Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yar Yatsar ta sannan Ya taso ya Zauna a gefen Gadonta, Ya Karkatota gefensa,ya kwantar dakanta a kafadar sa.

"Suma Kikayi, Am sorry I caused it"

Sai A lokacin Brain ɗinta yayi mata Recalling Komai, Shima bai jima da Farkawa ba, Yana tashi Ita ya fara tambaya Sale da ya Kawo su Asibiti ne ya sanar dashi duk Abinda ya faru ,hakan yasa Hankalinsa yayi mugun Tashi,Ya miƙe ya Nufi inda Aka Kwantar da Ita.

Turo baki tayi, ta saki Wani sabon Kuka mai taɓa Zuciya, rarrashinta Yayitayi da kyar ya samu ta Tsagaita.

Da kanta Ya haɗa mata Tea, Ya zaunar da ita akan Gado yana bata a bakina ,ita dai Kallonshi kawai Takeyi tana sha, She can't Believe Yayanta ne yau zaune a gabanta yana bata kwatankwacin Kulawar da yake bata a da, She can't Imagine moment like this zai ya sake dawowa cikin Rayuwarta , ada Ta dauka Ashman ya fita a rayuwarta kenan Bazai sake dawowa ba, Sai gashi Allah ya turo mata shi a lokacin da take tsananin buƙatar sa.

Kuka mai Karfi ta fashe dashi, ta faɗa Jikinsa tana Shessheƙa,Ruɗewa yayi ,ya ajiye kofin shayin Ya hau Rarrashinta.

Banko ƙofar Akayi da Ƙarfi, Deejah ce ta shigo, hannunta Riƙeda basket din Abinci.

Ganin Mijinta tayi Rungume da Aeesh yana rarrashinta, Wani irin Kishi ne ya taso Mata ranta ɓace ta Afko Ciki ta fara Zazzagar Bala'i.

wani irin mugun bacin rai ne ya dira a zuciyan Ya Ashman ya ɗago Yana Kallonta ,Aeesh kuwa Cusa kanta Tayi a gwiwowinta ta fashe da sabon Kuka.

Cikin Tsawa Ya dakatar da Deejah da cewa

"Hey...!, How dare You Bust into My Client Room Without Seeking For consent ?What in Kin ganmu a Mummunar Yanayi?"

Take Kishin Deejah ya motsa, tayo kan Aeesh zata daka Cikin hayaniya, saurin Tsareta yayi

''Dont You Ever try this Rubbish, Wlhy Akanta Zan Iya Rabuwa da Koma wanene,Tunda ba wani Ya kawoni duniya ba, Kamar Yanda Kike ji dakanki ke Mata ta ce Ita ma haka nake ji da ita a Zuciyata Kaman Mata ta, Ita kadai ce macen da Zan Iya hada jiki da Ita naji daɗi and Zan Iya giving efforts Dina Dina Don ganin na Biya mata Buƙata''

Wani irin Supa Deejah tayi ta shaƙo wuyar Deejah dake laɓe a Bayanshi Tana Kuka tana cewa

"Wlhy sai na kasheki, Sainaga bayan ki,Dama na dade da Zargin kece Kika hana mijina ganina a matsayin mace, Na rantse Sainaga karshen Numfashinki"

Kuka Sosai Aeeah ta fashe dashi cikin Azabar Shaƙar da Deejah tayi mata ,ko Tausayawa Condition ɗinta batayi ba, Duk inda Ta samu take kai Duka.

Ko kallon Inda Suke Ashman baiyi ba, ya miƙe ya Nufi Drawern dakin , ya dauko Prescription Script da Biro ya Fara Rubutu, daga Inda Deejah take Ta hangoshi, ai Babu shiri ta Saki Wuyan Aeesh Tazo Wurinsa Da gudu ta Durƙusa Har ƙasa Tana Roƙonsa

"Honey Don Allah Kayi Haƙuri, ka rufa Mn asiri Karka Sakeni idan Ka Sakeni bansan Yanda Zanyi da Rayuwata Ba, ka taimaka Min, Bazan iya rayuwa batare dakai ba"

Takardar Hannunshi ya jefeta Dashi,yace

"Jeki Pharmacist Ki karɓo min Wannan Maganin”

Daukar Takardar tayi Ta duba ,PCM injection start dose ne kadai ya rubuta, ɗagowa tayi Cikeda haushi suna hada Ido ta sauke kai ta cigaba da kallon takardar Kaman yau ta fara Ganinshi.

