Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yace
"Yeah! Ina son tambayar wani abune fa.."

"Ehh! Muna yawan gaisawa dasu tun suna U.S.."

"Wacce ce kika fi sani a ciki..??"
Kallon tuhuma Mamma ta fara masa bcos bata fahimci mene ne alak'ar tambayar da yake mata da kuma su kansu y'an matan da yake mata tambayoyin akansu ba
"Duka mana..?? Kana da matsala da sanin da nayi musu ne..?"

"Mah.! Can u help nd tell me..!"

"Nd tell u what.!?"
Ta fad'a da sauri tana binsa da kallon da yasa shi jin wani iri
"Mah..! Sunan su kawai nake son ki fad'a min.. Please."

"I can't..!"
Shine abunda bakin Mamma ya furta,wani irin fad'uwa gabansa yayi daya tuna idan fa Mamma tak'i bashi had'in kai shi kenan bazai samu nasarar da yake nema ba tsayin shekaru
"Please Mah.. Help me.!"
Had'e rai tayi tana kallonsa
"Bazan iya ba nace,,idan banda kai da abunka mene fa'idar shigo min da wannan maganar a dai² lokacin da hidindimu suka hau kanmu..?? Mene ne jin sunan su ko inda suka fito zai yi maka.? Ahh.!?"

"Ni dai Mah please,,kawai ki taimaka ki sanar da ni,,daga haka nayi miki ALK'AWARI sanar dake ko mene ne ya faru,,please..!"
Kanta ta kawar gefe nd fuskarta babu yabo bare fallasa tace
"Shi kenan,,d'aya HAFSAT ne sunanta,d'ayar kuma ZAINAB,shi kenan kaji yanzun..?? Na gama ko..!? To matsa min na wuce ni,kada kasa ni b'ata lokaci a nan ga aiki can yana jiran mu.."

"Wait Mah..!"

"Zaman mene ne zanyi maka ne a nan d'in Hammad..??"

"Mah..! Magana nefa za muyi,,kuma yana da matuk'ar muhimmanci ne a guri na,nd u too.!"
Saurin kallonsa tayi sai dai bata yi magana ba
"Nasan Mah baza ki manta labarin dana baki ba a baya can ba,,wanda cikin kwanakin da suka gabata ma munyi su a lokacin da nake U.S.."

"Uhhuumm..! Sai aka yi mene ne yanzun kuma..??"
Idanunsa ya matse da yatsu biyu kafin yace
"Mah..! Duka komai daya faru akanta nefa,,itace yarinyar da kika sa a nemo lokacin da kika hana ni zuwa..! Shi ne bayanin da nake son yi miki.."
Saurin mik'ewa Mamma tayi ta rik'o hannunsa,fuskarta cike taf da mamakin maganar
"Ita wa kenan..!? Yaya akayi kuma ya zama ita..?"

"Ohh! Mah..! HAFSAT d'in nake nufi."
Rik'e baki Mamma tayi fuskarta cike da mamakin faruwar al'amarin tace
"Are u sure..!?"

"Am very much sure Mah.. Ita ce wollahi.!"
Sai kuma yayi shiru yana neman gurin zama dan yadda yaji lokaci guda kamar wanda aka hankad'a yana neman fad'uwa,saurin rik'o shi Mamma tayi tana fad'in
"Bi a hankali Son.."
Murmusawa yayi irin na babu komai fa yana sake girgiza mata kai
"Nifa duk kasa na kasa fahimtar batun nan baby.. Ya kamata ka bani shi a bud'e,ta yadda zan fahimci komai..!"
Kamo hannunta yayi shima ya zaunar da ita a kusa da shi sannan,a hankali ya d'ora kansa a join shoulders d'inta ya fara mata summary d'in labarin,,,fuskar Mamma lokacin daya gama mata bayani tsantsar mamakin dake shimfid'e samanta har ya wuce wanda za'a misalta,haka nan tunda tayi shiru ta tafi tunanin da neman mafita,yadda tayi shima haka yayi sai dai tunaninsu ya bambanta,duk da shima d'in tunanin hanyar da zai bi ya b'ullowa lamarin ta b'angaren Dad ya hana zuciyarsa ta samu sukuni,,kallonta ya d'an sake yi bayan ya sauke ajiyar zuciya,har lokacin bata yi magana ba nd babuma alamun tana cikin hayyacinta bcos duka alamu sun gama nuna tunaninta ya tafi wani wajen,tsintar kansa yayi yana fad'in
"Mah.! I need ur help.. Can u.!"
Da sauri ta d'ago tana amsa masa
"Ina sauraronka Yarona.. Fad'i ko mene ne kake son cewa,,in sha Allah idan har baifi k'arfin ikona ba kuma zan iya nemo maka shi a duk inda yake,nayi *ALK'AWARI* zanyi iya k'ok'ari na naga na sama maka farin ciki.."

