Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


"Uhhuumm.! Ku kuka sani,amma dai ku sani babu mai kwanciya wollahi sai anyi sallah damu a jam'i.."

"Haba dude,,wannan wane irin tsari ne to,tun ba'ayi sallar ba kace sai mun jira..?"
Ci gaba yayi da tafiyarsa ba tare daya juyo ba,Sultan cikin jin haushin dukan daya masa yace
"To wai ina ruwanka da yin sallar mu a jam'i..?? Idan munyi ai kanmu za mu yiwa ko.!? Wannan ai shishshigi ne.. Ina ruwanka idan ba muyi a jam'i ba..?"

"Uhhuumm.! Allah yasa ban ji me kuka fad'a ba.."

"Kaji sarai.. D'an iska babu abunda baka ji ba.."
Dariya yayi ba tare daya sake magana ba ya ci gaba da k'ok'arin saka jallabiyar dake ajiye saman resting chair,yana gamawa har yayi nufin kwaniya wani irin yunwa ya taso masa,a hankali ya fara tuna rabon daya sawa cikinsa wani abu tun safe daya sha coffee,cikinsa ya d'an tab'a a hankali daya fara damunsa bcos sosai yake jin yunwar a lokacin,tab'e baki ya d'anyi kad'an sannan a gaggauce ya kama hanyar fita daga room d'in,cike da nufin samawa cikinsa wani abu yaci kafin lokacin sallah ya riske shi,,har ya je bakin k'ofa Sadeeq ya d'ago ya kalleshi yana cewa
"Man.. Ka taho da mu.."
Bai juyo ba yace
"Me zan taho da ku d'in..??"

"Abunda duk zaka je nema,,ai mun san bazai wuce abinci zaka je nema ba.."

"Uhhuumm..! Da kun san kuna jin yunwa kuka kwanta za kuyi bacci..??"

"Haba mana,,kaifa wasu lokutan ka cika matsaltsalu wollahi..Baka uzuri ne kai a rayuwa..?"
Ci gaba yayi da tafiya yana kad'a kai,ba tare da yayi magana ba ya kama handle d'in k'ofar zai fita
"Dude! Muna jira fa..!"
Sai da yayi murmushi ya girgiza kai sannan yasa kai ya fita while yana fad'in
"Ku ci gaba da jira.."
Yana fita Sultan yayi saurin kallon Sadeeq yana cewa
"Dude.! Wollahi gara ka tashi mu bishi,wannan d'an rainin wayon wata k'ila daga can yaci gaba,dan bana tunanin zai dawo yanzun,,tunda kaga lokacin Sallah ya sake gabatowa bama zai dawo ba.."
Lumshe idanu Sadeeq yayi yana fad'in
"Kai bashshi da Allah,ni dama ba wani sosai nake jin yunwa ba,idan safiya yayi maci,tunda Allah yasa ya fice ni kwanciya zan idan an kira sallah ka tashe ni."
Harararsa Sultan yayi yana fad'in
"Ai ni d'in da yake gadinka zanyi ba,dole ka bani sallahu,,wollahi to nima kwanciya zan,Allah yasa dai daga can ya wuce kada ya dawo."
Yana maganar ya sake komawa yayi kwanciyarsa,shima Sadeeq d'in sake gyara kwanciyarsa yayi had'e da rufe idanunsa dake d'auke da bacci yana fad'in
"Asubah ta gari abokin..!"
(Ni da nake gefe na kallesu duka nace "asubah kuma ta yaushe banda wacce ke gabatowa..?")

