Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kawo ni.."
Inna ta kalleshi da mamaki a fuskarta
"Malam me kuma muka saka mantawa haka..??"

"Ehh! To dama na zo ne na shaida miki ki ya kamata a had'a abinci a kaiwa *MUHAMMADU..!"*
Fuskarta d'auke da alamun tambaya taci gaba da kallonsa kafin tayi k'arfin halin tambaya
"MALAM wane ne haka..??"
Shima ita ya kalla yana murmusawa kafin ya bata amsa da
"Yaron daya taimaki d'iyarki mana shi nake nufi ai..!"

"Aihoo! To..Bari kuwa na hanzarta..!"
Tana fad'a tayi saurin mik'ewa,shima baban fita yayi yana cewa
"Idan kin gama ki bawa uwata ta kai masa yana can tare da Yaya..!"
Da "to" ta amsa masa fuskarta sai murmushi take saki,tayi hanzarin d'auko wasu gidauniyoyinta sababbi dake ajiye ta fita,nan suka bar Sabina shiru tana tunani a ranta tana tambayar kanta
"Dama sunansa kenan..??"
Tun fitar Inna sai ta tsinci kanta da fara y'an tunanuka akan abunda ya faru d'azun,wani abu daya bata dariya lokaci guda shi ne tuna irin yadda yake bawa su LADO umarni tamkar wani fatherhood nasu,data tuna irin kallon da yayi mata sai ta sake sakin murmushi,tana cikin wannan halin sai ga Inna ta dawo d'auke da k'aton tray a hannunta tana fad'in
"Yawwa uwata maza taso da sauri ki karb'a.. Kada a bar mutum da yunwa ko..??"
"Toh" tace kafin ta d'auki wani hijab d'in tasa,tray d'in dake hannun Inna ta matsa ta karb'a kana ta fice a d'akin,Inna na bata sak'on ta gaishe shi idan taje,nan ma ta sai ta sake amsa mata da "toh" d'in,,,cikin nutsuwarta take tafiya har ta kawo bakin k'ofar bukkar da suke ciki,a dai² bakin k'ofar sai ta d'an tsaya shiru tana tunanin abunda zata yi,ko kafin tayi sallama nan kunnuwanta suka tsinkayi muryansa yana cewa baffa zai tafi,hakan sai yasa ta sake k'amewa a gurin tamkar wacce akayi sculpturing nata ba tare data motsa ba,haka nan sai ta shiga bin tray d'in hannunta da kallo,a zuciyarta tana jin rashin dad'in abunda ke shirin faruwa.....

_Aradun Allah zan dakata da posting a wattpad,saboda wannan lokacin naga bakwa Voting,,idan har bakwa jin dad'in littafin nan ku sanar dani,naga fan's d'ina na Facebook da whatsapp su kam suna so,dan haka zan koma yi musu posting su kad'ai.😧😧_


#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••
_Devoted to my lil 6ters *Real hafsy & Mamah Zee.*_
_Bestowed to *Sis Hubbeey.*_

*Bismillahir-rahmanir-rahiim.*

_Aunty *MOUNATH (O.G)* + Cweet *LEEMA* aradu ban tab'a iya manta daku,dan a duk lokacin da Aunty tayi kwana biyu bamu ganta ba ko bamu samu labarin inda ta shige ba,kune kuke sawa gida yayi albarka,a had'u a sada zumunci,,ina yi muku fatan alkhairin Allah ya ci gaba da wanzuwa a tare da ku a ahalinku,a kullum kuma akoda yaushe ina k'ara yi muku fatan kasancewa cikin amintattu kuma yardaddu a gurin Ubangiji (S.W.T),Rabb yasa yadda zumunci ya k'ullu a tsakaninmu a nan duniya har a aljannah ma mu zauna tare.✊_

_Kyakykyawar sanarwa kuma dama ga masoya mabiya rubutun *HAWWA M.U (REAL SMASHER)* hak'ik'a ina mai farin cikin son nayi amfani da wannan damar wajen shaida muku cewa shahararren littafin nan da muka kammala a y'an kwanakin da suka gabata mai suna *WANI AL'AMARIN Book 1&2* yana nan a manhaja ta YOUTUBE,ya fito ne daga zauren *DAUSAYI TV CHANNEL* wanda *MAMAN AL'AMEEEN* take jagoranta,an sarrafa shi zuwa audio novel domin sauk'ak'awa ga wad'anda zama su karanta littafin a page yake yi musu wahala,dan haka wannan sauk'ak'ak'k'iyar hanya ce kuma dama zuwa gare ku mabiya,ga masu buk'ata kai tsaye zaku iya subscribing na *DAUSAYI TV CHANNEL* akan wayoyinku a manhaja ta Youtube,domin samun naku a kusa.☝_

