Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Abba ta zauna sauran ma suka zauna suna Binta da kallo a firgice....
_Fatalwa ta shigo_ 😜🤪🤪

bata karashe zama ba Hafsah da Naseer sukayi tsalle ya faɗa Jikinta kaman ƙananan Yara, itama Rungumesu tayi wasu Hawaye suka sauko mata, bata Taɓa tunanin Ranar nan zaizo ba, ranar da zata Kasance da Ƴaƴanta Gabaki Ɗaya.

Ashman Da Rabeel kam Ido Suka Zura masu sun kasa cewa komai, Murmushi mai ɗauke da hawaye Na zuba a idanunsu

Kallon Saleem tayi Kansa na ƙasa ya kasa ɗagowa

"Juniorn inna...."

Ta faɗa tana Satar kallon Saude da zuciyarta ke barazanar Tarwatsewa,

"Look at me son.....?"

Girgiza kai yayi ahankali still be dagoba, wasu hawaye na sauka a Idonsa

Sake kiran sunansa tayi wanda hakan Yasa ya fashe da Kuka mai Sauti kaman ƙaramin Yaro.

Zaro ido Aeesh tayi sai ta fashe da dariya ganin ƙato dashi Yana kuka.

Shiru yayi still Hawaye nabin fuskar sa, kowa na falon shi yake kallo harda Maryam dake kallonshi ta ƙasan ido tanajin Tausayinsa na Ratsa zuciyarta.

Sallamar da suka ji yasa suka Sake maida hankalinsu ga masu shigowa, Yan sanda ne, nan take akayi Arresting Din Baffa Da Inna Saude, Ko a mafarki Baffa bai taɓa tunanin Wani Dan sanda zai iya kamashi ba saboda matsayin da yake dashi a shari'ance sai gashi Har gida yaya shi ya aiko a Kamashi kuma ya bisu.


Saida Aka natsa sannan akaga babu Saleem babu Maryam, wanda ya fice tun sanda yaga hankulan Su gaba ɗaya ya kau akansa, Maryam kuma ta bishi gudun Kada ya tafi kaman Yanda yayi a kwanakin Baya.

Ya Shiga motar sa, yana Shirin Tadata yaga an Buɗe an Shigo kallonta yake har ta zauna , idanunta sun cicciko da hawaye.

Muryarta a sanyaye tace

"Saleem Ina zakaje....?"

Ya kasa Amsata , ya buɗe lockern motarsa ya fiddo kwalbar Whisky cikin Jan numfashi zai kai bakinsa ta riƙe kwalbar gammm hankalinta a tashe, dama Bai daina shan Giya ba?.

Ture hannunta yayi yana ƙoƙarin Kai kwalbar bakinsa ta kwace da Sauri, taji yaja wani numfashi da ƙyar wanda ya fita tare da zubuwar wasu hawaye Masu zafi, ta girgiza masa kai

"Saleem you don't need this , kayita Maimaita innalillahi Wainnailayhirraji'un zakaji Sauki a zuciyarka"

Hawaye suka Dada Zubowa a idanunsa

"Maryam bakisan yanda nakeji a Zuciyata ba, I maltreated my Biological Mother, I treat her like a slave, Allah Bazai Taɓa yafe Min ba "

Sauke kwalbar tayi

"Kayi haƙuri"
Ta faɗa tana ƙoƙarin zame hannunta dake cikin nasa amma ya riƙe gam, sunkuyar da fuskarta tayi tana kallon hannunsu, taji Saleem ya sakala hannunsa ɗaya a saman wuyanta, tare da kifa fuskarsa a saman nata fuskar, idanunsa rufe wasu hawaye na sauka suna ɗiga a saman hannunta, jikinsa har wani rawa yakeyi

"Mostang....!"

Ya kira tada wata siga mai wuyar fasaltuwa

"Na'am..."

