Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai wanda na aminta dashi"

yafada yana jindadin moment din ya tabbatar Mata da cewa Har yanzu batayi matsayin da zata Gindaya Mashi Sharru'da Yabi ba, daga ita har yayan nata Sunyi kaɗan

"Bana so, Bana so ka bani wayata"

“Then Fine, Tunda Bakyaso Kinga Nima na huta da Fargabar wani zaiji min Muryar ki,Kinga Sai mu zauna Muyita jin Muryar Juna nida ke"

Lumshe idanu maryam Tayi tana qoqarin saita muryarta

"Look, Kai Kanka kasan Zaman Haya nakeyi a gidan ku babu Wata batun Bayan wannan, bakada hurumin Hanani Amfani da wayata"

tafada muryarta nadan cracking.

Un folding Hannayensa Yayi ya tako gabanta cikin takun qasaita.

"Really? Zaman Haya Kike yi Amma, kika tare a Part dina? Wannan wacce iriyar salon Zaman haya ne?"

Hadiye wani Abu daya toshemata maqoshi tayi kafin tace

"Ba aurenka nakeyi ba, kai baka kai darajar da zaka mallakeni ba, saboda kayi min kadan"

tafada idanunta na ƙara zubda ruwa.

"Then ki Shirya zaman hayan da kyau, Ni mijinki ne ,biyayya a gareni dole,and ban Amince ki taka ki fita koda bakin Ƙofa ne ba,don Makulli zan riƙa sawa, Bakida alaƙa da Mutanen gidan Don Haka bakida Hurumin Fita , idan kuma ya kama dole sai kin fita ki nemi izinin Mijinki"

Ya ida zancen cikin rad'a

Kasa riqe hawayen tayi, tayi saurin kauda Kai tasa bayan ta sharesu, ji take kamar ta shaƙeshi ya mutu don takaici.

Murmushin gefen baki yayi na mugunta ,Dukda digan Hawayen ta na taɓashi, amma ya dau Alwashin Ganar da Ita Kuskuren ta na Sashi Kwana a bayin Gidansu da Sawa da tayi karnukan Gidansu suka biyoshi da tayi.

"Bar kallona, ki maida hankali kan Abinda kike soyawa karki Ƙona Mana Gida"

Sai a yanzu ta tuna ashe ta zuba Irish Kan wuta, dubawan da Zatayi taga ya koma baƙin Ƙirin kaman Gawayi.

Lumshe idanu tayi tana qara bama hawayenta damar Gangarowa, Tsanar sa na sake cin zuciyar ta, a ƙufule ta Juya zata fice daga Kitchen din, ya riƙo hannunta

"Ina zaki?, Who'll clean All these trash?"

Ahankali ta dago idanunta ta zubamashi, gabanshi ne yafadi ganin kallon tsantsan tsana datake mashi sun kasa Ɓoyuwa a kwayan Idanunta,ƙwace hannunta tayi ta nufi Ɗakinta da Gudu tana kuka

Furzar da iska yayi yana lumshe idanu cikin jindaɗi, Koba Komai yau ya birkita yar Mutane, tunowa yayi da Uban Sharruɗan da Suka Gindaya masa , yayi dariya a fili yace

_Auren wata Ukun Bura*b*!_

Ɗakinta Yabita, kafin ya iso har ta Kulle ƙofar, cikin daga Murya yace

“ki fito ki gyara Min Kitchen,Or else I'll lock you In"

Daga haka ya juya ya nufi Dakinshi, yayi wanka ya Shirya sannnan ya fice, daga gidan Gaba ɗaya bayan yayi Locking Part ɗinta da Key......










THOFA 🏋🏻‍♂️, ANYA SALEEM BAI TARO RUWA BA KUWA?

DADDY NA HANYARSA NA ZUWA KD

KUMA DA AKWAI MATSALA IDAN YA ISKE MARYAM BATA GIDAN, (KUNSAN DAI BAISAN TAYI AURE BA!)

