Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Baka ya kyale.

Aikou Mama na fita ta haushi da masifa ta inda Take hawa ba tanan Take sauka ba harda yunkurin Dukansa, dan Aiken Na ganin Haka Yayi tafiyarsa dama Kuma da motar Maryam yazo.

Ganin Yar tsohuwar na Neman dizga shi akan Abinda Ba Laifinshi ba, Yasashi jan Ƙafarsa Ya bar Unguwar, a hanya ya Kira saleem Ya bashi Labarin Yanda Akayi ya Kara da Cewa Da Na Kara MINTI BIYU A WURIN Wlhy babu abinda Zai hana tsohuwar ta daukeni, Numfashi Saleem Ya Sauke Yana ƙara Jaddada Hamdalansa ga Ubangiji Dama Yasan Za'a Rina Shiyasa Baije dakansa ba, Shi dakansa Yasa Aka samo Masa Address dinta ya Tura A Kaimata Motar .

Motar Ta gyaru sosai Don Har sabon Painti Akayi Mashi Fitillun Da Suka Fashe Kuwa An sauya su Izuwa Sabo , Taji daɗi Kuma tayi mamakin Yanda Akayi saleem Ya Biye Mata, Yabi umurnin Ta

Taɓe Baki Tayi

"Ashe Jijji dakan Na Karya ne, Irinku Bakua Wuyan Moruwa Ga Mace ”


AEESH

Rayuwar Aeesh a gidan su Abba Ta zama Tamakar rayuwar baiwa a Kurkuku Sosai Inna Saude ke nuna Rashin Imaninta akanta Tana Gana Mata Azaba Ta ko ina.

Rufe ta tayi a small room na part ɗin ta ,Dakin Na Dauke da Toilet Sai Gado daya Madaidaici, Akwai Television da Fridge a dakin

A ciki take Gudanar da Komai nata bata fita ko'ina haka babu mai shigowa, Abinci ma idan za'a bata Sai sunci Sun Rage, Sai a Ajiye mata basu Damu ba idan taci Ko Bata ci ba, Wannan ba damuwarsu bane .

So tari sai Abincin yayi kanzo sai a kankaro Mata, Tun tanaci tana Amai har ta fara sabawa, Sun Maidata Mara Yanci, da Sanin Abba Ake zalinta mata, A Gaban Abba Take sawa a kai mata Abincin da suka Rage yana Gani, Saude ta riga Ta Gama dashi Bashida na faɗa,Baffa dama Ya tsaneta Baya Kaunar ta Hakan Da Ake Mata Shine daidai A wajenshi, Su Salem kuma ba wani zaman gidan Sukeyi ba a zatonsu Aeesh ta bar Kasar Tana Chan wajen Ummanta Kaman Yanda Inna Saude ta Gaya msu Tun Farko.

Tsabar Rashin Imanin Abba yana sane da Komai ya kasa Kama Gaskiya ya kawar dakai Akan Barazanar Saude ya ceci ɗiyar Ƴar uwarsa.


Sai a yanzu ta Gasgata batun Ammi da tace Batada Kowa a duniyar nan bayan Ita, Duk kaunar da Ashman kenuna mata da zarar mummunar ƙaddara ta sameta Kyaleta Zaiyi ,Ammi itace gatan ta Itace Gatanta a duniyar nan bata da Kowa bayan ita.


AEESH kullum Cikin Gudanar da Salloli take tana Kai Kukanta ga Allah domin Kuwa tasan shine Majiyin rokon bayi kuma zai yaye mata komai, Akoda yaushe Cikin addu'a take Allah Ya ba Ammi ta lafiya Ya dawo mata da ita Lafiya, Idan Ka ganta yanzu sai ta baka Tausayi, Ta ƙanjame taRame sosai Duk Jikin ta ƙasussuwa Ne Tako Ina Bata da kuzari Kullum Cikin Rashin lafiya Take Amma Babu wanda ya sani, dunkunewa Take tasha Kukanta har bacci Barawo ya sace ta.

Duk wannan Abubuwan da Inna ke mata Da cewar Tana Mata Haka ne don Cika sharudan Idda, A garin su Haka akeyi ma Bazawara idan Auren ta ya Mutu.

