Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne zaka takura yaron nan akan zab'in ka,ba zaka tambaye shi ba ko yana da wacce yake so,shi kenan ko wane lokaci sai abunda kake so ne za'ayi..? Sai kace saukar wahayi.."

"Asiya ki saurara min da wad'annan maganganun naki,,kada ki fusata ni,,umarni na bayar kuma dole ne ayi min biyayya akan dukkan abunda nake so.. Kinji na fad'a miki,ba wai Hammad kawai ba akan kowa naso yanke hukunci haka zanyi.."

"Shi kenan ai,,Allah ya bada sa'a,, kuma ni kaina na fahimta,kanka kad'ai kake so,dole Hammad ya fad'a dan kuwa baka yi masa adalci wollahi,yaron nan yana yi maka biyayya iya kar iyawarsa,amma yau har ta kai kasa shi fad'in maganar da bai dace ajita daga bakinsa ba,,ya kamata ka sauya shawara gaskiya..!"

"Ni kike fad'awa magana Asiya..?? Da kyau kinji ba,,yayi miki kyau.."
K'it ya kashe wayar yana furzar da zazzafar iska, zuciyarsa banda tiriri babu abunda take yi bcos kalaman Mamma sun k'ona shi da yawa.

Itama Mamma a nata gefen wahalallen ajiyar zuciya ta sauke,a hankali kuma ta tab'e baki sannan ta shige mota ko gaisuwar da ma'aikatan gidan suke mata bata iya amsawa ba,tasa driver yaja suka bar gidan.Tafiya suke amma gaba d'aya hankalinta yana kan maganganun da suka gama da Daddy,cikin zuciyarta zuciyarta sai sak'awa da kwancewa take kan lamuran Daddy,tabbas ko ita zata shaida da maganar Hammad Daddy'nsu ya cika son kansa da yawa,idan ba haka ba wane dalili ne zaisa ya dage akan zab'awa Hammad d'in matar da shi zai zauna da ita ba shiba..? Har sun sauka daga kan mayangu road sun d'auki hanyar state road zuciyarta ta kasa nutsuwa a fili ta furta
"Idan nayi maka haka yaro na banyi maka adalci ba,,tabbas ba tun yanzun ba ka fad'a min kana da wacce kake so.? Shin me zaisa ne ma Daddy'nka yace sai shi zai zab'a maka mata..?? Ya zama dole nayi wani abu idan ba haka ba lallai ne na tabbata wacce take son kanta da yawa.."
Lokaci guda ciwon Hammad da bayanin likita a wancan lokacin ya sake dawo mata,da sauri ta ce
"Tsayar da mota..!"
Saurin taka brake driver yayi yana fad'in
"Hajiya..!"
Ko kafin ya fad'i abunda yake ransa tuni ta riga shi
"Maza mu koma gida da sauri.."

"Hajiya gurin aikin fa..??"

"Cewa nayi ka maida ni gida.. Na fasa zuwa."
Cikin girmamawa ya amsa sannan ya juya kan mota suka kama hanyar gida,,suna isowa bayan ta shiga ciki direct d'akin Hammad ta nufa a gurguje, ko knocking bata yi ba saboda yadda gabanta yake tsananta fad'uwa da sauri ta tura k'ofar d'akin,yadda tayi tunanin haka ce ta faru sai dai bata kula ba tun farko,a hankali taci gaba da dubawa amma shiru babu ko alamar yana nan,fitowa tayi ta tambaya ko ya fita ne,gaba d'aya ma'aikatan gidan suka tabbatar mata da basu ga fitarsa ba,duk yadda Mamma take tunanin al'amarin sai ya nemi shallake tunaninta.Line Dad tayi k'ok'arin kira amma wani abun mamaki yak'i amsawa,sai daya masa miss call ak'alla sama da goma a lokaci guda sai dai ko guda bai d'auka ba,bare tasa ran zata ji magana mai dad'i daga gare shi,bisa dole ta sawa ranta hak'uri ta daina kiransa bcos bata da yadda zata yi masa.

