Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

58, Saida ya daidaita Muryarsa Sannan ya fara karantawa

Kanta na Kafaɗarsa tana kallon Littafin , a hankali ta fara jin wani irin Nutsuwa na saukar mata, ta Mike ta koma kan Gado tana sauraronsa, shi kuma yana zaune a ƙasa yana karanta mata Story din.


Murmushi taketa faman Zubawa, Sosai labarin Ke tafiya da imaninta muryarsa na saka mata wani irin shauƙi na musamman.

Hannu tasa a kwantaccen suman Kansa ta fara jagula masa cikeda jin daɗin labari, batare da ta sani ba tayi masa Manyan Kitso zane biyu a tsakiyan kansa.


A haka barci ya kwashe su.....










NAYI GABAS🚶🏻‍♂️🚶🏻‍♂️🚶🏻‍♂️😂

KANAWA MUTANEN MU, KUYI HAKURI LAMARI NE YAZO DA HAKAN😅



28TH OCT

BINTOU ✍🏽
[10/31, 9:49 AM] Bintou abdool: 🫀🗡️ *_WUƘA A ZUCIYA_*🫀🗡️


_(BLEEDING HEARTS)_



*046*



22:42
Ta farka da matsanancin Yunwa, ta tasheshi, Idanunsa cikeda Bacci ya dubeta.

"Menene?"
"Yunwa nake ji"

Lumshe idanu yanajin bacci na fizgarsa sosai

"Ki buɗe fridge Akwai Yoghurt dinda Na siyo miki ki dauka"

ta ture shi
"Ni kenan Kullum Sai shan Yoghurt Kaman Shanu?, Ni bazan sha Ba"

Tayi Maganar a shagwaɓe Hawaye na taruwa a idanun ta.

Juyowa yayi ya dubeta, sannan yasa hannu Ya kamo fuskar ta ƙwace fuskarta tayi ya ƙara kamo fuskarta kamar jira take ta fashe masa da kuka, kwantar da kanta tayi a kirjinsa he could feel how her tears ke jiƙa masa ƙirjinsa, shiru yayi Still holding onto her muryarsa a taushashe yace

"Am...Sorry ...ihty"

Sake rushewa tayi da wani kukan , yasa hannu yana patting bayanta yana jin ko wane digar hawayen ta har cikin Zuciyarsa

ɓoyayyen ajiyan Zuciya ya saki yace

"Tell me now, Why are You crying?" Ta girgiza kanta sai kuma ta fashewa da kuka

tace "Yunwa nakeji" ta faɗa tana sake cusa kanta a ƙirjinsa .

"Me zakici?" Ta ɗago fuskarta Sai kuma tace

"Anything Hot like rice, Yam, Spagetti , and Even Fate...i" da sauri Ashman ya ɗago kanta yace

"da daren nan?"

Ta Turo baki

"Eh..."

Ya kamo hannunta "tho tashi Muje kitchen din"

Kitchen din suka nufa ,Babu kayan Abinci a kitchen din sai , noodles ,Irish da Kwai,

Dubanta yayi,

"tho zauna bari in fere Irish sai in soya Miki ko?"

Ta Turo baki

"Ni nace maka zanci Irish ne?"

Sai kuma ta fashe da kuka

"Nidai gaskiya ana gana min Azaba a gidan nan ,kullum mutum kenan cikin cin kayan soye soye sai Kace mayya?"

Ya sauke ajiyan Zuciya yace

"Tho now what did you want"
Zama Tayi tana Turo baki Muryarta ciki ciki tace

"Noodles....."

"Okay Queen...!, Your request Is my Command "

Sannan ya Tattare hannun jallabiyarsa, Ya debo Medium size guda biyu don yasan daya bazai isheta ba Amma sai ji yayi tace

"Ni me Biyu zasu min...?, Irin yunwan da nake Ji ai sai hudu''

Batareda ya Musa ba, ya ƙaro Biyu, taja numfashi ba tare data ƙara cewa komai ba.

