Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kamu.!"

"Uhhuumm..!" Suka ce daga haka kuma kowa yaja baki yayi shiru,kallonsu ta sake yi bayan ta saki murmushin basarwa sannan ta juyar da kanta gefe itama daga barin kallonsu,sarai ta fahimci abunda suke nufi buh bata so maganar yayi nisa ne shi yasa tayi cutting d'insa,bata so suji ace ta dalilinta mutanen da suka d'auketa matsayin y'ar uwa ita kuma ta saka musu da jin rashin dad'i ta hanyar nuna k'in ahalinsu a zahiri,bcos ta jima da sanin bata da ikon sarrafa zuciyarta,dukan wani motsi ko soyayyarta wa mutum d'aya kad'ai ta mallakasu,nd tana ji a jikinta har numfashin ta na k'arshe ya risketa baza ta k'ara iya yiwa wani halitta kwatankwacin son da take masa ba indai har a wannan gefen ne.
Har suka gama abunda ya kawo su gurin babu wanda ya sake magana a cikinsu,sun tashi tafiya kenan zasu biya adadin kud'in da aka musu bailing waiter d'in yake sanar musu an biya musu,fuskokinsu k'unshe da mamaki suka kalleshi zasu tambaya sai dai tuni har ya riga ya bar wajen suma d'in ganin babu wanda zai tsaya yayi musu bayani kawai sai suka fice a gurin suka kama hanyar komawa hostel.

*NIGERIA..*
Yinin ranar gaba d'aya ya tafiyar da shi wajen zagaye cikin location d'in da bai sani ba,nd duka ma kusan zai iya cewa babu wanda ya sani a gurin bare ya nemi rakiyarsa ko taimakonsa wajen gano inda suke zaune,,zuciyarsa cike da wani irin k'uncin da lokaci guda ya sakko ya mamaye ilahirin farin cikin daya tsinci kansa a ciki,bayan ya gama gararin sannan ya hak'ura ya juya akalar motar da niyyar komawa gida.

Da kyar ya dawo da kansa gida saboda matsanancin headache da yayi masa mugun kamu,,ko daya iso mayangu road d'in ma a nan bakin get ya tsaya ba tare daya iya shiga da motar ba ya nufi k'aramar k'ofar shiga gidan,a haraba ya iske drivern gidan,ko kallonsa bai iya yiba yace
"Kaje ka shigo min da mota."
Yana fad'ar maganar yana tafiya da kyar
"Sir.. Buh key fa.?"

"Idan ka duba zaka ganshi."
Kai tsaye ya wuce cikin parlor,lokacin daya shigo babu kowa a parlor'n,direct ya wuce bedroom,alwala ya fara d'aurawa a daddafe sannan ya kabbara sallah a nan cikin d'akin.

Mamma kuwa da duka tashinta a gurin ko mintuna sha biyar cikakku bata yi ba ta shiga ciki da niyyar yin sallah ta jiyo motsin dawowar motarsa,ita kanta a gaggaucen tayi addu'o'i bayan ta idar da sallar sannan ta nufo d'akin nasa,zuciyarta na sake sanar mata kawai ta fad'a masa idan yaso tun kafin Daddy ya iske shi suyi wacce za suyi da shi,, a kwance ta iske shi idanunsa a rufe yana facing sama,sai dai yadda ya d'ora hannunsa d'aya a saman forehead ya isa mutum ya tabbatar ba bacci yake yi ba,kusa da shi ta samawa kanta gurin zama bayan ta k'araso sai dai bata yi magana ba ta tsaya ne kawai don tana son karantar yanayinsa
"Baby..! Tashi ka zauna ina son muyi magana da kai yanzun..!"
Idanunsa ya bud'e kad'an cikin damuwa yace
"Mah.. Lallai ne sai Yanzun kuma..?"

