Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata baki tana mata alama da ido akan tayi shiru saboda duka idanu na kansu,sai data lallab'a ta sosai sannan taja hannunta suka bar wajen.
A wannan daren suma dai a gidan su Falisha sun ga tashin hankali,saboda fitinar data kwana yi musu,,bak'in dake gidan kansu da kyar suka samu runtsawa cos ta hana kowa nutsuwa,suma d'in kuma sai suka kwana tattaunawa akan maganar.

*Sunday Morning..*
Da yake dama yau d'in shi ne ranar d'aurin aure kuma da wuri aka saka za'ayi d'aurin auren,shi yasa tun kafin ace 11am yayi ango da tawagarsa duk suka gama shiryawa,cikin wani irin farin cashmere wool fabric mai shara² ya fito sanye a jikinsa,har kana iya gane fari kar d'in sleeveless da yake ciki,tun daga sama har k'asa,ciki da waje da colour d'aya yayi amfani a jikinsa shi ne fari,komai daya sa babu wani mix colour fuskar san nan banda walwali babu abunda take,,su kansu su Sultan lokacin daya fito zuzuta shi sukayi ta yi,sai dai yayi musu murmushin san nan mai burgewa,,suma d'in dai kamar shi plain wool fabric ne a jikinsu sai dai su nasu clour d'in onions pink ne,sai suka yi amfani da farin colour a huluna da takalmansu,yadda suka zuba anko su uku Sadeeq,Sultan da Bassam kai ba zaka tab'a iya gane wanne ne yafi wani kyau ba,kawai dai kowa yayi kyau cikin sun babu na yarwa,,sanda suka fito suna tafe cikin wani farin Toyota tundra 2017 model,ko kafin su wuce sai da suka biya gida da yake suma ba a gidan suke ba,suka gaisa da jama'a sannan ya yima Mamma sallama,suka nufi gurin d'aurin aure cos a time d'in ma har Daddy ya fara kiran wayarsa,a gaggauce bayan sun baro gida kai tsaye sai suka nufi masallacin jumu'a na triumph dake fagge.
11:00am sharp shu ne lokacin da za'a d'aura aure amma saboda ganin family'n Falisha basu samu k'arasowa da wuri ba sai yasa aka jinkirta,wasa² abu tun wajen 11am har 12 saura babu su babu labarinsu,,kiran waya kuwa tun ana yi cikin nutsuwa har abun ya fara neman zama matsala,Daddy da kansa yadda ya dunga kiran wayar *ALHAJI ISHAQ BUNAWA* abun ba'a cewa komai,hankalinsa duk ya tashi saboda rashin sanin dalilin k'in halartarsu a gurin d'aurin auren,nd kuma bai san matsalar dake afkuwa ba.

*****
A can gida kuwa b'angaren Mammah a dai² lokacin da hidima yayi hidima,taro yayi taro jama'a ta ko ina shigowa suke yi mata Allah sanya alkhairi kama daga y'an uwa,dangi na kusa da nesa,sai ga sak'o ya riskota har cikin gidan gardener d'insu ya shigo da sauri ya sanar mata ana sallama da ita a wajen,da mamaki bayyane a fuskar Mamma ta amsa sannan ta rufo masa baya,guards d'in gidan suma suka biyo bayanta har zuwa bakin get cikin shirin ko zata b'aci.
A tsaye ta iske su mutim biyu cikin manyan kaya,a bakin get d'in jikin k'atuwar Jeep k'irar Prado,tun kafinma ta k'araso su da kansu suka nufo inda take,ita dai Mamma ganinsu kad'ai sai da lamarin yaso bata tsoro amma da yake jajirtacciya ce sai ta dake bata nuna musu tsoronta a fili ba,har suka gaisa cikin mutunci,sannan d'aya daga cikinsu ya antayo mata tambayar
"Da farko dai Hajiya mu mun kasance y'an aike ne,kuma dai Allah yasa ba muyi b'atan kai ba,nan ne gidan mai *SHARI'A..!?"*
Jikin Mamma har b'ari yake wajen basu amsa da
"Ehh! Toh wanne a ciki kuke magana..!?"
D'ayan da baiyi magana ba har lokacin tun bayan gaisuwar da suka yi ya sako baki wajen fad'in
"Cheap judge *ALHAJI ALIYU MUHAMMAD* muke nufi..!"
Kad'a kai Mamma tayi tana had'iye wani irin yawun tsoro dan tunanin Mamma zuwa lokacin ambaton sunan mai gidanta ya haddasa mata firgici fiye ma da ganinsu da tayi,da wani irin frightening looks taci gaba da kallonsu tana kad'a kai
"Ehh! Nan ne..! Wani abu ya same shi..!?"
Kallonta suka yi a tare cos sun san ba lallai bane ace ta gane abunda suke nufi kai tsaye ba har sai sun mata bayani
"A'a Hajiya.. A gaskiya mu wannan batun bamu da masaniya akansa,abunda kawai muka sani shi ne,an turo mu mu kawo sak'o daga..!"
Katse su Mamma tayi saurin yi cikin hayaniya tana tambayarsu
"Dan Allah kuyi min bayanin wane irin sak'o ne..!? Ku sanar da ni sak'on na mene ne,maganar ku ta tayar min da hankali.. Kuyi min bayanin daga inda sak'on yake..!"

