Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hak'uri a mafi yawan lokuta idan taga ransa ya b'aci amma kuma bata san mene ne yake faruwa da ita ba haka nan sai taji ta fasa ko baza ta iya ba,,ta shafe kusan minti biyu tana kallonsa yana tafiya kafin taja siririn tsaki ta bud'e motar a d'an fusace ta fito,tana tafiya tana mitar abun a ranta take ci gaba da biyo shi abaya har suka shigo cikin gidan.

Lokacin da aka rakasu offenders room k'in d'aga idanunsa yayi bare tayi tunanin zai kalleta,itama ko da taga hakan bata tanka masa ba sai ma wani sabon had'e rai da tayi ta basar da shi,,suna nan zaune shitu aka shigo da LADO,kallonsa duka suka yi,yadda ya rame ya sake yin duhu gwanin tausayi,,shi kansa jikinsa a sanyaye lokacin daya gansu ya k'araso ya zauna saman kujera yana jiran yaji meke tafe da su kuma,,sai data sake had'e rai tayi tamkar bata tab'a sanin yadda ake dariya ba tana kallonsa tace
"Gashi nan to yazo,,sai ka tambaye shi idan zai iya sanar maka..! Ni kam bazan iya biyewa wannan shirmen ba.."
Wani kallon mamaki yayi mata har zai yi magana sai kuma yayi k'wafa kawai bai ce mata komai ba ya juya ya fice,d'akin ya dawo daga ita sai LADON,,ko da ganin haka wani ajiyar zuciya ta sake saukewa kafin ta maida hankalinta kansa tana kallon yadda yake hawaye,cikin matuk'ar d'aure fuska fiye da zatonsa tace
"Kaga malam nifa ban zo nan dan ka sani gaba kana min kuka ba,,idan zaka iya bud'e baki ka fad'a min abunda nake son ji daga gare ka falillahil hamd,idan kuma baza ka iya ba wollahi kaji na rantse zamowata barrister bazai amfane ka da komai ba,,an sani na baro yarana da komai nawa a wata k'asar duk saboda ka samu kayi free amma saboda rashin sanin ciwon kai kullum kai baka sansu ba..?? Idan baka sansu ba ni ta yaya za'ayi nasan alak'ar ku,kuma idan baka sansu ba yaya za'ayi su ambaci sunanka a ciki..??"
Lado yana kuka ya d'ago idanunsa da suka koma jaa yace
"Na rantse miki har ga Allah,wollahi ban sansu ba,ni ban san mene ne nayi musu ba,amma wollahi koma mene ne ya faru nasan hak'k'in kine yake ci gaba da bibiyata.!"
Sai ya sake fashewa da kuka,,wani dogon numfashi ta sauke tana lumshe idanuwanta a hankali sai ta ware su tana kallonsa,yayin da wani irin tausayinsa ya fara bijiro mata,,ta d'auki kusan mintuna uku tana kallonsa da tausayawa kafin ta sassauta murya tace
"Shi kenan naji,na kuma yarda,,amma kasan abunda nake so da kai yanzun..??"
Saurin amsawa yayi da "A'aahh!" Yana goge hawaye,sai ta k'ifta idanunta sannan tace
"Kasan daga yau bamu da wani sauran lokaci ko..?? Kuma ka san wannan shi ne damar da muke da shi ta k'arshe,,daga wannan ranar idan har bamu samu shaidar da zata tabbatarwa kotu baka da laifi ba,na tabbata babu abunda zai sa a sake ka.. To amma ni yanzun abunda nake son ji daga gareka shi ne,kada kace min baka sansu ba,kada kuma kayi min kuka,dan kuwa kukan ka bazai tab'a fitar da kai ba,abunda kawai zaka yi yanzun shi ne kayi k'ok'arin tuna wani abu daga cikin rayuwar ka,la'alla wani abu ya tab'a had'a ka fad'a da wani,,ko ba haka ba..??"
Shiru ne ya ratsa gurin na wani lokaci,kamar LADO ba zai sake cewa wani abuba,can kuma sai ya d'ago yana kallonta yace
"Gaskiya babu da wanda nayi rigima.."

