Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kaɗai ya isa ki ƙarashe Rayuwarki cikin bauta"

Miƙewa inna tayi, ta dau morper zata Goge,Maryam tayi saurin karɓa a hannunta

"Ki tafi Mama, i'll clear it”

Wani irin kallo ya watsa Mata, rai ɓaci yace

"Sako hijabi mu tafi"

Ya fada Tareda Daukan Mukullin motarsa.

Bata Son Tayi masa Musu ya hanata fita, Hakan yasa ta bi umurnin sa, ta saki morpern ,ta shige ɗaki t dau Mayafi ta fito Tare suka bayan yabama Inna Yathai Makullin part ɗinsa.

Tafe suke babu maicewa kowa uffan, Maryam dama tunda tashigo tajuya kanta tana kallon waje ta window,tana Share guntun hawayen dake zubo mata.

Tuƙi yake hankalinshi rabi na kan tuqi rabi akanta jinshi yake cikin Farin ciki mara Misaltuwa, yau gashi ga Meron sa a matsayin Ma'aurata, the happiest Thing is Yana Bata Umurni yanda ya ga dama Tana binshi sau da ƙafa.

Murmushi Yake ta faman Saki shi ɗaya kaman Zararre.

Tsayuwar mota yasata sanin ta Ɗago, dan kallon window take Amma gaba ki ɗaya hankalinta baya wajenta.

Bin harabar tayi da kallo tacikin motar tana wondering har sun kawo!.

Jin an bude murfin Side ɗinta yasata dagowa suka hada idanu dashi tsaye riqeda murfin motar daya bude mata.

Sauke idanunta tayi sannan ta zuro kafarta ahankali ta sauko tana sake ƙarewa gidan kallo kaman yau ta fara gani.

Ganin yayi gaba zai shiga yasata saurin tsaidashi da
"Ehmm.. Malam ji mana"

Juyowa yayi ya ɗage mata gira

"What...?"

“ina zaka?"

Kallon mamaki ya bita dashi, bata damu ba tace

"Ka jirani a mota, yanzu zan fito"

Muryar Dad Sukaji cikin fada yana cewa idan ma ɓatar masa da ɗiya sukayi su fada mai .

Ja da baya yayi jin muryan Dad, Cikin ɓoye Rudewan sa yace

"30 mins na baki ki fito ina Jiranki "

Taɓe baki tayi a ranta tace .

_Ashe zaka ƙaraci zama_

Ta shige ciki, Abba na tsaye sai faman Masifa yake, ganinta yasa ya nufota Hankali tashe yace

"Princess where have you been?"

Wani irin Ajiyan Zuciya,baba Da mama harda ZEEYK suka saki a Tare.

Itama ta saki nata ɓoyayyen Ajiyan zuciyan.

Hankalin dad a tashe ya nufota da fadin

"Daughter Are you Alright?, Me ya same ki?, Daga ina kike"

Rasa amsar da zata bashi tayi don bata dasu.

Ƙara sawa tayi ta zauna tana sauke numfashi

"Whooh Na gaji, mama a kawo min Ruwa"

"Tambayan ki nake daga ina kike?, Kuma ina kika ajiye wayanki sai faman kira nake"

"Dad Ƙawata ce babu Lafiya, anyi admitting ɗinta a asibi shine Naje dubata, kuma wayata babu charji na bbarota a Asibin”

Ajiyan Zuciya ya saki Yace

"Ohh ya jikinta "

"Da sauƙi ,Dad Bari in Koma Dama na dawo in dau mota ta ne"

"Ok take care, Muzzammil Rakata"

Sai yanzu ta lura da Muzzammil dake zaune a Takure fuska a daure kaman an Takura masa shi a Rayuwanshi baya Son hulɗa da talakawa da alama tilasta mai akayi yazo nan.

Murmushi tayi ta shige Ɗakinta ,bata jima ba ta fito Dauke da Car key ɗinta.

Suka fito Itada Muzzammil,Inda ta Parka Motarta Nan ta sameshi, babu abinda yayi ,kullum sai Shuraym yazo ya wanke mata.

