Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na sake kaɗawa suna sake komawa jajur fiye da da.


"Abba ina Matuƙar Girmama ka a matsayin ka na Uba,haka Kai ma Baffa ,idan ba so kuke In Aiwatar da abin da zai zo ya dame mu Gabaki daya ba ,ku daga Bikin nan har sai Ammie taji sauƙi, Kuma ku Bari Aeesh ta zaɓi abokin Rayuwarta da kanta"


"A'isha Ni Takeso ko yanzu aka tambaye ta zata tabbatar muku da gaskiya,Aure mu da rashinsa Bazaiba mara lafiya lafiya ba"

Kallon Aeesh Ashman Yayi a kasashe yace

"Ihkty Da gaske kina son Saleem?"

Ɗagowa tayi ta dubi saleem, Ko Kallonta baiyi ba ya kauda kai gefe.

Bayan hannu tasa ta share Kwalla da ya Gangaro mata ,Cikin sanyi tace

"Ina Son Yaya Salee..."

Wani irin Damƙa yakai wa hannayenta biyu, ya zuba mata manyan idanunsa da sukai jazur da ɓacin rai yace

"Ƙarya kike Aees bakya sonshi "

"Ina sonshi "

Ta fada cikin hawaye

Saleem dake kallonsu idanu jazur ya ɗauke kansa daga garesu a karo na farko, murya a dakushe yace

"Kome zaka yi bazaka iya hana Aurennan ba, Nobody is against It"

"Shut up"

Ya faɗa cikin daka tsawa yana ɗaga hannu tamkar zai make Aeesh dake gabanshi.

Baya tayi da sauri tana rumtse idanu dan tama sadaƙar mazgeta zaiyi.

Kasa cewa komai yayi, sai jikinsa dake wani irin rawar bala'i.

"Ihkty karki yarda ki Aureshi , Bazai iya kula dake ba, kin manta ke amana ta ce , Ni nakeda Alhakin Nema miki Abokin Rayuwa Sam Saleem Bai Dace dake ba"

Ya fada Cikin Rawar murya kamar Zaiyi kuma ƙwanjinsa da jijiyoyin kansa na sake buɗewa, yanda ƙirjinsa ke sama da ƙasa kawai zai tabbatar maka zuciyarsa na gudu maiban tsoro dake neman fin ƙarfin gangangar jikin nasa.


Daga Irin rikon da yayi ma Hannunta ma ya isa ya tabbatar mata da Tsananin ƙunar da yakeji a zuciyarshi ba.

Sosai Taji zuciyarta ta karaya Amma duk da haka bata ji zata iya Sadaukar da mutuncinta da rayuwar mahaifiyanta Akan auren Saleem ba.....



Longest page ever🤭


Bintou ✍🏼

Nayi Gabas 🚶🏻‍♀️



*Masu complaining Aeesh ta cika sanyi, Saleem ta rike wuta dayawa kuyi haquri, everything will be alright insha allah, mutum Tara yake bai Cika goma ba, kowa da nasa Personality, Masu sanyin hali da Saurin Yarda da mutane Suke samun heart break da wuri,Masu Zafi irin Saleem kuma Suke Afkawa ramin da Fitarsu Keda matuƙar wahala, Banason rushing din komai ne, hope zaku fahimceni🙏*


Thanks 😍

Share
And
Comment

13th July😍
[7/18, 9:30 PM] chubby number: 🗡️🫀 _*WUƘA A ZUCIYA*_🫀🗡️

_[B l e e d i n g h e a r t s]_



*019*



Sosai Taji zuciyarta ta karaya Amma  duk da haka bata ji zata iya Sadaukar da mutuncinta da rayuwar mahaifiyanta Akan auren Saleem ba.

Rintse Idanu tayi ,ta sake maimaitawa

"Kayi haƙuri Arhy Ina Son Yaa Saleem"

Ta ƙarshe maganar Muryarta na cracking.

