Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yin bankwana duka zuciyoyinsu babu dad'i saboda sabo da suka yi da shi a cikin d'an tak'aitaccen lokacin,,,ni kuwa dai cewa nayi kuji tsofaffi da son a sani,sai kace wani jininsu duk sun damu dan kawai zai tafi..Tunma kafin su raka shi kenan,ina kuma ga sun rabu gaba d'aya..?
D'an kalle² ya shiga yi a tsakar gidan kamar mai neman wani abun,kafin ya maida kallonsa ga baffa da yake masa magana,,shi kansa a lokacin tambayar baffan yake son yi game da inda Sabina take,amma kuma sai yayi shiru dan ya rasa me zai ce masa,,a haka duka suka yi sallama da sauran mutanen gidan suna tayi masa addu'ar Allah ya tsare hanya,cikin masu sallamar kuwa harda Innarta amma itan ta gagara ganuwa,,,a iya tsayin lokacin da suka shafe a tun bayan had'uwarsu da yake zuwa gidan bai tab'a zuwa ya tafi bai ganta ba sai yau,wannan dalilin sai yasa shi shiga wani irin yanayin nd karo na farko kenan a yau daya tsinci kansa da jin rashin dad'in faruwar hakan.A hakan ba tare daya sa ran ganinta ba suka tasamma k'ofar fita daga gidan,sai dai ga dukkan wanda ya sanshi ko ya kalleshi a wannan lokacin dole ne ya fahimci akwai damuwa a tattare da shi.
Ganin yadda yake tafiya kamar baya so yasa baffa yayi saurin kallonsa yana tambayarsa
"Mai babban suna ince dai ko lafiya kake..!?"
Da sauri ya d'ago kansa dake sunkuye a k'asa ya kalli baffa yana masa murmushi,kafin ya d'an girgiza kai kad'an yana cewa.....


#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••
_Devoted to my lil 6ters *Real hafsy & Mamah Zee.*_
_Bestowed to *Sis Hubbeey.*_

*Bismillahir-rahmanir-rahiim.*

_*MAMAN PHATYMAH ZAHRA* of Novels by Hassan ATK nd *MOM SAYYEED & NOOR* of Zumunta novella,hak'ik'a comments d'inku yana sani nishad'i kuma yana k'ayatar da ni,ina matuk'ar godiya sosai da yaba muku..Wannan page d'in wa ku kad'ai nayi shi,rabb ya bar k'auna,,,So....#Aci gaba da gashi..✊_

*9*
_#The journey2_

Da sauri ya d'ago kansa dake sunkuye a k'asa ya kalli baffa yana masa murmushi,kafin ya d'an girgiza kai kad'an yana cewa
"Lafiya k'alau baffa..Buh kawai dai naga lokaci yana sake k'urewa ne,shi ne nace bari nayi saurin wucewa kada yamma ta sake yi min..!"

