Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yy..yamai sari'a"

Take kotu ta hautsine da dararraku ta ɓangaren yan Samarin dake zaune a wajen, Alƙali ya buga guduma akayi tsit, Dukda haka dariyarsu bai dame Bintou ba, inda sabo ta saba da dararrakun Mutane akan Tana In'ina, Hakan yasa koda ta gama karatun Sau ɗaya ta taɓa defending a Kotu, Inda ta yanke wa Mahaifinta hukunci da Kanta, Wannan shine babban Dalilin da yasa Ta shigo law, gashi Case Din Aeesh ya karya mata Budget.

gaban Aeesh tanufa tatsaya sannan tadubeta sosai ta saki Murmushi cikin tausasawa tace

"A'isha Kkk..ki share hh...Hawayen ki kinji"

Gyada mata kai Aeesh tayi, tasa bayan Hannunta ta share hawaye.

"Yawwwa Good Girl , Ina so Ki natsu ki Kwantar da Hankalin ki, ki tuna idan Kika cika saka tunani a Ranki zai shafi Ɗan dake cikin ki, ko kinaso ki haifi ɗanki da Brain Abnormality ne"

Saurin Girgiza kai Aeesh tayi, Tana share ƙwalla, haka nan Kawai taji Bintou ta shiga ranta.

Sai a lokacin da Bintou ta tuna mata ɗan dake cikin ta, ba ƙaramin daɗi taji ba, tana Son cikin kaman ranta.

Cikin kwantar da murya Bintou ta cigaba

"Idan Kinyi tunanin Wadanda kike so sun Gujeki ,ki tuna Ɗan dake cikin ki Yana Matuƙar Ƙaunar ki,yana buƙatar FarinCikin ki da walwalarki bazai so ya cigaba Da Ganinki cikin wannan yanayin ba"

Murmushi Aeesh ta sake saki a karo na farko wasu zafafan Hawaye suka sauko da gudu suka sake wanke mata fuska , Bintou ta gyara tsayuwa Cikin ƙwarin gwiwa tace

"Aa...'isha Mm..muhammad Hassan inaso ki...yima kotu cikakken bayani akan irin yy...yadda kk...ika d'auki Aareef a cikin zuciyar ki ? "

Ɗagowa Aeesh tayi, ta dubi Ashman ya Lumshe idanunsa, Sannan ya ware su a hankali yana Sakin Murmushi.

A hankali Bakinta ya fara motsawa, wanda hakan Yayi matuƙar bawa Kowa Mamaki, wasu Hawayen farin ciki suka wanke Fuskar Reey ,Sosai hankalinta ya tashi da ta ga ta daina magana, ta dauka Kurmancewa tayi.

Cikin yar ƙaramar murya ta fara magana a natse

" Ina matuqar son Aareef, Ina jinshi a zuciyata tamkar ɗan Uwana na jini, Dukda baya sona Amma kullum burina shine na Sama masa Farin ciki inaso yajini a zuciyarsa koda kaɗan ne , ina so ya nuna min so koda Kashi ɗaya ne a cikin Son da nake mishi, i think It feels nice to miss him, think about him, To disturb him and love hom, so i'm missing him, I think about him, disturb and love him, but he broke my heart ,today I admit that it was a wonderful start , he broke my trust so bad in life ,it's getting really difficult to survive Ina matuƙar Shan Wahala, Sonshi ba karamin kamu ya min ba, but love lost is like the most terrible thing ,now I can't really live this way Ni kadan nasan yanda nakeji a halin yanzu a kullum bana Cire Tsammani akan zaisoni but he only show me the way where should I go with broken heart!".....



Ta ƙarasa Maganar cikin raunin Murya hawaye Masu zafi na racing a Fuskar ta.










