Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amma still ban same ki ba,,sai lokaci guda nayi gam da katar.."
Yadda ya fad'a mata dalilinsa sai taji jikinta duk yayi sanyi,saboda jin bama shi ya ganta yace yana so ba had'a su aka yi,,shi da yake cewa yana sauri amma kasancewar hiran ya masa dad'i da yake yanzun ta saki jiki yada suka jima sosai suna ta hira kan yadda al'amura suka tafiyar musu a cikin shekarun da suka gabata da basa tare,kowa ya fayyacewa d'an uwansa yanayin daya shiga,kafin suka yi sallama ganin Maghreb ta kawo jiki,har k'ofar gida ta masa rakiya,suna tafe suna hira cikin farin ciki,,Sultan kuwa ko da Hammad ya shige ya barshi nan zaune ko daya gaji da zaman kad'aici ya fito yana d'an kewaye a cikin line,yana yi yana duba time,ganin su sun fito a lokacin yasa sai ya nufo inda suke tsaye suna murmusawa cike da shauk'i,tun kafinma ace ya k'araso Hammad daya ankare da shi babu shiri ya kalleta da fad'in
"My Lady.! Shiga gida,sai munyi waya.!"
Kallonsa tayi cikin rashin fahimtarsa za tayi magana,tunda dai ita tasan shi da kansa ya ce lallai² sai ta masa rakiya har mota shi ne kuma yanzun yake cewa ta koma,kallonta yayi saurin yi ganin ta kasa fahimtar abunda yake nufi
"Na ce kije za muyi waya.."

"Toh! Ka bari yazo mu gaisa.!"

"A'a.! Na ce kije.."
Juyawa tayi slowly zata shiga gida,tana yi tana kallonsa ganin da tayi yak'i kallonta sai ta shige ciki,a dai² lokacin da Sultan shi kuma ya k'araso,yana ganin yadda yake had'e rai yasa akwai abunda yake faruwa
"Wai kai mene ne yake damunka ne..!?"
Ya tambaye shi
Hammad kamar bai san abunda Sultan d'in yake tambayarsa ba yace "Meka gani..!?"

"Ban sani ba..!"
Shima d'in ya amsa,d'age shoulders Hammad yayi kafin yayi gaba abunsa yana cewa
"Kada Allah sa ka sani d'in.."
Ya shige mota da sauri yayi mata key,a slow ya sauke glass d'in side d'insa da fad'in
"Malam zaka taho mu tafi ne ko kuma na tafi zaka taho..!?"
Da yake sanin hali yafi sanin kama a gurin Sultan shi yasa sai bai sake tanka masa ba ya shige motar,k'wafa Hammad ya saki bayan ya d'age glasses d'in sannan ya juya kan motar cike da k'warewa suka bar unguwar.

Tun da aka sakko daga masjeed bayan fitar su Daddy a gidan y'an uwa suka fara hallara daga sassa daban² na Nigeria da k'etarenta,kafin ace Maghreb tayi tuni har gida ya d'auki harami,duk inda ka sanya idanunka jama'a ne har ba'a magana,,,suma dai can gidan su Sabina Baba duk ya bugawa dangin Inna waya ya farfad'a musu,a nan wasu daga ciki suka hau fad'a kan me yasa baza'a sanar da su da wuri ba,sai a k'urarren lokaci.? Hak'uri yayi ta basu yana fad'a musu lamarin ne ya taso a gaggauce suma duk basu san da zuwansa ba,,wasu dai sunyi uzuri amma wasu fir suka nuna basu yarda ba.Baffan Inna kuwa ko da Baba ya fad'a masa da yake shi d'in mutum ne mai sauk'in kai sai baiga lafinsu ba,yayi addu'ar fatan alkhairi sannan ya shaida masa zuwa gobe in Allah ya yarda duk suna kan hanya suma,bayan nan kuma sai suka yi sallama,shima kuma baffa a lokacin suna gama waya da Baba sai ya sake kiran wasu daga cikin dangi ya fad'a musu,wad'anda kuma suka sani yayi magana da su akan tafiyar su zuwa gobe da safe idan Allah ya nufa.

*A gurguje...*
Haka aka yi ta shirye² daga duka b'angarorin uku,wad'anda suke ganin sun shirya suka sake shiri wad'anda kuma dama basu shirya ba suka d'auki niyyar shiryawa.

