Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a wajenta baiƙi su dawwama a haka ba,ta dau nauyin komai na rayuwan shi zame masa Uba,indai harkar kuɗi ce Yana kawo kukansa wajenta take Share masa, koda batada shi sai ta nemo, cikin in Ina yace


"Now Aeesh Tell me, Kina Nufin zaki iya Rabuwa sani?"

"Aareef...!, Are You asking me that question?, After you insulted my parents?, Bai kamata na cigaba da Alaƙa da kai ba, And You said Bai dace kayi alaƙa da mara Tarbiyya ba"


Dariyan takaici yayi

"A'isha muhammad Hassan, Kin dauka zaki iya rabuwa dani haka cikin sauki ne?, Wlhy Ni dake har Abada Mutu ka raba"

Ranta ɓace tace

"Aareef It won't Be permanent condition dude, you can't even Put smile on My face For once"


"You must be a joker Aeesh, Ko kin Manta alƙawarin da kikay wa duniya cewa Bazaki Rabu dani ba?"

A fusace tace

"Then Suit it urself dude bazan Cigaba da kasancewa tareda kaiba, this relationship is over, and don't Expect me crawling into your life again, and I mean Every word this Time excuse me..."


"Don't dare cut the Phone out on me?, ba kince Zaki Rabu dani ba?, Wait and see ,zakiga abinda zanyi Miki"


"Do the worse....bye Okay"

Kit ta datse wayan, Ashman da tunda ta fara Wayan yake Binta da kallo yana saka abubuwa da dama a ransa, ganin yanda lokaci guda ta burkice masa tana Magana a matuƙar fusace.

Kallonta yayi na tsayin mintuna uku har yanzu kanta na ƙasa tana sauke Numfashi, sannan ya janye idonsa ya rankwafo da kansa kadan, saida yad'an cije lips d'insa sannan yasaka hannayensa ya karbe wayar hannunta, tamkar yaga abin ƙyama ,haka ya d'aukota yana jujjuyawa acikin hannayensa, sai wani kuma d'aure fuska yakeyi yana kauda kai, kaikace ya dau abin ƙyama ne.

"Ina Kika kai Wayan ki ZERO 20?"

Yayi mata maganar yana Bin fuskar ta da kallo

"Na Ba Aareef"

Ta bashi amsa kai tsaye

"Yayi kyau"

Ya faɗa a taƙaice kawai, kasancewar yau yan miskilancin sa ne suka motsa bai sake tofa komaiba .

Haka kawai ya samu kansa da faduwan Gaba,Tsaki yaja da rumtse ido kamar irin mai takaicin kansa ɗin nan.

Ya sake jan tsaki ,Tsawon mintuna ya kasa horn balle yunƙurin shiga gidan, Aeesh sai Huci takeyi, kuka take sonyi Amma kuka yaƙi zuwa..

Ga kiran Deejah dake shigo masa a waya, amma ya kasa yin komai. Sai da ya sake shafe kusan 15mins har mai gadi ya gaji da leƙowa ransa fal mamakin lafiya sannan ya sake danna masa horn, Mai gadi ya buɗe masa ya shigo.


Gabaki ɗaya Ransa a ɓace yake, a hankali ya tura murfin motar da kafarsa ya fito yana wani shan ƙamshi, itama fitowa tayi Tana Haɗe rai,babu wani karsashi tare da ita


Bataji daɗi ba da taga Ransa a ɓace, tasan Itace dalilin Ɓacin ransa, Kuma tasan Hukuncin Duk Macen da tasa Ran Mijinta ya ɓaci akanta, Dukda bata so yasan tasan da batun Auren Yanzu, amma bazata iya jure shiga Hakkinsa ba .


A hankali ta saƙalo Hannunta cikin nasa, Ya janye hannunsa yana watsa mata Wani irin kallo, bata ji dadin haka ba ,amma tasan yanda Zata rarrashi Abinta, da ƙyar ta iya haɗiye ɓacin ranta ta bibbayan shi.


