Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"Nd kin san abunda ya dace kiyi,,ko ba haka ba.!?"
Shiru tayi tana binsa da kallo,har sai da yayi zaton ba zata yi magana ba kafin tace
"A'aahh.!" Cikin d'aure fuska ya d'an kallonta cikin had'e rai yace
"Baki sani ba kika ce..?? So kike yi na yi miki bayanin abunda za kiyi yanzun..!?"
Sai ta bishi da kallon ban fahimta ba,tsaki ya ja ya fara mitan rainin hankalin da take masa tun daga farkon maganar case d'in,yadda ya fututtuke yana masifa a hankali ta sauke kanta k'asa tana hawaye cos ita fa harga Allah bata ga abunda tayi na laifi ba da za'a na mata fad'a haka kawai,sai da yayi mai isarsa a lokacin sun shigo harabar court sannan yayi shiru,bayan ya gyara parking sannan ya juyo ya kalleta yana fad'in
"Nifa ban ce ki sani gaba kina kuka ba,abunda ya dace kiyi ne a matsayinki na wacce Allah ya arawa dama,so idan kin tsaya kin taimaka,ahalinki kika siyawa daraja,kuma mahaifanki kika saiwa mutunci a idanun wad'anda basu d'auke su abakin komai ba,,nd mutuncin kin da kike magana a yanzun ne zai zama abun girmamawa,,if kin dage kan baza kiyi ba,fine kinga kenan nima ban kai matsayin da za'a d'auki maganata da muhimmanci ba ko..??"
Kasak'e tayi tana kallonsa idanunta da hawaye taf sai ta sake fashewa da kuka mai sauti,shima d'in tsayawa yayi kallonta kamar bazai ce komai ba kuma ko me ya tuna yace
"Can u shut ur mouth off..!?"
Tana kuka tace "To ni ya za'ayi a dake ni ace kuma za'a hana ni kuka..!?"

"Waye ya dakekin kuma waye ya hanaki kukan..?? Ni ko Inna ne muka hana kiyi.?? I thought yanzun ma kukan kike ko.?? Ko nace kada kiyi..??"

"To ba ka takura ni akan sai naje ba.."
Yana kallonta yace "Ohh! Ni nace dake dole sai kinyi..?? Kina iya bari ai tunda babu wanda ya isa yasa kiyi.."
Wani kallon mamaki ta bishi da shi a masife,duk da maganar tayi mata ciwo amma kuma haka nan sai bata kula ba ta dai ce
"Ehh! To ai gashi nan kasa na biyoka al'halin banyi niyya ba.."
Ajiyar zuciya yayi yana jinjina kai yace
"Kina iya komawa ai,,amma wollahi abunda zan fad'a miki shi ne,matuk'ar kika bar case d'innan baki karb'a ba,Allah matsalar da zamu samu zaki sha mamaki na.."
Yana fad'a ya mik'a mata ruwan gora dake kusa da shi yace
"Ki gyara fuskarki ina jiranki.."
Bai saurari abunda zata fad'a ba ya bud'e motar yayi ficewarsa ko waiwayen halin da take ciki ma bai sake yi ba ya tasamma entrance na shiga court d'in,sai lokacin da taga yayi mata nisa sannan a hankali ta janye idanunta tana sauke ajiyar zuciya had'e da furzar da iska mai d'umi.....


#Ni dai gaskiya na kasa gano kan matar nan fa,fan's idan akwai wanda ya san abunda ke damunta ya taimako..😉



