Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

time d'in jin jikinsa yake kamar ya wuce 5 hours ma da farkawa a baccin
"Hammad tambayarka nayi..ka tsaya min in'ina,, ina ka samo wancan kayan..!?"
Ba bakinsa ba hatta k'afafunsa jinsu yake sun fara neman kasa d'aukan sa,amma saboda dauriya irin tasa sai ji yayi bakinsa na fad'in
"Please Mamma.."

"Kaga bana son aikin wahalar da kai,,am just asking...Ni bance kamin dogon magana ba,,just tell me na wane ne..!? Kasan bana son wannan shashancin ko..!?"
Kai ya gyad'a cikin sanyin jikin da bai san sanda ya same shiba while yana furta
"Mamma na kune..!"

"Na su waye.!? Mu wai kake magana..!? Uhmm! Hammad kenan,mu da ba muje ko ina ba,ina zamu samo wannan kayan..!? Ke dai ka fad'a min gaskiyar ko na wane ne.."

"Ohh! Mamma i will explain how ya zama naku.."
Fuskarsa duk a marairaice kamar zai mata kuka idan ta sake magana
"Ehmm! Kai nake sauraro ai,,kasan ba ko wane lokaci nake son shirme ba..Ko dai ka nutsu kamin bayani ko kuma...!"

"No Mamma..I will explain,ba sai kin sanar da Daddy ba,zan sanar miki komai fa.."

"Ok..Go on,,buh ka hanzarta ni fita zanyi ina da aiki sosai a gabana,,nd Daddy ya sanar min suna hanya yau,ina so naje office na dawo da wuri,dan zan bada excuse nema shi yasa zan fitan,amma da babu inda zani.."
Da kyar ya had'iye yahu kafin ya ce
"Mamma to ki bari idan kin dawo sai muyi maganar ko..!?"

Sai data kalleshi up to down kafin ta wuce shi tana tab'e baki da fad'in
"Allah ya kaimu..Nd ka san bazan karb'i any excuse ba akan wannan maganar ko..!?"

"Yeah..! I know.."

"Good.. Sai ka kasance cikin shirin sanar min gaskiya..If not kuma i will try to inform ur Dad.."

"Ohhh! Mamma! I told u zan sanar miki komai..I promised u..!"
Jinjina kai tayi kafin ta wuce cikin sauri² tana fad'in
"Ok..Na wuce aiki,buh komai yana dining duk lokacin da kula gama k'ailular sai ku duba can.."

"Ok...Mah see u later.. Allah ya tsare.."