_kan abinda kake so baka fiye ganin aibu ba_

_so ya min bazata yasa ina fargaba_
_wasu sunce hali sai yazo ɗaya ake zama_
_ni kuma nayi musanta hakan ina tantama_

_so kan chanza hali, ko ko ra'ayin mu ma_
_Tunda shi kadai ne ke sarrafa zuciya_






_Da so kamane_
_kuma ɗan Adam ne_
_bazana bari ya shige mini Zuciya ba_


_Daga kanka na gane_

_so haddari ne_
_kumq wajibi ne, bamu tsallake ba_


_Halinka ba zaisani in gujeka ba_
_addua nasan ba abinda bata barshi ba_
_Raida zuciya ta Basu san waninka ba_

_taya ido zai rintsa bai ganka ba_





Nayi Gabas 🚶🏻‍♀️🚶🏽‍♀️🚶🏽‍♀️


Bintou ✍️

28 Nov
*WU'KA A ZUCIYA*

_(Bleeding Hearts)_


_Ina makukar godiya a gareku bisaga yanda Kuke bin labarin nan Sahu da kafa, dukda cewa bana kawo maku shi a kai akai, Amma kuma kuna bibiya batareda gajiyawa ba, nagode Allah ya saka da ALKHAYRI bisaga uzurin da kukeyi min, Allah ya bar Zumunci🤲🏼💕_


*057*

Jinjina kai Barr Bintou tayi
"Yayi kyau......"

Cikin dabara tasa ta gaya mata alakar dake tsakaninta da Aareeef da da Abokansa harda Ashman, ta kuma gayi gaskiyan abinda ya faru, ba itace tayi girkin ba Rahama kawarta ce tayi girkin, kuma Deejah tazo lokacin da take girkin, Amma bata jima ba ta tafi.


Ajiyar zuciya barrister Bintou tasauke bayan Aessh ta gama tace

" nagode yamai sari'a iya tambayoyin dazanyima Aeesh kenan "

daga haka takoma tazauna tsayin lokaci Justice Hamza na rubutu sannan yace

"kotu tana buqatar ganin Basheer ,Deejah da Rahama agabanta "

cikin sanyin bash, Deejah da Rahama sukafito suka tsaya, Deejah ta hada ido da Ashman ya auna mata mugun Kallo tayi saurin Sunkuyar dakai tana share hawaye

duban Rahama Barrister Bintou tayi cikin murmushin nan nata mai firgita Mara gaskiya sannan tasaka hannu cikin jakarta taciro wata yar karamar satchet da wata yar takarda, ta dubi Rahama wacce a halin yanzu ilahirin jikinta ya fara rawa tace

" Kafin nace komai ga list din da kika Rubuta ma Aeesh a ranar da kukayi girkin , bansan maiyasa kika rubuta wadannan sinadaran ba,ban kuma San dalilin da yasa kika nace lale a shagon bash zata siya ba, ohh Na manta fa, shi ya Kira yace ayi girkin, kunga ba abin mamaki bane tare kuka shirya kisan"


" Objection My Lord "

" barrister Abdul qorafi bai karbuba Barrister Bintou cigaba "

wani irin murmushi Ashman yasaki tabbas tunda Baffa ya sare a goyon bayan Danshi tho Akwai kamshin nasara a wnnan shariar


Bintou tayi Murmushin Gefen baki tana Jinjina kai, sanda zata fara Shariar da Fari taji tsoro matuka Saboda tasha Jin Labarin Justice Hamza Mutum ne mai Wayau da kwarewa wajen Daurewa karya Gindi a shariar da Dansa ke Jagoranta ,Amma yanzu sassaucin da ta gani a taredashi Shi ya bata kwarin gwiwa ta cigaba.