"Ko Bazaki je bane?"

Ɗagowa tayi Ta kalli Aeesh dake faman Ƙunshe Dariyarta, Ta kuma kallon Ashman da Ke tsaye yana Kallonta fuska a daure.

Cikeda haushi su duka taja ƙafarta ta fita, Tana Fita ya koma kan Gadon, pulse Oximeter dake Manne da Yar Yatsar hannunta Ya cire mata, Sannan Yayi Unpluging Drip din Hannunta ya dubeta.

"Taso Muje"

"My Place, Inda Aka kwantar dani"

Maƙe kafada tayi
"Nidai bazani ba, Salon Matarka ta shigo ta Ƙarasa Ni"

Tayi Maganar a Shagwaɓe

"Wane Mutum , Ai bata isa ba, Tun Kamin Ta shigo rayuwana that's how we used to be, And zuwanta Bai Isa ya sauya komai ba"

katseShi tayi
"A'a Ahky ,Abinda Kakeyi Mata Gaskiya bai kamata Ba baka Kyautawa, Matarka ce fa kaji tsoron Randa Allah zai Kamaka da hakkinta Akanka , Don baka Sonta bashi Zai baka damar Wulaƙanta ta ba, Karka manta fa da Ƙawata ce aduk lokacin da naga Ka mata ba daidai ba ,banajin daɗi"

Harararta yayi

"Yanzun nan fa Har dariya na kamaki kinayi"

"Tho ai Ni ba ita nake ma dariya ba, dakai Nake"

"Ohh Yau Bayan Abin tsokana Abin dariya Na zama Kenan"

Dariya tayi a bayyane sosai, Shima Dariyar yayi Dariyar da rabon Da Suyi irin shi Duk sun manta, they Both missed themselves , They Missed the old them 😁.

Tashi sukayi suka bar Dakin a Tare suna Hira Abin sai ya baka mamaki bazaka ce sun kwashe Watanni Basua ma juna magana ba, Bazakuma kace suna marasa Lafiyan da aka kawo Asibitin Ɗazu Kowannensu bai san inda Kansa yake Ba.

Hannunsu na cikin na juna, haka Sukayi ta Ratsa Jama'an dake Asibitin, Ko ina Sukabi sai An kallesu.

Gaaishesu Akeyi yana Amsawa Cikin sakin Fuska Abinda bai taɓa tamsa musu da murmushi akan faruwa ba, Tsawon shekarun da ya dauka yana Aiki a asibin kullum Fuskar sa a daure yake, ko da An gaisheshi ba Amsawa yakeyi ba, kuma idan Ya wuce Ma'aikaci bai gaidashi ba another Wahala ne

Escalator Suka Hau suka sauka a 3rd Floor Gabaki Daya daya bangaren Amenities ne, inda ake kwantar da Manyan Masu kudi da Masu Buƙatar Bedrest kaman masu brain Disorder ko Cardiac Failure .

Wurin Tsitt babu ma hayaniya a floor din ko kadan ba'a cika barin visitors ba.

Daga Kai da Ashman Zaiyi sai Ganin Saleem yayi ta Sama ya fito daga lab, Theater Attendant na biye dashi Riƙeda Kidney dish in ba Gizo Idonsa ke masa ba, Fresh blood ne a ciki, Cikin Sauri yake zai sauka 2nd Floor.

Mamaki ya Kamashi me ya kawo saleem Asibiti?, Me Zaiyi da Jini?, SALEEM Fa bai damu Da Damuwar Wani ba, Ayau Koda Abbansa ne a kwance yana buƙatar jini baya Tunanin Saleem Zai iya Tashi da ƙafarsa Yaje ya Dauko jini ba, Anya babu lauje cikin Naɗi kuwa?.

