Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"Ehh.! Mah"

"Shi kenan jeka,Allah ya dawo da ku lafiya.."
A sab'ule ya amsa da "ameen" har ya tashi zai tafi ya sake waiwayowa ya kalle ta,canjin da ya gani a fuskarta shi ya bashi tabbacin rantsuwar da tayi ba k'alau ba,nd dole ne akwai dalilin da yasa tayi masa hakan,,take yaji zuciyarsa ta fara raya masa fasa fita har sai daya koma ya d'auko wayoyin,,har lokacin tana zaune bata motsa ba ya zo ya fita,itama Mamma koda taga fitarsa da wayoyi a hannu a hankali ta saki ajiyar zuciya a fili kuma tana fad'in
"Allah ya taimake ka,,amma da yau na gwada maka fushin da baka tab'a ganin nayi ba.."
Yana fitowa daga cikin gida mota ya shige ya bar unguwar da mugun gudu,ba tare daya nemi rakiyar Sultan ba ya kama hanyarsa shi kad'ai though ma dai wannan ba shi ne karo na farko daya fara tafiya shi d'aya ba,,tsayin kwanakin da suka gabata shi kansa yasan bulayi kawai yake,amma tabbas baiji ajikinsa zai had'u da itaba tunda har gashi yana neman shafe yini na hud'u kan neman inda suke,amma amsar iri d'aya yake maimaita samu da wanda ya samu a baya
"Waii! Haka kullum zanyi ta yawon neman ki ba tare da na samu inda kike ba..?? Har ina kika b'oye ne.?? Ya kamata ace kin gwadamin inda kike rayuwa,tun gabanin zuciyata ta tsaya.."
A fili yayi maganar yana mai had'awa da sakin wahalalliyar ajiyar zuciya,,dai² yana karkata kan motan zai shiga cikin Kwanar Maggi a hankali d'aya a cikin wayoyinsa ta fara kuka,slow yayi da tafiyar gangancin daya d'auko sannan ya rik'o wayan,unexpectedly sunan Daddy yayi appear,da hanzarin sa yayi answering kiran ya jingina ta a kunnensa bakinsa har shaking suke gurin yin sallama.

Ga Daddy kuwa ko kafin ya kira Hammad sai daya fara kiran Mamma dan ya tabbatar Hammad d'in ya kunna wayoyin kamar yadda ya bada sak'o ko kuwa,yana samun tabbaci akan ya bud'e wayoyin kuwa daga gurin Mamma kai tsaye ko da suka gama maganar ya kira shi dai² lokacin
"Sannu ubana..!"
Cikin muryan fad'a² Daddy yayi furucin yana jiran yaji me Hammad zai fad'a
"Barka da safiya Dad.."
Kalmar tayi escaped a bakinsa ba tare daya tsara fitarta a lokacin ba,,ajiyar numfashi Daddy yayi,ba tare daya amsawa gaisuwarsa ba ya ci gaba da fad'an sa
"Hammad..! Raini ne yasa ka kashe wayoyinka ko mene ne dalilin yin hakan..?!"

"A'a Dad,, bana jin dad'i ne kwanakin nan.."