Ta Amsa murya a dishe
Shiru yayi yana kallonta sannan ya sake matsa jikinta ya rungumeta kadantana son kwacewa yace

"don Allah kibarni inji hugging sannan inyi kissing ƙinki for 5mins"

ta yi masa shiru yace

"Then Give me The wine 🍷"

Ƙin bashi tayi, Tana kallon idanunsa dake lumshe, numfashinsa dake seizing Yana shiga directly cikin hancinta,

gyara fuskarsa yayi a saman nata, ya saita bakinsa a daidai nata bakin, kafin gently ya buɗe bakinsa hakan yasa ɗan ƙaramin lips dinta shigewa cikin nasa kadan,idanunta ta zaro waje sbd tsoro.

Kwalbar dake hannunta ya suɓuce ya fadi, ta riƙo gaban rigar sa da Ƙarfi tana lumshe idonta da Sakin Munaafukin Ajiyan Zuciya.

Hankalin Abba a tashe ya fito, Ashman, Ashraf da Naseer suka fito suna duba su, ganin Motar Saleem a Parke yasa Ashman ya nufo wajen....!



Nayi Gabas🚶🏽‍♀️🚶🏽‍♀️🚶🏽‍♀️

Bintou ✍🏼✍🏼

11th jan

[1/14, 17:43] Bintou Abdul: *WUƘA A ZUCIYA*
_(BLEEDING HEARTS)_


*067*

*_The Semi final_* ♥️

Kwalbar dake hannunta ya suɓuce ya fadi, ta riƙo gaban rigar sa da Ƙarfi tana lumshe idonta da Sakin Munaafukin Ajiyan Zuciya.

Hankalin Abba a tashe ya fito, Ashman, Ashraf da Naseer suka fito suna duba su, ganin Motar Saleem a Parke yasa Ashman ya nufo wajen, bai ida Karasawa ba idanunsa suka hango masa Mayafin Maryam da ya leƙo ta murfin mota, ya juya yana sakin guntun Murmushi

"Abba Saleem Bai Tafi ba, yana Tareda matar sa''

Sun fahimci abinda yake nufi don Haka duk suka juya suka Koma ciki.

Kallon juna suke suna sauke numfashi ahankali,kowa na qoqarin daidaita numfashin shi.

Saleem Yayi ta maza ya kauda kanshi yana Shirin tada motar, ta riƙe hannunsshi, ya juyo ya auna mata wani kallo,ta marairaice murya chan kasa tace

"Please don't Go?"

girgiza kanshi yayi yace "i can't stay" gyada kai tayi hawaye na shirin saukowa tace "why....?, Saboda kayi kuskure?"


Baice komai ba , ta cigaba

"A kashi 100 na rayuwa kashi goma ne abinda da ya faru dakai, sauran 90% means how You React it, we learn From Failure than success idan bamua kuskure Taya zamu gane daidai?, Please don't Let this stop you the family is back don't ruin it"

Ɗago kansa yayi ya dubeta da Kwantattun hawayen dake idonsa, ta gyada masa kai

"Kana tunanin They won't Understand you Right?"

Still shuru yayi hawaye Masu ɗumi suka gangaro masa.

"People Who donot understand Your silence will never Understand Ur words ,idan ka tafi babu wanda zai gane tubanka, ka Fito ka nemi yafiyarta nasan Bazata ƙi yafe maka ba"

Sosai kalaman ta suka ratsa har Kwanyarsa ,har yaji Haushin Kansa nakin tsayawa Ya nemi yafiyarta da yayi, Amma abin da kunya, ya wulakanta ta sosai, ya zuba Mata Hot coffee a fuska Yafi a ƙirga , no wonder yaji mamaki in ya watsa mata Tea a fuska, duk zafinshi fuskar bata taɓa Chabewa ashe ta roba ce , ya kaskantar da ita kaskanci mafi Tsanani yayi treating dinta kaman ba mutum ba, Take ya fara da na sani Mara Amfani Har cikin Zuciyarsa.

Shuru ya ratsa Motar yana Sauraron kalamAn Maryam dake ratsa shi Kusan mintuna 20 baice komai ba .