" Deejah ada kowa yasan Ku tare Ku uku, dake da Reey da Aeesh Kawayen juna ne, hasali ma lokacin d kika fara ganin Ashman ita kika like mawa har kika samu ya Aure ki ta dalilinta,Amma sai auren shi bai Amfana miki komai ba , donshi Gabaki daya rayuwarsa ya taso ne a tareda Yar Uwarsa bashida Lokacin Wata Diya mace, Kafin yayi Mu'amala da kowace mace saida Amincewarta kaman yanda Amincewarta Ta shigo dake cikin rayuwarsa ,da Kika fahimci hakan sai kika dau karar tsana Kika daura mata bakya kaunar ganinta, kinsha Yin rantsuwa akan sai kin hallakata, akwai ranar da kika fasa mata kai ma tsabar haushinta da kikeji, Amma abin mamaki kwastsam Sai gaki a makarantarsu a ranar Da abin ya faru cikin salin fuska wai kinzo tayata murna Harda tayata Wanke kayan miya, mijin kune ya turo ki ki tayata girkkin saboda Lalurar dake jikinta ko kuma kece kikaga dacewar hakan?"

"Objection Ya mai shari'a...!"

"Objection denied..., Barr bintou continue"

Abdol ya zauna yana huci Cikeda Mamaki da haushin sauyin Halin abban nasa a zuciyar sa yana turrr da irin zuciyarsa mai Shegen son mata.

Wani irin zufa ne yake sauko ma Deejah, tasa bayan hannu ta share cikin in'ina wacce tafi Na bintou tace

"Ehmmm...m uhm... Ehm....Dama nazo wucewa ne..Sai naga ya dace in shigo mu gaisa tunda ranar ne graduation dinta, shine Na iske tana aiki Na tayata, amma Ban Dade ba iya kayan miya Na tayata wankewa"

Jinjina Kai Barrister bintou tayi tace
" Da kyau, Kodai dalilin hakan ne yasa Kika dawo Nigeria Cikin satinnan(Don ki wanke kayan miya?)"

Shuru Deejah tayi zuciyar ta Na racing, Barr bintou ta jinnina kai sannan ta juyo kan bash

"Malam Bash maiyasa ka kira Aeesh kace Aaareef yace tayi maku girki Alhalin Karya ne?"

Zaro ido Bash yayi yana hadiye numfashi tsabar tashin hankali, yajuya yadubi Barrister Abdool, rumtse ido yayi ganin Fuskar nan babu rahama a cikinta, cikin matuqar razana dajin tambayar da Bintou tayi masa yace

" Am...uhm...ehm dama hakanan kawai naga ya dace uhum ..eh yeah Haka ne"

"kkk...kenan babu wani dalili, just like dat ? "

d'aga mata Kai yayi alamar eh jikknshi na kyarma murmushi Barrister Bintou ta saki sannan tace

"Ttto bb bayan Ka Karbe kudaden Aeesh a lokacin da Tazo Siyayya wajenka meyasa Kayiwa guban mazubi da Robar Cccurry? Ko dama chan haka Kuka tsara kisan?"

"Objection My Lord yakamata Barrister Bintou ta daina jinginama Bash laifin kisa kai tsaye "

"Barrister Abdul qorafi bai karbuba duk tambayoyin da Barrister bintou ta keyi akan hanya suke cigaba Barrister "

Duban Abdul bintou Tayi ta saki murmushi, Sannan Ta gyara tsayuwarta ta cigaba

" kkkk...kotu tana sauraranka"

wata irin zufa tafara karyo ma Bash cikin in ina yace

"Eh Tabbas ba Curry bane a Mazubin Amma ban San Asalkn Meye a ciki ba, Nima Rahama ce ta kawo min tace in zuba, Sabd ya zama a madadin curry "

"If i guess kaima a wannan Game din bin umurni kake"

Girgiza kai yyi yace

" a a ni ban San Komai ba"

"Are u sure ? "

Jinjina Kai ta sake yi.

"Ka kira Kace ayi girki, ka siyarda Guba, ka ninka kudin cefane ka karbe yanzu fada Min cikin wadannan Biyun wacece asalin Wacce ta zuba Gubar?"