A hankali ta bude Ta shiga mazaunin Driver , Muzzammil ya shiga dayan Side din taja suka bar Harabar gidan, suna fita ta hango Motar saleem Ashe Bai Tafi ba, Murmushin Mugunta tayi taja motar ta Zagayo inda yake.

Ganin Mota ta tsaya a gabansa yasa ya maida hankalinsa kanta, a hankali ta Zuge Glass din Motar, ta ɗaga masa Hannu.

Dubanta Muzzammil yayi yace

"Wa kike daga ma hannu?"

Bata amsa masa ba, sai taja Motar ta sake matsowa gab da shi ,ta Zuge Glass na side din Muzzammil Tace

"BAMALLI, meet my friend, Saleem"

Friend ya Maimaita a ranshi ,lallai ma yarinyar nan👣

"Ohhh na sanshi"

Inji Muzzammil

Zaro ido tayi

"A ina?"

"Sanda na kawo Miki ziyara a Turkish he's the one who Dragged my hair Akan yaga ina magana dake, so Shima dan Nigeria ne, Wow Nice meeting you again Mr Saleem"

Muzzammil ya Fada yana Miƙa masa hannu ta window.

Tsayawa saleem yayi yana dubansu, lallai ma yarinyar nan ta raina shi dayawa Shi yana nan yana jiranta, ta dauko Motarta zata fita da wani ƙato.

Cije Lips dinsa yayi ya galla ma Bamalli harara,Yaja Motarsa ya Tafi yana auna mata kallon kuje ku dawo zaki gamu dani......

*Aeesh*

Kafin Aeesh ta isa makaranta ta fara jin wani irin sanyi na Shigan ta Alamar zazzaɓi, tana zuwa ta kwanta, zazzaɓi ya rufe ta , a takaice dai a ranar a school clinic Suka kwana.

Tana ganin Kiraye kirayen da Ashman yayita mata, Amma ta kasa dauka daga bisani ma kashe wayar tayi.

Zuwa washe Gari ta ɗan ji sauƙi ba Laifi, har ta shirya zasuje lecture zazzaɓi ya sake dawowa.

Reey Tace ta kwanta ta huta, zata sa mata attendance, da Tho ta Amsa ko Uniform Bata Cire ba ta kwanta, 9:40 AM ta farka.

Wayarta ta Kunna,tana kunnawa kiran Aareef na Shigowa Jikinta har tsuma yake, tasa hannu tayi Sliding ta Kara a Kunne, Muryar kamal Taji Cikin tashin hankali yana cewa Tazo Areef ba Lafiya.

Take ta nemi Nata zazzaɓin ta rasa tsabar tashin hankali ko Uniform Bata Cire ba ta Zura Mini Hijab Tareda Daukan Purse ɗinta ,ta Kulle dakin da Key ta fito .

Kai tsaye Department ɗinsu ta Nufa don taba Reey Makulli, taduba Agogon hannunta 9:58am , 2mins ya rage a fito lecture hakan yasa ta tsaya don ta jira fitowansu.

Ta jingina da Bike ɗinda tagani a Parke a wurin

Ganin Mutum tayi a gabanta kaman daga Sama,Kallonshi tayi ganin shima Ita yake kallo.

“Miss Nurse, don Allah zan ari Bike ɗinki"

Yayi maganar yana nuna Babur din, taja baya da fadin

"Sorry don Allah "

"Nooo ai ke zan bawa haƙuri na rage miki jin dadi" tayi shiru tana dan murmusawa.

"Mun ƙara haduwa"

Ta gyada kai , yace

"Kina jiran wani ne?"

"Eh ina jiran Ƙawata ne a ƙarasa Lectures na Bata key"

Zaro Ido Yayi

"Kina jiran ta?"

Ta gyada kai

Yayi yar dariya

"Bari na baki shawara, inni ne ke zuwa zanyi in shiga ajin, ince wa malamin kaji dalla malam tsaya da Lectur zan ba Ƙawata key"

Zaro ido tayi ta nuna kanta

"Wace?, Ni"

"Eh "

Ta girgiza kai tana Murmushi, da Alama ZEEYK akwai zolaya

Dariya yayi yace

"Wlhy daɗe wa Zasuyi na gaya miki Gaskiya,Gara Kizo Na rage miki hanya, daga nan ina zaki?"