Wasa² al'amari ya tsananta,tsakanin Mamma da Daddy an daina zaman dad'i duka akan tayi magana akan ta gaji itama bazata iya ba,tun daga ranar gaba d'aya sai kawai ya share ta bama ita kad'ai ba duka gidan yak'i kiran kowa kuma yak'i zuwa garin,shi kansa Hammad a bangarensa bai sake bi takan saba,dan ma kada suyi tunanin ya hak'ura ne da maganar,shi yasa har aka shafe tsayin satittika bai kuma tuntub'ar kowa cikinsu ba.
Ita kanta Mamma a nata b'angaren zuwa wannan lokacin gaba d'aya ta gama tabbatarwa zuciyarta ya hak'ura ya janye k'udurin nasa ne,amma abun mamakin cikin satin sai ga labari ya isketa next month auren,,cikin gaggawa ta kira line Daddy wanda har ta manta rabon da suyi waya ma,bayan ya d'auka sun gaisa duk da a sharce yake amsa mata tace
"Yallab'ai.! Wai mene ne kake k'ok'arin yi ne.?? I thought ka hak'ura da wannan batun tun ba yanzun ba,na rigafa na sanar maka Hammad yana da wacce yake so..!"
Banza ya mata bai bata amsa ba,jin haka yasa ta fad'in
"Hello..! Yallab'ai.!"

"Ina saurarenki Asiya..!"

"Uhhuumm..! Naji kayi shiru ne baka ce komai ba..!"
Murmushi yayi yana fad'in
"Me kike so nace ne Asiya..?? Nace na janye ko kuwa me kike nufi.!?"
Shiru Mamma tayi bata amsa ba,bcos maganarsa ya tabbatar mata da bai janye ba d'in,a hankali ta saki ajiyar zuciya tana fad'in
"Shi kenan Yallab'ai,, amma dai ina son ka kasance mai duba matsalolin wad'anda Allah ya d'ora alhakin kula dasu a hannunka,idan kana ganin ka kyautatawa wasu mu da muke makusantanka ka munana mana,Allah fa bazai bar hak'k'in mu akanka ba,,ka tuna da cewa Ubangiji (S.A.W) da kansa ya kyamaci zalunci sannan ya saka shi a tsananinmu a bun haramtawa,ina so kafin ka yanke hukunci kayi tunanin halin da za'a shiga,idan har ka takura shi akan abunda baya so to ina son shaida maka ka tsammanta ganin abunda baka yi tunanin faruwarsa ba a gaba..."
Tana gama fad'ar abunda take so itama bata jira taji me zai fad'a ba ta kashe wayarta,,ga Daddy kuwa tana kashewa baki bud'e yabi wayar da kallo,tabbas yasan gaskiya ta fad'a to amma idan har ya yarda yace zai janye lokaci guda,kai tsaye sai ya fito yace da aminin nasa ya janye batun auren daya nemawa Hammad d'in..?? Kai ina,ko kad'an bazai iya aikata haka ba,dole dai yayi wani abu akan matsalar,har yayi shiru kuma wani tunanin ya fad'o masa
Lallai ne ya kamata yayi wani abu akan wannan matsalar,,to amma tunda haka nema mai zai sa bazai jarraba yaga idan har da gaske ne akwai wacce Hammad d'in yake so ba,idan yaso sai ya sanar dashi ya amince,sannan ya sashi gabatar dasu gurin iyayenta kawai,idan yaso dai² lokacin da yayi niyya sai ayi komai a gama bcos ya gama shaidawa makusantansa nan da 1 month auren Hammad d'in,saboda haka ne baya son a sab'a daga yadda ya tsara,,idan kuma har aka samu sab'ani daga hakan ko yaya yake shi kenan sai kawai ya soke uzurinsu a gurinsa,kunga kenan faruwar hakan dole dai yasa abi nasa,ko ana so ko ba'a so,tunda har ya bada dama dole dai ayi hak'uri a karb'i hukuncinsa.
Murmushi yayi lokacin da wannan shawaran yazo masa,yana gama yanke hukuncin kai tsaye sai ya fara k'ok'arin kiran Hammad cike da son yi masa albishir.