Tunda ta kwanta bayan data idar da sallah ko k'wak'waran juyi ba ta iya yi saboda tsabar gajiyar dake bin cikin jikinta,hatta da shigowarsu Zee a d'akin da duk hirar da suka yi kafin baccin duka babu wanda ta sani bcos ta ruga su kwanciya,nd lokacin data kwanta ko mintuna goma bata d'iba ba bacci ya d'auke ta.
Around 4:15am wani irin muguwar shak'uwa ta farka da ita,cikin tsananin mayen bacci ta sakko daga saman bed d'in ta nufi mini fridge dake gefe can a room d'in,a hankali ta bud'e dan ko motsima a sad'ad'e take yinsa,ta fara neman ruwan da zata sha,kaf ta gama bincike fridge d'in bata samu ruwa ba,dan gaba d'aya ma babu komai a cikinsa,Mamma duka tasa a fitar da komai tun bayan tafiyar Badra U.S,a sab'ule ta maida ta rufe sannan ta koma bakin gado ta zauna tana tunanin yadda zata yi.Ita dai tasan idan tana wannan yanayin matsawar ba ruwan ta samu ta sha ba bazata iya komawa bacci ba,nd gashi bata san takan gidan ba bare tace ga inda zata yi saurin samun ruwa,a hankali ta mik'e ta shiga zagaye d'akin saboda yadda ta takura da shak'uwar data addabeta,,bayan kamar mintuna biyar data shafe tana zagaye d'akin,ta sake neman guri ta zauna,ci gaba shak'uwar tayi da taso mata maimakon ace ya ragu sai dad'a k'aruwa yake,,rashin samun mafita yasa tayi saurin nufar inda Badra take kwance,har ta mik'a hannu zata tada ita ta tambayeta ruwa,haka nan sai taji zuciyarta tana fad'a mata kada tayi haka,komawa baya ta sake yi tana toshe bakinta saboda sound d'in sosai yake fita musamman daya had'u da talatainin dare tsaf zai iya tashin wasu cikinsu,damuwa sosai tayi saboda bata tab'a irin wannan shak'uwar ba tunda take,k'ark'ari idan ta jimawar duniya ta kai minti biyu zuwa uku ta daina,amma yau har tana neman wuce mintuna goma tana abu d'aya,shawarar fita kawai ta yanke tunda ta rasa dukkan wani mafita,cikin sand'a ta tashi daga inda take ta nufi hanyar fita daga d'akin,taimakon da Allah ma yayi mata a lokacin har ta fita ta rufe musu k'ofar babu wanda ya motsa cikinsu,a hankali taci gaba da tafiya tana haskawa da wayarta data fito da ita tabi hanyar staircase ta sauka k'asa,,bayan ta sakko d'in ta sai tasa yatsanta guda ta rufe saman fitilar saboda ta rage k'arfin hasken,bcos bata so hasken ya ja hankalin kowa a gidan,laluben hanya taci gaba dayi a hankali tana tafe tana waige² har ta iso k'ofar kitchen,shigewa tayi saurin yi ko k'ofar bata tsaya bi takan ta rufe ba,,gawurtacciyar ajiyar zuciya ta saki mai tafe da shak'uwa lokacin data tabbatar ta shigo tsakiya,da sauri kuma sai ta janye hannunta akan fitilar ta nufi k'aton fridge dake cikin kitchen d'in,sai data fara d'auko robar guda na ruwa ta ajiye saman cabinet sannan ta bud'e drawer ta d'auko glass cup,cikin sauri ta sake d'aga robber ruwan ta b'alle murfin ta soma tsiyayawa a cikin cup d'in,kamar wani yace ta fara mik'o masa haka ta d'aga cup d'in ta kaishi bakinta,cike da son jin ruwan ya isa makogoronta ta fara d'ad'akawa cikinta,sai data shanye ta kuma k'arawa sannan ta ajiye cup d'in tana sakin sanyayyar ajiyar zuciya had'e da yiwa Allah godiya a lokaci guda,stool d'in dake gurin ta ja ta haye samansa da nufin ta huta,sannan ta janyo wayarta ta fara latsawa coz tasan ko ta koma yanzun babu tabbacin ta iya komawa bacci,,tana zaune cikin nishad'i tana kallon pictures d'insu da kusan kullum suka fita sai sunyi ta jiyo alamar kamar ana tahowa inda take,dakatawa tayi saurin yi da abunda take ta kashe hasken wayar yayin da ta maida gaba d'ayan hankalinta da idanunta a kan hanyar shigowar tana jira taga waye yake tafe.