A Parlor suka iske Deejah da Waya a hannunta, tana Latsawa ganinsu a tare yasa gabanta faduwa, ta kauda kai ko Amsa sallamar da Sukayi batayi ba.


Buɗe idanunsa yay ya saukar dasu akan Deejah da ta hade girar sama da ta ƙasa, yayi Murmushi haɗi da ware mata hannayensa

"Come on baby"

Dagowa Deejah Tayi ta dubeshi unbelievably ,Idanunsa ya ɗan lumshe ya buɗe akanta.

Ai da gudu ta Taso ta Rungumeshi, gaban Aeesh ne ya fadi hawaye suka zubo mata.

Batare da ya dubi Aeesh ba ya lakaci hancin Deejah da yatsansa.

"Where is my food?"

Aeesh Hawayen daketa faman ziraro mata ta share muryarta na rawa Tace.

"Kazo ka Maidani Gidan Mu"


Saida Ya sake rungumo Deejah jiikinsa da sumbatar hancinta Batareda ya kalleta ba yace

“bbu inda zaki"


Tayi masa shiru tuni hawaye ya far sauka idanunta.

Woohoho

Zokuga Farinciki Gun Deejah, ji Tayi kaman ta zuba ruwa a ƙasa tasha , Dukda tasan Ƙila laifi tayi Masa yake so ya rama ta Wannan Hanyar Amma sumbatar da yayi mata kadai Ya biyata.


Zama Aeesh tayi akan Kujera ta kaɗa kanta da cibiyoyin ta sai kuka, bata san adadin time dinda ta dauka a haka ba, ta dai ta ɗago taga babu Kowa a Parlor .


Kuka ta Saki mai Ƙarfi ta cire Small hijab dinta Tayi wulli dashi, ta kwanta a ƙasa tana Birgima tana Kuka kaman ƙaramar yarinya.


Ganin Deejah Ta shigo ranta a ɓace ne yasa ta zauna ta Nutsu tana Share hawayenta, Deejah tayi mata kallon Sama da ƙasa ta watsar Sannan taja dogon Tsaki ta wuce.

Miƙewa Aeesh tayi, ta kama hanyar ɗakinsa gadan gadan, tana jin Deejah na kiranta tana ina zata, tayi banza da ita.


Zaune ta iskeshi a gaban mirror Yana Goge Jikinsa da towel Alamun Wanka ya fito,Wani ƙaton abu taji ya tokare mata maƙoshi wato har sun Gama abinda zasuyi yayi wanka, Wasu zafafan hawaye suka sauko Mata, tasa Bayan hannu ta sharesu.


Ta zauna a kusa dashi, tana zama ya Tashi ransa a ɓace, binshi Tayi yana ganinta ya juya fuska,inda ya juya fuska ta zagaya, tsaye kawai yayi ya zuba mata manyan idanunsa da sukai jazur da ɓacin rai, tsawon mintuna uku kafin ya kauda kai Batareda yace komai ba, ya Zauna gefen gado hadi da dafe kansa dake sara masa.

Zama tayi a ƙasa, tana fuskantar sa,Hannu takai ta shafi gemunsa hakan yasa ya ɗago yana dubanta

"Haba Ahky....kayi Murmushi mana"

Baice komai ba ya Kauda dubansa daga Gareta, sakin Gemun sa tayi, ta koma kan gadon Itama ta zauna kusa dashi.

Bakinta ta kai saitin Kunnensa, ta hure masa iska a ciki, cikin Sigar Rarrashi ta raɗa mishi

"Haba Baby na ,don Nayi laifi ban Cancanci Irin wannan Fushin daga garekaba"

Ta ƙare Maganar da cije Kunnen kaɗan.

Ɗiff yayi kamar wanda ruwa ya cinye shi, komai nasa ya tsaya,

Wani Abu yaji ya zo zuciyarsa ya tsaya yaqi wucewa, is she sick?, Shi Zata duba ta kirashi baby?.