Sake ɗagowa yayi Ya kalleshi, yaga Tabbas shine Kuma da Alama Hankalinsa A tashe yake ,tofa?, Wanene Babu Lafiya? Shidai a iya tunaninshi Baiga wani Halitta a duniyan Nan ba da Zaiyi Rashin lafiya ya tashi Hankalin Saleem ba.

Saukar dakai Yayi, ya jinjina kai

_koma wanene That Person Means Alot To him, WHO IS THAT?_

Bashida Mai Bashi Amsa ,Shiyasa ya bar makansa.

Office ɗinsa Dake Floor din Ya shiga, dama Kuma anan Aka kwantar dashi.

*SALEEM*

Micro Theatre Aka kaita,anan Aka cire mata Bullet din , Ta Zubar da Jini SOSAI kuma ana Buƙatar Jini Urgently.

Nan take Saleem Yace a gwada nasa In Yayi Matching a sa Mata, batareda Ɓata lokaci ba aka gwada , Aikam Cikin Sa'a jinin Yayi Matching Zuwa yayi Aka Diba nashi Aka kai Labdon Ƙara tantancewa Bayan an tantance yakai aka sa mata.

Saleema na Zaune tana Kallon Shige da Fitarshi ko ba'a Gaya Mata ba Tasan Wannan shine Nasty Doctorn Maryam Dubada Yanda Yake wulaƙanta Ma'aikan Tun Shigowarsu, Gashi Exactly Yanda Maryam Ta kwatanta mata shi.

Suna Zaune har jinin ya ƙare Aka Sa mata D/Saline,Ganin Babu Waya a hannun Maryam Da Ƙanwarta hakan Yasa Ya Aika a je gidansu asanar Masu Da Abinda Ya Faru, Bayan tafiyarsu ta farka.

Yana Tsaye a bakin ƙofa ya kasa Zama Sai kallon Fuskar ta yake, Fuskar tayi Fayau, Fuskar babu Yabo babu Fallasa .

Sanye Take cikin Theatre Gown Light Blue, Hannunta na Dama a buɗe anyi Mata Dressing Wurin ciwon, Anyi Covering Ɗinshi da crape Bandage, Anyi clipping Finger ɗinta da Pulse Oximeter

A ɗayan Hannun Akayi mata setting line, Jinin da akayi Mata fixing na Diga a Hankali.

Tsayawa yayi yana kallonta yana Tuna Moment din Ɗazu, tunda yasanta be taɓa ganin murmushinta ba she's always moody or expressionless, Tunowa Yayi da Dariyarta da Shagwaɓa Face ɗinta da Ya gani Ɗazu.

sihirtaccen murmushin da Ta saki Wanda ya bayyana jerrarun haqoranta farare Tass da dimples Ɗinta da suka Loɓa ya Tuna ,tunowa tayi da Lokacin da ta juyo ta ganshi, ta wani haɗe Rai, Murmushi ya saki a fili...

A hankali ya maida Idanunsa Ya Lumshe su, Wasu Abubuwa Na Tsikarin shi.

Dubanshi yakai Kan Saleemah da Dake Zaune a gefenta tana cin Shawarman da yasa A kawo mata, hankali Kwance, ko kadan Jikin Maryam bai nuna Wahalar da na Yarinyar yayi ba, da Alama Yar Gata ce,kuma yar hutu duba da Sheki da kyan fatarta ,Saleemah kuwa Hannunta har yayi kanta.

Hannunta ya kafe da Kallo, a hankali yaga ta fara Motsashi,Saurin Karasowa Wajen ta yayi ya zauna Gefen Gadon.

A hankali bakinta Ya fara Motsawa cikin Muryarta da baya fita sosai take cewa

"Daddy ....Daddy Zan Mutu , Zafi ,Wayyo kaina Wayyo hannuna,Daddy please take me out of here"

A Hankali ya daga hañnu kaman zaiyi tapping Hannunta, sai kuma ya maida Hannun Yana Kallon Saleemerh.

