Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta ne a cikin y'an satittika amma idan ka ganshi sai kayi zaton ya shafe tsayin shekara a kwance,,wanda cikin wannan lokacin bisa taimakon ubangiji da yawan kai masa kuka da yake yi,baya ga addu'ar mahaifa gami data y'an uwa zuwa abokan arzik'i ya fara samun sauk'i har ya fara iya fita da kansa,sai d'an abunda ba'a rasa ba,ragowar b'urb'ushin ciwo,wannan kuma mun san dama sai a hankali sannan komai zai koma dai²,,,tun daga wannan jinyar gaba d'aya sai ya sake komawa tamkar wani hearing impaired,magana idan ba da wani na jikinsa ba shi d'inma shak'ik'i gaba d'aya ya daina yinta,kuma ko da tambayarsa kayi idsn bai so ba ko d'aga idanu bazai yi ba bare kasa ran zai kalleka ko samun damar amsa maka,,ya daina zaman hira da kowa,dariya ko murmushi duka ya daina yinsu ga kowa,yayin da ya koma tamkar wani namijin zaki,,a kowane lokaci ya gwammace ya zauna shi kad'ai yayi shiru yana tunanin,idan ya gaji kuma ya koma tuna irin moment da suka yi sharing a tsakanisu,,idan kuma yaji kewarta ya dame shi sosai haka zai d'auko head tie d'in data d'aure masa hannu yayi ta kallo yana sauke wahalallun ajiyar zuciya,,takardar da baffa ya rubutama lokaci zuwa lokaci yakan d'auko ta yayi ta kallo,idan hakan bai masa ba kuma sai ya koma karantawa,yana bin ko wane harafi dai² kamar lokacin da baffa ke karanta musu.
Yana zaune yayi zurfi cikin duniyar tunani wayansa dake ajiye gefensa tayi k'ara,a hankali ya kalleta sannan ya kauda kansa zuwa gefe,,duka idan yana cikin irin wannan mood d'in ko kad'an baya son wani abu ya shigo masa,,,dan haka nema ko daya kalla saboda baiyi niyyar d'auka ba sai ya d'auke kansa daga kallon wayar,har ta katse aka kuma kira bai yi attempting d'auka ba,tsaki yaja cikin fushi a karo na uku ya d'auka wayar ba tare daya kula da sunan dake kan wayar ba cikin fad'a² ya furta
"Bance bana son a dameni ba ne..!?"

"Sorry..! Sir..!!"
Muryan Mamma ya katse shi,saurin bud'e ido yayi yana duba screen d'in wayan,tabbas sai yanzun idanunsa suka ga abunda ke rubuce,surprisingly yace
"Mah..!?"

"Ranka ya dad'e..!"
Itama ta fad'a while tana sakin murmushi
"Am sorry Mah,, buh banyi zaton kiranki bane shi yasa..! Amma kiyi hak'uri.."

"I knew..! Ai yallab'ai.."
Katse kiran yayi saurin yi,yana sauke ajiyar zuciya had'e da matse forehead d'insa dan duka baiyi tsammanin Mammansa ce take kira ba tun farko da ko kad'an bai yi abunda yayi ba,tashi yayi ya fita da sauri dan yasan da kamar wuya ace ba nemansa take yi ba tunda ta kira shi,ta bedroom d'inta ya fara dubawa bcos yasan a irin wannan lokacin bazata wuce can ba,a nan d'in kuwa ya isketa lokacin daya bud'e k'ofa,tana zaune saman pray mat,k'arasawa yayi ciki ya zauna yana jira ta idar da addu'ar daya isketa tana yi,,itama Mamma ko da taga ya shigowa nan da nan sai ta tak'aita,bayan ta idar ta juyo tana kallonsa fuskarta babu yabo bare fallasa,sannan ta fara masa magana cikin muryan lallami
"Son..! Dama gani nayi tunda Allah yasa yanzun kaji sauk'i,, shine nake so muyi wata magana da kai.."
Sunkuyar da kai yayi k'asa a hankali kuma ya amsa mata da
"Toh Mah..!"

"Ina fatan ka san akan abunda zanyi maganar..!?"
Ta tambaye shi al'halin tana mai tsare shi da idanuwanta,sai daya girgiza kai kafin ya amsa da
"A'a Mah.."