#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••

*58.*
_#Trial 2_

A masife ta d'ago idanunta da kuka yasa suka sauya ta hau magana ita d'aya a cikin motar
"Ba dai an takura sai nayi ba..?? Shi kenan zanyin duk yadda kuke so ba.? Zanyi kam,,,zan kuma tsaya kan k'afafuna na ga na kwato shi,,but abunda yayi min ne dai ko zai yi me i...iii will never forgive him,, ever.!"
Tana k'arasa fad'a a hankali tasa hannuna a baki cike da muguwar damuwa,shiru tayi tana tunanin ta ina ya kamata ta fara b'illowa shari'ar nema?,,inwardly kuwa a lokacin wani irin takaici take ji yana taso mata,tun daga cikin zuciyarta yana sake mamaye ta,tunda ta janye idanunta a kansa bayan fitarsa bata sake kallon ko da hanyar ba,cos shi kansa a yanzun yadda yake wannan dagewar akan case d'in ji take ya fara kaita bango,haushin kowa take ji akan batun to amma sun kasa fahimtarta,,tasan dole ne sai tayi hak'uri ta kai zuciyarta nesa,sai dai wani lokacin ita kanta ba'a son ranta take yin wasu abubuwan ba,shi d'in daya kamata ace ya fahimci damuwarta yayi mata uzuri ya kasa,nd a yadda ya baud'e d'innan tasan komai zai iya faruwa barin ma yanzun daya fad'a taji,,zuciyarta taji tayi mata rauni tunawa da last word d'insa kafin ya fita babu jimawa,a hankali ta had'iye wani abu daya tsaya mata a throat yak'i wucewa,gaskiya ba zata iya wannan masifar ba,besides kuma ita bata jin zata iya jurewa rashin sa a yanzun,ko d'an fushin da yayi da ita cikin kwanakin wani lokacin ji take kamar zata zautu,to amma mene ne zaisa kowa yayi ta ganin laifinta ne dan kawai tace bata son jagorantar case d'in ne??,,siririn tsaki ta saki a bayyane sannan a hankali cikin rashin wadataccen kuzari ta bud'e murfin motar ta zura k'afarta d'aya waje while other half na jikinta kuma suna ciki,a hakan ta bud'e robber ruwan tana kallo,sai data fara shan ruwan har kusan rabin goran kafin ta wanke fuskarta,tana zaune bayan ta dawo da k'afafunta cikin motar sai ta bud'e handbag d'inta ta ciro powder,ta rik'e sponge d'in kafin ta fara bin fuskarta da shi gently,tana yi tana kallon idanunta da suka d'an birkice,bayan data gama goge shatin inda ta tabbatar hawaye ya bi saboda gudun kada ya fallasa asirin kukan da tayi,sannan ta kawo colourless lip bam tabi saman angelic lips d'inta da shi,tana kammalawa a hankali ta tattara komai ta tura a jakar cikin nutsuwarta sai kuma ta sake yin shiru,,kusan mintuna biyu ta sake d'auka zaune tana kallon kanta,can bayan d'an lokaci kuma sai ta lumshe idanunta bakinta ya shiga motsawa slowly
"Allaahumma innaa naj'aluka fiiy nuhoorihiim wa na'oozhu bika min shuroorihiim..Allaahumma anta adhudiiy,wa anta nasiiriiy,bika ahoolu,wa bika asoolu,wa bika uk'aatilu..Hasbunallaahu wa ni'imal'wakeel.!"
Har ta fito ta rufe motar bata fasa maimaitawa ba,kuma k'irjinta a lokacin taji yana d'an bugawa da sauri²,waiwaya tayi tana kallon inda ya bi sai taga ko hangen sa bata yi,which means ya zagaya kenan bayan mesh construction daya kare entrance d'in lawcourt d'in,da sauri itama sai ta kamo hanyar biyo bayansa,,da yake har lokacin ana kan zaman court shi yasa gaba d'aya sai gurin ya d'auki wani irin shiru,a bakin k'ofa ta ganshi tsaye bayan ta zagaye construction d'in ya hard'e k'afafunsa irin tsaiwar nan dai ta gefe amma kuma a zahirance duka k'afafun san suna kan k'asa,hannayensa zube cikin aljihun trouser d'insa,kad'an ta iya kallonsa ta saki ajiyar zuciya nd sai kuma ta d'auke kanta tayi kamar bata san yana tsayen ba,gently cikin wani takuna k'asaita tabi hanya kamar zata wuce shi tana mai sake had'e rai,tunda ta taho yake hangota between mesh construction d'in har ta zo wucewa ta gaban nasa,da sauri ya dawo da ita baya ta hanyar rik'o arms d'inta yana sake gyara tsaiwarsa zuwa ya koma dai²,idanunta tayi saurin d'agowa ta kalleshi sai dai bata ce komai ba,shima d'inma ita yake kallo har kusan minti guda,yanayin yadda fuskarta take ya sake kallo damuwa ta bayyana saman fuskarta,he knows ko mene ne yake faruwa yanzun kawai ta yadda za tayi ne amma bawai dan tana son yin shari'ar bane har zuciyarta,kad'an yayi twitching breathe then kuma yayi k'ok'arin breaking silence d'in nasu da fad'in
"Don't let pressure get a hold of u,stand strong with focus nd calmness... U are certain to succeed... So i wish u a very big best My Lady.!"
Ya k'arasa fad'a yana lumshe mata idanunsa,,yadda yake motsa lab'b'ansa da juya kalmomin abun gwanin burgewa ya zame mata,sai ta sake yi masa k'urii da idanu tana ta kallonsa har sai daya dasa aya,,sanyayyar ajiyar zuciya tayi ba tare data samu damar cewa komai ba sai dai ta d'an kwanta a jikinsa cos tana buk'atar nutsuwa kafin tayi facing matsalar dake gabanta,bai hanata ba ko dan ganin arean duka babu hayaniya nd yadda mood d'inta yake a lokacin yasan she need's calmness then a cikin aikintan,shi yasa shima sai ya samu damar rik'e ta sosai yadda zata samu nutsuwa,bayan kamar mintuna biyu sai ta d'ago kanta a jikinsa,tana sake sauke ajiyar zuciya tace
"Thank u.!" A hankali ta juya zata tafi,sake rik'e ta yayi yana kallonta da idanunsa masu birkita mata tunani,slowly ya dawo da ita inda take before then,ita kanta yadda yayi mata a hankali sai ta sake kallonsa tana kuma mamakin dalilin da yasa shi dawo da ita,dukan shoulders d'inta sai daya dafa su kafin yace
"I know u are strong,so don't let ur self down,,no matter what would going to happens kada ki manta da ubangiji,nd u know ina tare dake komai zai faru..Kinji ko.?"
Kai ta girgiza masa a hankali jikinta duk yayi sanyi da maganarsa,a yadda yake kallonta yaga ta zama wata speechless slightly sai ya matsa dai² fuskarta ya tsotsi lips d'inta had'e da sake bata kyakykyawan runguma,sanyayyun ajiyar zuciya ta saki a hankali sai ta sake d'aga idanunta tana kallonsa without tace da shi ko ci kanka,ganin irin kallonda take masa yasa sai ya d'age mata gira k'asa² yace
"Ya dai..!? Ko bai ishe ki bane.. Na k'ara miki..!?"
Murmushin da bata san yaushe ya taho mata ba ta saki kad'an sannan tayi k'ok'arin yin gaba,hannunta rik'e da nasa sosai yana murmusawa shima yace
"Yeah! I mean it,idan kina so sai mu koma na baki,,i know my lips are more than honey wajen d'and'ano.. Ki kwada su ki ji ko da sau d'aya,zaki gano sirrin dake cikinsu.. Zaaa.. Ki gwadaahhh!?"
Ya k'arasa fad'a cikin wani irin salon tafiya da nutsuwa,a lokaci guda kuma yana had'e jikinsu guri guda,saurin girgiza masa kai tayi tana ture hannunsa daga jikinta,fuskarta tana bayyanar da y'ar damuwa tace
"Ni dai ka bari,kaga fa ba gida muke ba,amma sai wani rungume ni kake,idan wani ya ganku fa..??"

