Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kawai yayi kamo ne a kwancen,haka ma maganar da suka fara da Mamma,sai dai tun daga lokacin da suka fita a d'akin nan ya bud'e idanunsa a hankali yana dafe kansa da yayi masa nauyi kafin ya d'an mik'e a hankali ya jingina bayansa jikin pillow,maganaganun Daddy ne suka fara masa yawo akai,tabbas yasan dole ne a samu matsala,kamar yadda yasan ko wane ne mahaifin nasa,haka ma ra'ayinsa akan su,,ya jima zaune yana tunani daban² akan matsalar kafin ya tashi a daddafe ya nufi bathroom.

A can b'angaren Mamma kuwa ko data fito daga bedroom d'in k'asa ta sauka tayi zamanta a parlor,tunanin abun duniya duk ya sata gaba,a lokacin ji take inama ace tana da hali,tabbas da sai dai ayi duk wacce za'ayi akan maganar,,ta jima zaune a parlor'n shiru kafin ta mik'e ta nufi kitchen da niyyar shirya ma mai gidan nata abinci.

A b'angaren Daddy shima tun daya fita a d'akin bai ko sake bi takan Mamma ba,haka halin da Hammad d'in yake ciki bai sake dubawa ba,a haka har aka d'ebi tsawon kwanaki biyu ba tare da wata maganar kirki ta gifta tsakaninsu da shi ba,duk da yana garin kuma a cikin gidan amma sam idan har yana zaune baza kaji yayi musu magana ba,idan har ka ganshi yana walwala ko hira to k'addara tsakanin Bassam ne ko *BADRA* a tare da shi,bayan su kuwa indai ya kama Mamma ko Hammad nan zaka ga yana shan k'amshi.
A cikin wannan yanayin ne jikin Hammad d'in yayi sauk'i,yayin da kwanakin suka yi dai² da lokacin da suke shirin komawa skul.Tun daren ranar Saturday bayan sun gama tsayar da maganar komawarsu skul shi da sultan,a lokacin bayan ya dawo gida misalin k'arfe 8:pm ya yanke shawaran sanarma Daddy.Kamar ko wane lokaci yana shigowa ya iske su duka a parlor suna sauraren labarai a BBC NEWS,gefen Mamma ya nufa sannan ya nemawa kansa guri ya zauna,cikin ladabi ya gaida Daddy sannan Mamma,duk da a ciki² Daddy'n ya amsa bai wani damu ba dan yasan dama za'a rina,,duk da dai har yanzun Daddy'n bai tada masa maganar ba,buh yasani tun a kwanakin da aka yita dole ne duk ranar da suka had'u ya zazzaga masa fad'an da yayi masa tanadi,Mamma kam cike da so da kulawa ta amsa masa,sannan Badra dake jikin Daddy ta kallo shi tana fad'in
"Yah Hammad sannu da dawowa.."
D'an murmushi yayi mata yana jinjina mata kai alamun amsawa,murmushin ta mayar masa sannan ta sake maida hankalin ta akan labaran da suke sauraro,nan Bassam ma ya masa barka da shigowa,bayan ya amsa masa duka parlor'n ya sake d'aukar shiru har zuwa lokacin da aka k'are labaran.
Daddy ya kalla yana son yi masa magana buh duka yaga ya maida hankalinsa akan Badra dake masa zancen skul itama,,Duk abunda yake yi idanun Mamma na kansa,dan haka cikin kulawa ta dafa hannunsa dake daf da ita tayi masa alama ta hanyar lumshe idanunta akan ya kwantar da hankalinsa,d'an murmushin k'arfin hali yayi mata sannan k'asa² kamar mai tsoron faruwar wani abu ya furta
"Daddy..! Dama gurinka na zo..!"
Da fari Daddy shiru yayi kamar bai ji shi ba,har sai da Mamma ta d'ago ta kalle shi kafin ta maimaita masa
"Yallab'ai..! Hammad yana magana,nd naji kayi shiru baka ce komai ba.."
D'agowa yayi da kansa cikin had'e rai kafin ya furta
"Sarai naji shi,,na kuma ji abunda ya fad'a.!"
Yanayin amsan daya bayar yasa dukansu da suke zaune kowa hankalinsa ya koma jikinsa,ita kanta Mamma'n yanayin da yayi maganar nan take yasa taja bakinta bata sake ko da tari ba,,Jikin Hammad a sanyaye ya sunkuyar da kai kafin ya furta
"Daddy..! Dama ina son sanar da kai ne cikin satin nan zamu yi resuming skul.."
Tun kafin ya rufe baki tuni har Daddy ya furta
"Allah ya tsare hanya..!"
Sannan ya sake jan baki yayi shiru,,sake sunkuyar da kai yayi cikin sanyin jiki duk da ya fahimci yanayin da Daddy'n yake ciki buh bai fasa magana ba
"Buh..Daddy..!"