"Ehh! Yanzun ne nake tunanin yafi na sanar maka.."
Had'iye yahun bak'in ciki yayi sannan ya tashi ya zauna buh ya jingina bayansa jikin pillow,,kallon sa tayi cikin tsanaki kamar yadda yake kallonta sai dai itan bata wani d'auki lokaci ba ta janye idanunta akansa,cike da sanyin jiki ita kanta ta fara masa magana
"I knew Hammad tun daga haihuwarka kai yaro ne mai tsananin biyayya,,nd ko wane irin magana muka zo maka da shi kana yin iya k'ok'arin ka kaga kafaranta mana cikin bin umarnin mu.. Amm..!"
Sai kuma ta d'an dakata kad'an tana tunanin abunda zata sake cewa next,tun data fara maganar yake jin gabansa na tsananta fad'uwa buh sam bai san mene ne alak'ar hakan da yake ji da kuma maganar Mamma'n nasa ba,d'agowa yayi kad'an ya sake kallonta,tun da tayi shiru har lokacin ta kasa ta sake cewa komai,cikin yanayin kwantarwa mutum hankali ya gyara zamansa bayan ya rik'o hannunta duka yana kallonta ya ce
"Mah.. Duka wad'annan abubuwan da kika riga kika sani ne akaina,so kada ki sama kanki damuwar komai,,ki fad'i duk abunda kike son cewa,i promised zan saurare shi ko da zuciyata bata so,barinma nasan bazaki tab'a yin abunda ni bana k'aunarsa ba.."
Kai ta rausayar gefe da alamun gasgata maganarsa,nd ta zame hannunta d'aya daga cikin nasa
"Kayi min *ALK'AWARI* habibiiy,, ko mene ne nace zaka yi min shi babu musu..!"
Haka nan tunda yaji ta furta kalmar *ALK'AWARI* gabansa yaci gaba da fad'uwa a kai² kuma zuciyarsa tana tsananta harbawa da sauri²,kansa kad'ai ya iya gyad'a mata cikin sanyi ya furta
"Mah..! No need nayi miki wani *ALK'AWARI* kin riga kin san waye dank'i,, so don't think lokaci guda zan canja daga yadda kika sanni,,ki fad'i duk abunda kike so,i knew my self,ko da *ALK'AWARI* ko babu u know zanyi duk abunda kike so matuk'ar kin sa ni yinsa.."
Chicks d'insa ta shafa da hunnunta wanda ta cire daga rik'on da yayi mata tun a farko
"Noo! Baby.. Nafi so ne ka tabbatar min ko mene ne zan fad'a baraka yi min musu ba.."
Zuwa yanzun kam jikinsa ya wuce ace yayi sanyi bcos yana jin matuk'ar bata yi gaggawa sanar da shi ba tofa gangar jikinsa tana gargarar mutuwa,haka dukkan kalaman da taje furtawa jinsu yake sukar zuciyarsa,a hakan ya daure bayan ya runtse idanunsa daga rad'ad'in da yake jin kwakwalwarsa nayi masa yace
"Shi kenan Mah.. Babu damuwa..! Ki fad'a kawai,in sha Allah zaki same ni mai biyayya akan dukkan maganar ki..!"

"Good..! Buh.!! Ina fatan ka rik'e maganar da muka yi da kai d'azun kafin ka fita..!?"
Kai ya gyad'a mata,itanma sai ta jinjina masa kai
"Idan har baka manta ba,nace maka Daddy'nku ya fara maganar aurenka ko..??"

"Ehh! Mah.. Kin sanar dani wannan maganar,,amma Mamma mene alak'ar wancan maganar da wannan ne..??"

"Uhhuumm..! Saboda dukansu abu guda suke nufi.."

"Kai.! Mamma to amma ni ai duka kinsa hankalina ya tashi ne,,nd nayi tunanin wani abu ne daban kike son sanar min."

"Hammad kenan,tabbas na yarda har yanzun kai yaro ne,,shi yasa gaba d'aya ka kasa fahimtar abunda nake son sanar da kai,,amma tunda baka fahimce niba,barin sanar da kai,kaga kenan sauran hukunci ya rage naka,,tunda dukkan wuk'a da nama yana hannunka sai yadda kaso za kayi da su."

"Yawwa Mah.. Tell me nasan labarin ki,ba mai haddasa damuwa bane.."
Yana d'an murmushi yayi maganar
"Hammad batun da nake son yi maka,bafa abun wasa bane,saboda haka ina son ka maida hankalinka jikin ka,,batune muke yinsa ni da kai akan aurenka.."

"I knew Mah,, shi yasa ai na fad'a nima,saboda nasan babu abunda ya had'a batun aure da damuwa.."

"Uhhuumm..! Shi kenan ai tunda haka ka d'auki batun,,amma kasan wace yarinya ce Daddy'n zai had'a ka aure da ita..??"
Fuskarsa da fara'a sosai yake kallon Mamma,har zai ce mata "Ehh" sai kuma kawai yaji bazai iyaba nan take ya sauya da fad'in
"Noo! Mah..!!"