"Promise Mah..!?"

"Promised habibiiy.."

"Thank u Mah.. Buh ina Badra take yanzun..??"
Sai da tayi jimm sannan tace
"Sunje su raka HAFSAT gida.."

"What..!? Gida fa Mah..?? Ina kenan..!?"
Ya tambaya yana zaro ido
"Gidansu mana.. Akwai wani gidan da zasu bayan nasu..!?"
Dafe kai yayi cikin sauri ya mik'e ya kama hanyar fita a bedroom d'in,sai dai bai ko k'arasa bakin k'ofa ba Mamma ta dakatar da shi
"Ina ne zaka je kake sauri..? Bayan kasan bamu gama maganar ba shi ne zaka tafi..??"

"Am sorry Mah,, yanzun zan dawo,,buh Mah zan rok'i alfarmar wani abu."

"Fad'i ina saurarenka.."
Shiru yayi kamar bazai fad'a ba kuma sai cewa yayi
"Please Mah..! Dama ina son ne nace ki gwada yiwa Dad maganar ta.."

"A wannan lokacin Hammad..!?"

"Ehh! Mah,,tunda ya bada dama ina tunanin ai har yanzun lokaci bai k'ure ba ko..?"

"A'a ni kam ban sani ba,,buh zanyi masa in sha Allah.."

"Amma fa Mamma please kada ya wuce yau,,ina son nayi fighting ne akan right d'ina cikin tak'aitaccen lokaci,,hope zaki taimaka min nayi winning over My Dad..?"

Murmushi tayi masa wanda ya tabbatar masa da hundred percent tana tare da shi,da saurinsa sai ya juya yana fad'in
"Thank u Mah.. I love u.."

"Love u too habibiiy.."
Da gudu² ya fice daga d'akin zuwa nasa,wayoyinsa ya fara bincikar a inda ya barsu,nan a saman drawer ya gansu kamar yadda tun dare ya zubesu,d'auka yayi ya fara k'ok'arin kiran line Badra,,cikin seekonni da shigar kiran aka amsa,lokacin data d'auka ko gaisuwarta bai iya jira ya amsa ba yace
"Ina kike yanzun..!?"
Can daga gefenta ta amsa masa da fad'in
"Yaya bana gida nefa yanzun,mun d'an fita.."

"I knew ai.. Amsar tambayan da nayi kawai nake son ji.."

"Uhhuumm..! Ban san sunan unguwar ba Yah,,amma barin tambaya naji.."
Juyawa tayi dai² lokacin tana kallon Sabina dake kwance gefe tayi kicin² tace
"Friend.. Mene ne sunan unguwar nan please..??"
Bata d'ago ba ko ta kalleta ta bata amsa,yana jiyo sautinta a lokacin da tace itama bata sani ba,,sai yayi saurin fad'in
"Ba sai kin fad'a min abunda tace miki ba,just go nd ask someone.. Maza da sauri,,sannan ki turomin address da duk wani information d'in inda kuke,,yanzun da sauri kada ki b'atamin lokaci.."
A ladabce ta amsa masa da toh,sannan ta mik'e tsam ta fita daga d'akin,,d'akin Inna ta nufa,bayan tayi sallama Inna daga ciki ta amsa tana fad'in
"Shigo mana Bilkisu.."

"Toh! Inna."
Da zata shigama bayan ta d'age curtains sai data sake yin sallamar,amsawa Innar ta sake yi fuskarta da fara'a,tana shiga ta nemi guri ta zauna da fad'in
"Inna sannu da hutawa,,dama tambaya ne dani,na tambayi waccan matar tak'i fad'a min,,I dunno why tunda muka tashi da ita yau take wasu irin behaviours,wollahi duk mun kasa gane inda ta nufa.."

"Allah sarki,,aifa sai dai kuyi ta hak'uri da Maman nan tawa,wani lokaci wuyar sha'ani gareta,,to amma akan mene ne zaki yi tambayar ko Allah yasa na sani..!?"