"Alal hak'ik'a Hajiya muma da kika ganmu nan y'an aike ne,kuma kin san d'an aike a kullum hausawa sukan ce baya laifi ko..!?"

"Ehh! Haka ne,,to amma ni abunda ban sani ba shi ne,kun ce an aiko ku,buh kun k'i sanar da ni wane irin aike ne aka yi muku,kuma daga ina ne aka aiko kun,nd gurin waye aka ce muku.!?"
Ajiyar numfashi mai maganar yayi sannan yace
"Gaskiya ne wannan Hajiya,a bisa hak'ik'anin gaskiya mu dai y'an sak'o ne da muka fito daga gidan *ALHAJI ISHAQ BUNAWA.."*
Wani irin fad'uwa gaban Mamma yayi duk da bata san dalilin aiken da akayi musun ba,sai ta jinjina kai without tayi magana ta ci gaba da sauraronsa
"Sako ne aka aiko mu da shi aka ce mu kawo nan,sannan mu tabbatar mun dank'a su a hannun wani daga cikin masu gidan.."
Cikin hayaniya Mamma ta sake tasowa kansu duk da bata so ace an san halin da ake ciki d'in,sai dai ganin yadda suke mata maganar kamar basa son fad'a matan yasa dole sai data had'a musu da hakan,hak'uri suka shiga bata cikin sigar kwantarwa da mutum hankali sannan suka fad'a mata ko wane sak'o ne,bayan sun shaida matan kuma suka fito da kayan dake cikin booth d'in motar,akwatunan lefen da Daddy ya had'a aka kai gidan su Falisha na aure da komai da aka kai take gani a gabanta,lamarin daya matuk'ar d'aure mata kai,cos bata san dalilin faruwar hakan ba,,su kam ko da suka gama fito mata da kaya suka yi sallama da ita sannan suka ja motarsu suka yi gaba,,guards da suke gefe wad'anda suka biyo ta,da sauran workers na gidan suka d'ebi kaya zuwa ciki,,cike da damuwa nd rashin sanin dalilin faruwar hakan,yasa tun kafin Mamma ta isa cikin gidan ta fara k'ok'arin kiran Daddy a waya cos ita dai bata ganewa lamarin ba.

A can gurin d'auri auren ma dai zuwa lokacin ko da ganin time yana ta dad'a k'urewa nd still babu wani magana akan an samu *ALHAJI ISHAQ BUNAWA* ko wani a cikin makusantansa a waya yasa dole aka fara tunanin hanyar da za'a bi ayi solving lamarin,,wannan dalilin yasa shi kansa limamin da zai jagoranci d'aurin auren ko da yaga lokaci yana sake tafiya sai ya nemi da yayi magana da maganbatan ango saboda b'ata lokacin yayi yawa,,at dsame time da yake k'ok'arin ganin waliyyan ango,shima Malam a nasa b'angaren bisa yadda yaga babu alamun zasu zo d'in sannan duk wani k'ok'arin kiran aminin na Daddy da ake har da shi a ciki,buh shiru sai dai waya ta shiga ta katse an k'i amsawa,sannan gashi sai amfani ake da different numbers duka ko za'a same shin amma abu ya gagara,wannan dalilin yasa sai ya yanke hukuncin za'a d'aura auren Hammad da Sabinar idan yaso daga baya idan an tashi a gurin d'aurin auren sai suje su duba ko lafiya hakan ta faru.
Hakan ce ta kasance a lokacin da misalin 12pm aka d'aura auren *MUHAMMAD ALIYU MUHAMMAD (HAMMAD)* da amaryarsa *HAFSAT AL'AMIN USMAN (SABINA)* abisa mafi ingancin sadaki,,taron d'aurin auren daya samu halartar masu manyan muk'amai a cikin k'asar nan,,kada kuso ganin fuskar Hammad lokacin daya tabbatar an d'aura auren,duk wani farin ciki,nutsuwa gami da sukuni sai a lokacin ya tabbatar ya same su,farin cikin da yake jinsa a ciki,bakinsa kam ko rufuwa ya kasa yi,hamdala kawai uake yiwa Allah daya cika masa muradinsa.
Daga nan gaba d'aya taron suka d'unguma zuwa Tahir Guest Palace Hall,dake nan a Nassarawa G.R.A,,su Daddy kuwa da yake sun san da waccan matsalar ko bayan da suka baro wajen d'aurin aure,kai tsaye gidan su Falisha suka so wucewa saboda bin ba'asin dalilin rashin halartar ko mitim d'aya gurin d'aurin auren,daga cikin ahalin shi *ALHAJI ISHAQ BUNAWA* d'in bare kuma shi kansa.
A lokacin suna tare da Malam sun gama tsara yadda za suyi tafiyar dan dama da shi suka yanke zasu je d'in sai ga kiran Mammah ya shigo wayar Daddy,duk da bai so d'aukan kiran nata ba cos yasan dai maganar ta bazai wuce taji an d'aura auren ko A'a ba,,sai dai ko da ganin kiran nata ba mai k'arewa bane yasa shi tilas ya amsa.....