Ko kad'an shi kansa Hammad tun daya baro bedroom d'insa ya iske cikin parlor'n bak'i k'irin babu alamun haske,baiyi gangancin kunna wutar ba yaci gaba da tafiyarsa tunda dai yasan kan gidan su,dalilin k'in kunnawar kuma shi ne baya son asan yazo a lokacin,kawai yafi so sai da safe kowa ya ganshi tunda dama yasan yanzun kam duka ahalin gidan suna bacci amma kuma yana ganin lokacin tashin su ya kusa,,haka nan zuciyarsa da tunaninsa duka basu bashi tsammanin samun wani a cikin gidan da yake idanunsa biyu ba,da k'arfinsa yaci gaba da takawa har ya gama sakkowa daga upstairs without ya kunna even torchlight da zai kalli hanya ya tunkari hanyar kitchen kansa tsaye,lokacin daya iso a bud'e ya iske k'ofar,dan haka shima sai ya shige cikin kitchen d'in,ba tare daya damu daya rufe k'ofar ba saboda dama a haka ya isketa kuma shima hakan yayi niyyar barinta,kai tsaye yaci gaba da nufar inda switch na lamps d'in kitchen suke,,k'aran da switch d'in suka bayar a tare sakamakon had'a yatsunsa da yayi guri guda ya danna a lokaci guda yasa ta d'an firgita tana dad'a fito da mayan idanunta nd ga kuma mamakin abunda ta gani,wanda shi a nasa gefen har lokacin bai ga alamun komai ba a gurin ba bare yaga mutum sukutum a kusa da shi,,juyowa yayi cike da gaggawa a niyyarsa ta samarwa kansa ko da coffee ne yayi sauri ya sha kafin a kira sallah idanunsa suka sauka kan fuskar da ko mashashshara yake aka tambayeshi bazai tab'a iya mantawa da ita ba,a mamakance duka suke kallon juna while idanunsu d'auke da wasu irin frightens suke kallon juna,sun d'auki tsayin mintuna suna kallon-kallo a tsakaninsu ba tare da an samu d'aya cikinsu ya iya furta komai ba sai nuna juna kawai da suke still sunk'i cewa komai,,da kasala a jikinta ta fara juya idanunta kafin tayi saurin lumshesu tana tsuke d'an k'aramin bakinta,hawayen da bata san lokacin da suka taho ba suka fara mata ambaliya a saman chicks,cikin muryar kuka² ta fara magana
"I knew it's not u.. Always am just looking at ur shade,,wannan mafarki ne kawai dana saba yinsa tun ba yanzun ba buh i knew it wasn't happens genuineness,,na tabbata bazan tab'a ganinka ido da ido ba..!"
A hankali kuma kuka ya kwace mata hawaye suka ci gaba da zuba daga idanunta,kifa kanta tayi saurin yi a saman cabinet yayin da take jin zuciyarta tana mata wani irin k'aik'ayin da tun da take bata tab'a jin kwatankwacin saba,ci gaba tayi da rera kukanta ba tare data bari sound ya fita ba gudunma kada ta tada kowa a gidan a sakamakon abunda take kallonsa a matsayin shirmen mafarki ko ta kira shi da tunani,,maganar da tayi dai² lokacin shiya bashi tabbacin lallai² itace a gabansa ba mafarki ko tunanin daya saba yiba,sai dai abunda yazo ya tsaya masa a rai kuma yake son sani shi ne
"Ya akayi ya ganta a cikin gidansu..?? Mene ne kum yake zaune da ita a nan d'in..?"
Yadda take gunjin kuka shi ya taimaka wajen dawo da shi duniyarsa nd ya kuma tabbatarwa da gasken ita yake gani ba shade ba,within a few seconds zuciyarsa ta bayyanar da shi a gabanta yana mai jera sakin sanyayyun ajiyar zuciya da bai san ta ina suke taso masa ba
"My Lady..!"
Ya fad'a yana sake twitching breath da kyar nd har lokacin mamakin ganinta a gabansa bai sake shi ba,saurin d'agowa tayi jin muryarsa a daf da ita,a hankali sai ta fara kalloshi tun daga kan k'afafunsa dake sanye cikin wani benassi slide sandals na maza mai kalar bak'i da fari har ta dire akan fuskarsa,still bata yarda da abunda idanunta suka gani ba ta sake binsa da kallon ta sake direwa a k'afarsa da take ta lek'awa,duka zaton ta da tunaninta a lokacin bai wuce ta hango kofato ba,coz tafi tsammanta ganinsa da gamo
"My Lady..! Mene ne kike yi a nan..?"
Ya sake yin maganar cike da shakkun irin kallon da take masa,y'ar dariya tayi wacce ta bayyana asalin sirrin kyaunta,sannan tasa hannu tana whipping hawayenta,mamakinta yake still yana tsaka da sake kallonta kawai sai ganinta yayi tsam ta mik'e zata fice,saurin tare ta yayi yana sauke mata narkakkun idanunsa
"Where do u think to go..? Ki sake tafiya ki barni ina bulayin neman ki..??"
Saurin d'agowa tayi da kanta dake k'asa,duk da zuwa yanzun da take ganinsa a gabanta har numfashinsu yana had'uwa bata gama yarda shi d'in bane da gaske yake mata magana,,saurin tafiya tayi ta fad'a jikinsa tana sakin wani marayan kuka still mara sautin kamar na farko,cikin bin umarnin zuciyarta zuwa gangar jikinta da suke mata khud'ubar ko da ace gamo ne tayi ta rungume shi ko zata samu sassaucin yanayin da take ciki,,shi kansa wani irin mayen k'arfe ke fizgarsa tunda ya bayyana a gabanta cikin azama tana fad'owa jikinsa yayi saurin d'ora hannayensa a bayanta yayi holding d'inta tight ta yadda babu wani abu daya isa ya shiga tsaninsu,ba muryansa kad'ai data shak'e ba hatta da zuciyarsa gaba d'aya a lokacin jin komai yake daban a duniyar,komai ya gama rikid'ewa,cikin muryan kuka² ya bud'e baki da kyar yace.....



