Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Guba ce ba, Tunda Gashi daga Shigowarshi Rayuwarta ya rabata da Natsuwa da jin dadin Rayuwarta_

Jinjina kai Ashman Dake tsaye bakin kofa tun ɗazu yayi, Jiya ya hanata kuka wannan Karon bayajin zai Iya rarrashinta Domin Kuwa shima ya ɗanɗana makamancin Halin Da ta shiga ,Yasan yanda Takeji A halin Yanzu ,  _*Every BLEEDING HEART deserve a rain*_  ,Hawaye ne kadai zai iya wanke kadan Daga Cikin raunin da take fama dashi

A sanyaye ya juya ya bar dakin, Tasha Kuka sosai anan Barci barawo ya sake D'auketa.


Ashman na nan a gida ya kasa ya tsare yasa ma Part din Saleem Ido yaga Fitowar shi, Amma shiru , Saida Aka kira sallar Azahar sannan Ya hango Fitowarshi Ya nufi masallaci shima yana Ganin Fitarshi ya fita izuwa masallacin, Amma ga mamakin sa Tunda ya dawo bai sake sa Saleem a Ido ba har washe Gari ,Da Alama ba'a Gidan Ya kwana ba.


Washe Gari ya kama Monday Babu Aiki sakamakon hutun Amarci da Angwancin da suka samu.

Jiya Kwana Deejah Tayi tana Shan takaici Domin Kuwa Ashman bai bari Komai ya hadasa da ita ba, Throughout Yana maƙale da Aeesh dinsa da zarar tayi masa Magana Ko ta nuna kishin ta akan hakan sai ya taso mata yace da ya riga ya saba da Aeesh, tun tasowar su haka Suke barci ke Rabasu, idan Bazata iya jure ganinsu a Tare ba ga hanya Shi dakansa Ma Zai kaita har Kofar Gidansu .

Ko tayi Girki baya ci Dakansa Yake shiga Kitchen Yayi msu Girki na iya su Biyu shida Aeesh, yakai mata dakin ta, suci tare a nan dakin don Tunda Deejah ta kirata da Bazawara ta daina fitowa Gudun abinda Zai sake hadasu Yasa Ta sake kiranta da Bazawara, Tattali Kulawa Kuwa Babu wanda Aash baya bata duk don Ya kwantar mata da hankali, Sunyi waya da su Ammie tsakanin Jiya da yau yafi a ƙirga kuma Alhamdulillah ta fara samun Sauki An samu Improvement Sosai, Har zuwa wannan Lokacin Su Ammi Basu san Da maganar Sakin Ba,domin Kuwa cikin Su Babu wanda ya hau media tsakanin Jiya da yau .


A Dole Deey ta haƙura ta zura Musu Idanu, Ita kanta Aeesh bata San Deejah najin Haushin Kulawar da Ashman Ke bata ba domin Kuwa tana daki bata fito ba, Saidai in ya fita taga ya fita da dawo da Damuwa a tattare dashi .


Yanzu haka ma Kitchen ya shiga Ya shiga ya haɗo msu Na rana Fried Rice ce sai Ƙamshi yake da ɗaukan Ido, ga Banƙararren kazar da tasha suyan Abban Mero sai Maiƙo yakeyi.


Rubawa yayi a babban mazubi Sannan ya dauko Plates, Knives, cups da spoons ,ya azasu duka kan Tray, babban Jug dake Dauke da Sassanyar Lemun cocumber da yasha Kayan Ƙamshi daddaɗan Ƙamshi sai tashi yake...


Deejah na zaune Parlor tana Kallon Korean Series *business Proposal* Sai Dariya Takeyi ita kaɗai kaman Zararriya, Dawowarta kenan daga Raka Kawayenta, Sun gama Kodata da cewar Allah ya bata miji na gari mai Jida Ita ,Girki ma Shike yi mata.

Ta gabanta Ya wuce,ta bishi da kallo tana Shaƙar daddaɗar Ƙamshin Girkin da Ya bar mata .

Samun kanta tayi da Ambaton Sunansa a sanyaye

"Baby..!"

Chak ya tsaya amma ya kasa Juyowa.

"Baby Please ka rage Min Abincin?"

