Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da jin haushi yana tamke fuska ba tare daya kalli inda Sultan d'in yake ba yace
"Mene ne kai kuma ka sawa mutane ido haka..?? Idan wani abu ka zo d'auka kayi sauri ka tafi mana ka tsaya kallon mutane kamar baka sansu ba.."
Murmusawa Sultan yayi a hankali ya shigo cikin kitchen d'in yana binsu duka da kallon mamaki
"Kai d'in mene ne kake yi a nan da wannan talatainin daren..??"
Bai kalle shi ba bare yasan dashi yake ya samu damar ba shi amsa,sai dai ya sassauta rik'on da yayi mata,saurin zamewa tayi itama ko da taga ya cikata da nufin guduwa,yayi saurin yin magana
"Ina ne zaki je kike sauri..!?"
Da ido ta masa alamar tafiya zata yi,girgiza mata kai yayi alamun ba yanzun ba,ta sake narke masa idanunta tana masa alamun ita dai zata tafi,nuna mata yayi bai aminceba idan kuma ta tafi shi da ita ne idan har ta bari suka had'u,kamar za tayi kuka ta hak'ura ta tsaya sai dai ta sunkuyar da kanta a k'asa tak'i yarda su sake had'a ido,hankalinsa ya mayar kan Sultan daya rasa gano mene ne takamaiman abunda yake nema yana cewa
"Wai kai da Allah malam mene ne kazo nema ne..!?"

"Abunda duk ya kawo ka nima shine ya kawo ni,kuma shi nake nema.."
Murmushi Hammad yayi yana tambayarsa
"Kasan me nake yi ne..??"

"Sai dai ka fad'awa wad'anda basu gani ba."
Still murmushin ya sake yi yana fad'in
"D'an sa ido.. Zo ka fice da Allah.."
Juyowa Sultan yayi yana sakin dariya mara sauti
"D'an sa ido ko..?? Wollahi ka janyowa kankama na fasa zuwa ko ina,sai dai duk abunda za'ayi ayi shi a kan idanuna.."
Harararsa Hammad yayi irin na kayi tsararo kaga wannan hark'allar,ba tare da yayi magana ba ya rik'o hannunta
"Wuce muje my Lady.. Ina tsammanin idan mun bashi guri zai rasa wad'anda zai sama idon ko..?"

"Ur Lady fa.!? Dama itace amaryar kake wani nok'ewa,sai cewa kake baka so,,ashe duk munafirci ne abun.."
A fusace ya waiwayo yana kallonsa,yanayin kallon da Hammad d'in yayi masa da sauri yasa shi dakatawa iya haka bai ci gaba da magana ba
"Uhhuumm.!" Shi ne kawai abunda ya fito daga bakinta lokacin da suke kallon-kallo wa juna,,dan ko da Sultan yayi maganar duk da bai karasa ba,kuma ko da ba'a fad'a mata ba a iya tunani da kaifin kwakwalwarta da Allah yayi mata,a mafi yawan lokuta tana iya fahimtar maganganun da aka fara ba tare da an k'arasa ba,bcos law take yi nd dole ne dama sai ta lak'anci irin wad'annan yaren idan ba haka ba tsaf sai a iya hallakar da rayuwarta ta wannan fuskar kuma a gabata ba tare data fahimta ba bare tasan abunda ake shiryawa,tana fad'in haka kai tsaye ba tare data jira ta k'ara ko minti guda ba tayi waje da saurinta tana had'awa da gudu²,,Hararar Sultan yayi sauri yi sannan ya bi bayanta da sauri,yana niyyar fitowa a kitchen d'in nan idanunsa suka hango masa Daddy yana sakkowa daga upstairs da alamun kamar zai fita ne zuwa masallaci,saurin komawa yayi da baya cikin tsananin jin haushin irin tab'argazar da Sultan d'in yayi masa duk da har lokacin bai gama tabbatarwa kansa dalilin tafiyar nata ba,amma yafi danganta hakan da ta fahimci abunda maganganun Sultan d'in suke nufi,,matsowa kusa da shi Sultan yayi yana dariya
"Dude..! Wai wace ce ita wannan d'in.??"
A fusace ya waiwayo ya kalleshi yana fad'in
"Tambaya kake..!? To ka jira idan na nemo sani akan wace ce ita sau na fad'a maka.."
Yadda ya d'auki d'umi yasa Sultan saurin fad'in
"Allah baka hak'uri,,amma me yayi zafi har kake tada jijiyoyin wuya haka..!?"
Kallonsa ya d'anyi na tsayin lokaci kafin a fusace ya fice daga kitchen d'in ya bashi guri,,kiran sallar da yaji an fara yi shi ya dakatar da shi daga niyyarsa ta son duba inda tabi,da sauri kai tsaye ko jiransu bai yiba ya nufi masjeed.