Ƙarar door bell dinda Yaji ne ya tsaida shi daga Tunanin da yake, ya Tashi ya Buɗe, Deejah ce Hankalin ta a tashe take cewa


"Honey...Yan sanda na waje suna neman ka a waje"


"Yan sanda kuma?"


Ta gyada masa kai, jim ya danyi yace

"Okay jeki Ina zuwa"


Dawowa yayi, ya ƙarasa shiryawa ,ya zura Milk jallabiyarsa Mai tsantsi, Sannan ya fito, Aeesh ta Mara Masa baya suka Wuce Deejah dake zaune a Parlor ta bisu da Kallo tana taɓe baki, a waje suka iske 'yan sanda Rashe Rashe ta ko ina, Aareef a tsakiyan su.


Suna fitowa Aareef ya nuna ta da Yar yatsa

"Yawwwa Oga, gata nan..... itace ita ta kashe shi"


"Shut up...!"

Macen Yar sandan cikinsu ta katse shi.


Daidai take Binsu da kallo,Aareef na tsaye, bayanshi police ne ta koina ,wani irin rawa taji jikinta ya dauka kanta nawani irin ciwo tana binsu da kallo daidai dai dai.

wani irin kallo ASHMAN ya watsa masu yace

"Lafiya...!"

Daya daga cikinsu Wanda aka rubuta A.K hayi ajikin tag dinshi ya Harareta

"Kece A'isha Muhammad"

Jikinta na rawa ta daga kai

"Kinsan wannan?"

Ya fada yana Nuna Aareef dake tsaye yana Huci, kafin ta bashi Amsa guntuwa baƙar Macen ta kamata Ashman ya kwaceta da ƙarfi, cije lips dinshi yayi yana kallon mummunar Fuskar ta mara rahama yace

"What are you up to "

Matar tace

"fine i think zata fadi gaskiya in munkai ta station"

Wani giant dansanda ne ya tako gabansu, hannunsa riƙeda handcuff

"Miss A'isha Muhammad Hassan you are under arrest for Poisoning and Attempted Murder, you have the right to remain silence because anything you say or do will be used against you in the court of law"

arude ta kalleshi heart dinta nawani irin racing da tunda take a duniya batajin zuciyarta yataba irin gudun nanba,ta kuma duban Aareef a ruɗe, ya Banka mata Harara.

Bakinta na rawa cikin Harɗewan harshe tace


"Wa... Wa na kashe?"

"Kamal Mana"

Aareef ya Bata Amsa, dafe ƙirji tayi hawaye Suka zilalo mata.


"Innalilahi Wainnailayhirraji'un....."


"Arrest her...!"

AK Hayi ya bada umurnin a kamata, nan take Baƙar gajeruwar matar ta ciro handcuff Itama, Aeesh ta koma bayan Ashman tana kuka, Ashman ya tare Yar sandan Dake ƙoƙarin janyo Aeesh a bayansa.


"Miss police lady...Babu Inda zata, Aeesh bazata iya kisan kai ba, Maybe Kun saɓa hanya ne"

"Mr Man kodai tare kuka hada baki Kuka kashe shine?"

Ɗaya daga cikin kurtayen yansandan yayi maganar cikeda rainin wayau.

Rintse idanunsa yayi cikin k'unar zuciya, murya a sark'e yace

"Babu inda zaku kaita, idan da gaske kuna Zargin ta aikata, kuje kotu ku karɓo Arrest warrant"

Wasu hawaye masu zafi suka zubo a kumatun Aeesh ta dubi cikin idonsa, cikin kuka sosai muryanta a dishe tace

"Ka yarda dani Zaujee.....ban sa ma kowa guba ba, wlhy bani na kashe shi ba ...."











Nayi Gabas 🚶🏽‍♀️🚶🏽‍♀️



Bintou ✍🏼


Nov 23rd


[12/7, 8:26 PM] { Queen_Hernah }: *WUƘA A ZUCIYA*
_(BLEEDING HEART)_





*055*



Wasu hawaye masu zafi suka zubo a kumatun Aeesh ta dubi cikin idonsa, cikin kuka sosai muryanta a dishe tace

"Ka yarda dani Zaujee.....ban sa ma kowa guba ba, wlhy bani na kashe shi ba ...."