#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••
_The gift u gave me was more than perfect in each and every way.Thank u so much for it *MY FENERH.* I will always preserve and keep it with me forever..Thank u once again *MATAR SOJA.❤*_

*36.*
_#His marriage plannings_

*NEW YORK CITY..*
Wani irin lafiyayyen sanyi ne daya gauraye da k'amshin dad'ad'an turaruka masu sanyaya ruhi suke tashi a cikin office d'in,ko ina ka kalla a tsaftace yake kamar ka yarda abu a gurin ka ci saboda yadda komai yake a zaune a muhallinsa,ko kad'an sanyin baiyi yawa ba bare ace zai cutar da ruhii,,cikin wani irin yanayi mai saukar da kasala k'amshin daya cakud'e da sanyin AC yake ci gaba da tashi d'auke da wasu irin yanayi daban² wanda su kad'ai ma sun isa su sanyayawa mutum zuciya tare da haifar masa da nutsuwa mai tattare da kwanciyar hankali,,yana zaune a saman had'ad'd'e kuma makeken table d'in dake cikin katafaren office d'in yana ta aikin binciken file's da aka shigo masa da su babu jimawa,,a zahirin gaskiya duk wanda ya kalleshi tabbas zai yi masa kallon mutumin dake cikin nutsuwarsa,,sai dai ko kad'an idan da zaka bincika zuciyarsa ba haka abun yake ba,musamman idan ace shi da kansa zai tono maka k'asan ransa,wansa babu komai cikinsa face tunanuka da damuwoyi da suka taru suka yi masa jingim,,yayi zurfi cikin aikin da yake kan yi kiran Daddy ya shigo masa,da wani irin mutuwar jiki da yake fama da shi tun bayan dawowarsa daga 9ja ya d'ago kyawawan idanunsa ya zuba su akan fuskar wayar,kallo d'aya ya yiwa wayar da sunan da yake lilo akai gabansa yayi wani irin mummunan fad'uwa,kamar wanda bazai amsa kiran ba tunda ya fahimci Daddy'nsa ne nd yasan kuma dalilin da zaisa Dad d'in kiransa,kawai sai ya share yaci gaba da kallon fuskar wayar,daf da kiran yana shirin katsewa wata zuciyar tace masa
"Kada yayi haka Hammad,ko dai ace babu komai Daddy mahaifinka ne,duk abunda zai maka bai cancanci wannan wulak'ancin ba,kai d'in kana da ilimi bai kamata kayi aiki irin na jahilan mutane ba,,kawai ka d'auka kaji mene ne yake faruwa da har ya sashi kiran naka.."
Dakatawa yayi saurin yi da aikin da yake yayi answering call d'in,bakinsa k'unshe da cikakkiyar sallama.Muryan daddy kamar ba shi ba jin Hammad d'in ya d'auka kiran,bayan sun gaisa cikin hikima Daddy'n yayi ta d'an jansa da wasa,dole ba don ya shirya ba ya d'an saki jiki kad'an sai dai bai zarme ba,,a mafi yawan lokuta musamman irin wannan lokacin da yake cikin danuwa sosai al'amuran Daddy suke d'aure masa kai,sai dai duk da hakan ko kad'an baya tab'a nunawa,kuma hakan baya tab'a hana masa sakin jikinsa suyi magana ko wane iri ne duk da yadda yake tsananin jin haushin Dad d'in nasa musamman a yanzun da yake nuna son kansa.
"Hammad! Duka na samu labarin abubuwan da suka gabata.. Saboda haka nema na yanke shawaran sanar da kai wani daddad'an albishir,,ina fatan kuma kaima zai faranta maka..!"
Cije lip d'insa yayi kad'an zuciyarsa cike da bak'in ciki,a hankali ya maida idanunsa ya lumshe yana jin saukar wani abu kamar ruwa a cikin zuciyarsa,shi kam in dai ba k'addara ba ta ubangiji ya tabbata babubwani lokaci da rana zata fito ta gabas ta fad'i a yamma Daddy ya kira shi ya masa wani albishir,kuma a hakan ma wai har yana ik'irarin mai dad'i,,how comes Daddy zai bashi irin wannan albishir d'in..? Yaushe ne hakan zai faru..? Da wane lokaci.? Wata zuciyar ce tayi saurin bashi amsa da
"Maybe a mafarkin ka daka saba yine hakan zai kasance."
Murmushi yayi mai ciwo tunawa da abubuwan da suka faru cikin satittikan da suka gabata,dama na can baya da suka faru a cikin rayuwarsa.Haka kawai sai yake jin zuciyarsa babu dad'i duk da dama ba'a cikin jin dad'in take ba,tabbas yayi abunda bai kamata ba a baya,duk abubuwan daya aikata da maganganun da ya fad'awa Mamma ko kad'an basu dace ace shine yayi su ba,kenan ba don Allah ya rufa asiri ba,Mamma'n bata tsaya biye masa ba mene ne kenan zai faru.? Sake matse idanunsa yayi while hannunsa a saman forehead d'insa yana murzawa a hankali² saboda ciwon da yake ji yaba shigarsa
"Hope kana sauraren abunda nake cewa Hammad..!"
A d'an firgice yayi saurin bud'e idanunsa da damuwa tasa su k'ank'ancewa
"Ehh! Dad ina saurarenka.."
Ya amsawa Dad d'in murya a shak'e
"Good.! D'azun munyi magana da Mamma'nka ne sai take sanar da ni wata magana,to shine nake son yin confirming,,kuma kaima ina son ka fad'a min gaskiya,shin da gaske ne akwai wata wacce kake so...?"
A bazata yaji kalaman Dad sun zo masa,cikin sauri ya gyara zamansa yana sake rarumo wayar ya rik'e ta sosai a kunnensa
"Haka ne Dad..!"
Sai da Daddy yayi jim sannan ya amsa masa
"To da kyau..!"
Shiru Dad ya d'an sake yi yana tunanin mafita,while shi kuma Hammad a lokacin ji yaje kamar ya bud'e baki ya tambayi Dad d'in abunda yake shiryawa,muryan Daddy ce ta katse masa hanzari inda yake sake tambayarsa
"A wane gari/unguwar ne gidan nasu yake..?"
Shiru yayi ya d'auke wuta zuciyarsa cike taf da fargabar abunda zai fad'awa Daddy kan wannan tambayar,bcos yasan duk abunda zai fad'a a yanzun zai fad'a ne kawai amma bawai dan ya san gaskiya ba ko kuma ya sani ba,sai dai zai fad'a ne kawai don tsoro da gudun kada yaje wani target ne Dad d'in ya shirya masa,,a zuci ya tsaya shawara da tambara kansa abunda ya dace yayi tun kafin Dad ya harbo jirginsa
"What should i tell him..!? Shin na fad'a masa ban san inda suke ba yanzun ko kuwa na k'irk'iro wani abu daban na shaida masa..??"
Wata zuciyar ce tayi saurin kwab'arsa ta hanyar bashi shawara
"A'a Hammad kada ka sake kayi gaggawa,,ya kamata kafin kayi magana ka fara duba abunda zai iya faruwa a gaba,shin idan ka fad'awa Dad d'inka haka yazo yace tunda baka sani ba sai dai ka auri zab'insa fa..?? Ita shi kenan kun rabu..? Hakan na nufin ka hak'ura da neman burin zuciyar taka.?"
Saurin girgiza kai yayi yana kiyastawa a zuciyarsa
"Ko kad'an bazan tab'a rabuwa dake ba,,a ko wane irin lokaci,halinvtsanani ko farin ciki zuciyata taki ce ke kad'ai.."