Dubanshi tayi da mamaki

"Ikon Allah"

"Ikon Allah?, yo ai unguwar mu daya kenan, ki hau Babur na rage mu tafi"

Yay maganar yana hayewa kan Bike ɗinsa.

Harararsa tayi tace

"Ya kasan Unguwar mu daya?"

"Ba kince Ikon Allah ba?, Yo ai sunan Unguwar mu kenan!"

Murmushi tayi ta girgiza kai, guy Dinnan ya fiye tsokana, tace

"To kaje Ni Hostel ma Zan Koma"

"Allah idan Kika cigaba da jira dadewa zakiyi, don ba yanzu zasu fito ba, Gara ki bini Na kaiki har ƙofar Hostel din"

Tace "eh naji zan cigaba da jira har su Fito "

"Bakiji sharawarata ba kenan"

"Ai shawarar banza kake bani "

Yayi dariya yana gyara zamansa kan Machine dinsa yace

"Har kin tuna min da wani Labarin likita da majinyaci, Patient ne yaje asibi sai ya samu likita, bayan Likita ya dubashi yace kafin kazo wurina kaje wurin wani?, Sai majinyaci yace Eh Naje Gun native doctor, sai Likita ya Fusata yace To native doctor Banda ƙarya da shawarar banza me zasu ma?, wane shawara ya baka?, Sai Patient yace yaace inje wajen likita"

Dariya tayi sosai tace "malam akwaika da ban dariya"

Daidai lokacin da Reey ta iso gurin don Tun da suka fito ta hango su

"Aahh baƙo Mukayi?"

"Yawwa ZEEYK ga Besty na ka tura mata Hotuna na, Besty ga key zanje na dawo"

Karɓar key din Reey tayi tace

"MashAllah jiki yayi sauƙi kenan ,tho Ina Zaki?"

“Sadaukina ba lafiya, zanje dubashi na dawo "

kafin tace wani abu har ta wuce

Binta tayi da kallo, tana mamakin yanda tafiyar ta ya sauya Lokaci guda ,tun Jiya ta lura da yanayin tafiyar ta isn't normal Amma sai ta dangantashi da zazzaɓin da ta kwana dashi .

Tana Fita ta Tare Napep ya kaita har gidan Su Areef, halin da ta isheshi yayi matukar gigita ta, yana kwance sai juyi yakeyi yana ambaton Sunan Allah, Numfashin sa ma Da ƙyar yake fita.

Cikin tashin hankali take Tambayan su Kamal abinda ke damunsa Sukace an rabu Maganinshi kwana biyu Shiyasa ciwon ya dawo mai, bata fahimci abinda suke nufi ba, sai ta musu kallon neman Ƙarin bayani, Bash yace Ga alluran da ake masa nan Amma yanzu sun hana ayi masa wai ya fara yi masa Illa ,kuma idan ba'a yi masa ba zai iya rasa Rayuwarsa.

Hankalinta yayi matuƙar tashi sosai dajin Wannan zancen batason ta rasashi, duk wanda yayi Furucin mutuwa akansa haushinsa take ji.

Ledojin magungunan da suka zuba mata take Duddubawa, babu komai a ciki sai Uban Alluran Pentazocine da turnicate,syringe sai Kuma cannulas Blue, pink da yellow da mamaki ta dubesu tace

"Is he addicted to drugs?"

Cikeda damuwa suka daga mata kai alamar Eh.

A take hawaye ya fara kwaranyowa daga idonta,

_innalillahi wa inna ilaihirrajiun, Allah kasa mafarki nake yi yanzu ace min ba gaske bane ba_

Ware idonta tayi ta diresu akan Aareef dake cikin wani yanayi yanda yake Fitar da nishi a wahalce kadai ya isa ya tabbatar mata da cewa ba mafarki take yi ba, Areef dan ƙwaya ne, Cikinsu ma yana cikin jiga jigan yan ƙwaya.

