Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zahiri?, take a look at them , They're Both naked "

Juyowa Abba yayi ya dubesu, ganin haka yasa Ashman ya sunne Kai a Kunyace, wannan abu da me yayi kama?

Kilingin🔔🔔 ƙarrawar Kan Abba ya buga, abin yazo masa kaman daga sama, Cikin Zazzare Idanu ya haɗe yawu da ƙyar

_da gaske Ashman Yake so yake ya kashe shi kafin lokacin sa'

Lumshe idanunsa yayi da kyar ya tattaro jarumta ya yanama kansa, Ya dubi Saleem Fuska a Daure yace

"Banaso in sake Jin wannan Kalmar ya fito daga bakin ka, Zargin Aikata zina ba ƙaramin Abu bane, wannan maganar a barshi anan, Ke Yathai Kaita dakinki ki dubata ki tabbatar da Abinda ake zargi...."

"Dad..."

Abba ya daga Mishi hannu

"Dakata saleem , A dangin mu babu mazinaci Kalaman ka basu isa Su tabbatar min da abinda kake zargi ba don Ni ko alama ban ga me ka gani kake jifansu da wadannan Munanan kalaman ba..."

"Dad are you taking His back or what?"

"No am not, but Am trying to secure the family Dignity, don Haka bana Son Sakejin Komai daga gareka Get lost ..."
Ya dubi Aeesh yace

"Keh Jeki ɗaki, innarki zata zo ta dubaki"

"Dad...."

"I said Get lost ka ɓace min da gani..."

Maryam taja Hannunsa ganin Yana shirin huce Fushinsa akan mahaifinshi, cikin Takaici tace

"Saida safe Abba"

Ba don yaso ba sai don shaukin da tattausar hannunta ya sanya masa, Yabita suka tafi Yanajin Zuciyar ta kaman zata faso ƙirjinsa.

Suna wucewa Abba ya maida Dubansa Garesu fuskar nan kaman an aiko masa Mala'ikan mutuwa Yace

"Kaf fadin Duniyar nan Sun san Kaza ke sassaka kwai ,Amma Daga kazar har kwan duk mallakin Mu ne, haramtattu ne a gare mu, Muna iya sarrafa su a duk Lokacin da muka ga Dama!"

Daga nan bai sake cewa komai ba yayi tafiyar sa ya barsu tsaye Cikin takaici.

Dubanshi Inna Yathai Ranta a ɓace tace

"Ashman Da gaske Kayi mata fyaɗe"

Sunkuyar da kansa yayi, Muryar matan na cigaba da Sauya Abubuwa da dama cikin Jikinshi, muryarsa ƙasa ƙasa yace

"Da amincewar ta"

"Ban gane ba"

"Ba fyade nayi mata ba, da son Ranmu muka aikata"

"Ashman ba haka kake ba, Nasan Bazaka iya aikata wannan mummunar Ta'asar ba ,fada Min Asalin Abinda Ya faru"

Baisan Meyasa ba, a duk lokacin da Ya haɗu da wannan Matar Yanajin wani iri ,wani irin Girman Ta yake gani yanajinta har cikin zuciyarsa ,tausayi take bashi sosai

"Ka yarda dani....ka gaya Min Asalin Abinda ya faru"

Ya tsinkayi muryarta tana tambayansa a karo na biyu, kasa jurewa yayi Hawaye suka digo masa Muryarsa a matuƙar sanyaye yace

"Inna Matata ce ihkty , Baffa ne yadaura min Ita a ranar da zai bar Duniya ”

A takaice ya bata Labarin yanda akayi, hawaye na tsiyaya daga Idanunsa, ya dora da cewa

"Na kasa Samun Ƙwarin gwiwan da Zan gaya ma Wani, ina tsoron Kada na fada a rabani da ita"

Ya ciji Lower lips ɗinsa , Slowly Hawaye suka Gangaro saman Kuncinsa

"I don't know why, but I feel my Secret is safe with You "

Ya ja Numfashi Yana sake Bama Hawayen damar gangarowa

"Bansan Me yasa zuciya ta zaɓe ki ba, amma Don Allah ki fahimce Ni"

Murmushi tayi, irin wacce bai taɓa ganin tayi Makamancinshi ba tun bayan zuwan ta gidan

"Kayi Abinda ya dace, na fahimce ka Ashman"

Kallon mamaki yayi mata, she trusted him even without presenting Any reason !, Lallai Akwai wata abu na musamman dake tattare da ita.