"A'a ka dai tuna,,ko bayan rabuwarmu da ku,ko kafin nan,dole ne zuwa yanzun akwai wani abu daya tab'a faruwa,,kayi k'ok'arin tunawa..!"
Shiru ya sake yi cikin halin zurfafa tunani,ya jima yana juya maganarta a zuciyarsa kafin da confidence yace
"Tabbas..!"
Da sauri ta kalle shi tace
"Ka tuna...!?"
Yace mata "Ehhh! Tabbas! Na tuno wani lokaci da rigima ya had'amu da wani dealer na kayan maye..."
Sanyayyar ajiyar zuciya tayi sannan ta sake nutsuwa tana fad'in
"Uhhuumm.! Maza sanar da ni mene ne ya had'a ku ko nace akan me kuka yi rigimar a lokacin..?"
Kamar mai tunani ya d'age kai sama sannan ya fara da cewa
"A wancan lokacin mun samu sab'ani da shi ne akan rough na tabar wiwi.."
Kallonsa ta d'anyi kafin tace
"Bai yi maka wata barazana ba..??"
Yace "A'aahh.! Yayi min barazana sosai,,kuma har a lokacin ma yake cewa,na rubuta na ajiye sai ya jefa rayuwata a bala'in da har na k'are rayuwata bazan tab'a mantawa da shi ba,,idan kuma har naga na tsallake to tabbas shi zai zama AJALI NA.."
Shiru Sabina tayi tana kallonsa da mamaki har ya gama zayyana mata duk yadda suka yi,,bayan tayi masa tambayoyi akan matsalar da sunan wanda yace d'in ya bata amsa,,sai ta d'anyi jim tana tunani kafin tace masa
"Shi kenan,ina ganin zan tafi yanzun,,amma abunda nake son sanar da kai shi ne,ko da za'a tambayeka gobe ka tabbata abunda ka fad'a min shi zaka maimaita musu a court.. In sha Allah ko da ace bamu samu wani shaidar ba,wannan d'in zaisa a sake d'aga mana k'afa har mu samu damar yin bincike mai zurfi.."
Godiya sosai LADO yayi ta mata kamar zai mata sujjada,ita dai sai binsa take da kallo har aka fita da shi,,bayan d'akin ya rage ita d'aya sai ta d'auki jakarta da wayoyinsa daya bar mata tana niyyar fita,sai ga shi ya dawo cikin room d'in yana fad'in
"Daka ta,,bamu gama abunda muka zo yi ba..!"
Tsayawa tayi kallonsa har ya k'araso inda take tsaye,gyara tsaiwarsa shima yayi yana rik'e waist yace
"Kin tuna cewa wad'anda aka kamo su tare har yanzun basu ce komai ba tunda ake tambayarsu alak'arsu..!?"
Ta girgiza masa kai da sauri tace
"Ehh! To amma ai ni ina ganin ba sai mun sake bi kakansu bama.."

"A'aahh.! Dole ne suyi magana,,idan ba haka ba kuma case d'in nan,kafin a gano inda ya nufa tabbas sai an sha wahala."
Jinjina masa kai tayi tace
"Me yasa kace haka..??"
Juyawa yayi zai fita sai kuma ya waiwayo yace
"Just wait nd see,how the truth is going to revealed.. Ni zan tabbatar miki yanzun da yardar Allah...!"
Juyawa yayi ya fita yana mata sanyayyan murmushi mai nuni da lallai sai ya tabbatar da abunda ya fad'a,haka ya fits ya barta da jan gwaurayen numfashi tana kuma tunanin ta ina ne gaskiyar zai bayyana.....