"Amm! Dama Inna ba akan komai bane,sunan unguwar nan ne kawai nake son sani..!"
Murmushi Inna tayi kafin tace
"Sunan unguwar nan dai kamar yadda naji tun zuwanmu ana ce mata *KAWO* to amma da yake kamar akwai b'angarori ne dai ko mene ne dai ban sani ba,mu dai nan b'angaren da muke suna cewa *KAWON MAI GARI.."*
Tiryan² Inna ta rattafa mata bayanin duk abunda take son ji,godiya tayiwa Inna sannan mik'e da niyyar fita a d'akin dai² nan sai taga wayarta tayi haske,murmushi tayi saboda ta san duk yaji komai so ba sai tayi wahalar tura masa ba,sannan ta k'arasa fita ta koma gurinsu.

Yana kashe wayar shima shiri ya sake yi sosai,banda murmushi babu abunda yake ajiyewa karamar wanda aka yiwa kyakykyawan albishir,Sultan dake kwance tun shigowarsa yana kallon abunda yake da duk wayar da yayi ya jishi ya mik'e ya zauna yana tambayarsa
"Dude..! Ina zaka jene da wannan ranar..??"
Bai juyo ba bare ya kalleshi yace
"Ina ruwanka..?? Ko kuma dai ka aike nine da kake tuhuma ta.?"

"Allah baka hak'uri jarumi.. A dawo lafiya."
Bai sake kula shi ba yayi ficewarsa,,shoulders Sultan ya d'age da fad'in
"Idan tayi wari zamu ji ai.."
Sannan ya sauka akan bed d'in yana mik'a saboda har lokacin gajiya bata bar jikinsa ba,bayan ya gama mik'ar ya shige toilet da nufin yin wanka.

Lokacin daya fito bai iya tafiya ba,sai daya biya ta kitchen ya yiwa Mamma sallama,bayan tayi masa addu'ar fatan alkhairi da samun nasara sannan ya fita cikin sauri da farin ciki,,tiryan² yabi duk kwatancen da Inna ta bawa Badra,abu kamar wasa da tambaya da komai sai ganinsa yayi a line da Inna ta kwatanta d'in,sai abu guda daya kasa tantancewa,wato gidan daya b'ace masa dan bai san wanne ne ba a cikin gidajen,,line Badra ya sake kira tana d'auka tace
"Yah Hammad..!"
Ko gama fad'a bai jira tayi ba yace
"Da Allah ni fito waje na kasa gane gidan.."
Da mamaki a fuskarta tace
"Yah..! Zuwa kayi ne.!?"

"Ke bana son kinibibi,,da Allah fito da sauri kada ki b'atan rai.."
"Toh" tace masa,cikin sauri taja mayafinta tayi waje,,tana fitowa da motarsa ta fara arba ashema a k'ofar gidan yake tsaye,shima d'in yana ganin fitowarta ya saki ajiyar zuciya,followed by sauke glasses na side d'insa
"Ina ita k'awar taku..??"
Abunda ya fara tambaya kenan,a zaton Badra ko da yayi mata tambayar duka ta d'auka Mamma ta bashi labarin abunda ya faru,shi ne ya biyo ba'asin abunda ya janyo tahowar tasu da gaggawa,da hannu tayi masa nuni da gidan data fito
"Je ki kiramin ita,yanzun ku fito tare."

"Toh" ta sake cewa sannan ta juya ko k'arasowama inda yake bai bari tayi ba,,a yadda ta barsu shiru haka ta dawo ta riske su,tana shigowa ta tsaya daga bakin k'ofa fuskarta babu yabo kuma babu fallasa tace
"Wai ance ki zo..!"
A tare suka d'ago su duka ukun,ko da ganin idanunta akan Sabina sai duk suka d'auke kai suna dariya k'asa²
"Inji waye..!?"
Ta tambaya babu damuwar komai akan fuskarta
"Yah Hammad ke kiran ki.."

"Kije ki fad'a masa bazan zo ba..!"
Amsar ta matuk'ar bawa gaba d'ayansu mamaki,a tare suka kalli juna sannan suka kalleta
"Baza kije ba kuma princess..!?"
Jannat da Zee suka ambata lokaci guda,kallonsu tayi tana kad'a idanu ta sake maimaitawa
"Ehh! Haka nace bazan je ba..! Ko da wani abu..?"

"Uhhuumm.! Amma kin san wane ne shi d'in da zaki fad'i haka kice a sanar masa..?? Kin san kuma matsayinsa a gurin wacce kika bawa sak'on..??"

