Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abokan gaba zaki tarwatsa miyagun namun daji, ku kuka gajeshi Masu fasa taron yan Adawa"

Dakatar dasu ZEEYK yayi ta hanyar ɗaga musu hannu , Maryam kam Murmushi take ta faman Yi, She missed Them All.

Part ɗin Anty Mamy Suka nufa kai tsaye suna shiga Anty mamy tamike rungume Maryam, Wanda hakan yasa ta fama ma ta Ciwon kafaɗar Hannunta, ta ɗan Tureta tana Sakin ƙara a shagwaɓe tace

""Wayyo Matar dad Zata kashe Ni"

Dariya Mamy tayi ta ɗan bugi dayan hannun tace

"Raguwa Kawai, yanzu dan wannan ciwon Kike ma uban Ihu haka?"

Marairaicewa tayi tace

"Lallai ma Matar Daddy, Harbin Bindiga ne fa, ke na tabbata Ko karar Harbin Kikaji Bazaki tsayaba Tuni Zan Hango ki a ambulance ”

Dariya duk Suka saki suka shiga Ciki, sai nan nan da ita akeyi ,haka ma'aikata kaman zasu duƙa suyi mata Sujjada.

Sai a lokacin Maryam Taji dama bata dawo ba wannan irin abu haka ai dole asamu ɗinbin makiya da munafukai musmman akan ZEEYK, ta tabbata da sa hannun Ma'aikatan aka lalata Rayuwan Yayanta dukda batasan yadda aka dasa masa Cuta ba amma Kasantuwar ada shiɗin ɗane mafi soyuwa acikin wannan Gida ,irin Sonda Abba ke nuna masa a da kafin ya samu matsayin da ya samu yanzu Dole ya tara maƙiya, Amma tunda yayi Kuɗi, ya kuma samu matsayi a siyasa kakanshi ya hau Mulki, sai Soyayyar da yake ma ZEEYK ya koma kan Maryam , zan Ma iya cewa Sonda yake mata a Yanzu ya zarce wanda yakeyi ma ZEEYK din a baya.

Kamar yanda Abokan AREEF suka bashi shawarar ya sake koma mata, Hakan ce ta kasance Baisha wahala ba wajen Shawo kanta ba, Saboda tsananin Soyayyar da take Masa.

Cikin kankanin Lokaci soyayya ta Dawo sabuwa Tun daga lokacin suka daidaita.

Shakuwa ce sosai ta sake shiga tsakanin Aeesh da AREEF, Tun Suna Soyayyar a ɓoye , har ta fito fili Kowa ya sansu tare.

DA ANGA AEESH ZA'AGA AREEF

Kullum suna tare ,Shike rakata lecturers in sun dawo kuma su dasa Daga inda suka tsaya.

Bakin Gate din Hostel ya zama permanent gurin zaman su akoda yaushe

Tun ana mata surutu tana damuwa har ta saba, Zan iya cewa a halin yanzu kusan kusan komai na AREEF ta sani,Abinda ke zuciyarshi dangane da ita ne kawai Allah ya ɓoye mata

Shima haka Yasan komai na Rayuwarta duk wani abu da tayi idan basu tare in suka hadu sai ta bashi labari,Duk abinda ke faruwa Reey na sane tayi Fadar har ta gaji, Yanzu ido ta zuba musu taga iya gudun Ruwansu, haka ko kallo bai isheta ba balle ya samu fuskar tunkarar ta da yaudararriyar saƙon zuciyarsa.

Yau Dawowan Su kenan daga Lectures, ya rakota har bakin Hostel ,anan Suka ƙaraci hirarsu, saida Suka Kusa Hour Daya sannan yace Zaije akwai match dinda zasu buga ,tayi masa fatan Alheri ya wuce ita kuma ta shige ciki.

Zaune ta iske Reey tana Rubutu ko Kallonta batayi ba, inda sabo yaci ace ta fara sabawa da halin Ko in Kula da Reey take mata a dan Kwanakin nan ,ta lura duk akan Aareef ne, ita kuma akan AREEF bataƙi ta ɓata da koma waye ba.