Noodles din ya haɗa Mata ya dafa mata kwai biyu,Tana zaune sai Hamma take bugawa, tasowa tayi daga inda take zaune ta rungumo shi ta baya tana layi kaman mai shirin Yin barci a hankali ta kira sunanshi

"Ahky...."

“Na'am ihty..."

Ya Amsa yana Jin Rungumar da Tayi masa Har Ƙwaƙwalwarsa.

Ta ɗora kanta a bayanshi tana Hamma tace

"Bana Son Dafaffen kwai, Soyayye nake So "

“Shikenan Abinda Kike buƙata?"

Shuru tayi masa ta Lumshe idanu,tana Sake murza kanta a bayanshi.

Kwan ya soya mata bayan Ya dafa noodles, ya zuba Mata har a lokacin Tana Rungume da bayansa , Amma tayi shuru .

Shurun da yaji ne yasa yake Motsawa a hankali a tunaninsa tana jin dadin yanayin ne shiyasa bata magana.

Saida ya gama ya haɗa komai, sannan a hankali ya sa hannu ya ɓanɓaro hannunta yana fadin

"Ihty your food is ready"

Shurun da yaji ne yasa shi juyowa da ita a hankali, Ganin Idanun ta yayi A Lumshe Alamar tayi bacci, ya tasheta a hankali

Ta buɗe idanunta kadan akansa

"Menene?"

"Your food is ready...."

Bai Ida maganar ba ,ta Lumshe ido sai bacci.

_Na shiga uku_

Ya furta a hankali, yana sake ɗago kanta ,kuka ta saka masa

"Ni ka barni inyi bacci"

"Hasbinallahu wani'mal wakeel"

Ya furta a zuciyarsa, a fili kuma cewa yayi

"Tho Muje dakin ki ki kwanta"

Rungume shi ta sake yi tana Lumshe ido, baccin na janta sosai

"Ni ka barni anan zan kwana"

Ta fada cikin Muryar bacci.

Bai sake cewa komai ba, saima Murmushi da yayi yana jan gemunsa, a hankali ya sake manna ta da ƙirjin sa har baccin ya kwashe ta ,daukan ta yayi kaman jaririya, ta rungumo kafaɗarsa cikeda jin daɗin baccin , ya Kaita Dakin Ta ya kwantar da ita bayan ya ja mata bargo.

Sannan ya koma kitchen ya sa mata noodles a warmer in case in ta sake farkawa...

Da haka ya nufi ɗakinsa, Alwala yayi ya shimfida Darduma ya tada Sallah.

Ko kadan Ashman Baya wasa da Sallar dare, bai yarda ya bata zuwan dare har tafiyar ta Batareda ya raya ta ba.

kiyamunlayl yana kusanta Bawa da Allah Shiyasa ko kadan Ashman baya wasa da Kowane dare a rayuwarsa.

Uluwun ka'ibi bi himanil'awani wa izzul mar'i fi sahrillayal ❤️

_daukakar darajar mutum da himma shine izzar sa wajen Ƙiyamun layl_

Ina mamakin Yanda zamu kai ɗaya, biyun dare Muna danna waya instead muna gamawa Mu Raya wannan daren koda da nafila ɗaya ne Sai Mu kwanta Batareda Munyi ba.

Bayan A daidai wannan Lokacin Allah da kansa yake Tambaya ina Masu Neman biyan bukata Su rika in biya musu.

Munada Buƙatun mu rututu, kannin mu , yayyin mu da ma iyayen Mu duk suna buƙatar Addu'ar Mu, Al'ummar Musulmi ma gabaki daya ,uwa uba ƙasar Mu itama tana Buƙatar Addu'ar Mu a wannan Lokacin.

A daidai gabar da zaɓe ke gabatowa Kamata yayi mu dage dayima ƙasa fatan Shugaba da muƙarrabai na Gari ɓata garin yan kasan Kuma Allah ya shirya Su ,Allah ya zaunar da kasar mu Lafiya.

Mafificin Sallah a cikin Salloli shine _Salatul Layl_ (Sallar dare)

_Allah yasa mu dace_

Yana nan kan Dardumar har aka kira sallar Asubah, yayi sallah sannan ya tashi Sadeeq Yaje dakin Habeeb ya iske shima ya tashi yana kan Darduma yana Sallah, ɗakin Aeesh ya nufa itama yaga har ta farka tana Sallah .