"Jin dad'i kace..?? Yo yanzun waye zai ce maka yana jin dad'i dama..??"
Shiru yayi bai iya magana ba,jin haka yasa Daddy ya rufe shi da fad'a ta inda ya shiga ba tanan yake fita ba,sai da yayi masa tas²,bayan daya gama balbala ruwan fad'an then ya watso masa jawabin abunda yake faruwa da fad'in lallai² su shirya shi da Sultan a gobe su kama hanya,zai turo musu da sak'o bada jimawa ba,a yau duk abunda suke buk'ata suyi su gama,duk shirye²n da zasu yi su zuwa gobe su tabbatar sun tafi baya son a b'ata lokaci,,ba don Hammad yaji dad'in hukuncin da Daddy ya zartar ba,sai dan kawai son yayi masa biyayya ya amshi umarnin nasa,sannan suka yi sallama duka maganar Daddy kadaram kadahan (babu yabo bare fallasa).
Gefen route (hanya) ya gangara yayi parking,tunani iri daban² suka ci gaba da kawowa kwakwalwarsa ziyara,a hankali yake tunani kan maganar da suka gama da Daddy yanzun bada b'ata lokaci ba,,ya d'auki lokaci shiru ba tare daya san abunda ya kamata yayi ba kawai dai yana tsaye ne a gurin kamar wanda aka tilastawa yin hakan,,kansa ya d'ago daga jikin seat daya kwantar ya d'ora saman steering wheel had'e da rufe idanunsa,a fili yayi magana mai nuni da yana buk'atar taimako
"Why so soon.. Zan sake tafiya al'halin ban ganki ba..!? Yah Allah ka taimaki wannan gajiyayyen bawan naka.."
Tun daya tsaya a gurin bai iya fita a motan ba,sai dai idan yaga mutane sunzo wucewa ya d'ago kai zuciyarsa cike da fatan ganinta,haka napep ma dake shige da fice a unguwar sai dai idan baiga zasu gifta shi ba amma sai ya duba,haka yayi ta kalle² ko Allah zaisa yayi dacen ganinta kamar rannan,,har yamma yana tsaye a gurin da yayi parking ya kasa motsawa,ba shi ya bar unguwar ba har sai da akayi salatul asr,shima d'in sanadin kiran da Sultan yayi masa ne akan maganar tafiyarsu goben nd yace zai shigo gidan yanzun,dalili kenan da yasa shi kamo hanyar dawowa cikin sauri tun da ya riga yace da Mamma tare zasu fita da Sultan,,yanzun idan ta ganshi shi kad'ai ta d'auke shi matsayin me..? Dama yaga yanayinta tun a d'azun,so hakan yaba nuni da komai zai iya faruwa da shi matuk'ar ya bari Sultan ya riga shi zuwa gidan.
Tuk'in ganganci,tuk'in jeka ka mutu ya shiga shek'awa,daga kwanar maggi zuwa Mayangu road ko minti sha biyar baiyi ba ya k'araso,a dai² ALU avenue ya tsaya,bayan yayi parking ya shiga k'ok'arin kira line Sultan d'in cike da fatan Allah yasa bai riga ya fita daga gida ba
"Dude.! Kana ina ne..??"
Abunda ya iya fad'a kenan zuciyarsa na daka
"Gani a gida..Wani abu ne..?"
Ajiyar zuciya Hamma ya sauke cikin samun nutsuwa yayi hamdala a zuciyarsa,while a fiki kuma ya furta
"Yi sauri ka fito gani bakin line ku.."

"Ok" Sultan yace sannan ya ajiye wayar,shima d'in duka tsakanin yi masa waya da fitowarsa ko mintuna biyar baiyi ba ya k'araso inda yayi parking,daga nan suka d'auki hanyar gida.

Shirin duk daya kamata ace sunyi saboda tafiyar dake gabansu sunyi bisa tsari,kamar yadda Daddy ya shaida masa,hatta Sadeeq ma da suka yi waya da shi ya sanar musu shima ya kamalla komai suna dai jira ne wa'adinsu ya cika,nd sun ajiye batun akan kawai zasu had'u da juna a airport goben idan rabb ya nufa,daga nan suka bi juna da fatan alkhairi kana suka ajiye waya,bayan nan shima Sultan yayi sallama da shi ya wuce gida dan k'arasa sauran y'an abubuwan da suka yi masa saura.