Amma Dukda haka sai ya tsinci kansa da fadin

"Please ki riƙe min wannan Sirrin"
Ta gyada masa kai tana cigaba da Murmushi

"Dukda Alhaji Mahaifinka ne ,Nafika sanin halin shi, zai iya yin komai domin Ya rufe wannan maganar, domin Kuwa sarai ya Gano Abinda Ka aikata, duba da yanda yanayinsa Ga sauya Lokaci Guda bayan ya kalleku, Amma dalilin sa nayin hakan ne bamu sani ba*

Cikin mamaki Ashman yace

"Ya akayi kika sani?"

Kai tsaye tace

"Yana Son Aisha!, Shekaruna 15 da Fara aiki a karkashin shi Nasan komai dangane da Gidannan na ɓoye da Zahiri, babu Abin dake ɓoye a ido na"

Ajiyar zuciya Ashman ya sauke yasa bayan hannu ya share hawayensa,tabbas Shi shaida ne akan hakan , Inna Yathai Ta fisu sanin Komai na gidan Don babu inda bata shiga, Tana zaune a gidan ne a matsayin mai Taya Goggo Aiki, Amma babu wanda bata Wahala dashi ,hatta su Baffa da Matarsa da 'ya'yansu.

Cikin Marairaicewa yace

"Inna Don Allah Ki min alƙawarin boye sirrina"

Tayi Murmushi tace

"Nayi , ka yarda dani ,Bari in bi bayansu Karsu ga na daɗe"

"Please take care of her"

"Tho Saida Safe, Ka kula da kanka " ta fada yayinda Take juyawa Izuwa ciki.

Tsayawa yayi yana Dubanta har ta shige, Ji yake kaman an cire masa wani ƙusa da ya daɗe yana Chacchakar zuciyarsa, Tun daga Ranar da Baffa Imam Ya daura Aurensa Da Aeesh Yakejin wani Abu mai Nauyi ya Toshe masa Zuciya rashin bayyana wa wani yasa Abin yake caccakar sa, amma a yau Sai yaji wasai, bayan ya bayyana ma Inna Abinda ke damunsa.

Shi kanshi Mamaki yake Dalilin da yasa ya kasa Gaya ma kowa sai wannan Matar, Ƙasƙantacciya cikin Masu Aikin Gidansu.

Abba ya kasa Natsuwa ya kasa Tsaye ya kasa zaune sai safa da marya yake yana Sharce Zufa.

Inna Yathai na shiga ya Tsareta da faɗin "me kika tsaya yi tun ɗazu?" ,Tace "Ba komai" , ya harareta sannnan Yace "Nasan ya faɗa Miki Komai, a yanda naga Kun jima kuna Zantawa nasan bazai Ɓoye Miki komai ba"

Murmushin Takaici Inna tayi tace
"Haba Alhaji me kake tunanin zai gaya min?,bayan da kanka ka ƙaryata Saleem!, Ko kana zargin Wani abun ne?"

"Yathai Karki raina Min Hankali ,Nasan da bai Fada Miki Komai ba Bazaki shigo kina Murmushi ba"

Yayi maganar cikin ƙasa Da murya Gudun Kada wani ya jisu, Inna ta Gyada kai tace

"Tsoron me kake ji MALAM KHAMEETH?, kodai fargaban ka kada Digon Ruwa ya fasa ƙwai kake yi ne? ,Tho Kwantar da hankalinka koda ya fasa ƙwan baza'a Kirashi da shege ba don saida Aka tara shaidu Aka shafa fatiha tukunna"

"Ya gaya Miki Komai...?"