*#Few Page's remaining in sha Allah...👏*



#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••

*59.*
_#Gestation_

Bai jima da fita ba aka shigo da mutum na farko cikin wad'anda ake zargin sun aikata laifin tare da LADO,,tunda ya shigo ya kalleta yake murmushi k'asa² da yaga ta d'ago sai ya d'auke kai zuwa gefe yana fad'in
"Y'ar wahalaaa..!"
Tana jinsa sarai lokacin da yayi furucin,buh saboda akwai abunda take buk'ata daga gare shi sai ta d'auke kanta gefe itama duk da yadda zuciyarta take k'una tana fad'in
"Zauna ko..!?"
Harararta ya d'anyi kafin yaja kujerar ya zauna cikin tak'ama da isa,yana yi yana hura hanci kamar wani babban shege,,d'an kad'an tayi twitching breathe tana kallonsa kafin ta tambaye shi sunansa,ko kallon inda take baiba,hakan da yayi sosai ya fusata ta,but haushin da take ji d'in sai bai sa ta kasa sake yin magana ba,still banza da ita yayi tamkara tana magana da gini,,a hankali ta tsaya kallonsa without ta sake cewa da shi komai tana tunani,tunda take iya tsayin rayuwarta daga lokacin da ta gama karatunta zuwa fara aikinta zata iya cewa had'uwa da case d'in LADO yafi komai sata a damuwa,cos ita dai bata tab'a fuskantar irin wannan matsalar ba,bak'in ciki,haushi da damuwa duk su had'e mata,besides kuma rashin gane bakin zaren inda case d'in ya nufa yafi b'ata mata rai,cikin k'ank'anin lokaci damuwa tasa ta cika tayi fam,amma a hakan sai sake daurewa take tana nuna babu komai,al'halin cikin zuciyarta ji take tamkar ana kwarara mata ruwan dalma,still bata daddara ba ta sake danne zuciyarta tayi magana nan ma yayi shiru,sun d'auki ak'alla mintuna goma tana masa magana ko kallon ta ya k'i yi bare tasa rai da zai sanar mata abunda take son ji d'in daga gare shi,,tunda tayi² ya fad'a mata yak'i sai ta koma baya ta jingina da kujerar da take kai had'e da rafka tagumi ta zuba masa idanu kawai tana kallo without tana blinking,, a zahiri duk wanda ya kalleta zai ce shi take kallo,amma a bad'ininta tunani kawai take da ace zaiyi sub'utar baki ya fad'a mata maganar banza zata iya zazzabge masa fuska da mari.
Tunda tayi shiru a tunaninsa ko da yaga ta kafe shi da ido,yayi tsammanin wani abu take kallo a jikinsa,a hankali sai ya tab'e baki yana jan tsaki,kallonsa tayi da sauri tana had'e rai itama,sai kuma ta mik'e tana shirin d'aukar jakarta ta fita,kamar wanda aka matsa bakinsa yace
"Yaah daiii..! Lauya ko har kin gaji ne??"
Cak ta tsaya a inda take ba tare data waiwayo ba ko ta kalleshi,dariyar shak'iyanci yayi mata sannan ya juyo yana k'are mata kallo daga zaunen da yake while ya goya hannunsa a cikin arm d'in kujerar,from head to toe yake kallonta yafi a k'irga kafin ya sake yin dariya da fad'in
"Banyi tsammanin zaki yi saurin karaya ba ai lauya..!"
Idanunta ta runtse cikin b'acin rai,har zata juya ta zazzage masa wutar bala'in dake cin jikinta kuma sai ta dake tak'i ta tanka masa
"Mene ne damuwarka da gajiyawata ko akasin haka..!?"
Dariyar shak'iyanci ya sake yi wannan lokacin harda dukan table dake gabansa sannan ya mik'e tsaye yana zagayeta da k'are mata kallo,d'an kad'an ya lashe lips sannan ya tsaya yana kallon fuskarta
"Babu..!" Yace yana d'age shoulders,,sai data d'auke kai gefe saboda warin da yake,dan a time d'in ji tayi zuciyarta ta fara harbawa tsoronta d'aya kada amai ya taso mata a cikin gurin,a dabarance sai ta matsa baya tana kauda kai gefe
"Ya kamata ki hak'ura haka nan cos baza ki tab'a yin nasara ba.!"
Kallon kayi kad'an tayi masa kafin tace
"Ko me yasa kace haka..!?"

"Saboda saina bada damar ki san komai da ke faruwa ne zaki sani.."
Dariya tayi masa tana binsa da kallon to mahaukaci kafin tace
"Kai awa kenan kake wannan maganar..!?"
Dariya ya kece da ita yana nuna kansa da k'arfi yace
"Ni a gagara badau..!"
Murmushi tayi at the same time ta tab'e baki,duk yadda taso tayi control anger d'inta kasawa tayi
"Da kyau *IBLIS* uban shaid'anu.. Kai har kana tunanin wata tsiya ce.? Ko kana tunanin ka isa ka b'oye abunda Allah yaso ya bayyana.?"