Lokacin da aka idar da sallah a masallaci a gaggauce ya dawo gida,yau ko zaman daya sabama bai iya jira yayi ba ya kamo hanya ya dawo,,tun daya shigo gidan yake ta dubawa ko zai ganta amma ina abu ya gagara duk inda zuciyarsa ta sak'a masa kaf ya duba bai ganta ba,plan d'in daya shiryama akan sai dai kawai a ganshi,wajen nemanta duk mutanen gidan sun gama ganinsa,,a parlor ya yanke shawaran zama,dan yasan nan ne kad'ai zai zauna yaga fitarta ko shigowarta matsawar tana cikin gidan,tun wajen k'arfe 6am da yayi zaune har 7am saura y'an mintuna ba tare daya motsa ba.Around 7:10am Daddy ya shigo gidan yana tafe yana addu'o'i da motsa yatsunsa dake nuna alamun yana yine da gab'b'ansa ba da wani abu ba,har ya gota inda yake zaune ya waiwayo cikin muryar zolaya yana fad'in
"Babanah..! Barka da hutawa.."
Waiwayowa Hammad yayi saurin yi while yana rage tsayinsa duk da a zaune yake yace
"Morning Dad..!"

"Ka tashi lafiya..? Ya hanya..?"

"Alhamdulillah..!"
Yace daga haka ya sunkuyar da kansa k'asa gudunma kada garin bincike Dad ya fahimci wani abu na daga damuwar da yake ciki,,murmushin jin dad'i Dad yayi har ya juya ya fara tafiya ya dakata yana cewa
"Hammad..! Ka sameni bedroom akwai maganar da nake so zamu yi da kai.."

"Toh" ya amsa sannan ya mik'e jikinsa a salub'e,sai daya bari Dad ya wuce zuwa bedroom d'in sannan ya biyo bayansa,yana tafe yana mitar Dad zai hanashi gano inda ta shige a ransa.

Tunda ta samu ta fice da gudu² bayan ta haura staircases d'in,tana fad'awa d'akinsu ko iya rufe k'ofar d'akin a hankaki bata yi ba saboda yadda kwakwalwarta ke tafarfasa,direct ta wuce toilet da kayan jikin nata da komai ba tare data tsaya cirewa ba ta shiga kwance kan shower ruwa ya fara sauka a jikinta
"Me yasa za kayi min haka..!?"
Shi ne kalmar daya fara zuwa bakinta cikin tsananin damuwa,dan har lokacin bata bar tuna maganar da Sultan ya fara fad'a ba,kenan hakan yana nufin ba bikin wani suka zo ba a gidan daya wuce nasa..? Wannan shi ne sakayyar da zai nuna mata..?? Hakan shine soyayyar da yake ik'irarin yana yi mata..? Bayan ta sgafe d'umbin shekaru tana jiransa,yanzun ace wannan shi ne tukuicinta..?? Lallai kuwa idan haka ne ta dad'e tana jahiltar kanta,tunda har tasa a ranta zai dawo gare ta,,ashe duk soyayyar ta bogi ce..?? Yake mata,bayan yasa ta rabu da duk masu zuwa gurinta ta hanyar shaida musu anyi mata miji a gida,,shi ne zai saka mata da wannan sakayyar..??
Hannayenta ta d'ago tana kallo zuwa jikinta daya gama rungumarta yanzun babu jimawa,duk wannan abun daya faru da ita dama ba itan yake so ba,romon baka kawai yake mata..??
Wani irin haske ta gani ya gilma a idanunta take ta fara k'ok'arin fad'uwa,taimakon da Allah yayi mata a lokacin tana daf da katangar toilet d'in,sai tayi saurin dafawa da duka hannayenta ta tsaya sosai,hawaye masu zafi suka fara tahowa da sauri²,,ta d'auki tsayin mintuna sama da sha biyar tana kuka a cikin toilet d'in ba tare data sassauta ba kafin tayi k'arfin halin yin addu'ah,bayan ta share hawayenta ta d'aura alwala sannan fito a lokacin idanunta har sun haura,,tana fitowa kai tsaye inda jakar kayanta take ta nufa bayan ta sauya kayan jikinta da doguwar riga sannan ta daidaita akan abun sallah,,tun tana sallah kafin ta idar dukansu d'aya bayan d'aya suka fara tashi suna k'ok'arin yin alwala.

