!"

Yabata light kiss a lips dinta wanda saida tajishi har cikin ranta.

Hasken Flash Suka gani from No where, Saurin Juyowa Duk sukayi a dan Tsorace.

Saleem Suka gani tsaye  Riƙe da waya.

Cikin dabara ta gyara zama tanasa style tana dan matsawa daga gefenshi.

Cikin Muryar mara gaskiya tace

"Ya Saleem Dama kana Na....”

Bata ida Furta Kalmar dake bakinta ba taji Ashman ya Jawota ta faɗa jikinsa ,Kankameta yayi Sosai Yana rawan sanyi Dramatically.

Wani irin Shock taji wanda hakan yasa tasake dagowa ta kalleshi cikin kulawa ta fara Tambayan Sa Ina ke masa ciwo Cikin Ƙankanin lokaci ta Ruɗe a zatonta zazzaɓin ne ya Tashi, kasa bashi Amsa tayi sai ƙara rungumeta yake  ya kasa jikinsa Na kar kar kaman Da Gaske.

Saleem Ya shaƘa iya shaƙa zuciyar sa kamar ta buga,ya buga kwafa a fusace ya fice yana Zayawa a ransa Koma me zai faru saiya Auri Aeesh,Kafin nan kuma Dole ya raba Alaƙar dake tsakanin Aeesh da Aaash.

Yana Fita Aash ya Cikata Yana Sauke Ajiyan Zuciya, Cikin Kulawa Take masa Sannu iyakarsa Gyaɗa mata kai da yayi.

Haka ta cigaba da Jinyarsa yana  Langwaɓewa Kamar da gaske ,Tunda Saleem ya Fita bai sake dawowa ba kai tsaye Gidan su Baffa Imam ya nufa gun su Umma saude Anan ya bayyana mata burin Ransa cewa yana Son Aeesh Kuma dole saiya aureta,Haƙuri ta Ringa bashi akan Yayi haƙuri in sun Isa Gida Xasuyi maganar Gudun Bakin Mutanen Gidan makoki da kyar ya haƙura don ba ƙaramin zafi yaji da yaga Aeesh Rungume a Ƙirjin Aash Ba, ji yayi kaman Ya kma Aash yay ta bugu Har sai raɗaɗin Da yakeji a zuciyarsa y ragu, Amma ya kudurta a ransa Zai Kawo karshen Alaƙar Aeesh da Aash ko ta larfi ko ta Arziki.

Aeesh bata bar gidan Ashman ba ba sai bayan An idar da Sallar Isha'i kafin lokacin kuwa ya wattsake harya biye mata sunyi Wasan tsalle Tsalle.

Tana isa Gida Umma ta tambayeta Daga ina take Kai tsaye ta bata Amsa Da Daga Gidan Yaya Aash Shine ma ya dawo da ita.

Sunanta Umma ta kira a sanyaye hakan yasata dawowa Da baya itama a sanyaye jin yanda ta kira sunan nata Cikin sanyin murya.

"Na'am Umma"

“ya kamata ki Rage Alaƙar Dake Tsakanin Ki da Suff"

     Da kallon mamaki Aeesh ta bita, dan bata san manufarta na furta haka ba.

“Aure Zakiyi ,Haka Suff ba Muharraminki bane ,a matsayinki na ɗiya mace bai dace ki rinƙa Keɓewa Dashi Har Ki kai wannan Lokacin ba,Ba wai ina zargin wani Abu bane Ko thinking Down On you ba ,But inaso ki fahimta Suff ba kowa bane a gareki face Cousin brother, Daga yau na Haramta Miki zuwa Gidansa!”

"Mum...."

Inji Aeesh Lokacin da taji zuciyarta tayi wani irin Bugawa.

"Yes Daga yau kar na sake Ganinku a tare inba wani Mahimmin Abu ne ya haɗaku ba, Abincin da Kukeci a tare da  yanzu na hana ,Idan Yana jin yunwa Yazo muci tare a dining basai kunci a Plate daya ba, Koda Kun Haɗu a asibiti ban Amince ki je Office ɗinsa ba Koda Wasa inba Aiki ya kaiki ba daga Yanzu har a daura Aurenki Da Aareef Kada ki sake Wata alaka makamancin Haka ta sake faruwa a tsakanin ku, yanda kika dau Saleem ya Zama Dole kidau Shima haka Zakiyi masa Dukkansu Saleem da Sufyan Din Matsayinsu ɗaya a wajenki They are All ur Cousins Daga yau baki bashi"

"w.. What?" tafada unbelievably

"yes, Babu shi babu ke, Gabaki Dayanku Aure zakuyi idan Alakarku ta cigaba da kasantuwa ko wannenku na iya samun matsala a Gidan Aurenshi"

Qara jada baya Aeesh tayi tana girgiza kai

"no.. No.. It can't be....No bazan iya ba Umma bazan iya Rabuwa da ya Ash ba, Koda nayi Aure, A gida Ɗaya zamu Zauna na Amince zamu Dinga Hira tare muci abinci tare kamar yanda muka Saba ,Umma Koda na auri Aareef Matsayin Yaya Aash Yana na..."