Ji yayi ta bashi kwarin gwiwa tare suka fito suka koma ciki, duk kunya yabi ya isheta Ganin irin kallon da suke masu , gani Take kaman Sun ga abinda ya faru, a kunyace ya duƙa gaban kowa yana Hawaye ya roki gafarar ta, ta dagoshi tana Murmushi

"Babu Abinda ka min Saleem, Rayuwanka gaba ɗaya abin Tausayice, banga Lafinka akan Komai ba, na zama Coffee maker ɗinka ne domin In bama ɗana kulawar da ta dace, in Sama Masa farin Cikin da ya rasa a wajen Kowa"

Rungume ta yayi yana Hawaye

"AM sorry Mum....Am sorry , am sorry I love you"

Kuka yakeyi kaman Ƙaramin Yaro, Ya wani kankameta, ta shafo kansa tace

"I love You more..."

Hawaye suka sauko mata.

Ganin dakin nan shirin Komawa filin Koke koke sai Naseer ya mike da Sauri

"Guess what...!"

Ya buga tsallle
"Shettima's Family is back whoop"

"Yeah....!

Inji Ayyan Yana Tsalle,ganin kawun nasa nayi.

Dariya suka baje ana hira cikin farin Ciki, yau jinta suke kaman Ranar sallah Dama sun Tsani Inna Saude Basu sonta ko kadan ,Baffa ma Ya zame masu Ciwon ido don Kawai babu yanda suka iya dashi ne, gashi Lokaci ɗaya Allah ya Kore su ya Maye masu da Gurbin su da farin Ciki a cikin Ahalin, Ashman yayi ordering Abinci daga Restaurant aka kawo , Lokacin da Abincin Ya iso ana kiraye kirayen Sallahr Zuhur, suka Nufi masallaci a tare,cikin tawagar Zaratan Mazajen gidan , matan Gidan Kuma suka maida hankali wajen Gyara Abinda aka kawo kafin su dawo, suma sukayi sallar Suna hira, Inna Yathai sai Tsokanar Maryam Takeyi ganin taƙi sakewa, sai Wani sunkuyar dakai take, da zarar Sun haɗa ido sai ta tuna Sanda take a matsayin yar Aikinsu, ita ke tayata girki suyita hira kaman Kawaye ashe surukarta ce _Wayyo kunya🙈_ .

Bayan Sun dawo suka Hallara a Katon General Dinning area, Hafsah , Maryam da Aeesh sukayi Serving kowa ,Abba ya zauna kusada Inna Yathai sai Faman shisshige mata yake ko kunyar yaransa bayaji, ita kou sai Faman daure fuska take tana Basarwa, Saida Saleem Ya Bari Maryam ta zauna sannan ya Mike ya Koma gefen ta ya zauna, Ji tayi kaman Ta nutse don Kunya, Aeesh na zaune kusada Ashman Sai Shawgaba take Masa Duk tabi ta Janye nutsuwar bawan Allah, su Ashraf ,Naseer , Da Hafsah kou sun cure waje guda sai wulla idanu suke kaman Wasu kadangaru, ammie na tsakiyan Goggo da Sureey Goggo sai Tsokanar Sureey takeyi.

"Ance batada Da lafiya gashi Sai kwadayi takeyi"

Ashman Ya dubesu Yana Murmushi,sai ya tuna Itama Aeesh sanda takeda cikin Aeerah, batayi Laulayi ba illa Kwadayin da ta rinƙayi har da Tashin Dare, ya girgiza kai ya dauko yankakken Apple zai kai bakinsa , Ta kawo bakinta yana Shirin kaiwa baki ta kwace.

Ya juyo fuskar ta da sauri, ya zura hannunsa cikin Bakinta ya shiga laluben apple ɗin, ta Gantsara mishi cizo.

Da Sauri ya cire hannu yana

"Wash"

Ji yayi duk Sun Kwashe Da dariya, sai yanzu ya tuna Ashe a gaban Family Yake, ya Sunkuyar da kai yana hararar Aeesh ta gefen ido, tayi masa gwalo a fakaice.