Agidan su Hammad kam duk da biki ne na namiji amma shirin da suke yi masa kamar duka shirye²n gidajen uku aka had'o aka dawo yinsu a nan,yadda mahaifansa duka suke nunawa kamar ba bikin namiji za suyi ba,,a gefen Mammah lokacin da labarin neman auren da su Daddy suka je nemawa Hammad ya dawo kunnenta tana cike da tsananin farin cikin da idan har aka cire Hammad ita ce mutum ta farko da take biye masa,,cikin lokaci kad'an kafin kace me tuni itama ta fantsama shiri,da bada umarnin abunda za ayi,Daddy kam yadda yaga tana yi da jikinta a nan sake tabbatarwa kansa lallai yanzun ne ta d'auki lamarin da muhimmanci,tunda an musu yadda suke so daga ita har Hammad d'in,duk sun ware suna tsare²n yadda al'amura zasu tafi,kafin wani lokaci mai nisa tuni har an canja komai daga shirin auren mutum biyu zuwa uku....



*Fan's ku fara shirin tafiya yinin biki fa,,wad'anda kuma zasu yiwa amare rakiya ma duk ku had'a jakunkunan ku,,coz jirgi yana daf da tashi..* 😉


#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••

*44.*
_#The missive_

Da yake suma d'in ba wasu shagali suka shirya masu zafi ba,amma yawan taron al'umma kad'ai ya isa abun mamaki,saboda duka bikin ma gaba d'aya so ake a tak'aita yinsa a iya ragowar kwanaki biyun da suka rage,cos a yadda aka tsara da zaran anyi d'aurin aure a washe gari zasu tattara su bar k'asar,wannan dalilin yasa ko da aka tashi tsara event's sai ba'a k'irk'ire su da yawa ba,bare har su sa al'ummah gajiyawa,aka barshi daga yini da Mamma za tayi da su kansu gidajen amaren,sai kamu da d'aurin aure,wanda dama shi ne a k'arshe,kuma daga shi d'in washe gari sai subi jirgi zuwa U.S.

Kasancewar a b'angaren Mamma tun bayan da Daddy suka dawo ta samu labarin canza tsarin bikin shi yasa sai ta nemi Badra suka yi magana,a bakin tane taji komai dangane da yanayin gidan su Sabinar,nan ta tashi nata hidimar bayan ta sata ta kira mata Sabinar,ko da suka gaisa duk dama a kunyace ne,sai Mamma tasa ta turo mata number Inna,saboda wasu secret maganar da take so suyi,a taken ba tare da b'ata lokaci ba,suna gama waya ta mata sharing number,a lokacin ita kanta Mamma bata iya jira zuwa wayewar gari ba saboda gudun k'urewar lokaci tayi ma Inna bayanin tana son zata turo masu shirya amarya ne dama shi yasa ta kira don taji nata ra'ayin,,ko da Inna taji batun tayi farin ciki sosai,daga zuciya har ranta taji ta amince da Mamma fiye da tunani,nd tayi matuk'ar dad'i da Allah yasa tilon yar tasu ta samu gidan mutunci kuma masu sonta,dan daga alamun yadda suka yi magana da Mamma kad'ai ta fahimci matar tana da halin dattako,cike da k'arfin guiwa da yarda duk da bata san Mamma'n ba bare ace ko sun tab'a had'uwa wani gurin haka Inna ta amsa mata akan babu damuwa sai ta turo sun,daga nan sai suka yima juna godiya sannan kowacce ta fad'a nata sabgogin.