*#Comments first...😉 Cos i know after kun karanta chapter nan zaku yi dariya,nd u all love it,so kuyi k'ok'arin faranta min nima da comments d'inku,duk da nasan akwai masu k'ok'arin yin hakan a ko wane chapter da nake muku updating...* 🧘🏻‍♀


#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••

*45.*
_#Their proximity_

*Masoyana kuma masoyan littafin alk'awarin jini,duk naga comments d'inku,sai dai kuyi hak'uri ban samu na amsa muku ba,,a gaskiya ina alfahari da ku kuma bazan iya fad'a muku tsantsar farin cikin da nayi ba bisa ganin hakan,,buh ina sake baku hak'uri saboda lokaci yayi min k'arancin samu ne yanzun,online d'inma ba sosai nake samun yinsa ba cikin kwanakin nan,nd NEPA suna mana wulak'ancin kawo wuta yanzun,sai tsakiyar dare suke bamu,wannan dalilin yasa bakwa ganin posting d'ina kamar baya,,amma ku k'ara hak'uri dani in sha Allah komai ya kusa zuwa end.*

*****
Sallama shi ne farkon abunda Daddy yayi cikin muryar damuwa cos bai san mene ne yake going through ata b'angaren Mamma'n ba da har take masa irin wannan kiran babu sassautawa,,itama Mamma'n a nata b'angaren lokacin da yake tana cikin damuwar kayan da aka dawo da su,bayan ta amsa masa bata jira ya sake yin magana ta tari numfashinsa da tambayarsa
"Daddy.! Yanzun kuma ina kenan.!?"
Ajiyar zuciya yayi cike da damuwa cos baima yi tunanin abunda zai fito daga bakinta kenan ba sai ya bata amsa yana cewa
"Gamu a hanya zamu je gidan *ALHAJI ISHAQ BUNAWA.! Da akwai wani abu ne.!?"*

"Gidan sa kuma,,mene ne dalilin da zaisa kuje.!?"
Ta dawo masa da tambaya,numfasawa Daddy yayi yana lumshe idanunsa irin yadda Hammad yake yi sannan a hankali ya waresu yana amsawa da fad'in
"Ya kamata ne muje mu duba,saboda cikin ahalinsa ko mutum d'aya bamu gani a gurin d'aurin aure ba,,mun kira waya babu amsa,yanzun haka ma maganar da nake miki tafiya za muyi.."
Muryar Mamma duk da tana tare da damuwa sai tace da Daddy
"Ai ina ganin Yallab'ai bama sai ta kai ku da yin haka ba.!"

"Me yasa za kice haka Asiya.!? Bayan kuma kinji na fad'a miki ko mutum d'aya bai halarci d'aurin aure daga ahalinsu ba.!?"
Ajiyar zuciya tayi sannan in a calmness way tace
"Ina tunanin ya kamata ne ku fara zuwa gida ku duba sak'on da ya aiko da shi kafin kuyi tunanin zuwa inda yake.!"