GASHI SALEM YA RUFE GIDA YA TAFI DA MUKULLI 🤔

YAYA KENAN?, WANE MATAKI KUKE TUNANIN MARYAM ZATA DAUKA AKAN SABA ALƘAWARIN DA SALEEM YAYI?.

SHIN MENENE ALAƘAR DAKE TSAKANIN INNA YATHAI DA ABBA?

YA ZATA KASANCE TSAKANIN AEESH DA ASHMAN...!, DA KUMA ASHMAN DA MATARSA?

YA JIKIN AMMIE?, NAGA ALAMA KAMAN KUN FARA MANTAWA DA ITA KO?, THOFA TANA NAN ASIBIN MU MUNA BATA MAGANI🏋🏾‍♀️😃

NAYI GABAS 🚶🏻‍♀️

BINTOU ✍🏼

23rd September 🤸🏽‍♀️🏋🏾‍♀️
[9/25, 1:26 PM] Bintou: 🫀🗡️ *WUƘA A ZUCIYA*🫀🗡️
_BLEEDING HEARTS_




_*GAMJI WRITTERS ASSOCIATION*_

_Home of Exceptional writters_





*Bintou✍️*



*039*





*RECAP*

Furzar da iska yayi yana lumshe idanu cikin jindaɗi, Koba Komai yau ya birkita yar Mutane, tunowa yayi da Uban Sharruɗan da Suka Gindaya masa , yayi dariya a fili yace

_Auren wata Ukun Bura*b*!_

Ɗakinta Yabita, kafin ya iso har ta Kulle ƙofar, cikin daga Murya yace

“ki fito ki gyara Min Kitchen,Or else I'll lock you In"

Daga haka ya juya ya nufi Dakinshi, yayi wanka ya Shirya sannnan ya fice, daga gidan Gaba ɗaya bayan yayi Locking Part ɗinta da Key......


*CONT....*
Abba na Dawowa Daga Sallar Subh ya nufi ɗakin Aeesh , kudi ya bata yace ta tattara inata ta koma Makaranta, babu musu ta karɓa ta tattara inata ta bar msu gida batareda ta bari wani ya sani ba ,A ranta ta dau Alwashin bazata sake dawowa cikin gidan Nan ba, Koda shine ƙarshen Hope ɗinta a nan gaba, ta gommace Ta kwana a gidansu Ita ɗaya inda babu mai Takura mata.

Babu wanda yasan ta tafi saida akazo yin Breakfast Inna Saude Ta Lura da babu ita ,Abba yace Ta koma makaranta, hamdala tayi Dama Bata ƙaunar Yarinyar nan.

Inna Yathai kou Bata ji daɗi ba Ko kadan ,Amma Babu yanda ta iya, haka Goggo koda ya kasance Duk zuwanta sai sun samu saɓani Amma tafiyar ta bai mata daɗi ba.

Tana Fita ta Tare mai Napep,ya Sauketa a Kano Road, tana tsaye a inda ake Lodin KASU GATE,yau Sunday Babu Masu zuwa KASU sosai hakan yasa Ta jima tana jira, tana zaune har kusan 39mins babu Passenger ,Sai ta fito ta jingina da Napep din.

Ta saka Airpod a kunnenta bayan tayi Connecting da Wayarta ta kunna Karatun Alƙur'ani Ahankali tahau bin kira'ar datake ji acikin Airpod dinta na ƙira'ar Abdullahi Abba Cikin Suratul Nisa'i.

Tun dazu take jinta somehow tanajin kamar ana kallonta ga wani Strange ƙamshi wanda bazata iya cewa na menene ba datakeji amma dayake hankalinta baya wajen bata kawo komai aranta ba.

Ita Ayi ayi A cika Napep ta tafi kafin gari ya Ida wayewa don har yanzu garin bai gama wayewa ba , Idanunta a Lumshe a hankali Ƙira'ar ya fara wanke Damuwar da ta ke tattare dashi.

Yana jin Labarin Aeesh a bakin Ƙanwarsa, tasha Gaya masa Kamanninsu Sak da Sureey, yasha Ganin hotunanta hatta hotunan Bikinsu ya gani, Amma ganinta a zahiri bai Hanashi girgiza ba, Tabbas Allah mai iko ne, Babu Abinda Aeesh ta baro cikin kamannin Sureey komai nasu iri ɗaya.