"Ka gani ba,shi yasa ai na fad'a maka tun da farko ka cire batun wasa,muyi maganar serious amma kake ganin A'a,, to ba kowa bace face y'ar gidan amininsa *ALHAJI ISHAQ BUNAWA...!"*

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.."
Shine kad'ai abunda ke iya fita daga bakin Hammad a dai² wannan lokacin da dukkan damuwa ta lullub'e shi,banda wasu irin mahaukatan gumi da suka fara tsere a cikin jikinsa gaba d'aya a lokacin shi kansa babu lallai ya iya gane a duniyar da yake.....




#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••

*35.*
_#Confusion_

"Mah.! Me yasa Daddy zai yimin haka..?? Please ki fad'a min..? Har sau nawa ne Daddy zai dunga yanke min hukunci ba tare da yaji ra'ayi na ba..? Anya Mah.! Daddy yana yiwa rayuwata adalci..??"
Shiru Mamma tayi ta kasa magana saboda yanayin da taga ya shiga ba k'aramin so yayi ya tada mata hankali ba,totally he's out of control bare ta iya lallab'a shi ya saisaita kalamansa bcos sunyi kaishi da yawa
"Please.! Mah kiyi min magana,did he do..?? Wannan fa rashin adalci ne,me yasa sai ni kad'ai Dad zai yima haka..?? Duk dan ina iya hak'ura da abunda zuciyata ke so akan nasa,shi yasa anytime yayi ra'ayi sai ya murd'a min nawa tsarin..??"

"Ya isa haka Hammad,,ya kamata ace ka iya tauna lagazin bakinka,sannan ka san irin words d'in da bakinka zai furta akan mahaifinka,ko mene ne zai yi maka mahaifinka ne yana da right yayi maka koma mene ne.."

"Amma Mah saboda kawai yana matsayin mahaifina sai ya dunga yanke min hukunci kan rayuwata..?? Me yasa bazai yimin adalci ba.?"

"Hammad.! Idan baka maida nutsuwarka a jikinka ba zan nuna maka KUSKUREN da harshenka yake k'ok'arin yi yanzun.."
Murmushi ya saki irin wanda da gani kasan da kad'an yafi kuka ciwo
"Uhumm! Good. Mah.! Da kyau.! Saboda na fad'i gaskiya shi yasa zaki bi bayan Daddy..? Me yasa tun farko kika kasa fahimtar da Daddy wannan gaskiyar..?"
Kallonsa tayi tana girgiza kai dan tasan matuk'ar ta biye masa a irin wannan halin da yake ciki komai zai iya faruwa,shi yasa ta ga gara kawai tayi shirun coz zai fiye musu alkhairi,dariya ya saki mai sauti idanunsa na fitar da hawayen bak'in ciki
"Why Dad..!? Why.? I dunno why things suke tafiya min so hardly,,kullum rayuwata sai juyi yake kamar waina,da farko yak'i zuwa nema min aurenta,nd he says ban kai matsayin rik'e gida ba,,after ya sani tafiya karatu duk da bana so nayi hak'uri na tafi,next k'addara ta shiga tsakaninmu yeah! Wannan kam na yarda Ubangiji ya tsara faruwarsa buh saura kam Dad shi ne ya janyo min faruwarsu,still now kuma yana preparing yi min aure without na san da maganar sai da lokaci ya k'ure..?? Uhmmm! What a surprise things,,Mah mene ne kenan Dad zai yi a gaba.? I know kin san duk tsarin Dad a kaina.. Please Mah ki sanar da ni kawai."
Wani dariyar sake fashewa da shi kamar zararre,hawaye naci gaba da sauka a saman chicks d'insa
"Mah..! U know what.?? Tun yanzun gara fa ki sanarma da Dad bana son auren san nan da zai yi min.. If yak'i ya fasa kuma i must fleeing.."
Kallonsa ta tsaya yi fuskarta taf da damuwa
"Son.! Baka jin magana ko..?? Yaushe ka koyo fitsaran da zaka kalle ni kana min wad'annan maganganun ne..??"