"Toh to..! Ehh! Kayi gaskiya kam,gara mu hanzarta kada almuru ya riske ka baka tafi ba.."
Sake kallon baffa yayi da sauri,kamar zai ce wani abun,dan shi gaba d'aya har ga Allah a cikin zuciyarsa bawai rakiyar tasu yafi damuwa da shi ba,buh haka nan kuma sai yaji bazai iya fitowa fili ya fad'awa baffan abunda ke mak'ale a k'asan zuciyar tasa ba,sannan kuma ganin da yayima babu lallai ace ya samu abunda yake muradin nan take ya daure yana cewa da baffan
"Ahh! Baffa ina tunanin da kunyi zamanku ma,yanzun yamma yayi sosai,ba sai kunyi wahalar rakani ba.."
Murmushi baffa yayi yana girgiza masa kai kafin ya amsa maganar tasa
"A'a baza muyi haka ba,,abu da ba yau aka fara ba,bare kace ka yafe..Abu ne daya zama jiki a gurin mu,tafiya a gurinmu bama ganinta a matsayin abu mai wahala,,dan haka muje kawai kada wannan ya dame ka..Kamar yanzun ne zamu je mu dawo.."
Wucewa yayi gaba sai dai har lokacin deeply yana jin babu dad'i aransa da rashin ganinta da bai yi ba,buh ya san tunda aka kawo yanzun zai yi wahala su had'un kafin ya wuce,,yana tafiya yana sak'e-sak'e a ransa har ya kai zauren gidan inda ya d'an sake tsayawa yana jiran fitowar sa,,,baffa kuwa a nan inda ya barshi tsaye a tsakar gida sai ya juya ga yaran dake zazzaune suna aikin b'are masara daga cikin ganyenta suna fiddata waje
"Kai Hamudan..! Maza kai da Sule ku zo ku d'auki wannan kayan muje ko..!?"
Baffan ya kwallawa yaran biyu kira,,cikin sauri duka suka bar aikin da suke yi sannan suka fara kiciniyar d'aukan sacks da aka masa packaging tsaraban da zai tafi da su,sannan kuma a tare dukan su suka yi hanyar fita a gidan while suna tsokanar sauran da baffa bai ambata ba,,har baffa ya waiwaya zai fita kamar wanda yayi mantuwa ya dawo da sauri yana fad'in
"Mairo..!! Ina uwata ne..? Yau duka banji d'uriyarta ba tun safe..Anya ma kuwa sun gaisa da MUHAMMADU..!?"

Duk abunda ake yi a gidan tun zuwansa da hirarrakin su babu wanda kunnuwanta basu saurara ba,buh ta b'oye kanta a d'aki a dalilin jiyowa da tayi ana cewa zai yi tafiya,,wanda itan kanta duk da bawai suna wani shahararren shiri da juna ba ko dogon hira idan yazo gidan sai duk take jin kamar tace masa kada yayi tafiyan,,tun fitowarsa tare da baffa da duk sallamar da suke yi da y'an gidan tana tsaye jikin labule tana lek'e har zuwa lokacin daya fita,ko da jin bai tambaya tana ina ba a hankalk wasu irin tears masu d'umin gaske suka fara gangarowa daga idanunta,komawa tayi saman gado ta kwanta tana ci gaba da kuka k'asa².
Lokacin ko da baffa yake tambayar Innarta tana ina,take tayi saurin mik'ewa tana wiping tears d'inta kana tayi wuf ta fice daga d'akin cikin matsanancin jin dad'i,zuwa lokacin kuwa dama duk ta k'agu,jira kawai take taji anyi magannarta.
Ko kafin Innar ta bawa baffa amsar tambayar da yayi mata tuni hat ta fito daga d'akin kamar wacce aka cillo waje,kallonta Inna tayi da mamaki shimfid'e a fuskarta,sai dai bata iya cewa da ita komai ba ta juya tana girgiza kai dan ita dai AL'AMARIN Sabinar a y'an kwanakin yana matuk'ar d'aure mata kai,,inda baffa yake tsaye ta nufa cikin rashin kuzari while kanta a k'asa tak'i bari su had'a ido da kowa dan gudun kada a gano damuwarta,tun bata k'araso ba baffa ya kalleta yana cewa
"Uwata yau kuma zaman d'aki kike sha'awar yi ne..Duka ban saki a idanuna ba..!?"
D'an kad'an tayi murmushi wanda yake daf sawa ta saki sabon kuka nd cikin muryanta mai tattare da sanyi ta ce
"Laaa! Baffa bayan mun gaisa da kai d'azun dana dawo daga makaranta,,kuma fa har tambayar kama nayi nace zani gidan yagwalgwal anjima.."