"Ok.. Da kyau toh.."
Saurin kallonta yayi cikin sark'ewar baki yana fad'in
"Buh Mah.. Why baza ki sanar da niba,,da gaske nake ban san akan mene ne zaki yi magana ba. I swear.."

Idanu ta lumshe masa alamun shi kenan nd ya kwantar da hankali,,shiru yayi yana kallonta da had'iye yahu,ita kuma Mamma taci gaba da magana
"Na san baka sani ba,,nd duka abunda nake magana akansa ba wani abu bane face akan rashin tafiyarka,,dan ni dai har yau ina zaune ne cikin duhu,ba tare dana san takamaiman dalilin faruwar al'amarin ba,sannan ku duka babu wanda yayi k'ok'arin sanar dani daga kai har shi Sultan d'in da na ganku tare,,na tambaye shi kuma ya nuna min shima bai sani ba,to abunda dai ban sani ba shi ne mene ne abunda kuke ta b'oyewar tsayin wannan lokacin..??"

"Mah..! Bafa wani abune,,kawaifa dama damuwa ce ta haifar da ciwon..Amma bayan nan babu komai.."
Tsare shi ta sake yi da idanunta tana jifanshi da kallon ban yarda ba kafin ta magantu
"Ni wai kake fad'awa wannan shirmen..?? Nd kana so na yarda ko..!?"
Marairaicewa yayi yana fad'in
"Da gaske Mammana babu komaifa,,ki yarda dani..Kin san ban saba yi miki k'arya ba.."
Yadda yayi da fuskarsa nd tasan har yanzun yana kan matakin shan magani,yasa sai kawai ta jinjina masa kai badon ta amince ba,sai don kawai tana tsoron abunda takurashi ya fad'a mata gaskiya zai haifar,,bayan ta gama kallonsa tace yaje ta sallame shi,a sad'ad'e ya tashi ya bar d'akin dan tuni ya gama karanto rashin yarda afuskarta,bayan yayi mata sallama yayi saurin ficewa a d'akin danma kada tace ya dawo,a hankali Mamma ta girgiza kai bayan taga fitarsa tausayinsa fal zuciyarta.

Washe gari tun da safe kiran wayar Daddy ya shigowa Mamma,bayan ta d'auka sun gaisa,ya tambayeta yaransu da gida,itama ta tambayi aiki,sun gama gaishe² Daddy yake sanar da ita labarin skul d'in da su Hammad suka yi *UNIVERSITY OF NORTH FLORIDA* tana neman mutum goma daga cikinsu,nd gudun ma kada a samu sab'ani wasu daban da basu ake buk'ata ba suje,yasa suka yi specifying sunayen wad'anda suke buk'atar,,Mamma dai kam ko da taga bata fahimci inda maganar Daddy ta nufa ba tayi caraf ba tare da tayi k'waron baki ba ta tambaya
"To amma Daddy,, mu mene ne had'in mu da wannan labarin..!?"

"Haba Asiya..! Yanzun duk baki fahimci komai ba daga cikin maganar da nayi..!?"

"Wollahi alhaji ni kam dai ban fuskanta ba.."
Takaitaccen murmushi yayi mata
"Ai matsalar da aka samu dama tun farko baki tsaida hankalinki kan yadda za'ayi ki gane ba,al'halin kuma ko a cikin magabata na fad'a miki mak'asudin kiran.."

"Me kace to..!? Ina tunanin ban jiba kam gaskiya.."
Sai daya sake murmusawa kafin cikin zolaya ya furta
"Idan na maimaita mene ne tukuici na..!?"
Murmushin itama tayi tana fad'in
"Ka fad'a tukuna,,idan dan tukuici ne ai sai ka zab'a..!"

"Sure.!?"

"Ehh! Da gaske.."
Still ya sake yin murmushi sannan yace
"Toh shi kenan,,ki duba wayarki zaki ga amsar tambayar ki a ciki.."

"Haba Daddy..! Maimakon ka fad'a min da bakinka shi ne sai an bani aiki..!?"

"Ba aiki bane,,ki duba d'in dai da kanki ina ganin zaifi miki sauk'i ma.."