Allah Sarki SADAUKI, Meyasa ka Tsoma kanka cikin wannan mummunar aƙidar mai wuyar tsamowa?, Meyasa Zaka min haka.

Kuka Takeyi sosai da iya ƙarfin ta, jikin Su Kamal yayi sanyi, tabbas Aeesh nason Areef sosai Kwatankwacin yanda abokinsu keson Ƙawarta Reey, tausayinta ne ya kamasu da suka tuna Matsayinta a wajenshi.

"Please Miss, ki taimaka ki masa Allurar zai farfaɗo immidiately"

Cewar bashh

Take hawaye suka sake wanke Fuskarta ta girgiza kai

"Bazan iya ba, Bash bazan iya ba"

"Please Ki ceci rayuwarsa"

"No Idan namai mutuwa zaiyi"

"Bazai mutu ba, zai dawo hayyacin shi, ki ceci rayuwansa don Allah"

Inji Kamal lokacin da Aareef yayi wani irin Gurnani mai ƙarfi yana Wani irin mimmiƙa kaman mai shirin Mutuwa.

Hankali tashe ta Fiddo Alluran, ta ɓabballa su, ta ɓare syringe ta zuƙo Ruwan Allurar, sannan Tasa Tunnicate ta kulle hannunsa, nan take Jijiyoyin sa suka bayyana, batareda tayi wani dogon Nazari ba tayi masa Alluran bayan su Bash sun Rirriƙeshi.

Da ƙarfi ya saki wani ƙara, ya koma da baya nan take jikinshi ya saki, Babu Alaman Numfashi a Tattare dashi

Wani irin kuka ta saki ta jefar da syringin Ganinshi mimmiƙe a ƙasa babu alamar Numfashi a Tattare dashi.

Ta rintse idonta hawaye na bin kuncinta, cikin rawan hannu da tashin hankali ta ɗaga Hannunshi tana dudduba wa ,amma babu Pulse Babu alaman shi, Breathing process Ɗinshi ta duba taga No Response, a Hankali ta maida Duban ta ga Cardiac region Nan ma stopped.

A Ruɗe cikin matsanancin Hawaye take jijjiga shi tana Faɗin

"No....No...Bai mutu ba, Sadauki na Ka tashi”






Nayi Gabas 🚶🏻‍♀️

Drop your comments

Fisabilillah🔔👏

Bintou ✍🏼

25th September 2022


[10/27, 10:11 PM] Bintou abdool: *WUƘA A ZUCIYA*
_(BLEEDING HEARTS)



*040*



Ta rintse idonta hawaye na bin kuncinta, cikin rawan hannu da tashin hankali ta ɗaga Hannunshi tana dudduba wa ,amma babu Pulse Babu alaman shi, Breathing process Ɗinshi ta duba taga No Response, a Hankali ta maida Duban ta ga Cardiac region Nan ma stopped.

A Ruɗe cikin matsanancin Hawaye take jijjiga shi tana Faɗin

"No....No...Bai mutu ba, Sadauki na Ka tashi”

Iya rudewa Aeesh ta gama rudewa sai kiran Suna shi take tana jijjigashi amma no response .

a hankali jiri ya jata,tayi baya ta faɗi tana ganin duhu a idonta, daga baya ta daina ganin komai.

______

A hankali ta fara dawowa haiyacinta, sanyin fanka na ratsata.

Ɗigar Ruwan da taji a fuskar tane yasata saurin ware idanun ahankali, ta motsa hannayenta kadan tana son ta dawo da karfin jikinta, muryar Aareef taji yace

" A'isha? Aeesh kina ji na?"

Dishi Dishi take ganinshi, Ta dan bude ido ta kadan ta kalleshi, yana duƙe kanta hannunsa Rike da Karamar Gorar faro.

Dire gorar yayi ya riko hannunta fuskarsa tayi ja alamar abuge yake, ta danyi kokarin kwace hannunta tana masa murmushi amma sarawan da kanta yakeyi yasa murmushin ya zama kamar yaƙe.