Hamdala yayi a ransa Kasancewar Matarsa bata Wasa da Sallah itama, ba kaman Deejah ba da Kullum sai sunyi faɗa Akan Ta tashi Tayi Sallah, lokacin farkon Aurensu ma Ko Cikakkiyar Sallah Khamsu Salawat batayi a cewar ta ba dole bane tsayda su, tunda bata taso taga ana haka ba a gidan su, saida ya taka mata burki tukunna ta dawo haiyacinta ta rinƙa yi...

Komawa yayi ya kwanta, bai farka ba sai 8:54 , Babu Kowa a ɗakin.

Bathroom ya Fada yayi taking shower sannan yayi Brush ya fito Batareda ya bari ruwa ya taba kansa ba saboda Wani masifaffen ciwon kan da ya farka dashi.

Fitowa yayi sanye da Armless Shirt da 3quater.

Zaune ya iske su duka a dinning Suna Shirin karyawa.

Shima karasowa yayi, yaja Kujera ya zauna.

Habeeb ya ɗago yana shirin gaidashi yaga Manyan Kitson da Aeesh tayi mishi jiya.

Yayi saurin duƙar dakai Sosai yana Gimtse dariyarsa, Shima Sadeeq kallo daya Yayi masa Ya hango Kitso a tsakiyar kansa, sosai sadeeq yayi qoqari wajen danne dariyar dake cinshi yace

"Maaan Anya Kayi Sallah kuwa yau?"

Ashman Ya jingina da Kujerar, yana Lumshe idanu kansa na cigaba da sara masa, murya chan kasan maƙoshi yace

"Banyi sallah ba kasan Ni Arne ne"

"Ahh da Alama tunda ga, Bob Marley da Shark 🦈 a tsakiyar kanka"

sadeeq yafada yana kai Tea mug Bakinshi, dukda yadda yakeson bursting to laughter Amma ya danne.

Dagowa Aeesh tayi, ta dubi kan nashi taga Kitson da tayi mashi da daren Jiya, ta waro mayan idonta

Daga hannunsa yayi daga dafe kansa dake sara mashi, not taking it serious ya kalleta da idanunshi dasuka kada yace

"Good Morning "

Kasa amsawa Aeesh tayi don tasan muddin ta bude baki da niyyar amsawa to tabbass dariyace zata fito, nonstop laughter, Habeeeb kou Tuni ya fara nashi dariyar

"Dariyar Me kake yi??"

Ya fada yana tsareshi da ido

Girgiza kai kawai yayi, yana Tuntsirewa da dariya.

Kuramashi idanu Ashman yayi sannan ya girgiza kai yace

"Allah ya baka Lafiya.."

Dariyarce ta kufce musu gabaki daya daga Aeesh din har Sadeeq batareda sun shirya ba suna kallon Kanshi.

Kallon su yayi cikeda rashin Fahimta, sannan Yayi tracing Inda Idanuwan su ke kallo

A hankali ya daga hannu ya taba kan nasa, jin Wasu Manyan Manyan Ƙaho yasashi saurin Ware ido, ya dube Aeesh tayi saurin sa tafin hannu ta toshe baki yana yi sosai tana Gimtse dariyarta.

Ya maida dubansa kan Habeeb da Sadeeq , suma duk sai suka haɗiye dariyar.

"Ahky Don Allah karka kwance bakaga yanda kayi kyau ba"

Ihty Tayi maganar a shagwaɓe

Murmushi Ashman yayi

"Dole Sadeeq yace banyi Sallah ba, Tunda kin maida Ahky Mai ƙaho"

ya faɗa yana jan basket ɗin fruit, tare da ɗaukan Banana ya ɓare ya shiga taunawa a hankali yana ɓata fuska saboda sarawan da kansa Keyi, Sadeeq yayi Murmushi yace

"Tho Sai a kwance Kitson ko, ko yau babu Gyaran Gashi ne?"