*Saturday morning...*
Yau gaba d'aya da yake tun da gari ya waye,bak'i ke shigowa cikin gidan yasa hidimar ta sake yin k'arfi,,y'an Had'ejia ma duk sun samu halartar bikin,amma da yake tafiyar ba nan ba shi yasa sai tsakiyar rana suka iso,a nan gida ya sake d'aukan harami,inda mak'ota zuwa wad'anda basu san meke wakana a gidan ba,ganin taron jama'a ya fallasa musu hidimar da ake yi,,kafin ace yamma ta gabato tuni gida ya gama d'inkewa da y'an uwa da abokan arzik'i har babu masaka tsinke.
Sabina kuwa da yake tun safen kafin ma ace bak'i sun fara zuwa su Badra suka zo suka d'auketa,shi yasa duk abunda ake a gidansu bata sani ba,kuma ko da suka fito d'in ma basu tsaya b'ata lokaci ba kai tsaye suka wuce gurin saloon,,daga can suna gamawa sai suka wuce gidan su Jannat kasancewar a can zasu shirya kafin lokacin kamun yayi,kuma dama can ne Mamma ta aika da masu gyaran jikin da take so su sille mata itan,a yadda Mamma ta d'auki Sabina tun data bayyana a matsayin wacce Hammad yake tsananin so,itama take k'aunarta har zuciyar ta kuma sam bata mata kallon suruka,ita a y'a ta d'auke ta,shi yasa ma ko data tashi basu umarnin yadda zasu mata,tace tana so tsakanin kwana biyun suyi mata gyaran da duk wanda ya santa ba lallai ya iya gane taba,nd mutane da sun kalleta su san cewa yes itan ta kai amarya y'ar gaske,,saboda yadda Badra ta fad'a mata ta san gidan su ba lallai ne a samu gurin da zai ishesu ba shi yasa tace su tattaro su dawo gidan su Sultan,,,komai tare suke yinsa kamar yadda Mamma tayi musu,cos duka ta had'a su hud'u,sai dai nata daban da nasu cos haka Mamma tace shi yasa ake yin yadda ta tsara,dole tasa a komai sai an bambanta ta da su,,tun da suka dawo daga gurin saloon,a gidan suka iske masu gyaran jiki suna jira,kafin wani lokaci da dawowarsu tuni har sun duk'ufa a kanta,tun kafin 12pm har wajen Maghreb basu kyaleta ba,sune lik'a mata wancan,goga wancan,murza wancan,,before ace awanni hud'u masu kyau sun wuce tuni ta fara d'aukan kyalli,jikinta daya sake karb'ar gyara nan fatarta taci gaba da haskawa tana walwali fiye da da.
Sai da aka idar da sallar Maghreb sannan suka sa tayi wanka da wasu irin ruwaye na zallar sinadaran k'amshi,tana fitowa kuma kafin ruwan jikinta ya gama bushewa suka hau turareta tun daga kan gashi har kayan da zata sa,baiwar Allah komai akace sai dai kallo kawai ta rasa bakin magana,,da aka zo batun kwalliya ma da kayan da zata saka duka da suka fito cikin hidimar Mamma,wani had'ad'd'en plain material suka bata tasa da aka masa d'inkin doguwar riga,yadda rigar ta d'inku duk nacin mutum da son ya gane wane irin d'inki ne aka mata abun sai ya so bashi wahala,cos ba simple d'inki ne da kallo d'aya zai saurin sawa ka gane ba,daga samanta can wajen shoulders d'inta rigan yayi slide ta duka side biyun yana showing shoulders d'inta,yayin da ta wajen hannun zuwa k'asa tayi wani irin bud'ewa kamar bubu,sai dai sam ba itan bace,tana sawa suka zaunar da ita,special make-up artist da Mamma tayo hiring ta fara baje basirarta a kan fuskarta,ta b'ata sama da 1 hour tana painting all over her face sannan ta kammala,kwalliya y'ar ubansu ta shirya mata ta yadda da wuya a iya ganota farat d'aya,sannan ta mata rolling vail d'in rigar,tamkar wata baby doll da aka zana haka ta fito saboda kyau d'an ubansu da tayi,ba iya masu shiryata ba hatta su Badra abunda kawai suke fad'a a lokacin da aka gama shiryata shi ne "Masha Allah",,wani irin open toe high heel shoe,mai feather accent da rufaffen dunduniya suka kawo suka saka mata red colour,saboda jikin material d'inta asalinsa white ne sai adon fulawoyi jajaye masu ratsin bak'i² a jiki,y'ar k'aramar Po's mahad'in takalmin suka sake kawowa suka bata ta rik'e mai azabar kyau a hannunta,tun kafin ta mik'e tsaye tuni ta fara amsar hasken flashes,dan ta ko ina haskata kawai suke suna ihun murna,nd kowa burinsa ace shiya fara ma Hammad sharing picture ta,ita kam lokacin binsu kawai take ci gaba da yi da idanu sai d'an murmushin dake kwance saman fuskarta wanda ya sake k'awata kyakykyawar fuskar tata,deeply tana jin hawaye kamar zasu zubow mata,magana kam sam ta kasa yi musu,after sun gama shiryata,an kuma gama yiwa su Badra kiran Mamma suka yi niyya sai ga nata ya fad'o,suna d'auka itama abunda kawai ta tambaye su shi ne "Sun gama!?" Suka ce mata "Ehh! Sun kammala",amsawa tayi da "Okay" Sannan ta katse kiran ta kira gidan su Leesha taji ko suma sun gama d'in dan gab'a d'aya so ake ayi kamun a guri guda,bayan ta kira su,daga nan ta aika da motoci gidan su Sabina dan su d'auko y'an uwan su zuwa gurin da za'ayi taron,,da yake itama Mamma'n ko da suka gama sallamar bak'i ita da Maman su Sultan sai suka wuce zuwa meena events centre d'in,saboda yafi kusa da su shi yasa suka ajiye event d'in a nan ba sai sunsa mutane wahala ba,nd gurin yana da yalwar da zai d'auki duka jama'ar su,cos ak'alla gurin yana d'aukan one thousand guests,,nd sun san dai duk taron da zasu had'a zai ishe au,,suma su Sabina ko da suka gama Mamma ta sake kiransu ta sanar musu su taho cos already har ta tura musu drivern da zai taho da su,,kafin lokaci mai nisa kuma da yake basu da nisa sai ga su sun k'araso kusan a tare suka shigo harabar event centre d'in da tawagar Falisha,kada kuso ganin yadda ake kallon-kallo tsakanin dangin amare,saboda izuwa lokacin babu wanda bai san da zaman kowa ba,labari ya gama zagayawa,haka amare yadda suka wanku ko wacce nata ahalin suna so suga ita ce akan gaba dan ta zama y'ar gaban goshi,,a tare suka jero Badra tare da su Jannat suna takewa Princess d'insu baya,suma duk sun sha ado kamar ba y'an matan hausawa ba,dama duk kuma sunfi Sabina haske shi yasa ko da suka sata tsakiya sai abun ya bada wani colour mai kyau da ma'ana,nan fa gidansu Falisha ko da ganin dangin ango a tare da ita lamarin ya fara juya musu tunani,cos duk yadda suka d'auki lamarin yaso ya zarta da tunaninsu.