"Sak'o..!? Wane irin sak'o ne wannan da zai aiko da shi a irin wannan lokaciny.!?"
Daddy ya tambaya cikin muryar jimantawa da mamaki
"Ehh! To nima dai da yake ban tsaya duba sak'on ba,amma gashi nan dai ya aiko da shi yace a tabbatar an dank'a hannun masu gidan.."
Slowly Daddy ya d'ago kansa yana kallon Daddy'n Sultan dake opposite d'insa sannan yace
"Shi kenan bari yanzun gamu nan dai zuwa har Malam,,zamu ga wane irin sak'o ne tunda sai kiransa muke yak'i amsawa,kada zamuyi wahala muje mu tarar da wani abu daban.!"
Ajiyar zuciya ta sake yi sannan tace
"Allah kawo ku lafiya..! Sai kun iso d'in."
Daga haka suka ajiye wayar,a gefen su Daddy ko daya gama magana da Mamma da yake su Malam duk sunji wasu daga cikin maganganun Daddy a lokacin da yake wayar,na Mamma'n ne dai da yake ba a hands free wayar yake ba sai basu san abunda ta sanar masa ba,shi kuma Daddy'n ko da suka gama wayar bayanin abunda duk tace yayi musu tunma kafin ya k'arasa Malam yace suje su fara duba sak'on kafin su nufi gidan nasa,daga hakan kuwa gaba d'aya sai suka d'auki hanya zuwa mayangu road.

Tun da suka d'auki hanyar Tahir guest palace daga masallacin triumph,saboda tsananinfarin cikin da yake ji yake tunanin yanzun wane irin yanayi ne take ciki.!? Tayi farin ciki ko A'a.? Yaya yanayin fuskarta take murmushi ko kuma yanayin kuka take.? Duk yadda ya so ya gwada yanayinta a lokacin tunaninsa ya kwace,ya kasa tsayar da yanayi guda a ciki,,a hankali kuma sai zuciyarsa ta fara kawo masa tunanin anya ma zai iya zuwa wani waje yanzun ba tare daya duba ya san halin da take ciki ba.? Saboda shi dai tunaninsa a lokacin shi ne ya samu ganinta ko da bata farin ciki,shi tunda yana yi zai yi k'ok'arin ganin sunyi sharing farin cikin da yake ciki,duk da shi nashi ya zama mix-feelings ne ya tsinci kansa a ciki,,haka nan yaji dole yana so ya ganta a yanzun,,k'ayataccen murmushi ya sake saki kafin yace da Bassam
"Bassam.! Muje gidan Mamah yanzun kafin mu wuce.!"
D'if suka yi a cikin motar kowa yana mamakin wannan abu irin na Hammad,shi bazai iya hak'uri bane gar suje banquet d'in su dawo dole sai yasa sun biya wani gurin
"Amma Yaya ai naji Daddy yace mu wuce,me zai kaimu gida kuma bayan itama Maman bata nan.?"
Bai tsaya saurarensa ba yace
"Idan baza kaje ba yafi min sauk'i kace,,Yah bazan jeba,ko ka fita ka bani motar na ja kaina.!"
Girgiza kai yayi saurin yi yana fad'in
"Wane mutum,,ai duk yadda kace haka za'ayi,ranka ya dad'e na Aunty Hansai..!"
A zabure ya kalloshi da fad'in
"Me kace.!?"
Bai ita maimaita masa ba yayi shiru sai dariya da suka d'auka duka su uku
"Kan ubah.! Uban waye yace maka haka sunanta yake.!?"
Murmushi Bassam yayi bayan ya tak'aita dariyarsa da fad'in
"To shi suna Yah har sai ance ga wanda ya fad'a.!?"
Had'e rai Hammad yayi cif yana jifansa da wani warn look
"Wollahi kada ka sake KUSKUREN fad'ar wannan sunan a gaban ido na,,idan ba haka ba zan sab'a maka,kaji dai na fad'a maka,sunanta ne baka sani ba ko mene ne,da zaisa ka kirata da wabnan d'in.? Idan baza ka ce mata Aunty ba,ka kirata da sunanta HAFSAT Ko ka kirata da SABINA ya wadatar,amma kada na sake jin wannan daka fad'a..!"
Yadda yake ziraro bayani yasa take Bassam ya gane kuskurensa tun kafinma aje ko ina sai ya bawa Hammad d'in hak'uri,shi dai bai tanka masa ba yayi musu shiru har suka shigo ALU avenue,a dai² get d'in gidan yayi horn mai gadinsu daya taso da sauri yana ganin su sai ya shaida musu ai basu jima da barin gidan ba suma d'in,tambayarsa Bassam yayi ko yasan inda suka nufa ne,sai yace musu bai sani ba amma yana tunani ba zai wuce gidan Hajiya ba,ma'ana dai gidansu kenan,godiya yayi masa sannan daga nan ya juya kan motar zuwa hanyar gidan nasu.
A lokacin kusan a tare motocinsu suka shigo cikin harabar gidan dasu Daddy,sai dai motarsu tana kan gaba yayin da tasu Daddy take biye musu,fitowa suka yi dukansu da mamakin dalilin da yasa su Daddy suka yo nan d'in al'halin sun barsu a masjeed gurin d'aurin aure suna batun zasu je gidan *ALHAJI ISHAQ BUNAWA* shin mene ne kuma ya faru yanzun suka dawo gida.? Duka suka yiwa kawunansu tambayoyin without sunyi expecting samun amsa a gurin wani,,wucewa suka yi zuwa cikin gidan,duk da y'an uwa da suke ta jan Hammad da tsokana,shi dai bai wani sake musu ba,saboda yanayin da yaga su Daddy sun shigo wanda yasa ya fahimci akwai damuwa,hanyar guesting room yaga sun nufa while shi kuna Daddy yana tafe yana waya,ko k'arasa wucewar basu yi ba su kuma suka shiga main parlor,lokacin dai² suna shigowa su kuma Mamma da Maman su Sultan suna niyyar fita,danhaka suka gaisa,duk dama dai gaisuwar nasu a tsaitsaye ne su Maman suka amsa duk da sun shigo gidan before su tafi gurin d'aurin aure,sai dai yanayin da suka gaisa d'azun ba shi suka gani ba yanzun,kowa dai cikinsu da abunda yake sak'awa a zuciyarsa,a hakan su Mamma'n suka wuce suka barsu a nan cikin taron y'an uwa,a tsaitsaye suka sake gaisawa da sauran mutane,sai dai ganin babu alamunsu a gidan dole yasa su fitowa suma suka bar gidan,,suna tafe a hanya bayan fitowarsu Sultan yake cema da Bassam
"LB.! Wai anya lafiya kuwa.? Nifa naga fuskokinsu Daddy cikin yanayin damuwa,,bakwa tunanin wani abu ya faru ne.!?"
Ta cikin mirror Bassam ya d'ago ya kallo su da yake suna bayan da fad'in
"Gaskiya dai nayi wannan hasashen tunma a gywin d'aurin aure,buh baza muyi saurin yanke hukunci ba,dole dai mu jira muji daga bakinsu.!"