"Kwarai kuwa,,ni ne nan uban duk wani shege da shegiya,,shaid'ani ne ni,kuma hatsabibi,girman sharrina yafi na shaid'an. "
A k'ek'ashe tabi shi da kallon wulak'anci kafin tace
"Allah ko.!?"
Yace "Yessss! Ko kina da jaa ne.!?*
"Ta ina zan ja ni kuwa tunda gani ga IBLIS.. Uban duk wani shege da yake tak'amar shi d'an iska ne.?"
Dariya ya sake kyakyatawa yana nuna kansa proudly da abunda yake fad'a yace
"Kawai ki kama gabanki,,cos the jurist was over.."

"It's not.."
Ta fad'a tana kallonsa k'asan zuciyarta ko fad'i take
"Yah rabb,,ga bayinka ka taimake su ka fiddasu cikin wannan k'angin."
Katse ta yayi ta hanyar fad'in
"Keeee! I told u wannan shari'ar yazo k'arshe,, ke har wata kwararriya ce da zaki nuna min akwai saura..?? Ba keba ko manyanki ne suka zo baza su tab'a yin nasara ba.."

"Sai ka hana ai uban shaid'anu.."

"Ni ne nan.. The father of all the devils..!"
Ya kuma shek'ewa da dariya,lips d'inta ta cije ta ciki,tana tunanin yaya zata yi da d'an iskan ya sanar da ita,a hankali sai ta saki murmushi tana kallonsa tace
"Ehhmm.! Zan iya tambayarka wani abu..?"
D'age gira yayi yace "Yeah! U can",, jinjina kai tayi kafin tace "Mene ne ya had'a ka da HALADU ne wai..?? I mean ko kun san juna ne da shi,irin somewhere else.?"
Dariya yayi yace "Ke yarinya ce.. But barin fad'a miki actual inda muka had'o alak'a da shi.." Kasa kunne tayi tana saurarensa da addu'ar Allah sa wahami (mantawa) yayi yake shirin fad'a mata
"Shekara guda baya,mun tab'a had'uwa da d'an uwanki akan case d'in K'ANWATA,so ina tunanin shi ya manta ne,amma ni da yake bana mantuwa kuma bana yafiya,,,wannan dalilin ko yanzunma kika ga ya fad'o trapped d'ina..I have plan it since dated back da aka kama mu gurin da muke robbery.."
Kallon bai² tayi masa tace
"Ban fahimceka ba..!
"Ohhh.! Lemme summarise it for u babe,, a wancan lokacin da nake fad'a miki ya taba yiwa d'aya ckin sibglins d'ina k'wace,, so after then nasa aka kamo min shi da nufin na hukunta shi,,duk da naso na azabtar da shi ne ta hanyar da ko wani ba zai sake sha'awar yayiwa ba bare cikin ahalina,but a lokacin sai ya nuna min yayi nadamar abunda yayi,bayan nasa ya dawo min da abunda suka kwace sai nasa aka kyale shi,,kwatsam wata rana muka sake had'uwa da shi,but a lokacin yana tare da gang d'insa ne da suke yiwa mutane k'wace,kasancewar ni kad'ai ne time d'in su kuma suna da yawa shi yasa sai banyi k'ok'arin yin wani ba,cos babu komai a jikina time d'in nd i know at that time idan rana ya kwace suna iya yimin illah,da fari gaskiya bansan ko su waye ba saboda fuskokinsu a rufe suke da mask,har suka kwace kaf kayan da suke tare da ni ban iya na gane mutum d'aya ba a cikinsu,,har lokacin da suka juya zasu bar wajen ban fahimci daga inda suke ba,buh lokacin da suka d'anyi nisa da ni ina ji wani cikin wad'anda suke taren yayi masa magana,a wannan lokacin KUSKURE da yayi shi ne mafi girman KUSKUREN sa a rayuwa,tabbas da ya san zanyi wani abu na tabbata bazai bari yayi magana ba,sanadin wannan amsar daya bawa wancan,ita ce tasa na gane shi ne kuma sunyi b'adda kama saboda kada na gane su,,haushin wannan abun da yayi min yasa tun daga wannan lokacin na k'udurce sai na d'auki FANSAR abunda yayi min akansa.."
Tsananin mamaki ne ya bayyana saman fuskar Sabina sanda ya gama bata labarin hankali a d'an tashe tana kallonsa tace
"Idan har na fahimce ka,wad'annan abubuwan da yayi maka su suka sa daka k'udurce ramuwa sai ka jefa shi cikin wannan bala'in ko..!?"
Dariya yayi yace "Yeah! Gaskiya kina saurin ganewa,,,to amma me yasa da fari baki gano bane.!?"
Murmushi tayi daya bayyana hak'oranta tace
"Komai nufin Allah ne,,sannan ko wane case dole kafin a gano bakin zarensa dole ne sai an fuskanci wahala,,gwargwadon binne shi,gwargwadon wahalar da za'a sha kafin a gane,,, so na gode sosai da wannan bayanin daka yi min,nd i know ko babu komai yanzun na samu hujjar da idan har na tabbatar da shi a court ko da ace k'arya kayi min,for sure zai taimaka a sake min d'an uwa.."
Dariya yayi yace "Ta ina ne zai je court d'in..!?"