"Shi kenan ai babu damuwa,idan yace dan me zan tab'a ki sai na fad'a masa u are my life partner,ko ba haka ba..?"
Yayi furucin cike da nuna ko a jikinsa,,k'wafa kawai tayi sannan cikin sauri ta juya ta barshi a tsaye da fad'in
"Ni kam ba dani zaka yi ba,,idan ka gama sai ka taho muje.."
Saurin biyo bayanta yayi yana murmushi da fad'in
"Ni kuma dake zanyi,,Allah kuma yarinya zaki sani ne idan muka koma,duk haushin da kika sa naji akan case d'in nan sai kin biya shi,,dama bashi kika ci so ki shirya biya.."
Sarai ta jiyo shi sai dai tana tunanin idan taci gaba da biye masa za'a samu matsala,,gashi a lokacin ko data kalli agogon dake d'aure a tsintsiyar hannunta taga lokaci yana nuna mata it's 10:37am,wani irin fito da ido ta d'anyi sai ta k'ara sauri har ta kai bakin entrance d'in da zai sada ta da lawcourt d'in,d'an kulle idanunta tayi cike da y'ar fargaba kafin ta arowa kanta wani mugun self assurance ta tura k'ofar shigar,,dai² lokacin data shigo cikin sa'a sai yayi dai² jin kunnenta inda alk'ali yake fad'in
_"Wannan court mai alfarma ta yanke musu hukuncin *KISA TA HANYAR..!"*_
Wannan shi ne abunda ya faru kafin zuwan nasu nd kuma babban dalilin daya janyo tana shigowar tayi magana.