"Ko wane ne shi,,i don't care na fad'a nace bazan jeba.. Sai me..?"
Mamakinta sosai ya bayyana a saman duka fuskokinsu,,ba tare da Badra ta sake magana ba duk da taji haushin maganar da tayi tace ta fad'awa d'an uwanta haka ta juya kanta tsaye zata koma ta fad'a masa abunda tace d'in
"Please dear,,kada kije ki fad'a masa dan Allah.."
Cewar Zeeharis da Jannat,,a fusace ta juyo ta watso musu wani irin kallo da fad'in
"Ban gane kada na fad'a masa ba..? Munafurtarsa kuke so nayi kenan..??"

"A'a dear,,ki dai samu wani abu da zaki ce please,,amma wannan maganar tayi nauyi da yawa kinji..!?"
Murmushin takaici tayi sannan ta juya tana fad'in
"Banyi kama da munafukai ba dan haka babu abunda zai hana ni fad'a masa gaskiya.."
Kusan k'aro suka yi da Inna dake k'ok'arin shigowa ranta a had'e,da sauri Badra ta ja gefe tana fad'in
"Afuwaan Inna,, ban san kina tafe ba.."
Hannu Inna ta d'aga mata alamar tayi shiru ba sai ta k'arasa ba,,gana d'aya suka d'ago jin Badra ta ambaci sunan Inna,jifanta Inna ta fara yu da wasu irin mugayen kallo har na tsayin lokaci,wanda suka sa ta tilas ta sauke kanta k'asa.

Fitar Hammad daga gidan babu jimawa sosai Daddy ya shigo,,a lokacin tuni har su Mamma sun kammala aikin duk da suke,tana jin wucewarsa zuwa sama tabi bayansa,dan itama dai a yau d'in tafi son ayi duk wacce za'ayi tsakaninta da Daddy,acewarta wannan mulkin mallakar ya fara isarta haka nan,gara tayi maganin matsalar,,a bedroom d'insa ta iske shi yana cire babbar rigar dake jikinsa,ko data riski inda yake tsaye bayan ya amsa mata sallamar da tayi sai tace
"Barka da dawowa Yallab'ai.."
Yana murmushi ya amsa mata da
"Barka dai uwar gida.. Ya hidimomi..??"
Tunda yaga yanzun kamar ta sake akan farkon maganar auren na Hammad
"Alhamdulillah.. Yallab'ai ya hanya..??"

"Hanya kam mun barwa wad'anda suka fita yanzun.."
Sai suka yi musayar murmushi wa junansu,,bayan nan kuma ta taimaka masa ya rage kayan jikinsa,bata d'auko masa maganar a lokacin ba sai data bari ya samu nutsuwa nd ya huta gajiya,sannan ta kalle shi tana fad'in
"Yallab'ai.. Ni kam akwai maganar da nake so muyi da kai fa.."
Fuskarsa a sake bayan ya d'ago ya kalleta yace
"Uhhuumm.! Ina sauraronki ai.."
Itanma sai data d'an kalleshi a nutse ta karanci yanayin da yake ciki kafin tace
"Dama ina so ne muyi magana akan yarinyar nan da kwanakin baya Hammad ya fad'a maka yana sonta.!"
Wani lafiyayyen murmushi Daddy yayi mata sannan yace
"Wace yarinya kenan..? Ina tunanin wannan magannar ta mutu tun ba yanzun ba..??"

"A'a ba mutuwa tayi ba.! Tana nan a raye.."
Murmushi ya sake yi sannan yace
"Toh! Ina sauraronki.."
Gyara zama Mamma tayi ta bada duka nutsuwarta akan Dad sannan tace
"Batun nema masa aurenta nake yi.. Ina ganin tunda akwai sauran lokaci har yanzun me zai hana kamar yadda yace min yana so a had'a auren lokaci guda,sai ayi masa hakan..?"

"Dakata Asiya.. Wai wannan wane irin zance ne kike son yi ne..?? Kina so ki nuna min ni naje nemawa Hammad aure yanzun wai..?? Mata nawa kenan zai aura..??"

"Biyu..!"
Ta bashi amsa a tak'aice
"Biyu fa..?? To ko ni da nake mahaifinsa ban zauna da mata biyu ba sai Hammad da yake yaro.?? Ina zai kai mata biyu idan ba wauta ba da rashin tunani..?"