"Offcourse ,And... Naga Alama Kaman kana daga cikin Shaidun da Suka Shafa fatiha Ko?, Don It seems Like You Already Know Anything ”

“idan Kika sake Wani yaji wannan Maganar Sai na kasheki"

Takowa tayi Gabanshi ta kalleshi ido cikin ido tace

“Naseer Wane Kisa Kuma bayan Wanda Ka riga Kayi Min?, ko ka taɓa ganin Inda aka kashe Matacce Ne?,Idan akwai Ka gaya Min , And Karka Manta Rayuwarka Gabaki ɗaya a hannuna take, kuskure kadan Zan iya tarwatsa Rayuwar ka da ta Mabiyan ka gaba ki ɗaya...!"

Daga Nan bata Jira abinda Zai ce ba Tayi gaba Tana Sakin Sihirtaccen Murmushin da ita kadai Tasan Ma'anar ta, ta barshi tsaye Cikeda Takaici.

Kai tsaye dakin su Qawwamah ta nufa, Qawwamah ta riga tayi bacci ,sai Aeesh Dake zaune ta kame waje guda Tana ta faman kuka kaman ranta zai fita, Zama tayi a Gefenta cikin Nutsuwa tasa Hannu ta Ɗago Fuskarta data ɓaci da Hawaye ,cikin Kuka Aeesh tace

“inna Wlhy Bansan ya Akayi na Biye mishi ba, Ban bishi da Niyyar aikata ba dai dai ba..."

Maganar take a matuƙar Tsorace, Numfashin ta har wani Sama da Ƙasa yake, kai da ka ganta zaka san a mugun Tsorace take ,ta kasa Nutsuwa tun bayan Abinda ya faru Hankalinta duk yabi ya tashi.

Inna taji Daɗin kalaman ta sosai, Ta saki Murmushi tace

"Kiyi haƙuri Ummi, Tunda Bada Niyyar Aikata hakan Kika bishi ba, ki dauka ba Mummunar Alaƙa ce ta shiga Tsakanin Ku ba, ki sa a ranki kaman Da Mijinki Kikayi tarayya"

"Inna Taya Zan Iya hakan bayan duniya ta shaida babu Aure a tsakanin mu?"

Inna ta Dafa Kafadarta tace

“Ba sai duniya ta shida babu Aure a tsakanin ku ba, ke da kanki zaki yarda da kanki tukunna sannan Ki samar ma kanki farinciki karki Jira sai duniya ta Shaida ba"

"Inna Idan Duniya bata shaida ba, ana nan Fa gidan wani zani Kuma dole sai ya gane Illar da yayi Min"

Inna ta Girgiza kai tace

“baki dau Shawara ta ba Kenan, ke da nace ki dauka mu'amalar da Kuka aikata tare tsakanin ki da Mijinki ne ,taya Kike tunanin Mijinki Zaiyi Tunanin Anyi miki Illa bayan ya riga da yasan Komai?"

Shuru tayi wani bangare na Zuciyarta na neman Amincewa da Kalaman Inna ,Inna ta cigaba da cewa

"Karki tsaya tunanin Sai wani ya yarda dake a cikin wannan Rayuwar ,ki yarda da kanki Sannan Ki Bama kanki ƙwarin Gwiwa, wannan Ƙwarin gwiwan shi zaikaiki ga matakin Nasara A Rayuwa, Rayuwarki takice ke kadai Masu tunanin Wani abu Akanki bazasu baki tasu ba idan Kika kashe kanki da damuwa Akan su”

Ai kam taji daɗin kalamanta, Kuma sosai Kalaman nata suka shige ta Har tanajin cewa koda Ace duk duniyan Nan ne akanta Sun shaida Lokacin Da Ya Abin ya faru bazata damu ba don Ita kadai tasan Abindake ɓoye cikin labarin ta.