Sosai zuciyarshi ta kumburo don shauki, ji yayi yayi Missing babe Ɗinshi Sureey,he wish she's here To see her Twin sis ,he can Imagine The joy, how happy she'll Be.

Ahankali yake sauke numfashi yana kallonta yanajin kanshi na qara girma don shauqi da FarinCiki Kai kace Yar uwansa ce ya gano, Camerar 📷 sa dake rataye a Wuyansa Ya zaro ya Fara Takawa a hankali, har ya iso gabanta.

Sai a lokacin Ya farajin sautin muryarta dake futa a hankali cikin Wata irin Raunanniyar Murya mai sanyi.

Sosai ƙira'ar ta fara affecting dinshi don jiyake kamar yana melting ne ahankali

Ahankali ya dago Camerar sa yanufota ahankali yana kallonta yana kallon yadda bakinta ke motsi a hankali .

Haka nan take jinta very uncomfortable jikinta harwani tsuma yake hakan yasa tadan ware Idanunta da Suka sauya kala zuwa Pure red.

Ganin kamar inuwar mutum a gabanta yasa tayi saurin Ɗagowa.

Ganin mutum daff da'ita ya haskota da camera yasata ware manyan idanunta ta bude baki cikin Ruɗewa tana ja da baya.

Kyssssss, Kyssssss

Taga ya D'auketa hoto,hannu tasa Ta rufe Fuskar ta ,nan ma sai ji tayi ya ɗauka.

Hannunta ta cire a fuskarta ta bishi da Kallo a mamakince, tace

"Malam Lafiya?”

Gyara tsayuwarsa yayi yace

"Lafiyar ce ta kawo hakan, Sunana Zayn Amma ana kirana ZEEYK "

Yamutse Fuska tayi tace

"And So?, Na tambayeka ne?, Meyasa Kake dauka na Hoto?"

"Saboda naga Kin mn Kyau, So biyani Kuɗin daukan Hoton Sannan Ki bani Numbern ki in turo Miki Ta WhatsApp Innayi documenting ɗin shi"

Hararar sa tayi tace
"Ji min Mutum Da ƙarfin Hali?, Na aike ka ne?, Ka riƙe hoton bana so"

Murmushi Yayi yace

“Tho na gode da wannan Gagarumin kyautar Ranki ya daɗe, ko ba Komai zanyi framing Ɗinshi a ƙaton Madauki na Manna shi a ɗakina Ya zame min Abin kallo a duk Sanda na farka daga Bacci”

“Hoton nawa?”

“Hoto na dai, Tunda kinƙi Biyana Kudin aiki Kinga ya Zama nawa Sai inyi yanda naga dama dashi”

Turo baki tayi tace

“Ni dai ban yarda ba, ai bance ka ɗauke Ni ba”

“Nima Bance ki tsaya inda zan ganki ba saboda..."

Sai ya ɗan yi Shuru yana kanne mata ido

"Saboda me?"

"Saboda kina da kyau!"

Cameran sa ya rataya a Wuyansa ,Ya zaro card ɗinsa daga Aljihu ya miƙa mata

"Idan kina Son Hotunan Ki Call me, Remember My name ZAIN ZEEYK *The Photographer* ,Bye"

Naga Nan ya Juya gudu gudu sauri sauri ya wuce batareda ya bata daman furta wata kalma ba

Mutuwar tsaye Aeesh tayi, da catin a hannu Haka kawai sai taji salonsa ya burgeta.

Murmushi ta saki ta saka Katin Cikin jaka, daidai lokacin da Napep din ta cika, ta shige ciki aka jasu sai makaranta.

Koda maryam tashiga daki kuka ya kufce mata ta toshe baki da tafin hannun ta tana kuka.