Duka hankalin court da jama'ar dake cikinta kanta ya koma har ta k'araso gaba Hammad na biye da ita,lokacin daya samu damar zama a kusa da Baba a lokacin ne alk'ali yake tambayar Sabina
"Shin ko zaki iya sanar da court wace ce ke da dalilin ki na dakatar da ita da kika yi..!? Sannan ki fad'a mata mene ne alak'ar ki da wannan shari'a..!?"
Rusunar da kanta tayi tace "Ina neman afuwa ya mai shari'a.." Alk'ali yaci gaba sa kallonta yana sauraren yaji ta bakinta,ba tare daya samu damar cewa da ita komai ba,a hankali bayan ta gyara tsaiwarta sannan ta fara magana
"Da farko.. Suna na *BARRISTER HAFSAT AL'AMIN USMAN* lawyer da take kare mutumin da ake zargin dasa hannunsa cikin wannan turka² wato *HALADU ISHAQ USMAN* wanda aka fi sani da *LADO.."*
Court ta sake d'aukewa shiru ya ratsa banda muryarta kad'ai dake tashi baka jin komai,,ga LADO kuwa kafin wannan lokacin hawayen idanunsa har sun kusa k'arewa saboda tashin hankalin daya shiga sakamakon jin za'a zartar musu da hukuncin kisa,but shigowarta da d'an tak'aitaccen bayanin da tayi ko babu komai sai ya d'an ji sanyin rahama a zuciyarsa,,bayan ta gama gabatar da kanta alk'ali ya bata damar ta gabatar da shaidun da suke bayyana babu sa hannun LADO kamar yadda tace tana kare shi ne,,a nan fa ake yinta dan ko da tace babu shaida a hannunta a lokacin tana dai so a bata y'an kwanaki tayi bincike ne sai tazo da su,gaba d'aya lawyoyin gwamnati suka yi mata caa akai suna neman hanawa,,sai da aka kai ruwa rana bayan alk'ali yaji uzurinta sannan ya bada order aka yi shiru,lokacin da court ta sake d'aukan shiru a nan alk'ali ya sanar cewa ya d'age ci gaba da sauraren shari'ar LADO zuwa nan da kwana uku,,bayan yayi y'an rubuce² kuma ya ce a wuce da sauran gidan maza a ci gaba da tsaresu har zuwa lokacin da zata tabbata LADO bashi da sa hannu a ciki,ko da ya gama jawabi nan zaman ya watse bayan sallami court,,lokacin da suka fito a court za'a wuce da su Lado kasa tafiya yayi security'n yana jansa amma ya kafe sai kallonta yake idanunsa d'auke da wasu hawayen nadamar abubuwan da yayi mata a baya.
Siririyar ajiyar zuciya tayi itama lokacin data samu yak'ini akan damar data samu,kafin ta fice a cikin law court d'in ba tare data bi takan kowa ba daga cikin ahalin nata,bayan security'n daya fito da LADO ta biyo ranta a mugun had'e har ta iso inda ake k'ok'arin sashi a mota,sai data kalle LADON tsaf kafin ta kauda kai gefe cikin had'e rai tana cewa
"Idan ka san dasa hannunka cikin abunda ake zarginka,kada kasa ni wahalar banza,,cos a tsarin aikina bana goyon bayan mara gaskiya.. Idan kuma kasan kana da gaskiya zan yi farin ciki ne ace na taimaka maka for the first time a rayuwata,kamar yadda aka rok'e ni,but to me nasan ba kowa zan taimakawa ba sai mutumin da..!"
Shiru tayi bata k'arasa ba sai kuma ta juya da sauri ta barsu nan tsaye,,kasak'e LADO yayi yana kallonta,har ta bar wajen idanunsa basu daina ci gaba da tsiyayar da hawaye ba,yana kallon y'an uwa suna kallonsa da d'aga masa hannu sai dai babu damar keb'ewa da su ahaka aka danna shi cikin mota aka yi gaba da su.