"Toh..! Shi kenan,bari na duba d'in, tunda so ake dai a wahalar da Shari'a.."
Dariya Daddy yayi mai sauti yana fad'in
"Wace shari'ar..??"
Sai bayan Daddy ya maimaita sannan Mamma ta fahimci abunda yake nufi,dariyar itama ta sake yi kafin ta rufe maganar da fad'in
"Irin wacce yallab'ai yake yi.."
Tana fad'in haka tayi saurin katse wayan tana darawa,shima Daddy a b'angaren sa ko da yaji ta katse kiran dariyar yayi a fili kuma yana fad'in
"Asiya kenan,,Shari'a irin wacce muke yi,ai ba dai² take da sauran shari'ar da kike ji a labari ba.."

Can a gefen Mamma kuwa,lokacin data katse kiran email d'inta ta shiga dan ta duba sak'on da Daddyn yace zata gani,da short video tayi arba wanda daga dukkan alamu kuma kana gani kasan a tsakiyar abu ne akayi cutting d'insa,murmushi tayi kafin tayi playing nasa,,,tsaf ta gama kallon videon yayin da fuskarta ke bayyanar da wani irin sihirtaccen murmushi.Ko bayan data gama dubawa ms ita ta fara neman Daddy suka yi magana akan lamarin,a nan tsakaninsu suka gama tattauna duk yadda tafiyar Hammad zata kasance,kafin suka yi sallama yana sake tabbatar mata da lallai ne nan da zuwa dare zasu sake yin magana bayan ya tuntub'i Hammad d'in,daga nan duka suka ajiye wayar.

A wannan daren saboda maganar da Mamma ta yiwa Hammad akan abunda yake damunsa kuwa tun daya fita gaba d'aya sai ya kashe wayoyinsa,dan haka ko da Daddy ya kira shi yaji a kashe sai ya sake kiran Mamma'n yana mata complain na jin wayoyin Hammad da yayi a rufe,hak'uri ta bashi dan itanma a lokacin bata san dalilin aikata hakan ba,,wanda a b'angarensa shi kuma gogan,wasa² tun daga ranar da tayi masa tambayar dalilin kwanciyarsa rashin lafiya ya koma wasan b'uya da ita kamar wasu surukai,duk inda yasan zai ganta baya tab'a bari yaje bare su had'u,yayin da a gefe guda kuma wayoyinsa suke kashe babu ta yadda za'ayi tayi saurin binciko shi,tun tana kiran cikin kwanciyar hankali har lamarin ya fara bata tsoro²,tayi kiran tayi jiran ganinsa amma duka bata sauya zani ba,a hakan kuma har lamarin ya fara neman fin k'arfinta,dan haka ko da taga zata jefa kanta a damuwa sai ta hak'ura ta fawwala lamatin wa ubangiji,duk da zuwa lokacin da abun ya fara damunta sai ta k'udurce tarfa shi a dai² lokacin da bai zato ba.A ranar kuwa tayi sa'a dan gaba d'aya ma baya gidan,dan haka bayan data bincike d'akinsa bata same shiba,ta koma parlor cikin shirin zaman jiran shigowarsa.

A bangaren Hammad kuwa dai² wanman lokaci da Mamma ta kafa tarkon son ganinsa,suna kan hanya suma d'in a tsakiyar traffic,,yayin da Sultan d'in ke driving kan hanyarsu ta dawowa daga *Y'AN KABA,,* k'addararsa ta kira shi,yayin da tasa su biyowa ta hanyar *MAIDUGURI ROAD.*
Dai² lokacin suna tsaye tsakiyar traffic,,tsabar tsokana irin ta Sultan dake driving a hankali sai ya juya bayan ya d'an kalle shi fuskar da murmushin zolaya kwance samanta,sai dai baiyi magana ba,,a lokacin kuma ba komai ya ja shi ba illa ganin da yayi,Hammad yayi shiru kamar baya cikin motar,,juyawa Hammad yayi daga kallon ginin gidan *INDOMIE* da yake na dai² kwanar maggi,wacce itace idan mutum yabi ta d'od'ar zata sada shi har cikin *UNGUWAR KAWO,,,* wani mahaukacin kallo ya watsa masa a dalilin dariyar da yake yi,wacce ta dad'a assasa jin tsaiwar da suke yi,,dama kuma gaahi tun bayan daya tashi daga jinya abu kad'an yanzun sai yasa yaji haushinka,,,sai daya ja tsaki fuskarsa a had'e babu alamun fara'a,har ya bud'e baki da niyyar tambayarsa abunda ya gani na dariya ,dan shi gaba d'aya haushinsa d'aya yaji ana dariya a kusa da shi baya ga takaicin mak'alewar da sukayi a traffic d'in daya dame shi,abu goma da ashirin sun had'ar masa,d'aga idanunsa daya zuba Sultan yayi cike da son shafe fushin da yake yi na ganin shima Sultan d'in ya had'iye dariyar,idanunsa suka masa bazata can daga d'ayan hannun nasu.....