"Good.! Hammad good.! To me zai hana baza ka iya b'oyewa Daddy ba,later sai ka sake tsananta bincike akan inda suke,,kaga kenan kafin duk wani hukunci da Dad zai yanke zai iya yuwuwa ka samo inda suka koma ko ba haka ba..?"

"Yes! Wannan shawarar ita zan d'auka,tunda tayi min zanyi amfani da ita kawai."
Kamar yadda zuciyarsa tayi saurin kwab'arsa,haka nan sai ya tsinci kansa cikin in'inar da baisanma lokacin daya watsowa Dad d'in nasa tambayar
"Dad mene ne za kayi haka da sauri kake neman gidansu..!?"

Murmushi Daddy yayi cikin wani irin yanayi mai wahalar fassaruwa ya bashi amsa da cewa
"Zanyi abunda ya dace ace nayi a matsayin mahaifi,,kamar yadda mahaifiyarka ta fad'a min tace kaina kad'ai na sani,bana duba matsalolin wad'anda suke k'ark'ashina.. Saboda haka na kira ka yanzun ba don komai ba,sai domin na shaida maka,tunda har Allah yasa kun nuna baku amince da zab'in da nayi ba,to ina so daga yanzun zuwa wata d'aya mai zuwa,four weeks kenan ko.? Ina so ka gabatar damu a gurin iyayen ita yarinyar da kake so d'in,,idan kuma ba haka ba,ko aka samu matsala koma dai yaya ne wani abu ya shigo tsakani ya nemi zarta k'aidar da na gindaya,tofa ina mai tabbatar maka sai dai kace ban fad'a maka ba,amma ko tantama babu dole kayi hak'uri kabi zab'in da nayi maka.. Ina fatan ka fahimci abunda nake nufi..?"
Har Dad ya k'are maganar da yake yi Hammad bai daina mamakinsa ba,wanitunani zuciyarsa ta kawo masa har ya fara waswasi² akan anya ma Dad d'in bashi da masaniya akan abubuwan dake faruwa da shi da duk halin da yake ciki..? Katse masa tunani Dad ya sake yi ta hanyar tambayarsa
"Ina fatan kaji abunda nace kuma ka rik'e..?"
A sanyaye kamar mutumin da aka zarewa laka ya amsawa Dad da fad'in
"Ehh! Daddy na fahimta.."