Sanyayyan kid'an da ke tashi da shirun jama'a,shi ya sake k'awata gurin,amare kuma ko wacce da wad'anda suka mata rakiya suka ja gefe suka kame,"Masha Allah " daga ko wane edge shi ne abunda ke fitowa a bakunan mutane,tun da suka shigo haka hasken camera's yake haska su daga fitowarsu a mota,ba'a daina ba har suka zauna,,sai da aka fara yin addu'o'i na neman zaman lafiya da kariya daga fitinannun mutane da aljanu kafin a gudanar da kamu,bayan nan sai aka ci gaba da shagali,,duka a gaba d'aya cikin gurin babu wani babba namiji kaf cikar gurin mata ne zallah iya ganin mai kallo,,ko da na hanga nima a cikin taron,nan na hango dandazon masoya *ALK'AWARIN JINI* daga shafukan sada zumunta,musamman na whatsapp,facebook dama wattpad wad'anda suka zo taya wad'annan masoya murna bisa cikar burinsu,kada ku so ganin adadin jama'a abun har yaso bani mamakin ta yadda aka yi suka samu labarin auren,abun dai gwanin burgewa kowa ya kame mutuncinsa,,Sabina aka fara kamawa,sannan Falisha saboda haka mai gidan ya tsara abunsa kuma hakan aka yi,bayan da aka gama kamu taro yaci gaba,daga nan har kusan 10pm,ana abu guda kafin taron ya fara bajewa a hankali.
Su Sabina still gidan su Jannat suka so sake wucewa sai dai tun kafinma su bar wajen da yake mutane sunyi sauk'i a lokacin sai ga kiran Hammad a wayar Badra,cike da zumud'i ta d'auka ta masa sallama,yana amsawa ko gaisawa bai bari sunyi ba yace mata su jira su a nan kada su taho zasu zo yanzun su gaisa da amaren cos shi har lokacin baiji zai iya zuwa gidansu Falisha ba,amsawa tayi sannan ta sanar musu,gaba d'aya sai suka fasa tafiyar kamar yadda suka yi niyya,,cikin lokaci kamar suna kusa da event centre d'in sai gasu sun k'araso a cikin mota d'aya,su hud'u ne hakimin yana front seat a kujerar kusa da driver daga shi Sultan sai kuma Sadeeq da Bassam daya rikid'e daga k'anin ango zuwa aboki,,dukansu cikin shiga ta alfarma irin ta *Y'AY'AN GATA.*
A inda su Badra suke Bassam ya Parker mota cos shi yayo drivern d'insu daga gida zuwa nan,tun kafin ace Hammad ya fito daga mota tuni har Falisha da taga zuwansu ta nufo su tare da tawagar k'awayenta without ta rik'e ajinta,,gimbiyar kuwa tun da suka shigo cikin harabar event centre d'in data tabbatar su ne wani sabon mulki ya motso mata,sai ta sake kamewa a back seat abunta tak'i yarda ta fita,su kansu duka y'an matan nata da suke zagaye da ita babu wacce tayi k'ok'arin barin gurin saboda aji,,ga oga Hammad kuwa,lokacin da suka fito kansa tsaye yana hango tawagar tsuntsuwarsa ya nufo inda suke cos yasan a matuk'ar ya gansu tabbas tana nan itama a kusa,,Falisha da ta riga ta taho bata kai ga k'arasowa inda yake ba ta hango faruwar hakan,dole tasa ta tsayawa,yayin da tsananin kishi mai had'e da b'acin rai ya turnuk'o ta,bata iya tsayawa ba,bare ta saurari maganganun y'an tawagarta ta juya ta bar wajen.
Yallab'ai Hammad kuwa duka da yake bai wani santa ba a fuska shi yasa da yaga taron mutane sun taho sai bai wani bawa saninsu muhimmanci ba,cos yayi zaton ko duk y'an biki ne,shi yasa sai bai ji komai ba,,yana k'arasowa kallonsu Badra kad'ai yayi suka bashi guri,cikin motar ya shige inda take hakimce,,tunda taga ya shigo ta sake d'auke kai tana basarwa,murmushi yayi mai sanyi had'e da yi mata sallama,kanta yana kallon waje duk da ba komai take iya gani ba sosai saboda glasees d'in motar da suka kasance masu duhu ta amsa without ta bari sun had'a idanu da shi cos ita kad'ai tasan abunda zai iya faruwa idan ta bashi fuska at that time,ta gaishe shi a yadda take,maimakon ya amsa shima sai ta jiyo shi ya kamo hannunta cikin nasa da fad'in
"A haka ne zaki gaishe nin kina kallon wani wajen..!?"
Sai da tayi murmushi mai sanyi buh ba mai sauti ba,kafin ta d'an juyo ta dawo dai² still bata yarda ta kalleshi ba ta dai fuskanci kujerar driver da idanunta da suke lumshe kamar mai jin bacci,,hannusa ya kai ya rik'o chin d'inta sannan ya juyo da fuskarta suna kallon juna,yadda taci uban gayu duk da ya santa fiye da tunani,nd ya jimawar da zai yi wuya ace ya kasa ganeta amma wannan lokacin daya so rikicewa,saboda azababben kyaun da tayi masa,cos komai a lokacin na daban ne a tare da ita,shi yasa kawai sai ya sa mata idanu without ya iya fad'in komai or even blinking his eyes yana yi yana shafo lips d'inta da suka ci uban red wine lipstick,murmushi tayi k'asa² kafin ta sake gaida shi,da yake gogan yayi nisa wajen kallonta da enjoying moment d'in da suke ko maganar ma bai san lokacin da tayi ba zuciya da tunaninsa duk sunyi gaba,knocking glass d'in motar akayi hakan sai ya sashi dawowa cikin nutsuwarsa,slowly ya sauke ajiyar zuciya sannan ya bud'e motar da nufin duba waye,a kan Mamma idanunsa suka sauka tana masa kallon me kake yi ne a nan d'in.? Kafin tayi wa Sabina tambayar
"Dama baku tafi bane tun d'azun.!?"
A rikice saboda rashin amsar da zata bata ta sunkuyar da kai k'asa cos ita bama tasan me zata ce mata ba,kallonsa Mamma tayi tana had'e rai da fad'in
"To rasai..! Maza fito ka basu guri su wuce,,ko baka san dare yayi ba yanzun..!?"
Saurin kallonta yayi yana marairaicewa
"Mah! Please gaisawa fa za muyi muma wucewar za muyi.!"