Ta fada Cikin kuka sosai

Wani irin rauni ya kama zuciyar Aash tausayi da ƙaunar Aeesh ya ƙara wanzuwa a zuciyarsa.

tsaye kawai yayi ya zuba mata manyan idanunsa da sukai jazur tsawon mintuna uku kafin ya kalli yan sandan dake tsaye suma kallon su suke. Cikin ɗacin murya yace,

“Are You inviting Her or you came to arrest her"

Shuru Sukayi don ba'a basu Izinin Arresting ba.

Ashman ya Girgiza kai cikeda takaici yace

"Ok ku tafi zamu Biyo ku"

Ya kamo hannunta suka shige ciki sukabar su a tsaye

Kuka yakeyi sosai tana Fidda wani Numfashi da kyar, hakan yasa Ashman ya saki hannunta ya yi tapping kumatunta


Cikin kulawa yace

"Ihty What's wrong?"

Bata iya bashi Amsa ba sai Numfashin da take fiddawa da kyar, a hankali ya zaunar da ita saman Cussion.

Ya daura kanta akan kafarshi ya tattare karamin scrub hijabin ta ya cire mata shi, hakan ya bayyanar da kananun zanen da ya zubo har Gadon bayanta, Lumshe ido yayi, a hankali yace _Masha Allah_

Da Hijabin ya Share mata zufan dake ɗiga a goshinta,a hankali yasa hannu ya tattaro rigar Scrub dinta yana Ƙoƙarin Zame rigar Jikinta ganin tana Zufa ,tayi Saurin Dafe hannunsa Tana girgiza masa kai hawaye na Kwaranya a Idanunta, Sakin rigar yayi , ya kira sunanta a hankali.

"Ihty ...."

A hankali ta ɗago jajayen Idanunta ta Kalleshi

Hannu yasa ya shafo kwantaccen Gashinta

"Tell Me ,What happened?, Wayace Kiyi Girkin?"

Jim Tayi tana Share ƙwalla, saida ya maimaita tambayan sa sannan ta fara magana cikin sanyi.

"Kawai naga ya Kamata ne shiyasa nayi masa....”

Tafukan Hannayensa yasa ya juyo face dinta, ta Kalleshi ,Amma ta kasa Kallon cikin Idonsa yace

"Tunda nake ban taɓa ganin Kinyi Girki ba, nasan Baki iya Girki ba.... tell me Waya yi Girkin?, A ina kika Siyo Abincin?"

Shuru tayi Tana ƙoƙarin Maida hawayenta

"Ahky...."

Ta kira shi cikin sanyi, sannan Ta ɗago ta dube shi cikin ido.

"Nasan kai kaɗai zaka iya fahimtar halin da nake ciki......!"

Riƙo hannunshi da tayi, ya saka shi saurin dagowa, lip ɗinta daya bushe ta ɗan lasa zuciyata na wata irin tsitstsinkewa take Hawaye masu Ɗumi suka silalo a kumatun ta.

“tun asali Aareef bani yake so ba, Reey yake so Kuma ya faɗa Min ,Tun a lokacin na yanke Zan rabu dashi, Amma zuciyata ta kasa bani damar Hakan, a kullum sai nakeji kaman Ana ƙara Min Son Shine a zuciyata"

Sakin Hannunshi tayi, ta dora akan fuskar ta hawayenta na bin hannun tace

"Kayi haƙuri Ahky ......"

Wani irin kuka ya sake cin ƙarfinta,shiru yayi kawai sai ya jata jikinsa ya rungume, yana jin kaman Ya kankare pains and emotions dinta yasa ma kansa.

"Kayi haƙuri.....!"
Kalmar da take ta maimatawa kenan.

Saida tayi kukan mai isan ta sannan ta ɗago kai ta cigaba.