Har yanzu ta kasa Tuna abinda ke faruwa, duban dakin da take,

Kamal yana zaune gefenta, Bash yana daga can baya ya jingina da jikin bango, Aareef kuma yana duƙe ya riƙe hannunta tsantsar tashin hankali ne a rubuce a fuskarsa.

Allurar da ta tsira masa ta tuno ,yanda yayi Wani irin jijjiga kafin ta ya koma kaman matacce.

A take hawaye ya fara kwaranyowa daga idonta,

*_innalillahi wa inna ilaihirrajiun, Allah kasa mafarki nake yi yanzu a ce min ba gaske bane ba, Shikenan na kashe shi Sadauki is gone_*

Sake riƙo hannayenta yayi
"Babe calm down babu Abinda ya same ni , Am fyn"

Dago Fuskan ta tayi ta rungume shi da sauri shima ya rungume ta kamar zai balla ta, sai jin saukar hawayensa tayi a bayanta da kuma sautin sheshheƙarsa, itama kukan take yi sosai.

Tausayin kansu yake yasan adadin yanda take sonsa a zuciyarta Amma shi ko kadan bayajin digon sonta a nasa zuciyar.

Itama kukan takeyi ta fara rarrashinsa tana bubbuga bayansa a hankali, cikin kuka tace "Why...!, why meyasa zakayi including drugs cikin rayuwar ka?,Kana son ka kashe kanka ne?, You know you're all I got, bazan iya juran rashin ka ba"

Tayi mgnr tana jin bugun zuciyarsa tamkar a kirjinta, ya dago idanunsa jawur ya zuba mata.

"Areef tell me mekake nema a wannan rayuwar?, me ya sa ka fada Drugs?, Kudi ne?, Ko Soyayyar da nake maka ne yayi kadan?, Fada min I promise to give you everything you request, Banaso na sake ganinka cikin wannan halin Pleaseee....."

Ya girgiza mata kai

"A'isha Bazaki iya sama min Abinda nake so ba, Bazaki iya yin wannan sadaukarwar ba"

Lumshe idanunta tayi, taba ma hawayenta damar zubowa tace

"Kasan yanda nake sonka kuwa?"

Bai ce komai ba sai kallonta da yakeyi

"Zan iya sadaukar da komai Akanka, zan iyayin komai domin sama maka farin ciki, farin cikin ka shi zaisa zuciyata ta cigaba da bugawa, ganinka cikin wannan hanayin shi zaisa Bugun zuciyata ta tsaya"

Hannu na rawa ta daga yar ƙaramar hijab dinta,ya zuba mata ido ,ta janye wuyar Scrub dinta , cikin rawar jiki ta damƙi hannunsa ,ta kai daidai saitin zuciyarta.

"Feel my heart beat, kaji yanda zuciyata ke bugawa , Saboda kai... saboda halin da ka shiga bugunshi ya sauya, idan ka cigaba da yin Drugs bugun zuciyata zata iya tsayawa"

Wasu siraren hawaye suka sake zubo mata, ta sake damƙe hannunsa a saitin zuciyarta, Tana jin zuciyar na barazanar rabuwa da kirjinta.

Duk da tasan hakan bai dace ba, amma this's the best way da zata iya describing How she feels him a zuciyarta.

"Ka fada min Nayi maka Alƙawarin sama maka komai da iya abin da nake dashi"

A hankali ta saki hannunsa dake dafe a ƙirjin ta, ta kalle cikin ƙwayar idonsa

"Tell me....."

Ji yayi ta daure shi da jijoyoyin jikinta, bakinsa na rawa yace

"Reeey....."

"What happened to Reeey"

"She's the one I love ,ita nake so ba ke ba”

Da ƙarfi zuciyar ta ta buga, ya kauda kai batare da ya damu da yanayin da ta shiga ba ya cigaba da fadin

"Ina Drugs buh saboda ita na fara Injectables, Nayi iya kokarina wajen Cireta a zuciyata, ki maye gurbin ta a zuciyata, amma Abin ya faskara ji nake idan ban same ta ba zan iya rasa rayuwata, ki taimaka Min kisa ta soni.."