Dagudu tafada kan gado tana kukan, Shikenan dagaske saleem na neman Kawo ƙarshen Rayuwar ta, Bazai Barta tayi Farin ciki ba, Yar auren da sukayi na Yarjejeniya ma so Yake ya Maidata Auren Gaske ta ƙarfi da yaji.

Tana kwance taji Muryarsa Yana cewa ta fito ta gyara msa Kitchen , dagannan taji ƙarar Rufe ƙofofi, take taji Duk ilahirin jikinta yayi sanyi, gabanta ya tsananta bugu ba dai kulle ƙofofin yayi ba?.

Sake cusa kanta tayi cikin bargo tana sakin wani marayan kuka wanda izuwa yanzu har idanunta sun gaji da tsiya yar hawaye, tausayin kanta yakamata ,tunanin yanda Zata kasance A cikin Gidan saleem Kuma a ƙarƙashin ikon sa take, Saleem Akwai iko da isa haɗida iya Mulkan mutum ,bai iya samun dama Ba, idan ta sake ta bashi damar da zai Mulke ta ta kaɗe.

Share Hawayenta tayi a bayyane tace

_*Baka isa ba Saleem..!, Dole kabi Ƙa'idojin mu yanda Muka tsara*_

Miƙewa Tayi tana Share hawaye ta fito Parlor , Da mamakinta ya datse Ko ina, Parlor da Two bedrooms dinsu ne kawai a buɗe hatta Ɗakunan sama Duk ya sa masu Key, cikin Tashin Hankali ta fara binciken gidan Tana neman inda ya ajiye mata waya da kuma bincike ko zata ga Spare key ammau Babu su babu labarin su, tayi kaca kaca da gidan ta tarwatsa hankade komai na dakinsa amma babu, Abinda Bata sani ba, bai bar wayan a gida ba, fita yayi dashi kuma Spare keys na chan Ɗakunan sama.

Cikeda takaici ta fara maida kayan da ta tarwatsa ma'ajiyan su Wata ƙaramar Closet ta Gani jingine a gefe ,ta jawoshi ta Buɗe ta fara fidda kayayyakin dake ciki, chan Kasan Closet din Taga Tsohuwar Wayarta wanda Aka ƙwace a hannunta bayan an harbeta kwanaki.

Tsayawa tayi tana mamaki, Ashe shi ya shirya Komai no wonder Shiyasa Ya Bata Jininta 🤔, a dai yanda Tasan Saleem mara Mutunci bazai iya bada Koda Yawun bakinsa ga mace ba koda ace tana gargarar mutuwa ne indai sai ya bata zata rayu Ya Gummace ta Mutu bai bata ba, amma sai gashi Harda bata jini abin ai is mamakious .

Tunowa Tayi da yanda ya ruɗe a kanta lokacin da take gadon Asibiti, kullum sai yazo , a lokacin ma'aikatan Asibin da dama sunce ya sauya don baya shiga harkar kowa koda sun taɓoshi ne saide ya dubesu ya Basar.

Kodai Ramuwa yayi?, Ramuwan Dukan da tasa Akayi masa sanda Suke TURKISH?, Tho ai shi ya fara Tsokano ta, kuma da ta rama anyi Raba daidai ☹️, Meyasa Bazai fita Rayuwar ta ya daina neman ta da faɗa ba?, tho yaseen Yanda yasa Aka harbeta aka zubar mata da jini Shima sai ta Zubda masa da Jinin Shima, Allah Sarki bawan Allah da aka kama akace shine ya harbeta Ashe babu ruwan shi , ga babban Criminal Nan, InshaAllah Anjima in sun hadu da Daddynta zata sa a sakeshi sannan sai Tasan yanda tayi ta koya ma Saleem Hankali.

_Allah sarki saleem 😔, Maryam Rashin Sani yafi dare duhu_

Fitowa tayi ta kunna wayar 7% ne a ciki , hakan yasa tayi plug-in Ɗinshi a charji, ta koma ta maida Komai ma'ajiyar Shi .

Atleast Ganin Wannan Wayar ya share more than 50% cikin Damuwan ta, Evidence dinda take Tunanin sun tafi Sun dawo, kuma Zata Kira ZEEYK ta sanar dashi Abinda ya faru, su shirya yanda za'a yi kada Dad ya fahimci komai.