Ta share hawayen da suka zubomata, ba tare data kalleta ba tace

, “Na haƙura inna, amma dan Allah ki rufamin asiri, kiji tausayin maraicina ki rufa Min Asiri ko dan Kare mutuncina, kalamanki itace mafakata ta ƙarshe da zanyi alfahari da ita Ko duniya ta gano abinda ya faru, shaiɗan ya riga lulluɓe mana ido ya sa na Bayarda kyautar Yancina ga wanda Baisan darajar ta ba"

Wasu sabbin hawaye suka sake gangaro mata

"Kuma ba laifin sa bane laifi na ne, Ayanda Muka taso Bana damuwa idan ya taɓani, Rungume Rungume da wasu Abubuwa kam Bamu Maidashi komai ba, Sometimes Shike kwaɓata akan wasu Abubuwan Dukda nasan haramunne a addininance,sannan cutarwace a garemu, wannan ba shi bane tarayya kamar yanda yake ga wasu masu sauya Al'ada, hakan ƙoface kawai ta saɓon ubangiji, wanda Hakan ce ta kasance Ƙofar Fasiƙancin da Muka aikata"

Cikin Kukan da ya fara fin ƙarfinta ta cigaba da faɗin

"Da ace ina Hanashi a duk lokacin da Yayi yunƙurin kama hannuna a koda yaushe ,kuma nima bana Riƙe nasa Da tuni Matsala bata Ginu ba, daga wannan ne matsalar ta fara, tun Bansan Komai ba har na san cewa Haramun ne, Amma sabo ya hanamu dainawa ,tun Yana kwaɓata akan wasu Abubuwan har shaiɗan ya ƙawatamasa yafara jin daɗi, Inna Yawan Gamayya da Junan da mukeyi shine Matakin farko na Samar Da sha'awarsa Mai ƙarfi a gareni da haka muka kai matakin sumbata wanda Anan ma nice na Fara buɗe masa wannnan damar, wacce ta kasance makulin buɗema shaiɗan ƙofa da komai na baɗala ya Wanzu a tsakanin Mu, duk takatsantsan da nakeyi saida Na kaimu ga aikata zina"

Idanunta Cikeda hawaye ta sake fashewa da wani kukan mai ƙarfi

”Wa'iyazubillah Inna Nasan cewa namiji da mace duk hukunci ɗaya garesu wajen Allah idan suka aikata zina, amma a zahirance ta rayuwar duniya mace itace ke fara ƙasƙanta a idanun al'umma makusantanta dama na nesa da ita, domin itace ke ɗaukar ciki, itace wasu almomi ke fara bayyana a gareta kamar yanda Kuka gano mu batareda na furta ga kowa ba, na rasa mutunci na, na ƙasƙanta mutuncin zuri'ar mu dama ahali gaba ɗaya ,Ina Matuƙar Tausayin Kaina dana Ammie idan ta gano Abinda ya wakkana, Tasha Jan kunnena Akan alaƙar mu da Akhy Amma nakiji kaicona Meye Amfani na a wannan Rayuwar"

Kuka mai ƙarfi yaci karfinta, Cikeda tausayinta Inna ta jawota Jikinta ta Rungume tanajin zafi a Zuciyarta


"Abinda na aikata Zaiyi ta bibiyar rayuwata har ƙarshen zuri'a ta, Ni za'a fara aibantawa kafin yaya Aash, babu namijin Da zai yarda ya Aureni a haka...!,, ko ina na Gifta Ni za'a nuna ma ƙyama, Inna Inada rauni sosai, Ance Kome namiji yayi Ado ne na gani Akanshi yau, Na tabbata Yau kwanar farin Ciki Zaiyi yana Murmushin ya Kwashi banza, Kuma da Gaskiyar sa yaci banza tunda ba SADAKI ya biya ya samu ba, raino yayi ya kwashi Rabonsa Abin tausayi ƴa mace na fuskantar Matsanancin matsalolin da Saɓani koda ace fyaɗe akai mata"

Ta sake ƙanƙame Inna cikin kuka har tana shiɗewa Murya a dishe take cewa

"Inna bazamu iya ma Allah Wayau ba duk zina sunanshi zina indai Ta bayan fatiha aka aikatashi ,inna banida ƙarfin Zuciyar Juran Wulaƙancin duniya Akan wannan Lamarin , Yanzu Wane kallo AAREEF Zaiyi Min in ya gano na Bada Kaina ga waninshi?”