*sorry guy's ban samu charge da wuri ba wollah yau,shi yasa na gaza yin typing da wuri,kuyi manage da wannan na san za kuyi farin ciki,#Team HAMMAD a daina min k'orafi,komai da kuke buk'ata ya faru,saura me kuma..??*


*If posting d'in yau yayi muku,just comments nd ni kuma nayi alk'awarin k'ara saka ku nishad'in da baku yi tunani ba,,,buh sai naga ruwan comments d'inku sannan zaku ga next page a kan lokaci,idan ban gani ba,nima zan koma gefe na huta dama ba jin dad'i nake ba yadda ya kamata cikin kwanakin nan..*

*#don't forget to comments idan har kun karanta,,bana son #Tnx ko stickers,all i want shine comments.. I told u idan babu comment's zan koma gefe musamman whatsapp charters.*



#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••
_*XEINAB ISMA'EEL KASEEM* of *ALK'AWARIN JINI FAN'S 1* sak'onki ya iso gare mu,My Mamma *(MARYAM I GITAL),I* & Habibtiiy *(MATAR SOJA)* duka muna godiya sosai,hak'ik'a bamu da bakin yi miki godiya,soyayya gamon jini ce,ubangiji shi ya dasa wannan soyayyar a tsakaninmu,muna fatan Ubangiji yaci gaba da wanzar da wannan soyayya har illah masah Allah,muna k'ara godiya sosai a gareki,ubangiji ya bar k'auna,,,#Nahna nahabbak-thtiir.❤_

*38.*
_#Blameworthy_

"Ina ne kika tafi My lady,,kinsa nayi nemanki har na kasa gano inda kika b'oye..? Me yasa zaki min irin wannan hukuncin..?? Shi kenan sai ki tafiyarki ki barni ina bulayi..??"
Bata iya d'agowa ba bare yasa ran samun amsarta taci gaba rera kukanta a ciki,wanda idan ba shi da yake manne da ita ba babu yaddaa za'ayi mutum ya san tana yi,shi kansa hawayen da suka taru a gefen idanunsa na tsabar farin ciki a hankali suka biyo gefe suna d'iga saboda ya tabbatarwa ransa idan bai zubar da su ba,ba zai dai ci gaba da jin rad'ad'in dake damun zuciyarsa tsayin lokaci ba
"Please gimbiyata..! Say something ko zan samu sassaucin abunda nake ji a zuciyata..! Shirunki yana sake sawa zuciyata shakku,da tunanin anya da gaske nake ganinki..?? Kin sa na kasa tabbatarwa kaina da gaske ne nake jinki a jikina,ko kuwa dai mafarkin dana saba yi ne har yanzun na kasa zuwa k'arshen sa..!?"
Yadda yake maganar yana k'ok'arin d'agota yasa tayi saurin sake maida kanta ta kwantar,bcos har lokacin itama bata gama tabbatarwa shi ne da gaske ba tsaye a gabanta har ta jingina da shi,rabuwa yayi da ita ta sakewa lafewa a jikinsa sai dai zuwa lokacin ta d'an sassauta kukan da take yi,muryarta a sanyaye irin na mutumin da yayi kuka ya gaji bayan tayi gyaran murta tace
"Kai zan tambaya ina ne ka tafi ka barni,,kasa na shafe tsayin lokaci inata jiran dawowarka.. Me yasa sai yanzun zaka dawo gare ni..?? Kasan tsayin lokacin dana d'auka ina jiran dawowar ka amma kak'i dawowa sai yanzun.??"
Ajiyar zuciya yayi mai nauyi a hankali yana ci gaba da caressing bayanta kamar mai rarrashinta,d'agowa ta d'anyi ta kalleshi,za tayi magana yayi saurin tarar numfashinta ta hanyar sanya yatsansa a saman lips d'inta yana cewa
"Shhhh! Ba yanzun ya kamata kiyi min duk wad'annan tambayoyin ba... Let us get some calmness Princess,sai ki tambaye ni duk abunda kike son sani,,kin ji.!?"
Girgiza masa kai tayi cike da sakarci,a hankali kuma sai ta sake d'agowa tana satar kallon fuskarsa duk da ba duka take gani ba sakamakon d'ora fuskarsa da yayi a saman kanta
"Yane My Lady.?? Ko nayi miki rowan ganin fuskar nawa ne.!?"
Kanta tayi saurin sunkuyarwa tana b'oye fuskarta a jikinsa,k'asa² ta saki murmushin da ita kanta bata san lokacin daya taho mata ba,shima d'in murmushin yayi na samun sukuni,a hankali ya sake matseta a jikinsa,zafin matsar da yayi mata yasa ta d'an saki marayan ihu,da sauri ya sassauta rik'on da yayi mata yana dariya a ciki²
"Yanzun kin tabbatar nine a kusa dake ba shade ba princess.??"
B'ata rai tayi saurin yi cike da shagwab'a tace
"To kuma dan kana so na tabbatar shi ne sai ka had'a da min mugunta..!?"