"Yallab'ai..! Nifa duka ba kan maganar zai iya ko bazai iya muke ba,all i want yanzun kawai shi ne amincewarka,,tunda shi ya nuna yana muradi mu mene ne namu a ciki idan har zai yi adalci Alhamdulillah..!"

"A'a Asiya,,ya kamata dai ki bar yimin wannan maganar.. Ke kina ganin ko da na amince ma misali akwai iyayen da zasu yarda su bashi aure a kwanaki uku kacal..?? Kiyi tunani mana.."

"K'warai baza'a rasa ba.."

"Toh ban amince ba,,kuma ba da yahuna za'a jeba,,in banda ke da abunki nawa Hammad d'in yake da zaki biye masa akan batun auren mata biyu,,ina ma laifin ace yanzun yayi auren idan an kwana biyu ya b'illo da batun k'arawar, amma lokaci guda yace mata biyu..?! Biyu fa².!"

"To wai Yallab'ai mene ne matsalar ne..??"

"Matsala kike tambaya ta..??"
Girgiza kai Mamma tayi tana fad'in
"Ehh! Matsalar da tasa kak'i amincewa nake nufi,,ni banga aibun auren bane,tunda shi ya nuna yana ra'ayi.."
Kallon baki da wayo Daddy yayi mata sannan yace
"Wato ke dai idan na fuskance ki,duk abunda yaron nan yace yana so shi kike k'ok'arin yi koh..? Kin fi so ko wane lokaci ki biye masa akan duk shirmen daya zo da shi.??"

"A'a Yallab'ai wannan fa ba shirme bane,,magana ce akan *SO* da kuma *BIYAYYA* tsakani da Allah idan ka kalli al'amuran yaron nan ko ba'a fad'a ba,kaima kasan yana tsananin girmama maganarmu,to mu akan mene ne baza mu kyautata masa ba..?? Tunda ka zab'a masa mata kace sai ya aureta ya hak'ura yabi ra'ayin ka yanzun da yace ga wata wacce yake so,ya kamata ace ko bai ce ka aura masa ita ba,kayi k'ok'arin yi masa hakan,dan gaba ya samu k'warin guiwar da ko motsi kayi baka ce masa yayi maka kaza ba,yayi hanzarin biya maka buk'atar ka,,tsakani fa da girman Allah.."
Kasak'e Daddy yayi yana kallonta har tayi shiru,hannayensa ya nad'e a k'irji ya zuba mata idanu sannan yace
"To naji.. Amma dai batun aure ni kam nace ba yanzun ba.."
Kallonsa Mamma tayi saurin yi da fad'in
"Ban gane ba yanzu ba da kake ta fad'a.. Idan ba yanzun ba sai yaushe kenan..??"

"Babu lokaci.. Ke nifa bari kiji ma k'arshen maganata,yarinyar nan da kuke maganarta,ko da zinare aka k'erata na haramtawa Hammad aurenta tunda har akanta ya nemi ya fara jayayya da ni..!"
A mamakance Mamma ta kalloshi
"Kace baka yarda ba..?? Sannan kace ka haramtawa Hammad aurenta..??"

"K'warai haka nace,kuma haka nake nufi.."

"Wollahi to bazai yiwu ba.. Saboda Allah don kawai wani ra'ayinka kace zaka hanawa yaro abunda yake so.. Idan kai baka da ra'ayin yin mata biyu,shi ka kashe masa muradinsa,,tsakani da Allah wannan maganar ai bama mai yiwuwa bace.."

"Kika ce bazai yiwu ba..?? Wato zaki yi jayayya da maganata kenan.."

"K'warai kuwa nima haka na fad'a.."

"Ai shi kenan sai mu zuba mu gani,,ni dai nace ban amince ba,,idan kuma kina ganin zaki yi masa auren ne bismillah,,kin zab'a masa,nima kuma na zab'a,zanga da yadda za'ayi mace taje neman aure,dan ni dai babu k'afata a ciki..."

"Ehh! Sai kasa ido ai,,wani abune dan baka jeba..?? Ni zanje kuma zan nemawa Hammad aurenta tunda har ita yake so,,in Allah ya yarda zaka sha mamaki..!"