Da "Ameen" ta amsa tana ci gaba da tafiya,har taje bakin staircase zata fara sauka ya kwalla mata kira da cewa
"Mah..! Wait.."
A hankali ta dakata,kafin ta d'an juyo tana kallonsa fuskarta d'auke da mamaki,cikin takunsa na isa ya nufo ta har ya k'araso,ko da yazo d'in sai ya sunkuya kad'an had'e da bata peck a chicks yana mata murmushi had'e da sake fad'in
"Bye Mah..!"
Kai ta jinjina masa itama tana masa murmushi sannan ta juya ta fara sauka,shi kam Hammad nan inda ta barshi a tsaye bai iya motsawa ba sai daya d'auki wasu y'an mintuna a gurin,kafin ya tura hannayensa cikin aljihun 3quarter d'insa yana sake binta da kallo har ta fice daga parlor'n,wani gawurtaccen ajiyar zuciya ya saki had'e da fesar da iska,a hankali kuma ya d'an runtse idanunsa while yana fad'in
"Mamma..! Huh..! U frighten me,,da wannan safiyar duka nayi tunanin ma wani abu ya faru..Ohhh..!"
Sai daya sake kwashe ak'alla mintuna goma kafin da kyar ya juyawa ya bar wajen,kai tsaye daga nan bedroom ya koma,da shigarsa bai tsaya b'ata lokaci ba ya shige wanka,mintuna sha biyar suka d'auke shi sannan ya fito d'aure da towel a jikinsa,a gaban mirror ya d'an tsaya ya zubawa kansa ido ta ciki nd ruwan dake kansa yanaa sauka a jikinsa ba tare da yayi k'ok'arin sa mini towel ya tsane ba,ya d'auki kusan 2-3 minutes yana kallon kansa kafin ya matsa baya kad'an had'e da rik'e waist d'insa nd continuously looking himself through mirrorn
"What should i tell Mamma first..!?"
Ya tambayi kansa nd yana d'an rik'e chin d'insa
"Nayi mata bayanin komai kenan..!?"
Sake yin shiru yayi yana kama waist
"No! Ba haka ya kamata nayi ba.."
Saurin kallon kansa ya sake yi kamar mai magana da shade d'insa kafin ya sake tambayar kansa
"Ohh! Ya rabb,help me..What should i tell her ne,idan ta sake min maganar..!? Shin zan mata k'arya ne ko kuwa zan fad'a mata gaskiya..!? I don't even halted my self akan abunda ya dace.."
Fuskarsa duk alamun damuwa ya bayyana akai saboda yadda ya rasa gane mafitan da zai yi amfani da shi gurin kare kansa a wajen Mamman,zuwa can kuma a hankali kamar mai rad'a ya sake furta
"No..Hammad! K'arya bai yi kama da kai ba,,u know tsakanin Mamma ko Daddy babu wanda ka tab'a yima k'arya ko..!? Why yanzun kake son fad'a mata haka duk dan ka kare kanka ne zaka yi k'aryan..!? Shin idan ka fad'a ma kana da tabbacin zata yarda da kaai ne..?? Baka saba ba,nd kada ma ka soma yau,,u know wannan dama ne ka samu da zaka fad'awa Mamma everything game da yarinyar,nd kasan zata sake yarda da kai ne,kana da daman sanar mata komai nd Mamma will help u,u just tell her the truth,kama daina batun yin k'arya,kasan zata ji zafi nefa idan ta gane...Try to explained her everything game da alak'ar dake tsakanin ku,,ita mahaifiyarka ce zata fahimci komai..!"
Akan wannan shawaran ya tsaya dan yadda yaji zuciyarsa tayi na'am da ita hundred percent,,tun daya fara k'ullawa da warwarewa bai ji ya amince da kowane shawarra ba sama da wannan,dan haka sai ya tsayar da yak'ininsa duka akanta,da fitowarsa a wanka zuwa yanzun ya b'ata kusan one hour ba tare daya morarawa kansa komai ba sai tunanukan da yake ta fama da su,,slender breathe ya saki kafin ya juya zuwa closet d'insa,kayan da yasan sunyi dai² da ra'ayinsa ya d'auka,after ya shirya kansa ya sake tsayawa gaban mirror d'in kafin ya kai hannunsa saman unique perfumes d'insa ya shiga feshe jikinsa dasu,yana ganawa hanyan fita ya tasamma har ya sakko k'asa cikin parlor cike da son barin gidan,cikin rashin sa'a dai² lokacin daya fito yana niyyan ficewa ba tare da yayi kobreakfast d'in da Mamma ta sanar da shi yaba jiransu a dining,sai ya jiyo alamun shigowar motan ta,a parlor kawai ya nemi guri ya zauna yana kad'a car keys d'in dake hannunsan,yayin da zuciyansa ke daka har ta shigo ciki,da shi ta fara yin arba zaune kamar mai jiran wani,ko data shigo d'in har zata wuce shi sai kuma ta dawo cikin parlor'n ta ajiye bag d'inta sannan ta zauna tana kallonsa k'asa²,da fari ki tayi kamar kada ta tambaye shi coz bata son yaga kamar ta damu da son jin maganar da suka yi da shi zai sanar mata idan ta dawo d'in,buh yadda taga yayi zugum kamar wani mara lafiya sai yasa ta kallonsa after taja numfashi ta fara magana da cewa
"Hammad..! What's going wrong ne,u look so pale..Akwai wani abu dake damunka ka kasa sanar min ko..!?"
Ajiyan numfashi yayi kafin ya d'ago idanunsa dake a birkice dan bai sanma ta yadda Mamma zata karb'i batun nasa ba
"Am asking u,,kasa min idanu kamar Yane ka fara ganinta,kasan dai nak'i jinin nayi magana amin banza ko..!?"
Gyad'a mata kai yayi sannan ya gyara zama yana fad'in
"Am really sorry Mah.. Buh..!"
Sai ya sake yin shiru yana jimanta abunda zai fad'a mata
"Buh what..!? Ni yau duka na kasa gane maka,I know kana tare da damuwa,amma ban san mene ne dalilin daya hanaka sanar min ba tun wuri...Ka fad'a min mana idan ina da daman magance maka ai ka sani bazan tab'a barin ka da damuwa ba ko..??"