Lokacin data idar kan kayanta ta koma,sai data tabbatar ta kimtsa komai nata sannan ta gyara jikinta,duka a lokacin ko bakwai bata k'arasa yi ba ta kallesu bayan taja luggage d'inta ta tsayar tana fad'in
"Toh..! Guys nifa ina tunanin zan wuce ne zuwa gida gaskiya cos idan naci gaba da zama zan iya samun matsala,,,jikina yau duka babu k'wari sosai,ina ji a jikina kamar akwai wani abu da yake daf da faruwa dani.. So gara na hanzarta isa gaban Innata koda mutuwa zanyi na tafi a gabanta,,buh idan Allah yasa wannan shi ne had'uwar mu na k'arshe ina fatan duka zaku yafe min.. Ni dai na yafe muku gaba d'aya.."
A sakarce duka suka bita da kallon mamaki,yadda take magana kamar mutumin dake bada wasiyya duka jikkunansu sai suja d'auki sanyi
"Princess..! Ki sanar damu dan Allah,, wani abu ya faru kike irin wannan maganar.!? Wollahi kinsa duka jikin mu yayi sanyi.. Please.!"
Kai ta kad'a musu a hankali tana sakin murmushin da kana kallo kasan bai kai zuci ba
"Ko kad'an babu abunda akayi,,haka nan naji jikina yana bani.. So please mu yafi juna,,ban sani ba ko zan kai jimawa ko bazan kai ba..!"
Saurin b'oye hawayenta tayi sai kawai ta juya da sauri zata fita,Badra da nata hawayen har sun fara sauka tace
"Princess please.! Dan Allah na rok'e ki kada ki tafi.. Wollahi bana son tafiyarki,,ki jira mu shirya sai mu tafi duka please.. Yanzun ko kince zaki tafi ma Mamma bazata bari ba,bcos zaki tadawa jama'ar gidanku hankali ne.. Ki bari mu shirya please sai mu tafi taren kinga dama haka muka tsara.."
Girgiza mata kai tayi a b'oye ta goge idanunta
"I can't wait anymore.. Tafiya ta shi ne masalaha,, Ku baza ku fahimci halin da nake ci ba,,kawai kuyi min fatan alkhairi,,na yi muku ALK'AWARI idan har na isa gida zan kira ku na fad'a muku duk yadda ake ciki da yardar Allah.."
Tuburewa suma suka yi akan lallai bazata tafi ba,yayin da itama ta kafe kai da fata akan sai ta bar gidan a kuna lokacin,duk iya yadda suka so su murd'a ta abu yaci tura sun kasa tsayar da ita,ganin lamarin na neman zama rikici yasa Badra kiran Mamma a waya ta shaida mata abunda ke faruwa,a gaggauce Mamma ta baro kitchen wajen masu yi musu hidima ta nufo d'akin Badran wanda tun da safiyar Allah har k'aramin tsunami ya fara tasowa,,tana shigowa duka suka yi gurinta suna fad'in
"Mamma dan Allah kisa baki ki hanata tafiya..please..!"
Kallonsu tayi duka tana tambayar
"Me kuka yi mata ne da yasa tace zata tafi da wannan safiyar da babu tabbacin wani gidanma sun tashi..?"
Gaba d'aya suka kaure da fad'in
"Wollahi Mamma babu laifinmu a ciki,,muma haka nan muka ji tace zata tafi.."

"A'a wollahi k'arya kuke,ku fad'a min wannan maganar na yarda.. Saboda Allah ina so ku duba girmansa ku sanar dani abunda ya faru,idan kuka b'oye min kun san baza ku b'oyewa ubangiji ba ko..??"
Rantse² suka mata akan basu sani ba,ganin haka yasa Mamma'n ta juya ga Sabina dake tsaye sunkuye da kai a k'asa tana fad'in
*"Y'ata.!* Ina so ki fad'amin gaskiyar abunda suka yi miki kike son tafiya,,kin ji..!?"