"K'warai..! Anyi haka..Na manta ne SHALELE shi yasa na tambaya..! Amma duk ba wannan ba,shin kinje kuwa kun gaisa da MUHAMMAD..!?"
Duk da tasan da zuwansa gidan ambaton sunansa da baffa yayi sai da yasa taji zujiyarta tayi wani irin mugun tsinkewa,cike da dauriya mai tattare da rainin wayo,nd tana yi tamkar bata san yazo gidan ba duk da karad'in da y'ay'an gidan suka yi tayi daya zo d'in kasancewar irin sabon da suka yi da shi sai cewa tayi da baffan
"Ehmm! Baffa yaushe ya zo..!? Ai ni banma sani ba,,buh ina jin ko lokacin da yazo ina bacci..!"

Yana daga tsaye a zauren gidan nasu kunnuwansa suka jiyo muryanta lokacin suna magana da baffan akansa,buh abun daya bashi matuk'ar mamaki shi ne yadda duk ihun da yaran suka yi wai tace bata sani ba,,nan take yanayin maganarta sai ya sake d'aure masa kai,a zuciyarsa yake k'iyastawa dan yadda muryanta yake fita sam babu wani alamun dake nuna yayi kama dana mutimin daya tashi a bacci,muryan baffa ya sake jiyowa yana cewa da ita
"To uwata kuma banda abunki ai yanzun sai kiyi sauri ki riske shi ko ku gaisa,,lokaci yana sake wucewa,bayan kinji na shaida miki yana da tafiya a gabansa..!"
Kamar wacce bata son zuwan ta amsawa baffa a kasalance da "Toh" sannan taja k'afafunta tana nufar hanyar soron gidan,tafiya take da kyar yayin da zuciyarta duka ta shiga cikin wani irin yanayin alhini na rashin son tafiyar tasa.Tun data nufo soron yayi hanzarin sauya yanayin fuskarsa zuwa wani irin mood mai wuyar fassara,ko data k'araso kanta yana sunkuye a k'asa nd bakinta d'auke da sallama har ta riske shi,,,kamar wanda baya son yin magana ya d'ago kansa dake k'asa ya zuba mata su had'e da amsawa,,shiru Sabina ta d'anyi tana tunanin abunda ya kamata tace masa bayan sallamar,amma sai taji duk ta zama wata speechless,,duk motsin da take akan idanunsa ko da yaga tana k'ok'arin d'agowa cikin sauri ya janye idanunsa akanta,itanma sai data kalleshi sannan ta iya furta
"Ina wuni..!?"

Sai daya sake d'agowa ya kalleta while deeply yana fad'in
"Lallai yarinyar nan akwaita da iya rainin hankali.."
Buh a zahiri sai yaja wani mugun space kafin ya iya amsa mata
"Lafiya..! Ya kike..!?"
Dogon ajiyar zuciya ta sauke nd tana kwantar da kai sannan ta iya amsawa
"Lafiya k'alau.."
Shiru duka suka sake d'auka a soron babu wanda ya sake magana,ga Sabina kuwa a lokacin tambayar kanta ta shiga yi a zuci,fad'i take
"Ohh! Ya rabb..help me..me zance masa ne...!? Aarrghh! Ya Allah.. Me ya kamata na aikata..!?"

"U must to tell him all what u want..Or else..!?"
A hankali ta maida idanunta ta runtse while zuciyarta na harbawa da sauri² sannan tayi jarumtar tambayarsa da cewa
"Ashe tafiya za kayi..!? Allah ya tsare hanya ya saukeka lafiya,,nd a gaida kowa da kowa..!"
Still idanunsa na akanta ya tsinto maganar nata har ya wuce shi,d'an siririn murmushi yayi duk da bata gani ba yana fad'in
"Ehh! Hakane..Ameen thumma ameen.. Na gode sosai *K'ANWATA* da addu'ar ki,nd in sha Allah sak'on ki zai isa ga kowa kamar yadda kika fad'a..!"
Haka nan ta tsinci kanta a cikin yanayin jin dad'in amsar sa wanda har yasa ta saki murmushi,,,duka sun sake yin jim ba tare da wani cikinsu ya sake cewa komai ba,a lokacin sai ga baffa ya fito,nan ya d'an kallesu duka kana yana fad'in
"Toh..! Mai babban suna, idan kun kammala sai mu tafi ko..!?"