"Yeahh! Mamma I know kina k'ok'arin ganin kinsamu farin ciki,buh Mah i don't even know ta yaya ne zan miki bayanin matsalar."

"Ok...Ok! Na fahimta,,Kaga ne ko Hammad,ina so ka fad'a min koma ta yaya ne,,kasan zan saurareka ai nd zan fahimci abunda kake nufin.."
Sai daya ajiye wani gauron numfashin kuma kafin ya fara zayyana mata duk abunda ya faru tsakaninsa da su baffa from the loins till an end ba tare daya rage mata ko wasali ba,ko da ta gama saurarensa itanma wani gawurtaccen ajiyar zuciya ta sauke kafin ta furta
"Amma Hammad wani lokacin idan kayi wani abun,ji nake kamar nasa maka hannu saboda takaicin ka (which means ta doke shi),yanzun dan Allah wannan d'an abun ne dama ya faru shi ne kaketa faman b'oyewa da shiga damuwa,,i thought ma ni wani abune daban ya faru can,,,ai shi kenan sai ka saki ranka yanzun ko tunda na sani,,nd nayi matuk'ar farin ciki daya zama ka bada himma wajen ceton rayuwarta a wannan lokacin,da ace baka taimaka mata bane a yau da kake bani wannan labarin da nayi fushi da kai,saboda Allah ya baka iko ka bijere buh babu komai,komai ya wuce kaji ko,har kullum dama bamu da fatan daya wuce Ubangiji ya kare bayinsa daga fad'awa halaka da mummunan yanayi..!"
Murmushin daya gani a fuskarta shine ya bashi k'warin guiwa,nan danan kafin kace me tuni sai ga shi ya ware sun shiga hira,nd fitar daya so yi d'azun sai ya fasa dan dama damuwa ne yasa shi jin fitar,buh ko da yaga yayi solving case d'in sai kawai ya some yinta,yayi zamansa a gidan ba tare daya ji son fita ko nan da can ba.

Har yamma yana tare da Mamma,a hakan driver ya dawo da kid sis d'insa daga skul haka ma lil brother sa wanda daddy's kiddo ke bi,kamar yadda Hammad d'in ke kiranta da shi wanda yasa sai sunanta ya b'ace a gidan duka suka koma fad'a mata hakan har shima Daddyn idan har yana garin kuma yana jin raha,dukansu sai suka taru suka zauna nan a parlor suna ta hira,buh ga Hammad duk da jefi² yake sa musu baki a hiran nasu,kasancewar hankalinsa duka da yayi wani nahiyan daban,sai dai yaji dad'in zaman tare da su a hakan saboda ya jima rabonsa da kasancewa cikinsu kamar wannan lokacin,har dare suka kai tare nd a gefe guda kuma suna ta saka ran ganin dawowar Dad d'in kamar yadda ya shaidawa Mamman tun safe sai dai sunji shiru,nd tun daya sanar ma da Mamma zuwan nasa suke ta baza idanu amma sai shiru har wannan lokacin,wayoyinsa ma duka idan sun kira sai dai ace musu a kashe,,kasancewar duka sun san yadda aikin Dad d'in yake sai yasa su bada uzurin ko tafiyar nasa ne bai yiwu ba,shi yasa suka jishi shirun,,nd sun riga sun san matuk'ar ace zai zo d'in to tabbas ne zai sanar musu ya taho d'in,wannan dalilin yasa sai duk zuwa lokacin yasa suka fidda rai da zuwan nasa a yau d'in,kusan 9pm bayan sunyi dinner nd sun sake tab'a hira after like 20 minutes duka suka yi sallama da juna sannan kowa ya shige room d'insa..