*5*
_#Journey_

Muryan Baffa ta jiyo yana cewa
"A'a mai babban suna baza muyi haka da kai ba,,ai tunda ka shigo gidan nan yau kam ba zaka tafi ba har sai ka ci wani abu..!"
Murmushi yayi mai sauti kafin ya bawa baffa amsa
"Baffa..! Wollahi sauri nake yi ne na koma makaranta saboda ina da aji yanzun,duk da ma dai nayi latti,tun d'azun ya kamata ace na koma makaranta na shirya.!"

"Ehh to.! Duk da haka nima bank'i ka tafi ba amma dai tabbas sai ka sawa cikinka wani abu kafin ka wuce d'in,ai kai yanzun ba bak'o bane,kaima d'aya ne daga cikin ahalinmu kaga kuwa babu ta yadda za'ayi mu barka ka tafi ba tare da ka ci wani abuba..!"
Murmushin dai still ya sake yi ba tare daya iya cewa komai ba bare yayiwa baffan musu yaja bakinsa yayi gum,,har lokacin Sabina tana tsaye a bakin k'ofar cikin rashin jin dad'in abunda taji yana fad'a sai dai ko da taji amsar da baffa ya bayar nan take sai ta saki siririyar ajiyar zuciya kana ta bud'e bakinta da ada yayi mata nauyi tana rangad'a sallama,dukansu ne suka amsa mata kafin baffa yace
"Shigo mana SHALELE kika tsaya a waje..!"
A hankali ta matsa jikin k'ofar had'e da janye jigataccen labulen dake k'ofar kana ta shiga tana sake yin wata sallamar
"Yawwa y'ar albarka kamar kuwa kin san maganar da muke yi kenan,ai gara da kika yi hanzarin zuwa.."
Murmushi ta d'anyi sannan ta matsa gabansa ta ajiye tray d'in,,muryan baffa taji yana fad'in
"Uwata..! Ki zauna tare da shi ni zan d'an fita na dawo yanzun nan,kada ki barshi shi d'aya yana jira kinji ko..??"

"Toh baffa..Allah ya tsare hanya..!"