"Buh daddy me..!? Me zanyi maka Hammad..??"
Kansa a k'asa ya runtse ido,cikin zuciyarsa banda addu'o'i babu abunda yake ja akan Allah ya sanyaya zuciyar mahaifin nasa
"Tambayarka nake, me zan maka..??"
Sai daya sauke dogon ajiyar zuciya kafin ya furta
"Daddy batun fare ne (kud'in tafiya) nake son yi maka.."
Sai da Daddy yayi murmushi kafin ya kalle shi yana fad'in
"Wane kud'in zan baka..!? Ni ne zan d'auki kud'ina na baka,al'halin ban isa na saka doka abiba..? To bari kaji,kasan Allah k'wandala idan har daga aljihuna zai fito daga yau matuk'ar baza ayimin biyayya ba,babu wanda zan sake amfanawa komai in dai da dukiya tane..Dan haka kana da zab'i biyu,ko dai kayi abunda nake so,nima nayi maka abunda ya dace a matsayin mahaifi,ko kuma kayi wanda ranka ya zab'a maka amma ka sani zan zare hannuna da duk wani tallafin da nake baka..Saboda haka zab'i ya rage naka.."
Shiru duka parlor'n suka yi gaba d'aya maganar Daddy babu wanda bata sa yaji damuwa ba
"Amma Daddy nifa banyi maganar aure ba,yanzun kawai dai..!"

"Hammad..! Kenan rainamin wayo za kayi ne..?? shi kenan mu bar wannan magana,,ina fatan kaji duk abunda na fad'a maka,dan haka daga nan zuwa lokacin da zaka zo ka same ni akan ka janye maganarka,ka shirya ganin abunda baka yi tsammani ba.."
Tun daga haka Daddy bai sake masa magana ba,,ga Hammad kuwa magana yake son sake yi amma sao Mamma tayi saurin dafa hannunsa tana girgiza masa kai alamun yayi shiru,sai daya kalleta kafin yaja bakinsa yayi shirun kamar yadda ta umarce shi,,bayan kammar mintuna goma,yayin da parlor'n ya koma shiru tamkar gidan makoki,dan haka nan Hammad yayi musu sallama sannan ya nufi sama,yayin da yake jin zuciyansa tana masa babu dad'i,akan yadda Daddy'n ya nuna maganar ma baya da buk'atar jinta,,yana barin gurin Mamma ma tabi bayansa,kai tsaye ta nufi bedroom d'insa nan kuwa ta tarar da shi zaune yayi shiru fuskarsa bayyane da damuwa mai girma,a kusa da shi ta zauna tana shafa kansa,sam bai san ta shigo ba sai data tab'a shi sannan ya farga da zuwanta,ajiyar zuciya ya sauke kafin ya zame ya kwanta a jikinta yana ci gaba da sakin ajiyar zuciyan,a hankali ta fara shafa kansa cikin sigar rarrashi da kulawa har na tsayin wani lokaci ba tare da wani a cikinsu yace komai ba.....






