Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dan haka koda zai kai shekara baya nan baza ta damu ba,duk da cewa abu mafi kyau shine indai da hali anfiso matafiyi yar ik'a tak'aita kwanakin da yake yi yana dawowa wajen iyalinsa idan yayi wata tafiya,amma idan ya kasance akwai wani uzuri to babu laifi akansa idan ya dad'e koda kuwa ya haura watanni shida (6) ne acan din idan bukatar hakan takama,kamar wanda ya tafi neman magani ko kasuwanci a wani gari ko wata k'asar mai nisa,ko kuma misali kai da zaka tafi neman ilimi,amma idan har yanajin tsoron faruwar wata fitina ga iyalinsa saboda kasancewarta mai yawan sha'awace ita ko kuma dad'ewar sa a can d'in zata haifar masa da sab'ani tsakaninsa da surukansa,to ya kamata ya rik'a dawowa da wuri saboda kaucewa wannan matsala,kada yayi dad'ewar da zata zama sanadin rabuwarsa da matarsa (domin neman k'arin bayani sai ku nemi Almughniiy na ibn k'udaamah cikin majmuu'ul fataawa 32/271),saboda haka abunda nake so ka fahimta a nan shi ne,ba wai yin auren ne matsala a gare niba,A'a abunda zai faru gaba shi nake ji,dan haka hukuncin da zan yanke a nan shi ne..!"
Saurin taron numfashin sa Hammad yayi da fad'in
"Na amince baffa da duk hukuncin ka,amma dan Allah kayi min rai ka yarda na bada sadakin kafin tafiyata,iya wannan alfarmar kad'ai ta isarmin baffa,daga shi bazan sake cewa komai ba,duk hukuncin daka yanke am ready na karb'a ko da zuciyata bata so,,amma baffa ka duba hakan..Pleasee..!"