Bintou ta fada tana nuna Su Deejah da sukayi tsuru tsuru.

Shuru basheer yayi yana binsu da Kallo
Bintou ta juya akalar tambayanta akan Rahama

"Malama Rahama ko zaki iya gayawa Kotu ya dangantakar ki take da wacce ake zargi wato Aeesh"

Rahama ta share zufa
"Ni yar makarantar suce, kuma munyi aiki a Asibitin Dr Sufyaaan Lokacin suna practical"

"Da kyau ko zaki iya gayawa Kotu dalilin da yasa kika shirya wannan wasan?"

"Ranki shi Dade ban shirya komai ba"

"Meyasa kika umurci bashir da Ya kira kuma kika Mikawa Deejah guban da zaa zuba a abincin.😰😱...?, in fact daga karshe kece kika zuba gubar"

Sunkuyar dakai Rahama tayi,jikinta na karkarwa tamke fuska Bintou tayi sosai sannan tajuya ta kalli baffa

" Mmm..my lord, Bashir ya tabbatar ma kotu cewa ya kira Aeesh yayi mata karyar aareef yace ayi masa girki, Sannan Ya siyar mata da Guba a matsayin curry ya kuma hada Baki da waennan mutane Wajen zuba Guban domin kuwa dukkansu Sun taru ne akan Kuduri daya wato haushin Aee..Aeesh ta shige masu gaba a Wajen Ashman, sunso su kasheta Sannan Shima Aareef ya mace bayan yaci guban sai Su Kalawa Kawarta reey, Sunsha Kawo ma Reey tayin Ta kashe Aeesh zasu biyata kaso mai Tsoka amma Taki, hasali ma tun daga lokacin takai report office din yan sanda ,Tuni muka shigar da wanchan report din cikin wannñan case din"

Hayaniya Sosai Kotu ta dauka, Alkali ya buga Guduma Kowa yayi tsittt.

Barr Bintou Ta cigaba

"Bayan nan Sunsha Kawo mata hari Allah Na tsallakar da ita, amma abin tambaya anan wacece Asalin wacce ta zuba Guban?, Wacce ta wanke kayan miyan ko kuma wacce Ta taya Girkin?"

A hankali ta juyo ta dubi Rahama

"Rahama Kince baki Tayata girki, Sai kuma Gashi CCTV camera Na hostel kichen ya damkeki dumumu "



Cikin kuka Rahama tace

" Na Rantse wallahi bansan komiba "

" da gaske? "

Wani faifai bintou ta fito dashi, ta mika alkali ya duba sannan ya bada umurnin a jona
Ta mika CDn aka jona Sai gashi Rahama ta bayyanana a bayan kitchen tana Girki, hayaniya ne ya kaure a Kotun, Alkali ya buga guduma akayi tsittt.

" yanzu idan har kin tabbatar babu Ruwanki a baki Alkurani ki rantse cewa wannan bake bace"


"Objection yamai sari'a Catset bashida Wani alaka da wannan case din don haka bai Kamata a tursasata akan dole ta rantse ba "

"Barrister Jaleel qorafi bai kar'buba yazama dole Deejah ta dafe alkur'ani kotafadin gaskiya "

cikin sanyi Barrister Abdul yakoma yazauna zuciyarsa Na karyewa ,Rahama tasa kuka tace

" Bazan iya dafa Alkurani ba"

dubanta Barrister Bintou tayi sosai tace
"Why..?"

sake fashewa da matsanancin kuka tayi tace

"Banida Sallah"
"Da gaske? "

"Na rantse da Allah, Amma watace ta shirya komai, ni kaina bansn Guba ne a ciki ba,Sabida kudaden da Akabani shiyasa na Amince,amma Allah nima bansan waye nide anzo har wajen aikina da rufaffun fuska an bani aiki"

" kina nufin bakison ko wayeba sabida sakarci da mugunta irin naki ko?"