Kallonsu Saleemah tayi ta ƙasan ido, Ta saki Murmushi a ranta tace

_Yau zanga Ƙarshen wasar_

Sake daga Hannun yayi Kaman Mai tsoron Kada wani ya gansa, yayi tapping Hannunta dake Rawa.
A hankali take buɗe idanunta da sukai mata masifar nauyi, taɗan motsa kaɗan tana cije leɓe kafin ta samu nasarar buɗe idon da ƙyau a kansa ta saukesu, Dishi Dishi ta Fara Ganinshi Kafin Daga Bisani Idanunta Su ware Tangaran a kanshi.

Ji tayi kaman An buga mata Guduma akai, Zumbur ta miƙe zaune Dukda batajin kwarin Jikinta Amma Hakan bai hanata Razana da ganin Fuskar sa ba.

Jin motsi yasa Saleemerh ɗagowa ta dubesu, Daidai lokacin da Maryam ta fashe da wani irin Kuka ta Damƙe Idonta da Ƙarfi tana cewa

"Wayyo Daddy ,ya kawoni Inda zaka kasheni....Wash Allahna"

Tayi maganar tana Ware Idanunta jin Wani irin zafin da Ya ratsata ta Kafaɗar Hannunta.

Sai a lokacin tayi recapping Abinda ya faru.

Kafin Ta ida Tunano abinda ya faru, Mama ta shigo Dakin Hankalin ta tashe ,ta ƙaraso Wajenta ta fashe da Kuka

"Mero!, Kece haka?"

Jin kamar Muryar Mama yasata dagowa ta dubeta ganin ita ce yasata qara qanqameta tana kuka kamar zata shige cikinta, Bata damu da Giving Set din Jini da ya zame daga Cikin Cannulan Hannun ta ba

"Take me out mama!, mama Ki fiddani daga nan ,Zai kasheni" tafada cikin kuka Sosai Jikinta na wani irin Rawa.

"Mero Kinutsu..."

"Please Mama! Take me out, Ki Fitar Dani, Bana son Ganinshi" tafada tana qara qanqame mama Jikinta na Kakkarwa.

"Ok....!, Kai Yaro fice min da Gani, tace bata Son Ganinka Fita Don Allah Fita"

inji mama da duk ta Rikice ganin Yannda Maryam ke Kuka sosai Jikinta har wani kar kar yakeyi, Numfashinta na fita da ƙyar, Tunda take bata taɓa ganin Tashin hankalin Maryam Irin Haka ba.

Ganin still Saleem Na tsaye bai fita ba yasata Daka masa Tsawa

"Kai Nace ka fice Min Da gani Kana Tsorata ta"

Sunkuyar dakai Saleem Yayi Yanajin ba dadi, jiki a sanyaye ya Fice.

Yana fita Saleemerh ta kwashe da Wani irin Dariyar Mugunta har tana Shiɗewa.

Bintou ✍🏼

Nayi Gabas 🚶🏻‍♀️
[10/3, 9:56 PM] Solace: *WUƘA A ZUCIYA*

_BLEEDING HEARTS_


*030*



"Mero Kinutsu..."

"Please Mama! Take me out, Ki Fitar Dani, Bana son Ganinshi" tafada tana qara qanqame mama Jikinta na Kakkarwa.

"Ok....!, Kai Yaro fice min da Gani, tace bata Son Ganinka Fita Don Allah Fita"

inji mama da duk ta Rikice ganin Yannda Maryam ke Kuka sosai Jikinta har wani kar kar yakeyi, Numfashinta na fita da ƙyar, Tunda take bata taɓa ganin Tashin hankalin Maryam Irin Haka ba.

Ganin still Saleem Na tsaye bai fita ba yasata Daka masa Tsawa

"Kai Nace ka fice Min Da gani Kana Tsorata ta"

Sunkuyar dakai Saleem Yayi Yanajin ba dadi, jiki a sanyaye ya Fice.

Yana fita Saleemerh ta kwashe da Wani irin Dariyar Mugunta har tana Shiɗewa.