Maryam Kou kasa sakewa tayi taci abincin sai Faman Jujjuyawa take kanta a ƙasa, Saleem ya dunguri kafadarta ta dan Ɗago tana harararahi, ya Kanne mata Ido ɗaya Ya fiddo bundles din yan dari biyar biyar guda biyu daga Aljihunsa ya tura su gaban Maryam hakan yasa hankulan Kowa ya dawo kansu

"Brothers ku zama shaida Yau Na biya Bashin Matata, na bata sadakinta"

Ji tayi Kaman Ta shige kasa tsabar kunya, yanzu Sai Kowa yasan bai bata sadakinta?, Ta take ƙafarsa tana Kwaɓe Fuska.

Ashraf ya hararesu

"Yoo mu Ina Ruwan Mu da bashin ka?"
Hafsah tace
"Yoooh dama Shi gauro ina Ruwanshi"

Dariya Ashraf yayi ya kai hannu ya shafi gemunsa yana Kallon Sureey ƙasa ƙasa.

"Yarinya Allah ne ya kashe ya Bani"

Maryam Kou ko kallon Kudin Ta kasayi Saboda kunya bata san Me tayi ma Saleem he keep Disgracing her 😔, har dare Suna Gidan, da la'asar Ammie ta koma Gida saboda Ta lura da irin Kallon da Ashraf yake mata, kada a shiga Hakkin Baiwar Allah mai takaba.

Cikin awannin da basu wuce biyar ba gidan Abba ya zama Kaman Ba'a taɓa yin Wasu Saude da Hamza a gidan ba.

Inna Yathai taso Tafiya, Yaranta suka Riƙe ta, Sun hanata tafiya Suma basuje ko ina ba , bayan sun dawo daga masallaci Sunyi Sallar isha'i suka yi dinner , Ashman Yace naseer ya kwashe kayan da sukayi amfani dashi Matansu sun gaji.

Naseer yayi fuskar tausayi ya kalli Ashman zai yi magana Ashraf ya Harareshi, ya tashi yana turo baki kamar wani jinjirin kaza, ya kwashe ya kai Kitchen.


Shima Saleem duban Agogonsa yayi..

" Nidai gaskia i cant sleep here, Wifey tashi mu koma gida"

Da sauri marayam ta Mike tabi bayansa, dama Tuni Ayyan yayi Bacci Anan Suka barshi.

Aashman Ya dube Aeesh yace..

"Ihty Muma yaushe Jirgin mu zai daga?"

Aeesh da bacci ya fara Cin idonta, ta Lumshe su tace

"Pilot is Already there,saura passenger"

Aash Ya kamo hannunta

"Open ur eyes ,Ki kora baccin nan ZAUJAH, We have along way to go"

Naseer yayi gyaran murya yace

"Ahky I want to be like you when we grow up"

sukayi daria duka, Aash ya kamo hannun Aeesh suka fice tana tangyadi,

Yana cewa

"Oya Gauraye good night"

Tsokanar ta yayi tayi har Suka isa Gida, ganin da gaske baccin Ke son dauketa, a Wani Katon Eatery ya tsaya ya siyo kaza Da Fresh milk kafin ya koma mota har tayi Bacci.

*SALEEM*

Maryam taga take taken Saleem yau ganin kansa yake kaman Ango tunda taga ya tsaya a eateryn da take kai Kaji taji tsoro ya kamata, barin Ma da taga ya dawo Katon Leda sai Kamshi yake tashi, duk ta tsorata da yanayinshi, sai Tsokanar ta yake tana kauda Fuska.

Suna Isa yayi wanka, tana Parlorn ƙasa tana Danna waya ta kasa cire Mayafinta.

Dawowa yayi bayan yayi wanka ya dubeta yace..