"Toh baffa.."
Abunda ya fito daga bakinsa kenan,nd tun bai kaiga gama fad'a ba tuni tayi saurin d'agowa tana kallonsa,yayin da a lokaci guda taji wani irin tashin hankali ya sake ziyartar ta,gaba baffa ya wuce zuwa waje,nan shima ya motsa daga inda yake da hannayensa zube cikin aljihun trouser d'insa,sai daya kalleta sannan ya fahimci itanma shi take kallon buh yanayin da fuskarta ta bayyanar sai yasa zuciyansa tafiya tak'aitaccen yajin aiki,,sam bata kula da abunda yake yi ba,sai dai taji muryansa daf da ita,da sauri ta dawo hayyacinta tana sake kallon yadda suka yi closer da juna,d'an ja baya tayi kad'an tana jingina bayanta da katangan soron,ba tare daya sake matsowa ba ya furta
"Arrmm! *K'ANWATA* ni zan wuce ko..!?"
Kai ta rausayar gefe ba tare data sake iya yin k'arfin halin yi masa magana ba,still tana tsayen sai dai kanta yana k'asa tana wasa da yatsunta,,a d'an kaikaice ya kalleta while yana sake fad'in
"Ki shiga gida,,,sai na dawo ko..!?"

Kamar zata d'ora hannunta aka tayi ta zunduma ihu haka take ji a duk sanda yace zai tafi,,ganin ta kasa motsawa a gurin sai ya sashi juyawa ya kama hanyar fita yana sake maimaita mata
"Na tafi..nd ina son ki maida hankali sosai akan karatunki.."
Da sauri ta d'ago kanta dake sunkuye,slightly idanunta suna tara hawaye,har ya fice akan idanunta ba tare data iya ce masa komai ba,a hankali ta shiga silalewa a gurin har ta kaiga zama kan dandagaryar k'asa,yayin da hawayenta suka sami damar fara sauka,kanta ta kife a tsakanin guiwarta tana sakin sheshshek'ar kuka mai tsuma zuciya.