"Ammie ta sanar dani kai Mijina ne, a lokacin Naji ina son in Rabu dashi Amma sam zuciyata ta kasa Rabuwa Dashi..."

Bayan hannu tasa ta share ƙwalla

"Bansan Meke damuna Ba but I think I was a fool i believed Him , I could not see his hidden mask ,I used to believe in love that he bask ,he played and cheated on me ,a love lost which I couldn't see ,he broke my heart really bad ,He insulted my Parents, he disgrace and Molested me every Where baya ganin Mutuncina ko kadan, Dukda haka, bana Ganin kowa sai shi Ko kadan bana So inga fushin shi"

Dubanshi tayi taga ya haɗe rai tace

"Kayi haƙuri Ahky..…Koda nasan da Auren ka akaina, har cikin Zuciyata na yanke rabuwa dashi, but My soul Couldn't Allow me"

Rintse ido Ashman yayi yanajin da , Aareef na wajen da babu abinda zaisa ya karshi, cikin yanayi mai ban tausayi ta cigaba da fadin

"Har Allah Allah nake Yi kada ya gane cewa inada aure ya rabu dani"

Ganin ya haɗe rai yasata kama hannunshi

"Ahky...."

Bai Amsa ba Sai Juyar dakai da yayi, ko kadan baiga laifinta ba, Tausayin ta ne kawai yaji ya kamashi,da haushin Aareef din.



"Dan Allah kada ka Rabu dani"


Ta faɗa tana kama hannun shi a sanyaye, tare da share hawayen dake bin fuskarta...

Girgiza kai Aaash yayi Yace

"Bazan rabu dake ba Ihky ,ina tare dake har abada....!"


"Ki daina Kuka Ki fada Min Me ya faru?"

Girgiza kai tayi

"Ahky Wlhy bansan Komai ba, Wlhy bani na kashe shi ba"


ya saketa ya kamo habarta yace

"fadamin maiya faru Stop crying babu abinda zasu miki I'll be there for you"


gyadamai kai tayi kafin ta shiga bashi labarin komi, girki kadai tayi, ta bashi ya raina sai ta ajiye Abincin tayi tafiyarta ta ɗora da cewa.

"Zaujee....Bash ne,yace In Yi masu Girki zasuzo Su tayani celebration, Amma wlhy bayan Wannan babu Abinda na sani"

"to tayaya aka zuba Poison din ?,dakike cewa ke kikayi Girkin kuma You Are Alone, Tayaya aka faki idonki aka zuba,And how did they get out after Poisoning The food, batare da kowa ya ganshi ba? Kodai Framing dinki Akayi?, kin ɗanɗana abincin Kafin Ki zuba masa?"

hawaye ta share tace

"Banci ba, Amma wlh am saying d truth ba karya nakeyiba"

ganin yanda takeyi yasa Ashman yace

"Ok Tashi Muje, And make sure You stand on Ur words, duk rantsi duk wuya kada ki chanza gaskiyarki"

Ashman dakanshi yakai Aeesh station d'in, aka Shigar da ita wajen I.P.O ya zaunar da'ita kan Kujerar dake tafuskantarsa sosai ya fara masa tambayoyi.

Bayan Ta gaya mata Sunanta yace shekarun ta nawa?

Tace

"21, zanyi clocking 22 next month"


"Kina da Aure?"

"Eh ...."

Saida ta danyi jimmm Yana Murmushin Mugunta Sannan yace

"Wane ne Aareef a wajenki?"

"Saurayi na ne"

"Kinsan Kamal?"

"Eh"

"Meye alakarki dashi?"

"Abokin Aareef ne"

"Kinsan Ya rasu?"

"Eh"

" yaushe kika sani?"


"Da Akazo akayi arresting ɗina"

"Kinsan Abinda ya kashe shi?"



"Eh Naji sunce Guba yaci"

Kallon Rainin wayo yayi mata

"Kinji Sunce Guba Yaci Right...?"