A hankali ya juyo, ya sauke Sharp eyes ɗinsa Akan nata ,Saurin Kauda Dubanta tayi daga Gareshi tanA ambaton Sunan Allah a ranta

Murmushin Gefen baki yayi Cikin salon Cusa Takaici yace

"Idan yunwa Kikeji ki Biyoni in Mun Rage zamu iya baki”

Daga nan Ya shige Ya barta zaune kaman Gunki tana Auna Kalaman sa Cikin Mizanin Hankali, Amma ta kasa Gano komai illa Zallar raunin hankali, Kasa karasa kallon Tayi ta miƙe ta nufi ɗakinta cikin Kunci.


Kaman Dai Yanda Suka saba, a tare suka ci abincin ,Suna ci suna hira kowanne cikeda murmushi a fuskarshi sai sun burgeka don sosai sukayi matching dajuna ta kowanne fanni, Idan an gaya Maka Aeesh ce aka saka shekaran Jiya Nan take zaka ƙaryata domin Kuwa Babu Alamar damuwa ko kadan a tattare da ita, Abinda bamu sani ba Kuwa Ashman Shine secret behind her Smile, da zarar ya Fita Damuwarta ke Dawowa, har yanzu bata daina Jin Kewar Aareef ba, Kalamansa na bankwana ma har yanzu sun gaza Goguwa a ranta.


Wayar Ashman Dake Hannunta ne ya hau Ruri , sunan ta duba *Uncle Hamza* ne Rubuce da Kananan baki.

Miƙa masa wayar Tayi bayan tayi Sliding , Kara wayan Yayi a kunne yana jin Gabansa Na Faduwa

Baffa ne yayi sallama daga Dayan Ɓangaren, Amsa sallamar yayi Baffa yace

"Sufyan kana gida ne?"

"Eh Uncle"

Ya Amsa masa A takaice

"To ka taho babban Gida Kaida Amaryar ka da dlsakakkiyar Matar saleem yanzun nan, ku kaɗai muke jira"


Maimaita Kalmar Sakakkiyar Matar saleem Yayi cikin ransa yana Haɗiye wani yawu mai ɗaci.

Duban Aeesh yayi yaga hankalin ta gaba daya baya kanta ,Hankalin ta ya karkata izuwa labaran Karfe biyu da ake Haskawa a Bintou Tv.

Ajiyan Zuciya ya sauke yace

"Uncle dama dan Turkish ya taɓa aure ne ban sani ba?"

Ya musanya sunan Saleem da ɗan Turkish Gudun kada hankalinta ya dawo gareshi .

Murmushin takaici Baffa yayi yace

"WhatEver!, you know what I mean muna jiranku nan da 20mins..."

Kit ya Kashe wayar ,bai bari Ashman Ya samu damar fadin abinda ke Zuciyarsa ba.


Dubanta ta maido kanshi,a sanyaye tace

"Hope dai lafiya"

Murmushin yaƙe yayi yace

"Lafiya, su Baffa ne suke neman Mu Yanzun nan a babban Gida"

Ji tayi Gabanta ya fadi

"Neman mu kuma harda Ni?"

Murmushi yayi mata "Eh , harda Deejah"

Ya bata Amsa , Tashi yayi ya Koma Dakin Deejah ya ce ta shirya zasu fita, Sannan Ya fada Banɗaki yayi wanka ya shirya Cikin dakakkiyar Brown Shadda Wacce Tasha guga sai Daukan ido yakeyi,Hularsa daketa maiƙo ya dauko yayi mata kari ya kafa bisa kansa yana dai-daitawa ya fito sak ango abinshi .


Itama Aeesh Cikin Kayan dake cikin Closet Dakin Ta dauko Wata Tsadaddiyar Atamfa Brown Mai ratsin Milk, Ɗinkin yayi mata kyau sosai yabi Jikinta Kallon kanta Tayi a madubi ta saki Murmushi ita kanta Tasan Tayi kyau sosai, bata daura Dankwali ba, Milk din jaka ta ɗauko a Bag hanger Ta saka dankwalin a ciki sannnan Ta dauko Zumbulelen Hijab 4yrds dake Ninke a nan Closet din ta saka, bataga Takalmi ba , fitowa tayi Tana Kumbure Fuska.