Inna taja wani bahagon numfashi saboda tausayi da Aeesh ta bata sosai,da ace zata iya da ta sanar da ita Gaskiyar Zancen Amma Fada mata ba zai kawo da mai ido ba, zata jira har ranar da Ashman zai sanar da ita da kanshi, yanda take kuka sai ta kumajin tausayinta na Ratsa ko ina a ranta, murya a sanyaye tace

“Na fahimceki Ummi, insha Allah Bazaki wulaƙanta ba, da sannu zaki fahimce Ni,,Sam babu Laifi ga Abinda Kuka aikata”.

Sauran hawayen da suke maƙale a Idanunta suka zubo.

"Inna A ina Kika taɓa ganin Zina ta zama abin alfahari?"
Tayi maganar batareda ta Ɗago ba

Inna Ta saki wani murmushi tana sake Rungume ta cikin jikinta ,a hankali ta furta.

“ummi zanso Ki san komai ,Ko na huta da wa'azinnan”

Dagowa Aeesh tayi Murmushin Yaƙe ne ya suɓuce mata.

Miƙewa inna tayi ta haɗa Ruwan zafi, dakanta ta Sake gasata a karo na biyu bayan gashin Ashman yayi mata, wannan Karon taji daɗi Sosai, Cikin Lallami da lallashi Inna take Kwantar mata da Hankali har bacci ya dauke ta.

Ashman Na Shiga Gida kai tsaye dayan Part ɗinsa wurin hutunsa ya nufa, ko Kallon Part ɗinda Deejah take Baiyi ba , ya fad'a kan gado cikin tarin k'uncin zuciya da zafi haushin kanshi da kanshi yakeji tunda ya kasa haƙuri ta fara sanin Matsayinsa a Wajenta tukunna,Gashi yaja ma kansa yarinya ta rainashi gaba d'aya sai yaji ya tsani kanshi da kanshi fuskar sa na kallon Sama cikin sanyi kuma a bayyane ya ke cewa

"Baffa kayi hak'uri ka gafarceni, na kasa riƙe Amanar da ka bani yanda ya kamata , Baffa bazan sake yin abinda zai bata mata raiba insha Allah nima zan sata farin ciki,Kamar yanda ta sani".

A ranar Ko Rintsawa baiyi ba, Raya daren yayi yana miƙa Godiyar sa ga Allah Tareda roƙon Allah ya sauƙaƙa musu Lamarin cikin sauri, Tun Deejah na jiran dawowanshi har barci ya kwashe ta, dama a gajiye take ta kwaso hanya ,a ranar baccin Baƙinciki tayi mai Kice da Ƙunci.

*MARYAM*
Suna Kaiwa Part dinsu ta saki Mai Hannu, sai yaji kaman ta zare Jijiyoyin Jikinsa ne daga Jikinsa bai so ya rabu da tattausar Hannunta mai daɗin Laushi ba, how he wished Yaso ta cigaba da Riƙe hannunsa har Ƙarshen Rayuwar su.

Tsaye yayi yana kallon Hannunsa da ta bari on Air Har ta Shige dakin ta bai sani ba, a hankali ya ɗaga hannun ya kai hancinsa ya shaƙi daddaɗar Ƙamshin da ta tafi ta bar masa.

Ɗagowar da Zaiyi yaga babu ita, Dakin ta ya bita, amma Saidai kafin ya iso har ta garƙame ƙofar ta ciki.

Tunani yayi ko ya dauko Spare key ne ya buɗe ƙofar?, Sai kuma ya tuno yarjejeniyar su,Bai kamata ya tarwatsa Alƙawari a ranar Farko ba, yin hakan zai ɓata Alaƙarsu,ina Laifi Washe Gari? .