Sakin Hannunta yayi A hankali jikinsa a sanyaye ,idanunsa jajur ta ɗago ta kalle saleem, shima kallon nashi yake, Murmushi Fall a fuskar sa,

Shima Ashman murmushi yayi ya tako gabanshi,

A hankali Ashman ya sauke idonsa akan Saleem har zuwa mutanen dakin ya maida Idanunsa kan Aeesh dake ƙoƙarin hana Hawayen Idanun ta Diga tamkar ba ita ba, sake maida kallonshi yayi ga Saleem a wani yanayi mai nuni da tsantsar Dakewa da jarumta.

Ashman yasa Hannu cikin Aljihu ya zaro Farar medicated Glass dinsa a aljihunsa ya rufe idanunsa sannan Ya tura hannayensa a aljihu duka biyun yana ja da baya fuskarsa na ƙara tsukewa.

"A duk lokacin da mutum mai idanu ya saka Farar Medicated Glass yana da matuƙar Ƙayatarwa, ta wane Bangaren Kuwa ,Yana Ƙarawa mutum karfin Ganin Idanu, wasu lokutan har kakan hango Abubuwan da Mai lafiyayyun Idanu baya hangowa saboda karfin da Bature ya Bama Gilashin, amma da tsautsayi zaisa mara lafiyan ido wanda Aka bashi Gilashin don Kara Kaifin Ganin (kaman Ni dai) ,Yayi gangancin Yin Mugun tseren da zaisa Gilashin ya fashe Zai iya shiga Alhinin har yayi Tunanin chanza wani, shi kuma gilashin da ya fashe kokarinka kawai Ka yar da Fasassun Gudun kar yayi maka illa, wanda ya Tarwatse a ƙasa kuwa sai kaga ana Kafa kafa Don Kar a taka ,musamman idan ya kasance irin Nawa mai d'auke da asalin Gilashi, Wanda zai iya Jawa Mutum Rauni Ko tayaya ya taɓa a fashe, glass Kuma Tsalle yake ya fada inda ba'a zato,  Saleem !, Bansan Ya Ka daukeni a zuciyar ka ba, amma Ni daukar da nayi maka Daidai yake da Glass Dinnan a Rayuwata ,Idan Kana tareda Ni nakan Hango Abinda Kai kanka baka hangowa a tattare da kai, Karka Sake Nayi tseren da zaisa Gilashin Ta kuɓuce ta faɗi ta Tarwatse ,Domin Kuwa koda ya Tarwatse na yarda Gangar Jikin Bazan bari Ragowar Fasassun Suyi Illa Ga Na kusa dani ba,Bansan Ya zaka dau zance na ba, Amma Ina umurtan Ka da ka gaggauta Kwance Kullalliyar da ka Kulla a zancen Aurenka da Ihkty...!"

Shiru dakin Ya dauka, Gabaki daya jikinsu Yayi sanyi kaman an zare Musu Lakka ,kalamansa Sun saka Dukkansu Cikin Lissafi kowannensu ya shiga Tunani da iya lissafinsa Yana auna kalaman Ashman a lizamin Hankali.

Da Karfi ya ciji Lower lip dinsa Ya raɓa Saleem ta gefe zai fice, Ya jawo kwalar Rigarshi ta baya hakan ya tilasta Mishi Dakatawa  tare da juyowa yana kallonshi.

Sakin Rigansa yayi yace

“ idan Eye Glass ta fashe gangancin Mutum ne ya jawo hakan,Kuma matsiyaci ne zaiji  zafi saboda Tunanin yanda Zai sayi wani, Amma Idan Ta mai hali ce ba zai damu ba saboda mai Yiwuwa Yanada Spare ,Gilashin Ido badon Kara Kaifin gani kadai Ake sashi ba,ana sashi Domin kare Ganin Wasu Abubuwa Da kuma ado, Mai yiwuwa A yanda ka daukeni ka daukeni ne a matsayin madubi rufe ido hanani Ganin Hanya, Irin Wannan Gilashin Kuwa ko sun Fashe ba Damuwa mukeyi dasu ba don Dama ba Amfani Suke mana ba, Ashman..!, kai Likita ne Aikinka duba marasa Lafiya da yankasu, Wannan ake kira da Aikin Maza a ɓarka mutum a kuma ɗinke shi,Nima fa Karka manta Na iya Ɓarka Mutum,Na kuma san Matsalolin jinsin Da nake Ɓarkawa ta wani Ɓangaren Auren nan a sati Biyu Ba tilastama wani Akayi ba, Taimako zanyi ,Domin kuwa na riga na hango Abinda baka hango ba,  Zaifi dacewa da ka tsaya a inda Allah ya ajiyeka domin kuwa idan Kace zaka Shiga sabgar da ba naka ba Gilashin da yayi TsilliTsilli shi zaka taka batareda ka sani ba Ka kiyayi Shiga Sabgar Masoya babu Abinda bazai iya faruwa ba akan soyyaya....!"