Shuru Rahama tayi tana hawaye
Bintou ta juya ta dubi Alkali

"yyy..yamai sari'a Ina roqon wannan kotu mai Albarka data wanke Aeesh agaban kowa tunda ayanzu kotu ta tabbatar batada laifi sannan Ina roqon abada umarnin mika gawar kamal danyi masa sssuuutura sannan a qarshe inaso kotu tad'age wannan shari'ar zuwa wani lokaci yadda zamu binciko duk wani mai hannu cikin wannan kisan nagode yyy yyamai sari'a "

Daga haka Barrister Bintou takoma tazauna bayan 'yan rubuce rubuce justice Hamza yace

" Bisaga qwararan hujjoji da kotu tasaurara ta tabbatar cewa Aisha Muhammad Hassan batada laifi dan haka kotu ta wanketa sannan tana bata haquri akan sakata cikin damuwa da akayi sannan wannan kotu zatatsare Rahama,Deeejah d bashir Har zuwa zama na gaba don haka wannan kotu mai albarka tad'age wannan shari'ar zuwa 12December Na wannan Shekarar Courrrrrt.....! "

Aguje Aeesh tarugo ta Reey ta saki wani irin kuka,Share mata hawaye Reey tayi
"Kukan ya Isa Haka Besty, Karki wahalar mana da Unborn"
Waro ido tayi, sai kuma tayi saurin fuskarta da tafukan hannayenta tana murmushi

"Nidai besty banida Komai ,single nake"
Harararta Reey tayi
"Yar rainin hankali baaa"

Daidai lokacin da Barrister Bintou ta iso wajen ta mika mata hannu tana murmushi

"Congratulations Mrs Ashman"

Wasu kwalla ne taji ya ciko a idanunta ta maimaita sunan a ranta

(Mrs Ashman) _Tabbas sunan ya dace d ita, Amma ada kenan snda akwai igiyoyinsa uku akanta, yanzu kam yayi mata Nisan nisa, Nisan da bazata taba samunshiba har abada.

Ji tayi an Kama hannun ana Share mata kwallah, dagowa tayi ta dubeshi fuskarsa dauke da wani annuri Na musamman.

"Ihty....Mu tafi kafin yan jarida su fara haska mn fuskar matata"

Zaro ido Reef tayi tana to she baki cikin dariya, ya harareta ta kauda kai tana dariya cikiciki.

janye hannun ta Aeesh tayi tana Kama hannun Reey tareda Make kafada tace

"Ni bazan je koina ba, Ba ka sake ni ba?"

taqarashe fad'ar hakan cikin tsananin kuka

Abba da Inna Saude suka zo wucewa ko kallonsu basuyi ba, chan ta hango Ya Sadeeq da Habeeb suna shirin Shiga mota, tabi su da gudu ta shige tana cigaba da kukan ,Ashman da Reey Suka bita da kallon mamaki Yayinda Zuciyar kowannensu ke ayyana Abubuwa da dama Musamman Kalmar data ambata wai ya sake ta.

*Bamalli*

A fusace ya Fito sai faman haki yake, dogarawa sai Zubewa suke suna masa kirari, amma ko kallonsu baiyi ba.

Inda aka tanada wajen parking motoci ya nufa, tun kan Ya iso driver ya bude masa yana Russunawa tareda kirari Shiga yayi Driver Ya figi motor da gudu suka bar harabar Masarautar, Sun danyi nesa Da Gidan Sannan Driver ya juyo cikin tsoro yace

"Ranka shi Dade Ina muka Nufa?"

Bai amsa masa ba sai tsakin da yaja
"Change The Aux..."

Nan take driver ya kure motor da Kida mai hawa kai.



*MARYAM*
Yau tashi tayi da wani irin bakin ciki, Wani Abu ne ya tsaya mata a makoshi yaki wucewa, Sosai take son tayi Kuka ,ko zata samu ya wuce Amma ta kasa gefe guda kuma ga wani irin faduwan da gabanta keyi.