Ya harareshi

"Babu Ruwanka"

Aeesh ta kamo Hannunsa dake rike da banana ,Yana Shirin Kaiwa baki takai bakin ta

"Kyaleshi Ahky Allah Kayi Kyau a haka"

Hararar Ta yayi da wasa

“Kwadayi...."

Batareda Ta saki hannun nasa ba tace,

"Karewar Kwadayi ma yau ina farkawa tun banyi sallah ba, naje kitchen nayi warming Abincin Jiya, na cinye Ashe bayan ka dafa Min Kwan Ka soya min Wani"

Ya Lumshe ido yana Jin dadin Yanda take murza Hannayen ta cikin Nashi.

Ya Sadeeq da Habeeb suka dubi juna ƙasa Ƙasa suna Murmushi.

Inaa basu ma san Sunayi ba, Kallon Fuskarta yake yana jin Sonta na Ratsa jijoyoyin sa yana shigewa Jinin Jikinsa.

🎶Sarauniya zinariya a guna kin wuce gimbiya🎶.

🎶Idaniya ba lafiya in basu ganki ba , ba dariya🎶

🎶Da soyayya kin mamaya kwatsam na jiyoki a Zuciya🎶

🎶Ta jijiya kika zagaya ,so da jini ya gauraya🎶

🎧Madubi sannu abin kallo na🎙️

Ohhh ohhh🎤🎤

📯A so ba mai chanzan ra'ayi na📯

Ahhh Ah ....!🎤🎤


Yau tare suka dawo daga Masallaci, Ashraf ,Naseer saleem , Abdul, kawu Da Abba

Suna shigowa kawu da Ɗansa Abdul sukayi Ɓangaren su.

Abba da Gwarazon Mazajensa Kuma suka nufi nasu ɓangaren , suna dan taɓa hira a hankali, Saleem sai Binsu yake yana jan tsaki, So yake su tafi ya samu ya zanta da Abba.

Saida Suka Shige Part din Abba Sannan, kowa ya kama gabanshi.

Saleem yabi bayan Abba, Abba ya juyo ya dubeshi

"Son Lafiya...?, Are You okay?''

Ya Girgiza kai

"No dad "

Cikeda kulawa Abba ya kafe shi da ido

"Meke damunka?"

Duƙawa saleem yayi har Ƙasa, yasa Gwiwowinsa a ƙasa, ya sunkuyar da kai.

Mamaki Ya kama Abba, shima ya duka, ya dagoshi yana Masa kallon mamaki

"Are You okay...?, What's Wrong with You?"

Saleem ya sake sunkuyar dakai yana jin Zuciyarsa babu daɗi, Especially Idan ya tuno Hawayen da ya gani a idon Mahaifinsa.

"Kayi haƙuri Dad....Ka yafe ...min"

Yay maganar a rarrabe Kaman Mai Koyon magana, yana jin Zuciyarsa wani iri , he can't believe Shi ke wannan Abin.

Da mamaki Abba ya dinga Kallonshi baki sake

"Nayi Sanadiyyar Zuban hawaye a idanun Mahaifina....!, Kayi Hakuri Abba "

Sai Kuma yayi shuru yanajin yanayin Somehow , Bai Saba da rokon gafara ba, bai san yanda akeyi ba, baisan ya zai fara ba, he need to explain Alot but he don't know how and where to start.

Hannu Abba yasa ya dagoshi, don ya miƙar dashi, amma sai ya kwace , ya sake sunkuyar dakai

"Bazan iya Tashi ba, until You Alter a forgiveness to me..."

"Ka tashi Saleem, babu Abinda kayi min, Ban taba Zubda hawaye na akanka ba, kuma bana fatan zan iya zubar da Hawaye na akanka"

Sai yanzu saleem ya ɗago kansa ya dubi Abban nashi

Abba ya gyada kai

"Tabbas koda kaga hawaye a idanu na, abu na tuno..."

"Dad....menene wannan Abin da har zaisa Hawaye ya zuba a idanunka"

Abba ya saki Ajiyan zuciya, ya furzar da Karamin huci daga bakinsa, sannan ya goya hannunshi a bayanshi, yanayin shi na komawa kalar tausayi.