Minti 30 tsakani ta ciro wayar a charji ta danna numbern Zeeyk ta kira , Bugu ɗaya ya dauka, Lokacin Ya shigo Gida kenan Already Dad ya Riga Yazo, sai Tambaya yake ina Princess Ɗinshi ?.

“Hello Princess kina Ina?"

“yaya Akwai matsala fa?"

"Ban gane akwai matsala ba?"

"Ya fita ya kulle ƙofa, kuma ya kwace min waya, kaga da dayan Layina na kiraka"

"Ban gane ba?"

"Ya karɓe Waya ta, kuma............................" Nan take ta bashi Labarin Abinda ya faru, harda Wayarta da ta gani a ɗakinshi Amma bata bashi ƙarin bayani akan zargin da take masa Ba, ta dai ce ƙila an bashi ne ya bata tunda shi ya shigar da case din, sai ya manta bai bata ba, Roƙonsa tayi akan ya kira saleem yace Dad ba lafiya an kaishi asibiti Sunanta kawai yake ta ambato yana Son Ganinta.

Haka kuwa akayi,bayan Sun gama waya ya kira saleem hankali tashi yace Yayi ta kiran Layin Maryam a kashe don Allah in Yana kusa ya bata, bata rai yayi yace bana nan me ya faru?, ZEEYK yace

"Dad ne babu Lafiya yana Son Ganinta Cikin gaggawa"

saleem yace "Meyasa Sai ita kadai zai gani?, Ku sauran baku isheshi FarinCiki bane?, Ko ganinta zaisa yayi lafiya ne?"

ZEEYK yace "Bazata bashi lafiya ba, Amma kai likita ne kasan Darajar Buƙatun mara lafiya, Maralafiya girmama Buƙatunsa ake, kuma idan baka manta ba Auren yarjejeniya kukayi da ita don Naga ka fara shiga Sabgar da ba naka ba, Idan ka isa gida ka gaya mata saƙona"

Dariya saleem yayi irin wanda ya jima baiyi irinta ba yace
"Lallai Yayana Kun dauka Ni shashasha ne ko?, Aurena ne akanta fa? Kuma kake tunanin zan wofintar dashi in Barta ta Fita a washe Garin Auren mu?, akan Dan karamin Dalilin da bai taka kara ya karya ba?, Ina ai ko babarta ce ta Rasu a yau Dinnan Bazan barta ta fita ko ina ba, In Gaya maka gaskiya ma Na kulle ko ina babu inda zataje"

Daga nan sai ya katse wayar, hankalinsa kwance ,Ya tattara inashi ya koma gida.

Tana zaune tana daddana wayar Taji Ƙarar buɗe ƙofa, Da sauri ta zura wayar cikin Rigar ta tana Zazzare Idanu irin na marasa gaskiya .

Murmushi manne a fuskarsa ya ƙaraso har inda take, ya dire Ledojin da ya shigo dashi a Gabanta da faɗin

"Sorry Wifey I Ieft you Alone"

Tsaki taja ta miƙe zata koma ɗakinta, sai ta tsinkayi Muryarsa yace

“ki shirya In kaiki gidanku, tsohonki babu Lafiya "

Wani irin sanyi Taji ya ratsa zuciyar ta ,Amma saboda jan aji irin nata bata nuna Ba, sai ma ɓata fuska da tayi tayi shigewarta.

Ɗaga kafaɗa yayi , Alamar bai damu ba, ya dau Ledojin da ya shigo dasu ya nufi Kitchen ,Ganin ko ina a tsaftace Yasashi Sakin Wani irin Murmushi a ransa Yace _Yanzu Nasan nayi aure, Dole in bada Umurni,ko ba'a so dole a bini_ .

🎑Ladar farko tsaftataccen Naman sa ne a ciki sannan kuma dayan mai dauke da kayan Miya, Leda ta uku kuma jibge yake da kayan Fruits kala kala, Saida ya zuba kowanne a masubinsa sannan ya fito, ya iske ta fito cikin shiri.