Tana barin gurin inda su Inna suke ta nufa fuskarta cikin wani irin yanayin da ba zaka tab'a fahimtar a farin ciki take ko akasin haka ba,bayan sun gaisa da iyayenta suka d'an koma gefe da Inna suka yi magana k'asa² sannan suka yi sallama tace sai ta zo gidan,daga nan mota ta koma ta zauna tana lumshe idanunta,bayan shigowarsa ya tarar da ita ta jingina jikin seat,kallonta yayi kad'an ya sauke ajiyar zuciya kafin yace
"How was the legalistic.!?"
Idanunta ta bud'e ta kalle shi sai kuma ta juyar da kanta gefe kamar bata so ta amsa da fad'in
"Ai a gabanka akayi,,mene na tambaya kuma..?"
Murmushi yayi ya d'auke kai sannan ya tada motar suka d'auki hanyar barin harabar court d'in,,tunda suka d'auko hanya babu wanda yayi magana har suka k'araso gida,get man d'insu yana yaye musu get yana musu barka da dawowa,hannu Hammad ya d'aga masa da murmushi a fuskarsa,sannan ya wuce da motar zuwa carport yayi parking,still a nan dinma sake ficewa yayi ya barta a motar yana tafe yana murmusawa tunawa da irin amsar data bashi,,saurin kallonsa tayi lokacin har ya kai entrance yana k'ok'arin shigewa,a sad'ad'e ta d'auki jakarta tabi bayansa tana tafe tana mitar dalilin da zai dunga barinta da rufe mota,har ta shiga bata fasa k'unk'uni ba cikin mitan abunda ke faruwa,,fizgota taji anyi ta baya kafin ta dawo ta had'e da k'irjinsa,a d'an tsorace ta d'aga ido ta kalle shi tana had'e rai
"Mene ne wai kake yi ne haka..?? Kasan fa naji tsoro.."
Chin d'insa ya d'ora saman wuyanta,hannayensa duka zagaye da cikinta,yayi magana cikin wani kasalalliyar murya
"Ba dai kin raina ni ba..?? Ina miki magana kina bani amsa any how ko..?"
Bakinta ta gyara tace "To ni me nace maka ne..!?"
Juyata yayi suka fuskanci juna yana kallon idanunta yace
"Baki san abunda kika yi ba..??" Ta d'aga masa kai kafin tace "Ehh.!"
"Zaki sani ne yanzun.."
Yana fad'a ya d'ago ta suka bar wajen.