Kayan Jikinta ta Cire tasa doguwar riga, sannan ta buɗe tukunya a Tunaninta Reey tayi girki kaman yanda ta saba, sai taga wayam Babu komai a ciki, da mamaki tace

"Reey yau baki mana Girki bane?''

Saida ta Fada taji nauyin Maganar, banza Reey tayi Mata ta cigaba da Rubutun ta kaman bata sanda zamanta ba.

Zama Aeesh tayi a kan Gado ta Zabga tagumi tana Kallonta Jikinta duk yayi sanyi, Yanzu fa Duk shariyan nan akan ta kula AREEF ne!, Meye laifinta dan taso wanda yake Sonta?, Ina Amfanin Rayuwarda babu soyayya a cikinta?.

Take taji wasu Hawaye masu ɗumi sun sauko Saman Kuncinta,taja Shessheƙa sannan Tasa bayan Hannu ta share, Reey na jinta tayi banza da ita.

Saida tasha Kukanta ta ƙoshi sannan ta miƙe ta yafa Mayafi ya fita bakin Gate din Hostel ta Siyo Fresh Yo da Pure Bliss, Aeesh kenan Bata iya jure yunwa duk halin da take ciki bata yarda ta azabtar da cikinta ba, Sai ta fara Bama Cikinta sannan Take samun Nutsuwa, Gata da ƙyashi bata Son Yin Girki, a Gabaki ɗaya rayuwarta zata iya Ƙirga So nawa ta taɓa kunna Gas.

Saida Taji ta ƙoshi sannan Ta ajiye raguwar Fresh Yo din ta kora da ruwa, sannan ta kwanta rigingine tana Kallon Celling, Sai a lokacin Reey ta gama Rubutun, ta taso ta ajiye Littafan akan gadon, fuska babu alamar wasa tace

"Tashi min akan Gado"

Kallon Mamaki Aeesh tayi mata tace

"Besty yau Ni kike kora akan Gadonki?"

“ba wannan na tambayeki ba, tashi min , I want to Rest’’

Jikin Aeesh yayi sanyi sosai, Tashi tayi cikin sanyi zata Haye up bunk ɗinta.

Sai Reey Taji babu Daɗi , Taji bata kyauta mata ba, Tausayinta ya kamata, ta kira sunanta cikin Sanyin Murya

"A'isha"

Fasa hawa saman Bunk din Tayi ta Amsa mata da na'am, itama a sanyaye

"Ga Abinci a flask”

"Na Ƙoshi!, Anjima zanci"

Murmushi Reey tayi , da gaske Aeesh bata da Zuciya akwai ƙarfin Jurar wulaƙanci ,Dole AREEF ya Mari banza kuma ya dawo a karɓeshi.

"Besty zauna Zamuyi magana"
Reey ta fada cikin tausasawa.

Zama Aeesh tayi ta dubeta a sanyaye.

Reey ta gyara zama tace

"Kin dauka tarayyar ki da AREEF ne bana so ko?"

Aeesh Gyada mata kai .

ta cigaba da cewa

"Ba alaƙarku ce bana so ba, Yanda yake cin Mutuncin ki ne Banaso”

Wani yawu ta Haɗiye, murya chan Kasan maƙoshi tace

“Reey Ki daina fadin haka, AREEF bai taɓa cin Mutuncina ba"

Girgiza kai Reey tayi cikin Tausayawa Lallai Aeesh abar tausayi ce bata iya son Abu ba, inta so Abu tana Saurin zautuwa akan abin, kamo Hannunta tayi cikin tausasawa tace

"Inaso kiyi takatsantsan da soyayya ,Saboda karta kaiki Gurin da bai kamata ba, ki janyowa kanki Abin kunya keda Family ,dama ya Lafiyan Kura?"

Sunkuyar dakai Aeesh tayi kalaman Reey sunyi matuƙar Ratsa Zuciyarta tace

"Inshallah Bazan Bari so takaini Inda zan halaka ba, zan kula dakaina"

"Bazaki iya gane zaki iya kula da kanki ba, sai kin yarda akwai mafita ,kada ki yarda da cewa don akwai kaza kaza bazai faru ba, akwai wasu yan hanyoyi, akwai wasu yan dabaru!, Ina fatan dai kin gane inda maganata ta dosa?"