Kallon mamaki ya bita dashi

"Ah madam Ina zuwa?"

Harara ta Zabga masa watou ya ma raina mata wayau, don takaici ma kasa ce wa komai tayi.

"Nace ina zaki? ,Ko bakida bakine?"

Wani ƙulutun bakin cikin da ya tokare mata maƙoshi ta haɗiye tace

"Gida mu"

Ya dage gira daya yace

"Har wata Ukun yayi kenan?"

"Ban gane ba, kaifa kace in shirya zani gida Abba ba lafiya”

"Owwh Ashe kinjini!, Na dauka da kurma nayi magana, tunda baki Amsani ba ,Nayi cancel sai ki tari gaba, idan miji na magana Natsuwa ake ana sauraron sa ba banzatar dashi ake yi ba Madam Understand?"

Cikin Takaici tace

“har Ka isa? ,Na ma fasa Auren Ka buɗe min Na koma gidan Mu"

“kofa a buɗe yake mrs You Are free to go, and in kin Tafi karki dawo"

Da sauri ta nufi ƙofar Jikinta har wani Rawa yake don Ɓacin rai, amma sai me?, Tana isa Ta iske ƙofar a kulle da Makulli.

Sulalewa tayi, sai hawaye

Ko Kallonta baiyi ba ya taɓe baki yace

"Na siyo Kayan Girki suna Kitchen Ki Shiga Ki gyara su, idan kin gama sai In kaiki”

Tsaki taja tace

"Babu wannan cikin yarjejeniyar mu"

Dage giran sa sama yayi

"Au har yanzu kina Zance akan Yarjejeniya?, Zaki sake yin taurin kai kenan Irin na Ɗazu Ince na fasa ko?"

Ba don Ranta ya so ba haka nan ta miƙe tana antaya masa Allah ya isa cikin ranta, ta faɗa Kitchen tabi Tarin Abubuwan dake baje da kallo , Lallai saleem In banda karambani ina zasu kai wannan Uban Kayan?.

Cikeda jin haushinshi ta wanke kayan miyan sannan Ta wanke naman Shima.

Tayi Grating Kadan cikin kayan Miyan, sannan ta adana sauran bayan ta ciccire hancinsu..

Cikin ƙanƙanin lokaci ta haɗa miya, ta kuma soya namar bayan ta tafasashi.

Tuni gidan ya Kaure da Ƙamshi, yana Nan zaune a Parlor sai faman santi yake, da wowa tayi bayan ta gama, ta dubeshi tace

"Muje..."

Da mamaki ya Dube ta yace

"Muje ina?, Har kin gama ne?"

"Eh Na gama”

“Tho zubo min nawa?"

Harara ta dalla masa ganin yana Ƙoƙarin kawo mata rainin hankali tace

"Miya da naman Ko kuma me?"

“Dama miya da naman kadai kika Yi?, Lallai Kinada aiki"

Ya fada yana Kallon Angry face ɗinta, ya ciji Lower lips ɗinsa

"I don't care how you gonna do it, Nide Ina son Ganin Abinci a gabana within 20 mins”

Wani Abu taji ya zo daidai maqoshinta ya tsaya yaqi wucewa.

Me wannan gayen ke nufi da itane? Yar aiki ya Maidata ne?, Yace ta sarrafa masa Kayan da ya shigo dashi tayi, yanzu kuma Girki yake Son Tayi masa, Me ya maidaita ne?

_He want to waste your time Yaji kince kin fasa zuwa_ wata zuciyar ta raya mata.

'Then he should Swallow his breath Huhh' tafadawa zuciyarta tana hararar sa a Zahiri

Kallonta yake gira a ɗage sai faman Karkaɗa kafa yakeyi

Dubansa tayi batareda nuna dumuwar
komaiba a zahiri amma Deep down she's Boiling, jitake kamar ta Dora hannu aka ta fasa ihu, gaba ki ɗaya sai taji Aurensa ya Fitan mata arai.