*"Mammah.!* Wollahi ni dai babu wanda yayi min komai,,haka nan ne naji ina son tafiya yanzun.."
Yadda ta kira sunanta da wani irin lafazi sai da yasa ta jin wani irin abu tun daga cikin kanta yabi ya sake tsirgawa ta cikin zuciyarta
"Kin tabbatar basu yi miki komai ba,,amma kike k'ok'arin tafiya..??"
Amsawa tayi da "Ehh babu" jinjina kai kawai Mamma tayi kafin ta juya zata bar wajen da fad'in
"Am sorry to say dear,,tunda babu komai ina so ki zauna dasu tunda sun nuna basu yarda ki tafin ba.. Ina tunanin hakan shine masalaha ko..?"
Saurin d'agowa tayi tana kallon bayan Mamma data kama hanyar fita ba tare data jira jin me zata ceba itan,,sannan ta dawo da kallonta kan su Jannat da suke ta ihun murna,ko kafin Mamma tayi wani k'wak'waran motsi a inda take tuni ta fashe da kuka mai tsanani,cikin kukan take cewa
"Wollahi ni bazan zauna ba,,sai na tafi gurin Innata da Babana..!"
Juyowa Mamma tayi saurin yi ta dawo inda take durk'ushe tana fad'in
"Subhanallah..! Ni Asiya me zan gani haka..?? Daga hanaki tafiya sai abu ya zama matsala..?? Allah ya baki hak'uri ya kuma huci zuciyarki.. Maza ke Badra kuyi maza ku shirya sai driver ya kaiku,,kunji ko..?"
Da girmamawa duka suka amsa jikinsu duk ya sake yin sanyi da lamarin k'awar tasu,ba tare da sun tsaya tunanin yin wanka bama saboda damuwar da take ciki duka suka nemi kayansu suka shirya,,suna gamawa a lokacin Mamma har ta jima da fita suma suka d'unguma suka fito,,sai data yi musu nasiha sosai lokacin da suka je yi mata sallama dukansu sannan tayiwa Sabina alkhairi da kyaututtuka masu girma,bayan sun sake yin sallama ta rako su har bakin mota,ba ita ta juya ba sai da taga fitarsa a gidan sannan ta koma ciki zuciyarta cike da jimanta al'amarin yarinyar a ranta.

Tun da suka shiga bedroom d'in Dad sai daya shafe tsayin awanni biyu suna maganganu wanda duka suka ta'allak'a akan batun aurensa,kafin ya fito daga d'akin,, Allah yaso ma Dad bai cika tambayarsa ba akan maganar dan yasan da yanzun yaji haushinsa,bcos hankalinsa duka a lokacin da Dad d'in yake maganar ko kad'an baya tare da shi,,shi yasa har Dad yayi ya gama baya tunanin akwai k'wararan kalmomi biyu daya rik'e a zancen.
Yana fitowa da k'aton wall clock ya fara katari wanda yake nuna masa 9:05am a lokacin,a gaggauce ya wuce zuwa bedroom d'insa ya sake kimtsawa,har lokacin duk da ya d'auki mintuna amma still Sultan da Sadeeq ko juyi basu yi ba tun da suka sake kwanciya bayan dawowarsu daga sallar asubah,wucewa yayi ya sake fita daga room d'in ba tare daya tashe su ba,,bedroom d'in Mamma ya nufa kai tsaye zuciyarsa cike taf da son yi mata albishir d'in yaga Tsuntsuwarsa.....


🥴🥴🥴 tofa wai Tsuntsuwa..


#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••

*39.*
_#Protests_

*Dad'i na da gobe saurin zuwa,,,dad'i na da fan's gajen hak'uri+ci da zuci.. Ammafa duk da hakan ana mugun tare ne..😘*