Jikinta na rawa tasa hannu ta juyo face din shi ,ta kalli cikin idonsa idonta na zubar hawaye

"Look into my eyes".

Kasa kallon ta yy ya dukar da kai

"Reeey itace ta saka a wannan yanayin?"

Ya gyada kai kaman karamin yaro

Hawaye suka gangaro mata ,ta sake cewa

"Don Allah kace min ƙarya ne''

Sake duƙar dakansa yayi jijoyoyin jikinsa na tashi

"Ba ƙarya nake ba, Itace rayuwata"

Idanunta cike da hawaye still hannunta bai bar face dinshi ba tace

"Idan Ka same ta zaka daina Drugs?"

Nan ma saurin Gyada mata kai yayi alamar eh

A hankali ta sauke hannunta dake saman Kuncinsa cikin kuka tace

"Ni kuma fa?, Zaka so Ni?"

Yayi shuru

"Bazaka soni ba Ko?”

Tasa bayan hannu ta share Hawaye, gonin tausayi

"Idan zaka kasance cikin Farin ciki wannan kadai ya isa ya sama min rayuwa"

Ta ciro Bundle din Kuɗaɗen dake jakarta wanda ita kanta batasan adadin su ba, ta dire masa

"Ku sayi kayan Abinci"

Sannan Ta dau hijab dinta, tasa , ta rataye jakarta ta fice tana sharar ƙwalla.

Napep ta tare ya Kaita har gaban Hostel.

Fitowa tayi fuskarta jagajaga da hawaye, ta biyashi Kudin sa ,Jikinsa a sanyaye cikin tausayawa yace ta bar kudin

Ta juya kenan taji an kira sunan ta, Zeeyk ne.

Saurin share Hawayen ta tayi gudun kar ya gani, amma ta makaro ya riga ya gani ga fuskar ta da tayi jazur.

"Kuka kikeyi?, Patient din naki ne ya rasu?"

Murmushi tayi ta gyada masa kai batare da ta iya cewa komai ba, ta juya zata tafi ya dakatar da ita.

"Aeesh...!"

Chak ta tsaya, amma bata juyo ba.

"Ina sonki....!"

"Tunda na ganki naji zuciyata ta aminta dake, don Allah ki bani dama zuciyata ta cigaba da bugawa domin ki"

Kasa juyowa tayi don jin kalaman sa taji tamkar saukar aradu.

Shikou ya cigaba da cewa

"Idan kin soni zan dandana miki zaƙin zumar dake cikin soyayya, in Zamo hawayen ki , in rayu cikin idanunki har abada"

Wani katon abu taji ya taso mata a maƙoshi, ta haɗiye batare da ta juyo ba tace

"So da ɗaci take babu hadin da za'a iya mata ta chanza daga dandanon ta, na tauna banji dadi ba, idan ka kasance ruwan hawaye na, ba a idanuna zaka rayu ba, a kullum a koda yaushe zan rinƙa zubar dakai ina gogeka daga idanuna zuwa fatar fuskata don Allah ka bar Wannan maganar idan ka cigaba da furta min wannan Kalmar zan iya tsanar ka!"

"Aaah me yayi zafi?, ai nafiso in zama hawayen naki ta yanda Kullum zan dinga diga kina shareni, Kinga a kullum sai kin kulani"

Yay maganar yana dawowa gabanta, har yanzu tana nan tsaye kaman an Dasata, kallon Cikin jiqaqqun idanunta yayi, ya haɗa hannayensa waye ɗaya kaman mai rokon abu

"Aeesh don Allah ki soni...."

Dago Kai tayi idanunta cike da hawaye tace

"Kafiso ka zama ruwan hawaye na mai sani cikin baƙin ciki a koda yaushe ko?

"Aeesh k...."

"Dakata Zeeyk ,idan ka cigaba da gaya min wadannan Maganganun zakasa na tsaneka"

Daga nan sai ta ratsa shi ta shige Hostel Tana kuka.