"Mahaifiyar Ashman....!,a kullum in na kalleta Sai Inji a raina banyi Mata adalci ba, sai inji dama komai Record ne da za'a Iya presenting domin ganar da mutum Abinda ya kasa fahimta, da nayi Presenting Record don Goge baƙin Fentin da Ake kallo na Dashi"

Ya ƙarashe maganar hawaye na taruwa a idanun sa.

"Mahaifiyar Ashman kuma?, Ba ta rasu ba?, A ina kake ganin ta?"

Hawayen da Abba ke kokarin Maidawa ne suka ɗigo, yasa bayan hannu ya share, fuskar sa dauke da Murmushi cikin In Ina ya d

"In... inaa nufin Mahaifiyar ka...!, Ai ita tana raye ko?"

Saleem ya gyada kai jikinsa yayi sanyi yace

"Abba me ya faru da hawaye ke zuba a idanunka a duk lokacin da ka kalle ta?"

Abba ya daga Masa hannu

"Kayi hakuri Saleem, Don Allah karka tambayeni komai dangane da mahaifiyar ka a halin yanzu ,bazan iya jure jin tambayoyi akanta ba, zan Iya karya Alkawarin da nayi mata na kasa Na Ɓoye Sirrinta ko bayan Idanunta, Don Allah saleem kar ka tambaye Ni komai....."

Duk karfin zuciya irin na Abba, kuka yakeyi sosai , Saleem Ji yayi zuciyarsa ta tsinke Jikinshi yayi Mugun sanyi.

_Da Alama Akwai Abinda Abba ke ɓoyewa dangane da Inna Yathai da inna Saude_

Kallon Da yaga yayi mata Jiya, kamin Hawaye ya gangaro saman Kuncinsa ya tuna, sai ya cije lips ɗinsa a raunane.

Ya ɗago yana duban Abba, take yaji Shima hawaye sun wanke masa Fuska, ganin hawaye a idanun Mahaifinshi ba karamin Tsorata shi yayi ba.

Kanshi yaji ya kara girma Jikinshi na wani irin Yan yam, wasu Strangers da bai san daga Ina ba yaji suna yawo da Nerves Dinshi, Ya rungume Abba, idanunsa na cigaba da Zubar da ƙwalla , Shima Abba ya rungume shi yana Sharar Ƙwalla.

Yau Satin Deejah Uku da Komawa gida Amma babu ko kira daga ɓangaren Ashman, babu inda ba'a Nemeshi ba babu shi babu Alamar shi ,Tuni Abba ya Damƙa ma Saleem Asibitin Ashman a cewar shi wannan Shine hukunci mafi dacewa a Gareshi Saleem kou dadi kaman Ya kashe shi, ai tuni Izza da Mulki da girman kai suka ƙaru dama ya lafiyar kura.

Hankalin Abban Deejah ya tashi, Deejah taƙi ci taƙi sha, Ita a nemo mata mijinta kar a raba su, dole Abban Deejah y Samu Abba Ya rage Murya yace don Allah a nemo Ashman

Babu inda Abba baije ba Wajen neman Ashman amma babu Shi babu Labarin shi, Hatta Abokansa na Kano Lameer Da Mahfouz duk ya tambaye su Suma cewa Sukayi sun manta rabon da su haɗu.

Hankalin Abba ya dada Tashi masamman In ya tuna ya gudu ne da matarsa Aeesh.

Tunda Salem ya zama mai asibiti Maryam ta fara samun Sakewa, da zarar ya fita take fita Ta shige Part din Su Inna Saude.

Cikin Kwanaki Uku ta samo hujjar da take buƙata ta barayinsu, a halin yanzu batada Burin da ya wuce ta shiga Part din Barr Hamza(Kawu) don Ta lura 80% na zargin Da Takeyi Yana Kansa ne, Inna Yathai kou Taƙi Gaya mata komai dangane da mahaifiyarta saboda Matsalar da yin Hakan zai iya kawo wa a zamantakewarsu.