Da Ashman Taci Karo yana Shirin Shigowa ,Kallon ta ya tsaya yi yana jinjina kyawun Halitta irin na ubanGiji dukda Hijab Tasa Hakan bai boye Zallar kyawnta ba.

"Yaya ban ga Takalmi ba"

Duban ƙafarta yyi, Sai a yanzu ya tuna ashe Bai Haɗo Takalmi cikin Kayan ta ba, Dafe kansa Yayi yace

"Ya Salam Ko zaki Ari na Matata?"


Harara ta wulga masa Hakan yasshi chanza maganar da cewa

"Muje Sai Mu tsaya a hanya Mu saya ko?"


Murmushi yayi , Ya kama Hannunta suka fito,Deejah na zaune a Parlor har ta Gaji da Jira, Ganin su Cikin matching Color Outfit ya sake ƙona Mata Rai ,farashin tsanar Aeesh sai Sake hauhawa yakeyi.


A bakin Kofar Fita yace ta tsaya, sannan ya nufi Parking lot yayi driving Motar Izuwa bakin Kofar, saida Ya shimfida Mata steping carpet Kasancewar babu takalmi a ƙafarta, Gudun karta taka ƙasa, a haka ta shige Cikin Motar ta samu wuri a baya ta zauna.


Deejah na Tsaye a Parking lot tana Kallon su, Zuciyarta kaman Ta buga don bakin Ciki.


A wani Katafaren Kanti suka Tsaya Sukayi Siyayya ya siya mata takalma kala-kala , Itama Deejah wannan Karon Ya kara mata dukda yasan an sako mata su cikin kayan lefenta.



Basu isa Gidan Ba sai arround 3 na rana,kafin nan kuwa Baffa ya kirasa yafi a ƙirga.


Kowa ya hallara Kama daga kan Daddy da Inna saude, Uncle Hamza (kawu) da Matarsa, Matar Uncle Imam Wacce a halin yanzu Batada Kafa Daya, Da babban 'danta Wazeer dake aiki a nan jaji Kaduna, Shi kadai ya tsira Daga Tuggun yan ta'addan da suka Kashe Baffa a ranar baya nan Yana Chan wajen Aiki, Sannan Ashraff, Abdul Jaleel, SALEEM ,Naseer, nafeesah ,Zainab da Ƙanwar ASHMAN Hafsah wacce suka fi sani da qawwamah su SADEEQ da Kawu Auta ne kadai Basua Nan suma din saboda Basua Ƙasar ne....


A babban Parlon Gidan aka Yada zango Ko ina ya cika ya batse sai Ciye Ciye akeyi domin Kuwa Musamman sukayO odar abinci daga Eatery for refreshment.


Su Ashman Na zuwa aka fara Gudanar da abinda Ya tarasu, Wai Ashe Dawowa Kaduna Sukayi, Sun baro Gidansu Na chan Kano.


Daga nan aka kamo zance akan Sakin Da Saleem Yayi ma AEESH, Babu Wanda Yaji dadin hakan abin mamaki ciki kuwa harda Abba ,Sosai ya nuna Bacin Ransa da haka Ya kuma ce Tunda ya Saketa hakan na nuni da Ya rasata kenan Na har Abada Sosai Ashman yaji dadin Furicin Abba hakan Yasashi sakin gajeruwar Murmushi..

Kama kafar Abba Saleem Yayi yana Roƙosa ya taimaka masa Ya maida Matarsa yana matuƙar Ƙaunarta Sosai ,Idan aka bashi dama ta karshe bazai bari ta Kufuce masa Ba.

Mugun kallo Abba ya watsa masa, Ya dubi Ashman Dake zaune Kusa da Aeesh sai Faman Danna waya yake Amma kacokan hankalinsa na Kansu

Sunan sa ya kira a hankali

"Sufyan"

Ɗagowa yayi ya dubi Abba, kowa Ya zuba masa Idanu.