#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••
_Devoted to my lil 6ters *Real hafsy & Mamah Zee.*_
_Bestowed to *Sis Hubbeey.*_

*Bismillahir-rahmanir-rahiim.*

_A new year is like a blank book,the pen is in ur hands,it's ur chance to write a beautiful story for yourself. *Happy Islamic New Year 1441A.h.* to u my F³(Family,Friends & Fan's.💝_

_Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un..😢 Innalillahi maa akhaza walahu maa a'ad'a wakulli shai'in indahu bii ajalin musamma, faltasbeer waltahtatheeb,,Allahummagfirha allahummarhamha..👏_
_We were disturbed and saddened by the untimely death of our sister,,yah Allah ka jik'an sister Maryam ka kyautata makwancinta,sannan ka raya mana abunda ta rasu ta bari cikin kiyayewa da karewarka..👏_


*17*
_#Doubtable_

A hankali Hammad dake kwance jikin Mamma ya d'ago kai ya kalleta,yadda tayi shiru tun shigowarta har yanzun ta kasa cewa komai,yanayin da ya ganta ciki sosai yasa shi jin damuwa dan yasan ko mene ne yake damunta a lokacin,tofa baya rasa nasaba da damuwarsa nd haka dama take idan har zata ga d'aya cikin yaranta a damuwa yanzun sai aga duk ta koma cikin damuwan itama,kansa ya sake mayarwa ya kwantar a saman cinyanta while yana facing fuskarta,a hankali cikin damuwa ya bud'e bakinsa da yake jin yayi masa nauyi ya furta
"Mah..! Me yasa Daddy zai min haka ne,,me yasa bazai fahimci halin da nake ciki ba..I have already know myself,me yasa daddy shi ya kasa fahimta,,anya Mamma Daddy yana son farin cikina..!? Ya kamata ki fahimtar da shi matsalar da zan iya shiga idan ya hana ni..Please Mah..!"
Sai data sauke dogon ajiyar zuciya while idanunta suna kansa tana kallon fuskarsa kafin ta nisa ta fara magana
"Kada kace haka Yarona,,mahaifinka na sonka kuma yana son farin cikin ka,ba iya kai kad'ai ba,dukanmu ya damu damu,,kamar yadda na san halayensa nasan kaima ka san wasu a ciki,dukan ku babu wanda ban san halayensa ba,saboda ina rayuwa a tsakaninku,,,na san halayen mahaifinka ba bak'on abu bane a gurin mu,ni da ku duka mun san shi,mun kuma san shi d'in mutum ne mai kafewa akan ra'ayinsa,dukkan maganar daya fad'a baya tab'a canjata,saboda haka bamu isa muce zamu ja da shi ba ko mu iya canja masa tsari,,sai dai abu d'aya ne zan fad'a maka a yanzun,kuma shi ne ,an ta maimaita muku,a duk halin da zaka tsinci kanka abu na farko da nake son ka fara tunawa shi ne Allah,,nasani kuma kaima ka sani matuk'ar ka kai kukanka gare shi bazai tab'a tab'ar da kai ba,idan har ka ambace shi da lafazin daya dace ka nemi k'ariy'arsa da taimakonsa na tabbar zai taimake akan ko wane irin AL'AMARI,sannan abu na biyu ahi ne ka kiyaye kanka da bawa shaid'an hanyar da zai gurb'ata maka rayuwa da tarbiyyar da muka yi shekaru muna ginawa,abu na uku shi ne duk runtsi duk wuya ka kasance mai biyayya akan maganar mahaifinka,matuk'ar bawai ya sab'a dokar ubangiji ba,in sha Allah da sannu alkhairi zai kwankwasa maka k'ofa,,idan har kana da damuwa kada ka gaza wajen kai kukanka ga mahaliccinmu,dan shi kad'ai ne zai yaye maka duk wani k'unci daka tsinci kanka a ciki,ta hanyar musanya maka shi zuwa sauk'i,,abu na k'arshe kuma shi ne ka kasance mai rik'o da addini a duk inda ka tsinci rayuwarka,ka zama mai kiyaye amana,sannan ka kasance mai cika *ALK'AWARI* idan har ka rik'e wad'annan a matsayin abokan rayuwa to ina tabbatar maka cewa za kayi rayuwa ba tare da samun wata matsala ba,idan kuwa har kaga wani damuwa ya same ka,to ka k'addara cewa ya faru ne ba don komai ba sai don saboda ubangiji (S.W.T) yana son ya jarrabi imaninka.!"
Doguwar ajiyar zuciya ya saki,,yayin da yake jin kalamanta suna masa yawo had'e da ratsawa ta cikin jini da b'argonsa,nd cikin k'ank'anin lokaci sai ya fara jin wani irin sanyi da rahama suna sauka a jikinsa,tabbas shawaran Mamma'nsa a irin wannan halin na damuwa abun so ne gare shi,a duk lokacin daya tsinci kansa a damuwa matuk'ar tana kusa da shi takan yi k'ok'arin tunatar da shi,haka nan takan sashi jin samun nutsuwa akan harma yayi kokarin mantawa da damuwarsa da irin wad'annan nasihohin nata,shin shi kuwa da wane irin abune ya kamata ya biya ta irin wannan alkhairin..? Tabbas babu,sai dai ya k'udurcewa ransa a kullum zai kasance mai yi mata addu'ah tare da fatan dacewa duniya da lahira.
Magana yake son sake yi,amma maganarta duka ta saukar masa da wani irin kasalan da har yasa shi jin bazai iya sake cewa komai ba,dan haka ko da yayi shiru,Mamma'n nasa bata fasa masa nasiha ba,tsayin lokaci suna tare ba tare data tafi ta barshi shi a halin damuwa ba,a hakan da suke tun shigowarta tana ta fad'a masa sanyayyun kalamai bacci mai nauyin gaske ya d'auke shi,lokacin data tabbatar yayi bacci,fuskarsa ta zubawa idanu tana kallonsa,yayin da zuciyarta take cike da tausayinsa.
A wannan lokacin ba ita ta tashi barin d'akin ba sai data tabbatar baccin sa yayi nisa sannan ta kwantar masa da kansa a saman pillow,mantle taja ta rufe shi half sannan tayi masa addu'ah had'e da d'ora masa peck a chicks ta kuma shafa kansa,hanyan fita a d'akin ta kama bayan ta tabbatar tayi masa deactivating na fluorescence ta fita,fitowarta tana k'ok'arin rufe masa k'ofan yayi dai² da lokacin da Daddy yazo wucewa,bai yi mata magana ba illa binta da kallo kawai da yayi,dan haka itama bata ce masa komai ba,nan kowa ya wuce ya nufi hanyar bedroom d'insa,cikin zuciyar Mamma kuwa ko da taga ya wuce,sai data rakashi da ido sannan ta sake binsa da fatan Allah ya ganar da shi gaskiya kafin ta shige ciki itama.