Ya dade tsaye yana nazarin ta kamin daga bisani ya kama hanyarsa zuciyarsa Cike da tausayin Aeesh.

Tayi Sa'a kofar dakin su a bude yake kuma Su Reeey sun shiga lectures .

Ta fada kan gado ta cusa kanta tayi cikin bargo tana sakin wani marayan kuka wanda izuwa yanzu har idanunta sun gaji da tsiya yar hawaye, tausayin kanta yakamata Ashe duk soyayyar da Aareef yake nuna mata duk na ƙarya ne?, Ashe Son maso wani take yi?.

Kukanta tasha sosai nan baccin wahala yayi awon gaba da ita

*Ashman*
Yana dawowa daga masallaci kai tsaye part din Deejah ya nufa don ya karta mata warning .

Tana nan inda ya barta jiya tana shaƙar barci.

Ji yayi ransa ya ɓaci Tuni idanunsa sun sake kaɗawa sun koma jajur, yayinda jijiyoyin kansa suka sake fitowa raɗa-raɗa, yasan ko rantsuwa yayi baza a bishi bashin kaffara ba akan batayi sallar asuba ba.

Hambarinta yayi da ƙarfi, ta farka tana mazurai,Bai sake kallon inda take ba ya fada bandaki.

Duk da wani jirijiri da yake gani saboda yunwar da ke cin hanjinsa , rabonshi da Abinci tun bayan wanda yaci bayan daurin Auren Saleem , yq jima a bayin sannan ya fito bayan yayi wanka ɗaure da milk towel , karamin rataye a wuyansa, ya kama can ƙarshen tawul ɗin yana goge gefen fuskarsa da gemunsa.

Deejah na zaune tana jirar fitowar shi, ta dago ta dubeshi hakan yayi daidai da kai nasa duban gareta shima.

Fuskar nan a tamke kaman yaga mutuwar sa,ya kauda idonsa daga kanta tare da nufar mirror kansa tsaye. Kamar yanda baiyi magana ba itama sai bata ce uffanba amma zuciyar ta kaman tayi bindiga sai kumburo fuska takeyi.

tana so ta nuna.masa fushinta akan Fasiqancin da yayi da Aeesh amma da ya dubeta sai taji ta kasa furta komai jikinta yayi sanyi ,sosai kwarjininsa ya hanata sai binsa da kallo takeyi.

Duk da Yasan tana kallonsa amma bai juyoba, amma yana kallonta ta cikin mirror, murya kaman an tilasta shi yace, "Kinyi sallah?".

Kauda kai tayi tace

"Bana sallah"

Ya gyada kai

"Good..."

Sannan Ya dauko abin gyaran Gashinsa cikin natsuwa yake gyara gashin nasa, yana kallon yanda take kallonsa daga inda take zaune.

"Abinda kikagani jiya ya kasance tsakanin Na dake sannan kuma Aeesh, idan kika saki wani yaji abakin auren ki"

Saurin dagowa tayi suka hada ido ta mudubi, ya dage mata gira.

"Ba don tsoro ba,ba don Neman rufin asirinki ba, sai don nasan Bazaki iya rike sirri ba,hakan ce hanya mafisauƙi da zan datse igiyoyin ƙaddararren auren dake tsakanin mu, kuma Inaso abinda kika gani ya zamo ajalinki domin barin Abu irin wannan a zuciya babban makami ne na sanya zuciya ta buga"

"Ashman kaji tsoron Allah"

Ya dakatar da ita

"Ki adana ma ubanki wannan Kalmar yafini buƙatar shi"

Rai bace tace

"Ubana fa kace?"

Ya ɗan ciji lower lips dinsa yana ƙare mata kallo a yatsine yace

"Eh uban naki...!, Yafi ƙarfin a kirashi da kalaman uba ne?”