"Aisha zata dawo Gidannan Da zama As From tomorrow, Anan zata Cigaba da idda ta har zuwa lokacin da Allah zai Dawo da Mahaifiyarta lafiya"

Dadi ne Ya cika Zuciyar Deejah,Duban Abba Yayi akaikaice yace

"But Dad sai nake Ganin Kaman Kun shiga Sabgar da ba naku ba"

Duban juna abba da Kawu Sukayi a tare suka hada baki wajen fadin


"Sabgar da Ba namu ba?"

Ginjina kai yayi

"Eh ... Sabgar Habeebty bai kamata Ya shafe ku ba ,domin kuwa ko ada chan Lamarin ta bai taɓa damun ku ba"


A fili Suka maimaita Kalmar Habeebty, Shi kansa Bai san haka yace ba saida yaji Suna Maimaitawa, Sunkuyar dakai yayi a dan Kunyace, Gabaki daya yan matan Dakin Suka kwashe Masa Da Dariya.

"Me kake nufi?"

Abba Ya faɗa cikin Tsare shi da Kallo

Ɗagowa yayi ya dubeshi ,Amma ya kasa Cewa Komai domin Kuwa bashi da amsar da zai bashi.

Duban Deejah Da Idanunta Ya da idanun ta ya fara kawo Ruwa Yayi ,ya kuma maida Dubansa Ga Ashman Da ya kasa Kauda Idanunsa Akan sa.


"Kiyi Haƙuri Daughter...!, Cancantar Da mutum ke bukata domin FarinCikin Aure shine haƙuri, nasan Kina fama Amma daga Yanzu komai yazo Karshe I have the final say! ,na Karɓe ɗiyar Yar uwata, Ta dawo gidan Nan da zama"

Ya ƙarashe maganar Cikin Dakakkiyar Murya


"Dad Bana son jayayya dakai Amma barin Ihty a tare dani Shine mafi cancantar Adalci a Gareta"

Ashman Ya fada a Sanyaye, Duban Ashman Abba yayi yana Hango Wasu Abubuwa Masu kaifi Cikin kwayar idanunsa, Ga Fuskar sa Da ya Fara Tashi Alamun Mutumin Ya fara Harzuƙa.

Cikin fushi Abba yace

"Really?, kanaso Ta dawo gareka!, tabbas Zata dawo gareka Ni dakaina zan baka Ita, In damƙa maka ita a matsayin Mata Ka kasance Da Ita na har Abada"


Take bugun zuciyar Saleem da Deejah ya k'aru, razane duk Suka Ɗago Suna duban Abba fuskar ko wannensu dauke da Matsanancin tashin Hankali.

"Amma Ka Amsa Min A gaban Kowa...!, kana SON TA?"


Wannan Karon Ashman ne ke duban Abba cikin Matsanancin tashin Hankali, Yana Haɗiye wani irin yawu mai ɗacin Gaske Tabbas Abba yasan Amsar da zai bashi Shiyasa ya gindaya Masa waNnan sharaɗin

Sake Sako masa Tambayar yayi a karo na biyu sannan ya dora da cewa

"This is Ur Last Chance, Idan ka Amsa Min a gaban Kowa Ka Amsa Kana Sonta itama Ta ce tana So Tana Gaba Idda Zan Aura Maka ita”

Dubansa Yakai ga Aeesh wacce Itama Shi take kallo, hawaye Sun tattaru a Idanunta , a hankali ya fara bin Dakin Da kallo kowa ya zuba masa Ido yana tsumayin Amsar da zai bada.

A hankali ya fara Motsa bakinsa Cikeda tashin hankali, Muryarsa ko fita bayayi sosai ,amma kasancewar Shiru ne ya Ratsa dakin Hakan Ya sa Muryarsa Fitowa a hankali

“Bance a bani Auren Ihty ba, Cewa nayi ta dawo wajena da zama.."

Katseshi Abba yayi da cewa

"Amsa Min Tambayata Sai Ka tafi da ita"

Shuru ya sakeyi For some Seconds, Saida Abba ya sake Maimaita Tambayansa Kafin Ya ɗago jajayen idanunsa Cikin Lowering Voice ɗinsa yace


"Abba Meyasa Ka nace sai na Amsa Maka?bayan Ka Sani Ihty Haramtacciya ce a gareni, ina Kaunar ta Kaunar da Ta wuce So, Amma a matsayin yaya Da Ƙanwarsa.....!"