Shuru Tayi Don gabaki ɗaya Jikinta kyarma yakeyi, I.P.O ya gyara zama yana Rubutu Batareda ya dubeta ba yace

"Da gaske ɗazu Kinyi masu Girki?"

Tunda ya fara tambayoyin tata zuciyarta na faman bugu da sauri ,Jikinta babu inda baya Rawa sunkuyar dakai tayi hawaye suka wanke mata Fuska, Batareda ta bashi amsan Tambayan sa ba, bai damu ba ya cigaba

“Amma an tabbatar a cikin abincin da kika dafa Aka sa Guba"

Shuru tayi tayi hawaye na gangaro mata still Bai damu ba, ya cigaba yayi da fadin

"Kuma an Ga Robar Guban a Nan Hostel ɗinku, bolar ɗakin da Kika yi Girkin....."

Nan ma Shuru tayi, daga nan bata sake amsa masa tambayoyinsa ba, haka ya ƙaraci Surutan sa ya bata takarda yace ta rubuta statement ɗinta, Hannunta sai rawa yake ta kasa rubuta komai.


Domin kuwa Babu wani gassasshen hujjar da zata iya Presenting don ta kare kanta, an Tsoma ta tsomo tsomo a ciki kuma ta kasa depending Kanta , Bawai hujjar ce batadashi ba, tsananin tashin hankali ne yasa ta zama kamar Kurma Duk abinda aka faɗa fa Saidai ta bisu da ido, haka Yasa I P O ya fusata, yace a Sata a cell, ta nemo lawyern da zai kare ta nan da 48hours.


Hankalin Ashman ya tashi Matuƙa, Aeesh tunda Take bata Taɓa Shiga Police station ba, Sai gashi an Kamata ana Zargin ta da aikata kisan kai, harda Sata a cell.


Aeesh tana da Rauni sosai ta fanni da dama, bazata iya kashe Mutum ba, a kullum burinta shine Tasa Murmushi a Fuskan Wani , ba ta damu ba Ko Ka ɓata mata Kullum Burinta ta faranta maka, Zuciyar ta mai rauni ce sosai bazata iya jure wannan zargin ba, Zargin kisa yayi mata Girma da Yawa, ga cikin Da ke Jikinta.


cikin tsananin tashin hankali ya kira Ya kira Barr Junayd ya Sanar dashi komai, nan take ya karɓi Case ɗin, ya kuma hadashi da babban Judge, Cikin Nutsuwa da Tattausan lafazi Aash ya fahimtar dashi halin da Aeesh take ciki, Sam Kulletan da akayi bai Kamata ba tunda ba'a Tabbatar ita ta Aikata Laifin ba, gata da Ciki Zama a cell babban haɗari ne ga lafiyan ta da na ɗan dake Cikin ta, sosai Judge din ya fahimce shi yayi masu Alƙawarin zaisa a saketa kafin nan da 5hrs sosai yayi masa Godiya sannnan ya kira Sadeeq ya sanar dashi an kama Aeesh hankalinshi yayi matuƙar tashi Especially da yaji tittle din Kamata da akayi Wato kisa, cikin Tashin Hankali Sadeeq ya gaya ma Ammie .

Ammie was shocked lokacin da taji Labarin, babu abinda yafi tayar mata da hankali kaman tarayyan Aeesh da Aareef, ta dauka ta rabu dashi Tun bayan da ta sanar da Ita Ashman Mijinta ne na sunna, Abin bakin cikin ma shine Kullum sai ta zaunar da ita tayi mata nasiha akan ta Riƙe mutuncin Auren ta kada ta bari shaiɗan yasa ta kula wasu mazan, tunda anyi Auren bada Sanin kowa ba, tayi niyyar tsaida Ranar tarewan ta Bayan ta haihu.

20mins Sadeeq ya dauka ya iso station din, parking yayi yafito yana gyara zaman black shade din Fuskar sa daya kara fito da Asalin farin shi, shiga police station din yayi gabaki daya ranshi abace, a wajen Station din ya iske Aashman sai safa da marwa yakeyi ransa a ɓace, tare suka Shiga Office din Inspector bayan An nema masu Izini.