Tun dazu ta fito daga wanka, ta kasa Shiryawa, ta fiddo duka kayan sawanta Babu Wanda yayi mata, sai Turo baki take tana Jan tsaki.

Closest Din da ta zuba Kayanta Na Turkish ta bude ,Shekaru biyu kenan da dawowanta Amma bata taba yunkurin bude Shi ba saboda Tsanar da takeyi ma Wanda yayi sanadiyyar samunshi a gareta.

Hannunta har wani rawa yakeyi ta bude Shi tana jin bacin ranta Na daduwa.

Da Diary dinshi ta fara tozali, Sunyi Exchange garin Sauri ta dau nashi ta manta da nata a wajenshi, kasancewar a lokacin Ma'ajiyan Litttafansu daya ne.

Lumshe ido tayi tana tuno abubuwa da dama , Tabbas Saleem ya taimaka wa rayuwarta a baya, kuma ya wulakanta ta.

Ajiyewa tayi a gefe Sannan ta fara Dudduba kayan, almost duka kayan Kananu ne kuma Shima yana da shigen su, kasancewar sanda suke tare komai iri daya yake siyo masu.

Material daya ne a ciki cream color Dinkin simple bubu ne, Tsadaddar Material ne Wanda yasha adon stones sai kyalli yake, ta sama anyi mata aiki kalar golden Brown yasha Adon diamond stones sai kyalli yakeyi.

Gashinta da yasha gyara ya sauko har saman bayanta ta tubke shi da golden brown ribbon.


Ita kanta data kalli kanta a madubi sai da tayi mamakin irin kyan da tayi, Wannan Shine Karon farko da kayan da Saleem ya Siya mata ya burgeta har cikin ranta.

Dairy dinsa da ta ajiye a gefe ta dauko ta fara bubbudewa da Farko hotonshi Na yarinta ne ya farayi mata Sallama Murmushi tayi ganin yanda ya wage baki yana faman dariya, hoton yayi kyau Sosai.

cigaba tayi da bubbudewa tana wuwwuce hotuna da surutai batareda ta kranta ba.

Hotunanta da gani Shi yaja hankalinta, Hotunan Ta randa aka kawota makaranta Tana yarinya, idanunta Shabe shabe da hawaye sai a yanzu ta sake tabbatarwa Itace Umman Ayyan saboda tsananin kamannin da yakeyi da ita , ta kasan hoton ya rubuta

*I hate her*

Tabe baki tayi a fili tace
_I know..!why Sai ka sani a Dairy Naka?_


Cigaba Tayi da bubbudewa tana Wuce rubutun sa batareda ta Karanta ba, Abin mamaki Kowane shafi a littafin Akwai hoton ta da rubutu a kasa Duk kalamai ne Na nuna tsananin kiyayyarsa a gareta, Chan Tsakiya ta hango Wani hoton ta a ranar da ta fara attending lectures a Renal Department fuskar nan nata dauke da murmushi a kasan shi ya rubuta *Her smile oppressed* _I Feel her here_ Sai yayi zanen Zuciya a kasa.



Wani wawan Murmushi ne ya kufce mata, hoton ne yasa taji tana son karantawa, ta Maida Page din Farko a natse ta fara karantawa.

Tun daga First page taji jikinta yayi Sanyi , kowane Dan Adam da nasa irin kaddarar ni tawa irin kaddarar kenan, Inada Uwa da UBA ga yan uwa takoina Amma a tsakiyan su Na kira kaina da maraya ,Kuma na Amsa da Zallar shauki.

Ban San komai ba Sai tsana da kyara bansan wata soyayya ba saboda baa Nuna min shi ba, shiyasa nima banason kowa ,Na tsani kowa .