"Gaisuwar ne har sai an shiga mota.? Me yasa ba'a yi a gaban mutane ba.!? Nifa shiririta ce bana so kuma ka sani ko.!? Maza ka fito ka bani wuri kamar na sab'a maka.!"
Sake marairaice fuska yayi yana kallonta a sanyaye sai yace
"Mah.! Please to bari muyi sallama.."
Juyawa kawai tayi tana ba tare da ta sake masa magana ba,ta kallo su Badra dake gefe tare da su Sultan suna hira,sai dai suma d'in bata musu magana ba ta wuce,ma'anar kallon da tayi musu kad'ai yasa su yin sallama da samarin suka bar wajen.
Yallab'ai Hammad dai tunda Mamma tayi magana ta kashe masa k'arfin guiwa,babu shiri suka yi sallama ya fito jiki a sanyaye,,tunda ya fito su Sultan suka sa masa idanu,haka nan suka hau masa dariya,bai tanka musu ba shi dai ya wuce ya shiga mota yana k'wafa,buh duk da haka yasan sune a ciki,coz shi dai ya kusa ganin abunda gobensa zata haifar,haka suka bar gurin duk bai yi magana da kowa ba,,suna tafiya suma su Badra suka d'auki hanyar barin gurin,direct daga nan gidan su Jannat suka nufa,a wannan daren gaba d'aya tunda suka koma suka dasa hiran yadda program d'in ranar ya wakana,ba su suka samu suka kwanta ba sai da dare yayi nisa sosai.