Kaman yanda Aeesh take Cikin Ƙunci Ashman ma haka domin Kuwa Rashin da Karfin Tsiya yake Kokarin Yakice Aeesh a rayuwarsa baya kaunar abinda Zai sake Hadashi da Ita , Hakan Ba ƙaramin Takura ma rayuwar Auren Su da Deejah Yayi ba ,Har yanzu babu Abinda ya taɓa shiga Tsakansu Da ita , ta kai masa Hari yafi a ƙirga don taga yaji Sha'awar ta Amma kaman Dutse haka Ya nuna mata bata Gabanshi.

Ada a Kullum burinta,ta auri Aash Gashi ta Aureshi Amma bata samu Abinda Takeso ba, Illa ma Rabata da yayi da Ahalinta da kawayenta, tun tana satin farko ya chanza Mata Waya Da sabuwar layi bai Kuma Bata Damar Mu'amala Da Kowa Ba sai Iyayenta da Yayyinta, Bata fita ko ina Saide azo Mata, Dukda hakan baiyi mata ba Amma ta dau Alwashin Kawo karshen Takurawan da yake Mata Sai Ta maidashi nata Ita kadai ta juyashi yanda Taso.

*Bayan Watanni huɗu*

Abubuwa Da dama Sun Faru Cikin su kuwa harda Komawan AASU daga Strike, wannan ne ya fidda Aeesh daga Ukubar da Su Abba suka sata , Sun Koma makaranta ,ba don Sun So ba Suka Koma zaman Hostel ita da Bestynta Reeey.

Kowa ya ganta sai yayi zancen Ramar da Tayi , Reey ce ke basu Amsa daidai Da Tambayar su.

Dama Reey ce Me Bakin Ita ke tare mata Rashin arzikin Da ake Mata , ba'a Taɓota ba Ta tanka Ballantana An Taɓosu!.

A lokacin Da Saleem ya Gane Cin Mutuncin da Umma Saude Tayi mata Fada yyi tayi Sosai kaman zai rufesu da Duka ya Kuma ce Ko Labari Yaji Ran Aeesh ya Ɓaci a gidan Sai ya bata wa Kowa, Da yike shalele ne Sai binshi akayi da Rarrashi, Salem ne ya Biya mata School Fees a haukansa Cewa Yayi har Yanzu tana nan a matsayin matarsa Tunda Ya riga ya furta ya dawo da ita Tun kan ta gama idda.

Kaman yanda Ashman yayi watsi da ita haka itama tayi watsi dashi, Tasha Zuwa Gidansa ana Wulaƙanta ta Tun daga Gate don Ya Riga Ya ba masu Gadi Umurnin baya son Ganin ko me kamarta a gidansa.

Yasan Da Komawar ta Makaranta haka Kuma labarin Zalincin da akayi Ta mata Da cewar tana zaman idda labari Yazo gareshi Amma bayajin zai iya yin Wani abu Dangane da hakan a halin Yanzu tsanar ta yake Yi Sosai aduk lokacin da ya tuna da ita sai ya tuna Da Mummunar Gamon Da yayi 😭, *Da idanun Sa Yaga Abbansa Na kokarin Raping ɗinta Bayan ya Gama Lalata da Ammi a lokacin Ammi bata cikin Hayyacin ta ,a ranar Aka kashe Masa Mahaifiyar sa, a Ranar saleem Ya kashe masa Mahaifiyar sa, Ranar itace Rana mafi muni a rayuwarsa Ranace mafi firgici da Tashin Hankali da bazai taba mantawa ba, Gigicewan da yayi ne yasa Sensories dinsa Bugawa Ya koma kamar Mahaukaci mai bugun mutane ba daman a matso Kusa dashi ya kama Mutun Sai Ya suma , Zai kyale shi*

Da Karfin Tsiya aka ɗaureshi Aka Buɗe masa File a Psychiatric, Yyi Jinya sosai Kamin daga Bisani Allah ya Kawo masa Sauƙi ya samu Lafiya amma da zarar Yaga Saleem Fa Mai raba su Sai Allah ,Haka Daddy Yasha Azabar Ashman ,don Akwai Ranar da Ya siyo fetur Ya daidaici Lokacin da Abba ya shiga Ban daki Ya shiga Part din Abba Zazzageshi a ko ina ya Kunna masa Wuta yafito Da kyar Abba yasha....

