Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"Ni kike fad'awa wannan maganar..!? Ina tambayarki kina bani amsa a tsaye,saboda kin mai dani abokin wasan ki ko dan mene ne.? Wata rana idan baki yi wasa ba sai na mare ki.."
Tureta yayi daga jikinsa ya mik'e a fusace ya bar ta a wajen,abunda ta hango cikin idanunsa yasa ko motsi ta kasa yi a gurin,,shima d'in kuma tunda ya shige bathroom sai daya d'auki kusan mintuna sha biyar sannan ya fito sanye da bathrobe,fuskarsa kana kallo zaka san baya cikin yanayin jin dad'i,ba tare daya kalli location d'in da take ba yace
"Zaki tashi ne ki bani guri ko saina zo kanki..!?"
A sad'ad'e ta mik'e idanunta suna zubar da hawaye,ta gefensa ta rab'e za ta wuce,sai ya d'an waiwayo kad'an ya sakar mata harara,kallon yadda take hawaye tana tafiya cikin rashin kuzari ne yasa shi cewa
"Zo nan..!"
Babu musu ta dawo a hankali ta tsaya d'an nesa da shi kad'an dan ita dai tsoronsa take ji gaba d'aya musamman yanzun nan,ajiye dryer d'in hannunsa yayi da yake busar da kansa da ita sai ya k'araso inda take a tsayen,a hankali ganin ya kusantota ta yi baya ya sake matsowa,ta d'aga k'afarta zata sake matsawa yace
"Idan kika sake ko taku d'aya kika k'ara Allah zaki gane baki da wayo.."
Tsayawa tayi a gurin ta kasa motsawa sai hawayen da suke ci gaba da sauka,har ya k'araso daf da ita bata kuma attempt na matsawa ba,palms d'insa ya d'ora saman shoulders d'inta had'e da janyo ta jikinsa,a tare suka yi ajiyar zuciya.....




*Afuwaan..! Kuyi manage da wannan wollah yanzun nayi muku shi,saboda farin cikinku ne,amma da sai gobe zanyi posting gaskiya,cos bana nan nd ciwo ya riske ni,buh Alhamdulillah am feeling better.*



#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••
*On today's day,let us thank God for the rain,for the sea,for the sky,for the rainbow,for the air we breathe nd for the people we meet.But most of all,let us not forget to thank him for the sweet gift of life..Alhamdulillahillaziiy bii ni'imatihi tatimmus'salihaat.🙏*
*Lemme remind u my pepz,,tomorrow it was the day da nake k'ara shekara,,so! let's see su waye zasu taya ni alhinin tafiyar kwanaki na a duniya.😢*