Tace "Kai zaka bada bayanin a gaban al'ummah.."

"Ba zai tab'a yuwuwa ba,,tunda d'an uwanki ya shigo cikin wannan matsalar ya fad'o kenan babu shi babu fita.."

"For sure zai fita,,kasa ido zaka yi kallo.."
Tana fada tayi murmushi sai ta juya zata fice,mistakenly yasa hannu ya rik'o gefen hijab d'inta yana huci da nufin jawota ta dawo shi kuma Hammad ya sako kai cikin d'akin,,akan hannunsa daya rik'o hijab d'inta idanunsa suka fara sauka,yana shirin mata magana ya shigo amma abunda ya gani yasa kalmomin duka sai suka mak'ale suka k'i fita,nan da nan b'acin rai ya fara bayyana akan fuskarsa,kafin k'iftawar idanu tuni har ya bayyana a gabansu,cikin tsananin hucin kishi ya shak'o wuyansa ya had'e shi da katangar d'akin guda d'aya,,ko ita kanta Sabinar lokacin data juyo a bazata taji an rik'o mata hijab,so ta waiwayo da nufin hukunta shi sai kuma taga Hammad tsaye a gabansu rik'e da wuyan wancan d'in,ran y'an maza ya gama b'aci ko gama daidaituwa a gurin bai ba ya fara kai masa mari,naushi,bugu,a jere² yake sauke masa su babu k'ak'k'autawa har sai da ya fara fitar masa da jini,tsabar mugunta irin na Hammad a time d'in dukansa kawai yake da iya k'arfin da Allah ya bashi,yana yi yana cije lips d'insa saboda zugin kishi dake sosa masa zuciya,shigowar wani prison officer da dama shi ya shigo musu da shi yayi saurin rik'e Hammad daya zare k'aramar pistol d'insa dake mak'ale jikinsa yana bashi hak'uri,sam baya jin abunda yake fad'a cos ya riga da yayi loosing temper a lokacin,rik'e shi ya sake yi dan ganin har ya d'ana kunamar bindigar yana fizgewa sai ya harbe shi,,hankalinta a mugun tashe itama tayi saurin rab'a jikinta a nashi ta k'ank'ame shi tana bashi hak'uri amma still fizgewa yake yana huci da fad'in
"Ku banni da shi na hallaka shi,,dan ubansa bai san matar aure ba..?? Ku rabu da ni na koya masa hankali tunda shi mahaukaci ne.."
D'ayan jami'in yana rik'e da hannun Hammad a sama gudun kada ya aikata abunda yayi niyya,yake alerting security'nsu akan su kawo musu agaji,kafin wani lokaci d'akin ya cika da jami'an tsaro anata bawa Hammad hak'uri,shi kuwa cikin k'arajin masifa sai cewa yake
"Wane hakur'in zan yi..? Mata ta zai rik'e..?? Da ban zo ba wa yasan me yayi niyyar yi mata..?? Kaiiiii..! Kaii!! Kaii!!! Dan Allah ku kyale ni na hallaka shi ko zan samu sassauci.."
Ya wani runtse idanu yana murza forehead,idanunsa tsabar damuwa tuni suka rine sun koma jajaye dasu tamkar wuta
"Ku barni na hukunta shi ko zan samu sauk'in abunda nake ji a zuciyata.."