Ya ƙarashe Maganar da Kallon cikin kwayar idon Ashman da yayi jazur kaman Wuta.

Ashman bai sake ce masa Komai ba ya fice a Fusace, Ashman yanada Fushi Sosai Amma abune mai wahala ganin fushinsa , idan yayi fushi kuma yakan dau lokaci kafin Ya sauko ,fushin sa nada Muni sosai Don Kuwa hatta wanda Bai kamata ya Shafa ba Saiya shafa.

Su Abba sun San halinshi Shiyasa Basu shiga tsakaninsu ba, yasan ya Zalunci Ashman dayawa,Ya kuma fifita saleem Akan Kowa ,Yasan Yanda Ashman Keji a Halin Yanzu Shiga tsakanin Fadarsu Bazai Sulhunta su ba sai dai abin ya dawo kanshi.

(_Da Ace ya kasance Uba na Gari Da Babu Abinda zaisa yaji Shakkar bawa 'dansa Umurni, Da Ya kwatanta adalci a tsakaninsu dukda kokwanto baishiga zuciyarsa ba, Ashman yana matuƙar ganin Girman Mahaifinsa zai iya bin duk hanyar da yace yabi matuƙar hakan bazai saɓama Shari'a ba, Amma Abba gani yake kaman Rashin Adalcin da yake nuna masa bazai sa yabishi ba, Yaji mamaki Matuƙa da ya Amince da Auren Deejah da kuma rage lokacin auren da akayi batareda ya tada Hayaniya ba ,Shiyasa a wannan Karon ya ƙyalesu Dukda ba tarbiyya bane fada a gaban Iyaye Especially a irin wannan taron da ya haɗa Gabaki daya ahali, Suma ganin Uban gayyan bai dakatar ba Shiyasa Suka zuba ido Suna kallo_ )

Shima Saleem Fita yayi Don Dama da Aiki a gabansa Kiran gaggawar da ya samu daga Abba ne yasashi Barin Komai ya taho.

Da fitan Salem sai daki ya Kacame da hayaniya jin Hayaniyan yayi yawa yasa Nurse dindake tareda Umma tayi Msu magana akan Su taimaka su Fita Don Mara lafiya na bukatar hutu.

Tunda saleem ya baro ward din  maganganun Ashman ne kawai ke yawo a zuciyar shi, gaba ɗaya ya kasa fahimtar alaƙar batun Aurensa da Misalin da ya kawo, Tabbas Ashman Nada Wani ɓoyayyen sirri a zuciyarshi, Kuma wannan Sirrin Zai iya daƙusar da Aurensu Cikin Ƙankanin Lokaci ,ya zama Dole ya gano Sirrin Gudun kar yayi Masa harin Sama.

Tunowa yayi da Irin Zurfin Cikin Ashman mai ban haushi , Koda faɗin Abu nada Muhimmanci a wajensa bai Cika fada ba , Ballantana ajega sirri.

  guntun tsaki yayi ya dan shafo gemunsa a hankali, yayinda idanunsa ke kallon hanya.

  Daga nan office ya koma, inda ya tarar da Maryam, Shigowar ta kenan ,gaba daya yau bai ganta ba,Dama idan Anyi Ward round aka maidata Labour ward ba cika ganinta yakeyi ba ,Saboda Akwai ayyuka achan sosai Basua zama .