Tun daga Lokacin Al'amarin Ashman ya fara bashi Tsoro ya fara jada baya a Lamarin shi.

Cikin ikon Allah kuwa Lokaci Guda Allah Ya Yaye masa Wannan Matsalar, Amma fa da zarar wani Abu makamancin Abin da Ya faru a ranar ya Gifta a ganin sa Yake birkicewa, Daga nan Samo kansa sai Allah,da kansa Ya nema Ma kansa Mafita Ya tattara kayansa Ya bar Gidan Su Abba , ya koma Gidan sa na kansa Idan suna tare da Abba Da saleem Zai iya aikasu Lahira.

Zurfin cikinsa Ya Hanashi Bayyanawa Jama'a Abin da ya gani,har yau babu Wanda yasan abinda ya faru, ita kanta Ammi bata san Abinda Ya faru da Ita Ba.......!

*Kaduna State University (kASU)*

*_Kaduna Hostel_*

Dawowan su kenan Daga lecturers Yau lecturern ya buga Msu zafi ya kuma basu group Presentation Zasuyi presenting Zuwa Next week......


Sarah Ce ta Banko Ƙofar da Karfin Tsiya tana Waƙa bakinta cike da Popcorn 🍿

Su Hdu ne a dakin Reey Aeesh Sarah da jasmine

Saratu Wacce akafi sani da sarah Yar calichali ce kuma yar rawa Ga Tsokana Da neman Tsiwa.

Jasmine Ita kadai ce Addininsu ya banbanta da nasu, Batada Wani matsala amma Akwaita da Shegen Iyayi hakan Yasa Basu shiri da Reey ,Kullum cikin Fada Sukeyi.


Cika Bakinta sarah ta karatu Da Popcorn

"Yeeefgth....!, Soyayya dadi idan Har dakai Zanayi in bakai wazana Kalla a bayan Rai 🎶🎵, Guys Guess Ina Na je?"


Tsaki Jesmine dake Kwance kan Gadonta tayi, Aeesh tayi Murmushi kusan a tare suka hada baki da Reeey wajen Cewa

''nope Sai kin faɗa"


"Hmmm babes Yau saurayina Yazo munje yawo"

Gyara Zama Reey tayi

"Inyeee yarinya anyi Upgrading to da Ina da ina kuka je?"


"Munje smart kid ,Da Domino Pizza Omo Come See love, Bansan Haka Muhammad ɗina ke sona ba sai yau, Awwwwn Guyen na iya sadaukar da Komai nasa Akaina fa"


Tsaki Jesmine taja Ta kwashe Littafanta ta fita karatu, yayinda Su Reey suka zauna Da ita tana zuba Msu zance.....🎤.


Washegari ta tashi da zazzaɓi sosai, yau babu lecturer din safe gashi ta tashi da Ciwon Ciki wanda ke nuna alamun zata ga menstrual flow dinta a kowanne lokaci.

Kwance take sai Faman Juyi Take tana Rintse Idanu ita kadai tasan Yanda takeji.


Reeey ce Ta shigo da bokiti a hannu, Taje Shanyan Kayansu ne a waje ne dama


Ganinta a kwance yasata Saurin dire bokitin hannunta, ta ƙaraso wajen ta cikin Kulawa

Duminn hannu taji a wuyanta Hakan yasa ta sauke Ajiyar zuciya ta bude gajiyayyun idanunta tana kallon Reeey dake taɓa wuyanta

"Babe Are you sick?" inji Reey tana qara taɓa Wuyanta zuwa Face dinta


Lumshe idanu kawai Aeesh tayi batareda tace komai ba

"Babe Talk Meke Damunki?"

"Menstrual pain"

Ta Fada a hankali tana rintse Idanu


"Ayya Sorry Tashi Muje Chemist Mu siyo Magani ,Daga nan Mu siyo Kayan miya a Bakin Gate”

Yamutsa fuska tayi zatayi magana Reey ta girgiza mata kai alamun karta musa

"tashi mutafi"

Babu yadda ta iya haka ta tashi dakyar ta Yafa Mayafi tanajin kamar taita kuka.