Hayayyaƙo mata Mama tayi cikin masifa

"Naga abinda ya isheni, to ke naki salon kenan?, Haka kawai sai ki kama Dariya kaman Zararriya?, ko dai murna kike da ciwon yar Uwan taki ne?"

Dariya saleemerh ta sake Kwashewa dashi

"Allah Sarki mama, kin Kora mata masoyi, saurayin ta ne fa! ,Ji fuskar ta Kuka take son yi haushinki takeji"

Zaro ido mama tayi

"Au Meron Har saurayi Gareta kenan?,

"Kai mama dama baki sani ba?, Ayya ansha dake Baki nan da Kinga Zallar Soyayyar Zamani ba irin taku ta tsofaffi ba, harfa Jininshi ya bada asa mata"

Harara maryam ta Galla mata cikin karfin hali kanta na sara mata, ta Lumshe Idanu da Muryarta mai rauni tace

"Saleemerh Are You serious!"

"Na Rantse Da Allah Jininshi aka sa miki"

Tsabar firgici Maryam ji tayi gaba daya ba ciwon ta fara kiciniyar sakkowa kasa da sauri jikinta na rawa, riƙe ta Mama tayi da Karfi, kaman Jira take tafashe da kuka hakan yasa duk suka tsaya suna kallonta.

Mama datafi kowa rudewa tace "wai menene kike kuka eh mero?,Ciwon ne?"

Kwace rikon Da mama tayi mata tayi, ta share hawayen da bayan hannunta...

Hannu tasa Ta zare Giving Set din dake Manne a hannunta, take Cannulation dinda Akayi Mata ya kwance , jini ya fara Zuba , wurgi tayi da Jakar jinin da Ke Rataye a Drip stand ta saki Ƙara mai Ƙarfi.

Mama tasa Tafukan Hannayenta ta toshe mata baki ta riqota da ƙarfi

Jin an riqota yasata fasa wata Qarar tana qanqame jikinta cikin fitan hayyaci

"Mero..!! Maryam!! Innalillahi Wainnailaihirraji'un, Salima kira likita!"

Inji mama tana riqeta sosai ganin yadda take kiciniyar qwacewa.

"Mama ƙyale ta, jinin Likitan nan ne ya fara Aiki a cikin Jikinta zata bari In Ya ida Gaurayewa da nata"

Takaici ya cika Maryam lallai Saleemah ta raina ta, ya akayi Tasan Saleem tukunna ma?, Dukda halin da take ciki ji tayi kaman ta tashi Ta Kifeta da Mari.

Tsawa Mama ta daka Ma Saleema A Karo na biyu Hankalin ta tashe, ganin Yanda Maryam ke dizgar kuka kaman Ranta zai fita, Ga wani Irin Shacking da Jikinta keyi, Kallo ɗaya zakiyi mata Ta baki tausayi,duk tabi ta ɓata jikinta da jini a dole bata Son Abinda Ya fito daga Jikin Saleem, Kuma ta Ƙudurta ma Ranta In Allah ya Yarda sai taje Renal Unit an ɗebe Jinin dake jikinta duka an musanya mata da sabo.

SALEEM na Fita ya jingina da bayan Ƙofa yana cizon leɓenshi na qasa tareda runtse idanunshi da qarfi zuciyarshi na mashi wani irin zafi, ya kasa Yarda Yabar dakin Gabaki ɗaya Gani Yake kaman Idan ya tafi zai dawo ya ga sun Gudu.

Ya daɗe a tsaye a haka yana sauke Numfashi , Wani iri Yakeji cikin Jikinsa He's feeling some how Abinda bai saba jiba

Tabbas wani abu na shirin faruwa dashi, wani irin yakeji don tunda yasan kanshi bai taɓa damuwa da Lamarin mutum ba, Duk muhimmancin abu a Wajen Mutane shi maidashi yake ba komai ba, bai yarda Da Akaƙar da zata sa Yayi Tendering Feelings ɗinsa akan wani ba, wani abu yakeji a zuciyarshi Mai Rauni, He's Weak, he's not who he used to be, a Halin yanzu bazai iya kwatanta Halin da yake ciki ba.