"Ameen uwata..Allah yayi muku albarka..!"
Baffan ya fad'a yana dafa kanta,sannan ya juya ga MUHAMMAD yana cewa
"To mai babban suna zan fita na dawo amma ba jimawa zanyi ba,in sha Allah yanzun zan dawo.."
A hankali ya d'ago kansa ya kalli baffan yana murmusawa shima ya amsa masa da cewa
"To baffa Allah ya kiyaye hanya..A sauka lafiya..!"
Nan baffan ya fita yana amsa musu,,bayan fitar baffa a d'akin sai Sabina ta bud'e babban kofin silver dake saman tray d'in wanda ta shigo da shi,,kyakykyawan damu ne na fura daya ji nono tayi haske,banda k'amshin kayan yaji babu abunda take,ba tare data kalle shi ba ko ta tambaye shi taji zaima sha ko a'a kawai tasa masa ludayi kawai sai ta ajiye masa a gabansa,tana gama abunda zata yi sai ta koma d'an nesa da shi kad'an ta zauna tana wasa da gefen hijab d'inta kanta a k'asa ba tare data sake waiwayarsa ba bare taga abunda yake yi,,d'agowa yayi a hankali lokacin da yaga ta koma gefe ba tare data yi magana ba kana ya tab'e baki,ba tare daya ce mata ko ci kanki ba shima,ya d'auki mug d'in ya fara shan furan,lokacin daya fara shan furan tun a karon farko sanyayyan dad'i irin na furan daya ratsashi sai yasa a hankali ya shiga lumshe idanunsa,while yana yabawa wanda yayi furan a ransa,nd yana ci gaba da kaiwa cikinsa ba tare daya saurara ba,,har ya gama bai yi magana ba,haka itama tana zaune bata ce masa komai ba,ajiye mug d'in yayi dai² lokacin data d'ago kanta dan yadda zaman ya fara damunta gashi duk ta kasa sakewa a gurin,,shi kuwa a gare shi duk motsinta tana yi ne akan idanunsa,dan haka duk abunda take yi yana kula da harma da yadda take yawan yamutse fuska,akai² kuma ta sauya yanayin zamanta,lokacin kuwa ko data d'ago a karo na sau babu adadi karaf sai idanunsu suka had'u,buh ga Sabina sai tayi saurin janye idanunta tana sake sunkuyar da kanta a k'asa,,sake tab'e baki yayi can kuma kamar wanda akace dole sai yayi mata magana,muryansa cike da mulki kamar wani d'an sarki ya furta
"Mene ne dalilin da yasa kike fita da safe.? Ina nufin a irin wannan lokacin da ba kowa ne ya fito ba..??"
Yadda taji yayi maganar haka nan sai taji k'irjinta ya tsananta bugawa,within few secs duk sai ta fara neman nutsuwarta ta rasa,nd bakinta nan take sai yayi mata nauyi ta kasa amsa masa,,yana kula duk da yanayinta dan haka ko da yaga bata amsa ba sai kawai ya share bai sake tambayarta ba,duk da ya gama abunda yake zuwa lokacin amma sai bai musu sallama ba ya ci gaba da zaman jiran dawowar baffa kamar yadda yace ba jimawa zai yiba,,,sun sake shafe tsayin lokaci a hakan ba tare da wani a cikinsu yace da d'an uwansa ci kanka ba,,wanda shi kansa Muhammad d'in a da zuwa lokacin ya gama gajiya da zaman sannan lokaci bayan lokaci tunda yaji shiru baffan bai dawo ba sai ya d'ago hannunsa ya duba lokaci,haka nan kuma sai ya kalli k'ofar shigowa yaga ko baffan yana kan hanyan shigowa,,ko da dai yaga shirun na neman yin yawa sai ya sake kallon sashin da take cikin isa yana sake d'aure fuska
"Daga yau kada ki sake fita idan har baki ji alamun mutane sun fara fitowa ba ko kuma ba tare da wasu zaki fita ba,idan har dan ke kad'ai ce ki hak'ura da fitan,,sannan abu na biyu idan ina magana bana so naji anyi min shiru al'halin ana jina,,dole ne idan har nayi tambaya a nemo amsar daya dace da tambaya na,,,bana son shirme ko wasa a lokacin da nake serious magana da mutum..Hope kin fuskanta..??"
Sai data d'ago kanta jin yadda yake bata command tamkar wani Babanta ko Innarta,zuciyarta cike fal da mamakinsa dan yadda yake nuna mata isa,al'halin tasan basu had'a wata alak'a da juna ba,,sannan abun daya ke sake bata mamaki da shi kuma ta kasa fuskanta a maganarsa shi ne shin idan ya tafi ba shi kenan ba..?? Duk wani abu kuma daya had'asu zai wuce tunda dai taimakonta yayi idan ya tafi ai shi kenan kuma babu tabbacin acema su sake had'uwa,,to amma taji yana cewa idan yayi magana dole ta nemo amsan bashi,shin da ita yake ko kuwa dai kawai yana nufin ga kowama da wani alak'a ya had'a su haka yake..? Ita dai duk ta kasa gane mene ne actual abunda yake nufin,,,yadda tayi shiru ya sashi sakin wani slender breathe kafin yaci gaba da watso mata tambaya
"Mene ne alak'ar ki da wannan guys d'in..??"
Sai data sake damk'an gefen hijab d'inta kafin tayi karfin halin yin magana
"Wanne a ciki..??"
Cikin salon sake had'e rai ya kalleta yace
"What do you want me to do..? Na maimaita miki tambayar..??"
D'agowa ta sake yi ta d'an kalleshi,a hankali tayi k'wafa dan ita dai wannan nuna ikon da isar nasa ya fara hawa mata kai,sam a rayuwarta bata son d'abi'a irin wannan ga koma waye idan har ba wai ace iyayenta ba,had'e rai tayi itama sannan tace
"D'an uwa nane..!"
A ransa yace "ashe taji abunda na tambaya,take son kuma na maimaita mata" amma a fili sai ya d'an harareta yace
"Shi wanne kenan a ciki..??"
Kamar bazata bashi amsa ba can kuma sai ta ce
"Wanda suke cema sarki.."
Jinjina kai yayi kafin ya sake jefo mata wani tambayan
"Sunansa kenan shi d'in..?? Ko kuwa wannan ne sunansa kad'ai..??"