Yau Sunday, Saleem Yaje asibiti yaje yayi Attending wani emergency Call, Akoda yaushe in zai fita tare Suke zuwa Da Ayyan, yana Gudun Ya ajiye shi Wata ran Yazo ya iske shi babu rai don Ya lura Idon Maryam a rufe suke akan Kiyayyar da take ma Ayyan, Amma yau kasancewar Emergency ne sai ya barshi ya tafi.

Tana ganin Fitarshi ta tafi sashen su inna Saude, suna zaune Suna hira Suka hango dawowan shi, tayi Saurin komawa Amma ta makaro kafin Ta shiga ya riga ta.

Ya tsareta da tambaya daga ina take, kallonshi take tana Mamakin ƙarfin hali Irin na saleem sai kace Auren gaske sukayi, yana Abu like Boss ,Itafa bata dauki zaman Da take yi a gidanshi a zaman aure ba Daukan zaman nasu take a matsayin zaman Yarjejeniya.

Ya cije lips ɗinsa cikeda Jin Zafin irin kallon da take masa yace ya maidata bakin Aiki kuma a karkashin Office dinshi zatayi Aiki.

Bata ce komai ba, tayi wucewan ta tana Taɓe baki, ya bita da kallo yana mamakin Girman kai irin nata.

Washegari Monday Yayi mamaki da yaga ta dau shiri bayan ya tunasar da ita akan batun Aikin

TaShirya Cikin sabbin Scrub dinda ya kawo mata, a karo na farko da tasa wani kaya da ya fito daga hannunshi , tun bayan Auren su.

As usual, fuska a tamke ya fito,Sanye yake cikin dark Ash suit, sai light Ash shirt dake ciki da baƙar necktie, Shima Ayyan Yana sanye cikin Shigar sa ta suit irin ta mahaifinnasa, Ya zura hannayensa a Aljihu Tafiyarshi har wani chanzawa yayi cikeda tarin Nutsuwa.

Wow, gaskiya yau Father and Son Sun haɗe😘
a hankali yake tafiya kamar wanda baya ƙaunar takawa, sai ƙamshi yake bazawa hannunsa riƙe da key.

Suna isowa Parlor yaja ya tsaya yana Jan tsaki ganin Har lokacin bata fito ba.

Ya gyara tsayuwar sa hannaye zube cikin aljihu, fuska tamke ga uban baqin shade daya kwama, alamar Yan Rashin Mutuncin ne a kusa.

Saida ta Ja aji sannan tafito itama ta tako wajen Saleem itama fuskar nan a haɗe.

Tana Sanye Cikin Ash Scrub Mai Layin baƙi a neck edge, Biros dinta blue and Red Saƙale a Biro Pocket, Kanta yane cikin Baƙar mayafi tayi rolling, sai bakar hand sleeve, Wanda ya rufe mata gwiwan hannunta zuwa sahun Hannun.
Tsaki yaja, ya miƙa ma Ayyan Hannu, Ayyan Ya riko hannun, suka fito Cikeda takaicin jiran da tasa yayi.
Ko kallon Part din Abba Baiyi ba, yayi wucewar sa parking lot Driver ya Buɗe masu Back Seat.

Babu yanda ta iya haka ta shiga motar tanajin dama tun farko bata yadda ta fara Aikin a yau ba, ita a tunaninta ma da ya maidata aikin Wata satin zata fara, amma da ta tuna Yau ta cika wata uku a gidan shi sai ta saki Murmushi.

Maida kofar tayi tarufe tana gyara zamanta, saida yayi making sure tashirya sannan shima ya shiga suka sa Ayyan A tsakiya Driver yaja motar sukabar gidan.

Tafe suke babu maicewa kowa uffan, maryam dama tunda tashigo tajuya kanta tana kallon waje ta window while Ayyan Sai Faman zuba Surutu yake cikeda farin cikin Yau gashi ga Daddy ga Mummy a gefensa.

Jinshi yake so happy having her next to him and again Idan Sun ISA asibitin She'll Always remain Next to him.