"Ohh! Sorry³.! Barin bari kada na jiwa y'ar amaryata ciwo ko..? Ko da yake ma ai idan naji miki ciwo ni zanyi jinyar ki ko.?"
Saurin d'agowa tayi ta kalleshi,shima sai ya d'ago d'in yana sauke mata idanunsa masu cike da tuhumar abunda aka yi take nasa irin kallon
"Uhhuumm.!" Tace a hankali ta fara ja da baya tana matsawa daga jikinsa,biyota ya fara yi while tana ci gaba da tafiya,a haka har sai da suka k'ure duka girman kitchen d'in,suna isa jikin cabinet ta dakata tana saurin kallonsa,kome ta tuna ta sake sauke kanta k'asa zuciyarta fal tsoro,tana tsaka da tunanin abunda ta aikata bayan ganinsa,without tayi tsammanin faruwar wani abu ta tsinto hannunsa a k'asan chin d'inta yana d'ago fuskarta,zuba mata idanunsa yayi,gaba d'aya yanayin da yake kallonta ya k'arasa saukar mata da kasala,still duk da idanunta na k'asa amma tana jin idanunsa akanta da suke k'ara yin tasiri akanta suna sawa tana dad'a daburce masa,gashi ta rasa abunda ya kamata tayi,,da gayya ya sake matsarta duk da ya fahimci a halin da take da abunda kallonta yake nufi,sai dai gaba d'aya yana ji a zuciyarsa bazai tab'a iya barinta tayi nisa da shi ba bcos yana ganin kamar wani abu zai sake ratsowa tsakaninsu har yayi nasarar rabasu ko kuma dai ya bud'e idanunsa ya tarar bacci yake yi
"My lady..! Me yasa ba zaki kalle ni ba ne..?? Baki san ina missin.."
Sai kuma yayi shiru ya kasa k'arasawa
"To ai bazan iya bane,,shi yasa.."

"Baza ki iya mene ne ba.??"

"Kallon naka..!"

"Uhhuumm.! Da gaske..??"
Ya tambaya yana matso da fuskarsa saitin nata
"Ehh..!"
Tace cikin dashewar murya saboda yadda yake kusantota jikinta har ya fara rawar da bata san dalili ba
"Me yasa to bakya iya bari mu had'a ido ne..?? Ina son haka.."

"Nifa na fad'a maka,,bana iyawa ne kawai.."