Ta bishi da kallo tana sake kullum fuskar sa a haɗe babu rahama Shiyasa bata banbance yanayin Farin Cikinsa da kuma akasin hakan, tasan sarai ya ganta a tsaye Kuma shi ta take jira, amma ya basar abinsa..

Guntun Tsaki taja tana gyara Tsayuwarta, File din hannunta Ta dire Masa kan Desk Ta Kauda Kai Ko kallonshi batayi ba ta fara magana a Natse.

"Sir Wannan Patient ɗin ta samu cervical tear munyi Mata Episiotomy, Batada Kuɗin Biya so Sun Roƙi alfarmar a kara Musu time Mijin Matan Zaije ya nemo Zuwa Anjima, Na gayawa Incharge tace in Gaya maka in ka yarda , sannnan wannan Ta haihu lafiya but she's in Postpartum Haemorrhage She's in Severe Bleeding,Munyi iyakacin Ƙoƙarin mu don Ganin tayi Stopping Bleeding But Abin sai gaba Yakeyi So ur attention is neede...!"

"Really..!, Why Me?, Ina sauran Gynecologist na asibitin?, Ni kadai ne?"

"Sir You're The one Oncall Shiyasa na kiraka”

Tsawa ya daka mata
"Hang It,macen da ta samu Bleeding After birth Kema kinsan Mutuwa Zatayi inba anshawo kan Abinda Wuri ba, Na tabbata Zuwa iyanzu Jinin Ya rigada Ya taɓa internal Organs Dinta!, so kike in Ɓata Lokacina Akan Dying patient?”

Yayi maganar Yana kallon Cikin idonta da ta fiddo waje a mugun mammakince.

"So Allow her to die in Peace ,Kinga Mun rage Msu nauyin Biyan treatment Fee, And Your first Complain Akan Me cervical Tear Dinnan Ku je ku kwance ɗinkin da Kukayi mata, Mijin yasan bazata iya haihuwa dakanta ba sai an ƙarata yaje ya Auro gajeruwar Mace?, Duk wanda Ya Auro gajeruwar Mace yasan abinda ya auro, yasani sarai wajen haihuwa Dole sai an Ƙarata saboda Nature of their Pelvis , So Ku kwance Ɗinkin Da Kukayi Kuma ku biya mu Stiches dinmu wannan Asibiti ne ba kasuwa ba da Za'ayi Aiki a bashi"

Ido Maryam ta Runtse da ƙarfi ta sa hannayenta Biyu ta toshe Kunnenta after Listening to the worse words of her life, Saleem Bashida Imani ko kadan ,Ta saba da ganin rashin Imaninsa Akan Mata marasa Lafiya Amma Nayau ya gigita ta Sosai, Inba Rashin Imani irin na saleem ba mace ta samu Yagewa wajen Haihuwa sun dinketa Mijinta Bashida Kudin Biya sai yace su kwance Ɗinkin kuma su biyasu kudin Stiches ɗin da sukayi amfani dashi?, wannan Wane irin Rashin Adalci ne?, Karshen Rashin Imani Shine wanda ya nuna akan dayan case din, Matar da ta haihu bayan ta haihu jini ya Ɓalle mata,Da gaskiyarsa idan aka kasa Dakatar da Zuban Jinin ana iya rasata ,Amma ai akan Shawo kan Matsalar In Allah Ya Nufa da sauran Rayuwa nan Gaba.

A karo na farko da ta fara taka masa Burki akan Rashin Imanin da yake nunawa Akan mata, Cikin Fusata tace

"Ba Iyawarka ta kawowa wannan Matsayin ba,A wannan Asibin aikinka shine kula da marasa Lafiya da Cetan Rayukansu, Babu ran kowa a hannunka baka isa ka tsaida Lokacin Mutuwan Wani ba Baka isa Hana mutuwa daukan Rai In Lokaci yayi ba, da har kake cewa baka son Kayi wasting Time ɗinka akan Dying patient Ka tuna Saida Uwarka tayi labor sannan Ta haifeka, Da Ace ta samu Postpartum Haemorrhage Anƙi dubata da Baka san Uwarka ba, don haka ko kaƙi ko kaso sai ka dubata ka kuma ceto Rayuwarta ,ka sani idan aka samu akasi ta rasa Rayuwarta saina Shigar da ƙara akanka, kuma kasan mafi kankancin Hukuncin da za'a zartar akanka shine su amshe License ɗinka ka dawo Normal Mutum kaman Kowa, Aikin da Kake taƙama dashi zai zamana babu Shi, and wacce mukayi ma Episiotomy kace mu Kwance bazamu Kwance ba, idan har ka isa Mara kunya kaje ka kwance dakanka sannan Ka cire Kudin Stiches daga cikin Albashin Mu,In ka cika mara Kunya Ka nuna Min Kai Isasshe ne!"