Tsintar Kansa Yayi da Leƙensu ta budadden ƙofar da bai Rufe ba.

Gani yayi tana Kuka ta Koma abar tausayi ta kasa nutsuwa kuma ta kasa Yarda a Kira Likita ya duba ta, hakan yasashi jin wani iri cikin jikinshi a Raunane ya janye idanushi yayi Taking Deep breath

"Ya Salam...!"

Ganin idan ya cigaba da Tsayuwa a nan zuciyarsa zata iya Bugawa yasa shi jan Ƙafarsa zai juya ya tafi

Cak ya tsaya jin an riqomasa hannu ta baya.

Tsayawa yayi daga yunkurin juyawa baterada ya juyoba gabansa na faduwa.

"Saleem who's Sick?"

Ashman ya tambaya ahankali

Shiru yayi kuma bai juyoba.

"SALEEM Tambayan ka nake waye ba Lafiya?"

Shiru yayi bugun zuciyarshi na qaruwa sosai, he' feeling guilty, at the sametime he's Weak He can't believe he's doing All these Akan Mace !, Macen ma Mara Kunyar yarinyar da ba ganin Girmansa takeyi ba, yanajin wani iri sosai bai san Ko menene ba but He knows he's In trouble,cus he believes weakness of a man is a failure.

"Saleem Are you Okay?"

Muryar Ashman ta sake Shiga Kunnnensa A karo na biyu.

juyo dakai yayi yana wani irin pikipiki da ido ya kalleshi yana sauke ajiyan zuciya sanyaye.

"Ina Ruwanka?"

Yafada muryarshi nadan cracking

Shiru Ashman yayi yana kallon shi na wasu mintuna sannan ahankali ya Rage Kaifin idanunsa yana Kallon shi ta ƙasan ido

Saurin runtse idanu yayi don Yasan Da zarar Ashman Ya kalli cikin idanunsa Zai fahimci Abindake damunshi and he's Not Ready To face Another challenge.

Zame hannunsa Yayi cikin sanyi ya juya ya bar wurin Yana Takawa a hankali Cikin Sanyi.

Binshi da kallo Ashman Yayi Yana Karantar yanayinsa, tabbas Akwai Wani Abu muhimmi dake Faruwa And he need to Find out.

Shiga dakin yayi Bakinsa Ɗauke da sallama ,Mama na Ganinshi tace "yawwwa Likita dan ALLAH DUBA MIN ITA Abu Takeyi irin na masu taɓin ƙwaƙwalwa "

Bin dakin yayi da kallo ,kafin daga bisani ya maida Dubansa Akan Maryam Da Ta nutsu tun Bayan Shigowarshi Amma bata bar sharar Hawaye ba.

binta yayi da kallo kafin ya zauna akan kujeran dake wajen saboda jirin da yakeji, yana dan lumshe Idanu Zuciyar sa fall da farinCiki, indai hasashenshi Gaskiya ne Tho fa babu Wanda zai kaishi Farin ciki a duniyar nan

"Ehmm Garin Yaya Jini yaɓata gurin Nan?"

bata Fuska Mama tayi

"Haba Likita,fisabilillahi kana ganin jini ga Mara lafiya jiki ba daɗi Amma ka Samu guri kayi zaman Ka kana Ganin Kayi Mana Adalci kenan?"

Ko kallonta baiyi ba balle tasa Ran zai Amsata, saida yasaci kallon yadda maryam tawani makure can gefe guda yayi murmushi yana kada kauda Kai, Dubansa Ya sake Maida wa Kan Blood Bag dake yashe a ƙasa, jini sai tsiyaya yake, ga Hannunta dake ta faman Digar jini, Wani irin Ƙasaitaccen Murmushi ya saki , Sannan Ya miƙe tsaye batareda yace komai ba ya fice, Ya turo ,cleaner da Nurse aka gyara ɗakin Tareda Maida Mata da Jinin, Wannan Karon Bata Musa ba Saboda Kwarjinin da Ashman Yayi mata lokacin da ya shigo, tana Tsoron Bijirewa tasan idan Yaji labari yar sauran Mutuncinta da yake Gani Ma daina Gani Zaiyi.