Jimm baffa yayi yana nazarin maganarsa,ganin hakan da yayi dai² yake da baffa yak'i amincewa buk'atarsa yasa shi had'e hannayensa guri guda ya shiga rok'on sa kamar idan yak'i amincewa zai kece da kuka,ajiyar zuciya baffa ya saki cikin kaiwa mak'ura kafin a hankali baffa ya furta
"Shi kenan Muhammadu,,,idan har dan wannan ne na aminc..!"
Tun kafin ya k'arasa cikin k'arajin murna tuni Hammad yayi sujudush-shukhur,lokacin daya d'ago bakinsa sam yak'i rufuwa banda kalmomin godiya babu abunda yake jerawa ga ubangiji (S.W.T),,Baffa kansa yadda yaga yana murna sai da lamarin ya sake d'aure masa kai,nd yau rana ta farko ya sake tsinkewa da lamarin ubangiji,cikin zuciyarsa fad'i yake "idan ba Allah ba babu wanda ya isa ya sanya soyayya mai k'arfi tsakanin bayinsa kwatankwacin wannan da idanuna suke ganemin",,sun jima sosai a zaune banda godiya babu abunda Hammad ke yiwa baffa,kafin daga bisani baffan yayi masa bayanin ya kamata a rubuta yarjejeniya akan maganar,gudun ko da gaba idan yajewa mahaifansa da batun suka k'i amincewa zai zamanto akwai gagarumar hujja da dole tasa su yarda,cike da k'warin guiwa Hammad ya amsa nan baffa ya aika domin a nemo masa k'annensa wato baban Sabina da baban LADO,sai wasu amintattun dattawa daga abokansu da ake zaman lafiya a garin da yasa aka fad'awa,ko da suka zo a gabansa baffa ya zayyana musu bayanin duk yadda suka yi da shi da irin hukuncin daya zartar akan lamarin,babu wanda yaga laifinsa cikin abunda ya aikata kasancewar dama tuni duk wani hukunci shi yake yankewa akan ahalin nasu,kamar yadda ya ambata tun da farko nan Baffa ya wakilta dattawan nan biyu domin su zamo waliyyai ga Hammad yayin da baban LADO da baban Sabina suka kasance waliyyan Sabina,bayan nan baffa yasa aka kawo masa takardu da alk'alami daga cikin gida yayi musu jawabin abunda za'ayi sannan ya fara rubutu da larabci akan takarda ta farko,yayin da yake karanta duk abunda yake rubutawa a fili har ya gama rubuta takardun *ALK'AWARIN* da suka k'ulla d'in akan Sabina da Hammad,sannan batun sadaki daya bayar wanda za'a ajiye kamar yadda ya buk'ata daga nan zuwa lokacin da Allah zai dawo da shi,bayan ya gama ya sake karanta musu sannan ya tambaye su ra'ayinsu dan gane da hakan,ba'a samu wanda ya musanta batun ba a cikinsu,ko da baffa ya tabbatar babu wanda yake da abun cewa nan ya ja layi guda shida a k'asan kowace takarda ma'ana inda kowa zai sa hannu wanda kuma shi yake sake tabbatar da kowa yayi na'am,daga nan baffa ya rattaba sa hannu,sannan Hammad da waliyyansa daga nan aka mik'awa baban SABINA da baban LADO duka suma suka sa hannu,takarda d'aya baffa ya d'auka ya mik'awa waliyyan Hammad yana fad'in
"Wannan takarda dana baku,na baku ita ne ba don komai ba,sai dan ta zama shaida agareku da kuna tunatarwa bisa *ALK'AWARIN* da kuka d'aukarwa kanku,wanda na tabbata kallonta a koda yaushe zai kasance yana tunatar da ku muhimmancin rik'on amana da cika *ALK'AWARI* da Allah (S.W.T) ya ambata a cikin suratun-Nisa'a (aya ta 58):"Lallai ne Allah yana umarnin ku da ku bayar da amanoni zuwa ga masu su.Kuma idan zaku yi hukunci a tsakanin mutane,ku yi hukunci da adalci.Lallai ne,Allah madalla da abunda yake yi muku wa'azi da shi.Lallai ne Allah ya kasance mai ji ne,kuma mai gani ne". Sannan Allah mad'aukakin sarki ya sake fad'a a cikin suratul ma'idha (aya ta farko) inda yake cewa:"Ya ayyuhallazhiiyna aamanuu aufu bilk'u'uud... Ma'ana:-Yaku wad'anda suka yi imani! Ku cika alk'awurra..(ilaa akhirul aya) kamar yadda mu duka muka shaida kuma muka amince zamu cika wannan *ALK'AWARIN*,saboda haka nasan tunawar zai zame mana alkhairi baki d'aya sannan kuma ya bamu iko tare da damar aiwatar da wannan umarni na mahaliccinmu.."

"Wannan gaskiya ne,,Malam Ibrahim kayi gaskiya,hakan ya kamata sosai.."
Wata takardar ya sake d'auka ya mik'awa su baban Sabina yana mai fad'in
"Kuma ina son ku ajiye wannan a gurinku dan ya zama shaida ko da zuwa gaba.."
Bayan nan ya bawa HAMMAD guda shima ya rik'e guda,daga nan baffa ya yiwa waliyyan Hammad umarni da su bada sadaki ga waliyyan Sabina,sunyi komai yadda ya dace kuma bisa tsari,sannan suka tabbatar da batun aure bayan dawowarsa,daga haka sai baffa yayi umarnin da a rufe taron da addu'ah bayan nan ya sallami kowa..