Washe gari tun misalin k'arfe 6:30am suka bar gida,tare da ahalinsu duka suka yi musu rakiya,wannan karonma cikin masu raka Hammad sam babu Daddy kamar lokacin tafiyarsa na farko,duk da bai so yin tafiyar ba musamman a irin wannan lokacin haka nan ya sawa ransa dauriya,ba don komai ba sai dan yana so ya farantawa Daddy a matsayinsa na mahaifi,shi yasa komai zai ce masa baya tab'a yi masa musu,,da misalin k'arfe 7am da y'an mintuna bayan sun gama sallama da dangi,jirginsu ya bak'unci sararin samaniya,,,sunyi tafiya ta ak'alla awanni goma sha uku da mintuna daga 9ja zuwa k'asar Amuruka kafin jirginsu ya samu damar sauka,,kai tsaye bayan saukar su cab suka nema da zai kaisu cikin Florida,bayan isowarsu Jacksonville kasancewar a gajiya suke duka yasa a ranar ba su samu damar shiga UNIVERSITY ba,sun dai bari akan sai zuwa washe gari idan sun huce gajiya,sannan su tunkari mak'asudin abunda ya kawo su.

*NIGERIA..*
Duka tunda satin ya kama take jin jikinta babu dad'i,ga exam da kullum idan ta fita bata samun dawowa da wuri,nd idan ta dawo d'inma sai dai ta had'a da neman medicine saboda headache daya takura mata,a gefe guda kuma tunanin sa daya addabeta fiye da lokacin baya.
Tun data fito daga exam take zaune ita d'aya yayin da ta buga uban tagumi a bakin class d'in ta zubawa hanya ido,yadda take jin zuciyarta ta cika taf da tunaninsa yasa hawaye gangaro mata,sam bata san abunda ke faruwa da ita ba,sai dai ta jiyo saukar abu ajikinta,a hankali tasa hannu ta gogo fuskarta,sosai abunda ke faruwa ya bata mamaki ganin tana kuka without sound sai zallar hawayen dake sauka,jakarta ta bud'e ta zaro handkey d'insa daya bata tun karon farko kafin suyi sabo,gently ta fara goge fuskarta yayin da wasu hawayen ke sake sakkowa kamar ana tunkud'osu,bata fasa gogewa ba taci gaba har sai da tayi mai isarta dan kanta kuma ta rarrashi ranta sannan ta tattara y'an kayayyakin ta tayi hanyar fita a school d'in ba tare data jira wad'anda suke area d'aya ba ta kama hanyar komawa gida.

Kwanaki sun dad'a turawa a b'angaren ta,sai dai kullum babu wani ci gaba ta da take gani dangane da damuwarta,a kullum idan ta zauna bata da aikin daya wuce tunani da zubar da hawaye,cikin k'ank'anin lokaci fuskarta ta saje yin pale (fayau) saboda rashin wadataccen nutsuwa,,Inna kanta a cikin wannan y'an kwanakin lamarin ya fara damunta,duk da tasan damuwarta amma idan ta tambaye ta sai dai tace mata stress ne yayi mata yawa,,sai dai kawai tasa mata ido,amma abun yana damun zuciyarta,a duk sanda zata kalleta ta kan ji babu dad'i saboda yadda take zaman shiru,ko aiki idan za tayi sam babu wadataccen kuzari a tare da ita kamar da can baya,itan data kasance mai kazar² soyayya da damuwa yasa ta koma kamar ba ita ba,irin kunyar nanma da aka san d'iyan Fulani da shi duka shima a yanzun ta ajiye gefe saboda yadda damuwarta yake bayyane a fili.
Ganin lamarin bana k'are bane yasa Inna yanke shawaran neman mafita ta hanyar bin umarnin da zuciyarta take bata,lokacin da suke maganar da Baban Sabina kawai ta bar shine akan tana son yi tafiya buh shima d'in bata fito fili ta sanar da shi dalilin tafiyar ba,ko daya takura ta da son jin dalilin da zai kaita,kawai tace masa tana son taje ganin gida ne sannan ta samu ta d'an zaga danginta kasancewar ta jima sosai bata je ba,besides kuma anyi mutuwa babu adadi a family'n nata,bukukuwa da haihuwa duka ba tare data samu damar zuwa ba,sai dai a gefe d'aya duk da tana son zuwan tayi gaishe²,can k'asan ranta zuwan nata ya ta'allak'a ne akan lamarin yarinyar tata,tana son karb'o mata taimako a gurin baffanta ko Allah zai sa ta dangana (sawa ranta hak'urin rashinsa),idan kuma Allah ya nufa suna da rabon ganawa,tofa tabbas zata fi kowa farin ciki da faruwar al'amarin,,duka a cikin tak'aitattun kwanaki Inna ta yankewa ranta shawaran tafiyar sai dai ta barshi akan nan da zuwa k'arshen sati,ma'ana weekend idan ya zagayo,duk inda akace ta tafi Friday zuwa Sunday sai ta kamo hanyar dawowa.