Itama a 6angarenta Duban Window take Morning weather na samar mata nutsuwa tana kallon yanda Nature keda kayatarwa, tarasa dalili amma saijitayi yanayin har zuciyarta, tanasa jin wani sense of emotion a tattare daita.

Haka duk sukayi shiru suna sauraron Surutan Ayyan kowa da abinda yake saqawa azuciyarshi harsuka qaraso Asibitin.

Fitowa sukayi bayan Driver ya Buɗe musu, ta zagayo zata wuce taji ya riko Hannunta, ta ɗago da sauri ta Galla Masa Harara haɗida Ƙoƙarin kwace Hannun ,Amma ta kasa saboda ba Ƙaramin Riko yayi ma hannun Ba.

Wucewa suka yi mutane hudu na take masu baya, daya daukeda suitcase dinshi, Ɗaya da white coat ɗinsa while Sauran Na Empty handed duk sunyi appearing ne bayan Fitowan su daga mota.

duk wani Ma'aikaci da zarar ya gansu sai yaja gefe yana rike baki, babu Wanda yasan Saleem yayi Aure.
Tambayan Kansu suke

Dama Maryam matar sa ce?
Harda Rabon ɗa a tsakanin Su?


Wasu na Gulma No wonder ita kadai take masa ya kyale

Kan kace me Asibiti ya dauka, Maryam Matar Saleem ce Kuma Baturen yaron da yake yawan zuwa dashi a kwanan nan Yaronsu ne.


Kai tsaye Gynecology Dept suka nufa, ya tsaya a bakin Ƙofa daya daga Cikin masu Binshi yasa hannu Ya cire mishi AshCoat ya maye masa gurbin shi da Farar Labcoat .

Duban Maryam yayi fuskar nan a haɗe a natse yace

"Welcome To My Department, as from now zaki fara aiki a Gynea Ward na sanar dasu Zuwan ki "

Sunkuyar dakai tayi cikin ladabi

"Ok sir"

Ya dubi mutanen da suka rakoshi

"Excurt her "

Kai tsaye Gynecology Ward suka rakata, a ranar ta fara Aiki kaman Da gaske, ya Leƙo Ward din yafi Sau Goma yana dubata.


12:49
Dawowan shi kenan Daga consulting Room, ya shigo Office ɗinsa ,zama Yayi akan Kujera fuskar sa dauke da Murmushi yau wani irin farin Ciki yake ji mara misaltawa.


"Daddy....!, mummy gave this to me"

Inji Ayyan yana Miƙa masa wata yar kwali.

Da mamaki yake dubanshi

"She Gave it to you...?, For what?

"She Just said I should give it to you"

Karba Yayi cikeda mamaki ya ɓare kwalin, yana duddubawa.

Scrub dinda tasa da safe ne, Sai kuma wata yar takarda

Ji yayi gabansa ya fadi, jiki na rawa ya dau takardar

_Mr C.E.O, na gode da ka fitar dani daga gidan ka dakanka_
_nagode da ka cika min Alkawari na na karshe_
_Nagode da ka ara min kayan Da nasa da safe_
_Ga Kayanka na dawo maka dashi_
_Happy 3mounths wedding anniversary 🎤😆_

_Today with due respect sir, I ended Our Contact_

_in Ka ga dama ka sakeni in Ka ga Dama ka cigaba da zama cikin Auren_

Your Ex maid
Monstang ✍🏽

Dakatawa yayi sai zufa yake dukda sanyin A.c din office din,Hannunsa na kyarma takardar dake hannun shi ta suɓuce ta faɗi


Da ƙarfi yace NOOOOOOOoooo







MARYAM DAI TA ARCE
Nima
NAYI GABAS🏄🏾‍♀️



30th Oct

Bintou ✍🏽
[10/31, 8:42 PM] Bintou abdool: *WUƘA A ZUCIYA*
_BLEEDING HEARTS_






Gaskiya naji dadin comments dinku na page daya gabata, sai jiya nasan BLEEDING HEARTS Nada masoya dayawa.

To All Bleeding Hearts group members
Da ma Sauran Members na sauran Groups din❤️❤️❤️


Wannan page din taku ce.