"Yallab'ai dan Allah kayi hak'uri,, mu ma nan zamu d'auki mataki a kansa.. Ku dai kawai kuje abunku.."
Sake k'ank'ame shi take yi tana shafa bayansa amma ko kulawa baiba k'ok'arinsa ta sake shi,ita dai duk a tsorace take ta yi masa dabaibayi
"Ki sake ni mana.."

"Please HABIBIIY relax.. Ka kyale shi kawai.."
Wani banzan kallo yayi mata yace "Saboda kin mai dani sauna ko dan me..?? Akan mene ne zai rik'e miki mayafi..?? Sai na hallaka shi.."
Yana fad'a yana b'amb'are hannunta data zagaye shi da shi,,in a calmness way take sake rik'e shi tana fad'in
"Dan Allah ka bari HAYAT,,idan ka kyale shi da zafin hukuncin dake kansa ma ya ishe shi,ni dai ka bari kawai mu tafi gida.."
Tana gama fad'a tace jami'in su fita da shi kawai,,ita kuma ta sake rik'e shi duk da ba k'arfinsu d'aya ba,shi kansa dan yana tsoron yayi kwakwaran motsi ya ji mata ciwo ne yasa ya rabu da ita ta rik'e shi,amma da tuni ita kanta yayi cilli da ita saboda b'acin rai,cikin sauri kuma da kyar aka janye wancan d'in aka fita da shi daga d'akin a tsorace,,sai data tabbatar sun fita d'akin ya rage daga ita sai shi sannan taja hannunsa ta zaunar da shi kan kujerar data zauna d'azun,ta kamo kansa ta rungume da duka hannunta tana tsayen tana shafawa slowly,tunda ta fara shafa sumar kansa zuwa fuskarsa ya runtse idanunsa yana sauke ajiyar zuciya,ba ita ta sake shi ba sai data tabbatar ya fara dawowa nutsuwarsa sannan ta rik'o hannunsa tace
"Muje..!"
Babu musu ya mik'e amma kana kallonsa kasan har lokacin ba wai ya gama dawowa dai² bane,tafiya take yana binta tun daga Offenders room d'in har inda yayi parking,sai daya fara bud'e mata ta shiga ta zauna ba tare daya kalleta ba yace
"Jira ni ina dawowa.."
Sai ya juya ya bar gurin,magana take son yi masa dan bata san ina zai jeba da yace ta jira shi,hankalinta duk a tashe kada ya koma cikin prison d'in sai kuma taga ya matsa can kusa da wasu mutum biyu dake gefe yayi magana da su,ko me ya tambayesu bata sani ba,sai dai ta ga ya sake matsawa jikin wani k'aramin shop,duk bata san me yayi ba a gurin amma hankalinta ya d'an kwanta tunda taga bai koma ciki ba,cikin k'ank'anin lokaci ya sake dawowa jikin motar ta b'angaren da take,knocking window d'in dake side d'inta yayi bayan zuwansa,a hankali ta sauke glasses d'in saboda masu duhu ne,sai taga ya mik'o mata hannunsa da fad'in
"Ciro min wannan abun ki bani..!"
Kallonsa tayi da mamaki tace "Me zan baka ne..!?"

"Wannan abun na jikin ki nake nufi.. Ciro ki bani.."

"Hijab!?" Ta tambaya tana zaro idanunta,,"Ehhh! Shi nace.. Mik'o min kafin raina ya sake b'aci.. "
Babu musu ta cire ta mik'a masa,ko daya karb'a bai jira ba ya matsa can gefe had'e da sawa hijab d'in wuta akan idanunta tana kallon,,tsananin mamaki sosai ya bata dan tab'a zato ba,yana tsaye a wajen yana kallon yadda wutar ke ci har hijab d'in ya gama k'onewa sannan ya zagayo ya tada motar suka bar wajen.

Har suka k'araso gida babu wanda yayi magana,shi da abunda yake damunsa,itama kanta da nata damuwar,but na tan a lokacin kam a iya cewa da sauk'i akan nasa,ko da ya gama parking bai jirata ba da sauri ya fice a fusace,itanma da saurin tabi bayansa,lokacin data shigo sai

Please Login or Register in order to submit comment