"Yeah! It's true,koma mene ne zai fito mu sani,idan ya shafe mu amma.!"
Shi dai Hammad baiyi magana ba cos tunanuka yake akan inda suka tafi a lokacin, side d'in da yake Bassam ya kallo saboda jin yayi shiru bai ce komai ba da fad'in
"Yaya.! Wai lafiya kuwa kayi irin wannan shirun.!? Ko dai Sahibar ce.!?"
Sai a lokacin ya waiwayo ya kalleshi yana squeezing face cike da damuwa
"Wace ce.!?"
Duka a tunaninsa ko daya fad'i haka bai kawo da Sabina yake ba shi yasa ma ya tambaya d'in
"Ur helpmate.!"
Wasu ajiyayyun murmushi ya saki yana kallonsa sai dai bai ce komai ba,murmushin shima Bassam yayi sannan ya d'auko waya a nan tsakaninsu yana clicking yana kuma ci gaba da drivern,gently yasa wayar a kunnensa yana fad'in
"Hello.! charming! Ina kuke ne.!?"
Saurarawa yayi kad'an sannan yace
"Okay good.!"
Daga haka bai sake magana ba yayi disconnecting kiran ya sake maida hankalinsa kan titi suka ci gaba da cin taya,in less than 20 minutes suka k'araso Tahir Guest palace.