Haramtacciya Kuma?

How Comes!


Nasan Duk yanda Akayi Something went wrong Somewhere 🤨🤨🤨





Nayi Gabas 🚶🏻‍♀️
Comment
And
Share 🙏🙏🙏


Bintou 📌✍️

31st July 😌
[8/1, 11:04 AM] Bintou: 🫀🗡️ _*WUƘA A ZUCIYA*_🫀🗡️


_[B l e e d i n g H e a r t s]_


*025*



"Abba Meyasa Ka nace sai na Amsa Maka?bayan Ka Sani Ihty Haramtacciya ce a gareni, ina Kaunar ta Kaunar da Ta wuce So, Amma a matsayin yaya Da Ƙanwarsa.....!"

Wani k'asaitaccen murmushi Abba yasaki, Wanda ban ta6a Sanin ya iya shiba

"Speak Up so that munsan decision ɗinda ya Kamata muyi Making"


Shuru Ashman Yayi masa Tareda Duƙar dakai Yanajin Gabansa Na wani irin Faɗuwa, Yana matuƙar tsoron Irin faduwar da gabansa keyi a halin yanzu saboda ba alheri Yake haifarwa ba,

Gefe guda kuwa Sai a yau Ya tabbatar Da Rashin Mutunci Tareda Rashin Kunya Irin na Abba, Ya zama sanadiyyar Da Aeesh ta zama Haramtacciya a gareshi Tun tana Yar Ƙarama ,a kullum Cikin Addu'a Yake Allah ya Goge Masa Abin A ransa, Amma Sai gashi Yau Abba dakansa Yake neman Tado da zancen, ko Kunya bayaji.

"Ashman Ka Amsa Min Tambayata Kana Sonta?"

Muryar Abba Ya sake Dokan shi a karo na biyu.

Girgiza Kansa yayi batareda Ya iya cewa komai ba, ya matse idanu kaɗan saboda sara masan da kansa yake na azabar ciwo gabansa na Cigaba da bugawa da karfi, ya sauke numfashi kafin ya Dafe kansa da Ƙarfi.

Idanunsa da ke jajir ya ɗago yana saukewa akan Abba Da Baffa , cikin hanzari suka Kauda dubansu daga Gareshi.


Sake Maida Kansa Yayi kasa ba tareda ya ce dasu Uffan ba .

Sosai Dakin Ya dau Shuru ana duban Abba da Ashman Cikin Tsananin Mamaki da Alama Su biyun Akwai wani Boyayyen Abinda Suke ɓoyewa, Gashi Kalmar Haramtacciya Sai yawo yakeyi a zukatan su.

"Yayana Are You Okay?"

Jin sunansa Muryar Wacce ta kirashi ne yasashi janye hannunsa daga Kansa tare da ɗago manyan idanunsa da ke a jajur ya sauke akan ABBAN nasa, cikin dakewar murya yace

"Abba Bana Sonta....!,"

A mugun Mamakimce Duk suka Kai dubansu Gareshi ,Aeesh Ma Kallonshi take Cikin Firgici Amma Ya riga Ya maida Kansa Duke bai ma san Sunayi ba, A hankali ta rintse Idanunta Hawayen Da suka taru a Idanunta Suka samu Damar Gangarowa.

Baki Abba ya washe, Wannan shine Right Moment ɗin da ya Kamata yayi Amfani dashi don Cimma Burin sa ,Dole Aeesh ta zama nasa Shi kadai.

Dadi ne Ya cika Zuciyar Saleem a cewar sa yanzu babu Abinda Zai shiga Tsakanin Auren sa Da Aeesh, zai maidata cikin Salama Babu wata Matsala.


Deejah kuma murna Ta hauyi ayau Allah ya rabataa da Fargabar Za'a Kwace mata miji,Yanzu zata maida Hankali ne kan Yanda Zata jawo Hankalin Ashman ya karɓi Soyayyar ta.

Cike da kasala mai tare da nauyin jiki Ashman Ya miƙe ya fara Takawa da niyyar barin wajen.