Fitarsu a d'akin ya rage daga shi sai Hammad kawai dan haka a nan sai baffa ya samu damar yin magana da shi cikin nutsuwa,yayi masa nasiha mai shiga rai,bayan sun gama kasancewar duk maganar tasu a gaggauce ne ya tura aka kira masa Sabina don itama yayi mata bayani,ko da tazo bayan ya had'a su duka sai da yayi musu nasiha sosai,kafin yayi mata bayanin abunda ya faru a tak'aice,sunyi sallama da Hammad sannan baffa ya fita ya basu guri domin suyi sallama,lokacin ko da baffa ya fita a d'akin wani irin kallo Hammad ya shiga binta da shi kamar zai had'iyeta,,ita kuwa tun da baffa ya fita ya barsu bata iya d'agowa ba bare ta kalleshi ta gano a yanayin da yake ciki,duk da dai ta tabbatar itan tana cikin matsanancin farin ciki ta san ko shakka babu shima d'in haka yake,tayi nisa cikin duniyar tunanin makomarsu a yanzun da kuma gaba ta tsinto hannunta cikin nasa,a matuk'ar firgice ta d'ago ta kalleshi,kwantaccen murmushin da taga yanayi mata yasa ta sake kallon hannayensu ba tare data iya cewa komai ba ta kuma sauke kai k'asa
"My Lady..! Shin baza ki dago ki kalle ni ba..?? Am ur's fa daga yanzun,kina da right na kiyi ta kallona har sai kin ji kamar ki maidani ciki dan..."
Siririyar dariya ta saki tana k'unshe baki da d'ayan hannun,shi kuwa gogan nan ya shagala da kallonta,sai da tayi mai isarta kafin yasa hannu ya d'ago chin d'inta yana tambaya
"My Lady.. Na fad'i wani abune da yake ba dai² ba..??"
Dakatawa tayi daga dariyar da take tana girgiza masa kai,murmushi ya sakar mata,zuwa wani lokaci ya saki ajiyar zuciya muryarsa cike da sanyi yana fad'in
"My lady..! Kafin na tafi..I have only one wish da nake son sanar dake...Ina fatan baza ki gagara yi min ba..!?"
D'if wuta ta d'auke mata jin lokaci guda ya ambaci tafiya wanda ita idan a son ranta baza tak'i ace ya zauna tare da ita fover a k'auyensu ba
"For da sake of Allah..! Ina rok'onki ki kasanace mai rik'e min amanar kanki,nd *ALK'AWARI* na akanki,i know tafiyan da zanyi zan jima ba tare da munga juna ba,buh ki kasance mai kiyaye kanki da amanar kanki dana bar miki,in sha Allah zan kasance mai rik'e miki amanar kaina,bazan tab'a manta *ALK'AWARIN* ki akai na ba,har naje na dawo..Kin ji..!?"
A hankali ta girgiza masa kai irin na bata so ba d'in nan hawaye suna sakko mata
"Ohhh! Ya rabb,,pleasee mana baby don't cry,tun ban kai ga tafiya ba kina son yin kuka,kina son sawa kanki ciwo ne ko.?? U have to know tafiyan da zanyi nan kawai zan yi shi ne amma ba dan ina so ba,sai dan kasancewarta umarnin mahaifina nd idan na tafi na tabbata zan rayu ne cikin k'unci da damuwar rashinki,wannan dalilin ya sanya a kullum nake cewa,idan babu ke ba zan iya rayuwa ba,,,please my Lady kada ki nuna min haka dan Allah,domin kuwa yin hakan ka iya tarwatsa sauran farin cikin da zan tafi da shi.. Ina Son ki sosai,ba zan iya barin *ALK'AWARIN* ki akaina ba,ya kamata kisan da wannan.."
Fad'awa tayi jikinsa tamkar wacce mayen k'arfe ya fisga ta k'ank'ame shi,duk da yanayin da suke ciki hakan bai hana su jin ratsawar kyakykyawan electrification a cikin jininsu ba,murmushi ya saki mai sauti yana caressing bayanta a hankali yana sakin sanyayyun ajiyar zuciya,ita kanta ajiyar zuciyar take dan yadda take jin kamar kada ta rabu da jikinsa,yayin da kyakykyawa kuma daddad'an perfumes aroma d'insa suke ratsata suna sake taimakawa jikinta wajen sanyaya duk wani gab'ar dake da aiki,luf ta sake yi a jikinsa har na tsayin mintuna kafin ya d'ago ta yana fad'in
"My Lady.. Ya kamata kiyi min izinin tafiya bcoz tafiyan da zanyi yana da nisa sosai nd lokacina ya kusa cika.."
B'ata fuska tayi cike da sakarci tana son yi masa kuka,cikin sauri ya janyo ta yana fad'in
"No..! Babe do u know..!?"
Da sauri ta furta
"Me ne..!?"