Cije Lips ɗinsa yayi a sanyaye ya juya yayi nasa Dakin Cikeda zafin zuciya , har yanzu abinda ya gani dangane da Su Aeesh ya kasa Goguwa a idanunsa, a ranar kwanar baƙin ciki yayi Yana tunanin yanda akayi Kwado yayi masa Ƙafa, ya kuma dau Alwashin yanda Aash ya ɓata masa Budget ya sashi Kuka a gaban Mata sai ya sashi Kuka a gaban Al'umman duniya Gabaki ɗaya😬, Sai ya maida Aeesh dakin ta yaga Ubanda ya isa ya Hanashi.

Maryam na shiga Dakin ta ta hango Wayarta na suwwa, tasa hannu tayi Sliding ta Kara a Kunne ZEEYK ne

"Hello Yaya na"

Wani irin Numfashin Relief Ya saki kana ya ce

"Princess Are you okay?"

Ta narke Murya cikin Shagwaba tace

"Am totally Not...!, Am not ,Nide gaskiya Gaskiya na fasa kazo ka kaini gida Bazan iya ba😭"



"What Princess!, Kinsan Me kike cewa kuwa? "

"Eh Nide gaskiya Bazan iya ba tsoro Nakeji, ina kama da Ummi na abu mai sauƙi ne ganoni a gare su, Nide Yanda Nake Gani Just do them Favor, revenge can't never Bring The dead back"

"Kehhh....!"

Ya Daka mata tsawa

" Kinsan Me kike fada ?, Are you Out of your mind?, You're Mentioning Favor as if Kazar gidanku suka yanka !, You'll show mercy to an enemy? The People Who betrayed our trust"

Ya Dan yi Shuru Yana panting

"Mercy is for the weak people (Alfarma ta masu rauni ce) , Princess You're Pathetic...!, Listen To me if you're determine To prove Yourself Weakling I should cast you out!, I shouldn't Bother about You Anymore, Do As you wis..."

Diffff ta Katse wayar saboda Kukan da yafi Karfinta, sai taji Rasuwar mahaifiyarta ya dawo mata Sabo, tasha kuka sosai a ranar Raba dare tayi tana Mata Addu'an Samun Rahma inda take, Kuma Allah ya gaggauta Tono asirin AzAluman da suka raba 'ya'ya da uwa, kuma Suka saka cuta a jikin Yayanta 😭, da taji ƙwarin gwiwan Cigaba da Zama a gidan Don Bankaɗo miyagun Sai taji ta karaya saboda Abinda ta gani a yau Dinnan Daga Shigowar ta.

Washegari , bata yarda tafito daga dakinta ba saida ta tabbatar yabar gidan gabadaya ta yar Windownn Ɗakinta ta hango fitarsa ta waje.

Sai a sannan tasamu kwanciyar hankalin fitowa don gyara Gidan ganin Yayi ƙura.

Saida ta share koina, ta goge, ta kakkaɓe ta kunna Burner ta saka turare sannan ta fada Bathroom Tayi wanka, ta shirya cikin Sabuwar Atamfar ta wacce ɗinkin ta dace da Kalar yadin, as usual wannan Karon Ma Daurin ture kaga Tsiya akayi , sannan tashiga kitchen don samarma kanta Breakfast.

Cikin Kayanda aka kawota dashi Ta dauko Kayan hada Coffee ta haɗa Sannan ta fere Irish potatto ta Yanka ta fara suya ,tana cikin suya taji wayarta na suwa,hannu daya tasa ta amsa kiran tare da manna wayar a kunnen shi, shiko ZEEYK yana jin ta daga ya sauk'e numfashi tace,

"Princess fushi kikeyi da nine?
toh kiyi hak'uri kanwata ki gafarce ni, I yelled at you yesterday."

kai maryam ta Girgiza tare dasa tafin hannun ta ta share guntun hawayen da ya taru a Idanunta, tayi murmushi mai d'an sauti sannan tace,

"In dai zanyi fushi da yaya na kenan zanyi fushi da mutanen duniya baki ɗaya yaya na ni zan nemi gafararka ba kai zaka nemi nawaba ka gafarce ni Yaya na, I was rude yesterday Am sorry karkayi fushi dani".