"Wifey azo ayi wanka "

Batayi masa Musu ba, ta tashi ta shiga dakinta dake sama, tayi Wankar ta fito sai a lokacin taji dadin Jikinta.

Tana shiga ya Shigo, ya janyo Akwatin ta ya ciro mata wata doguwar riga ta Bacci mara hannu.

Saida ta dau kusan 20mins tana wanka ta shirya ta fito daga toilet din.

Zaune ta ganshi kan chair hannunsa na jikin table yana Latsa waya, daga Shi sai Bathrub, ba tare da ya kalleta ba yace

"Wife kin fito? "

"Uhm ''

tace dashi, ya rufe zura wayan a Aljihunsa ya nufota yana fadin

"Muje ɗakina"

"No nan ya wadatar"

Ta faɗa tana ta runtse ido wai ita bacci takeji,

"Ka tafi bacci nakeji"

kana ganinta zaka hango tsoro a idanunta, ta haye gado tana Son yin bacci,

hayewa gadon yayi, idonta ra ƙara runtse wa, ya matso bayanta ya kai bakinsa saitin kunnenta, cikin wani irin salo yace

"Muje ɗakina ki kwanta zakifi samun Lada"

Zumbur ta bude ido, Tana Matsawa daga kusa dashu, tace

"Saleem please kayi... kayi hakuri DanAllah, not now"

Ya dora kanshi kan wuyanta, yana kamo hannunta dake shirin ture shi.

jikinta ya fara rawa , ta tashi zaune, idonta ya fito don fargaba, abun da ya jima yana so ya gani kenan , tsoro ƙarara ya gani a kwayar idonta Murmushi yayi yace

"i love the way I scared somebody's daughter"

kukan shagwaba ta fara yi, ya sake Murmushi saitin kunnenta ya rada mata

"Is the shagwaɓa for me?

Ta sauke kai sai Hawaye, cikin Rarrashi yace


" Keep Calm Baby, i got you kinji?, Babu Abinda zanyi miki, now ki Tashi muyi Sallah"

da kyar ta gyada kanta tare da runtse idonta ta mike nufi toilet tayi Alwala shima Alwalar yayi, ta saka wani Dogon Hijabinta, yajasu a Sallahr, bayan sun idar ne Saleem ya dafa kan maryam, yana karanto Addua kaman yanda hakan ta kasance a ɓangaren su Aeesh a daidai wannan Lokacin sun dade suna ma Matayensu adduoi da adduoi zaman lafia a tsakaninsu kafin suka shafa, bayan sun danyi lazimi ne Maaan ya kalli Aeesh da ta natsu yace

"What next"

Ta kalleshi ta ƙasan Ido tace

"Kaaza"

Murmushi yayi ya girgiza kai, ya dauko Please ya shinfida Kajin, ya zauna yana Kallon yanda yake cinshi hankalinta a kwance, saida taci Kusan Rabi ta kora da Fresh milk sannan Ta kwanta tana gyatsa, shima ya kwanta a bayanta yana rada mata

"Babu kyau bacci immediately after eating, Tashi Muyi Exercise before You sleep"

Da haka Ashman ya lallabata yayima yar mutane wayau.

A wannan daren ma'aurata huɗu dinnan sun raya daren nan mai Albarka, daren da suka na lak'abi da Daren Alheri, dare Mai dimbin Tarihi a rayuwarsu, inda Babban Yaya ya angwance da Amaryar sa A karo na biyu bayan haɗuwan Farko na Shekarar da ta wuce, shi Kuma karamin Da ƙyar ya lallaɓa mai kajinsa ta Bashi tukuicin sadakinta, sai a yanzu yake dana sanin Tsanar mace da yayi a baya, sai yanzu ya gane ni'imar dake tattare da Wannan halittar , hakika duk wanda ya rasa mace a rayuwarsa yayi Mummunar rashi, a iya shekarun da yayi a baya , babu mace a rayuwarsa, Rayuwarsa ta kasance abin tausayi, amma a iya yau kadai da Allah ya maido msa mahaifiyarsa da Matarsa a cikin rayuwarsa yaji kaman bai taba Shiga kunci na rayuwa ba, yaji shi cikin duniyar da bai san da akwaita a rayuwaba, yajishi Kaman sarki a fadarsa, rabon da yayi Farin ciki har ya manta, Amma Sanadin Mace yau Shike jin kanshi Kaman bai taba shiga wani Damuwa ba a rayuwarsa , addu'a yake ta faman kwararo mata tareda Alƙawarurruka da dama wanda Shi kansa yasan Sunfi karfinsa , amma tsabar Shauki cewa Yake
_"Na mallaka miki kaina da Komai nawa harda masoyana na Wuƙa a Zuciya"_ 🤣🤣