*Daga dukkan alamu dai na samu mataya,,sai dai ina son yin jan hakali ne ga masu min maganar kada na tsawaita labari,amma am sorry to say,,labari ni nake rubutawa nd nina tsara shi tun kafin yanzun,saboda haka na san mene ne zanyi a gaba,,ko da maganar da zan fad'a baza tayi muku dad'i ba,shi yasa tun a farko nace kuyi hak'uri da abunda zaku ji,,i knew sak'on da nake son isarwa idan har ban kai k'arshe ba za'a samu matsala,sai dai tun yanzun wasun ku suna cewa ai na isar da sak'on da nake son isarwa,ta yaya ne za'a ce sak'on da bai kammala ba ya isa..?? Idan an kawo matsala ba'a warwareta ba,me kenan aka yi.? Dole sai na ce na gama ko na ajiye alk'alami na,sannan ne zaku kira cewa sak'ona ya kammala,ku da kanku zuwa yanzun ya kamatama ace kun shaida,tunda har kuka ga nazo nan ku fara tabbatarwa kawunanku labari ya taho gangara,ba sai kuna min maganar na tak'aita ba,labarina bashi da alak'a da True Life bare kuce na ajiye shi haka nan,idan batun hutu ne kuke nema min,nima zanso ne ace yau na kammala na samu hutun,bcos nasan typing ba abune mai sauk'i ba nd research too,kullum mutum cikin tunani da bincike akan abunda zai rubuta yake,kunga kuwa dole bawa yaso ya huta,,saboda haka don Allah masu maganar ku tak'aita please n please,a tsarina bana son karatun summary shi yasa nima ban fara yinsa ba,duka idan kunyi hak'uri bana tunanin zamu kai ko da 80 pages,,saboda haka wad'anda suke bina suka ga kuma zasu iya ci gaba da tafiya tare da ni basu gaji ba,ku taho mu ci gaba da shatar burtali,wad'anda kuma suka ce zasu daina karantawa ko ma nace sun daina har suka fad'a naji kuma na gani ina godiya sosai 🙏,Allah saka da khairan sai mun had'u a gaba,buh nasan ko iya hakan kuka tsaya kamar yadda kuka ce babu komai dan kuwa kun amfana da wasu daga cikin darussan da nake son ku fahimta d'in,,so Alhamdulillah.! Sai dai kuma nace ba haka aka so ba,wai k'anin miji yafi mijin kyau,,a k'arshe ina k'ara yi muku fatan alkhairi gaba d'aya masoyana,ban cire kowa a cikin ku ba..Real Smasher tana gaida ku all..🙏*

💞

Lokacin daya shiga bedroom d'in Mamma da kiranta ya fara while yana dubawa ya gano ta inda zai ganota,sai dai har ya k'araci lek'ensa bai tarar da ita a ciki ba,fitowa yayi da sauri yayi hanyar downstairs kasancewar safiya yasan da wahala ace bata kitchen,sanda ya sakko ta cikin parlor ya ratso nan ma bai tarar da ita ba,kai tsaye ya wuce ya nufi kitchen cike da k'warin guiwar zai sameta a can,sai daya fara lek'awa duk dan saboda ya tabbatar tana nan d'in ko a'a saboda ya gama d'ora tsammaninsa akan tana nan d'in,amma sai ya iske sai hadiman gidan kawai a ciki,,juyawa yayi ransa a d'an b'ace ba tare da yayi magana ba,har ya kama hanya zai bar wajen kuma ya saks dawowa yana tambayarsu inda Mamma'n ta shiga,kiran da aka mata a waya da futarta da tace tana dawowa suka shaida masa,ko gama saurarensu bai yi ba ya juya da sauri ya bar gurin dan shi a yau d'in nan tunda Allah ya nuna masa ita bazai yi sanya ba sai sunyi maganarta da Mamma'n,kuma idan ta kama ma da labarin ya isa ga Dad duka shi dai zaiyi dan a san yadda za'a yi da shi kafin ayi masa sakiyar da babu ruwa.
Cikin parlor ya dawo ya zauna yana jiran ganin ta inda zata fito tunda duk inda yake tunanin samunta ya duba bata nan,a k'asan zuciyarsa yana k'issimawa duk tsayin lokacin da zata b'ata bazai gaji ba zai jira fitowarta,ba don komai ba sai don saboda Tsuntsuwarsa,ya tabbatar idan yayi sakaci a wannan karon ta sake tashi tofa baisan kuma a inda zai riskota ba.
Ak'alla ya d'auki tsayin lokaci zaune shiru shi kad'ai kafin yaga fitowar Mamma kuma daga saman dai itama ta sakko,fuskarsa d'auke da mamakin ganinta ta wannan hanyar yaci gaba da kallon tahowarta har ta k'arasa sakkowa,,hanyar kitchen yaga tayi,cikin sauri ya kauda tunanin da yake a zuciyarsa ta hanyar maye gurbin sa da fad'in
"Morning Mah.!"
Dakatawa tayi da tafiya cos gaba d'aya ma ita bata san yana zaunen ba saboda tunanin abunda ya faru d'azun tsakaninsu Badra da Sabina daya d'auke mata hankali
"Morning habibiiy.. Ka tashi lafiya ko..? Ya hanya.?"
Murmushin yak'e yayi da fad'in
"Alhamdulillah Mah..!"
Murmushin itama ta mayar masa da fad'in
"Ina zuwa ko..?"