Mahaifiyata Wacce ta kawoni duniya ita nafi tsana, Meyasa ta haifoni Alhalin tasan bazata so ganin Farin ciki na ba?, Meyasa take azabtar dani?, a kullum burina bai wuce in wayi gari inga babu ita ba.


Tun ina Karami nasan Wahalhalun rayuwa, abban na bai Damu da Rayuwarmu ba, iyakacinshi ya sauke nauyin da ya rataya a wuyanshi na kudi, bayan haka babu Wata alaka a tsakaninmu a lokacin, da ciwon bakin ciki na tashi, Masifan Nan nawa ya samo asaline tun daga yarinta ta sanadiyyar azabar da aka gana min.

Wacce na dauka a maysayin Uwa ban tabajinta a raina ba ko kadan kiri kiri nake nuna na tsaneta a fili don Ni ban iya kara ba, idan abu bi min ba sai kowa yagane,, Shiyasa Duk Cikimu tafi tsanata, a gaban Kowa Nunawa take kaman tana Kaunata, Amma ni kadai nasan azabar da nakesha a wajenta

Da ruwan Karara take min Wanka azaba da kaikayi suka kusa zautar dani Da Na fito wanka nakejinshi ,Sai inyita gurzan jikina duk abinda Na gani ,Jikina kullum cikin jini , tsabar kaikayi kona sa kaya abin ya motsa yaga su nake ,haka zan waje fito ina ihu a tsirara nake gurza jikina a kasa don azaba babu mai taimaka min a ganinsu haukacewa nayi.


, Hakan Yasa aka kai ni asibiti, Amma koda muka Nufi asibitin cewa akayi abin yafi karfinsu Take Sukayi Referring dina i zuwa Psychiatric Hospital anan nayi jinya har Abin ya lafa min, Watanni Na Uku cur kullum sai an min Electro convulsive Therapy nasha azaba a wajen su sosai ,Jikina kullum a kumbure da karfi da yaji suke son maidani mahaukaci, koda da Na dawo ma abin babu Sauki.

Kowa kallon mahaukaci yake min, wasu har kirana da mahaukaci suke saboda na taba Zama a asibitin mahaukata ,babu wanda yasan Abinda ke faruwa dani, kaman an rufe min baki ban taba gayawa kowa ba, Tsoron mahaifiyata ya shigeni Na dage akan bazata cigaba da yi min wanka ba, Na komayi da kaina, Amma abin babu Sauki sai ta koma zuba kararan cikin pipe din Part dina hakan yasa abin yyi kamari aka sake maidani chan asibitin mahaukata wannn karon nafi shan wahala akan zuwana Na farko Amma dukda haka naji dadin zaman da nayi Sosai Saboda Na koyi Hauka Wacce tafi illa a cikin jama'a irin haukan nan Na duka da cizo.

Koda Na koma ban yarda a sake cuta Na ba, da zarar an cuce ni nima ramawa nake da haukar duka duk wanda abin ya juyo ta kanshi a lokacin Sai na fitar mas da jini nake kyaleshi

A rayuwata ban San Wata soyayya ba, yan uwana Duk yan gata ne dukda ba Soyayyar gaskiya take nuna masu ba , kowanne da Nashi tanadin da tayi masa.

Kallon littafin takeyi hawaye na truwa a idanunta, tausayin Saleem na neman Shiga zuciyarta tana mamakin meyasa Inna Saude zata Tsaneshi?, koda tayi zaman Gidan taga Babu Wanda take nuawa Kauna da soyayya irin Saleem, taya Uwa zata azabtar da Danta ta wannan Sigar?, wanka da karara fa?, Anya....?

Amma kuma saleem Bazai rubuta karya ba.


Rufe Littafin Tayi don Ji tayi zuciyar ta bazata jure cigaba da Karanta Azabar da aka gana masa ba, bata son Abinda zaisa taji zuciyar ta taraunana akan Saleem.


Tunani ta shigayi akan rayuwarsu ta baya, allah Sarki Ashe dalilin da yasa ya zabi zama shi dayansa kenan babu dangi?.