Hankalin Kowa ya Karkata kansa Gabaki Daya ido su Akansa yake, wasu Kallon Tausayi Suke binsa dashi Domin Kuwa yanayinsa Na yanzu yafi kama da siffar Tausayi.


Dakatar dashi kawu yayi da ambaton Sunansa


"Sufyaan!"

Chak ya tsaya Amma bai juyo ba

Baffa dake ƙoƙarin zubama kansa Malt a kofi ya sake katseShi da faɗin

“ina Zaka ba'a tashi Taro ba?”.

Ya kai ƙarshen maganar yana Kurɓar Malt din

Juyowa yy a hankali,idanunsa jajur ya ɗago ta kalle Abba, shima kallon nashi yake, amma sai Abba ya janye nasa idanun ganin yana neman rikitashi,

Murmushin yaƙe Yayi a Cikin bazata yace

“Ga Ihty Kuyi yanda Kuke so da Ita , Ba gidan Ka ba, Ko a dakin ka ne Kasata, Abba Kayi Yanda Kaso, Amma Ka sani Na harhaɗa komai Kiris ya Rage ...!Ka gaya Min A baya Hujja Ake buƙata domin a kama Me Laifi Hakan yasa Na zama Mai ɓoye sirrin Kowanne a cikinku !, Amma ba shiru nayi Ba Motsi nakeyi cikin Duhu"


Cikin ɗan ruɗewa da kalaman Ashman na bazata Abba ya maida Dubansa Ga yan dakin da a halin yanzu Shi Suke kallo, Suna binshi da kallon tuhuma.


Gira ɗaya Ashman ya ɗage sama, ya janye idanunsa da ya fara canja launi ba tare da ya tankama Sake Furta komai ba, cikin nuna halin ko in kula ya mai da hankalinsa ga Baffa

“Tabbas bai kamata in Tafi ba, Ya kamata In tunasar daku Abinda Kuka manta, Naso na Tafi na Bar su Daku ta yanda zaku Fahimta ,Amma da Alama so Kuke Kowa Yasan komai"

Nan Take Hankulan Kowa Ya sake Karkata akansa Taɓe Baki yayi Shifa ya tsani Kallo, Shiyasa Ya tsani taro Ko wanne ne,fuska a ɗaure yana wani hura hanci da fesar da iska yace

"Abba Mema kace?, cancantar Da mutum ke bukata domin FarinCikin Aure shine haƙuri?"

Yyi Maganar Yana Takowa Gaban Abba Da ya Koma Tamkar Gunki, banda Zufa babu Abinda Ke karyo masa


"Bayan Wannan Akwai Wani Abu BABA ,Kun Gani a tarayyar mu *Shaukin Tarayya* shine Cancanta Mafi Dacewa , Ya kamata Ka gane cewa Shaukin Tarayya Yafi Soyayya girma, Rayuwar Aure Mai Cikeda Shauki Take Buƙata ,Ka Aura Mata Shalelenka don Yana Sonta Da Ace Akwai Shaukin Tarayya da bai Saketa akan Abinda bai Kai ya kawo ba"

Dubansa Yakai kan Saleem Dake Duƙe a kasa Ya kasa Ɗagowa Ya haɗa Ido dashi

"Ba Tilastawa ko Auren Wacce Kake so bane ,Shauki na nufin Nuna soyayya a aikace !, kowa Cewa Yake yana Soyayya Amma nawa ne ke nuna Soyayyar Su a aikace? , Soyayya bashine Samun Wacce Kake So ba, Kaso Asoka sannan kuma ka kaddamar mata da su ne cikin farin ciki ta hanyar da dakanta zata Gamsu dakai ta kuma Amince"

Sake kafe saleem da Idanunsa Yayi ya kankantar da Murya

"Inda Ace ka kwantar dakai ka Nuna Mata Soyayya a aikace, da Ka ɗanɗana Zallar Soyayya, Nasan Ihty Batada Matsala Akwaita da Tausayi Zata Soka da Aminci, Idan ka kasa Iyawa da Kanka Babu wanda Zai iya maka, ma'anar Aure tsakanin Mutane biyu ma'ana ce ta Farinciki , Amma kuma sai taka ta kare a Gantale ma'ana Baka san Darajar Auren ba ma"