Aeesh ta gyada kai Still Fuskarta na Kallon ƙasa tace

"Na gane"

Reey ta cigaba da cewa

"Babbar dabarar ki itace, ki gane duk wani dabarar da namiji Zaizo miki da ita, karki yarda Sonshi yasa yasamu tasirin da Ashman ya samu Akanki Kija ma kanki Abin magana, in Yana Sonki ya jira akai mishi ke"

A Mamakince Aeesh ta ɗago ta dubeta Ranta yaso ya sosu da Kalaman ta, amma sai taba kanta Haƙuri tunda tasan gaskiya ta faɗa, Taɓe baki Reey tayi tace

"Ina gaya miki wannan ne saboda naga kamar Zakiyi saurin zautuwa a cikin so"

Aeesh ta kauda Kai tace

"Ko na zautu Bazan halaka ba inshaAllahu"

"Naga Kaman bakiji daɗin Abinda na gaya Miki ba ko"

"Eh Gaskiya Naji wani iri, amma sai Gani nayi kaman Kin Karfafa dayawa, Areef bazai iya Aikata Komai a gareni ba, bayada wannan interest din akaina ma"

"Haka kikace ko?"

"Haka dai Gaskiyar take, Areef Ko kallon Ƙurilla bai taɓa haɗani dashi ba, am sure Koda Yanzu za'a Ce yayi describing how exactly I look Bazai iya ba, Don Allah taya zanyi tunanin innocent Guy like him zai Iya Aikata Min ba daidai Ba, haba Besty don Yaya Ashman Ya kauce hanya sai aka ce miki maza iri daya ne?, Akwai bambanci tsakanin SO Da SHAƘUWA, Shaƙuwa ce tasa nake jin Wani Abu akan Ahky har ta kusa samu aikata ba daidai ba, Amma so daban Yake, son gaskiya baya kai Mutum ga Halaka "

Kallo Reey ta bita dashi tana jinjina sakarci irin Na AEESH, Lallai Maganar Masu soyayya Gaskiya ne da suka ce So Takalmin Sakarai.

jikinta taji duk yayi sanyi, kirjinta yayi nauyi, tasan son gaskiya Aeesh keyi ma AREEF amma anya kuwa yana Sonta kwatankwacin yanda Take Sonshi kuwa? Murya a sanyaye tace

"Aeesh bakya tunanin Kina zaƙewa dayawa a cikin soyayyar ki da AREEF?"

Murmushi Aeesh tayi Ta ɗan ware Idanunta tace

"Abinda Kika lura dashi kenan?"

Reey tace
"Gaskiya"

Aeesh tace

"Idan Ma na Zaƙe a rabu dani, sabuwa ce Ni fa a soyayya!"

Reey ta lumshe idonta tanajin tausayinta a ranta, cikin karfin Hali tace

"Idan Harbin Soyayya ya tashi zuwa, baya ware sabo ko tsoho, kada Ki sakankance dayawa kada ki manta da ke kadaice mai rauni a wurin mahaifiyarki, haka ke ɗaya ce gareni nima, Bazan Iya jure Rashin Ki ba"

Ta ƙarashe Maganar da ware Idanunta akanta

Murmushi Aeesh ta saki Tana dan Gyaɗa kai, fuskar ta Normal Tace

"Na sani Shiyasa nake son Ture Duk wani abu da yake cikin Ransa, Ni kuma nawa ya zauna ta hakan ne kadai xan samu kwanciyar hankalin da kuma zaku cigaba da ganina a raye ina walwala''

Dariyar yaƙe Reey tayi ganin yanda take maganar Hankalinta kwance tace

"Ke wato duk inda aka bi dake sai kinsan yanda Kikayi kika zille ko?, Tho Idan Kun sake haɗuwa dashi ki ce Ina nan Kullum ina wasa Masa Wuƙar da zan Soke zuciyarsa dashi idan Ya sake ya raunana Mana Zuciyarki, kuma ba da wasa nake ba, I'll kill him if he break your heart"

"Me zai hana Ki dau waya Ki kirashi ki gaya masa ?, Naga Alama kaman Zaifi ji idan yaji daga bakin ki”

Harara Reey ta dalla mata

“Allah ya tsareni da harkar ƙaranta, wannan Yaron Ai saike ,Ni Ko kallon Arziki ma bata taɓa haɗani dashi Ba”

Haka suka cigaba da tattaunawa cikin dabara Reey ke bata bayani akan ta rage Zaƙewar da Takeyi akan Soyayyar AREEF don Zuciyar ta nada Rauni Bazata iya Jurar Wahala ba.