"Mah..! Serious fa ki sanarma mijinki this time around ba zan tab'a yi masa biyayya akan abunda yake so ba,matuk'ar ya dage sai dai..!"
Lafiyayyen mari ta sauke masa a chicks d'insa na hagu,sai dai duk da hakan da tayi ko kad'an bai sa Hammad ya damu ba,saima dariya daya sake sawa kuma itama sam bai ji haushin abunda tayi masa ba,kallonta yaci gaba da yi da jajayen idanunsa da suka k'ank'ance yana shafa gurin data mare shi
"Thank u Mah.! Saboda na fad'i gaskiyar abunda yake raina shi yasa zaku tarun min kan abunda babu shi a zuciyata..? Shi kenan zan koma inda na fito tunda bakwa buk'atar zamana a kusa daku,buh kada kusa rai a kusa ko nesa zan yi muku biyayya kan wannan hukuncin,,ko da kuwa ace zaku nemi a d'aura min aure ne da thousands Ladies a rana guda,ku sani bazan tab'a son ko d'aya daga cikinsu ba,matuk'ar ba *ABUNDA RAINA KE SO* bane,zan hak'ura da yin auren gaba d'aya kowa ya huta.."
Yana gama fad'ar abunda duk yazo masa cikin kwakwalwarsa ya dire k'afafunsa daga saman bed d'in zuciyarsa na tafasa,direct inda ya ajiye muhimman kayansa daya zo dasu ya nufa yana zuwa ya tattara komai nasa cikin gaggawa,sannan ya sauya pyjamas d'in dake jikinsa da wani suit mai kalar red wine daya fitar a cikin closet d'insa,sai daya tabbatar ya gama komai sannan ya nufo inda take zaune shiru kamar wacce aka sassak'a,a hankali ya tsuguna gabanta yana d'ora hannayensa asaman laps d'inta
"Please Mah forgive me..! Duk abunda nayi miki ki yafe min,hakan bazai sake faruwa ba da izinin Allah.."
Dogon ajiyar zuciya taja,duk wannan abun da ake ita kam bata ma san ya tashi a kusa da ita ba,sai ganinsa tayi cikin shirin da ta kasa tuna yaushe yayi shi
"Son..! Mene ne haka..?? Ina kake shirin zuwa da wannan daren..??"
Kansa a k'asa without ya d'ago bare ya kalli fuskarta yaga irin yanayin da take ciki ya ce
"Zan koma inda na fito ne.. Bcos idan naci gaba da zama nan zuciyata zata iya samun damuwa.. Nd na baro aiki a gabana.."

"Ba yanzun ba son,,ka bari ko da zaka koma zuwa da safe sai ka tafi.."
Shiru yayi bai bata amsa ba,ya juyar da kansa gefe,can k'asan zuciyarsa shi kad'ai yasan abunda yake sak'awa
"Mah.! Ai idan kika ga ban koma a yau ba,sai dai idan na samo labarin inda suka koma ne,amma idan ba haka ba mene ne zai zaunar dani a inda ake fatan ganin rayuwata tazo k'arshe..??"

"Son.! Baka ce komai ba.. Naji kayi shiru..!"

"Allah ya kaimu Mah,, yau da gobe duka d'aya ne.."
Kansa ta shafa a hankali kafin ta ce
"Taso kazo muyi magana to tunda ka dawowa nutsuwarka.."
D'an kallonta yayi kad'an fuska babu wani alamun annuri,da farko kamar kada ya tashi bcoz ita kanta Mamma'n ya fara ganin laifinta akan maganar da take yi na umarni daddy akan san,ko me ya tuna kuma sai ya mik'e ya zauna a gefentan
"Baby..! Mene yasa baza ka bi maganar mahaifinka ba..?? Shin baka so kaima naka yaran da zaka samu nan gaba suyi maka biyayya..??"

"Noo.! Mah! Buh ya kamata ne ace Dad ya gane zamanin daya wuce yana da Bambanci da wanda muke ciki,,idan har ace da anyi auren dole yanzun fa..?? Ko mata fa an daina yi musu dole,bare ni da nake namiji,,ki fahimtar dashi Mah nima ina da nawa Zab'in,me zaisa ko wane lokaci sai shi ne zai zab'a min yadda zanyi..?? I have my own lifestyle fa."
Hannu tayi saurin d'aga masa alamun ya isa haka,shiru yayi yana ci gaba da binta da kallon mamaki
"Hammad.! I have already told u ya kamata kasan irin maganganun da zasu na fita a bakinka game da mahaifinka,amma baka ji ko..??"

"Sorry Mah.. Buh..!"

"Bana son jin komai daga bakinka yanzun,,maganar da nake yi maka ba wai cewa yayi na nemi shawarar kaba,,umarni ne ya bani,dan haka ko kana so ko baka so abunda ya tsara shi zai yi ba wai wanda kake so ba,,hope ka fahimce ni..??"