Yawan comments dinku zaiyi determine cigaban littafin, ku zubo Comments yadda zan zubomuku flows of updates🤭🤭


Bintou ✍🏼

10th August

NAYI Gabas 🚶🏽‍♀️
[10/19, 9:09 PM] Bintou abdool: *_🫀🗡️WUƘA A ZUCIYA🫀🗡️_*

_(Bleeding Hearts)_


*027*

*_Say No To Drugs_*

Washegari ta tashi da zazzaɓi sosai, yau babu lecturer din safe gashi ta tashi da Ciwon Ciki wanda ke nuna alamun zata ga menstrual flow dinta a kowanne lokaci.

Kwance take sai Faman Juyi Take tana Rintse Idanu ita kadai tasan Yanda takeji.

Reeey ce Ta shigo da bokiti a hannu, Taje Shanyan Kayansu ne a waje ne dama

Ganinta a kwance yasata Saurin dire bokitin hannunta, ta ƙaraso wajen ta cikin Kulawa

Duminn hannu taji a wuyanta Hakan yasa ta sauke Ajiyar zuciya ta bude gajiyayyun idanunta tana kallon Reeey dake taɓa wuyanta

"Babe Are you sick?" inji Reey tana qara taɓa Wuyanta zuwa Face dinta

Lumshe idanu kawai Aeesh tayi batareda tace komai ba

"Babe Talk Meke Damunki?"

"Menstrual pain"

Ta Fada a hankali tana rintse Idanu

"Ayya Sorry Tashi Muje Chemist Mu siyo Magani ,Daga nan Mu siyo Kayan miya a Bakin Gate”

Yamutsa fuska tayi zatayi magana Reey ta girgiza mata kai alamun karta musa

"tashi mutafi"

Babu yadda ta iya haka ta tashi dakyar ta Yafa Mayafi tanajin kamar taita kuka.

Babu Chemist Din makarantar a kulle yake, Don Haka Dole yasa Suka Fita.

Dakyar Suka iya gano Pharmacy a bayan Layin saboda babu Inda Suka sani a Layin ,daga cikin Makaranta babu inda Suke Zuwa bayan nan.

Sun Tarar Pharmacist din na attending Ma wani, Sai Faman Zazzaga Bala'i take

"Haba Muhammad, kana Son Kashe Kanka ne?, Tun tuni na gaya maka Penta nada Illa a jikin Mutum ka ƙiji, So nawa kake So na Gaya Maka illar dake Tattare da Wannan Allurar?, so kake ka Kashe Kanka at ur Young age?, kana So ka Mutu ka bar Mahaifiyar ka ne?"

Shuru Pharmacist din Tayi, da Alama Tana jiran Answer ne daga bakin Wanda ta kira da Muhammad ɗin, Shuru ne ya Ratsa Wajen, Wuri Aeesh Ta samu Ta zauna ta kifa kanta akan Cinyarta saboda Irin Murdawan da Cikinta keyi mata.

Matar Cigaba tayi da cewa

"Dubi Gluteal Muscle Ɗinka!, ya ruɓe abin ba kyan Gani,Duk saboda Alluran nan, Gaskiya Ni AM afraid Daga yau Bazan Sake Yi Maka Allurar ba ,An sorry gaskiya bazanyi ba, kaje wani Gurin"

Wani irin Murɗawa Cikin Aeesh ya sakeyi ta saki Yar Ƙaramar Ƙara, Riƙeta Reey tayi Pharmacist Din ta dubesu Tareda Basu haƙuri don Da Layi sosai a gabansu,Daga Nan Aeesh bata sake jin Abinda Suke Fadi ba, Gabaki daya Ciwon Ya nannaɗe ta takoina, sosai Mutumin Ke bata haƙuri akan Ta taimaka tayi masa Allurar, Idan ta Hanashi To tabbas zai iya rasa Rayuwarsa.

Amma Firrr taƙi Amincewa, Daga karshe ma Banza tayi dashi ta cigaba Da attending ma wasu.

Layi na Isowa kansu ,Reey ta fada Musu Maganin da Suke buƙata, kai tsaye Matar tace Bazata siyar ba saida doctor's Prescription.