*49.*
_#Probability_

Wani irin sonsa ne mai had'e da fargabar yadda yake treating d'inta a lokaci guda suka sake shigarta a hankali hawaye sai suka ci gaba da sakkowa saman fuskarta,kula da yanayinta sai yasa shi zagaye ta da duka hannunsa yana sake sauke wahalallun ajiyar zuciya,shi kansa ya sani son da yake mata da kusancin da suke da shi ba zai tab'a iya bashi damar d'aukan wani matakin kirki akanta ba,nd her tears too,it hots him within shi yasa baya jurewa ganinta a irin yanayin,,ita kam jin irin rik'on da yayi mata ne yasa hawayenta k'ara gudu,tsoro da fargaba masu girma suka sake shigarta,sheshshek'ar kukan da take a ciki jinta kwance a jikinsa ya kufce,dama she is in need of arms da zata kwanta tayi kuka,sai gashi ya bata damar kwanciya a jikinsa,luf ta sake yi a jikinsa tana kuka mai tsuma zuciya a hankali sai ya d'ago fuskarta ya zuba mata idanunsa,kafin yasa hannun ya goge mata su yana kad'a mata kai,buh still a gareta hawayen ci gaba suke da sauka uncontrollable,d'an b'ata fuska ya kuma yi kamar can baya kafin ya bud'e baki da kyar yace
"Stop shading tears.."
Cak taji komai ya tsaya kamar anyi ruwa an d'auke,sai ta d'ago ido tana kallonsa itanma,ita dai haka nan bata san me yake faruwa ba amma sai take kallonsa da wani irin fuskar mamaki,duk da bata san mene ne yake going through ba amma yadda yake mata a wasu lokutan sai take ganinsa kamar wanda ya had'u da matsalar shafar aljanu,yanzun zai murd'e da fushi amma ana jimawa zai koma tarairayota,"me hakan yake nufi ne.?" Ta tambayi zuciyarta,,sake goge mata fuska yayi sannan ya jata cikin jikinsa yana sake rik'e ta sosai kamar wani zai kwace masa ita,sun d'auki lokaci a tsayen har ta ji a ranta ina ma ace zasu dawamma ne a hakan,amma sai ta ji shi yana k'ok'arin raba gangar jikinsu,saurin rik'e shi ta sake yi cike da damuwa cos gani take yana sakinta zasu koma kamar da,hannunta ya b'are daga jikinsa a hankali sannan ya rik'e hannunta suka wuce bathroom,sai daya goge mata make-up d'in fuskarta da remover sannan ya had'a ruwan wanka,duka tana gefe tana kallonsa har ya k'are bata bar kallonsa ba da tsantsar mamakinsa,inda take tsaye ya k'araso da zuwa bai yi shawara da ita ba ya kwance mad'auran rigar daya sa mata ya jata cikin tube,a bakin tube d'in shima sai yayi detaching nasa ya zubar a gurin,a tare suka yi k'asa suka shige cikin ruwan,cikin zuciyar ta kam zuwa lokacin ta daina mamakin dalilin da yasa shi tarairayota bayan yasa ta kuka,haka nan sai take ganin kamar dama manufar buk'atar tace tasa shi yin hakan,,wanda a tunaninta da zaran ya samu nutsuwa shi kenan,zuwa anjima tayi masa laifi sai yace zai sake hukunta ta. Wasu hawayen taji suna k'ok'arin sauka amma sai tayi k'ok'arin mayar da su,,tana a cikin yanayin alhinin gently ta tsinto palms d'insa ta cikin ruwan suna yawo a jikinta,da sauri ta sauke idanunta a gurin,ilai d'in kuwa sune suke yawo suna mata wani irin cud'ewa da wani soft sponge,shi ba cotton ba kuma ba woolen ba,bata iya magana ba sai ajiyar zuciya data yi tana lumshe idanunta masu cike da bacci,har ya k'are tana mamakinsa da dalilinsa na sake yin wanka bayan fitowarsa kenan ya tarar da ita a d'akin ya fara mata fad'an dalilinta na saka kaya,,bayan fitowarsu daga wankan shiya shirya ta cikin wani sexy pyjamas na mata mai taushi da kyaun tsari,sannan shima d'in ya shirya,after kuma sai suka kwanta nd har a lokacin tun daya mata maganar ta daina kuka ko a bai sake furtawa ba,,a saman bed d'in ma cikin jikinsa ya sata a hankali sai take sauke ajiyar zuciya,duka sunyi wani irin shiru yayin da garin duka ya d'auki shirun,k'asa² har bacci ya fara fizgarta ta jiyo shi yana fad'in
"Nayi miki tambayan dalilin ki na saka kaya kin maida ni sakarai ko..!?"
Wani irin fad'uwa gabanta yayi cos a tunaninta tayi zaton zuwa lokacin ya hak'ura da jin amsar ne tunda taga ya jata jikinsa,ashe ba haka bane yana sane da abunda yake,a d'an rikice ta d'ago kanta ta kalle shi,idanunsa a rufe suke amma alamu sun gwada baiyi baccin ba,,maganarsa ta sake jiyowa yana fad'in
"Am asking kina kallona ba tare da kin bani amsa ba."