Ashman Sai lallaɓa Rigimatunsa yake tanata Faman zuba masa Shagwaɓa, ranar da kyar suka rintsa.

Da safe Ashman da kanshi ya Shiga Kitchen ya haɗa masu karin Kumallo, har yanzu Mutumiyar na nan sai kuka take, taji ta maza tayi laushi.

Ya kawo mata Har inda take

"Zaujah har Yanzu kukan kikeyi?"

Bata Amsahi ba, ta shagwabe masa Gabaki ɗaya ta gama Ruɗa Bawan Allah , sai Rarrashinta yake da kyar ya shawo kan ta Taci Abincin Kuma kadan taci, Saida yaga ta koma bacci sannan Ya nufi Part din Deejah Don Yaga ya Ta kwana.

A hargitse yaga parlorn wanda hakan ya haddasa masa mummunan faduwar Gaba da ƙyar ya ɗaga kafarsa ya nufi dakin ta, amma tun kamin Ya shiga yakejin gabansa na tsananta faduwa Abinda Ya gani Shi ya firgita shi, kayan Wani ne jere a ƙasan ɗakin

Take kwakwalwar sa ta daina aiki na wucen gadi, ganin wani sangamemen gardi kwance a gadon Matarsa Ta sunna daga shi Sai vest ya rufe Almost Rabin Jikinsa da blanket, fuskarsa akan Wayarsa yana Dannawa

Innalillahi Wainnailayhirraji'un

Ya furta a Bayyane, dai dai Lokacin da Deejah ta fito daga Bathroom Wanka ta fito,

"Honey lafiya?"

Ta faɗa tana kallonShi ,ganin yana kallon wani waje yasa ta kai Dubanta wajen ,ganin ƙato kwance a gadon ta yasa ta Zaro ido duk ilahirin Jikinta rawa yake.

"Khadeejah Wane ne wannan Who's he?"

Ta tsinkayi muryarsa a dake, jikinta ya hau rawa jin yanda yay maganar babu alamar wasa a cikinta.

Ta haɗiye ƙwallar da suka taho mata a ido cikin rawar murya tace

"Wallahi Ban sanshi ba"

Jin An Kira Khadeejah yasa shi ɗagowa ,bai tsammani ganin Deejah ba, wajen Aeeesh yazo me hakan Ke nufi?, Dama Aeesh mai mata ta aura?, Kuma mijin Deejah?.

Zumbur ya mike yana rarraba idanu

_what have I done!_

Bamalli ya faɗa to himself hankalinsa a matukar tashe, Tunda Aeesh Ta mareshi ya dau Alkawarin ganin Bayanta da aurenta, Tunda akanshi ta daga hannu ta mareshi, Abinda ba'a taba yi masa ba a duniya, ko Uwar da ta haifeshi Bata taba marinshi na, Abban shi ma tsoron Yi masa faɗa yake.

Akanta yayi missing abubuwa da dama a rayuwa, bai taba neman abu ya rasa ba, akanta ya fara,yasa a zuciyarsa Koda tayi aure bazai bar bibiyan Rayuwarsa ba har sai ya Kashe Auren Ya kuma aureta.