Side Bag dinta ta fiddo ta dau takarda Da biro, tayi Prescribing Drug din Ta miƙa mata Duddubawa Matar tayi Tana Yamutse Fuska

"Ba zaiyiwu na Baki maganin Nan ba,Sai likita yasa Hannu"

Id card dinta ta nuna mata

"I'm a student Nurse, colleague dita ce Batada Lafiya Gata can Please help Us"

Reey ta faɗi hakan tana Nuna mata Aeesh Dake Gefe tana Faman Murkususu.

"Madam Please Help us, Sister na har Suma Takanyi idan Abin ya motsa"

Tausayinsu Taji ta basu maganin, Reeey tamiƙa kuɗin chanjinta aka bata ta amsa tajuyo tana zura kudin a cikin purse dinta

"Firdausi don Kin hanani Allura ba Shi zai hana Naje wani Wurin ayi min ba, akwai Pharmacist dayawa A gari ba ke kadai bace"

Muryar Mutumin da Pharmacist ta Hana Ayi masa Allura ta doki Kunnen Reey.

Ɗagowa Tayi da sauri ta zuba masa Ido Tabbas Aareef ne, dama addictor ne?, Dan kwaya?, No wonder Ashe Shiyasa Ta tsaneshi.

Bata So Su hada hanya da Aeesh, tasan Idan Aeesh Taganshi Zance zai ɓaci, zata Nemi Tayi magana dashi, Kuma ita Fatanta a koda yaushe yanda Allah ya Rabasu Cikin sauki ya zamana Rabuwar su kenan ta Har Abada.

Cikin dabara Ta Raɓa Gefenshi Batare da ya Ganta ba, Ta kama Hannun Aeesh ,Ta tayar da Ita da sauri suka fito daga Pharmacy din Aeesh na Yatsine Fuska Saboda Azababben ciwon Cikin Da ya Riƙeta .

Zamewa Kasa tayi Tana Shessheƙar kukan Azaba.

Haƙuri Reey tayi ta bata tana Rarrashinta Cikin Tsananin TTausayawa , Burinta subar wurin Batareda Daya cikin su ya haɗu da Wani ba.

Da kyar ta samu Ta miƙe tana kakkame Hannun Reey, Hawaye na Fita a idonta.

wani irin Bugun Zuciya Tareda kamshin Turaren da Bazata taɓa mantawa dashi ba ya ziyarce ta a lokacin Guda.

"ya Salam ...!, Reeey Zan Mutu!" tafada ahankali Zuciyarta Na Tsananta Faɗuwa.

"Bazaki Mutu ba Besty, Bari Na siyo Pure Water a Shagon Chan Kisha Maganin ,Zauna anan ina zuwa”

Da Gudu Reey ta nufi Jerin Shagunan dake Facing Pharmacy din don Siyo Pure water,Yayinda Aeesh ta samu Guri ta zauna tana Cigaba da sauraron Bugun zuciyarta dake daɗuwa after each seconds.

Sosai Ƙamshin Turaren Ke Tsananta yana Kusantota, hakan Yasata Miƙewa Cikin Hanzari ta fara Bibiyan Ƙamshin Turaren.

Batayi auneba ji tayi ta bigi da abu wanda Daidai lokacin da mararta ya sakeyin Wani irin Murɗawa Da ƙarfi

"Ooush Allahna"

Ta fada tana Kama saitin Mararta da ya murɗa

Juyawa tayi a wahalce ta kalli mutumin da ta buge wanda yaqara gaba kamar bashi ta buge ba.

Ganin yayi nisa yasa ta sakin Ajiyan Zuciya a kasalance.

Chak Bugun zuciyarta ta tsaya Daidai lokacin da wani abu yayi Flashing Cikin Brain dinta

Dagowa Tayi da Sauri ta Maida Dubanta ga Mutumin da ta buge wanda a halin yanzu Yayi nisa, ya kai Inda ake Parka Ababen hawan Costumers Yana Shirin Tada Machine dinsa.

Wani irin Bugawa zuciyarta ta sakeyi a karo na Biyu

Zumbur ta miqe tsaye ta Kwala masa Kira da Karfi

"Sadauki.....!"
Banza Yayi mata, saida ta sake Kwala masa kira a karo na biyu sannan ya tsaya da Tada Machine dinda yake Shirinyi, a hankali ya waigo ya zuba mata ido.

Tun daga nesa Juwairiyyah ta hango Aeesh tana Shirin Ƙarasawa Gareshi.