"Amm! Wane kayan wai..!?"
Ta tambaya saboda rashin bambance d'aya a cikin biyu da tayi,idanunsa ya bud'e ya sauke a kanta da yake itama shi d'in take kallo,sai ya had'e fuska yana fad'in
"Kada ki rainamin hankali,za ki ce ne baki gane wanda nake magana akansu ba.!?"
Rau² idanunta suka yi tana shirin fara masa hawaye,da sauri ya tare ta da fad'in
"Kada ki sake kimin kuka,,tambayar ki nayi,ki bud'e baki ki amsa min idan ba haka ba..!"
Sai yayi k'wafa kawai ba tare da ya k'arasa fad'ar abunda yayi niyya ba,,marairaicewa tayi cikin muryar kuka tace
"Amma! Ai naga kai kace na sa su.."
Kallon k'asan ido yayi mata da fad'in
"Wanne d'in nace kisa.!?"
Sai tace "Wanda muka fita da su."
Sai daya harareta sannan yace
"Am i querying about it..!?"
Shiru tayi tana sake kallonsa sannan tace
"To ai ni ban san me kake tambaya ba."
Kansa ya gyad'a a hankali yace
"Ban yarda ba,,za ki fad'a ko saina miki wulak'anci yanzun..!?"
Kuka ta fashe masa da shi,a hankali sai ya saki tsakin takaici da fad'in
"Rufe min baki,,ko na yi miki wani abu ne.!?"
Kai tayi saurin girgizawa
"Toh! Rufemin bakin ki a nan.."
K'ok'arin had'iye kukanta tayi,sai daya bari tayi shiru sannan yace
"Oya! Tell me,whom allows u to wear..!?"
Jikinta har wani irin zillo yayi saboda tsoron abunda zai iya faruwa amma sai ta dake tace
"Dan Allah kayi hak'uri.."

"Uhmm! Zan yi ai,amma first ki fad'a min waye yace kisa su..!?"

"Me d'in..!" Ta tambaya cikin damuwa,lafiyayyen tsaki ya sake yi kafin ya dage ya ture ta gefe,ransa a mugun b'ace ya fara masifa
"Da Allah kada ki maida ni wani ba gidaje mana,tun d'azun kin sani sai maimaita magana d'aya nake,ina tambayarki kina ta wani neman raina min hankali,i know ai kin san akan abunda nake magana,amma shi ne zaki nuna kamar baki sani ba,,to kayan da kika fara sawa nake magana akansu,waye ya baki permission na sawa har ki fita da su gabansu.? Da a haka zaki ratsa dubannin mutanen can...?"
K'amewa tayi a gurin daya turata kamar an dasa ta,cikin kuka tace
"Kayi hak'uri,, Allah bazan kuma sawa bama duka.."

Tsaki yaja yace "Ni bance ki bani hak'uri ba,all i want to know shi ne ki fad'a min wanda yasa ki sawa."

"Babu kowa." Tace

"K'arya ne,,dole akwai wanda yasa ki,idan kin dage akan babu kuma sai ki fad'amin dalilin ki na sawar."
Saurin tsallakowa jikinsa tayi cikin kuka ta sake k'ank'ame shi tana bashi hak'uri,amma da yake uban y'an taurin kai ne ko kulawa bai ba,ya dage akan sai ta fad'a masa,k'arshe dai da kyar tayi claiming kanta a matsayin mai laifin,ai kuwa yadda ba ta yi zato ba sai daya nuna mata KUSKUREN ta,bayan ya yanka mata warnings masu zafi akan kada ko da wasa ta kuskura ta sake gangancin sawa matuk'ar ba wa shi kad'ai ba sai ya sab'a mata,tana kukan tayi ta bashi hak'uri,,yadda yayi mata da ganin irin damuwar data shiga k'arshen da yaga tana ta kuka sai ta bashi tausayi,a hankali ya sake janta ta koma samansa,sai daya gama rarrashinta,bayan ya tabbatar rayi shiru sannan yayi preparing masu hanyar samun nutsuwa dukansu,tsakanin miji da mata sai Allah,cikin k'ank'anin lokaci tuni duka suka manta da abunda ya faru tsakaninsu,suka shiga faranta ran junansu.
Washe gari da safe kuwa k'in barin kowa ya shigo apartment d'in nasu yayi,,duk wani aiki kuma shi ya taimaka mata suka yi,cikin so da amincewa da juna,,after sunyi wanka sun shirya sai suka kwaso gifts d'in da suka samu jiyan,cikin tsantsar k'auna da kulawa suke bud'ewa,yayin da mafi yawancin kyautukanta suke d'auke da wasu irin necklaces masu azabar kyau cikin tsari mai burgewa da tsada,,washe gari ko da yake Monday ne duka suka shirya komawa skul yayin da Hammad yake hutun angwanci,shi ya kaisu can Pennsylvania d'in,kuma bai dawo ba har suka gama abunda suke suka dawo tare,,yayin da b'angaren su Sultan kuwa tun daga kan abunda ya faru a daren Sunday d'in da aka yi dinner d'in nan sai ya canjawa musu fuska,magana ko sunyi masa ita a dak'ile yake amsa musu,tun abun yana damunsu har ya zama sun saba da halinsa,shi d'in a nasa gefen duka yana yi musu haka ne ba don komai ba sai don gane illar karb'ar sak'o a hannun wani mutumin ba tare da sun duba ba,a cewarza tunda har suka kasance masu kula da al'amuran da suka shafi bincike dole ne sai sunyi takatsantsan da rayuwarsu gudun wata rana kada a samu damar cutar da su.