Bisa al'adarta duk dare kafin ta kwanta takan yi shafa'i da wutri,dan haka kai yanzunma ko data shigo d'akin kai tsaye ta wuce toilet da niyyan d'aura alwala,sai da tayi wanka sannan ta d'auro alwala,tana fitowa bata tsaya shafe² ba,ta shirya cikin kayan baccinta masu taushi sannan tabi duka jikinta da sanyayyun turaruka masu sanyin dad'i,ta kuma yi shirin fuskantar mahaliccinmu,,ko bayan data idar da sallah ta jima tana addu'o'i kafin ta tattara hijab d'in da pray mat ta adana.Kana ta fita bisa al'adarta ta biyu a duk dare bayan tayi sallah idan har ta fita kafin ta wuce d'akin mai gidan nata sai ta duba duka yaran idan ta tabbatar duka suna d'akunansu sannan ne itama take tafiya ta kwantar da hak'ark'arinta,fitowar ta sai data fara duba d'akin Badra,nan ta isketa a kwance a lokacin tuni har tayi bacci,addu'ah tayi mata had'e da gyara mata kwanciyan sannan ta fita zuwa d'akin Bassam,shi kam zaune ta ganshi saman bed yana latse² a computer gefensa kuma litattafai ne yana ta aikin research,addu'ah tayi masa had'e da fatan alkhairi daga nan kuma ko data fito sai ta nufi d'akin Daddy.Da sallama a bakinta ta shigo sai dai fuskarta babu wani isashen walwala,zaune ta tarar da shi saman royal bed d'insa ya mik'e k'afafu,gefe da gefensa kuma tari takardu ne yana dubawa,k'arasawa tayi ciki ta nemawa kanta gurinzama a d'ayan side d'in na gadon sai dai bata yi magana ba har zuwa tsayin lokacin data tabbatar ya gama abunda yake,hannunta tasa ta taya shi tattara takardun while tana d'an kallon sa k'asa² sannan ta saki ajiyar zuciya
"Yallab'ai..! Ni kuwa tun d'azun nake son muyi magana da kai akan matsalar Hammad..!"
Yana gaban wooden vault d'insa yana jera takardun dake hannunsa tayi maganar,ba tare daya juyo ba bare tasa ran ya d'auki maganar da muhimmanci ya furta
"Idan kin san maganar da za kiyi ba shida amfani a gurina kadama ki fara yi min ita.."
Wani iri ta kalleshi saboda maganar daya fad'a ko kad'an baiyi mata dad'i ba,amma duk da hakan sai ta daure taci gaba da fad'in
"Amma fa Yallab'ai ya kamata ace kayi nazari akan maganar nan,sannan ka duba irin hukuncin daka yanke,yana da kyau ka saussauta wannan masa,a rayuwar nan da muke ciki a yanzun,kuma a matsayinka na babban alkali da k'asa ke alfahari da kai nasan da wuya ace ka iya k'ididdige adadin rape cases da ke wakana a cikin jihar nan ma,bare ace mun tafi lissafin na k'asa baki d'aya,baka san dalilin da yasa yaron nan ya fito kai tsaye ya nuna maka abunda yake ransa ba,ni dai har ga Allah ina jin tsoron faruwar wani AL'AMARI akan rayuwarsa...!"