"A'a ba sunansa ba ne,kawai dai su d'in ne a tsakaninsu ne suke fad'a masa hakan,buh i think kamar dai sunan sune dai can na kangararru kuma fitinannu..!"
Jinjina kai ya sake yi yana sakin murmushin irin amsan data bashi
"Okay..! Wannan dai kina nufin kamar sunan ne da su a waje suke amfani da shi..?? Nd akwai wani sunan nasa kuma daban da kuke kiransa dashi a gida ba..??"

"Ehh! Akwai..!"
Ta fad'a a k'agauce dan ita tambayoyin nasa sun fara isarta,jinjina kai yayi cikin gamsuwa sannan cikin salon son takurata ya sake cewa
"Yayi kyau..! Amma yaya kusancinki da shi yake..?? Uhmm! saifa kinyi hak'uri da ni,haka nake da yawan son tambaya..!"

"Babu komai.."
Ta fad'a duk da ta gajin kamar yadda ya fahimta da kansa,amma kuma sai taci gaba da bashi amsar a hakan
"Shi d'in d'an k'anin Babanah ne..!"

"Ohh! Kenan family'n ku d'aya da shi..!?"

"Ehh! Haka ne.."
Jinjina lamarin yake a ransa nd yana kuma hasashen dalilin da yasa d'an uwa na jini zaiyi k'ok'arin zaluntar d'an zuwansa,kamar dai yadda ya kusa faruwa da ita a yau banda dai Allah ya kiyaye,,buh duk iya tunanin sa da son binciko ainihin gaskiyar dalilin da zai sa LADO aikata hakan iya hangensa da k'ulluwarsa ya kasa fahimtar komai,,ba tare daya kalleta ba sai dai ta jiyo muryansa yana magana
"Ina mamakin yadda za'a ce duk alak'ar dake tsakaninku da kusancin ku amma ace yayi k'ok'arin cutar dake,,buh shin kun tab'a samun wani sab'ani da shi ne..?? I mean something haka like kunyi fad'a akan wani abu da zaisa ya rik'e abun a ransa ko kuma dai wani matsala haka na cikin gida ya had'a ku..??"
A hankali ta d'an cije lip d'inta,bayan ta numfasa sannan tace
"Ehh! To nima dai gaskiya ban san wane irin dalilin ne zaisa shi yin hakan ba,buh all i knew dai ba zai wuce kan maganar aurenmu ba da aka k'i amincewa da shi..!"
With much marvel yake kallonta kafin ya maimaita
"Aure..!? Wane iri kenan..??"

Duk da maganarsa ta bata mamaki amma hakan bai hanata yin murmushi ba dan gani take kamar baya fahimtar hausa sosai ko kuma dai me yake nufi ne bata sani ba
"Aure dai irin wanda ake yi a kowane k'abila da jinsi na mutane..!"
Ta fad'a ba tare data kalleshi ba dan dama duk tambayan da yake mata tana daga yadda take tun zamanta take bashi amsa sai dai idan ya fad'i wani abu da taji shi wani iri sai ta d'ago ta kalle shi,jinjina kai ya sake yi yana tab'e baki ba tare daya sake tambayan ta komai ba duka suka sake yin shiru,,kusan mintuna biyar sun sake shud'ewa ita harma ta manta da sunyi batun aurenta da LADO sai ji tayi ya ce
"Kuma kina sonsa dama can..!?"

Idanunta ta d'ago ta tsare shi da su tana nazarinsa tana kuma nazarin amsar daya kamata ta bashi,jin yadda tayi shiru bata ce komai ba gashi ta kafe shi da ido kamar mai neman amsar a kan fuskarsa sai ya mata waving had'e da fad'in
"Hello..!!"
D'an firgita tayi kafin ta saita nutsuwarta tana jan dogon ajiyar zuciya,kana ta girgiza kai da cewa
"A'a..! Kawai dai shi ne ya samu Babanah da maganar,buh shi kuma baba sai yak'i amincewa shi ne dai ina jin sai abun bai musu dad'i ba,acewarsu wai me yasa Babanah ba zai aura masa niba tunda dama haka ake yi a gidan,shi ne sai shida Innarsa suke ta fad'an maganganu tun daga lokacin,kuma kullum cikin neman fad'a suke da Innata,amma ita bata kula su,Babanah ma da baffa sai suka ce mata duk abunda za suyi kada ta kula,shi yasa ko suna maganarma bata tsayawa a gurinsu..!"
Tun data fara maganarbyake kallonta yadda take yi tana gesturing face sai ya tsinci kansa da yin murmushi a b'oye ba tare daya bari taga hakan ba
"Ehmm! Amma me yasa d'azun dana tambayeki baki bani amsa ba..?"
Jim ta d'anyi tana son tuna mema ya tambaya,sai aka yi sa'a a lokacin yace
"Akan dalilin da yasa ki fita da safe nake nufi..!"