*4 month leave..*
Bayan kimanin wattani hud'u da komawarsu New York,wanda yayi dai² da kwanakin auren su,rayuwa ta ci gaba da tafiya musu,yayin da yanayi yake dad'a sauyawa wata rana jin dad'i wata rana kuma sai yazo a kishiyarsa,dole ne dama kuma a rayuwa sai an samu hakan ya kasance,tunda har tsakanin harshe da hak'ora ma akan samu sab'ani,,a Nigeria kuwa a dai² wannan lokacin tuni maganar auren su Badra tayi nisa,dan Daddy da Abba'nsu Sultan tuni sun tsayar da lokaci nan da watanni biyu masu zuwa auren,,a b'angaren Sadeeq shima da yake tare da su a nan U.S d'in tun kafin lokacin tuni ya sanar da iyayensa batun Zeeharis wacce tun bayan zuwansu bikin Hammad d'in bayan komawarsu New York sai suka mak'alewa juna,kuma shima d'in zuwa lokacin har iyayensa sun je sun nema masa aurenta,,soyayya mai tsafta suke gudanarwa a tsakaninsu wacce bata b'uya,duk yayin da aka ce kayi zama d'aya da su duka sai ka gane asirin zuciyoyinsu,zuwa yanzun kam da komai ya bayyana a gare su sai duk suke mamakin yadda akayi a bayan suka kasa fahimtar soyayyar Sadeeq d'in da ita Zee.
Lokaci yaci gaba da tafiya,yayin da suke ta shirin komawa 9ja auren su Sadeeq,duka da yake wata d'aya ne ya rage sai suka yanke shawaran tafiya da wurin cos suna so suyi shirye² da dama a bikin,,amma kasancewar a lokacin su Badran suna kan zana exam sai suka d'aga tafiyar tasu,,sai da biki ya rage musu saura sati biyu gaba d'aya sunnan sai suka tattara su ka yo Nigeria,,cikin y'an kwanakin da suka saukan wanda duka sune suka rage musu a fara gudanar da events Mamma ta shiga gyare su babu ji bare gani,kasancewar irin sabon da Sabina tayi da Mamma da yake tun suna U.S kusan kullum ne sai sunyi waya taji lafiyarta,yaaa ko da suka diro k'asar sai tak'i yarda su tare gidansu da tuni ya kammala,acewarta idan za'a kai amare itama sai su tare rana d'aya dan kuwa itama amarya take,,hidima sosai suka shiga yi gaba d'aya tunda suka zo k'asar basu wani zauna ba su ne can su ne nan,kusan kullum idan suka fita basa dawowa sai wajen maghreb,hidimomin biki kuma sai dad'a kusantowa suke.
Kwanakin su goma duka da isowa k'asar aka fara gabatar da programs,yadda basu zauna ba suma haka su Hammad basa samun lokacin zama,shi yasa ma sai Hammad bai wani damu da takurata ba,dan su kansu suna nan suna can ne,,rana guda aka kawo lefensu su ukun,Badra,Jannat da Zeeharis,ko wacce kuma Alhamdulillah anyi bajinta sosai a lefenta,dan an zuba musu kaya na gani a fad'a,,ita kanta Sabina a lokacin wasu irin fitinannun d'inkuna da tayi ta adana har mamakin kanta take,,wasa² an fara shagali gadan²,ta inda aka fara da kamu a ranar laraba,sannan sauran events suka shiga biyo baya,cikin tsari mai burgewa sai dai duk da kasancewar su y'ay'an gata hakan bai sa su yin k'arya da matsayinsu ba,biki tun daga ranar Wednesday suke yinsa sai da suka shafe kwanaki hud'u,a rana ta biyar data kasance ranar Sunday da safe aka d'aura aurensu su duka a masallacin umar bin khattab dake dangi,inda amare da angwaye suka had'e cikin shiga ta alfarma,Hammad da Sabina ma sai duk suka shige cikinsu shi yasa duk mutanen da basu san sunyi aure ba suke zaton auren mutum takwas ne ake yi,biki yayi kyau Alhamdulillah kuma ya tafi yadda ya kamata,babu hayaniya bare tashin hankali har aka yi aka k'are ba'a yi hayaniya ba,,a cikin wannan tsukin nefa Sabina ta samu labarin abunda ya faru dangane da auren Hammad da Falisha,godiya tayiwa Allah sannan ta sake k'udurcewa a ranta zata zage ta sake yi masa shamaki da duk wata macen da zata yi k'ok'arin rab'ar sa.