murmushi yayi jin dad'in Maryam batayi fushi da'shi ba sannan yace

"Ni bakiyi komai ba na yafe miki,Kawai dai ban ji daɗin furucinki na Jiya bane and now Komai Ya wuce, kema ki yafe min sannan kuma Ki taya Ni Bama angonki haƙuri na Ɓata ran Amaryarsa a Ranar farko"

dariya Maryam tayi tace
" kai yaya babu laifin da Aka masa kamata yayi ya bamu haƙuri, Ya baroni daga Gidan Su Mama ya kawo Ni nan, da ina gida da Yanzu ina Gindin Murhu Ina dafa Kaji".

murmushi yayi yace,

" Princess da kina kusa dani da sai na rangwashe miki kai na kuma matsemaki kunne tunda bakijin magana".

dariya Maryam tayi sosai dan taji dadin hucewar da yayi ,Shima haka ,ko kaɗan baya Son Ganin ɓacin Ranta Jiya da Ƙyar ya iya bacci yana Tunanin Halin da ya sakata Yana Ganin Kaman bai kyauta mata Ba, Amma Yar Dariyar da tayi Yanzu yasa hankalinsa Kwanciya,yace

"Yanzu muka gama waya da Muzzammil, yace suna hanya shida Dad, zasu zo KD, So you have to come karya gano bakya Gidan"

"Muzzammil ya dawo ne?"

"Jiya ya dawo Amma Gobe zai koma"

"Kaii Muzzammil Rigima shi dai zaman Ƙasar ce Bayaso”

Shima Murmushi yayi yace

“Idan kin iso gidan Ki kirani"

“hmm yaya Fita daga gidan nan fa ba Ƙaramin Aiki bane"

Ya fada tana Zuba kwashe Irish dinda Suka Gama soyuwa, ta zuba wasu

"Wani ya Ajiye ki ne?, I thought zaman Kanki kike Kinada Yancin Fita da shiga a duk lokacin da Kika ga dama ko dai kin karɓi sadakinsa ne?"

Zaro Idanu tayi

“A'a kawai ina tunanin me zasu zarga idan Akace an kawo Amarya Jiya ta fita yau abin ai ba ma'ana”

“kin dai san Halin Daddy, Kisan Yanda za'a yi kizo koda Bai sani ba,karki bashi ƙofar da Zaiyi zargin Wani Abu "

"Inshallah Zan Ƙoƙarta, yaya Ga Irish”

Ta fada tana Jujjuya shi a kan wuta

“Irish sai Ku Princess ”

“Ayya Malam Garin daɗi na nesa"

"Eh ba Komai, bari in shiga Shago, ki kula Min da kanki”

"Love You , muah..."

Ta Kai Wayar da niyyar tayi pecking Ɗinshi ,Wufff taji an Fige Wayar.

Saurin Juyowa tayi, Ganin mutum a Tsaye bayanta Yasata sakin Ƙara ,Hannu yasa ya Toshe mata baki Kar ihunta ya Fito,ya sa hannu ya riƙota ta baya Gudun karta faɗa mai ganin tayi baya, Tayi saurin Rufe Idonta Gam Cikeda tashin hankali.

Jikinta ne ya dauki rawa nan take don firgici ,Jikinta na rawa take qoqarin kwacewa daga riqon dayayimata, idanunta sun rufe don ko ganinshi batayi ba, a Tunaninta Wani ƙaton ne ya faɗo musu gida da Sassafen nan

Lura da haka yasashi qara riqota batareda ya saki bakinba yace

“A gidan Mu ba'a Ihu...!zaki tsorata mana ƴaƴan Aljannun dake bamu kariya"

Ahankali ta sauke numfashi ta ware Idanunta,ta kalleshi nutsuwarta na dawomata ahankali , Ganinshi Tsaye a gabanta Yasata jin Haushin Kanta

_Ashe wannan Abin ne ya tsorata ta?_

A bayyane taja Tsaki da bakinta dake rufe da tafin hannunsa cikeda Takaici, jin saukan Numfashin sa saman Fuskar ta Yasata daga Ido ta ƙare masa Kallo ,Sai yanzu ta Lura da yanayin Tsayuwarsu, hannu tasa ta Mintsili Hannun sa dake Dafe da bayanta Amma ko gizau baiyi ba.