"Ke dalla Shashasha rufe min baki,Bakida Hankali ne?, me kika dauki Aurene?Aure ya wuce da duk yanda Kike tunani Aure yafi Karfin Shashancin da kike Tunani idan Kin shirya zama da Aareef Dole ki yanke Duk wata Alaƙar dake tsakanin Ki da Suff"

Narai narai Tayi da Idanu kaman Zatayi kuka ta Turo baki

"Nidai umma "

Sai kuma tayi shuru tana Turo baki

"Na baki Zaɓi is Either u choose  between ASHMAN ko AAREEF!, Da zarar kin Auri Aareef dole ki yanke duk wata Alaƙar ki da Ashman ,Idan kuma Kin Zaɓi Ashman Babu batun Auren ki da Aareef,bazan Zuba miki ido kina Abinda Kikaga dama ba Kinji na gaya Miki, Ɓace min Da gani"

"Kiyi haƙuri Ummy,Ummy Pls Kiyi haƙuri please... please"

Ta faɗa tana fashewa da kuka jikinta na rawa sosai.

Jin sautin kukanta yasa Zuciyar Umma karyewa sosai ,Cikeda rauni Umma ta juya ta wuce tana saka abubuwa a ranta .

Da gudu Aeesh ta shige Ɗakinta kaiwa tana Rusa Kuka.

binta da kallo Umma dake bakin Kofa tayi da rinnanun idanunta harta fice.

Aeesh na shiga ta faɗa kan gadonta  , ta reda fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciya tajawo pillon kusada ita ta cusa fuskarta aciki tana cigaba dayi.

Ringing din wayarta ne ya katseta

Ganin mai kiranta yasata sakin tsaki ta cusa ƙasan Pillow, karo na farko na Rayuwarta da Aareef ya kira ta taƙi dagawa, tun Ɗazu yaketa faman kiranta yana Tambayar kudin da tace zata Bashi duk yabi ya ishe ta.

Call din na katsewa wani ya sake shigowa,Tsaki ta sake bugawa a karo na biyu sannan Ta dauko wayar don maidata silent .

Tsayawa tayi tana kallon sunan dake yawo a screen din wayar batareda ta iya dagawa ba yayinda takejin qaruwar bugun zuciyarta.

*_Na baki Zaɓi is Either u choose  between ASHMAN ko AAREEF_*

Kalaman Umma suka dawo mata.

Kasa dagawa tayi har kiran ya tsinke, babu ɓata lokaci wani kiran yasake shigowa again.

Limshe idanu tayi ahankali tayi ta bude tana kiran sunan allah.

Cikin rawar hannu tayi picking din call din ganin zai qara tsinkwa ta kara a kunne .

"Yaya na"

Ta furta cikin Raunanniyar murya.

"Ikhty....,Me ya faru?,You Sound some how"

''Na Gaji ne"

Ta furta Hakan cikin Kwantar da Murya.

"Ayyah Sorry Nine na Gajiyar dake ko"

Turo baki tayi kaman Yana gaban ta Tace

"Eh"

"Ko inzo In miki tausa ne?"

"A'a Kaida bakada Lafiya?”

"Ai na warke, Umurnin ki kadai nake jira Yanzun Nan zaki ganni"

Dariya Tayi sosai,Ta sake kankame Pillow ɗinta

"Haba dai yaya abar cika baki Kar ince kazo Naji,diff"

Murmushi Mai Sauti yayi ,ita kuma ta cigaba da cewa

"Yawwa yaya na Ɗazu fa ya Saleem Ya ɗaukemu hoto cikin Mummunan Yanayi,ina matuƙar tsoron abinda zai je ya dawo bana son Abinda Zai taɓa mutunci na"

Jim kadan yayi yana hararo halayyar Saleem da kuma Abinda Zai iya aikatawa,Tabbas kadan daga Cikin aikinsa Ne ya gyara hoton ya baza a duniya kowa ya gansu Wannan Ba komai bane a wajensa,Da ƙarfi ya cije Lips dinsa Sannan ya furzar da Iska Daga bakin nashi  _yanzu da ansan matarsa ce me zaisa ya damu don Wani ya dau hotonsu a wannan yanayin?_

"No Share Saleem Babu Abinda Zaiyi dashi i know him"

Y Fadi hakan don ya kwantar mata da hankali.