Haka takoma ta dafa farar shinkafa yana zaune Ya riƙe remote Yana Chanza channels , ta kawo masa, ta dire saman Rug batareda tace komai ba .

Shima banza yayi mata, wato tafi ƙarfin tayi masa magana tace gashi ,ta isar da sakon sa shine ya zame mata aiki.

Haka Suka zauna shuru babu mai magana Cikinsu, Athletic Channel Yasa don yasan ta Tsani ire iren channel ɗin, sunsha Samun Saɓani Akan Kallon Game, ko a asibi in tazo Office dinsa taga shi yake kallo, Allah Allah take taga ta fita.

Miƙewa tayi a ƙufule ta fice rai ɓace,Bin bayanta yayi da kallo, ya jinjina kai yayi Murmushi

“za ki dawo"

Ya fada yana Chanza channel din zuwa Kung Fu.

Almost 30mins bataji motsin sa ba, Sai ta fito taga Ƙila ya gama Shiryawa, Amma Abin takaici ko motsawa baiyi daga inda yake ba, yana nan zaune ya tasa TV da kallo.

Haɗiye bakincikin da tazo mata tayi, tazo inda yake Saida tayi jimm kaman bazata yi magana ba sannan ta ƙaraso gabanshi ta tsaya.

“Time na Wucewa, bani Key in Tafi"

Dagowa yayi yana kallon yadda taketa faman kumburo fuska, tawani tsaya mashi akai.

"Ina Abinci na?"

Ya tambaye ta Cikeda rainin hankali.

"Gashi na kawo maka, Tun ɗazu"

Ta fada cikin Son Danne fushinta

“a ina kika ajiye min?"

Ya fada cikin Son Ƙular da ita.

"Ba gashi ba"

Ta fada cikin turo baki tana Nuna mai inda ta ajiye.

"Kin ajiye min for how long"

Kai Tsaye tace

"More than 30mins"

"Banacin Abinci idan ya huce, zubo wani"

Wani Abu taji ta taso ya toshe mata maqoshi, Kutt ta haɗiye shi

"Bakijiba? Nace ki zubo wani,ko so kike nace ki dafo wani?"

Yafada yana kallon yadda fuskarta ke ya Kumbura, yasan da zata samu dama da babu Abinda zai hana ta Nakaɗa mai Shegen duka.

Batace komai ba ta figi Flask da Plates din ta fice tana bugomashi kofar da ƙarfi.

Binta yayi da kallo yana cije Lips ɗinsa sannan ya jinjina Kai yana murmushi.

“I'll clear Away your pride Maryam"

Bata Jima ba ta Dawo, wannan karon da ƙaton Tray, ta dungure mashi a Gabanshi.

Ɗagowa yayi yana Kallonta da tarin mamaki,sannan ya maida Dubansa kan wani Ƙaton Flasks da ya Kusa cinye duka Tray dinda Plates dinda ke kan Tray din yace

“duk wannan Din na menene"

Banza tayi Mshi a ranta tace ka buɗe ka gani, a hankali yasa hannu yana bubbuɗewa Ƙaramin Flask din cike dam Da shinkafa , A hankali yasa hannu ya buɗe ƙaton, shinkafar dake ciki dan kaɗan sai kace na dan Goye.

Sauran Kuma miya ne a ciki ,Jibge da manyan namomi.

Murmushi yayi ,ya haɗiye yawu

"Now zuba min "

Haka ta zauna ta zuba masa ,cikin mai yawan nan ta tura Gabansa tana Kumburo Fuska.

Dubanta yayi yace

"Kinci abinci ne?"

Kauda Kai tayi tace

"Wannan bata shafeka Ba”

“zauna anan"

Ya nuna mata gefen sa fuska a ɗaure,babu alamar wasa a tattare dashi.

Bata Musa ba ta dawo kusa dashi ta zauna tana Kumburo Fuska, Idanunta na kawo Ruwa .

Wayarsa ya ciro ya kira Inna Saude yace, a aiko Yathai da Coffee ɗinsa two cups.

Yana Kashe wayar ya dubeta, Zuwa wannan Lokacin kuwa Hawaye sun gama wanke mata fuska.