Gabaki daya hankulan su a tashe yake tare suka yakarasa gaban table din, Ashman yayi tsaye yana kallon Inspector Balarabe da shima kallon su yake, Sadeeq ne ya zauna Ashman na tsaye sai faman Zuba masa Kallon banza yake daga Tsaye.


„Nine brothern Aeesh and i demand to see her"

gyara zama yayi Inpecta yayi yayi balancing a khjery ya ciji biron hannunshi

"Ka san dalilin da yasa Mukayi Arresting ɗinta?"


Harara ya ɓalla Masa Cikeda Rainin Hankali yace

"Ban sani ba"

Inspector Balarabe yayi Murmushi yana zare biron daga Bakinshi

" munyi arresting dinta saboda tayi poisoning Abokin Saurayinta , Ta sa Masa Guba a cikin Abinci, da farko tayi niyyar kashe Saurayinta ne, Sai Allah ya nufa akwai Sauran Shan Ruwan sa,Yaƙi cin Abincin ya Bama Abokinshi , har yanzu muna kan binciken dazaran mun gama kammala Komai zamu shiga kotu"


wani irin kallo Ashman yamai yanajin zuciyarsa kaman tayi bindiga, sadeeq yace

"But kasan She's pregnant, condition dinta baya Son Azabtarwa"

Inspector ya ɗage gira da kafada alaman he don't Care.

"inaso na ganta nace"

Inji sadeeq

"sure, but kai kaɗai zaka Shiga ,Wannan shegen Guy din na bayanka have been Trying to be Rude tun dazu, ji yake kaman Ya shaƙe Ni na mutu ya huta ,As if....."

wani irin wawan mari Ashman ya ɗauke fuskarshi dashi har saida hular kanshi ya suɓuce ya faɗi, ya Shaƙo kwalar rigarshi ya haɗa da wuyan shi ya shaƙe jikinsa na rawa.

“kai ɗin banza, sai in Kashe ka kaima...."

Yanda jikinsa ke karkarwa dolene ya bama mai kallo tsoro, tunda sadeeq da shi bai taɓa ganin Ran Ashman ya ɓaci irin yau ba.

A fusace ya buga tsaki, ya jefar dashi kaman kayan wanki, Cikin zazzare idanu Inspecta yace

"I'll Sue you for Disgracing the Officer Of the law"


"Do the worse... idiot"

A fusace shima ya bar office din yana Huci, kad'an yarage ya hankade Kurtayen dake bakin Ƙoƙarin.


Inspecta sai zazzare ido yakeyi, tsoro da fargaba Duk sun bayyana a fuskar sa, cikin in Ina yace

"Da ... Da..ka tsaya da na nuna maka ikon yan sanda"

Yayi maganar tareda duƙawa yadau hulan polisawan shi da ya fado ,ya kafa akai yadau kulkin shi yana wani irin bubbuga wa a hanunshi ranshi ɓace har yanzu jikinshi na Kyarma don ba ƙaramin Shaƙa Ashman yayi masa ba, Inba don Yasan Kawun shi ne Barr Hamza Lawyern ba da ya hukunta shi da Ikon yan sanda.

Jikinsa na rawa ya zagayo ya kalli Sadeeq dake auna masa Kallon Tausayi yace
"follow me"

fita yayi daga office din Ya Sadeek biye dashi, tafiya kadan Sukayi ,suka isa inda aka Kulle ta Cikin jerin cells Dinda Ake kulle mata, ya tsaya ya zare key din daya makala jikin wandonshi ya yabude kofan.

Babu komi acikin dakini,ko siminti babu Balle aje ga Plastern bango, sai wani Baƙin Plate din Abincin da Kudaje sai yawo sukeyi Akai .

Tana zaune akasa saman Yashi ta jingina da bango ta cusa kanta acinya tana kuka kayanta duk sunyi daga Daga da ƙura.