Ta ida atsawace hawaye na taruwa a idonta sosai kamar Wanda akace Uwarta ce akwance babu Lafiya.

Daukar files din tayi sannan ta watsa mishi wani kallon tsana da rinnanun idanunshi tabuga tsaki tareda fadin *"Bloody Bastard"*

Fuu tafice tana banging kofar da karfin tsiya.

Har tsakar kanshi yaji tsakinta ,kalamanta da kuma bugawar kofar.

Bin bayanta yayi da kallo kamar an ce masa zata dawo, zuciyarshi inbanda bugawa babu abinda take.

*_ko kaƙi ko kaso sai ka dubata ka kuma ceto Rayuwarta ,ka sani idan aka samu akasi ta rasa Rayuwarta saina Shigar da ƙara akanka, kuma kasan mafi kankancin Hukuncin da za'a zartar akanka shine su amshe License ɗinka ka dawo Normal Mutum kaman Kowa, Aikin da Kake taƙama dashi zai zamana babu Shi_*

Kalaman sai yawo suke masa, Tabbas Da gaskiyarta idan har ya saki Patient ɗin ta rasa Rayuwarta batareda ya dubata ba zai iya rasa license din Aikinsa Kuma hakan Ba karamin abin Kunya bane a gareshi.

Tsaki yaja ,Ya fita izuwa labor Ward din, Karo na farko a rayuwarsa Da yace bazaiyi abu ba kuma ya dawo yayi.

Yasha Matuƙar wahala kafin Ya ceto Rayuwarta don Saida Ya nemi taimakon colleagues dinsa, Koda Dayan Matan Kuma Yasa akayi mata uzuri har Mijinta ya samu Ya Kawo.

A ranar Wuni yayi Cikin ƙunci, Ashman Kuma yana Fita Bai Zarce ko'ina ba sai Company dinda yake Rulling Ya damƙa ragamar Komai a hannun Minal P.A dinsa, Sannan Ya dawo asibiti ya damƙa Komai a hannun Dr Aaryaan, Batare da ya gayawa kowa ba ya Kama Hanyar Lagos don a binciken da ya gudanar akan Bamalli an Gaya masa yana Lagos ,Abinda Ashman Bai sani ba kuwa Bamalli baya zama waje guda Duk inda yayi sai yayi barna daga nan Sai Ya Chanza Jaha, Bayayin Kwana biyu a gari idan ya jima ne yayi Kwana ɗaya.

Da yamma Su Kawu da tawagar su suka Koma Kano, Suka bar Abba Goggo, inna Yasai, Aeesh da Habeeb a Wajen Umma.

Yau Student doctors Dindake karkashin sa sunci ubansu don Sauke bala'in sa  saleem yayi akan su, Abu kadan saiya rufe mutum da fada kamar zai Dakesu, Sun saba da rashin Mutuncinshi Amma na yau ya fi Tsoratasu,Abin har Patient Relatives Saida Ya Shafa.

Ko maryam tsoron tunkarar Office din tayi don A yanda ta gasa Masa Magana Tasan Ya kamata kashinta ya bushe.

Haka yau Shift din yazama ran boss a6ace yake hakan yasa kowa ke taka tsantsan dashi, ta ɗayan Ɓangaren Kuwa Babu wanda yasan Big Boss ya bar Gari....

Bai sake Komawa duba Umma ba , Haka bai san Su Kawu sun Wuce ba.