*047*


Your Ex maid
Monstang ✍🏽

Dakatawa yayi sai zufa yake dukda sanyin A.c din office din,Hannunsa na kyarma takardar dake hannun shi ta suɓuce ta faɗi

Da ƙarfi yace NOOOOOOOoooo


Ya fito hankalin sa a tashe, kai tsaye Wajen Securities ya nufa ya tambaye su ko suna wucewar ta?, ɗaya daga cikin su ne ya iya tanka Shi, yace yaga fitanta da wani a Mota, bai ida maganar ba Saleem ya Tsinke Shi da mari.

Ya fito cikeda tashin Hankali ko ganin Hanya bayayi, Kai tsaye parking lot ya nufa ,Driver na ganinshi Ya Buɗe masa.

Daga can nesa Ayyan dake Binshi Ya Ƙwala masa Kara ganin yana shirin tafiya ya barshi.

Driver ya dauko shi ya sashi a Motar, sannan Yaja Batareda ya san ina Suka nufa ba, saida suka hau Titi sannan Ssleem ya iya buɗe baki yace

"Barnawa Zaka kaini"

Kai tsaye gidan su mama Suka nufa, Driver na sauke shi ya Shige Gidan da gudu yana haki, da shigar shi sai ya tarar da baƙin fuska suka tabbatar Masa da cewa Sun sayi Gidan ne watanni biyu da suka wuce, Masu gidan Sun bar Gidan Tun tuni.

Yana Fita yaga Shuraym ya fito daga gidansu yana shirin hawa kekensa, Shuraym na ganinshi Ya iso Gareshi ya bashi hannu sukayi Musabaha.

Saleem ya tambaye shi

"Shuraym Ina Maryam?"

Kallon Rainin wayo Shuraym yayi masa.

"Ba ance kai ka aure ta ba?"

Ganin saleem ya shaka ya sa ya rage murya yace

"Ai tuni mero ta siya ma Su Mama Gida sun Tashi Sun bar mu, Ni kaina ban san gidan da suka koma ba"

Inji Shuraym Yana jan Kekensa ya bar Wajen .

Saleem ya dafe kansa da yaji ya sara masa Lokaci Guda yace

_innalillahi Wainnailayhirraji'un Saleem what have you done To ur self?_

A fili yace

_Maryam ina Kike?,ina kikaje?, Don Allah Ki dawo na Amince Zan zamto Mai Amana da riƙe alƙawari a wajen Ki, bazan sake ɓata Miki Rai ba don Allah ki dawo_


***

"Ai na dawo kenan No more Going back, Kaya na na Gidan sa ma na bar ma sabuwar Amaryar shi"

Zeeyk ya dubeta ta gefen ido yana Murmushi hankalinshi na kan tuƙin da yakeyi yace

"Ina Bayan ki ƙanwata💯, ai Ni tunda saleem ya karya mana Alƙawari naji ya fita raina, yaron bashida Tarbiyya ko kadan"

"Hmmm yaya kenan kaida bakayi rayuwa dashi ba ka karanci haka ballantana Ni da nayi Spending more than half of my life a tare dashi?, babu irin halinshi da ban sani ba ,A yanda nayi rayuwa da saleem zan iya cewa nafi Mahaifinshi sanin Halin shi"

Zeeyk yayi dariya

"Haba kede kice kin san halin Mijin ki , Amma ki daina hada sanayya da na uba"

Ta Harare Shi

"Yaya Zamu hau sama da kai bana so"

Ya ɗan waro ido, yana karya Kan Stirring Izuwa Layin Su mama

"Me nayi kuma?"

"Kafini Sanin Abinda ka Aikata and next time I won't remind You"

“So kike Ki Nuna Min Ke yar boko ce?, Ko wane ithkancin ne Muna Magana da Hausa Kina juya mana harshe?, ohhh na manta Kin yi Rayuwa Cikin Turawan Nigeria 3mounths wasa ne?, Allah dai yasa ɗan iskan yaron nan baiyi Miki Ciki ba don Naga har wani Fresh Kika

Please Login or Register in order to submit comment