Kwanaki sun sake tafiya a b'angaren Hammad da ahalinsa,yayin da rayuwarsu ya kasance gwanin sha'awa,wanda a gefe guda kuma ya kasance kullum cikin lissafin k'arewar hutunsu yake,dan yadda zuciyarsa ke azalzalarsa da son komawa zuwa garin ya gano halin da suke ciki,sai dai yana ganin kamar a hakan duk da ya d'an kwana biyu da zuwan kwanakin basa wani raguwa,,dan haka ne yau ko daya tashi da safen haka nan sai yaji shifa duk duniya babu inda yake sha'awar zuwa sama da wudil d'in,ba don komai ba sai don kawai yana jin idan bai ganta a yau ba zai iya fuskantar ko wane irin matsala a rayuwarsa....


_Iyyyeee! Tofa fan's kun dai ji Hammad da k'ok'ari, buh bari mu bishi muga mene ne zai wakana,,,kada ku manta yanzun ne labarin ya fara,dan haka wasan zai fara ne daga yanzun..._



#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••
_Devoted to my lil 6ters *Real hafsy & Mamah Zee.*_
_Bestowed to *Sis Hubbeey.*_

*Bismillahir-rahmanir-rahiim.*

_Sak'on fatan alkhairi,tare da fatan rabb ya k'ara muku lafiya ingantacciya mai d'orewa,Cweet Safiyya Bala (Mom Hanan),My cweet mommah Maryam Naseer (MANAB) & Cweet Sis Nerja'at.💞_

_Ina yiwa d'aukacin al'ummar *HAUSAWA* na duniya barka da zagayowar ranar *HAUSA* ta duniya, *MARUBUTA* da *MAWAK'A* wannan rana ce mai d'unbin tarihi kuma abar alfahari a gare mu,fatan rabb ya k'ara mana hak'uri da juriya a tsakaninmu,,Allah ya jik'an magabatanmu baki d'aya.. Ameen👏_