Da yamma Ashman ya kawo mata ziyarar bazata, Saida Yazo Daidai Department ɗinsu sannan Ya kirata yace yazo, a lokacin kuma zuwan AREEF kenan suna Bakin Hostel suna Shirin fita yawo ,tare suka ƙarasa Department wajen Ashman.

Ashman na ganinsu yaji wani Ƙulutun Baƙin ciki ya dokeshi a Zuciya lallai ma Wannan Gayen wato dawowa yayi dan ya birkita masa lissafi!, Itama Da yike bata da wayo da Auren shi akanta take kula wani?

_Tho fa🤔,Kaji Min Mutum Neman magana, idan baka son Ganinta da wani Ka sanar da Ita mana_

Da Murmushin ta Ta ƙaraso wajen shi, Ya wani haɗe rai yasha murr kaman bai taɓa dariya ba.

Hannu AREEF ya bashi su gaisa, saida Ya watsa masa kallon Banza sannan Ya Bashi hannun fuska a Yamutse, yasa hannu a Aljihu ya fiddo yan rafan dari bibbiyu Guda biyu ya miƙa masa

"Gashi ka hau Adadaita"

Kallon mamaki AREEF yabi kudin dashi,ya kuma kallon Ashman Cikeda mamaki yace

"Ban fahimce ka ba”

Tsaki Ashman yaja ransa a ɓace

"My hand is hanging On Air, zaka karɓa ne ko in Maida Abina?"

Ganin da Gaske yake idan bai karɓa ba zai maida abinsa, ba kuma a yanda ya ga ranshi a ɓace idan ya masa Gardama Zai iya jin mazga.

Jiki na rawa ya karɓa kudin yana zuba Masa Godiya, ya yi mata sallama ya tafi, Kallon Mamaki tabishi dashi Tasan AREEF nason kudi, Amma halin da ya nuna a yau Dinnan ya bata Mamaki, ita a Tunaninta zai ba Ashman Haƙuri ne ya ƙyaleshi suyi Hira Tare su Uku ta yanda zasu Ƙara fahimtar juna Sosai, Amma sai ya nuna Yafi buƙatar Kudin akan abinda ya kawoshi.

Tayi Nisa cikin Tunani, sunanta da Taji Ashman ya kira ya sata dawo Hayyacinta, ta amsa da Na'am ta ɗago fuskarta ta Dubeshi idanunsa Sun kaɗa sunyi jazir har kana iya hango tiny veins din dake Cikin Outer layer na Idon.

Yace

"Ihty Kinsan Abinda nafi tsoro?"

"A'ah Ahky"

Ta faɗa a Sanyaye

"Ba Mutuwa bace,Ba Talauci ba,Ba ƙuncin rayuwa ba, Ba harin magauta ba, Ba yaƙi da Mafarauta ba, ba Shiga Fadar da tafi ƙarfina ba, Wani Yaƙi ne dake tattare dake...!"

Ya dan Dakata yana kallon fuskarta, ya sauke zazzafar Huci sannan ya cigaba

"saboda kinada Matuƙar muhimmanci a tare dani"

Sai ya sake Dakatawa yana Ƙoƙarin Saita Muryarsa

"In fada Miki Gaskiya?, bansan ya Rayuwata zata Kasance batare dake Ba"

Dagowa tayi a kasalance ta kalleshi batareda ta iyacewa komaiba ya cigaba da cewa

"Gagarumin Tsoron da Nakeji akanki Shine na wayi gari inga Wani ya Kwace min ke, ban san yanda Rayuwata zata kasance batare dake Ba, Ke amana ce a gareni ,Tho ko Zaki taya ni sauke wannan Nauyin ,Ki min Alƙawarin Bazaki sake kula wani namiji Ba bayan Ni?"