*FLORIDA STATE (U.S.A).*
Cike da samun gagarumar nasara,ya fito daga k'aton theater,hannunsa d'auke da had'ad'd'en briefcase nasa mai d'auke da jimillar takardunsa,sai dai fuskar nan a had'e take cif babu alamun farin ciki,k'arasowar sa a gurin ita tasa Sadeeq dake zaune dafe da chin d'agowa ya kalleshi,saboda sanin halinsa da suka yi bai cika magana akan minor things ba shi yasa yanzunma da yake su nsan idan har ba tanbayarsa suka yi ba babu tabbacin ya iya fad'a musu abunda ke faruwa a ciki,wannan dalilin yasa ko da suka kalleshi a tare suka ambaci
"Dude..! Ya ake ciki..?!"
D'auke kai yayi kamar bai jisu ba,bayan ya zauna a seat d'in dake kusa da su,cikin nuna halin ko in kula da maganar da suke yi ya furta
"Idan kun shiga zaku san komai.."
Kallon juna suka yi,ko kafin Sultan yayi kwakwkwaran magana wani bature ya lek'o yana tambayansu *ALIYU MUKHTAR*,karkata kai suka yi su biyun jin an kira sunan Sultan,a hankali kuma sai ya mik'e bayan ya kallesu duka bakinsa d'auke da addu'ah yayi gaba Sadeeq ya bishi da fatan samun nasara amma gogan ko d'aga kai baiba,murmushin k'arfin hali Sultan yayi sannan ya wuce ciki,baturen ya maida k'ofa ya rufe,nan gurin ya rage daga Sadeeq sai Hammad sai kuma sauran abokan karatunsu da aka kiransu tare,amma magana ta fatar baki ko d'aya bata sake had'a su ba,bayan Sultan ya shafe ak'alla tsayin mintuna talatin ya fito yana murmusawa,canjin da Sadeeq ya gani tun daga kan fuskarsa yasa shi ambaton
"Alhamdulillah alaa kulli halin..!"
Duk da bai san mak'asudin sauyin da aka samu d'inba,a kusa da shi Sultan ya zauna,kamar wasu yara ya sak'ala hannunsa a saman wuyar Sadeeq d'in cikin tsananin farin ciki yana fad'in
"Dude..! Gaskiya Allah kad'ai ya isa abun godiya..Tabbas mu d'in masu nasara ne tun daga haihuwa."
Murmushin gefe Sadeeq yayi cikin salon nuna farin cikinsa yace
"Allah mutumina..!?"

"Sosai ma..Amma dai bari ka fito mayi maganar,kasan yanzun babu lokacin yinta..Idan mun koma zamu tattauna.."
Dariya suka yi suka bawa juna hannu,sannan Sadeeq ya mik'e yana fad'in
"Sai na fito y'an uwa..?"

"All the best dude..!"
Sultan ya fad'a yana masa murmushi,kafin ya wuce shima sai daya kalli Hammad sannan ya juya ya tunkari k'ofar shiga zauren ganawar.