"Uhmmm.! Shi ne ai nima na tambayi dalilin.. Za ki iya sanar dani..?"
Idanunta ta matse gam,a hankali bakinta ya motsa tace
"Nifa haka kawai ne bana iyawa.."
Murmushi yayi da gefe yana kallon kyakykyawar fuskarta sannan ya sake cewa
"Sai dai ki kalle ni a sace ko..!?"
K'irjinta ne ya d'aga da sauri sakamakon maganar da yayi wacce tasa ta jin tsoron gano lagonta da yayi,can daga k'asan zuciyarta tace
"Dama yasan ina satar kallonsa ne..?"
Ta tambayi kanta without tayi tsammanin samun fitowar amsar daga gareta
"Am asking.. My Lady.!"
Ya k'arasa maganar da wani irin yanayin daya sake sawa taji kasala yaci gaba da bin jinin jikinta yana k'ona ta,shiru tayi ta kasa magana hakan sai ya bashi damar yi mata rumfa har numfashin su yana had'uwa,,yadda ya kusantota fiye da baya yasa ta d'an turo bakinta kad'an har lokacin idanunta a rufe tace
"To ni dai ka d'an matsa sai na fad'a maka.."

"I can't.. Kawai ki fad'a min a hakan,,idan ba so kike nayi miki..!"
Da sauri ya sake rik'e kalmominsa bai bari sun k'arasa fitowa ba,sake d'agawa k'irjinta yayi da sauri cike da tsoro,idanunsa ya sauke a hankali yana kallon yadda k'irjinta ke sama da k'asa a lokaci guda
"Please.. Ni dai kayi hak'uri ka matsa to na wuce,bacci ma nake ji.."
Wani irin kallon sama da k'asa yayi mata kafin yace
"Bacci..!? Yanzun ne kike jin baccin..??"
Kai tayi saurin d'aga masa alamar "Ehhh"
A hankali ya girgiza kai yana sake fad'in
"Ke yanzun baki ji kunyata ba kike fad'a min kina jin bacci..??"

"Ni ba wani kunyar da naji..Naga dai gaskiya na fad'a ai..!"

"Really..!?"

"Ehh. Mana..!"

"Uhhuumm..! Yanzun idan nace jeki ki kwanta,zaki iya tafiya da gaske..??"
Kai tayi saurin girgiza masa alamun "Ehh" murmushi yayi mai nuni da lallai ke yarinya ce,yadda yaga ta tsuke fuska lokaci guda yasa shi tab'e baki kafin ya matsa side d'inta ya jingina bayansa da cabinet d'in yana cewa
"Ok.. U can move,,tunda haka kika zab'a.. Allah bamu alkhairi..!"
Bata kalleshi ba,sai murmushin da tayi while a k'asan ranta tana cewa
"Zaka san ni kayiwa gatse.."
Bata tare data jira ya sake ceaa komai baduk da dagayya tayi maganar sai ta ja k'afafunta cikin zolaya zata bar wajen,ko dan taji me zai fad'a nema tayi masa hakan oho mata,,ko taku guda bai bari ta k'arasa yi ba ya fizgota da sauri ta fad'o jikinsa,a firgice ta d'ago idanunta ta kalleshi dan yadda yayi mata bata yi tunani ba shi yasa ta tsoratar,babu damuwan komai a saman fuskarsa yake kallon tsakiyar idanunta yana d'age mata gira
"Uhhuumm.! Ban san idan nace ki tafi zaki iya lafiya ki barni ba..! Wannan shi ne kalar naki damuwar da zaki nuna akaina..?? Duk kukan da kike yi da jiran da kika ce kinyi min iya abunda zaki iya yi kenan..?"
Janye idanunta tayi tana murgud'a masa baki,cikin rashin sani ya riga ya ganta,murmushi yayi ya sake matseta har sai da ta sake sakin y'ar k'ara,still hakan yayi masa dad'i har ya sake murmusawa,k'irjinsa ta kaiwa duka while cikin muryarta mai sanyi tana fad'in
"Ni Allah ka daina min mugunta.. Idan ba haka ba ina tafiya bazan bari ka sake gano inda nake ba..!"
Rik'e baki yayi yana fad'in
"Me yayi zafi haka my Lady da zaki furta zaki guje ni..?"

"To ba kai neba kake ta min mugunta.. Kuma ai ban san mene ne nayi ba kake min haka."

"Ohh! Sorry toh na daina,,ai kin hak'ura ko..?"
Baki ta sake murgud'a masa sannan tayi masa alamar "Ehh" da ido,murmushi yayi a hankali ya nufo fuskarta ko me yake shirin yi ita dai bata gama fahimtar saba,abunda kawai zata iya cewa taga yana kallon lips d'inta,daf da fuskarta ya tsaya bisa kuskure kamar ance ya kalli k'ofa,yana d'agowa suka had'a ido da Sultan daya kafe su da idanu ko kyaftawa ba yayi,,had'e rai Hammad yayi cike

Please Login or Register in order to submit comment