"Shi kenan ma barshi kawai.."
B'ata rai tayi tana k'ok'arin matsawa yayi saurin kamota yana murmushi
"Sorry.. Sorry babe..!"

"A'a ni dai ka sake ni,,kaga fa babu kyau yin haka.."
Murmushi ya saki mai sauti cike da zolaya yana kallonta
"Ohhh..! Dama babu kyau..!?"
Kallonsa tayi saurin yi itama da mamaki kwance a saman fuskarta tana fad'in
"Ehh! Ai nasan kaima ka sani.."

"Nooo! ni ban sani ba.."
Harar wasa ta masa sannan tace
"To d'an sake ni.."

"Na k'i.!"
Yayi maganar yana mak'ale shoulder,"uhmm" tace ba tare data sake yin magana
"Uhmm! What..!? Speak ur mind.. Kin san idan baki fad'a yanzun ba babu lokaci ko..?"
Gimtse fuska tayi cikin sauri ta fizge jikinta daga rik'on da yayi mata,da saurin shima ya sake kamota ya dawo da ita jikinsa,rik'on tsam yayi mata wanda yasa ta kasa kyakykyawan motsawa
"Pleasee..! Ka sake ni.."

"Idan nak'i fa..!?"

"Zanyi ihu kowa yaji.."

"Da gaske za kiyi ihu..??"

"Ehh! Mana.."

"Uhmm! Bismillah to yi maza ina sauraronki.."
Yana fad'a yana juyo da ita suna fuskantar juna still yana rik'e da ita tsam a jikinsa har k'irazansu na had'uwa,marairaice masa tayi kamar za tayi kuka tana fad'in
"Pleasee..! Ka sake ni..Kada wani ya shigo.."
Dai² fuskarta ya matso da tasa yana cewa
"I can't.. Till kin yi ihu kowa yaji.."

Jin abunda ya fad'a,ba tare da zuciyarta ta kawo mata tunanin komai ba ta kalleshi bayan ta murgud'a masa baki can k'asa ta ce
"Ai dai kasan zan iya yi..!"
Gira ya d'age mata shima yana cewa
"Yeah! I know u can,,buh try kiga abunda zai faru.."
Sam bata san me yake shiryawa ba,dan haka kawai sai ta b'are masa baki cike da shagwab'a za tayi ihu,cikin azama shima ya fizgota kana ya had'e bakinsu guri guda......




#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••
_Tun farko kafin na soma rubuta littafin nan na fad'a,littafina bai had'a alak'a da yak'i ko abun tsoro ba,dan nace *ALK'AWARIN JINI* ba yana nufin horror novel ba,it's a matter of *PROMISE* fa nasan wad'anda suke bin littafin sun san inda labarina ya nufa,saboda haka mutane na aci gaba da kaftawa..Allah ya barmin ku,ku jima kuyi k'arko,,ina matuk'ar k'aunar ku fisabilillah..!💗_