Koda Deejah ta dawo ta iske babu Kowa a Dakin hakan ba ƙaramin Tayar Mata da hankali yayi ba, Ta nemeshi ta ko ina na Asibitin Amma bata ga me kama shi Ba, duk wanda Ta tambaya a asibin ce mata yake bai gan su Ba.

Zuciyarta ce ta ayyana Mata cewa Tabbas Mijinta ya fita da Aeesh suna can Suna Aikata Alfasha dama ta daɗe da fara zargin yana neman ta, Wannan Karon Anzo gaɓar da bazata iya jure Rashin Mutuncinsa Ba ya zama Dole yasan Yanda Zaiyi da ita , inba haka ba zata nuna mishi Asalin Color ɗinta ,Dama chan kawaici take masa Taga iya Gudun Ruwansa, Amma yanzu Lokaci yayi da Bazata juri cin Amana daga gareshi ba,tunda tabishi ta Lalama yaƙi karbar soyayyarta yazamo wajibi ya karɓi Soyayyarta ta ƙarfi ta Tsiya, tana Fitowa ta koma Gidansu da cewar tayi yaji sai ya nemeta...

*Ashman*

Yau Throughout Suna Tare, tunda ya dawo daga Side din Maryam bai sake fita ba, a Dakin da aka kwantar dashi ya maida Mata medications ɗinta ya ce ya Warke yanzu itace mara lafiyar shi Kuma mai jinya

Maida wayarsa Flight Mode Yayi ma don kar kiran Deejah ya dameshi itama haka tasan dole Reey zata nemeta.

Aikam hasashen ta ya bata daidai Ranar da ƙyar Reey ta iya Rintsawa Saboda An kawo mata Gulmar Wani saurayinta yazo sunyi fada ya shaƙeta har ta suma shima Yana ganin ta suma sai Yabita, tanajin Haka tace ASHMAN ne don Aeesh ta taɓa bata Labarin yanda Ciwonshi ya tashi bayan Meeting dinda Sukayi kwanaki, tayi ta Trying layinta Amma Abu daya yake gaya mata wato switch off, d ƙyar ta iya kwanciya da Cewar Safiya nayi zata bazama nemanta inya kama ma har Gidan su zataje duba ta, Amma kafin taje nan saita tabbatar bata ganta a ko ina ba.

Tuni SALEEM ya baza jami'ai wurin neman wanda ya kwace wayar Deejah ,Kuma cikin Sa'a An samo shi da taimakon CCTV cameran dake manne a Jikin street Light na Daidai inda Abin ya faru, ya bada wayar A halin yanzu ma wayar na hannun Saleem Kuma an Kamashi , an kuma baza jami'an tsaro ta ko'ina na asibin domin Kuwa Case din harbi ba lamarin Wasa bane, me yiwuwa Wani ke shirya mata Bita da ƙulli.

Mahaifin Maryam dakanshi ya ƙaro jami'ai na musamman domin kular masa da Tilon Diyarsa.

Gabaki daya Jinta take wani iri, ta kasa yarda cewa a halin yanzu Jinin Saleem Yana Gauraye da nata jinin , Ji tayi Gabaki ɗaya ta Tsani kanta ta Tsani duk wani mahalukin dake tare da ita a lokacin gani take duk laifinsu ne da sa bakinsu Aka sa Mata jinin Saleem, Jinin mara Mutunci Jinin dan shaye Shaye.

Dadaddare hanasu bacci tayi, sai kuka takeyi wai Jinin Jikinta na mata ciwo, a kaita Renal Unit a ɗebe jinin Jikinta a musanya mata da Wani.

Tun Mama na ganin Abin kaman wasa har ya fara bata tsoro, dare ya tsala Sosai sai sun fara bacci Kukanta ya Tashe su ta hanasu bacci, ta tashi hankulansu ta kuma hana ayi mata Allurar bacci, Cikin daren Mama ta Dannawa Abban Maryam Kira ta sanar dashi, Da kyar ya Rarrasheta ya samu ta kwanta bayan Ya dauka mata alƙawarin Zaizo gobe da safe kuma ta kwantar da hankalinta za'a chanza Mata jinin Jikinta.