Har dare yana Cikin Fushi, Jira yake Ashman ya dawo Ko ina yaje ya sauke masa Nasa Buhun Masifar yana ji idan bai Zazzage raguwan bala'in Akan Ashman ba ,Bazai taɓa samun natsuwa ba.

Shiru babu Ashman har Sha'dayan Dare, kasa haƙura yayi , har yayi Shirin Kwanciya bayan yayi wanka ya saka kayan barci, tashi yayi ya Cire su ya saka farar armless da Ƙaramar Nicker Iya Gwiwa.

Fridge ya buɗe ya dauko Kwalbar Wine dinsa ya kafa a baki, bai dire ba saida ya tabbata ya shanye, ya sake dauko wata kwalbar Nan ba saida ya shanye sannan ya dire, Kwalabe Uku Ya shanye a nan take, Cikin Kankanin Lokaci Yajishi a Chan sama , Ya fara Layi yana tangyaɗi

Jakar Goyo sa ya dauko Cikin Drawer ya kwashe Kwalaben barasan dake Fridge ya zubesu ciki, Sannan ya goya a bayanshi, Ya zura takalma ya fito yana Layi.

Karan Takunsa security Sukaji hakan yasasu Farkawa Suna rarumar Makami, Ganinshi yasasu maida makamai Suka buɗe masa Kofa Daya daga Cikin su ya biyo Bayansa, dama ya saba Duk Randa ya uni Cikin baƙin Ciki Sai ya fita daddare Yasha ya bugu sannan ya dawo don Kansa Idan ya bugu dayawa Kuma ya kwana a waje sai gari ya waje ya dawo yayita msu faɗa akan Meyasa Suka barshi Ya fita shi kadai?, Shiyasa Idan Abin nashi ya tashi suke bin Bayanshi gudun Abinda Zaije ya dawo,Dukda ba ƙaramin Wahala yake basu ba amma alherin Da sukesamu a wajenshi yafi ƙarfin wulakancin da yake mishi,ko kadan Ashman Baisan Saleem na shan komai ba don yana kiyayewa sosai wajen Ganin Ya kaucewa Ganinsa A duk lokacin da zaisha, Haka ya gargaɗi masu gadi akan Kada su sake Ashman ya samu labarin.

Garin Yayi Tsit bakajin Sautin Komai sai na tsuntsaye dake shawagi a sararin Samaniya.

Tafiya Sukeyi yana Kurɓar Barasarsa yana Zuba Surutai security dinda ke taka masa baya na Biye mashi.

Sunyi Tafiya mai nisa Sannan Suka Iso wani Eatery sai a lokacin Suka Fara ganin Mutane Kaman Ba dare ba, sai Shawagi suke suna kaiwa da dawowa Mafi yawancinsu mashaya ne da masu Fita taɗin dare da kuma matafiya da suka tsaya don Kore Yunwa Jakar bayansa Ya Sauke ya Fiddo Kwalabe ya diresu a gabansa.

_idan Kana tareda Ni nakan Hango Abinda Kai kanka baka hangowa a tattare da kai, Karka Sake Nayi tseren da zaisa Gilashin Ta kuɓuce ta faɗi ta Tarwatse ,Domin Kuwa koda ya Tarwatse na yarda Gangar Jikin Bazan bari Ragowar Fasassun Suyi Illa Ga Na kusa dani ba,Bansan Ya zaka dau zance na ba, Amma Ina umurtan Ka da ka gaggauta Kwance Kullalliyar da ka Kulla a zancen Aurenka da Ihkty...!_

Maganar Ashman yashiga amsa kuwa a kunnensa.

_Don haka ko kaƙi ko kaso sai ka dubata ka kuma ceto Rayuwarta ,ka sani idan aka samu akasi ta rasa Rayuwarta saina Shigar da ƙara akanka, kuma kasan mafi kankancin Hukuncin da za'a zartar akanka shine su amshe License ɗinka ka dawo Normal Mutum kaman Kowa, Aikin da Kake taƙama dashi zai zamana babu Shi, and wacce mukayi ma Episiotomy kace mu Kwance bazamu Kwance ba, idan har ka isa Mara kunya kaje ka kwance dakanka sannan Ka cire Kudin Stiches daga cikin Albashin Mu,In ka cika mara Kunya Ka nuna Min Kai Isasshe ne!_

Kalaman Maryam Suma suka gifta kwanyarsa

*_Bloody Bastard_*

Ya sakejin Zagin da tayi Mshi har Cikin Jikinsa Yaushe yayi lalacewar da mace zata Dubi tsabar idonshi Ta gasa masa Magana kuma ta tafi bai hukunta ta ba?,Ita wacece ?, waye Ubanta a wannan Garin?Meyasa Ta shigo Rayuwarsa?.