#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••
*Alkhairin Allah yaci gaba da kasancewa tare da ku masoyana..Ina matuk'ar alfahari da ku.💗*

*27.*
_#Prodigy_


Fuskarta ya hango zaune ita kad'ai sanye da uniform farin hijab nd light blue d'in riga da wando a cikin keke napep,banda murmishi abunda take ta zabga abunta alamun dake bayyanar da tana cikin farin ciki,fuskarta a lokacin tana kallon wani gefen daban,,Idanunsa ya dasa a gurin yaci gaba da kallon kyakykyawar fuskarta dake cike da fara'a ba tare da yana blinking idanunsa ba,,yadda take cikin farin ciki a lokacin haka nan shima sai ya tsinci kansa da mugun farin cikin daya jima bai yi irinsa ba,wanda sakamakon ganinta a dai² lokacin da baiyi zato ba ya haifar masa
"Shukhraan ya k'adiiyr.."
Ya fad'a k'asa² yayin da yaci gaba da yiwa Allah godiya a zuciyarsa daya had'a shi da farin cikin rayuwarsa a lokacin da yake tsananin buk'atar hakan,,hannun da abun hawansu yake aka fara bawa hannu,ko kafin yayi magana da Sultan tuni har Napep d'in da take ciki ya fara tafiya,suna baro wancan hannun sun shigo dai² kwanar gidan maggi yaga napep d'in ya sake tsayawa,maza ne guda biyu a gurin tsaye wanda da dukkan alamun su suka tsayar da shi,idanunsa ya sake d'orawa a gurin yana jiran ganin ta inda zasu bi su shiga sai ganinta yayi ta fito a ciki su kuma sun shige,a lokacin guda ta sake yin murmushi bayan ta d'anyi magana da mazan da suka tsayar da napep d'in nasu fuskarta da wannan uban murmushin,wani mahaukacin kishi ne ya fara rufe masa ido,nan da nan ya fara ganin duhu na mamayarsa,lokaci guda fara'ar dake saman fuskarsa ta fara disashewa,gashi su d'in har lokacin ank'i basu hannu,zazzafar iska ya fesar yana sake kallon side d'in da napep d'insun yake tsaye sai dai a lokacin har sun bar gurin,kallon Sultan yayi yana fad'in
"Dude..! Ka bi wannan hanyar.."
Yana maganar yana kallon napep d'insu da yayi nisa,kallonsa Sultan yayi saurin yi da mamaki a fuskarsa
"Me yasa..!?"

"Cewa nayi kawai ka bi nan,,ban ce ka tambayeni ba.."
Harararsa Sultan yayi yana tab'e baki
"Idan nak'i kuma fa..!?"
Da sauri ya juyo a fusace ya kalleshi
"Idan ka k'i kace..!?"
D'age masa gira Sultan yayi alamun haka yake nufi,,girgiza kai kawai Hammad yayi kafin ya nuna masa waje da fad'in
"Fita..!"

"Idan na fita ina kake tsammanin zanje..!?"
A tsawace ya sake magana yana cewa
"I said,,get out..!"
Murmushin yak'e Sultan yayi masa yana fad'in
"Kai yanzun idan nace zan fita a tsakiyar traffic d'innan sai ka bari..!?"
Tsaki yayi yana kallon hanyar da suka bi
"Ooh! Shet..!"
Ya fad'a yana runtse idanunsa dan a lokacin tuni suka yi mugun nisa,,juyowa yayi idanunsa jajir ya kalli Sultan a dai² lokacin da fitilar bada hannu ta sake su,take motar Sultan yayi kafin ya karkata ya d'ebi hanyar data shiga Kwanar maggi
"Dallah malam idan bazaka iya tuk'inba ka fita ka bani guri,kana abu kamar baka da kuzari.."
Kallonsa Sultan yayi ya masa murmushi sannan ya sake bada wuta suka bi hanyar da mahaukacin gudu.