Shima d'in kamar su,dai² adadin lokacin da suka b'ata a ciki haka shima ya d'iba kafin ya fito fuskarsa k'unshe da fara'a mara misaltuwa,yana zuwa dai² inda suke ya sake bud'e baki cikin tsantsar farin ciki ya rungume Sultan yana fad'in
"Kaii! Dude..Gaskiyar ka daka ce mun tabbata masu sa'a,,lallai wannan ba k'aramin abun farin ciki bane a garemu."
Murmushi Sultan yayi masa yana shirin yin magana suka ga Hammad ya mik'e,kallonsa duka suka yi yanayin yadda suke jinsu cikin farin ciki amma shi duka fuskarsa bata gwada komai ba,farin ciki ko akasin haka ba zaka tab'a ganewa ba,magana suke shirin yi sai dai babu wanda yasan actual abunda d'aya zai furta a taren sai suka furta
"DUDE..! Are u happy..!?"
Ba zata suka ji ya amsa musu da
"Am not..!"
Da mugun mamaki shimfid'e a fuskokinsu suka matso kusa da shi,bakunansu har sark'ewa suke wajen tambayarsa
"Me yasa haka..!?"
Bai tanka musu ba ya wuce yana tafiya nd yana sassauta d'aurin tie d'in dake wuyansa
"Baza ku gane ba."
Yayi furucin k'asa² ba tare daya basu damar jin abunda ya fad'a d'in ba,,da sauri² suke binsa yayin da kowanne ke watso masa tambayar dalilin da yasa baya farin ciki da samun gagarumar dama irin wannan da kowa ke burin samu,sai dai tun daya ce musu baya farin ciki bai k'ara magana ba har suka dawo masaukinsu,,yadda yaga duk sun nufo inda yake yasa shi saurin mik'ewa fuska babu alamun fara'a ya wuce ya barsu nan a tsaye,ya d'auki tsayin lokaci a bathroom kafin ya fito sanye da bathrobe yana sake had'e fuska,saboda ko kad'an bai shirya yi musu bayanin dalilin da yasa shi fad'ar haka ba
"Dude..Wai me yasa kake haka ne..?"
Sultan daya gaji da shirunsa ya fad'a,yana daga tsaye a bakin mirror yayi saurin waiwayowa yana kallonsu
"Me akayi ne..!?"
Ya tambaya fuska da alamun neman k'arin bayani
"Kafi kowa sanin abunda akayi ai,,mun tambaya ka kasa bamu amsa ba,nd ka wuce ka barmu tsaye..Me kake nufi ne..?"
Murmushin gefe yayi sannan ya juya ya sake barinsu a tsayen ba tare daya ce komai ba,shirun da yayi musu har ya gama abunda zaiyi yana niyyar fita sannan ya juya kallesu,kamar zaiyi magana kuma sai ya fasa ya fice abunsa,,matuk'ar haushi Sultan yaji akan lamarin a hankali shima ya juya ya fice,nan d'akin ya rage sai Sadeeq kawai,shi kam tsabar d'aure masa kai da lamarin Hammad yayi zama yayi agurin ya had'e hannayensa duka ya d'ora chin d'insa akai yana tunanin halayen Hammad masu matuk'ar d'aure kai.

*NIGERIA..*
Juyowa Daddy yayi daga tsayen da yake yana cire wayarsa daga jikin kunnensa,a hankali kuma ya saki siririn tsaki kafin ya sake daddannawa ya maida ita kunnensa,kusan minti guda ya d'auka kafin yaji wayan ta fara fitar da sound na alamun kiran da yake yi ya tafi,ajiyar zuciya ya saki kafin ya maida wayan hands free
"Assalamu alaikum warahmatullah..!"
Muryan Hammad ya ambata cikin sanyi mai tattare da nuna damuwa
"Wa'alaikas salaam warahmatullah..!"
Daddy ya amsa,yanayin yadda yaji muryar Hammad cikin sauri ya fara tambayar lafiyarsa saboda yadda yaji yana magana kamar yana cikin wani yanayi sab'anin farin ciki,ko daya tabbatarwa Daddy lafiyarsa k'alau nan Daddy'n ya sake watso masa wani tambayar
"Ina fatan anyi nasara..!?"
Numfashi ya shak'i sannan ya furta
"Ehh! Dad..Munyi nasara.."