Wulla idanuwa yakeyi Yana kai Kwalba baki yana saukewa, bibbiyu Yake Gani Ammà hakan bai hana idanunshi Hango Mata wata Delivery Agent dinda ta sauka akan Machine ba, kanta sanye cikin Helmet Cikin nutsuwa ta bu'de Akwatin dake jogane da bayan Machine dinta ta Fiddo Wasu Ledoji sannan Ta shige ciki, Babu jimawa ta dawo ta sake kaiwa ciki ta fito tana Kirga kudi still hemlet din Rufe a kanta, Binta da kallo yayi tayi har ta Hau Machine ɗin Ta burga ta tafi.

Zumbur ya miƙe yabi bayanta, Mutumin da ya buyoshi na biye dashi ,Tayi masa nisa baya Hangota, Amma sai bin hanyar yake dake miƙakkiyar hanya ce.

Sunyi nisa sosai babu Ita babu Alamarta, Hakan Yasashi Juyawa yana fadin

"Ba komai In Babu yau akwai Anjima, Gobe da jibi Saina Gamu dake...”


Buuum karan bike yacika wajen,
Daga dan nesa dashi black Agency Bike din ya tsaya batare da an kashe machine dinba sai kuka machine din yake mara ƙara Sosai as usual irin na Delivery Agents bike dinan, Kallonta ya farayi Tun daga dan yatsun Ƙafarta tana zaune a Kan Bike din Bata sauko ba, Baƙar Snicker ce akafan ta dake sanye da Ash socks, ta saka bakin straight trouser, sai baƙar Leather Cardigan hannunta sanye cikin wani irin hadadden Ash hand Sock Mai ɗauke da Hoton Teddy a bayanshi, ahankali ta daura hanun akan key machine din ya juyashi hakan yasa machine din ya mutu, ta daga Kafarta ta taba break din machine din ta tsayar da ita da kyau kafin ta sauko daga kan machine din ya tsaya tana wani kare masa Kallo.

Saleem dogone sosai cikakke dan yacika kayan dayasa fam, Kuma Murdadden Murtum ne mai cikakken haiba da Kwarjini.

duka hannayen ta ta daga ta daura akan hamlet din dake kanta tayi kaman zata cire sai Kuma ta fasa.

Saurin Jada baya Yayi ya ware Lumsassun Idanunsa yana haƙora cikin Layi.

"Hhhhhhhhh Nasan xan Gamu dake, Nasani zaki dawo!"

Kallonshi Take a kaikaice,Dama yana ShayeShaye?, sake duban Agogon Hannunta tayi to 12pm Me ya fitoyi?, Wato bayan Rashin Imanin da yakeyi Harda ShayeShaye Yakeyi _to yau Saleem Allah ya jefoka hannuna Babu Mai fitar dakai_ ta faɗa a zahiri.

Takowa Gabanta yayi Cikin Layi, Bata motsa daga inda Take tsaye ba har Ya iso Gareta

"Baiwar Allah....Me...ki..ke Siyarwa Naji ƙamshin Abinci!, ki bani inci"

Toshe hancinta tayi saboda Warin giyan dake tasowa a bakin nashi ta matsa baya cikin Tsananin Jin ƙyamarsa tace

"Kazace Kuma 'daya ta rage”


"Eh yawwwa Kwaso Su...!,Bani Su Bani kajin manah!"

Waro manyan Idanunta tayi tana sake Dubansa ,Tabbas Saleem Ya bugu da yawa baya gane komai, Wannan Shine Daidai lokacin da ya kamata ta rama wulaƙancin Da yake mata a Asibiti Wayarta ta zato daga aljihunta ta danyi danne danne ,Sannan ta ajiye shi kan Bike dinta.