Sosai Suka sha Hirar su Cikin Wannan daren

Kallon Agogon Wayarta tayi 2:26am a lokacin

"Yaya After 2😲, Bari in je in kwanta kar Mum ta shigo''

Ta fada tana Kokarin katse wayar

"Dakata, Ikhty "

Dakatawa tayi shi kuma ya cigaba da cewa

"At this moment Ba barci ya kamata kiyi ba, Kamata yayi Mu tashi Muyi Alwala muyi Sallah,ba ƙaramin asara bane ki kai Wannan Lokacin idon ki Biyu baki raya daren ba"

"Tho Yaya Ai na zata sai Kanada matsala kake sallar dare?"

"No Ihty Ai ko kinada matsala ko bakidashi Ya kamata ki zama mai godiya ga Allah Ubangijin mu, Annabi Muhammad (S.A.W) Wata rana yana sallar dare Sai Matarsa Nana A'isha taga har Ƙafafuwansa Suna Kumbura Saboda tsananin Tsayuwa Sai tace dashi, Me yasa bazaka dinga hutawa bane Bayan Allah ya yarda dakai Sai yace mata, yanzu bai kamata in kasance mai Godiya ga Allah ba? Da baiwar da yayi Min?,Kinga Ihty Annabin Allah ma kenan Ballantana Mu Taron Kwai ba Kaza?, Allah yayi mana Abubuwa da dama Ya kamata Mu kasance Masu godiya A gareshi, idan Muka gode masa Zai Kara mana Akan wanda ya bamu ,Sahabin Annabi (S.A.W) Abdullahi bn Abbas ya kasance a bayan annabi wata rana yace dashi " _Ya kai yaro ,ka kiyaye, Ubangiji Ya kiyayeka,Idan zakayi Roko ka roki Ubangiji Idan Zaka nemi Taimako Ka nemi Na Ubangiji , kasani cewa da ace da Ace Dukkanin Al'umman Duniyan nan zasu hadu domin su Cutar dakai bazasu iya ba,Saidai Abinda Allah ya hukunta zai Sameka,Haka zalika da zasu hadu don su Amfanar dakai da abinda Allah bai hukunta zaka samu ba ,bazasu iya Amfanar dakai da komai ba sai Abinda Allah ya hukunta akanka,An riga An dauke alkalamin kaddarar mu, takardun Sun bushe ,Dani dake da kowa ma duk mabukata ne Gun mahalicci Mu tashi Mu miƙa lamurran Mu ga mahalicci ki tashi muyi Sallah Ihty"

Da sauri Aeesh ta miƙe tana cewa

"Allah Sarki Patient Doctor ɗina Kayi Gaskiya bari In tashi In dauro Alwalar"

Daga nan Ta ajiye Wayar ta dauro Alwala ta gudanar Da Salloli Daga bisani Ta ɗora da Shafa'i da witiri.

Anan Inda Tayi sallar Bacci ya d'auketa bata farka ba saida taji Umma na Tashinta Akan ta tashi Tayi sallar Asuba.

Sallar tayi ta koma bacci Nan ma saida Umma ta sake Tashinta Akan tayi wanka, Tana Gama wanka ta Shirya Ko Breakfast Batayi ba Ta Fice zuwa Asibiti kafin nan saida Umma ta daɗa jaddada Mata Kashedin ta na daren jiya,Turo baki Gaba kawai tayi Tayi gaba Abinta tana Kunkuni Ita dai bazata iya Rayuwa batareda Dayansu ba ,Umma fa saidai Kiyi Haƙuri.

               *N3p Specialist Hospital*
shigowar motocin Su Ashman ne ya saka Securities da Masu Aiki a  harabar Asibitin maida hankalinsu a kansu, ballema Sunga yau Shigowar nasu da Mugun Gudu suna tada Kura sun san an taɓo Masu Abin .

Cikin Azama Drivern Ashman Ya Zagayo ya Buɗe masa,Saida Yaja Almost 1min kafin Ya zuro ƙafarsa Ya fito,As usual Karema Asibiti Kallo yayi Ko ina fess ma'aikatan Sun GyaraKo ina.

Farar  eye glasess ɗinsa ya ɗora saman ido yana Taɓe baki, Fuskar Nan a murtuƙe alamar dai babu sassauci kenan,a hankali Ya fara Takawa izuwa cikin asibitin yana tafe Drivern sana take masa baya cikin bajinta mai nuna alamun fushi tattare dashi.

Shima Saleem Yana Ganin Fitowar Aash Ya Kashe tasa Motar sannnan Ya bugo ƙofar Motar Da karfi,shima kallo ɗaya zakayi masa Ka fahimci Babu sauƙi fuskar nan kou a murtuƙe take tamau.

Cikin Tafiyar tasu Nan ta isa Kamar koda Yaushe Suka Shiga Ciki ma'aikata sai Gaidasu,Ammma Kamar Da Iska suke ko Kallo basu Ishesu ba.