Bude kofofin idanunta Aeesh tayi Ta kalleshi bugun Zuciyarta na Sauyawa Abnormally, Sam Bata Fahimci inda Kalamansa Suka dosa Ba, ta dai ji Jikinta yayi Sanyi, Cikin sanyin jiki tace

" babu mai rabaka dani yayana, am Alll yours, forever and ever"

Sai yanzu yaji Sanyi a ransa, ya saki Murmushi gamida Huramata iska a idanu tayi saurin lumshe su tana murmushi

"How I wish Ki duba Wedding Gift dinda na Baki a ranar Aurenku da Saleem, it'll tell the Un told story"

Yafada yana sa dan yatsarshi a ramin kumatunta daya loɓa sanaddiyar murmushin datayi

"Na duba ai, there Nothing Special in it, it's just 100k, A brand new car and Nothing more "

tafada tana qara fadada murmushin ta.

"What of the Siled Letter?"

Ta Dan waro Idanu Waje

"Ohhh I know it contains Best wishes so I don't bother my self, Auren da Tun a ranar Farko ya Kwance me zanyi da wani Letter?"

"Hmmm...."

Kawai ya iya cewa, ji yayi kaman ta watsa masa Garwashin wuta a Zuciya, ashe ɓata lokacin sa yayi wajen Aika mata saƙo ta written method, Ashe Rubutun da ya zauna ya tsara duk a banza

"Yawwa yaya yaushe zaka Fara koya Min Mota?, Nima na Ƙosa in Fara tuƙa mota ta"

Murmushin yaƙe yayi, ya Kauda Maganarta da cewa

"Ihkty a jikin Dubu ɗarin da na baki akwai wata yar Rubutu da akayi a takarda Kin duba me aka rubuta a jiki?"

Ta danyi shiru kaman Mai tunani sannan ta Jingina da Motarsa, tana yamutsa fuska.

Ta kuma ɗagowa ta dubeshi, shima Ita yake kallo calmly, so peaceful, fuskarsa sam babu alamar damuwa, Yayi Matuƙar ƙoƙari wajen ɓoye tashin hankalin da yake ciki a daidai wannan Lokacin.

muryarta a nutse take magana tace

"Your Dowry wato Sadaki ki, abinda na gani a rubuce kenan, Dama Tun a Ranar nake son in Tambayi dalilin da zaisa Yaya ya ba ƙanwarsa sadaki bayan Wanda Mijinta ya bata?”

Wannan Karon ji yayi kaman zuciyarsa zata harba tayi bindiga,ya hadiye wani abu da ya tsaya masa a makogwaro yace

"I was Fool, Ni kadai nake haukana, ihty Dole ki min kallon fasiƙi”

Ta juyo tana kallon cikin idonshi tace

"Ahky nifa yau Gabaki ɗaya yanayin ka Tsorata Ni Yakeyi,kasa Jikina ya fara Rawa, Ga Zuciyata sai wani salon Bugawa Takeyi na daban don Allah ka bar min Irin Wannan kalaman ,suna sani jin wani iri sosai"

Tayi maganar kaman Zatayi kuka , Murmushi yayimata cikin Ƙarfin Hali ya buɗe mata Mota

"Tho Shiga muje yawo, na kaiki kisha Ice cream , Ya sanyayar miki da zuciya"

ta Shiga ,yaja su Suka bar makarantar suka zagaye Gari, kai tsaye Choco store ya kaita, ta Gibgo kayan maƙulashe, daga nan suka Wuce Eatery suka ci abinci dama Yunwa Takeji, da ka gansu kaga masoyan da suka Shauƙantu da soyayyar Juna without knowing that both of them were Dying in darkness.

A Ranar ya Fara Koya mata tuƙi, Saida suka kusa zagaye wuraren Shaƙatawan dake cikin garin Kaduna sannan Suka Dawo Da manya manyan Ledoji jibge da kayan Maƙulashe a lokacin har an fara Kiraye kirayen Sallar Isha'i.

Kafin su tafi tayi ma Reey text message Shiyasa bata damu ba ,nan fa suka tasa Tsaraba suka Fiffigeta 😁😁, suka ba Su Sarah da Jesmine Rabonsu.