A masifance ta ɗago idonta,Cikin Sa'a yayi nasarar Saita Nasa Idanun cikin nata, take taji wani irin Kasala ya saukar mata, ta kasa Janye Idanunta daga nashi, Shima kallonta yake batareda ya saketa ba ko ya budemata baki ba yana hango yanda Bugun zuciyarta ke Sauyawa.

Haka sukaita kallon juna for more than a minute, a Hankali ta fara janye nata idanun a kasalance jin yanda nashi suka haskemata nata.

Hannu tasa ta cire Hannun sa dake bakinta,Ganin yacigaba da kallonta batareda ya saketaba tasata qara jin Kasala na cigaba da diran Mata, tasa hannu ta sake yaƙushin hannunsa ta Baya.

Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya saketa.

Wani nannauyan ajiyar zuciya ta sauke, Numfashin ta na Racing, ta dan jada baya don matsawa daga kusadashi.

Kallon Yanda take sauke numfashi yayi yace

"Da wane dan iskan kike waya da Sanyin safiyar nan?"

Sai yanzu ta lura da Wayarta dake riƙe a hannunsa ,tasa hannu zata karɓe,ya dan ja da baya

"I Have seized the Phone"

Wani Abu taji ta taso ya toshe mata maqoshi, Kutt har ya isa?.

Sake Mika hannu tayi ,fuska a daure tace

"Ban wayata"

"Bakijiba? Nace nayi Seizing "

yafada yana kallon yadda fuskarta ke sauya Colour, Lallai Saleem Ka samu Guri da yawa.

Nufoshi tayi da niyyar Ƙwace wayar ranta a ɓace

“Idan kika ƙara One more Step Am gonna Hug You and Wayar ki ta tafi kenan ”

Dakatawa tayi zuciyarta na suya, gaskiya ZEEYK yagama daita, wannan wulaqancin har ina?, Dama Tasan Saleem bazai taɓa bin Ƙaidojinsu ba, tunda Burinshi ya cika ya samu abinda yake so thofa sai yanda Yayi da ita, Shiyasa Hankalin ta ya gaza kwanciya da auren.

Dagowa tayi tana kallonshi Jitake kamar ta rufeshi da duka.

"Look mallam inada abubuwan yi,Lemme have my phone"

Shima Dagowa yayi ,yayi Folding Arms ɗinsa a ƙirjinsa ya jingina da Bango yana dubanta cikeda izza kamar irin Boss dinnan ,Zubamata cat eyes dinshi yayi ya qureta da kallo.

"Ni mijinki na hanayin Waya a gidana"

"You have no right For that Saleem ,hand my Phone over to me?!"

Tafada tsakankanin abinda ya toshe mata maƙoshi cikin jin haushi , ko motsawa baiyi Ba yawani zubamata na mujiya.

Cikeda Salon Mugunta ya Cije Lips ɗinsa ,Yana Cigaba da kafeta da Idanu yace

"Are You talking about Right MRS SALEEM?, kin manta yanzu a ƙarƙashina kike inada Damar yin yanda nake so dake? ,Ko kin manta?"

Ya faɗa cikin isa.

“bakada wannan damar Saleem "

"Ni kam nake da dama Maryam tunda nayi Nasarar Raboki da Gidan iyayenki na Kawoki nan Ai na gama samun iko a kanki"

Shiru tayi tana kallonshi unbelievable, Iko? Iko akanta? A tunaninshi auren gaske Sukayi? , innalillahi Shikenan ta kashe kanta da kanta 💔, ta kawo kanta inda za'a kawo ƙarshen Rayuwar ta.

Hawaye taji yana naneman saukomata, ga wani nauyi da zuciyarta tayi.

Qoqarin maida hawayen take don bataso yaga saukarsu yayinda farashin tsanarshi sai ƙara hauhawa yake azuciyarta.

"Mrs Saleem ,I'll buy you new phone Dashi zaki rinƙa amfani ,Bada kowa zaki rinƙa waya ba

Please Login or Register in order to submit comment