Suna Shiga Drivern Aash Ya dakata a bakin Ƙofa Tareda Miƙa Masa briefcase ɗinsa, karɓa yayi ya Shige Ciki yana dan Dingisawa Don Har yanzu Yanajin Raɗadin ciwon Kafarsa.

Saleem kou Tuni ya raɓa gefensa yawuce side ɗin su ,Kai tsaye Office dinsa Ya nufa ya Ajiye Jakarsa ,Wata Attendant ce ta Shigo Ta miƙa masa wata yar jaka karɓa yayi da yatsu biyu bayan Ya saka Surgical Handgloves yana ɗan yatsine fuska kamar Wanda aka miƙa wa kashi, Ko kadan Attendant din bataji Dadi ba, inda sabo ya kamata ace ta saba Da Salon Wulaƙancin Saleem Amma tamayi sa'a yau bai Zageta ba ,Kullum Sai ya Zageta Ya aibanta ta da guntuwa mummunar Banza.

Jakar ya buɗe bayan Fitarta ya fiddo sabon blue scrub dinsa da tasha Guga sai faman Tashin Ƙamshi Yake, Da sabon Labcoat shima a Goge sai Daukar Ido Suke.

Nan ya cire Suits Din jikinsa Ya ninke ya saka su cikin Jakar Ledar da aka kawo masa Kaya dashi ,Sannan Ya Saka Scrub Din ya Dora labcoat dinsa akai,

Yana cikin saka Medicated Glass din sa Sis Maryam Ta Shigo hankalinta a tashe dama tun Ɗazu Tazo Suna Conducting wani Complicated Delivery ne, tun Daren Jiya matar ke naƙuda Amma ta kasa Haihuwa Yanzu haka Ma shigowa Tayi ta Gayama Saleem Tunda Shine Gynea doctor oncall Yau ,Ya duba mai  labourn inya gagara sai suyi Booking dinta for CS.

Cikin Muryarta Mai Nuna alamun gajiyawa haɗe da tashin hankali take gaya masa condition din matar,Ko kallonta Baiyi ba bare tasa Ran zai tanka mata.

Sake Maimaita masa tayi ,Amma maimakon ya Amsata sai Cewa yayi

"Get my Breakfast Ready"

Hadiye wani Abu daya toshemata maqoshi tayi kafin tace

"Ba Aikinka nazo yiba Tsare Rayukan Jama'a da Nema msu lafiya nazoyi"

Hankalinsa na kan wayarsa yace

"Really?"

Tace

"da ba don haka ba U won't see me here, if not ko sanin da wanzuwarka bazan yiba bare ko kallo ka isheni ,Ko tausayi baka dashi?, I told you Mace na in Critical pain of complicated labour buh Instead Zancen Break fast kakeyi" tafada idanunta na qara durar ruwa.

Ya ɗan ɗago ya dubeta a lalace

"And So..?,You Work Under me, kiyi biyyaya gareni, Find me some thing to eat " Ya ida zancen cikin rad'a

Kasa riqe hawayen tayi, saurin kauda kai gefe tayi don karyagansu, Sosai take jin Zafi sa Tausayin Matar na sake tasiri a ranta Tunda Ta fara aiki as a Midwife Bata taɓa Yin arba da Complicated labour irin Wannan Ba Gashi babu Asibitin dake nan Kusa bale suyi mata refer, jitake kamar wankeshi da mari don takaici.

Murmushin gefen baki yayi na mugunta ganin tana hawaye, Dama ya dauki alwashin saita raina kanta tunda ta sake Tsautsayi yasa Ta zama mace ta farko da Tayi masa Rashin Kunya a asibitin dan uwansa .

"Kinada minti Goma kacal Get my break , please Out of my office karkisa numfashina sarqewa you Stinks "

Ya ƙarashe maganar Da Toshe hanci da farar hanky dinsa Still bai ɗago ya dubeta Ba tun Shigowar ta .

Juyawa tayi tana Goge hawayenta ta Fita izuwa Staff canteen ta Karɓo masa Coffee da Sandwich harda Fried egg Monday Breakfast dinsa kenan Kamar yanda ya tsara Mata a time table.

A table dinsa Ta dire Tana Dubansa ,sake balancing yayi akn Kujerar sa yana Mata kallon ƙasan ido

"Stand untill I finish"

Lumshe idanu tayi tana sauraron Sautin Bugun zuciyarta.

Shiru tayi atsaye still idanunta lumshe, in banda deal Dinta da yayanta bataga Dalilin Da zaisa tazo tana Bin yaron Nan sahu da Ƙafa ba,Infact ko kallo bai isheta ba.

Tana Nan Tsaye Har ya Ida Cin Abincin Sai a lokacin ya ɗago ya dubeta a kaikaice ,Kanta A kansa Idanunta

Please Login or Register in order to submit comment