"Asiya..! Me yasa ne bakya jin magana.? Tun da farko na shaida miki na gama yanke hukunci akan wannan maganar, saboda haka ki kyale ni da wannan magannar,aure ne banyi ra'ayin yi masa a yanzun ba,dan haka zan gargad'e ki akan tayar min da maganar,ko da wasa daga yanzun har zuwa lokacin da Hammad zai hattama karatunsa bana so na sake jin maganar nan ta sake tasowa..!"
Sakato tayi tana kallonsa har ya k'are maganar,duk da jikinta yayi sanyi da lamarin zuwa yanzun,dan a yadda take ganin yana nuna fushi akan maganar hakan kad'ai ya isa yasa ta fahimtar lallai ba zai tab'a canjawa ba,a jiyar zuciya ta sauke mai nauyi tana jinjina kai,cikin takaici gami da zullumin irin wannan baud'ad'd'en ra'ayin nasa ta sake kallonsa
"Shi kenan Yallab'ai.. Naji na kuma amince kamar yadda kace,in sha Allah bazan sake tada maka maganar ba,amma ina son ka san cewa,kamar yadda kace baka so maganar mun barta da izinin Allah,daga yanzun bazan kuma yi maka ita ba,haka shi kansa Hammad zanyi iyakar k'ok'arina nayi calming nasa akan maganar,,amma ina so kaji tsoron Allah,sannan ka tuna da lahira,kamar yadda ubangiji ya sanyaka ka zama shugaba a garemu baki d'aya,ka tuna da cewa ubangiji zai tambayeka akan hak'k'ok'inmu da suka rataya a wiyanka,sannan kada ka manta da hadisin Annabi (S.A.W) da yake cewa:"Dukkaninku masu kiwo ne,kuma dukanninku ababen tambaya ne abisa kiwon da aka baku,shugaba mai kiwo ne,za'a tambaye shi akan kiwon da aka bashi,namiji/miji mai kiwo ne abisa iyalinsa,haka kuma za'a tambaye shi akan kiwon da aka bashi,mace mai kiwo ce abisa gidan mijinta,haka nan itama za'a tambayeta abisa kiwon da aka bata,bawa mai kiwo ne abisa dukiyar uban gidansa,za kuma a tambaye shi akan abin kiwonsa" Sannan Annabi (S.A.W) ya sake cewa:"Ku saurara,dukan nin ku ababen tambaya ne akan kiwon da aka baku.!" Shin Yallab'ai wannan ba lamari ne da ya kamata ace munyi duba akansa ba a matsayin mu na mahaifa wad'anda Allah ya bawa kiwo ba.? Ya kamata ace muyi iya k'ok'arin mu wajen kiyaye tarbiyyar yaranmu fa,bai kamata ace kai da zaka tunatar da wani kayi k'ok'arin aiki da abunda ka san babu shi addini ba,kayi nazarin magana ta.."
Ajiyar zuciya ya sauke yana sake kallonta har zuwa lokacin da ta yi shiru
"Shi kenan na ji,na kuma gode,amma ki bani lokaci zan duba maganar ki.."
Daga haka ya rufe vault d'in sannan ya nufo gadon,inda ya tashi nan ya koma yanzun ma,sai dai wannan karon yana zuwa kwanciya yayi had'e da rufe idanunsa ya shiga jera addu'o'i,,Mamma kuwa jin abunda ya fad'a sai yasa hankalinta ya d'an fara kwanciya amma duk da hakan bawai ta sa rai hundred percent bane akan zai bi shawarar tata,sai dan kawai tana saka rai akan la'alla ubangiji zai karkatar da hankalinsa zuwa ga hanyar gaskiya,dan haka take ta sake k'udurcewa ranta zata sake jajircewa wajen yin addu'ah har zuwa lokacin da Allah zai sa ya yarda ya amince da abunda yaron nasu yazo da shi
"Yallab'ai.!"
Ta sake kiransa a lokacin daya kwanta,ba tare daya d'ago ba ya furta
"Dan Allah Asiya ki kyaleni haka nan da maganar nan,ya kamata ki san cewa dare fa yayi..Yanzun ba lokacin daya kamata ace muna wannan maganar bane.."
Sunkuyar da kanta ta d'anyi kad'an kafin tace
"Haka ne Yallab'ai.. Buh dama ba wani abu zance maka ba illa maganar fare da Hammad yayi maka d'azun,,ina son baka hak'uri ne dan Allah,kaga yazo matakin k'arshe,idan aka ce ka janye tallafin ka akan karatunsa,komai fa yana iya faruwa.."