"Ohh!"
Ta fad'a kafin ta tab'e baki tana cewa
"Uhmmm! Goggo Tani ce ta aike ni na samo mata ruwa wai zata yi girkin safe bata da ruwa..!"

"Dama ba Inna ta aikeki ba..??"

"A'a ba ita bace..!"

"To ita d'in wace ce d'inki a gidan nan..??"
Sake kallonsa tayi sannan tace
"Itace Innar LADO.."
Shiru yayi yana nazarin sunan a ransa a fili kuma sai cewa yayi
"Babar wanda kika cemin d'an uwanki ne shi..??"

"Ehh! Shi.."
Ta fad'a tana sake gimtse bakinta daga haka ba tare data sake cewa komai ba
"Ok..na fahimta..!"
Abunda kawai shima yace kenan sai shima d'in yayi shiru yana nazarin abun a ransa da dalilin da yasa Gwaggon nata zata aiketa a safiyar nan al'halin tana da d'a namiji
"Shin me yasa bata aike shi ba shi daya kasance namiji kuma wanda take da ikon aikashi ko ina nema ta so,sai y'a mace kuma ma yarinya kamar Sabina..??"
Zuciyarsa ta watso masa tambayar
"Dole ne tana da wani dalilin da yasa ta aike ta..!"
Wani sashi na zuciyarsa ya bashi amsa a take,buh duk da haka tunanin sa har yanzun ya kasa kaiwa inda yake da buk'ata duk da yadda yake son sake takura kansa da son lallai shifa sai ya gano dalilin Gwaggon nata na aikenta a irin wannan lokacin,,dai² lokacin baffa yayi sallama wacce itace ta taimaka wajen dawo da shi daga duniyar tunanin daya nausa,,dukansu suka amsa masa,nan baffan ya shigo yana murmushi had'e da fad'in
"Kuyi hak'uri ko,na tafi na barku kuna jira na..!"
Shi kansa duk da ya gaji da zaman da fari kasancewar zaman shirun da suka yi a bayan fitar baffan,sai kuma daga baya daya dunga tambayarta tana bashi amsa sai zaman duk da yayi kuma bai wani sake damun shi ba sosai kamar da farkon,,haka nan itama gare ta,,,duka suka had'a baki a tare shi yana cewa baffan "babu komai" while ita kuma Sabina tana yi masa barka da dawowa,,one after d other duka ya amsa musu sannan ya nemi gurin zama yana kuma yi musu sannu dan yasan ya barsu sun jira shi sosai,,koda taga baffan ya dawo sai ta fara tashi,a hankali ta mik'e ta shiga tattara kwanukanta duk da dai bai tab'a abincin ba iya furar kad'ai yasha,sannan tayi hanyar k'ofa zata fita ba tare data ce komai ba,da idanu ya bita har ta fice,,yana ganin fitar ta nan sai yayi saurin kallon baffa yana cewa
"Baffa ni zan tafi..naga lokaci har ya tafi sosai..!"

"Toh..! Zaka tafin..??"

"Ehh! baffa zan koma makaranta saboda akwai wasu ayyukan a gabana,duk da dai yau nayi latti bazan samu shiga aji ba..!!"

"Toh to..! Allah sarki Ubangiji ya tsare ya kuma maida kai lafiya,,mun gode sosai da alkhairin ka gare mu,Allah kaima ya dubi lamuranka.."

"Ameen baffa..nima na gode sosai,,Allah ya k'ara girma.."

Baffa yana murmushi ya amsa masa da "ameen",sannan suka mik'e tare baffan yana cewa
"Ince dai ko zaka dunga kawo mana ziyara idan ka samu sarari..?? Tunda Allah har ya had'a mu ko..Ba wai ace shi kenan mun rabu ba..??"

"In sha Allah baffa zan dunga lek'owa idan al'amura sunyi min sauk'i a makaranta..!"

"Toh..! Masha Allah,, Allah ya bada iko.."