*SALEEM*

Tun bayan Barin Maryam asibin su ya shiga wani hali She's no where to be found, Yaje har gidan Su Saleemah Amma sai mama tace Ita kanta bata san Sunan Unguwar da suke ba a Lagos, amma idan zai Kaita Zata gane hanya don Ta taɓa zuwa so Biyu.

Haushi ta bashi a Ganinshi ta raina masa hankali, Saida ya ci mutuncinta ko ince suka ci mutuncin juna sannan Ya bar Gidan,daga Ranar bai sake Komawa gidan ba, kuma daga ranar ya dawo da Ɗabi'ar da ya Fara Watsawa wato Wulaƙanta dan adam.

Wannan Karon Wulaƙancinsa Kara karfi yayi Abinka da mai Ciwo a zuciya, duk Girman Mutum baya raga Masa ,Mistake kadan za'a mai ya hau mutum da faɗa , har ya kai bai Ƙyale Inna Saude da Abba Ba,ko wannensu ya shigo hanyarshi takashi yake babu ruwan shi , Abba baya kasa tsawatar masa Gudun Ɓacin ransa, Inna Saude ma Haka Dama Tafiso rayuwarsa ta tafi a hakan, hakan ne kadai zai sadata da Cikar mafarkinta akan Jinin Amma.

A halin yanzu shayeShayen da yakeyi a ɓoye ya fito dashi Fili, baya Shakkar a ganshi yana maye, ya Maidashi Tamkar Abincinshi Sunan Maryam kuwa ya zame masa tamkar Salati a fatar Bakinshi akoda yaushe yana ambaton sunanta, koda yana bacci ne idan Kanason ka tashe shi ka ambaci sunan Maryam, zakuga ya tashi da sauri yana nemanta.

Yauma Saida dare ya tsala duk sunyi barci, Ya gama Kwalbewansa kaman yanda ya saba, ya Fito yana Layi, Masu gadi na Ganinshi suka buɗe masa ƙofa ya fita,ɗaya daga cikin Security ya bishi a Baya.

A daidai SHURASH EATERY Inda Maryam ke yawan Kawo Delivery ɗin gasassun kaji, nan Yaje, ya zauna aka kawo masa Abinci, Amma ya kasa ci, Kwalbar Giyan dake hannunsa Kawai yake ta faman Kwankwaɗa.

As usual Kaman Ba dare ba, Mutane sai Shawagi suke suna kaiwa da dawowa Mafi yawancinsu mashaya ne da masu Fita taɗin dare da kuma matafiya da suka tsaya don Kore Yunwa Jakar bayansa Ya Sauke ya Fiddo Kwalabe ya diresu a gabansa.....

Wulla idanuwa yakeyi Yana kai Kwalba baki yana saukewa, bibbiyu Yake Gani Ammà hakan bai hana Shi sauke Kwalbar ba, bai dire ba Saida Ya Shaye shi tassss.

Pizzar da aka Kawo masa ya yanka cikin ya kai baki bayan yayi fara da bismillah yafara tauna ahankali
















NAYI GABAS 🚶🏻‍♀️

TUE
30TH AUG

BINTOU ✍🏼
[10/3, 9:56 PM] Solace: *_WUƘA A ZUCIYA_*
_bleeding Hearts_

*035-036*




_*Inshallah daga wannan Page zan Dage pen sai October Inshallah*_

_Saboda Exams da Muke shirin Farawa on Nan bada Jimawa ba inshaAllah🙌🏽_

_I know i have written and keep enough.... thanks for understanding_😉

_please a Taya mu da addua_🙌🏽




Saukan Ruwan sanyin da yayi a fuskarshi Yasashi Farkawa a Gigice yana Ambaton Sunan Allah

"Kai Tashi Kayi sallah Asuba yayi"

Dishi Dishi yake ganinta har ganinsa ya ware Tangaran Akanta, tana Tsaye Hannunta Riƙe da Gorar Ruwan sanyin da ta watsa masa, ji yayi kansa Yayi masa nauyi sosai, ya kasa Tuna Komai.

Ta dire Masa Gorar a Gabanshi.