Ta sake maida Dubanta gareshi

"Mr Saleem What did you Want"


"Am Hungry....Buy me something"

Ya fada cikin Tangyaɗi.

Kafeshi da ido Tayi dariya na cinta

"What did u want from a lowly Person like me?"

Ta faɗa tana Cire Hemlet din kanta, Fuskarta ta bayyana.


Sake Ware Lumsassun Idanunsa yayi akanta cikin Layi yana Tangyaɗi kaman Zai faɗi ƙasa.

“Dr S-Shettima I am Resigning Anyway!, I can take you Down too!, Nan Waje ne ba ASIBITI ba!, me ma kace ɗazu?, You cannot Treat a dying Patient Right?, Saiga ka kuma a gabana a Buge Drunkard!"


"Have You lost your Mind....!?"



"Shut Up Nan Unguwar Muce, Idan Kayi Yunƙurin Fadar Wani abinda ba daidai ba, I won't Let you Slide So Easily...!"

"What....!"

Ya fada cikin Muryar maye yana Kyafkyafta ido.

Murmushi Mai ƙayatarwa tayi

"Kace kanajin Yunwa ko?"

Saurin Gya'da Mata kai yayi kamann dan karamin yaro.

Sake sakin Murmushin mugunta tayi tace

"Inada Kaza 'daya Ya rage, price Ɗinshi 10k in baka?"


Nan ma Saurin Gyada mata kai yayi, tunowa tayi da Wulaƙancin da yayi mata a satin da ya fara zuwa aiki, Akan Ta sa masa Albasa Cikin Sandwich hakan ya tabbatar mata da cewa ba ƙaramin Tsana yayi ma Albasa ba.

Murmushi ta sake saki ,ta buɗe Box Din bayan Babur Dinta ta fiddo Ragowan Kazan ta shimfida masashi a Plate ,Sannan ta dauko Kit dinda take zuba Albasan ta Ta zazzage masa dukka Batareda ta duba Yawan su ba, Tunowa tayi da Randa yace Ta sayo masa Pizza 🍕 a Canteen aka sa Yaji a ranar kifeshi yayi a fuskarta bai damu da yajin dake ciki ba tasha wahala matuƙa ranar saida tayi kuka da Idanunta Shikou ko kallo Bata isheshi ba.

Kwalbar garin Yajin ta ta dauko ta zazzage masashi Dukka Sannan Ta yayyanka masa Kazar kanana.

A ƙasa ya zauna Idanunsa a Lumshe yana Layi,tasan da cikin Hayyacinsa yake bazai iya zama a ƙasa ba saboda shi Mutum ne mai Kyamar datti duk kankantansa.

Kazar ta dire Masa Bayan Ta chakuda Shi da man Albasa mai warin Albasa Sosai.

A kaikaice yake kallon kazar sannan ya dago ya Dubeta yace

"Anty Maryam kazar Da daɗi?"

Tsoro ne ya kamata, taja da baya tana Zaro ido, Tunda take dashi bata Ta ɓaji ya ambaci Sunanta ba ,Saidai ya kirata da Quack ko kuma Miss Renal Nurse Ko Kuma yace Keh, Bata yi zaton Yasan Sunanta ba, Shikenan ta kaɗe tunda ya ambaci Sunanta ta shiga Uku dole ya Koreta a Aiki Gobe 🙆🏻‍♀️.

Yamutse Fuska yayi bayan Ya tauna tsokar kazar mai dauke da Albasa da yaji

"Kai Anty Kazarki babu daɗi"

Ya fada yana Ture Robar, Da yunƙurin Miƙewa.

Waro Manyan Idanunta tayi a fili ta furta ,“In ka isa Shegiya nake sai kacishi!"


Zama tayi Gabansa Ta Gutsuro naman Ta haɗa da Albasa, Already dama Akwai barbadadden Yaji a jikin kazar, Dayan hannun tasa Tabuɗe bakinshi da karfin

Please Login or Register in order to submit comment