*22.*
_#Blood pledged❣_

Idonta ta waro waje tana kallonsa da matuk'ar mamaki ba tare data iya yin ko da tari ba,nd a hakan da suke a mak'ale da juna kowanne tunanin da ke damun kwakwalwarsa daban,,lower lip d'inta dake cikin bakinsa ya sake rik'ewa sosai,,a hankali ya shiga murzawa da lip's d'insa cikin wani irin birkitaccen salo yana kallon tsakiyar idanunta,saurin lumshe nata idanun tayi cikin yanayin mutuwar jiki,bcos a yanayin da suke ciki bata jin zata iya jurewa kallon k'wayar idanunsa,a lokaci guda kuma tana had'awa da sauke sanyayyar ajiyar zuciya,shirun da yaga tayi ba tare data yi k'ok'arin k'wacewa ba ko son hanashi yasa shi cikin nutsuwa ya fara socking nasu gently nd calmly kamar wanda ta cewa tana buk'ata,salon da yake tafiyar da su shi kansa a lokacin bai san ya iya shi ba sai a yanzun,a hankali yaci gaba da socking nasu kamar ya samu lollipop,,ganin yadda tun a kiss notice d'insa sun fara k'ok'arin kwancewa har yana neman wuce gona da iri ne yasa tayi saurin rik'e masa hannu tana marairaicewa kamar za tayi kuka,wanda sai a lokacin ya fahimci a inda yake da abunda yake k'ok'arin aikata wanda yasa shi dakatawa sannan ya raba bakinsu,a hankali ya maida kansa saman wuyanta yaci gaba da sauke wahalallun numfashi,sai daya tabbatar ya saisaita nutsuwarsa buh har lokacin bai daina twitching breathe ba ya fara mata magana cikin muryar rad'a
"My Lady..! Allow me to go.."
Saurin bud'e ido tayi wanda ke bayyanar da tsoro k'arara a saman fuskarta haka nan muryanta duk da cikin shagwab'a ne amma ana iya rarrabe tsoron dake cikinta,tana kallonsa ta furta
"Ina..!?"

"Lokaci yana tafiya..! Nd bana so mu samu sab'ani da Daddyna akan tafiya ta.."
Kai ta girgiza kawai ba tare data yi magana ba
"Kin amince na tafi..!?"
Nanma ta sake girgiza masa kai,a hankali ya saki numfashi sannan yasa hannu ya d'ago chin d'inta
"Thanks..Babe.! Zanyi kewarki.."
Sai ya d'ora mata peck a chicks,muryansa a k'asa yana kallon yanayin da fuskarta ta bayyanar mai cike da damuwa
"My Lady..! Do u have any problem with my trip..!?"
Girgiza kai tayi a hankali alamun babu,murmushi ya sake yi mata
"Ok..Shin kina da sak'on da zaki fad'a..!?"
Kai tsaye tace "A'a babu.."

"Toh..! Ni ina da shi..Kina son ji..?"

"Ehh!"

"Shi kenan..Ki kula min da kanki..!"
Runtse idanunta tayi saurin yi,dan yadda ta fara k'osawa da jin kalmar "Ki kulamin da kanki" a bakonsa sam tak'i k'arewa,ga shi ta rasa dalilin da yasa yake ta maimaitawar
"To ni kuma nace masa mene game da nawa amanar..??"
Bcos kalmar tasa tana tab'a mata zuciya a duk lokacin daya fad'eta,a hankali wasu irin pain tears suka gangaro mata sai tayi saurin kai hannu zata goge ya rigata,jin lallausan palms d'insa a fuskarta yasa ta sake lumshe ido hakan sai ya sake bawa sauran hawayen dake mak'ale damar zubowa saman kyakykyawar fuskarta
"Ohh..! Ya rabb! Ka ceci wannan bawa naka..!"
Yadda yayi furucin yasa ta saurin bud'e idanunta ta sauke su a kansa,one eyebrow ya d'age yana tambayarta a hankali ta girgiza masa kai,murmushin k'arfin hali yayi mata sannan ya mik'e while yana sake cewa da ita
"Please my Lady... Ina son ki kasance mai yawan tunawa *ALK'AWARI* na akanki,kamar yadda nayi miki *ALK'AWARI* ba zan tab'a barin damuwa ta wanzu a cikin zuciyar ki ba matuk'ar muna a tare da juna,kema ki kasance kamar haka,bcos ina fatan nan da wani d'an lokaci ki tabbatar da hakan,bayan kin zamo mata a gare ni,,,ke kad'ai zuciyata ta amincewa my Lady,,saboda na tabbatar dake ne kad'ai zan iya rayuwa...Ki kula min da kanki..Ina son ki sosai abar k'auna..!"
Sabon kuka taji yana son sake taho mata,nan da nan ta tsaya cak a inda take,dakatawa yayi shima yana kallonta cikin muryan tashin hankali yana fad'in
"What's happened..!?"