Da kyar ya gano gidan dukda ba Boyayyiya bace, sai don Aeesh bata jima da dawowa gidan Ba don Haka ba'a wani santa ba, ya shigo ne a matsayin cousin din madam, ya labe a kusurwar ɗakin Yanajin alamar ta shiga Bandaki ya Shigo ya kwanta,a cewarsa Aeeshce, Yasan Deejah tun a University sunyi soyayya Amma bai kaiga aure ba saboda withdraw ɗinta da akayi a First year.

da wani irin Karfi Ashman ya shaƙo wuyar Bamalli ya hada shi da bango nan take kansa ya fashe ya fara jini, tsabar tashin Hankali kasa gane fuskar sa yayi, dukansa yake kaman an Aiko shi, yayi masa jina jina da kyar ya samu ya kwace kansa ya face da kumburarren baki.


Kuka take tana Rikonshi akan Wallahi bata sanshi ba ,Cikin Matsanancin fushi Ya sauke mata tafi

Ta dafe kuncinta Hawaye na zirya a fuskar ta

"Kayi hakuri Dr Amma wallahi babu abnd..."

Tasss ya ɗauke ta da mari, ya Shiga marinta ta ko ina, kafin Kace me ya kumbura mata fuska, ya korata gidan su danna mata saki ɗaya, rasa Inda zata saka Kanta ji tayi duniyar na juya mata, ko tsinke bata dauka ba ta fice daga gidan, tana Fita jiri ya kwashe ta ya kifa da ƙasa, Bamalli da Takaicin Duniyar nan ta hanashi Tafiya ya hangota ta cikin Motarsa cikin tsananin Tashin Hankali ya nufota amma kafin ya kaiga isa gareta har ta fadi kasa Sumammiya.


A firgice ya Kaita asibiti, nan take aka bata taimakon Gaggawa, Jininta yayi Mugun hawa da yike Asibitin Da ya Kaita sun San Dr Umar nan da nan aka buga masa waya aka fesa mata komai, cikin Kankanin lokaci ya iso asibitin hankalinsa a tashe, ganin Halin Da tilon Yarsa take ciki yayi matukar tayar masa da hankali, har yakaiga ya fidda hawaye.


Bamalli Dake tsaye yana Kallon Yanda hawayen dattijon ke fita , cikin takaici da Haushin Kansa ya nufi shi ya durkusa har ƙasa yana neman yafiyarsa ya yafe masa shine Musabbabbin fadawanta cikin wanann halin, A takaice ya gaya masa gaskiyan abinda ya faru cikin fushi Dr Umar ya Daukeshi da mari ya chakumoshi Yana Kai Masa duka tako ina, Dr ne ya fito yana fadin Ta farfaɗo, a tare suka shiga dakin a firgice, Deejah na ganin Bamalli hankalinta ya tashi Abinda Ya faru ya dawo mata ta fara hawaye yanzu shikenan Aurenta da Ashman Ya mutu?, Innalillahi Wainnailayhirraji'un,

Cikin tashin Bamalli ya duka har ƙasa yana bata Haƙuri, Dr Umar sai koransa yake yana Masifa, cikin karfin hali Deejah tace

"Daddy ka Ƙyaleshi , he did it because of love ka manta har attempting kisan kai nayi akan Soyayyar Aashman?, Then in Wannan Was Understandable why bazamu yafe masa ba?, wane Laifi ne ya kai na kashe rai muni a duniyar nan, In har za'a yafe Min wannan mai zai hana Nima na yafe masa?"

Cikeda takaici Dr Umar yace

"Yanzu idan Mun yafe masa da wani Ido duniya zasu kalle mu?, Yasa an sake ki da tabon zina da Aure!"

Bamalli yace

"Kayi Hakuri ranka shidade, Ka amince min Na aureta idan ta gama idda, nayi maka alkawarin zan Bata gata fiye da tsohon Mijinta, Zan kula da ita tamkar Sarauniya"

Deejah tayi numfashi, tana Tuna zamanta a gidan Ashman ,babu Abinda Ya amfanar matA illa tarin Baƙin ciki da ƙunci

Ba tareda tayi dogon Nazari ba tace

"Na amince zan aureka, Basai nayi Idda ba, babu Abinda Ya taba shiga tsakanina dashi"

Dr Umar ya dubeta da mamaki ganin tayi saurin Amincewa yace

"Kin sanshi ne?, Meyasa zakiyi saurin Amincewa?"