Hankalin Ya sadeeq a tashe yatako zuwa wajen ya tsaya yana kallonta sosai heart dinshi yay breaking gabaki ɗaya ta koma ta zama wani iri, ahankali yace

"Aeesh..."

dago fuskarta da hawaye yagama wanke wa tayi jin muryan Ya Sadeeq ta kalli Yayan nata idanunta tsabagen kuka har kumbura sukayi wani irin tashi tayi jiri na dibanta tayi kan Ya Sadeeq da gudu, fadawa jikinshi tayi tafashe dawani irin kuka mai ban tausayi tana shesheka, a hankali ya taɓa bayanta yace

"is okay, stop crying"

dago kanta yayi ya tallafo Fuskar ta da tafukan hannayensa,yana jin yanda jikinta yayi zafi sosai tareda kallon fuskarta ya zaro hanky a cikin aljihun ya share mata fuskarta cikeda Tausayin ta

yace "stop crying, tell me what exactly happen?"

Kuka take Yi sosai ta rirrikeshi tayi tana nishi tsabagen yanda kuka yaci ƙarfinta, ta kasa cewa komai ,tunda take bata taba shiga irin tashin hankalin nan arayuwanta ba , ko a Mafarki bata taɓa ganin kanta police station ba, ɗazu agabanta ake dukan criminals ana Fitar masu da jini gonin tsoro.

Iya kokarin Ya Sadeeq yayi tayi masa bayani Amma ta kasa Cewa komai sai kuka ,a hankali yayi tapping fuskarta damuwa Kwance a Fuskar sa

"Take a deep breath and Explain Please... "

"Stop bothering ur self dude ,ai bazata yi magana ba, shuru tayi tunda aka Kawo ta batayi magana ba,babu yanda bamuyi ta bamu Bayani ba Amma taƙi, dama idan criminal yayi committing act aka kamashi he always come up with stuff like this dan mu tausaya musu mu..."

Cewar Inspector Balarabe

" shut d fuck ,and Hang it up, Me Kukayi Mata, what have you done to her?"

Ya Sadeeq yayi maganan angrily, Yana Zazzare ma inspector idanu.

wani irin kallo Inspector yayi mai yace

"Why u dey shout at me?, Ko kaima dukan nawa Zakayi?"

wani irin mugun bacin rai ne ya dira a zuciyan Ya Sadeeq ya kalli baƙin Inspectorn yanda yake baki haka zuciyarsa take, ji yayi kaman ya shake shi ya mai yanda Ashman yayi masa haɗiye fushinsa yayi yace

"Idan Wani abu ya sameta,am gonna Sue you for it ,sai nayi Shari'a dakai"

Taɓe baki inspector yayi ya dan sassauta murya yace

"You can Excuse her time yayi"

wani kallo Ya Sadeeq ya watsa mai ya ,ya maida Dubansa kanta yaga tana rawan sanyi, yasa hankerchief ya goge mata fuskarta dake digar hawaye ya dagata, fashe mai da kuka tayi tana rikemai hannu tana kallon Inspector dake tsaye yana Zazzare mata ido.

kankameshi tayi sosai tafashe da kuka tana kallon kofa bakinta na rawa amma ta kasa magana sai nishi take yi kaman mai Athma.


Jikinta yayi zafi sosai, Cikeda jin Tausayin yar uwan nasa yace

" look Mr inspector, ya kamata a kaita asibiti She's sick"


Tsaki Inspector Yayi yace

"Time yayi Get Out...!, We know how we handle our client"

Sadeeq Ya Dora kanta akan kafadarshi yana shafa kanta, yana Auna ma Inspector kallon Mara tausayi

Shafa bayanta da yakeyi yasa tasomajin natsuwa, sunfi more than 3mins ahaka sanan ya ɗago kanta calmly yace

"I'll be Back right now"

Fita yayi, Inspector ya Kulle Ƙofar da Makulli, Sadeeq ji yayi hawaye Sun sauko masa, yayi saurin Share su karta gani.

A

Please Login or Register in order to submit comment