A gefen su Sabina kuwa,lokacin da mai napep d'insu ya tsaya,kasancewar ita kad'ai ce a ciki,ko da ganin zai d'auki mutum biyun nan duk da bata ji dad'in had'a ta cikin abun hawa d'aya da maza da mai napep d'in yake shirin yi ba,sai bata yi magana ba tayi shiru,har suka gama daidaitawa,suna niyyar shiga ta d'an kallesu fuskarta da fara'ar dole
"D'an uwa dan Allah ko zaku shiga ciki,inda zan sauka babu nisa sosai,dan ina ganin kamar zan riga ku sauka.."
Kai d'aya daga ciki yayi saurin girgiza mata yana murmushin shima sannan ya ce mata
"Babu komai.."
Fitowa tayi saurin yi daga ciki suka fara shigewa,a dai² lokacin ta sake yin murmushi tana fad'in
"Na gode.."
Sannan ta koma ta zauna a takure daga gefe,tana kallon waje ranta duk babu dad'i
"Aikin banza kawai,su masu abun hawan nan sam basu san hak'k'in wad'anda suke d'auka ba,,in banda tsabar wulak'anci ina dalilin had'a mace da namiji a cikin abun hawa d'aya..Sai kace ba musulmi ba.!? Kawai dan suna tak'amar abun hawansu ne sai suyi ta wulak'anta passenger.! Wollahi duk ranar da wani ya sake min haka Allah sai ya yabawa aya zak'in ta.."
Na kusa da ita ne jin tana mita duk da ba jin abunda take fad'a yake yi ba ya d'an kalleta yana murmushi
"Hajiya magana kike yi ne..!?"
Saurin juyowa tayi ta kalle shi,cikin zuciyarta tana addu'ar Allah yasa baiji me tace ba,,murmushin yak'e tayi masa tana girgiza kai
"A'a'a..! Babu komai.."

"Uhhuumm..! Na zata kince wani abu ne..!"

"A'a..!"
Sake juyawa tayi tana kallon waje,cikin mitar abun tana fad'in
"Kaji min mutum,,sai kace wanda na kasa da shi,har da wani tambayata abunda nace..Kamar nayi magana da shi.."

"Uhumm! Hajiya nace ba..!?"
Saurin waiwayowa tayi tana murmusawa
"Meya faru kuma..!?"
Ta tambaya cikin rashin sanin abunda zai sake cewa
"Sunanki nake so ki fad'a min idan babu damuwa.."

"Me jin suna na zai amfana maka kuma..!?"
Tana fada tana murmusawa
"Babu komai,,kawai na tambaya ne,idan babu damuwa a taimaka a fad'a min.."

"HAFSAH.."
Ta fad'a a tak'aice, murmushi yayi da fad'in
"Suna mai dad'i.."
Bata juyo ba bare yasa ran zata kalleshi ta furta
"Na gode.."
Sai ta kuma yin shiru tana sake karkata kanta gefe
"Ranki ya dad'e..!"
Runtse idanunta tayi cikin zuciyarta ta furta
"D'an anace kenan..Me kuma zan maka..!?"

"Idan babu damuwa zan iya sanin inda zaki.!?"

"Gida..!"
Ta fad'a cikin yanayin gajiya da amsa masa,girgiza kai yayi yana fad'in
"Da kyau.."
Sai kuma yayi shiru shima bai sake magana ba,,sunyi tafiya mai d'an tsayi daga kwanar maggi zuwa *KAWON MAI GARI* sannan Sabina tayi magana
"Malam idan ka samu guri zan sauka.."