"Gashi kayi Alwala kayi Sallah"

Daga Nan Bata sake Cewa Komai ba ta fice tajawo mishi ƙofa, Sai a lokacin ya samu damar ƙare ma wajen kallo, ba daki bane Haka ba a cikin Gida bane,wurin yafi Kamada tsohon Toilet na wajen Gida, Kuma da Alama Kaji Sun zauna a nan duba da Fararen fiffiken su tako ina.

Bin wurin Yayi da Kallo sosai Yana sake nazari,Dakin sai warin Kashin Kaji yake da Alama Kaji Sun taɓa zaman wajen, Dukda Ko ina a tsaftace yake Amma Hakan bai hana warin busowa ba, Sake Bin dakin yayi da Kallo yana Mamakin Ganin Tsoffin Abubuwan da Aka tara wajen gina Bayin.

Tabbas nan Toilet ne,kenan a Toilet ya Kwana?, No never hakan Bazata Taɓa faruwa ba!,He must be dreaming, To nan din ina ne?, Me Maryam Keyi a nan? Kodai Ita ta kawoshi?.

Duk Bashida amsoshin Tambayan sa ,Jikinsa na Rawa ya dau Gorar Ruwan Yayi Alwala ya fito yana Dan kalle kalle Ko Zai samu tsabtataccen wajen da zai dan Raɓe yayi Sallah.

Daga Chan Gefe yaga Dadduma a shimfiɗe Anan Yayi Sallah,bayan ya idar Yana Tsaka da lazimi Zain ya ƙaraso wajenshi, Ya zauna Gefenshi yana Dubanshi, Jikin Saleem Banda rawan Sanyi babu Abinda Yakeyi ,Ko kadan saleem baya ƙaunar ruwan sanyi ko yaya ruwan sanyi ya taɓeshi saiya kwanta cikin Rawar murya yace.

"Please Dude me yasa Kuka kawoni nan?"

Batareda ya bashi Amsar Tambayarsa ba zayn ya dafashi cikin Sakin Fuska yace

"Saleem Kace kana Son Maryam Right?"

Saleem ya Gyada kansa yace

"Eh Ina Sonta, Amma ban Gayawa Kowa ba"

Zayn ya dafa kafaɗar shi yace

"Zan Aura maka ita"

Saleem ya ɗago fuska cikeda Murna yace

"Da gaske?"

"Eh Amma da Sharaɗi"

Da sauri yace

"Menene sharaɗin nayi Alƙawarin Binshi Duk rantsi"

Tsayawa Zayn Yayi Yana Kallonshi,Farin Cikin da ya gani a fuskarshi Mara Misaltuwa, a yanda Maryam ta bashi Labarin shi, baiyi zaton Zai Tsinci Kansa Cikin Wannan Yanayin Kuma aga FarinCiki a fuskarshi ba, Kallonshi take Yana Ayyana Soyayyar dake zane Cikin kwayar idanunsa.

"Please Babban yaya Menene sharaɗin, i Promised Bazan Baka kunya ba"

Ya faɗa Muryarsa a Raunane.

ZEEYK Yayi gyaran murya sannnan Yace

"Auren Wata Uku zakuyi Nan Da Sati biyu idan Kana Sonta dole ka amince"

Ahankali fara'ar fuskarshi yafara gushewa ,ya Dube shi da mamaki, amma ZEEYK bai bashi damar fadar wata magana ba ya cigaba da cewa

"kuma da Sharrruɗai kaman Haka!"

*Ban yarda Taɓata ba ko bayan Auren ku har lokacin da Allah zai nufi Rabuwarku*

*A gidan Mahaifanka zaku tare*

*Bazaka Shiga Ɗakinta ba Saida Izininta*

*Bazata yi maka Komai a matsayin Mata ba*

*Kama daga Lefe, kayan daki da, Kayan Abincin da Zataci zuwa nan Da watanni uku duk mu zamu siya dai dai da Ruwan sha Mu zamu siya, wannan Ba hurumin ka bane*

*Maryam bata Wanki bata guga, Kai ne zaka Zama Mai Wanki da Guganta*

*Babu Ruwanka da shiga Sabgar ta,Rayuwa zakuyi a gida Ɗaya Amma babu ruwan wani da wani, bazata buƙaci komai daga gareka ba, kaima karka buƙaci komai daga Gareta*

*Ka riƙe sadakinka bamua so, sunan Abinda Zamu Kulla aure a idon Duniya Amma a baɗini alaƙar Ɓoye ce*

Qara gwala idanu yayi ya kallon ZEEYK unbelievably, Idan dole sai yabi wannan Ƙa'odojin to ina amfanin Auren.