*12.*
_#Love triangle_

A gefen Sabina kuwa musamman cikin wad'annan y'an kwanakin da suka gabata kusan ma iya cewa rayuwan ta a wannan lokacin bata tare da ko wane irin damuwa idan aka cire na tafiyarsa,wanda tun a bayan barinsa garin kawo tsayin wad'annan kwanakin duk da takan yi tunani akan har zuwa yaushe ne zai dawo.? Sai dai a mafi yawan lokuta zaka sameta zaune tayi shiru more especially idan tasan bata da wani aiki walau na gida ko na makaranta,haka nan zata zauna tayi zugum a d'aki ita kad'ai,fita kuwa idan har bawai ya zama mata dole ba,zata iya yini shiru ba tare da anji kanta da kowa a cikin gidan ba dama can asalinta ba mai hayaniya bace (buh ba wai ina nufin idan an tab'a ta tana da hak'uri bane,itan mafad'aciya ce ta gaske sai dai wani abu bai shiga tsakaninta da wani ba,wannan hali ne na masu sunan na fad'a) wannan dalilin yasa sam zaman d'aki a y'an kwanakin baya damunta,haka nan rashin fita da bata yi,a mafi yawan lokuta kuwa idan har ta zauna tayi irin wannan shirun ba komai ne yake damun zuciyarta ba sama da tunanin duk wani abu daya shafi alak'ar su da juna,duk dama dai ba wai ace wani alak'a ne na azo a gani ba d'in ya had'a su ita kam tana yawan tunawa da hakan,,nd a kullum cikin lissafi take tun daga tafiyarsa,adadin kwanakin da yayi sannan a ranta tana sake lissafa wasu y'an kwanaki da sunan sune suka rage masa duk da bawai sunyi magana da shi ya fad'a mata ainihin kwanakin da zai d'auke shi kafin ya dawo ba,,yauma d'in kamar ko wane lokacin ne da yake zuwa mata bata da sauran abunyi banda zama tunaninsa,kamar ko wane lokaci tayi zugum yayin da zuciyarta tayi nisa da gangar jikinta,a hanakali cikin zancen zuci wanda a wasu lokutan har bata sanin lokacin da yake bayyana a fili take juya sunansa da kiransa tana tambayan yaushe ne zai zo,shiru ta sake yi ta nutsu kamar mai sauraren a bata amsa,zuwa wucewar wasu sa'o'i sai ta mik'e a hankali ta nufi adakarta had'e da bud'ewa,turaren *beyonce midnight heat* hannunta ya kai kai,nan ta d'auko shi had'e da bud'ewa tana sunsunar k'amshinsa,ta d'auki ak'alla mintuna biyu da rufaffun idanu kafin ta kai shi jikinta tayi spraying kana ta mayar ta adana,kafin cikin rashin kuzari da tun farko ta kasance a cikinsa ta mik'e ta koma saman gado ta sake kwanciya,nd tana sake dulmiyar cikin tunaninsa.