Da karfi Ta Kwala mata Kira da ta dawo amma Ina Kunnuwanta sun dode, idanunta sun rufe, hankalinta ya tashi, babu abinda take gani a idanunta sai fuskarshi, Tuni ta nemi Ciwon Da takeji ta rasa.

Tana Karasowa Wajenshi Ta fashe da matsanancin Kuka mai ban tausayi

Cikin Muryar kuka ta Ambaci Sunanshi

"Sadauki n..."

"Karki ƙara Kiran sunana"

Ya dakatar da ita fuska a murtuƙe

"Menene?,Dama Kin sanni me?, Idan Ma kin sanni kisa a ranki baki Sanni ba,karki Karajin cewa Kin Sanni a rayuwar ki"

Wara idanu Aeesg tayi in out most shock

Taji gabanta Ya bada Wani razananniyar sauti, wani katon Abu ya taso ya Tokare mata maƙoshi.

Wani abu Reey taji ya soki zuciyarta nan take ,Haushin Shi Ya kamata.

"Aareef Ka saurareni don Allah"

"In saurareki inji me?, Inji Kinyi Aure Kinada Juna Biyu?"

"No Arif A Halin yanzu banida Aure!"

''karya Kike Jibeki kin Rame sosai, Ga yanayinki Sak na Mai laulayi Niba Wawa bane Nasan Abinda Nakeyi"

"Ba Ramar Ciki bane, Chanjin Rayuwa ce"

Ta fada da Karfi, Wanda hakan Yasashi Saurin kawar da Dubansa Daga Gareta yana Huci

" Ban Tsara Rabuwa dakai ba tun farko, Aure ne ya So ya rabamu, Amma Wlhy A duk Bugu na numfashina kaine A Zuciyata soyayyarka itace take juya Ragamar Rayuwata"

"Ki fice min da Gani"

Ta daka mata tsawa yana Kashe Machine Dinsa

"Nima zanso na Fice don a halin Yanzu jin Zuciyata nake kamar zata fice daga Mazauninta, Amma AREEF ka fada Min Me nayi maka da nayi deserving wannan Terrible Look din?"

Saukowa Yayi daga Machine din ya Zagayo Gabanta a fusace

"Terrible Look?, kinci sa'a Terrible Look Kadai na baki , A'isha Wlh idan Baki ɓace daga ganina ba Sainayi mugun baki mamaki ,na ce Bana Sonki Bana Ƙaunarki Kuma ina Rokon Allah da ya Shiga Tsakanina Da mayaudariya"

"AREEF Niba Mayaudariya bace"

"Tafi Ki bani Guri"

Hadiye abinda ya tsaya mata a wuya Reey Tayi cikin Fusata Ganin Yanda Yake wulaƙanta Aeesh bigairi dalil

"Arif Bazan Tafi ba, ba Yaudarar ka nayi ba, ba yaudarar ka nayi ba, Tilasta min Yayi Ban taɓa Sonshi ba Ni kai nake so Har yau har gobe kai kadai nake so AREEF ina Son ka"

"Keh Nace Ki bace Min Da Gani"

"Ari...."

"Bace min Da Gani"

"Please Hearme ou..!"

Bata ƙarasaba Taji Saukar Wawan Mari bisa Kuncinta.

"Karki Ƙara cewa Kina Sona Kiyi Rayuwarki Ni na Riga na Cireki a Nawa Rayuwar"

Sosai zuciyar REEY tayi zafi, who on earth is this guy?, me Yake Takamada shi da har Zai iya daga hannu Ya Mari mace?,
Is he this heartless?.

Wasu Siraren Hawaye Suka gangaro akan Kuncen Ta

" AREEF Idan Marina shi zaisa Zuciyarka tayi sanyi ka fahimci irin kaunar da nake maka na yarda kayi ta marina har saika huce tak...."

Tassssss !, Ya sake Kifeta da Wani Razananniyar Mari Wacce tafi Ta farkon...!

Bai ida Sauke hannunsa Ba yaji an wankeshi da Zafafa bibbiyu a ko wane Kunci nashi

"Kai Wane irin Mara Imani ne?, wane Irin zuciya Gareka?" Tafada cikin tsananin 6acin rai

"Kai ShashaSha Ne baka San Ciwon Kanka ba don Kayi Sa'a Zuciyar ta na Kaunarka sai Ka rinƙa Wulaƙanta ta yanda Kaso?, A tunaninka Hakan Shi zaisa Ta Rabu Dakai?"