Dagowa yayi yana kallonshi in shock yace

"Shirme kenan Wannan Ai ba Aure bane ,Menene Manufar Haka?"

"Saboda Kana Sonta, bata sonka , idan Kayi nasarar sace Zuciyarta a iya wadannan Watannin Tho ta zama taka Har a bada, Zaka bata sadakinta zata Karba, amma idan Ka faɗi cikin Izgili zamu Biyaka Bautar da ka zage kanayi akanta"

"Nayi maka Alƙawarin A sati biyu zan sace Zuciyarta kaman yanda Ta sace tawa, Cikin Alfahari Xansa Ta karɓi sadakina ta nunawa Duniya Ni din Mijin ta ne, na Amince da Auren na Kuma amince da Sharruɗan"

ZEEYK ya fiddo masa wani file ya miƙa masa yace yayi signing, daukar takardar yayi ya karanta Sharruɗan Da ya lissafo ne a Rubuce.

Hannunshi Har wani irin rawa yake ,ya dau biro ya sa hannu.

Thofa Anya saleem ba ciccika baki kakeyi ba?🤔.

ZEEYK yayi masa bayanin akan yanda Akayi suka kawoshi Gidansu, Bacci yayi a EATERY Jiya bayan ya bugu sai ya Kwanta anan , Su kuma Sukayi using Opportunity Din Wajen Cika burinsu.

Koda saleem ya koma gida Direct Banɗaki ya fada ya shiga Gurzan Fatarsa kaman zai sauya Saida Ya ƙarar da Sabbin Sabulan wanka masu Ƙamshi a Jikinshi ,har wani ƙyama Jikinshi yakeji.

Bayan Tafiyarshi Maryam ta Shigo fuskarta tamkar ba Maryam da muka sani ba, idanuwanta sunyi circle din baki alamar kuka da rashin bacci, bakinta duk a bushe ta wani koma kalar tausayi.

Tana Shigowa ta rufo kofar sannan ta Ƙaraso inda ZEEYK yake, yana Karyawa

Hawaye na Bin Fuskar ta tace

"Yaya am afraid , Ina Jin tsoro sosai"

Yace

"Tsoron Me?"

Ta goge Hawayen da suka Zubo a idonta tace

"Tarihi ne zai maimaita kansa!, Mamy Mahaifiyata a haka taje gidan a matsayin mai aiki a lokacin bamuda Komai bamuda,zuwanta Gidan ne ya zama Sanadiyyar ajalinta, Ina tsoron Nima hakan ta kasance dani, Ina Tsoron Zuwa gidan, ina tsoron haɗa Mu'amala da wadanda suka Maida Sassan Jikin Mutum hanyar cin Abincinsu....."

Ta fada Cikin kuka sosai , Tun Jiya da Suka dauko shi taji rayuwar gaba daya Ta fita kanta, ji tayi kaman Amincewa Auren Saleem shine zai zama ajalinta, Bata Son Saleem ta Tsani Family ɗinsu bata Son wata Alaƙar da zata Haɗasu, Kuka Takeyi Sosai harda shassheƙa.

Cikin Sigar Rarrashi ZEEYK yafe

"Har Yanzu bamu tabbatar da Silar Rasuwar mamy ba, Kalmarta na Ƙarshe A garemu itace Muke bibiya don Samo Gaskiyar Lamarin, Zuwanki gidan Shi zai War ware mana Komai Maryam, Be Strong please ki tuna Fa Jaleel da Jannerh yan biyun ƙannen mu duk a gidan aka neme su aka rasa ko gawarasu bamu gani ba, Ki tuna Azabar da Mamy tasha Kafin Mutuwar ta, a yayin da take Mutuwa Ma Ki tuna wahalan da tasha a gaban Idanunmu tayi Last breath ɗinta Da Kalmar kar mu bar Jinin su Jaleel Unjust, clear the dust In ur head an Face the coming War, nasan It could

Please Login or Register in order to submit comment