"Toh..! Hajiya",ya fad'a yana tsayawa a gefen hanya,jakarta dake rataye saman kafad'arta ta nemi saukewa ta sallami mai napep d'in,mutumin da yayi ta mata surutu d'azun ya lek'o daga ciki yana fad'in
"Hajiya..!"
A sad'ad'e ta d'ago dan ita kam zuwa lokacin Allah ya sani kuma har zuciyarta ta fara tsoron yin magana dashi,haka nan take jin fargabar tsaiwar da take bare kuma maganarsa da a duk kalma d'aya da zai tambayeta takejin zuciyarta tana tsananta bugu,baya ga gargad'i da wani sashi na zuciyarta ke yi mata
"Nace ba..!?"
Idanunta akansa ba tare data samu damar amsawa ba,irin kallon da take masa ne ya sashi yin murmushi kafin yace
"Zaki iya tafiya.."

"Me yasa zan tafi,bayan ban sallami mutum ba..!?"

"Ki barshi kawai.."
Kallon rashin fahimta taci gaba da binsa da shi,murmushin still ya sake yi,sai dai bai ce mata komai ba,kallon mai napep tayi da shima yake murmushi lokacin,za tayi magana yayi saurin taron numfashinta
"Hajiya kinga kawai kije tunda ya fad'a miki.."
Fuskarta cike da mamakin kalaman mai napep ta sake yunk'urin yin magana again ya tare ta
"Hajiya an riga an biya miki,kije kawai Allah ya sanya alkhairi.."
Maganganunsu duk a hard'e taje jin suna shiga kwakwalwarta,tana tsaye ba tare data tafi ba suka ja napep suka yi gaba abunsu,tsaiwa taci gaba da yi a gurin tana mai bin hanyar da suka bi da kallo,sai da taga sunyi mata nisa sosai kafin ta juya ta kama hanyar da zata kaita line gidansu,a zuciyarta tana tunanin kalaman mai napep da suka tsaya mata a rai in da yace
_"Hajiya an riga an biya miki,kije kawai Allah ya sanya alkhairi.."_
To itafa wannan Allah ya sanya alkhairin ne ta kasa fahimtar abunda ake nufi da shi,har ta shiga gida bata daina tunani da juya maganar a ranta ba.Shigowarta kenan ta iske Inna sunkuye a bakin rijiya tana janyo ruwa,sallama tayi jikinta a d'an sanyaye sannan ta k'araso ciki,d'agowa Inna tayi bayan ta amsa tana fad'in
"Sannu Uwata.."
D'an murmushi tayi tana amsawa,kafin ta durk'usa tana fad'in
"Inna barka da gida.."

"Yawwa y'ar nan,,yanzun nan na gama zancenki ashema kina tafe.."

"Ehh! Inna ai yau jarabawar ce bamu yi da wuri ba,shi yasa ban dawo tun d'azu ba.."

"Toh! Allah dai ya fito muku da kyakykyawan sakamako.."
Da "ameen" ta amsa sannan Inna tayi mata izinin ta shiga ta cire kayanta ta huta,amsawa tayi cikin ladabi sannan ta mik'e ta shige cikin d'aki.

Iya k'urewar gudun daya kamata ace mutum yayi musamman inda yasan ba hanyar motoci bane kawai Sultan yake yi amma cikin wani hukunci na Ubangiji duk iya kar dubawarsa da hangawa ya duba sai dai ya nemi napep d'in daya d'auko ta ya rasa,,gashi sai ci gaba suke da tafiya kamar zasu k'ure malejin hanya,sabon tashin hankali ya sake ziyartarsa,yayin da gumin tsananin tashin hankali ya shiga keto masa,bai juyo ba bare ya kalli Sultan ya ce
"Tsayar da mota.!"
Kallonsa Sultan yayi da rashin fahimta dan shi bai san me yake faruwa ba har lokacin
"Kamar yaya na tsaida mota..!?"

"Cewa nayi ka tsaya..Idan baza kayi ba zan fita."
Mahaukacin brake Sultan ya taka,ko gama tsaiwa motar bata yi ba tuni har ya bud'e murfin ya fice,lek'owa Sultan yayi ganin ya tafi baice masa komai ba
"Malam..Wai me yake damunka ne..!? Da fari kace mubi hanya,yanzun kuma ka fice baka cemin komai ba...Me yake faruwa ne wai..!?"

Bai juyo ba nd still yana ci gaba da tafiya,cikin muryan jin haushi yace
"Zaka iya tafiya.."
Saurin fitowa

Please Login or Register in order to submit comment