"Mah.. Me yasa ne to lallai sai ni kad'ai Dad zai yima irin wannan tsarin,me yasa ba zai gwada yima Bassam ba..? Gaskiya Mah am tired,, fisabilillah nayi masa biyayya fa,,ya kamata ya bari na zab'i abunda nake muradi bawai shi ya dage kan lallai sai shi ne zai zab'a min abokiyar zama ba,,nifa zan zauna da ita ba Dad ba.. Gaskiya Mah idan Dad ya takurani a wannan lokacin wollahi komai na iya faruwa..!"
Sabon mari ta k'ara sauke masa a chicks d'insa,dafe da gefen ya sake d'agowa yana kallonta cike da mamakinta
"Kada ka fad'a min zancen banza Hammad,, ko dan kaga ina binka ne yasa kake fad'ar duk abunda ranka yaso,dan kaga nayi maka shiru ko..?? To barin fad'a maka,ko kaji ko kada kaji,aure babu fashi,duk inda zaka shiga kaje kada ka fasa,,dan kawai kaga ina lallab'a ka,soyayya ba hauka bane da zaka nemi ka jani a k'asa,, kada Allah yasa ka yarda d'in ka tafi duk ma gidan uwar da za kaje mana wata tsiyar ce..??"

"Mah..! Yau kece kika sa hannu kika mare ni.?? Akan kawai nak'i amincewa da wannan maganar shi yasa kema zaki juya min baya.? Shi kenan Mah! saboda na fad'i gaskiyar abunda yake zuciyata sai kema ki ga laifina.? Me yasa ba zaku duba halin da zan iya shiga bane.? U know idan da ace bani da wacce zuciyata ke muradi zanyi hak'uri na karb'i zab'in ku,buh tunda na riga na shaida muku ina da wacce nake muradi ya kamata ace kunyi hak'uri,,shi kenan Mah,na fahimta.."
Saurin mik'ewa yayi daga inda yake cikin fushi zai bar wajen tayi saurin rik'o hannunsa
"Ko kad'an son ban so na d'ora hannuna akan kaba,kai ka sani aikata haka,nd saboda bani da yadda zanyi ne,dole tasa ni dakatar da kai daga KUSKUREN da kake k'ok'arin aikatawa,bani da wani zab'i sai nayi hakan,,ya kamata ka tausasa zuciyarka ka karb'i zab'in mahaifinka.."

"Me yasa ne Mah baza ku fahimci abunda zai iya faruwa ba..? Ko kuwa dan iyayenta sun kasance talakawa ne Daddy baya son alak'ata da ita..?? Ita kad'ai nake so,kuma da ita bake son k'are rayuwa.."

"Bana son ka aikata abunda zai janyo maka fushin ubangiji Hammad,,rashin bin umarnin mahaifinka zai iya haddasa maka shiga matsala,kayi k'ok'arin bud'e idanunka ka kalli gaskiya."
Murmushi yayi mai ciwo yana kallonta
"Shi kenan Mah,,buh *ALK'AWARIN* dana d'aukar musu fa,na kai shi ina.?? Ita,iyayenta da sauran relatives nata duka nayi musu alk'awarin zan dawo,idan ban koma ba,mene ne ubangiji zai yimin a matsayin hukunci..?? U know umarnin ubangiji ne cika ALK'AWARI,idan banyi k'ok'arin sauke nauyin da yake kaina ba ubangiji ma bazai kyale niba.."
Jinjina kai tayi cikin sanyin jiki ta ce
"Na sani Hammad,buh yaushe ne kayi musu ALK'AWARIN.?? Kasan dai Daddy'nku ba zai fasa abunda yayi niyya ba ko..??"
Kai ya jinjina mata ba tare da yayi magana ba
"Shi yasa nake so kayi hak'uri kaci gaba da yiwa mahaifinka biyayya,wata rana sai labari.."