"To! Me kace..? Shin hakan yayi maka ko bai maka ba mu canja wani tsarin..?"

"A'a Dad yayi..?"

"Ka tabbatar yayi maka..??"

"Ehh! Dad,,yayi sosai.."

"Idan bai yi bafa ka sanar da ni.. Tun kafin gaba a samu matsala,,ya kamata ka fito ka sanar da ni kai tsaye tunda ni na buk'aci ka sanar dani d'in.."
Guri d'aya ya zubawa ido zuciyarsa cike da fargabar abunda zai iya faruwa ya sake amsawa da
"A'a Dad in sha Allah babu abunda zai faru.. Hakan yayi.."

"To shi kenan,saboda haka sai ka fara shiri,aurenka na riga na yanke lokaci nan da wata d'aya,idan kuma har kayi sake aka samu sab'ani sai dai kayi hak'uri,amma baka da yadda zaka yi,dole ka karb'i zab'in da nayi maka,,saboda haka sai ka fara shiri daga nan zuwa wata d'ayan.."

"Toh! Dad.. Na gode sosai,,Allah ya k'ara girma.."
Jikinsa a matuk'ar sanyaye yake maganar,,lokacin da suka gama magana da Dad bayan sunyi sallama,gaba d'aya ya kasa ajiye wayar daga hannunsa,damuwa mai girma ta sake zuwa ta rufe shi,wayar ya shiga jujjuyawa a hannunsa yana sake binta da kallo
"Shin ta ina ne zan fara..!?"
Ya watsawa kansa tambayar da a halin da ake ciki yana jin ba shi da amsarta nd bai san yadda zaiyi ya samo ta ba,duk wani hope da yake jin yana da shi a lokacin zuciyarsa taba sanar da shi ya rasa shi,,kalaman Dad d'insa na kusan k'arshe suka sake dawo masa a kwakwalwa
_"Zanyi abunda ya dace ace nayi a matsayin mahaifi,,kamar yadda mahaifiyarka ta fad'a min tace kaina kad'ai na sani,bana duba matsalolin wad'anda suke k'ark'ashina.. Saboda haka na kira ka yanzun ba don komai ba,sai domin na shaida maka,tunda har Allah yasa kun nuna baku amince da zab'in da nayi ba,to ina so daga yanzun zuwa wata d'aya mai zuwa,four weeks kenan ko.? Ina so ka gabatar damu a gurin iyayen ita yarinyar da kake so d'in,,idan kuma ba haka ba,ko aka samu matsala koma dai yaya ne wani abu ya shigo tsakani ya nemi zarta k'aidar da na gindaya,tofa ina mai tabbatar maka sai dai kace ban fad'a maka ba,amma ko tantama babu dole kayi hak'uri kabi zab'in da nayi maka.. Ina fatan ka fahimci abunda nake nufi..?"_

Duniyar tunani ya sake lulawa,yayin da maganganun da suka yi da Daddy gaba d'aya suke yi masa amsa kuwwa a cikin kunnensa
"Lallai ne ya zame masa dole kafin wa'adin da Dad ya bashi yayi duk iya k'ok'arin da zaiyi ya samo inda suke,,idan kuwa ba haka ba,tofa ya sawa ransa salama komai da duk wani shirinsa zai lalace ne a lokacin da baiyi tsammani ba.."
Cikin k'ank'anin lokaci gaba d'aya lissafinsa ya shiga k'wacewa,a hankali ya tattara duka file's d'in daga gabansa ya tura su gefe,yadda yake jin jikinsa a wannan lokacin aikin gaba d'ayansa ya gama fita a ransa,hatta da zaman ma ji yayi ba zai iya ci gaba da yinsa ba,tsam ya mik'e tsaye bayan ya tattara wayoyinsa da keys d'insa ya fice daga office d'in,ko daya fito d'inma direct ya kama hanyar k'onawa gida ko sauraren su Sultan bai yiba bare ya tambaye su yaji idan sun kammala abunda suke su wuce tare,lokacin daya shigo cikin gidan ma kasa zama yayi,nan yayi ta zirga² daga nan zuwa can,ya jima cikin wannan halin kafin ya fara k'ok'arin kiran Mammansa,zuciyarsa sai azalzalarsa take akan son sanar mata abubuwan da suka faru tun bama tsakaninsa da Daddy ba,hatta da wad'anda suka faru a can baya.