"Alhamdulillah..!"
Daddy ya fad'a cikin yanayin nuna tsantsar farin ciki
"Yanzun zaku dawo kwana kusa,ko kuwa sai nan gaba..!?"

"A'a Dad,, sunce mu jira nan da two days,duk yadda ake ciki zasu sanar damu.."

"Toh.! Babu damuwa,,ai sai ku jira d'in ku gani ko.!? Amma sun sanar da ku wane irin aiki ne zasu yi da ku..!?"

Ajiyar zuciya ya sake yi sannan ya amsa
"Ehh! Dad sun sanar mana,sunce ne za muyi aiki da hukumar binciken manyan laifuka ta *FBI* (Federal Bureau of Investigation).."

"Masha Allah..!³ Ubangiji yayi muku kyakykyawan jagoranci."

"Ameen" ya amsa a sanyaye dan shi har ga Allah bai shiryawa zama a k'asar ba,duka tunaninsa akan zai juyo 9ja ne a kwanakin,sai dai yadda yaji Dad yana farin ciki dole jikinsa ya sake yin sanyi

"Shi kenan kace mu da kai yanzun sai da ziyara ko..??"
Daddy yayi furucin cikin yanayin barkwanci,murmusawa yayi bisa dole
"Haka dai suke nufi Dad,,amma..!"
Sai kuma yayi shiru ya kasa k'arasawa dan yasan muddin ya fad'i abunda yake zuciyarsa yanzun Daddy zai rufe shi da fad'a,shi kuma abunda yak'i jini kenan,shi yasa ma yayi shirun
"Amma mene..!? Naji kayi shiru baka k'arasa ba."

"Nothing Dad,,buh dama zance ne a gaida min kowa.."
Murmushi Daddy yayi sannan suka yi sallama.....




#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••

*30.*
_#Memorability_

A can gidan su Sabina kuwa a dai² wannan lokacin sosai Inna take shirin barin gari,dan ta jahirce tace tafiya babu fashi,yadda ta d'aura niyyar tafiya ina tunanin a wannan lokacin babu wani abu da zaisa ta fasa yinta,cikin hukuncin ubangiji kamar yadda ta tsara za tayin hakance ta kasance,ranar jumu'a bayan an sakko daga masjeed,a ranar ya kasance Sabina bata da exam,suka yi sallama bayan tayi mata nasiha sosai akan ta kula da kanta sannan ta kula gida,dahga nan ita da Babanta suka mata rakiya har car station,sai da suka ga tashin motarsu sannan suka koma gida,jikinta duk a sanyaye,yayin da take jin zuciyarta nayi mata wani iri kamar tace da Inna zata bita.
Kwanaki biyu kacal da Inna tayi bata garin,alamura suka dad'a cakud'e mata,yadda take d'aukan kwanakin tafiyar Inna sai take ganin kamar ta share sama da wata guda bata nan,kasancewar ranar yau ta kama Sunday kuma ranar da Inna zata dawo,tun da safe tana gama aikin da zata yi ta d'auko littafinta da niyyar karatu,akai² kuma sai ta d'ago kanta ta kallo hanya cike da sa ran zata ga shigowar Innarta,,har kusan Maghreb tana zaune tana dakon shigowar Inna sai dai shiru har lokacin aka rana ta gama b'uya,jikinta duk ya gama mutuwa ta kuma saduda akan Inna ba zata dawo a ranar ba,da b'acin rai mai tattare da jin haushi tayi cilli da littafin hannunta gefe,ta mik'e tana k'unk'uni,niyyarta ta shiga d'aki ta d'auko hijab dan duka zaman kad'aici ya isheta,tana so ko k'ofar gidansu ne ta d'an lek'a taga gari,shigarta ciki babu jimawa Inna tayi sallama a cikin gidan,da sauri ta lek'o saboda duka tunaninta sallamar da taji ba gaskiya bane,bcos tun safe yake mata amsa kuwwa a kunnenta shi yasa ko data ji yanzunma sai bata fito ba ta dai d'an leko a tunanimta duk dan ta damu ne yasa,,ido hud'u sukayi da Inna tana shigowa,bata saurari k'arasowarta ba ta kwaso aguje zuwa gaban Inna,wawar runguma ta bata cikin ihun murna take fad'in
"Innata oyoyo..!"
Murmushi Inna tayi mata mai tattare da soyayya while tana fad'in
"Mama na oyoyo.."
Duka suka sake yin murmushi,ga Sabina kuwa tsabar farin cikin dawowar Inna har y'an hawaye tayi,,sun d'auki mintuna biyu zuwa uku a rungume da juna kafin Inna tayi magana
"Uwata.. Sake ni ko nayi alwala naji ana niyyar tada sallah.."
Muryar ta a sanyaye ta ce
"Kaii Inna ki bari na gama jin d'umin ki mana..!"