*Falisha's Domicile..*
Tunda ta izgi k'afafu ta bar gurin gaba d'aya tawagar k'awayenta da k'ananun maganganu suma sai suka rufa mata baya,kafin su kai inda take har ta fad'a cikin mota,shi kansa drivern tunda yaga a yanayin da ta shigo bai jira ta bashi umarnin tafiya ba ya ja suka bar wajen da mugun gudu,tana ganin sun d'auki hanya take ta kalle² da neman ruwan hawaye saboda yadda take jin zuciyarta babu dad'i amma sun gagara sakko mata,,yadda komai ya faru take sake haskowa a idanunta,har suka shigo harabar gidansu hawaye bai samu damar sakko mata ba,amma suna shiga cikin parlor'n su ta kece da wani irin kuka hawaye tamkar an b'alle tap,,jikin Mamah ta fad'a cikin gunjin kuka tana fad'in
"Wayyo! Allah na Mamah,shi kenan rayuwata ta shiga garari,wollahi Mamah na tsaneta.."
D'agota Mamah tayi tana tambaya
"Leesha.! Mene ne yake faruwa ne..!? Yi shiru ki sanar da ni abunda yake damunki.."

"Bazan iya zama da ita ba Mamah,,wollahi zata sa zuciyata tayi bindiga.."
Gaba d'aya parlor'n yayi tsit kowa su kad'ai yake saurare,can wata dattijuwa daga gefe da tayi tsuru tana kallon ikon Allah tayi tsaki da fad'in
"Mttssww.! Yo zancen banza zancen wofi ma kenan,,ke yanzu FULAISA akan kishiya kika zo kina mana wannan gunjin kukan.? Amma wollahi kinyi asara,yo ni ai na d'auka wani abu ya faru,har ta katse min d'an baccin dana fara,,to Allah ya wadaran naka ya lalace dai.."
Sai ta sake juyawa ta gyara kwanciya tana ci gaba da mita,babu wanda ya kula da fad'an da matar tayi a tsakanin Mamah da Falisha,sai ma haushin ta da Falisha'n taji kamar ta shake ta saboda kiranta da wani irin sunan da ta tsani taji suna fad'a mata,ta kalli Mamah still idanunta na tsiyayar da hawaye
"Mamah please kiyi wani abu,Allah ni bazan zauna da ita ba.. Sai dai tayi hak'uri ta barni da shi ni kad'ai,ni gaskiya gidana bana son mu zauna mu biyu,kuma bana son muyi sharing miji,,ki taimake ni Mamah.."
Shewa wasu abokan wa'anta suka yi daga b'angaren babanta suna fad'in
"Allah sarkin dad'i inji b'arawon zuma,,yo ke Falisha har kina da bakin cewa ba zaki zauna da ita ba..!? Kece fa zaki shiga tsakaninsu cos soyayyarsa ba ta yanzun bace,mufa munji yo tarihin komai yau a gurin kamo, saboda haka ita ya kamata tace bata zama dake bawai ke ki fad'i haka ba.."
Kururuwa ta dasa cikin hayaniya ta taso kansu da masifa
"Allah sawak'e na auri ragowar wata,ai kowa yasan ni yake so ba ita ba.."
Kafin ta k'arasa rufe baki aka samu wata cikin cousins d'inta itama tayi caraf
"A'a fa Leesha, wollahi da ace je yake so ba zai miki wulak'ancin da yayi ba,,haba ni idan nice ai wollahi bai isa ba,kuma saina nuna masa KUSKUREN sa.. Har namiji ya isa yayi min haka ina matsayin mace..!?"
Zabure tayi zata sake yin magana Mamah tayi saurin rufe

Please Login or Register in order to submit comment