Kaf yadda suka yi da Daddy sai daya sanar mata bayan nan kuma ya d'ora da zayyana mata komai dangane da abunda ya faru da shi a can baya,bcos wancan lokacin data gwada taba son yi masa maganar k'in yarda suyi zancen yayi,sai yanzun da yayi ra'ayi dan kansa ya sanar da ita,yadda yake magana da damuwa kad'ai yasa Mamma ta fahimci irin girman damuwar da yake ciki,dan haka ko daya gama zayyana mata kaf abunda ya farun itama sai tayi amfani da wannan damar tayi ta bashi shawarwarin da zasu taimaka masa,had'e da k'ara masa k'arfin guiwan akan kada ya karaya yaci gaba da addu'ah sannan kuma yaci gaba da neman inda suka koma d'in,itama in sha Allah tayi masa *ALK'AWARIN* zata sa a bincika mata,tunda har Allah yasa ya fad'a mata inda ya tab'a ganin nata,bata kyale shi haka kawai ba sai data tabbatar ya d'an samu nutsuwa sannan suka yi sallama tana sake bashi hak'uri da shawaran kadafa ya fasa addu'ah,,yace mata
"In sha Allah,,bazai fasa ba."
A haka har suka ajiye waya.

Cikin haka rayuwa taci gaba da yin nisa yayin da kwanakin da Dad ya d'iba suke zuwa suna wucewa tamkar zubar ruwa daga famfo,,sai dai har kawo wannan lokacin shiru ne babu wani labarin gano inda suke,,ata b'angaren Mamma na tun daya fad'a mata take bincike saboda tasan shi d'in ba lallai ne ya samu damar zuwa k'asar ba,sannan lokacin da suka yi maganar da yace mata zai d'auki hutu ya zo kawai,sai ya bincika da kansa ita tace masa ba sai yazo ba itama tana bincikawa,bcos bata so ya d'auki hutu yanzun lokacin auren kuma yazo yayi masa dai² da lokacin da zai koma bakin aiki,,ba don ya so ba sai don fad'in Mamma'n yasa yaci gaba da zama a k'asar,,ita kuma Mamma da take a 9ja ta baza masu mata bincike ta ko ina.
Tunda kwanakin suka fara tafiya hankalinsu duka ba a kwance yake ba,musamman Hammad da kullum cikin yiwa Mamma'n waya yake da tambayarta labarin an samu..?? Sai dai takan ce masa "A'a" idan ya sake kiran waya kuma ita take sanin yadda zata yi ta kwantar masa da hankali,a haka har suka kusan cinye sati uku daga wa'adin da Daddy ya d'ibar masa.Ranar da kwanaki suka cika sati uku dai² kuwa Daddy ya sake kiransa a lokacin yana gida kwance damuwa duk ta dabaibayeshi aikinma da kyar yaje ya dawo,,tun kafin wannan lokacin Daddy ya fahimci akwai matsala,sai dai ya b'oye ya nuna masa bai gane ba,sai tuni kawai da yayi masa akan maganarsu,nan kuwa Hammad ya rasa bakin da zai yi magana ya kare kansa da shi,a haka har Dad ya gaji ya kashe wayarsa coz ya gama fahimtar inda ya nufa sanar masa ne kawai bazai iya yi ba,,ko daya kira Mamma a lokacin itama bata iya sanar da shi ba,duk da a maganarta akwai damuwa,babu wanda ya takura a cikinsu akan lallai sai sun sanar masa ya rabu da su duka yaci gaba da shirinsa don yace aure babu fashi a wannan karon,dama² ma da ace sun sanar masa

Please Login or Register in order to submit comment