Cikin sauri² yake komai har ya kammala shirinsa tsaf ya fito,can k'asan zuciyarsa banda addu'ah kan Allah ya taimake shi babu abunda yake,dan yadda yake sauri ko kad'an baya fatan wani uzurin yazo masa a wannan lokacin,cikin sa'a kuwa har ya gama duk abunda zaiyi ya fito bai had'u da kowa ba,a lokacin kusan 11am har ma ya soma gotawa,,kai tsaye mota ya d'auka kafin ya fice daga gidan ba tare daya sanarma da kowa inda za shi ba,gudun ma kada a samu wani matsalan shi yasa hatta da wayoyinsa sau ya kashe su ya barsu nan a gida,,shi kad'ai cikin motan yake tafiya ba tare daya nemi rakiyan kowa ba,sai dai ya kunna karatu cikin k'ir'ar Maheer Al-mu'ak'illiy cikin suratun NISA'A wanda ya sanace ya d'auke masa kewan rashin abokin taya hira da yayi duk dama dai shi d'in ba gwanin zama ayi hira da shi bane buh tafiya ko da tsakanin kurame ne yafi dad'i,yana driven yana saurare had'e da bii,a hakan har ya k'araso dai² mararraban inda ya saba tsayawa,can daga gefen yayi parking sannan ya nemi mai shop d'in da yake barwa ajiyar motansa,bayan ya shaida masa zai shiga ciki kamar ko wane lokaci kasancewar mutumin ya gane shi yasa tun daya ganshi fuskarsa cike da fara'a sai ya tarbeshi,nd daya tunma kafin ya sanar masa da abunda ya kawo shin yayi masa fatan alkhairi tare da fatan fitowa lafiya,bayan daya amsa nan ya tsallaka had'e da fara takawa da k'afafun sa zuwa cikin d'an k'auyen.
Tafiya kawai yake yana kallon yadda amfanin gona yaui kyau,duk kuwa da kasancewar ba damuna bane,da yake gurin akwai ruwa shi yasa amfanin gona a ko wane seasons zaka tarar yayi shar gwanin sha'awa,tafiya kawai yake amma a yau sai yake ganin kamar ana k'ara masa nisanta,duk da irin dogon hanyan daya kwaso daga cikin Kano zuwa wudil d'in wanda duk bai ga nisan suba,sai wannan da yake daf ma da isa cikin d'an k'auyen nasu,shi kansa zuwa wannan lokacin duk da yana jin ya kusa isa,hakan bai hana shi fatan yayi ya tarar da castle na rugan ba,ak'alla sai da yayi tafiya mai d'an nisa daga main road na wudil kafin yayi reaching castle na rugar,ko da idanunsa suka sauka akan k'ofar gidan nasu bai san lokacin da wani irin farin cikiya fara ziyartarsa ba,a hankali ya saki sanyayyan ajiyar zuciya while a fili yana fad'in
"Alhamdulillah.. Alaa kulli halin..!"
Kafin yaci gaba da tafiya yana sake nufar k'ofar gidan,dai² lokacin daya iso yana niyyan tsayawa a k'ofar gidan da hangen inda zai samu yaro ya aika duk da baffa ya sha masa fad'an idan yazo ya shiga kai tsaye hakan ba matsala bane amma sam ya gagara dainawa,domin kuwa a ganin Hammad yin hakan dai² yake da rusa dokar da ubangiji (S.W.T) ya shimfid'a ne,shi yasa har kullum idan yazo d'in ya gwammace ya fara tsayawa ya nemi d'an aike,idan ya samu iso daga gurin masu gidan falillahil hand,,,dai² lokacin daya k'araso yayi dai² da fitowan su Hamudan suna daga gidan zasu je d'iban ruwa rafi,da yake duka babu wanda bai san Hammad ba a gidan walau babba ko k'arami nan da nan ganinsa tsaye sai yasa duka suka nufi inda yake suna washe masa baki,abunka da yaro baya manta alkhairi ko mai k'ank'antarsa kaza lika sharri duk k'ank'antarsa baya tab'a gogewa a zuciyar yarinta,idan ka kyautata ko akasin haka duk mun tsayin lokaci abun tunawa,(Saboda haka k'alubale gare ku jama'a masu zaluntar yara suna fad'in ai basu da hankali baza su gane ba,kana cutarsa a lokacin daka samu dama,shi kuma yana rik'e abun aransa,baza kasan kana yiwa kanka mugunta ba sai lokacin da ya kamata wannan yaron yaji k'anka yazo na tabbata a nan ne zaka ji zance ya sauya salo,,saboda haka garemu gyara ya rage namu) lokacin da suka k'araso kusa sa shi suna masa dariya shima sai ya sake sakin fuska nd yana fad'in
"A'ahh! Samarin baffa,daga nan sai ina kenan..!?"
Cikin hanzari Sule ne ya karb'a masa yana fad'in
"Wollahi rafi zamu je d'iban ruwa.."

"Ohh! To maza Allah ta tsare hanya,,sai kun dawo ma had'u ko..!?"
Amsawa suka yi da to,har sun juya zasu tafi sai kuma yayi saurin tambayarsu
"Hameed..! Baffa yana gida kuwa..??"
Wani dariyar jin dad'i Hamudan yayi dan yadda Hammad d'in ke kiran sunansa a gayance,a mafi yawan lokuta yana matuk'ar k'aunar zuwansa gidan nasu dan yadda yake kiran sunansa cikin lafazi mai dad'i ba kamar y'an gidansu ba da suke kiransa Hamudan,akan wannan dalilin nema a yanzun ya tsani yaji an kira shi da Hamudan,wanda tun can da bai tab'a jin ya tsani hakan ba,sai a bayan zuwan da Hammad,,Sule ne yayi caraf ya amsa masa dan shi Hameed ko nace Hamudan tuni ya lula duniyar farin ciki
"Ehh! Yana nan..Bai dad'e ma da dawowa gida ba.!"