"Uhhuumm.!" Yace k'asa² ba tare daya sake magana ba yaja bakinsa ya b'ame bcos yasan duk abunda zai fito a bakinsa a irin situation d'in da yake ciki ba zai yi dad'i ba,ganin haka yasa Mamma taci gaba da lallab'a shi sai dai tunda yayi shiru,bai ko sake d'aga kai ba,itama sai kawai tayi shirun,bayan sun shafe tsayin lokaci a hakan tayi masa sallama ta bar bedroom d'in,,tana fita a d'akin ya mik'e cikin sauri ya had'a nasa ya nasa ya ajiye gefe,after kamar awa guda da tafiyarta a lokacin wajen 11pm har ya wuce,yana gama tabbatarwa kansa babu yadda za'ayi ta dawo ya tattara ya kama hanyar barin gidan.
Daga gida direct airport ya nufa,cikin gaggawa yayi bucking night flight,a daren wajen 12am jirginsu ya d'aga zuwa U.S,tun daya fito daga gida gaba d'aya zuciyarsa ta kasa samun nutsuwa bcos maganar duka ya tsaye masa arai,gani yake kamar Daddy baya son farin cikinsa ne shi yasa yake masa irin wannan karan tsayen.Sama da awa goma sha uku suka d'auka cikin gajimare suna tafiya amma dai² da sau d'aya gyangyad'i bai kama shi ba bare yayi bacci,tsayin awannin idanunsa biyu sai dai yayi wani irin shiru,zuciyarsa cike da fargabar abunda zai iya faruwa,,a haka suka sauka a New York.

Tun daya bar garin,shirun da suka ji babu alamunsa yasa da daren Sultan yayi ta kiransa a waya amma duka ya kasa samunsa,tun suna d'aukan maganar daya fad'a wasa har dai abu ya fara neman zama serious,,ga shi yau tsayin kwana biyu kenan amma shiru kake ji babu shi babu labarinsa,sunyi jiran,sunyi kiran duka a banza coz amsa d'aya suke samu wayoyinsa a rufe suke,wannan dalilin yasa Sultan yanke shawaran ya kira gida Nigeria yaji ko yana can d'in kamar yadda ya fad'a musu,duk da sun d'auki maganar tasa a wasa.
Gama yanke shawaran yin hakan babu jimawa yana niyyar kira,kiran Daddy ya shigo wayar Sultan d'in cikin hanzari ya d'auka,bayan sun gaisa Daddy yake tambayarsa ko lafiya yaji wayoyin Hammad a rufe..? Sai daya saita nutsuwarsa shi kansa sannan ya yiwa Daddy bayanin abunda yake faruwa,cikin tsananin mamaki bayan sun gama maganar suka yi sallama.

A gida Nigeria kuwa lokacin da Daddy suka gama magana da Sultan line Hammad na nan k'asar ya kira amma sai ya ji shima d'in ana shaida masa a rufe,ya sake trying line da yake amfani da shi a U.S shima d'in same abunda yaji kenan,line Mamma ya kira ya ji ko gaskiya ne Hammad d'in yana nan,a lokacin fitowarta kenan babu jimawa tana sauri zata je office kiransa ya shigo mata,da sallama a bakinta ta d'auka bayan ya amsa mata ya d'ora da fad'in
"Yaushe Hammad ya zo k'asar..!?"
Amsa masa tayi da "jiya ya zo ranka ya dad'e.."

"Toh amma mene ne ya samu wayoyinsa duka suke a rufe..?? Ko kunyi magana da shi ne..!?"

"Ehh! Munyi magana daren jiyan,, sai dai yak'i saurarena,ban san yaya ne zanyi masa ba.."

"Haba Asiya,,wannan ai zancen banza ne kike yi,ta yaya ne zaki fad'a min wai yak'i saurarenki..?? Duk yadda za ayi ina so kiyi,bcos dole ne Hammad yaso abunda nake so.."

Gauron numfashi ta saki da fad'in
"Ni kam gaskiya Yallab'ai am tired, ta yaya zaku sani tsakiya kai kana fad'a min dole ya saurareka nd shi d'in ina fad'a yana gaya min bazai yi ba..?? Gaskiya nima k'ok'ari na ya gaza,wannan karon kam na kasa yin nasara,saboda haka ka neme shi kuyi maganar,bazan iya ba gaskiya.."

"Asiya ni kike fad'a ma baza ki iya ba..?? Kada Allah yasa ki iya d'in, aure ne babu fashi, ko HAMMAD na so ko baya so sai ya karb'i zab'in da nayi masa.."

"To shi kenan ai,,in dai wanna maganar ne,gaka nan ga kuma Hammad d'in, kuyi a tsakanin ku ni kam ba sai na sake shiga ba,zan zama y'ar kallo ne kawai a tsakaninku.. Amma gaskiya alhaji wannan lamarin yayi yawa,fisabilillahi ta yaya

Please Login or Register in order to submit comment