"Toh Mah.. A fito lafiya."
Juyawa tayi har ta fara tafiya yaji ya kasa nutsuwa da sauri ya d'ago ya sake yin shiru yana tunanin me zaiyi wanda zai bashi mafitar da yake nema.? Ya sake kallon hanyar data bi a lokacin har ta kai bakin k'ofar shiga kitchen,da sauri bakinsa yana b'ari yace
"Mah..! Idan kin gama zanzo muyi magana.."
Dakatawa tayi a bakin k'ofar tace
"Shi kenan habibiiy.."
Tana fad'ar haka ta shige ta barshi zaune a parlor.

*After some hours..*
Tunda Mamma ta barshi zaune,yake kallon agogo,da yaji bazai iya zaman ba ya mik'e yayi sama,duk bayan mintuna sai ya fito ya duba ko ta fito,amma sai ya riski still tana cikin kitchen d'in,haka yayi ta safa da marwa tsakanin bedroom d'insa zuwa parlor,zuwa nata bedroom d'in amma sai ya tarar bata fito ba still,tun yana kallon agogo yana duba lokacin daya d'auka yana jira har abun ya kusan fara neman ya janyo masa damuwa,,ji yayi sam bazai iya ci gaba da jiranta ba,dan haka ko daya sauko a karo na k'arshe ya nufi kitchen d'in wajenta,aiki sosai ya tarar dasu suna yi,bayan ya d'an dakata a wajen a hankali ya furta
"Shi wannan aikin baya k'arewa kenan.. Ko kuma dai dan ina son magana da ita ne yasa nake ganin tsayin lokacin..?"
Katse zancen yayi da fad'in
"Mah.! Mintuna kad'an please..!"
Yana maganar yana rausayar da kai gefe
"Ok.. Muje gani nan fitowa.."
Kasa matsawa yayi a gurin har sai data ajiye abunda take yi,yana tsaye har ta wanke hannunta bayan ta tsane da mini towel sannan ta fito tana tafiya tana bada sallahu wa masu yi musu hidiman
"Ina dawowa yanzun.. Amma kuci gaba kafin na dawo d'in,, ai kunga yadda na gwada muku ko..?"
Suka amsa mata da "Ehh"
"To kuci gaban nima ina nan dawowa in sha Allah.."
Sai da yaga fitowarta sannan ya iya juyawa a tare suka jero da ita,ganin da Mamma tayi ya kama hanyar staircase yasa ta kalleshi tana fad'in
"Hammad..! Maganar bazai yiwu a nan bane da sai mun koma sama..?"
Kai ya girgiza mata alamun A'a,amma kuma sai cewa yayi
"Mah.! Zai fi mana zama secret ne,,bcos ban shiryawa kowa yasan mene ne zamu yi maganar akansa ba yanzun..!"
Jinjina kai tayi itama sannan taci gaba da binsa suka wuce saman,bedroom d'inta suka shiga,bayan ya zaunar da ita saman resting chair ya d'an tsaya kad'an da hannayensa nad'e a k'irjinsa yace
"Mah.. Ina son tambaya ne,akan su waye suka zo gidan nan..?"
Fuskarta k'unshe da fara'a tace
"Ga ku nan.! Mu ina muka ga wasu da zasu zo yanzun..?? Tunda ba'a fara biki ba,,ku kad'ai ne daga kai sai k'annenka kuka zo gidan nan.."
D'an rufe idanunsa yayi yana girgiza mata kai
"Noo Mah.! Ba wannan nake tambaya ba,bayan mu babu wasu da suka bak'unci gidan nan..?"
D'an jim tayi bata yi magana ba,alamun kamar tana son tuna fuskokin da suka shigo musu daga jiyan zuwa yanzun da yake magana
"Ki tuna Mah..!"

"Babu fa,,ku kad'ai ne kuka shigo.."

"A'a Mah..! Definitely akwai bakin fuskar da suka zo mana,,buh ya kamata ki tuna.."

"Ohh! Na fad'a maka fa babu,,sai dai kuma ban sani ba ko friends d'in k'annenka kake nufi,,nasan dai bayan ku da kuka yi zuwan k'arshe cikin gidan nan sai su,,after wannan ban san kuma wanne ne kake magana ba.."
Murmushi yayi kafin yace
"Do u know them Mah..??"
Kallon mamaki tayi masa tana cewa
"Ban gane azancin na sansu ba..? Su suwa kenan na sani..?"
Wani murmushin ya sake yi sannan

Please Login or Register in order to submit comment