Idanun ta Gaba Ɗaya sun Sauya Launi sbd tsananin Bacin Rai, Ga Hawayen Da Suka taru a Idanunta.

Shima AREEF kallonta yake cikin tsananin 6acin rai wanda har kana ganin yanda chest dinshi ke sama da qasa ta transparent White Yardin da Ya saka.

"Soyayya ba Rayuwa bane haka Ƙiyayya ba Hauka bane, Idan Baka Sonta Gaya Mata zakai Ta yadda zata Fahimta, Ka dauka Dukan Mace Shi zaisa Namiji Ya samu Abinda Yake so ,Ko ka dauka Marin da Kayi mata Shi zaisa ta Rabu dakai?"

Rintse Idanunta tayi Da Karfi, Hawayen da Suka Taru a Idanunta suka samu damar Gangarowa Saman Kuncinta

"Soyayyar da Aeesh Ke maka ta zarce Misali Dawowan Mu makarata ne yasa Na tabbatar da hakan, a Kullum Akalla saita Ambaci Sunaka fin Sau Biyar,burina a kullum Allah ya cire Mata Kai completely daga Rayuwarta"

Hannu tasa Ta Share Hawayenta

"Banga laifinka ba don Ka mari mace, What did you Expect From a drug taker? ,Banza Dabba Psychiatric Patient Dan kwaya kawai"

Da karfi Reeey kama Hannun Aeesh tana Huci hawaye na Cigaba da Kwaranya daga Idanunta, Itama Aeesh Kuka Takeyi sosai .

a mugun fusace ya haye Machine dinsa ya bashi wuta Shima ya bar Gurin a 360.

Wasu Siraren hawaye ne suka sake Zubo ma Aeesh, Tausayin AREEF ɗinta ya kamata Tasan Yanda yakeji a zuciyarsa Kwatankwacin Yanda takeji a nata zuciyar ne, Ga Reey ta Ƙara masa Zafi Da wanne zai ji?.

Kallon Ƙurar Da ya tafi ya bari tayi, cikin Shakakken Muryarta tace

"SADAUKI please Karka Tafi ka barni"

Chak Reey ta dakata , ta dubeta a fusace, ganin Yanda Idanunta Sukayi Daga Daga Da hawaye yasa Taji Jikinta yayi sanyi, tausayinta ya kamata

"Besty, meya faru? Meyasa kike kuka?"

Wasu hawayen ne suka qara gangaro mata

"Marin Da yayi Miki ne ko Barinki da yayi?"

Saurin fadawa jikin Reey tayi ta rungumeta gamm tana kuka sosai

Sosai Hakan yasake hargiza ta, Haushi da Tsanar AREEF ya sake darsuwa a Zuciyar REEY Ji tayi kaman Tabishi ta cigaba da Zabga masa Mari har Sai Yayi Hawayen Shima.

"Yace fa baya Sonki, Ya tsaneki ,ki Cire Shi a ranki Duk namijin da Zai iya daga hannu Ya mari mace wannan Ba mijin Aure bane"

Cikin sauri Aeesh da ke Kuka duk jikinta na rawa ta dakatar da ita

"Karya yakeyi Yana sona, AREEF Na sona "

"Keh Ki dawo hayyacin ki baya Sonki"

"Besty Ya tafi....,Ya tafi kenan?, ya tafi bazai sake dawo ba?,Bazan sake Ganinshi Ba?"

Sai kuma ta fashe da Matsanancin Kuka a fili mai ban tausayi

Kuka Takeyi sosai hakan Yasa Hankulan Mutane karkato wa Garesu

“Yar Uwa Me ya faru ?"

Wata mata mai goyo, Wacce tazo wucewa Ta tambaya Ganin Yanda Aeesh Ke rera kuka mai ban tausayi.

Murmushin Yaƙe Reey tayi
"Babu Komai"

Ta amsa Mata a takaice Sannan taja hannunta Suka bar wurin,kuka takeyi sosai Har suka kai Makaranta bata damu da tsirarun Mutanen dake Tsayawa suna Tambayanta Dalilin Kukanta ba.