Gabaki daya Ma'aikatan Asibitin masu Aikin dare Babu wanda Baisan saleem yayi donating ma Maryam blood donation ba, kan kace me?, Sun zama Trend a media Platforms din Asibin,sai yawo da Hotunan su ake ana Yaɗa Labarin

Duk wanda ya gani sai abin ya bashi mamaki babu wanda zai yarda Saleem ne Dakanshi ya Bada Jininshi asa ma Maryam this's Unbelievable.

Daga Ashman Har Saleem Babu Wanda yasan irin Wainar da ake toyawa, shi saleem ba ma'abocin bude messages Din Groups bane, Ashman Kuma Already wayansa a Flight Mode yake.


Kaman yanda Maryam batayi bacci ba haka Saleem Shima bacci gagara daukarsa yayi , wani abu ne ya Hanashi bacci, ya kasa gane Ko menene , kwance yake ya kafe celling da kallo.

Hannu yasa ya shafo kanshi yana furzar da huci daga bakinsa

Abinda yafaru dazu sai fado mashi arai yake.

Fuskar ta ya sake bayyana a Gareshi a karo na babu adadi.

Murmushin gefen baki yayi yana cizon le6en qasa ,Tsikar Jikinshi na tashi.

Tunawa yayi da lokacin da ya Hango ta tana waya da dad ɗinta tana Zuba masa Shagwaɓa

Fararen idanunta data ware Akansa Lokacin da ta Kamashi yana Kallonshi ya tuna

Wani murmushin yasaki mai sauti yana daukar Pillow ya Rungume a ƙirji.

That looks Almost drive him craze.

Tunawa yayi da hararar da ta zuba Masa lokacin.

Murmushi ya Kuma saki Wannan Karon harda Lumshe Idanu, everything about her was perfect indeed super perfect.

Tunawa yayi da yanda ta qanqameshi a Jikinta tana kuka sanda yayi driving ɗinta Izuwa Asibiti , shi dakansa ya dagata ya kaita har Mini theater Inda Aka Cire mata Bullet din Jikinta , Duk da tana Cikin serious pain a lokacin he can Recall irin Shock dinda Ta shiga a lokacin, irin baddest Look dinda Tay maj

Haka yaita zuba murmushi shi kadai kaman Sabon Kamu, a haka barci mai daɗi yayi awon Gaba dashi .

Aeesh da Ashman suma yanda Bacci ya gagare su Maryam Haka suma bacci bacci yaso ya gagaresu Amma Nasu Case din ba irin nasu bane.

Bayan Sallar Isha'i ya ɗan Zagaya ta cikin asibin kaman yanda ta saba ya barta a dakin ita kadai

Yana Fita ta faɗa Bathroom don Ta tsarkake Jikinta, Tun Ɗazu Takejin ta Uncomfortable saboda Period dinda Takeyi , so Biyu kenan Tana Chanza Underpad Amma Still she fells So Uncomfortable,

Ruwan Zafi ta haɗa Ma kanta, tayi wanka, Ta dauko Kayan Da ta cire zata saka taga Yayi staining, gashi towel duk sai kanana ne a bayin, babu bathrobe kuma.

rasa inda zata saka kanta tayi, gashi kayan da ta cire riga da skirt ne ,Babu dabarar da zata iyayi akai, ta dauko wani towel da taga yana da dan girma ta daura iyakacin shi saman cinyarta ya tsaya sai dabara ta zo mata, ta daura daya a kugunta ta samu daya kuma ta daura a kirji, sannan ta dauko wani ta lullube kanta zuwa kafada ta dashi.

A hankali ta bude kofar ta fara lekawa, bata ganshi ba,a zatonta bai dawo Ba.

Fitowa tayi kanta Tsaye,ta zauna kan Gadon ta.

yana zaune akan kujera da waya a hannunsa, tana fitowa ya juyo yana kallona, dariya ce ta kubuce masa ganin yadda ta Har hada

Please Login or Register in order to submit comment