"Dad nasan shi, he's my ex boyfriend"

Ta faɗa Tana Jin Kanta na sarawa.


Abu kaman Wasa A ranar ya faɗa a gida aka zo aka tambayo Auren Deejah, aka saka rana Nan da sati Guda don tace bata da Iddar Ashman wannan Ne ya sake tunzura Dr Umar yace

"Dole ayi Auren nan ko dan Ya nunawa Dr Khameeth ba Ɗan kadai bane a duniyar nan kuma ba rasa masoyi tayi ba"

da yaga Bamalli dan Gidan Sarauta ne sai ya sake jin dadi, dama ya dade yana kwadayin Gidan Sarauta sati na zagayowa aka daura auren Khadeejah Umar da Muzzammil Bamalli akan Sadaki Dubu ɗari lakadan ba ajalan ba, ba'ayi wani Bidi'a ba, don ba kowa yasan da auren ba, aka kai Amarya gidanta, gidan da Bamalli Ya gina Masu inda ya tsara zaiyi rayuwa tareda Aishar sa, da Kayan Auren Da ya siyo a lokacin aurensa da Maryam.


Abba Baiji daɗin Sakin Da Ashman yayi ba, faɗa ya mai sosai Akan meyasa zai yanke hukunci cikin Fushi batareda yayi Wata bincike ba, ya kuma ce ya gaggauta mayarsa ,koda yaje gidansu Deejah ya tarar Har an kawo kaya.

Rayuwa kenan, So tari akwai Abinda muke so wanda ba rabon Mu bane, ko mun samu Dole mu rabu dashi ,idan Rabon namu Shine Mafi alheri sai kaga Allah ya musanya mana Dashi har mu manta mun taɓa neman abinda ba Rabon mu ba.

A cikin kwanakin nan kuwa, wani sabon Kwanciyar Hankali ya shigo Gidan Ahalin Khameeth Shettima , Basu da wata Damuwa, Suna zaune da junansu cikin Aminci da kwanar juna, Saidai Amma taki yarda ta dawo cikinsu tace ita a halin yanzu tafi Son ta zauna ita kaɗai, ƴaƴanta Suka ce basu yarda ba, In Ma so take ta hukunta Abban su ta tuna cewa ba Laifinsa bane duk abinda ya aikata ba a hayyacinsa yake ba , da kyar ƴaƴan nata suka Shawo kanta ta dawo gun Mahaifinsu bayan ta Gama Jan Masa aji.


Rayuwa Kenan, Gaskiar Hausawa da sukace Ramin ƙarya ƙurarre ne, In zaka gina ramin mugunta ka ginashi dan k'arami, kuma komai nisan Jifa kasa zai dawo, Kuma duk wani abu da ba a ginashi ta hanyar Allah ba, to ba a ganin daidai, saude ta raba Giatha da ƴaƴanta duniya ta shida ƴaƴanta ne, burinta ta mallake Shi da yaran Gabaki ɗaya ta yanda ko sun girma Zataci riba dasu , K'aryar Saude ta k'are yanzu ba ta da sauran gata don koda akayi Shari'a da ita babu wanda ya taimaka Mata, Baffa Kam masu Abu da abinsu kwanansa biyu a Cell aka sakeshi, Amma anyi Seizing license dinshi, Bai dawo Gidan Abba ba, ya koma Gidan Ɗansa da Niyyar ɗaukar fansa,

A ranar da ya dawo ya koma wajen malaminsa, yace zai turo Aljanaar sa tayi masa aiki da daddare.

Cikin dare yayi mafarkin amfani dashi,koda ya farka ya ga

Please Login or Register in order to submit comment