Reey Haushi Ya Cikata kaman me?, Babu abinda yafi qonamata rai kamar yanda Take Kuka akan Namijin Da bai damu da Ita ba, Yanzu Ya gama Wulaƙanta Ta, Amma Burinta bai wuce ta koma gareshi Ba.

Fasa Siyan kayan Miyan da Reey tayi niyyar siya Tayi , Suka kama Hanyar Hostel Gadan Gadan

"Keeh....!"

Wata Murya ta dakatar dasu ta baya, Basu Tsaya ba, Saida Suka Sakeji an ambaci Sunan Daya daga cikinSu wato Aeesh

"Keh Zo nan"

Muryar Saleem Ta sake Dokar Kunnenta a karo na Biyu

A tare Suka juyo Suna Kallonshi, Sam Reey bata gane shi ba don haka sai ta nuna kanta Cikeda Mamaki tace

"Mu...?"

"Ba kuba Ita!"

Sai a lokacin Ta gane Shi sakamakon zare Eye Glasses Ɗinsa da yayi

Duban Aeesh dake Hawaye tayi ,Cikin Kankanin Lokaci tsoro ya bayyana a Fuskar ta, Ita kanta Reey Tsoron saleem takeyi Sosai bata taɓa shiga Komarsa ba, Amma a Iya zaman da Sukayi tare a Asibiti ta gane Koshi waye, Ba wani hankali ya cika ba,Kai tsaye yake Aiwatar da Komai nasa batareda Yayi dogon Tunani ba ,Kuma babu wanda Ya isa Ya sashi Abinda Baiyi Niyyar Aiwatarwa Ba, Kaman Yanda Babu wanda Ya Isa Ya Haushi hakan ne Yasa Yayi Baƙin jini Sosai a Asibitin Ya zama Kowa Shakkarsa Yake kama daga Kananun Ma'aikatan Izuwa Manyan Ma'aikata.

Guntun Ajiyar Zuciya ta saki, Ta dubi Aeesh dake Goge hawayenta Hannayenta na rawa

"Jeki ...."

"Ko Bazaki Zo bane Ni inzo?"

Muryarsa Ta sake Dakan Kunnenta a Karo Na Uku

Cikin Tsoro ta daga Ƙafarta ta iso Gareshi.

Zaune yake a mazaunin Driver Gabaki Daya Ƙofofin Motar a buɗe Suke, Gabaki daya Wurin Ya Gaure da Daddaɗar Ƙamshin Turaren sa.

Tsayawa tayi tana Kallonsa, hankalin Sa gaba daya Yana Kan Wayar Hannunsa Sai daddannawa Yake Kaman Bai san Da tsayuwarta ba, kaman ba Shi ya kirata ba.

saurin janye idanunta tayi daga Kansa cikin takaici ga k'amshin turarensa ya gallabeta, Ga ciwon Mararta Da Ta Dawo Mata Sabo, Ranta Babu dadi, amma takula mugunnan soyake ya ƙara Ɓata mata Rai.


Kamar zatayi kuka ta gaidashi, Murya Chan Ƙasa Ƙasa tace

“yaya Ina wuni"

Shiru yamata, saida ya mula dan kansa sannan ya Ɗago Fararen idanunsa ya zubesu Akanta

“Daga Ina?” yayi maganar yana Kumburarren Face dinta da Red Eyes dinta da Yasha kuka.


"Munje Siyo Magani ne"

Ta fada kanta a ƙasa

"Maganin Me?, ina Maganin?, Waye babu lafiya?"

Ya Jero mata Tambayoyin Duk a lokaci Guda

Ta rasa Amsar Da zata Bashi Sai Ta Sunkuyar Dakai cikeda jin Nauyin Tambayan nasa

Tsawa Ya daka Mata

"Keh nake Tambaya Ko bakida Baki ne?"

"Ni ...nice Dama Babu Lafiya"

Ta bashi amsa a takaice

"Ina Maganin?"

"Yana Gun Juwairiyyah"

Ɗagowa Saleem Yayi Ya dubi Reey Dake Tsaye A dan Nesa Dasu Hannunta Riƙeda leda ko ba'a Gaya Masa Ba yasan Magungunan

Please Login or Register in order to submit comment