"Yau naji ja'ira,, sallar ce ba zanyi ba sai kin gama abunda kike yi..!?"

"A'a'a..! Za kiyi mana,amma Inna ki bari ba yanzun ba kinga fa da sauran haske a gari.."

Murmushi Innar ta sake yi kafin ta fara k'ok'arin janyeta gefe,sake k'ank'amota tayi da duka hannayenta
"Yau naji ikon mai mana ruwa da iska..Yanzun Allah baza ki sakeni nayi alwalar ba,sai kin sani na rasa jam'i kenan..!?"

"A'a,, to ai Inna bin jam'i a gurin mace ba wajibi bane,abunda akace shi ne mace tayi sallah a d'akinta ko masallaci,to kinga mu yanzu idan kika ce zaki je masallaci idan ba na Eid ba ko Jumu'a yanzun nan sai mutane su fara taruwa a kanki,wasu ma cewa za suyi kinzo da sabon addini.."

"Uhhuumm..! Haka ne,amma to sake ni dai nayi akwalar,tunda na dawo ai ba guduwa zanyi ba muna nan tare dake.."
D'agowa tayi da kanta dake jikin Inna ta kalleta sannan a hankali ta sake ta tana sake fad'in
"Allah ko Inna,, da kika tafi kika barni ni kad'ai,ji nake kamar na shekara bana tare dake.."
Y'ar dariya Inna tayi tana d'aukan buta
"Yo to ai da kinsan kin bini mun tafi tare kawai."

"Allah kuwan nima sai da kika tafi nayi ta tunanin haka.."
Shigewa Inna tayi bayan gida,yayin da Sabina taci gaba da magana
"Ai duk da nasan haka zanyi zaman nan babu dad'i da sai dai mu bar Baba shi kad'ai.."
Tana fad'ar haka ta d'auki buta tana zuba ruwa,har ta zauna zata fara alwala Inna ta fito daga bayi
"Ghufranaka..! Yo dama ai dan kink'i ne,shi yasa nima ban takura kiba,amma tun fari dake nayi niyyar tafiya,ganin da nayi kina jarabawa shi yasa nayi shiru da batun ban tilasta miki tafiya ba,kuma nasan za kiyi karatu.."
Murmushi tayi batace komai ba taci gaba da alwala,bayan ta idar ta tunkari d'aki still bata ce komai ba,,lokacin da suka idar da sallah Inna na zaune,ta matso jikinta ta d'ora kanta akan cinyarta,a lokacin Inna tana kan yin addu'ah,tana idarwa sai kuma ta d'anyi jim tana kallon fuskar Sabina da idanunta ke rufe,,,maganganun da sukayi baffanta a tafiyar da tayi suka fara dawo mata a kwakwalwa,,,tun shigarta gidan bayan sun gaisa da y'an uwanta da matar baffan ta shiga d'akinsa su gaisa, tana zaune gabansa bayan sun gaisa da shi tayi d'an jimm tana tunanin ta yadda zata bashi labarin abunda ke faruwa,tmuryarsa ta jiyo muryarsa yana tambayarta
_*"MAIRAMU..* Ince dai duka kuna lafiya..?"_
_Sai data d'ago ta kalle shi

Please Login or Register in order to submit comment