*K'ak'a k'ara k'ak'a... Ga kura ga kuma zaki,,maga wanda zaiyi nasara..*😱




#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••

*40.*
_#A family warfare_

*Godiya da jinjina mara iyaka ga Masoyan gaskiya,,hak'ik'a sak'onninku sun riske ni,nd am happy da duk abunda kuka fad'a,hakan da kuka nuna ya sake tabbatar min da k'aunar ku a gareni ba abun wasa bace,na gode³ sosai ubangiji ya k'ara dank'on love.. Real Smasher tana ji da ku,kuma tace kuji dad'in ku.. A ki wane lokaci da yardar rabb zata ci gaba da antayo muku posting,kuna shek'ewa..#Masoyan k'warai.❤*

*MUHAMMAD – FIRST 2 LETTERS=HAMMAD*
*Na d'anyi muku wani gyara ne,saboda masu cewa Hamma su gane bambancin dake ciki.. Hope u get it.😉*

💗

Ran Inna idan yayi dubu ya gama b'aci dan tunda suka fara magana tana jinsu,kuma duka maganganunsu akan kunnenta aka yi a lokacin tana fitowa daga bayan gida,gaba d'aya a cikinsu babu wanda yayi zaton ta fito shi yasa ma suka ci gaba da maganar basu saurara ba,abunda kawai zasu d'orar shi ne sun ganta ta shigo d'akin,sannan ita kanta Sabinar lokacin da take maganar bata yi tunanin za'a samu matsala ba shi yasa,lokacin da Inna ta shigo d'akin tana kallonta take ta sha jinin jikinta musamman kuma da taga irin kallon da take mata sai duk yasa jikinta yayi sanyi,da sauri ta mik'e ta zauna tana sunkuyar da kai k'asa bcos ba zata iya jurar kallon Innar ba,,sai da Inna ta sake jifanta da mugayen kallo kafin ta kalli inda Badra ke tsaye da sunkuyayyen kai tana kallon k'asa
"Bilkisu..! Wane ne yake kiranta ne ta bada wannan sak'on a fad'a masa..??"
Jimm Badra tayi ta kasa bata amsa har sai da Innar ta maimaita mata tambayar
"Yayana ne Inna..!"
Ta bata amsa kanta har lokacin a k'asa,juyawa Inna tayi a fusace ta kalli inda take zaune
"Ke yanzun dan baki da mutunci,,ko dai ace baki ji kunyar fad'ar maganar ba,ai kyaji kunyar ita wacce kika bawa sak'on,,idan ba rashin mutunci bama da iskanci har a aiko kiranki kice bakya zuwa..?? Zaman me zaki yi mana a nan d'in..? Ni dai kam *MAIRAMU* wollahi ban san ina kika aro wad'annan sababbin halayen ba,ace mutum shi kenan shi halayensa a murd'e..? To wollahi kiji ki kuma k'ara ji,ba dani zaki yi irin wannan halin rashin mutuncin ba,tun muna shaidar juna ma dake,sahunki a likaffa ki tashi ki fice kafin na b'atar miki.."
Sai da Inna tayi mata tatas a gabansu kafin ta juya a fusace ta fice,,a hankali hawayen bak'in cikin fad'an da Inna tayi mata a kan idanunsu suka gangaro mata,iya tsayin tasowarta yau rana ta farko Inna ta bud'e wuta ta mata fad'a,a hakan ma kuma ba'a barta taji da haushin fad'an da akayi matan ba,sai da aka k'ara da bata takaicin yi mata a gaban k'awayenta,ita wannan abu dame yayi kama.? Ace a rasa inda za'a mata fad'a sai a tsakiyar k'awaye. Hawaye ta ci gaba da zubarwa tana jan zuciya babu sassauci,,gaba d'aya daga su Jannat dake zaune kusa da ita har Badra dake tsaye sai da lamarinta ya basu matuk'ar mamaki dan dai su basu ga abun da za'a ce tayi masa kuka ba a wannan y'ar maganar da Innar tayi,,shiru² da Inna ta gani bata da niyyar fitowa yasa ta rafka mata kira followed by fad'an zata zo ta fita ko sai ta taso,tsananin haushi gami da takaicin takurata ta fita yasa ta mik'e a fusace ta fizgo k'aton hijab d'inta dake gefen katifarta tayi waje ko takan Badra dake tsaye tana jiranta bata bi ba tayi wucewarta,,cike da mamakinta da har lokacin bai barsu ba Zee data dawo da idanunta daga rakiyar da tayi mata tace
"Allah ya kyauta.."
Jannat dake gefenta ta amshe da
"Ameen dai y'ar uwa."


Please Login or Register in order to submit comment