"Nothing..!"

"Kina so na yarda..!?"
Shiru tayi bata amsa ba,d'an matsowa yayi jikinta yana kallonta k'asa²
"Tell me..what's..!"

"To ka d'an matsa,,sai na fad'a maka.."

"I can't,,ki fad'a a haka.."
Girgiza kai tayi
"A'a bana iyawa. "

"Me yasa..?? Kusancin mune bakya so..?"
Shiru tayi dan da kunya ta iya fad'a masa haka d'in ne,d'an murmushi yayi mata
"A haka kike so muyi sallama..?? Na tafi bana farin ciki..??"
Saurin girgiza masa kai tayi
"Ok.. Good..Tunda haka kike buk'ata.."
Ja baya yayi kad'an daga inda take while yana fad'in
"Na matsa my lady.. Hope hakan yayi miki..!?"

"A'a..!"
Da mamaki ya kalleta,a zuciyarsa yanaa fad'i
"A'a.!? Kamar yaya kenan..Me take nufi da A'a..??"
A fili kuwa kallonta kad'ai yayi ya jinjina kai
"Shi kenan tunda hakan bai miki ba..Lemme go..Ina tunanin idan muka kasance bama tare zaki fi haka sakewa ko..!?"
Sunkuyar da kai tayi k'asa can k'asan mak'oshi ta furta
"Nifa ba haka nake nufi ba.."

"Uhhuumm..! Yimin bayani to yadda zan fahimta.."
Yadda tayi k'asa da kai ta kasa d'agowa bare ta amsa masa yasa shi sake maimaitawa
"Am waiting.. Kimin bayani tunda ba abunda kike nufi ba kenan..Yaya ne kike nufi..??"
Bata d'ago ba bare ta kalle shi,cikin sigar son ta b'atar da maganarsa ta ce
"Halla tawa'adhniy.! annaka izha yunhiy..raja'ata ilayya.."
(Ina so kayi min ALK'AWARI cewa idan ka kammala abunda ya kaika..Zaka dawo gare ni)
Murmushin da bai san ya taho masa ba ya sakar mata
"Wane irin *ALK'AWARI* ne kike so nayi miki..Wanda zai tabbatar miki da cewa zan dawo gare ki.. Bayan wanda nayi a baya..?"

*"ALK'AWARIN* da yafi kowanne..!"
Yana murmushi yake tambayarta
"Wane *ALK'AWARI* ne kike zaton zai fi kowanne a gurinki..??"
Jimm tayi tana tunani,sake tambaya yayi amma tayi shiru ta kasa cewa komai
"Ok..Let us construct the most bigest pledges.."
Kallonsa tayi da alamun tambaya a fuskarta
"Me kenan..!?"
Yana murmushi yake bata amsa
"U ask me to promised..Shi ne nake son cika miki burinki..Kafin na tafi..Hope zaki kasance cikin farin ciki a duk lokacin da kika tuna ni.."

"To amma.."

"Stop..lemme preceed.."
Bakinta taja ta b'ame tana ci gaba da kallonsa,rufe idanunsa yayi a hankali kamar mai jin bacci zuwa wani lokaci kuma ya furta
"Do u have a razor.!?"