A k'ofar gidan ya iske baffa suna jiransa,dan haka ko daya k'araso fuskarsa cike take da fara'a
"Baffa mu tafi ko..!?"
Ya furta yana mai kallon dattijon,har baffa zai amsa masa,nan ya hango inuwarta a soron bata tafi ba,shima murmushin ya maida masa kana yana fad'in
"K'ANWAR taka ta shiga gida ne..!?"
Saurin waiwayawa yayi yana kallon soron ba tare daya amsawa maganar baffan ba,kasancewar kuma yafi baffa kusa da inda zai hangota d'in,ko daya juya d'in nan take ya hangota zaune dirshan,sake kallon baffa yayi kamar zai yi magana,kuma sai ya fasa ya juya da sauri zuwa soron,,tana zaune tana ta rera kuka abunta har ya k'araso kanta bata sani ba,a dai² gabanta ya tsuguna yana kallonta ba tare da yayi mata magana ba,k'amshinsa da yayi remaining a soron ne ya fara ziyartar hancinta buh this time around tana jinsa sosai ne ba kamar lokacin daya fita ba,saurin d'ago kanta tayi da hawayenta har lokacin suka gagara tsayawa,idanunta suka sauka akansa yana tsugune daf da ita,k'ik'k'ifta idanu ta shiga yitana son tabbatarwa kanta anya shi ne ya dawo da gaske..!? Ta d'auki mintuna tana kallonsa kafin ta amincewa ranta abunda idanunta suke gani,ko data tabbatar shi d'in ne a gabta da gaske,cikin sauri ta fara k'ok'arin goge fuskarta,shima cikin saurin ya zaro handkerchief yana mik'a mata,da kyar tasa hannunta ta karb'a sannan ta kai shi fuskarta tana goge hawayen,k'amshin da handkey d'in keyi a lokacin daya bugi hancinta ya sata lumshe idanunta kad'an
"Mene ne dalilin da yasa ki kuka..!?"
Tambayarsa ta shiga mata amsa kuwa a cikin kunnuwanta,saurin dawowa hayyacinta tayi da sauri ta fara k'ok'arin mik'ewa,malalacin kallon daya bita da shi ne yasa ta komawa ta zauna sai dai ta kasa amsa masa,a hankali ya tab'e baki jin tayi shiru bata amsa shiba sai yasa shi sake fad'in
"Tashi ki shiga ciki..Nd kada na kuma ganinki kin zauna a nan kina wannan kukan..Kin jini ba..!?"
Kamar zata bud'e baki ta fad'a masa dalilin ta nayin kukan,kuma sai taji ba zata tab'a iya yin hakan ba,har ta tashi zata wuce shi ba tare da tayi magana ba yayi saurin rik'o hannunta ta baya,kyam ta daskare a gurin tamkar ginannen dutse zuciyarta fal tsoro,shima a hanakli ya shiga dawowa ita baya har ya dawo da ita inda ta tashi,kallonta yake kamar bazai daina ba sai dai tuni ya saki hannunta daya rik'o
"Mene ne yake damun ki..!?''
Ya tambayeta
"Nima ban sani ba.!"
Amsan yayi escaping daga bakinta without ta shiryawa yin hakan,d'an murmushi yayi sama² kuma yana fad'in
"I don't think so.. Nasan kin sani buh kina k'ok'arin boy'ewa dai!"
Saurin kallon sa tayi sai kuma ta sake saurin sauke kanta k'asa tana girgizawa,sake matsawa yayi sosai kusa da ita har numfashin su yana had'uwa
"Ban yarda baki sani ba,,,shin zaki fad'a min ne ko kuwa sai na..!?"
Yana maganar yana sake nufarta,idonta tayi saurin rufewa cike da tsoron abunda zai mata ta sake fad'in
"Ka yarda da ni..Ban sani ba..!"
Cak ya tsaya ba tare daya k'ara ko da taku d'aya ba,yana sake zuba mata idanunsa
"Da gaske baki sani d'in ba..!?"

"Ehh! Ban s...Sa..Sa ni ba..!"
Daga yadda take magana ya tabbatar masa ba wai abunda take so ta fad'a ba kenan,sai dai haka nan yaji bazai iya takura mata ta fad'a masa ba,matsawa ya fara yi daga kusa da ita yana kad'a kai
"Ok good..!"
A hankali ta fara bud'e idanunta dake rufe,ko data gama bud'e su nan taga ya bar kusa da ita,ajiyar zuciya ta sauke mai k'arfin gaske,,har lokacin itan yake kallo,sai yaga ta d'an runtse idanu,a hankali kuma y'an guntun hawayen da suka mak'ale suka samu damar saukowa,hannunta da yake rik'e da handkey d'insa tasa ta d'auke su,kana ta juya da sauri ta shige gidan ba tare data sake bari sun had'a ido da shi ba,,kayataccen murmushi ya saki yana shafo moustache d'insa,sai daya shafe kusan minti biyu a gurin sannan ya juya cikin sauri ya fice,bai sake tsayawa ba bayan ya d'anyi gaba ya kalli su baffa yana fad'in
"Baffa mu je...Ta koma gida yanzun..!"
D'an murmushi baffa yayi masa sannan suka kama hanya dukansu,har sun d'anyi nisa kuma haka kawai sai yaji yana sha'awar sake kallon kofar gidan,a hankali ya d'an waiwayo ya kalli k'ofar gidan kafin yayi ajiyar zuciya,kana suka ci gaba da tafiya,duk hiran da su Hamudan sukewa baffa akan zuwa birni bai san suna yi ba dan shi tuni zuciyarsa tayi wani duniyar,,,har bakin titi suka rako shi,nd wannan lokacin sai basu tsaya inda suka saba ba,har tsallaken titin suka kawo shi sannan suka shiga ajiye kayan a k'asa yayin dabaffa yake fad'in
"To mai babban suna nasan dai abun hawa bazai yi wahalar samu ba a nan tunda mun fito."