Saurin maida kwallarta tayi ganin Suna Neman Digowa, Saleem bai cancanci a zubar masa da kwalla ba.

Tunowa tayi da Sakon da ya ajiye mata Ran nan "kenan yanada masaniya akan Umman mu?, ya karanta Dairy dina kenan"

Sai kuma ta Waro ido ta Dora hannunta a ka
"Saleem in ka karanta Dairy Na kasheni"

Hannunta Na rawa ta dauko wayarta cikin tashin hankali ta lalubo numbern sa wanda tayi saving da NASTY DOCTOR (Masifaffen likita)

Kallo yabi Wayarsa dake Kan Table kamar Wanda yaga abin tsoro sannan ya maida kallonshi kan system din gabanshi yana cigaba da danne dannenshi.

Ayyan dake zaune kusa dashi ya kalli Fuskar wayar ganin taki yankewa ganin Hoton Maryam yasa yace

"Daddy Mum is calling"

Janyo wayar yayi batareda ya Yarda da maganar sa ba, ya kalli fuskar wayar

"QUACK NURSE🐔" (fake Nurse, Wato nurse dinda bata iya aikinta ba) sai emojin Kaza a bayan Sunan

Kasaitaccen murmushi ya saki, Ya mika ma Ayyan Wayan bayan Ya dauka

Jimm tayi, ta rasa me zatace , Shuru ne wayan Ya dauka For some minutes chan taji muryan Ayyan yana cewa

"Mummy...!"

"Aayyan..!, ina Daddy?"

"Dadd...
Muryan Saleem taji yana cewa

"Bring the phone...!"

Difff aka datse wayan

Wani Abu Maryam taji ya ratsata Daga kai zuwa tafin kafa, ga wani dunkulalen Abu daya tokareta a maqoshi.

Tunda take bata taba wulaqanta kanta irin nayauba, she felt totally embarrassed, haushin kanta ya kamata ,ji tayi dama bata kirashi ba.


Mutuwar zaune tayi tana kallon wayar idanunta adan ware alamun mammaki qarara a fuskarta.

Dilin....!, wani sakon Ya shigo wayarta, Saurin dubawa tayi, Nasty Doctor ne.

Location da hotuna ne.

Ta bude hadi da zooming Hotunan
.*VINGO VULCH*
Ta maimaita a bayyane hadi da jinjina kanta, Simple makeup tayi ta dau dau jaka hadida yafa mayafi Golden brown ta fito tana karkada mukullin Motarta a hankali, Mama bata nan don haka bata wahalar da kanta Sai ta fada mata ba, Kai tsaye taja Motarta ta fice daga Gidan, Tana Fita motar Bamally ya danno kai.

Daidai Lokacin da Zeeyk ya fito harabar gidan Cikin washe baki , Waya ne a kunnensa yana fadin

"Baby Na aika Driver ya daukoki zaki ganshi da Red firari,....ki kiyaye please Nigeria ba kamar UK nace ..WELCOME TO NIGERIA"

Wani irin parking Bamalli yayi ya badeshi da kura hakan yasa wayan dake hannunshi ya Subuce ya fadi kasa, Sosai kuran ya shiga jikin Zeeyk ,Take ya fara wani irin Tari, Zuciyarsa Na masa wani irin zaafi sosai.

A fusace Muzzammil ya fito ya fara zazzage masa buhun Masifa, ta inda yake shiga bata nan yake fita b, akan me kanwarsa zatace shi take so?, gashi yanzu Mai martaba ya tsaida ranar aurensu nan Da Sati biyu.

Abu kaman wasa Wani irin Kakari Zeeyk ykeyi yana dafe da kirjinsa, Ko kulada yanayinsa baiyi ba, ya cigaba da zazzage Shi, Duhu ne ya mamaye ganinshi

Please Login or Register in order to submit comment