Dan Dakatawa yayi Yana jin kansa na cigaba da sara masa Sosai kaman Zata Rabe gida Biyu, Cikin dakakkiyar Muryarsa Ya cigaba da faɗin

"Madadin a koya Maka yanda Zaka gane darajar Aure?, Nan da kwanaki kana zuwa Masu da zancen Maidata Zakaga an goya maka baya ,An fara mata hudubar tayi hakuri,ita ba Mutum bace?, Meyasa Bazakuyi considering Nata Feelings dinba?, Nasan Taron nan Tun farko ba don haka aka Hadashi ba, Taramu Akayi domin a maida ma Saleem matarsa, ba don Matar Uncle Imam tasa baki ba sa yanzu ana shirin kai ta"

Idanunsa Ya rintse da Karfi

"Gani nake kaman tilasta ta Kuke tayi Rayuwar da babu Ruwan Wani !"

Duban sa Ya maida Kan Abba

"Banaso Ihty tayi irin Rayuwan nan Tareda Abokin Rayuwar ta,So nake su shaƙu, Su Samu matukar Yanci da shaukantuwa da juna"

Tsawaitawa Yyi yana Maida Numfashi kaman zaki, Ashman bai cika Dogon magana ba, yafi ganewa Ya dunkule magana Duk Girman Ta , Abinda zaisa Yayishi dalla dalla ba Karamin Abu bane.

Tsitt ɗakin yayi bayan tsawatarwar da akayi,Cigaba yayi da

"Ihty mace ce da ta iya Rayuwa, domin Tabbatar da farinCikin wani takan iya sadaukar da nata ,Ihty Mutum ce wacce tasan da cewa Shauki yanada matuƙar Muhimmanci , Tareda Sanin cewa Soyayya nada Matuƙar Illa Musamman idan kana so ba'a Sonka Shiyasa Ta sadaukar da nata jin dadin Ta yarje wa Auren wanchan shashashan, Amma da yake Shi Gaula ne Baisan Ni'imar da Allah yayi masa ba sai ya Banzatar da Alfarmarsa, ka kasance tare da Mutum ya nuna mata Soyayya suyi hira dashi mara ƙarewa Course ne na Shauƙi mara Ƙarewa"

Takowa yayi Gaban Baffa, Hakan Yasashi Saurin Miƙewa ,ya dire Cup din Malt ɗinsa A Hankali

"Me ma kace kawu?, Taro bai Kare ba?, tabbas Taro bai Kare ba, Kuma idan Ina wuri Bazai taɓa ƙarewar ba ,Akan Mutuwar Auren da Babu Soyayya kuma da Kokarin tauye hakkin Wacce bataji ba bata gani ba zan iya kwana Ina Jawabi, Rashin sanin Wadannan Abubuwan Shiyasa na boye sirrina domin Na bashi dama, Yanzu Cikin Alfahari a gaban Ahali gaba ɗaya na fada zan kuma maimaita *Bana Son A'isah* !, Ayi Mata aure da wanda Take so Yake Sonta wanda , Wanda Zasu Kasance tare da juna Cikin Shauki Tareda Hira mara Karewa!, zuciya takan Ba mutane da dama Dama, Amma Dama Ta haƙika Mutum daya Ake bawa Ita...!"

Komawa Yayi ya zauna A Kujerar da ya tashi, Ya ɗora kafa ɗaya bisa Ɗaya

"Mutane da Dama Suna Sonta,, Amma Ita tanada wanda Yake Sonta da gaskiya kuma Tana Sonshi,, Na fahimci akwai Shauƙi na tarayya a tattare dasu , Na yarda Ihty ta zauna anan har Yan gidan su Sudawo ,Kafin wannan Lokacin Ni zan Tabbatar Muku da Wanda Yafi dacewa da ita ... Har yanzu labarin bai fara Ba!, Wannan Somantaɓi ne"


Idanunsa ya rumtse da ƙarfi saboda Sarawan Da kansa yayi masa A lokaci guda.

Sam babu wanda jikinsa baiyi sanyi ba, Gashi Duk iya auna Kalamansu Basu Gano Asalin Inda Zantukansa Suka nufa ba.