Still a ranar da yamma yasa ta sake shiryawa,kai tsaye ko da suka baro gida sai suka wuce central prison,sun samu damar ganawa da Lado har ma da sauran da suka yi saka LADON a cikin case d'in,,sai dai ko da ta b'ukaci jin ta bakin LADO kalma d'aya yake maimaitawa shi ne "baisan su ba",sai kuma "ta yafe masa,yasan har da hak'k'in ta akansa shi yasa Allah ya jarabce shi",duk iya yadda taso ya nutsu ya mata bayanin alak'ar dake tsakaninsa da su har suka yi inserting nasa a ciki gagara lamarin yayi,,suma dai ata b'angaren wad'ancan d'in lokacin data nemi ganawa da su bata samu wani baya ni ba,cos babu wanda ma ya tankawa tambayoyin da take masa,a ranar dai haka suka dawo gida ranta duk a dame.
Wasa² duka kwanakin haka ta kusa shafe su kan bin diddigin yadda aka k'ulla case d'in amma saboda rashin samun cikakkiyar hujja sai lamarin ya nemi gagararta,,yau kimanin kwanaki biyu kenan da d'aga shari'ar wanda yayi dai² da saura kwana d'aya su koma court,tana zaune tun bayan data idar da sallah tayi shiru tana tunanin anya zasu fita a case d'in kuwa..?? Sai gashi ya shigo cikin tafiyarsa nan mai tattare da nutsuwa,,kanta kawai ta d'aga ta kalleshi ta masa barka da dawowa,bai amsa ba har ya zauna kusa da ita yana kallonta,zuwa wani lokacin kafin ya furzar da isaka yace
"Me yake damunki ne..!?"
D'agowa tayi ta kalleshi tace
"Komai ma yana damuna.."
Gyara zama yayi ya rik'o hannunta sai yace
"Zaki iya sanar da ni.!?"
Kallonsa kawai ta tsaya yi sai can kuma ta d'auke kai tace
"Ni fa gaskiya na gaji,dan haka ma na yanke shawaran zan ajiye case d'innan kawai.."
Murmushi yayi mai sauti yace "Ba zai yiwu ba..!"
Kallon me yasa tayi masa,shi kuma sai ya d'an b'ata fuska,hannunta ta fizge daga rik'on da yayi mata a masife tace
"To ni wollahi bazan iya ba,,haba dan Allah gobe nefa zamu koma court amma har yau babu wani kwakwaran dalilin da yake nuna babu sa hannunsa,,yaya kuke so nayi ne.? Kun sani dole na zo,na baro yara na da komai nawa a wata k'asar ba da son raina ba,,kana fa kallon ko wane lokaci aka tambaye shi wai bai sansu ba yake cewa,ni d'in na sansu ne.? Ko ni nake da sa hannu a kama shin,,fisabilillahi ni yanzun idan ma kuka ce na tsaya na bibiyi case d'in nan ban san yaya ne zanyi ba kuma,duk wani hope ya k'are min,bansan mene ne kuma zanyi gaba ba,amma dai har ga Allah am tired,tunda babu hujja ni dai mu koma kawai.."
Tunda ta fara magana yake kallonta yana jinjina kai da tab'e baki har tayi shiru lokacin da take sauraren taji abunda zai fad'a,bai ce komai ba sai mik'ewa da taga yayi yana mik'a mata hannu,kallonsa taci gaba da yi tana jan numfashi,shima yana kallonta yace
"Taso muje..!"
Sai data girgiza kai sannan tace "Ina zamu je.!?"
Yace "Ta so mana,ai zaki ga ko ina ne.! Yi sauri ki taso muje,babu lokaci yanzun da zanyi miki bayani.."
A hankali ta mik'a masa hannunta ya tada ita tsaye,bayan yasa mata k'aton hijab d'inta dake ajiye sai ya rik'e hannunta suka fice daga gidan,central prison d'in dai still taga sun nufo,tun kafin su kai ga isowa tana kallonsa tayi murmushin takaici da fad'in
"Ni wollahi da kasan nan zaka kawo ni,Allah da ka rabu dani nayi bacci,wannan ai aikin wahala ne kawai muke ta yi.."

"Really..!?"
Ya tambaya yana gyara parking
"Sosai ma kuwa,to ina amfanin zuwan ma,tunda dai abunda ake buk'ata ya gagara samuwa.?? Gara fa kawai a hak'ura,, haka Allah ya tsaro masa tasa rayuwar,, sai a bishi da addu'ar dacewa,mu kuma sai muce Allah ya tsare mu da mummunan k'arshe..!"
Shiru yayi ya zuba mata ido ya kasa magana saboda mamakin da take bashi ya wuce ya misalta,har ta gama fad'ar abunda yazo bakinta bai daina kallonta ba
"Muje ko tunda kin gama maganar..!"
Ya fad'a yana b'ata rai
"Ni babu inda zani,kawai kai kaje ka dawo ina jiranka.. Fisabilillahi zan jene yaci gaba da min kuka,bayan ni kuma ba abunda ya kawo ni kenan ba..?! Tsakani fa da Allah ni dai ban yarda ma yana da gaskiya ba.."
Kicin² yayi da rai muryarsa da fad'a yace
"Sauka nace.!"
Had'e rai tayi itama tace
"Nifa nace bana zuwa,,dan banga amfanin da zanyi ba idan na shigan,,kirana ne anyi kuma nazo sai dai baiyi amfani ba,,dan haka gara kawai ku kyale ni na koma gurin yarana ko zan samu nutsuwa,,Allah ma ya sani tunda na baro su hankalina duk ba'a kwance yake ba.."

K'wafa yayi sannan ya bud'e motar yana niyyar fita yayi magana
"Ki bari na sake cewa ki fito kiga irin wulak'ancin da zan miki,,kin fa fara kaini k'arshe! Haba! Sai binki nake kina min iskanci,, ke ba uwata ba amma ina binki kina jaana a k'asa..? Kada Allah yasa kije d'in,ki barshi kada kiyi kiga idan zai dame ni..!"
Sake tsura masa idanu kawai tayi tana kallonsa har ya fita ya barta sai ta tab'e baki,,duk da ita kanta tasan abubuwan da take basa kamata,amma kumafa ta rasa dalilin da yasa take masa behaving like this,tana son bashi

Please Login or Register in order to submit comment