"Uhhuumm..! Sai aka yi yaya kenan..!?"

"Ehh! Toh dama ina son ne nace maka..!"

"Asiya kenan,ni da Hammad ai mun gama magana,saboda haka babu ruwan ki a cikin wannan matsalar,magana ne tsakanina da shi,idan yaji maganar da nayi zai zo ya tuntub'e ni da zancen ko kuwa..!?"

"Haba ranka ya dad'e,, Kayi hak'uri mana, kamar yadda kace Hammad yaro ne,ni da kai duka mun san da hakan,amma ni abunda nake tsoro game da maganar nan,kadafa muje garin son gina rayuwarsa ya zama munyi k'ok'arin rusata da hannunmu,ka fahimci magana ta.."
Shiru ya sake yi yana jinjina kai sannan ya ce
"Shi kenan na fahimta,,amma dai ki bari nayi tunanin.."

"Toh Yallab'ai,, Allah yasa muji alkhairi.."
Da "ameen" ya amsa mata,daga haka yayi kwanciyarsa danma kada ta sake cewa wani abu sai ya juya mata baya,a lokaci guda d'akin yayi shiru yayin da zuciyar kowannensu take cike da tunanin abunda d'an uwansa ya fad'a,haka ma kowannensu tunanin da yake yi da hangen sa sai ya zama ya bambanta dana d'an uwansa.