Murmushi yayi kad'an yace
"Haka ne baffa,,amma da mota ma na zo.."
Kallonsa baffa yayi da mamaki sosai a saman fuskarsa,duk da hakan daya fad'a d'in ba wai abun ace yayi mamakin bane,idan har ace yayi duba da irin suturun da yake sawa,ahi kam Muhammad ba tare daya jira cewar baffa ba ya matsa kusa da mutumin da yake bawa ajiyar motansa a duk lokacin da yazo yayi masa sallama,bayan nan kuma yayi masa godiya kamar yadda ya saba had'e da yi masa alkhairi ya bud'e motan ya shiga,ko da baffa yaga ya shiga motan duk da yana cikin yanayin mamaki amma kuma hakan bai hana shi yin magana ba,a fili ya furta
"Ikon Allah..!"
Kafin ya matsa gurin motan,nan suma su Hamudan suka yi saurin d'aukan sacks d'in da suka ajiye suna rige² suka nufi kusa da motan nasa sai wangale baki suke murna fal zuciyoyinsu,sai daya gyara packing ya saita motan dai² yadda yana tashi zai hau kwalta sannan ya fito ya saka buhunhunan tsarabarsa a booth,,a hankali ya matsa inda baffa yake tsaye har lokacin shi dai yana cikin mamakinsa
"To baffa..Ni zan wuce..!"
Firgigit baffa ya dawo daga tunanin daya lula ya amsa masa
"Tohh! MUHAMMADU Allah ya tsare,Allah ya kiyaye ko..? A gaida magabatan..Mun gode sosai,ubangiji yayi albarka kuma ya saukeka lafiya.."
Kansa yana duk'e a k'asa yana amsawa da
"Ameen baffa..Na gode sosai nima,ubangiji yaja da nisan kwana.."

"Ameen" baffa ya amsa masa sannan ya kalli su Sule yana fad'in
"Toh ku malamai sai mu koma ko..!?"
Saurin dakatar da su MUHAMMAD yayi yana cewa
"Sulaiman..! Ku jira ni kad'an kunji..!?"
Motan ya koma da sauri sannan ya d'auko wasu lesser guda biyu masu kyau,yana murmushi ya sake fitowa inda suke,sai daya kalli yaran sannan yace
"Yawwa samarin baffa..ga shi ko..!? Wannan naku ne..wannan kuma ku kaiwa..!"
Sai yayi d'an jim kafin yace
"Ku bawa Auntyn ku.."
Kallon juna suka yi sannan suka kalleshi suna masa murmushi,cikin had'in baki duka suka furta
"Aunty *SABINA..!?"*
Kai ya girgiza musu yana lumshe idanunsa,baffa ne ya matso inda suke yana fad'in
"Anya mai babban suna..!? Kai da zaka yi tafiya me ya kaika tsayawa siye² haka..!?"
Murmushi yayiwa baffa sannan yace
"Babu komai baffa,, gani nayi idan na tafi yanzun zan jima ban sake dawowa ba,,,sannan na manta da sak'on ne tun d'azun shi yasa ban kai musu ba.."

"Toh! Ai shi kenan..An gode sosai Allah yayi albarka.."
Da "ameen" ya amsa masa sannan yasa hannunsa a aljihu ya zaro kud'in da bai san ko nawa bane ya mik'awa baffan,nan baffa ya nuna sam bazai karb'a ba,sai da suka kai ruwa rana kafin da kyar baffan ya amince ya karb'a,, sunyi masa godiya sosai,shima yana ta yiwa baffan godiya kafin ya shiga motan yaja ya barsu a nan,basu suka tafi daga gurin ba suma har sai da suka ga yayi musu nisa sosai sannan suka yi k'ok'arin tsallaka titin suka d'auki hanyan komawa zuciyoyinsu cike da alhinin tafiyar tasa.