"Ameen" ya fad'a yana juyawa da niyyan fita while baffa na biye da shi a baya suka fito daga cikin d'akin,fitowarsu tayi dai² da lokacin data matsa a bakin k'ofar d'akin tana tafiya cikin sanyi kamar kazar da k'wai ya fashewa a ciki,,sunkuyawa yayi ya fara k'ok'arin saka takalmansa while yana bin bayanta da kallo had'e da mamakinta,,har tayi nisa da su sai ta jiyo muryar baffa yana cewa
"Uwata yi maza ki ajiye kwanukan mana kizo kuyi sallama ko..?"
Da sauri ta waiwayo ta kallo bayanta inda suke tsaye da niyyar amsawa baffa,karaf sai ta tsinci idanunsa akanta yana kallonta,,yadda ya zuba mata idanunsa duk sai taji jijiyon jikinta sun saki hakama harshenta yayi mata wani irin nauyi,,bata iya amsawa ba sai kai data kad'a sannan ta juya taci gaba da tafiya buh wannan lokacin cikin d'an sauri² take yinta har ta isa d'akin su,,a tsakar d'akin ta dire tray d'in,sai dai ko data duba bata ga Inna ba nd tana son shaida mata zata je suyi sallama,dan haka ko data ajiye d'in sai kawai ta juya cike da niyyar komawa kamar yadda baffan ya bata izini.....




#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••
_Devoted to my lil 6ters *Real hafsy & Mamah Zee.*_
_Bestowed to *Sis Hubbeey.*_

*Bismillahir-rahmanir-rahiim.*

_Fan's d'ina a duk inda kuke ina alfahari da ku,wanda na sani da wanda ma ban sani ba,kamar yadda kuke aikomin da addu'o'inku na fatan alkhairi,,ina matuk'ar godiya a gare ku tare da fatan rabb ya bar zumunci da k'auna tsakanina da ku.💝_

_*ALK'AWARIN JINI FAN'S* Ina alfahari da ku,,iya wuya kuma muna tare da izinin rabb..✊_

*6*
_#Urgent call_

Cikin nutsuwarta take takowa kamar ko wane lokaci idan tana tafiya,,tun daga nesa daya hango tahowarta yake kallonta buh idan ba nutsuwa mutum yayi ba babu ta yadda za'ayi ya fahimci hakan dan yadda yayi kamar ba itan yake kallo ba,nd yana ci gaba da saka takalmamsa,deeply kuma yana mamakin yadda halayenta suke,gata dai karamar yarinya amma sosai Allah yayi mata baiwar nutsuwa da hankali,,iya yau kad'ai daya fara ganinta,amma har ya gama fahimtar halayenta,iya zuwa yanzun gaba d'aya a cikin d'abi'unta babu wanda bai fahimta ba cikin d'an k'ank'anin lokaci da suka zauna tare,,,har ta k'araso inda ta barsun,a lokacin tuni har ya gama abunda yake yana tsaye kusa da baffa suna ta hira kamar dama can sun jima da sanin juna,ko data k'araso inda suke da niyyan suyi sallama da shi nan baffan ya kallesu duka yana fad'in
"Muje ko uwata mu masa rakiya..!?"
Murmushi tayi sannan tace
"Toh baffa..!"
Daga haka bata sake cewa wani abuba suka kama hanyar fita daga gidan tare su ukun,,a bakin k'ofar gida suka iske baban Sabina yana k'ok'arin shigowa gidan,ko daya gansu fuskarsa d'auke da fara'a ya tare su yana fad'in
"Takwara tafiyar ce ta taso..??"
Fuska a sake Muhammad ya amsa masa da
"Ehh! Baba zan koma makaranta ne nasan anata nema na yanzun..!"

"To Allah ya tsare hanya,,mun gode sosai² ubangiji ya mai da kai lafiya.."

"Ameen ya Allah,, na gode sosai nima.."

"Yawwa to a sauka lafiya,,sai gani na gaba ko..??"
Murmushi yayi a zuciyarsa yana fad'in
"Allah kenan mai had'a zumunci a tsakanin bayinsa.."
Amma a zahiri sai ya amsa masa da cewa
"In sha Allah baba idan har na samu sarari zan dunga lek'owa mu gaisawa..!"

"Toh to..! Allah ya nufa..Allah kuma ya kaika lafiya..Mun gode k'warai ubangiji

Please Login or Register in order to submit comment