Tafi ASHRAFF ya farayi Cikin karfafa gwiwa yace

"Tabbas Saleem Bai cancanci Rayuwa da Aeesh ba, Shiyasa tun bai Shiga daki Ba Allah ya kawo karshen zamansu, a barta tayi Rayuwa Kaman Kowa!,a barta taji da Abinda ke Damunta ,and Nima na Bana Goyon bayan Ta cigaba Da Zama da Me mata dayan Nan Domin kuwa Takura msu Zatayi ,nan Dinne yafi dace wa da Ita”

"Kai Yaya Anya Maan zai iya Rayuwa babu ita kuwa?, Ni sai gani nake kaman ciccika baki ne kawai Irin nashi”

Cewar Abdul yana kallon Ashman A kaikaice

"Ni Bama Wannan ba, Ni So nake a maida ma Yaya Saleem Matarsa Asirin kowa a rufe, tunda Yana Sonta"

Inji Nafeesah

"Eh mana ban Taba Ganin Kukan Yaya Saleem ba sai a kanta, ji yanda Nagartaccen Namiji Irin Yaya Yake Durƙushe a ƙasa With his Pride lowered Duka Akan Mace, mutumin Da mata basu Gabanshi ,gaskiya idan Anbi ta Yaya Suff an cuci Saleem"

Cewar Zee Cikin Rashin Kunya.

Tsawa Ashraff ya daka mata wadda ta sakasu firgita har tana neman rasa Nutsuwanta

"Shi Tsararki ne?"


Tsaki mai ƙarfi Ashman yaja yana Miƙewa, dama zuciyarsa a saman maƙoshi take sosai.

Duban Deejah Yayi

"Mu je"

Miƙewa Tayi tabi bayansa ranta fesss,Taku yake a hankali har ya fita

Binshi Da kallo Aeesh tayi ta kasa Motsawa Daga inda take,Hawaye na Gangarowa saman Kumatunta,ta kasa dakatar dashi Har ya Fice, Bata Son ya Tafi ya barta, bata son Zama dasu Ko kadan, bata Ƙaunar Kaddarar Da zaisa ta sake zama Cikin wannan Ahalin a karo na biyu.

Kamar ruwa ya cinyesu haka falon yay tsitt suka bishi da kallo har ya fice.

tsitt falon yayi banda Kukan Aeesh babu Abinda ke tashi a dakin, Babu Abinda ya sata Kuka face Yanda Ashman ya fada a gaban Kowa cewa Baya Sonta , Kuma Ya yafeta ga Su Abba.

A masifance Umma Saude ta taso ma Ashraff Da masifan akan Me Zai daga ma 'ya'yanta Murya don Sun fadi Gaskiya...!, shima Tsawan ya daka Mata Cikin nuna mata Tsantsar Gaskiyan dake tattare da kalaman Ashman batareda Yayi la'akari da Ita din Mahaifiyar sa bace.

take falon ya hautsine da hayaniya, Aeesh dai tana daga gefe ta Takure waje Guda tana kallonsu, sai dai bata fahimtar komai.

Abu kamar wasa saiga gidan ya harmutse sosai, Matar Kawu Imam sai fama take dasu amma sunƙi suyi shiru, ganin hakanne ya sakata Ficewa ta ƙyalesu, Aeesh kuma ta fashe musu da kuka mai karfi.



Tsitt falon yayi , Cikeda Tausayin ta Qawwamah tayo kanta Ashraff kuma ya fice abinsa rai ɓace, da sauri Naseer yabi bayansa, Abba da Baffa ma suka fice, a sanyaye Saleem yabi bayansu.

A fusace Zee da Nafeesah suka hauta da masifa,batareda Sunyi la'akari da halin Tashin Hankalin da take ciki ba kiyayya ce sosai na hango a idanun Kowanne a cikinsu, In ka cire Qawwamah Ƙanwar ASHMAN

Wannan lamari nasu yayi matuƙar bani mamaki sosai, har yamma suna Rikici, Abinda bai taka Kara ya karya ba sai Su hau Fada akai, Dama Haka Ahalin Yake Kullum Cikin hayaniya,

Please Login or Register in order to submit comment