A gefen Hammad kuwa tun gabanin asubah ya farka,nan fa ko daya duba baiga Mamma ba,a lokacin sai ya kalli agogo,yadda yaga lokaci yayi nisa ne sai ya gane cewa yayi bacci mai nisa,,zama yayi shiru yana sake tunani akan maganar daddy da yace masa zab'i ya rage nasa,idan zaiyi masa abunda yake so,shima zai masa abunda ya dace a matsayinsa na mahaifi,to shin idan ya sab'a hakan na nufin hukuncin Daddy yana nan na cewa da yayi zai zare hannunsa akan duk wani tallafin da yake bashi..!? Irin wad'annan tunanukan sune suka yita ma Hammad yawo a cikin kai,tun daya farka yake zaune shiru ba shi ya motsa ba sai daya fara jin ana kiran sallah sannan ya iya tashi a gurin,toilet ya wuce ya d'aura alwala sannan ya fita zuwa masallaci.
Lokacin da aka idar da sallah bai dawo gida a lokacin ba,sai da gari ya fara haske,ko daya shigo a lokacin gidan shiru,sai yayi shirin fita morning exercise,kamar ko wane lokaci ya fito cikin shirinsa sanye cikin sport wear na company *NIKE* yayin da k'afarsa ke sakaye cikin buffer running leisure sports shoe masu matuk'ar kyau da suke d'auke da tambarin dake nuni da cewa suma d'in sun fito ne daga company Nike,ficewa yayi a gidan yana riding abun sonsa wato bike na specialized allez,kai tsaye cikin race course ya nufa inda a kowane safiya idan har yana gida tofa ba shi da gurin daya wuce masa nan d'in,,almost two hours da wasu mintuna ya shafe sannan ya fito daga race course yayin da jikinsa yake jik'e da gumi,,shigowarsa cikin gidan ya iske babu kowa a parlor ko da yaga haka shima bai tsaya neman inda suke ba ya wuce hanyan staircase,direct bedroom d'insa ya isa ko da shigarsa nan ya fara k'ok'arin cire kayan dake jikinsa,lokacin daya rage daga shi sai boxer's nan take duk wani suffar k'arfi ya bayyana a jikinsa,saman resting chair ya zauna yana ajiyar numfashi,sai daya samu ak'alla wasu mintuna yana zaune kafin ya tashi ya nufi bathroom da niyyar yin wanka.
D'aure da towel ya fito wanda ya tsaya masa iya waist yayin da hannunsa yake rik'e da mini towel da yake goge sumar kansa zuwa sauran sassan jikinsa,yana tafe yana fi gaba da goge jikinsan,har ya nufi gaban mirror kamar wanda akace ya dawo sai kuma ya nufi gefen bedside drawer inda ya zube wayoyinsa,a hankali ya mik'a hannu ya d'auko galaxy d'insa sannan ya shiga neman line Sultan dan a yau yake son su k'are magana da shi kan yadda zasu yi wajen komawa skul a goben,,kira kusan uku yayi masa ba tare da yayii answering ba,dan haka kawai sai ya yanke shawaran idan ya fita sai ya bi ta wajensa,mayar da phone d'in yayi ya ajiye yana d'an cije lip,har ya juya zai bar wajen ya sake dawowa,da sauri ya d'auko phone d'in yana sake dubawa,alamun sak'on daya gani ta inbox yasa shi saurin shiga da niyyar dubawa,sunan Mamma ya gani a guda while d'ayan kuma ko daya duba daga bank ne,sak'on Mammansa ya fara bud'ewa ya shiga duba abunda ta rubuto d'in
"Mrng Babynah..Na shigo ban ganka ba,buh nasan ka fita tun d'azun,, idan ka dawo ka same ni za muyi magana.."
Murmushi kad'ai yayi sannan ya fita ba tare daya duba d'ayan text message d'in ba da niyyar zuwa gurinta yaji maganar da tace masa za suyi d'in,lokacin da ko daya fito daga bedroom d'in d'akin ta ya fara dubawa sai dai bai ganta a nan ba,ganin haka

Please Login or Register in order to submit comment