Shi kansa MUHAMMAD tunda ya d'auki hanya yake ci gaba da hangensu ta cikin mirror nd yana jin zuciyarsa tayi masa wani iri,yana jin kamar ya koma gare su,,a hakan ya daure yaci gaba da driven tun yana iya hangensu suna masa waving har yayi nisa da su ya daina hangosu.

Kai tsaye ko daya taho sai daya shiga campus inda ya bar Sultan yana ta jiransa,a lokacin kuwa a b'angaren sultan zuwa lokacin tuni ya gama zuwa wuya dan yadda ya gaji da zaman jiran nasa,gashi tun tuni sai kiransa yake amma amsa d'aya yake samu shi ne yana ta rejecting calls d'in nasa,,lokacin daya k'araso bai ko kalli sultan d'in ba ya wani had'e rai yana fad'in
"MALAM ka taso mu wuce ko..!?"
Kallonsa sultan yayi cikin takaici sannan ya mik'e ya shiga motan ya zauna,sai dai bai kula shiba dan yasan fad'an zai iya juyawa ya dawo kansa,,,sai da yayi reverse sannan ya sake take motar da mugun gudu ya fice a cikin makaranta,har suka d'auki hanyan cikin garin Kano sultan bai ce masa ko ci kanka ba,haka shima gogan bai bashi fuskar da zai masa k'orafi ba,yadda duk suka yiwa juna shiru sai yasa tafiyan nasu ya zama bashi da maraba dana kurame.
In less than 1 one hour suka shigo cikin gari kasancewar bada wasa yake tuk'in ba,nan da nan sai gasu akan titin mayangu dake cikin unguwar ta nassarawa G.R.A,daf da race course ya karkata kan motan inda ya tsaya bakin wani katafaren gida na gani a fad'a,,wanda take ni kaina ko da naga ya tsaya a bakin wannan katafaren gidan yasa birona sub'ucewa daga hannuna,har ban san lokacin da bakina ya furta "Ya salaam...!" Ba saboda tsaruwar gidan tun daga waje....

_Hhhhh! Fan's kada ku gaji dani,ku dai kiui gaba da hak'uri,kwana biyun nan ne muna fama da matsalar wuta a gari sai kun k'ara hak'uri dan zaku ga bana posting akan lokaci kamar baya,,so ba daga ni bane,matsalan kusan duka gari ne.Ayi min afuwa._


#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••
_Devoted to my lil 6ters *Real hafsy & Mamah Zee.*_
_Bestowed to *Sis Hubbeey.*_

*Bismillahir-rahmanir-rahiim.*

*10*
_#Ponders_


Horn ya shiga matsawa cike da k'aguwa yana jiran a bud'e masa ya shige,,sai lokacin ya d'an waiwayawa a hankali zuwa gefen sultan yana kallon yadda ya gimtse tamkar baya gurin duk kuwa da irin surutun sa amma yau yayi masa shiru,d'an murmushi ya saki mai sauti kafin ya furta
"Heyy! Friend what's up..!?"
Wani mugun kallo sultan ya watsa masa mai tattare da jin haushin tambayar da yayi masan sai dai bai tanka masa ba,saima siririn tsaki da yaja kafin ya sake d'auke kai,a zuciyansa kuwa haushin Muhammad d'in duk ya cika shi nd yana ganin tambayar da yayi masa ma bata da maraba data rainin hankali,,wani murmushin ya sake yi masa kafin ya tab'e baki ya juyar da kansa zuwa kallon get d'in da ake bud'ewa,sai daya bari get man d'in ya gama janye masa get d'in sannan ya taka motan zuwa ciki

Please Login or Register in order to submit comment