"Ehh!.."
Ta bashi amsa kai tsaye Bcos bata san me zaiyi da shi ba daya tambaya
"Uhhuumm..! Can u help nd brought it for me..Please..!??"
Kallonsa ta d'anyi sannan ta mik'e tana niyyar fita,har taje bakin k'ofa yayi magana
"My lady.. And cup too..Please.!"
Ficewa tayi cikin sauri tana amsa masa,mintuna biyu da fitarta sai gata ta dawo,da sallama ta shigo d'akin tana b'oye hannunta a baya,murmushi ya sakar mata kafin ya mik'a mata hannnsa alamun ta bashi,sak'e dunk'ule hannu tayi tana kallon gefe
"To wai mene za kayi da su.??"

"Give it to me please,,koma mene zanyi yanzun zaki gani.."
Jikinta a sanyaye ta mik'a masa tana kallonsa,saboda ita dai jikinta yana bata lallai ne zai yi wani abu daban,sabuwa fil d'in razor data masa masa da k'aramin cup irin na cikin dinner set,ko daya karb'a idanunta na kansa har ya fara k'ok'arin fito da razor'n daga cikin shell,ko daya zaro a hankali taga ya bud'e palms d'insa na dama ya d'ora ta a kai yana saita hannun a kan cup d'in,,zuciyarta tsabar fargabar ganin abunda yake shirin aikatawa ji take kamar zata fito waje dan tsoro,cikin azama ta isa gabansa tun kafin ya kai ga yanka hannun tuni har ta rik'e shi idanunta suna fidda hawaye
"Mene ne wannan d'in kake shirin yi..??"

"Ohh! Babe ba wani abu bane zanyi,sake ki gani.."

"A'a.. Ni dai gaskiya ban yarda ba.."
Murmushi yayi mata yana fad'in
"Ok.. Naji *ALK'AWARIN* ne bakya so.. Ko har kin fasa..!?"

"To haka dama ake yin *ALK'AWARI..??* Ni ai ba wannan nace ina so ba,idai dan wannan ne ni kam na yafe.."

"Ni kuma kinga ina so ba,nd bana tunanin zan iya hak'uri na yafe.."
Marairaicewa tayi kamar za tayi masa kuka tana kallonsa
"Please..Ni dai na yafe,,kada kayi..Ka ji..?"
Murmushi yayi mata sannan ya janye hannunta data rik'e shi,yana kallonta fuskarsa d'auke da fara'a irin wacce kafin ta goge sai an d'auki lokaci,taga ya sake saita razor yana shirin yanka jikinsa,saurin rufe idonta tayi tana cije baki,tsakiyar tafin hannunsa yayi cutting kafin kace me tuni har jini ya fara fita,hannunsa ya zubawa ido yana murmushi kafin ya kamo hannunta yasa mata razor yana fad'in
"Ur turn my Lady..!"
A hankali ta bud'e ido tana kallonsa,irin kallon da yaga tana binsa da shi sam baiyi kama dana wanda zai iya yanka jikinsa ba,murmushi yayi mata can k'asa yana fad'in
"My Lady.! Ina son ki,ya kamata ki san cewa shi so da kike gani tamkar tab'o ne,adadin yadda ka yi tsalle ka fad'a a cikinsa adadin haka ne zai baka wahala a lokacin da ka tashi fitowa,,ina fatan mu rik'e juna da amana har abada.Tare da fatan d'orewar farin cikin mu.."
Rufe idonta ta sake yi a hankali tana matse rezar a hannunta d'aya,sam Hammad baiyi zaton zata iya yin hakan ba sai ganin jini kawai yayi yana d'igowa daga hannunta,cike da tsantsar mamakinta ya kamo hannunta,tafin hannun ya bud'e ya zare rezar dake ciki sannan ya had'e hannayensu guri guda,jinin dake tsatstsafowa ta cikin hannayen nasu yaci gaba d'iga cikin kofin a tare,ajiyar zuciya ta saki mai k'arfi cike da k'arfin hali ta bud'e baki duk da idanunta suna a kulle amma bata damu ba,bcoz burinta a lokacin shi ne ta iya fada masa abunda take ji game da shi
"A yau na shirya tsaf saboda ina son na k'ara bayyana maka matsayin ka a

Please Login or Register in order to submit comment