"Yawwa samarin baffa,maza kuyi min iso gurinsa kunji.."
A guje suka koka yi cikin gidan suna rige² kowanne burinsa ace shi ne a kan gaba wajen shaidawa baffa sak'on Hammad d'in,,ko da suka shigan maimakon ace duka sunyi hanya d'aya kamar yadda suka shigo da niyya d'ayan,nan Sule ya shiga gurin baffa while shi kuma Hamudan ya sai ya shek'a agujen ya nufi d'akin su Sabina,tun kafin ya k'araso k'ofar d'akin ya shiga rafka mata kira
"Yaya.! Yayah..!"
Tana kwance tun bayan data gama feshe²n turaren ta jiyo karad'in sa yana kiranta,a lokacin zuciyarta tana raunane a dalilin rashin nayi,tana shirin mik'ewa ta zauna Hamudan d'in ya fad'o d'akin sai haki yake yi,nd still yana sake kiranta
"Yayah..! Kina ina wai..!?"
Sai data ja siririn tsaki kafin ta yamutse fuska da fad'in
"Wai kawai Hamudan wannan wane irin takurawa ne sai kirana kake kamar naci maka bashi..Mene ne zanyi maka ne..!?"
Abunku da yaro baya son yaji an gwasale shi,matuk'ar ace yazo da wani abu na musamman nan da nan sai hakan yasa yaji haushi,bata rai yayi kafin ya kalleta yana cewa
"Haba Yaya..Kin sanfa bana son ana kirana da haka..Al'halin kin san Yayah Muhammad ma ya ce ba haka ne suna na ba."
Tsaki ta sake yi cikin takaici ta juya ta kwanta tana fad'in
"Wahalallen banza ai sai kayi tayi.."

"Yayah to albishir fa nazo miki shi ne amma zaki min haka,, shi kenan nama fasa fad'a mikin,,kinga tafiya ta.."
Tana daga kwancen ta tab'e baki kafin ta sake juya masa baya tana fad'in
"Idan ka gaji sai ka tafi ai..Ni bana son a dame ni.."

"Shi kenan Yayah tunda kin gwale ni..Daga yauma bazan kuma zuwa na fad'a miki komai ba.."
Har ya juya cikin jin haushin abunda tayi masa yana niyyar fita daga d'akin tayi saurin tasowa ta rik'o shi,haka nan sai take jin zuciyarta na shaida mata bata kyautawa yaron ba idan har tak'i saurarensa,cikin sanyin jiki ta kalle shi sosai kafin ta furta
"Yi hak'uri d'an k'anina,,yanzun ka fad'a min mene ne kake kiran nawa,kaji samarin baffa.."
Sake b'ata rai yayi nd yana ta k'ok'arin kwace hannunsa daga rik'on data masa
"Ni ki sake min hannu na tafi,,ai bakya son na fad'a miki tunda har koratama kika yi.."

"Kaii! Hameed d'in baffa nice fa..Wannan yayar taka..Mai k'aunar nan taka.Yawwa zo ka fad'a min kaji Hameed d'ina..!"
Jin da yayi ta kirashi da sunan da yake matuk'ar k'auna nan da nan sai gashi ya saki fuskarsa yana murmusawa,itama kanta Sabinar ko data ga yayi dariya haka nan sai ta tsinci kanta da yin murmushin da bata san dalilinsa ba
"Shi kenan Yayah.! Zan fad'a miki,amma kawo kunnenki kiji.."
Ya fad'a yana rik'o fuskarta,sake matsowa tayi tana masa murmushi
"To Hameed ga shi,fad'a min naji mene ne.."
K'asa² dai² kunnenta ya ce
"Yayah..! Ya zo fa yanzun nan.."
Saurin d'agowa tayi da kanta tana kallonsa kafin tace


Please Login or Register in order to submit comment