Shigarsu Mamma cikin guesting room a zaune suka iske su Malam amma Daddy yana tsaye ya kasa zama sai zagaya parlor'n yakw,har k'asa su Mama suka gaida Malam sannan suka gaisa da mazajen nasu,tunma kafin wani ciki yayi magana,urgently tuni har Daddy ya kallo Mamma da fad'in
"Asiya ina sak'on da kika ce *ALHAJI ISHAQ* ya aiko.!?"
Ajiyar zuciya tayi sannan ta nuna masa gefe inda tasa aka parker kayan da suka dawo dasu,fuskar su duk su ukun a lokaci guda ya bayyanar da mamaki sai Abba'n Sultan ya kallota yana cewa
"Ehh! To munga kaya,amma.! Bamu fahimci abunda yake faruwa ba."
Gyara zama Mamma tayi sannan ta koro musu bayani kamar yadda suka yi da y'an aiken alhajin,ran Daddy a mugun b'ace ya sake kallon kayan
"Tabbb' d'i jan..!"
Shi ne abunda ya fara fitowa daga bakinsa followed by sanya hannayensa duka biyu cikin aljihu yana girgiza kai
"Ni..!? Kamar ni *ALHAJI ISHAQ* zai yiwa haka.!? Ni.!?"
Sai yayi shiru yana sake jinjina al'amarin,Abba'n Sultan ne yayi saurin matsawa inda yake ya dafa shi
"Dan Allah ALHAJI kada kace komai,,idan hae yana ganin yayi mana haka ne dan ya tozarta mu,ai mu godiya ya kamata mu yiwa Allah,,saboda had'a zuri'ah da *ALHAJI ISHAQ* ko bala'i.!?"

"Ai shi kenan,,Allah yasa hakan shi ne mafi alkhairi.."
Daddy ya sake fad'a yana neman gurin zama,amma maganar kana kallonsa zaka san yaji ciwonta
"Uhhuumm.! Lallai *ALHAJI ISHAQ* wato wulak'anta ni yaso yi kenan,,yanzun da Allah yasa nak'i amincewa da batun waccan d'aya yarinyar shi kenan yasa na cuci Hammad.!? Ai shi kenan.!"

"Dan Allah ALHAJI kayi shiru da batun,tunda har Allah yasa ba ita kad'ai ce mace ba ai duk da sauk'i,fatan mu Allah ya tsare gaba,ita wannan d'in da akayi auren da ita,Ubangiji ya albarkaci auren nasu.."

"Toh ameen.! Nayi shirun bazan kuma cewa komai ba,amma dole sai ya gane KUSKUREN sa.."
Daddy ya sake fad'a yana jinjina batun
"Dan Allah ka rabu da shi,mu yanzun ma ba sai munje ko ina ba tunda anyi haka,,yanzun kam mun gano dalilinsa na k'in amsa kiransu ai.."

Malam dai kallonsu kawai yake sai dai har lokacin bai samu damar cewa da su komai ba,har sai da Daddy suka yi shiru sannan yayi gyaran murya ya musu sallama,amsa mishi suka yi suna maida hankulansu a kansa,after shi kuma Malam d'in ya fara musu nasiha cikin hikima dangane da abunda ya faru tun daga neman auren Hammad d'in daya gabata da irin rigingimu da suka faru tsakanin Daddy da su Mamma har kawo yanzun da wannan al'amarin ya faru,,sanda ya gama tsaf jikinsu yayi wani irin sanyi,sai suka sake yi masa godiya sosai sannan ya sallami su Mamma saboda yasan dai a cikin gidan za'a buk'ace su,, suna fita yace da su Daddy suma su wuce gurin banquet d'in saboda jama'ar su dake can suna jiran k'arasowar su.

Can d'inma dai gidan su Sabina yinin bikin ne dai suke yi,y'an uwa da abokanan arzik'i cika gida,amarya kuwa da k'awayenta sai suka zama ababen kallo ga al'ummah,ba wai iya kad'ai ga y'an uwa da dangi ba,saboda azababben kyau na d'aukar magana da suka yi.Har kusan Maghreb aka kai ana yini kafin masu shirya amarya suka zo cos a yau d'in za'a wuce da ita zuwa gidan su Hammad,washe gari da wuri su kuma zasu bar k'asar,,a mak'otan gidansu suka samu gidan wata amarya da bata jima da zuwa unguwar ba,masu shiryata suka duk'ufa suka fara nasu aikin,cikin abunda duka baifi a wanni uku ba suka kammaleta a cikin wani elegance wedding attire mai kalar red wine,paisley long sleeve ne mai masifar kyau amma ta k'asa sai ya zama wani irin style mai kama da fishtail,turban suka mata a kanta da wani irin tie mai kyalkyali da beads da aka masa ado da shi shima d'in sak kayan jikinta,sannan suka kawo vail na net suka rufa mata ta baya yana binta a k'asa,around 8:pm aka kammala kimtsata,masu kwaliya suna gama musu duka suka yi sallama da su sannan suka wuce,yayin da su kuma suka fice zuwa ainihin cikin gidan

Please Login or Register in order to submit comment