Taɓe baki yayi, yasa Spoon ya ɗebo Abincin ya kai bakinta ,Sai kawai ta sunkuyar da kai saboda wani ƙaton takaicin da ya taso mata, hakan yasa ya maida Spoon din

Hannu yasa ya ɗago Fuskarta,Hawayen datake dannewa ne suka kufcemata suka gangaro kan kumatunta, yasa hannu ya share su, kallonta yake yanajin kowanne digar hawayenta harcikin zuciyarshi, Shima take idanunshi suka fara chanza kala Tsikar Jikinshi na tashi, Amma ko kadan bai bari ta gano rauninshi ba yace

"Babe yau ko kukan Jini kike kina aman wuta sai kinci abincin nan, So open up”

Ya Fada yana sake kai Abincin bakinta, daidai lokacin Inna Yathai Tayi sallama, ya amsa Tareda bata umurnin Shigowa.

Shigowa tayi dauke da yar karamar Tray Mai Dauke da 2mugs of Coffee.

Duƙawa Tayi Har ƙasa ta Dire da faɗin

"Gashi Yallaɓai"

Ko Kallonta baiyi ba saida ya sake ɗebo Abincin ya kai bakin Maryam, Batada zaɓin da ya wuce ta karɓa a dole ta buɗe bakin Tana Hawaye , Kunyar matar taji, hakan Yasata duƙar dakai, itama inna Yathai kanta a duke,tana jiran Ya bata umurni ta tafi.

Haka ya cigaba da cusa mata ,tana Karɓa a kunyace don Harga Allah Kunyar matar takeji, Dukda itama kanta a ɗuke yake, Bai Dire ba Saida ya Tabbatar ta cinye Mai yawan ,har tana yunƙurin Amai, Sannan yasa hannu ya tsamo naman daga cikin miya,ya yaga, yajishi da Taushi, ɗanɗanon Miyan yajashi bai san sanda ya Lumshe ido ba,ya zuba ma kansa abincin dake Cikin ƙaton Flask din , takaici ya Kamashi da yasan haka Miyan yayi daɗi da bai sa ta cinye Uban Abincin ba.

Inna Yathai na Nan Duƙe har ya Gama, banda Kuka babu abinda Maryam keyi, amma bata Bari ya sake ganin Hawayen ta ba, da sun Zubo take share abunta ga lokaci sai Gudu yake.

Yana gamawa yasa Tissue ya Goge hannunsa da baki , ya ɗago ya dubi Inna dake duƙe har yanzu, shifa har ya mance da ita.

Mug din coffee Daya ya Dauka,Kur6a daya yayi, yajishi da sanyi yayi saurin furzoshi saman Fuskar ta.

"Meye Wannan, so kike ki kashe Ni?"

A gigice Maryam ta Ɗago ta dubesu, gaba ɗaya jikin tsohuwar ya gama jiƙewa da Coffee.

“so kike Sanyi ka kashe Ni?"

Ya fada cikin zazzare ido.

"Sorry Sir, kuskure aka samu"

Inji Inna tana sake Duƙar dakai

“kuskure?, so nawa zan gaya miki ban yarda da Kuskure ba?"

"Yi haƙ..."

"Shut up"

Ya Daka mata tsawa.

Ya watsa mata Raguwan Coffee dinda ya rage a Mug din da fadin

"Fu*k you Bitch 👎🏻"

Kallonshi Maryam Keyi a mamakince dama wannan mugun halin nasa a ko ina yake yinshi?, Lallai akwai ƙura a lamarin shi.

A Fusace ya miƙe ya dubeta cikin isa yace

"Clean the trash"

Allah Sarki Tsohuwar Babu damuwa a fuskar ta ,tace

"Yallaɓai bana jin *Turanci* ban fahimci abinda kace ba”

Yaja gajeren tsaki yace

"Daƙiƙiya, Kina aiki a gidan nan For more than 15yrs Amma you can't speak common Simple *English* , Damn You, daƙiƙancinki

Please Login or Register in order to submit comment