Sannan ya kauda dubansa daga gareta yace

"Idan kin cika Yar Halak please ki bari wani yaji maganar Nan,tuni na riga na adana Takardar ki, jiranki nake Kizo ki dauka''

Itama kauda kai tayi tanajin zuciyarta kaman wuta idanunta cike da hawaye tace

"Idan wannan Shine burin ka to Bazaka gani ba, bazanso ka sakeni ta wannan hanyar ba, idan baka sona nafiso ka gaji don kanka ka rubuta min takarda ta"

Yar ƙaramar Tsoki yaja

"Aikam yanzu kika fara ganin wulaƙanci,dakanki zaki nemi takardarki, don Ni bazan sakin mace bi gayri dalili"

"Bazan nema ba"

"Nima bazan saka ba"

"Allah na kallo"

"Ki shirya daukar duk wani abinda zaki gani ,ae Na fiki sanin Allahn"

A ɗakin ta ya shirya tsab ya saka kayansa dake dakinta, tana zaune tana kuka , karo na farko kenan da ya taɓa shiryawa a ɗakin ta.

Yana gamawa yace ya tafi duba Aeesh, ya barta anan zuciyarta kamar zata buga .

Kai tsaye gidansu ya nufa, yana isa qawwamah tace ai Abba ya sa ta koma school tun da sassafe .

Ransa a ɓace ya fada part din Abba, ya iske Abba bayanan ,Sai inna saude, Tana bedroom dinsa tana gyara masa gado.

Banko ƙofar yayi da ƙarfi ya fado dakin Yana huci

"Mum Ina ABBA"

A mamakince take binshi da kallo, cikin fushi ya kuma cewa

"Tambayan ki fa nake?"

“Nan dakin Tsarar ka ne da zaka banko kofa babu ko sallama?"

Nunata yayi da yar yatsa.

"Keh na lura da take taken ki kwanan , ke nan har kin isa ki min iyaka da dakin Ubana?, Ke wace da zaki min wannan tambayar?"


"Sufyan Ni kake gayama wannan maganar?, Ni?"

Dakatar da ita yayi cikin tsawa

"Who the hell are you, ke wacece?, Don kin samu na kiraki da mum shine harda min tambayar Rainin wayau?, Kin dauka bansan Abinda ke faruwa bane?, You're nothing but a worthless Househelper ko kin manta sanda Mahaifiyata ta dauko ki daga ƙauye ta rufa miki asiri?, Amma daga ƙarshe she got nothing But Hatred Feedback kika tura danta ya kashe ta...!"

"What ....!"
Tayi exclaiming a ruɗe, sai zufa take dukda sanyin A.c din dakin.

Gira daya ya dage mata

"Yeah I know everything starting from ur worthless life zuwa butulcin da kikayi ma Ammatah, da kwace su Saleem da kikayi daga gareta zuwa Juya ma Saleem ƙwaƙwalwar da kike ƙoƙarin yi da Kisan da kika sa ya aikata nasan Komai, idan na tashi juyowa sai na lashe kowanne a cikin ku, harda uban nawa da kike taƙama dashi a matsayin Miji da har kike ƙoƙarin Yin iko akanshi duk saina Jaku ƙasa, Bastard Winch butulu...."

Daga nan ya fice ya kullo ƙofar da ƙarfi, kai tsaye inda ya parka motarsa ya nufa ya figeta da ƙarfi yayi reverse da sauri securities suka wangale masa ya fita a 360.

Wayarsa ya dauko ya latsa layin Aeesh Amma bata shiga, kai tsaye makarantar su ya nufa, bai tarar da itaba , ya tura mutane sunfi biyar amma duk in sun dawo sai suce bata nan, ya kira layin Reeey itama baya shiga.

Hakanan Babu yanda ya iya dole ya koma gida ransa ɓace, Baya ƙaunar zaman gidan ko kadan don haka sai ya shirya ya tafi asibiti aikam yau Patients dinsa sunji ajikinsu Don gabaki daya a kansu ya sauke Masifarsa.

A asibiti ya kwana don baya ƙaunar abinda zai sa ya sake ganin Mummunar fuskar Deejah a yau dinnan.

Washegari da sassafe ya koma makarantar Amma fa still Babu ita, da ƙyar ya samu wata ta kaishi Inda suke lectures, Chan ya hango Reey da Zeeyk yana zuba

Please Login or Register in order to submit comment