Da dare kuwa ana ta shirin d'aukan amare,su Sabina ana gaba sai tsiya take musu suna kuka Hammad ya kira wayarta,lokacin tana zaune duk ta baje a gefen gado ana k'arasa shirya amare,da sallama ta d'auki kiran,ba tare da ya bari tayi magana ba yace ta same shi a mota,amsawa tayi sannan ta fice ko gyale babu a jikinta,sai data gama ratso taro ta fito zuwa inda yayi parking,motar ta nufa kai tsaye tana tafiya tana murmushi har ta k'araso inda yake,buh da zuwa sai ta tsaya ta wajen daga dai² gefensa,glass ya sauke slowly yana k'are mata kallo cikin d'inkin atamfa da tayi matuk'ar amsarta yace
"Nan zan biyo ki ne madam.!?"
Sai data rausayar masa da kai,kafin ta ja k'afafu ta zagaya d'ayar k'ofar,tana k'ok'arin shiga motar ne wata cousin d'in su Hammad ta taho da gudu² tana mata magana,,d'an dakatawa tayi har ta k'araso,sai Sabinar ta d'an kalleta tana murmushinta mai kyau tace
"Ya aka yine Fauzah.!?"
Y'ar dariya tayi mata while tana fad'in
"Dan Allah aunty idan tafiya za kuyi zan biku gidan amarya..!?"
Y'ar dariya tayi tana fad'in
"Ehh! Ai nima kinga ban shirya ba,,amma ki bari idan zamu tafin zan miki magana kinji.?"
Ta amsa tana ta yi mata godiya,sannan sai ta d'an matsa tayi ma Sabina rad'a a kunne,ai kamar mai jira k'amshin scent's d'inta suna kaiwa hancinta ziyara ta ja baya da sauri tana rik'e hanci,matsowa Fauzah tayi tana k'ok'arin rik'o ta tai saurin d'aga mata hannu tana mata alamun taje kawai,amma sai Fauzar ta kasa tafiya ta tsaya a rikice tana mata magana,hancinta da bakinta ta rufe muryarta da tashin hankali saboda yadda turaren yake sake hawa mata kai tace
"Fauzah.! Je ki dan Allah,,zan kira ki idan mun tashi tafiya."
Fauzah da damuwa ta bayyana saman fuskarta nd ta kasa gane abunda yake faruwa tace
"Amma aunty..!?"

"Jeki please.! Ina lafiya."
Saurin fitowa Hammad yayi daga motar yana jifan Fauzah da wani irin kallon tuhuma,cikin saurin kuma ya isa inda Sabina take durk'ushe tana kakarin amai ya d'agota yana tambaya
"Helpmate.! Me yake damunki ne.?"
Da hannu tayi masa alamun yace Fauzah taje,cikin damuwa da ganin canjin yanayinta a lokaci guda ya d'ago fuska babu wasa yace
"Tafi mana,ko saina maimaita miki.!?"
A ladabce ta amsa sannan ta bar wajen tana tafiya tana waiwayensu duk damuwa ta bayyana akan fuskarta,ko data tabbatar ta bar kusa da su ai ta kasa shigewa ciki ta rab'e tana lek'en abunda ke faruwa,tana tsaye a gurin tana kallon yadda Sabinar ke ta yunk'urin amai amma ta kasa,Yallab'ai hankali a matuk'ar tashe ya d'agota suka nufi mota,da mahaukacin gudu yabar gidan suka nufi asibitin nassawara da yaje shi ne a kusa da su....



*Via with it dudes,wollahi am not in the mood da zan iya muku dogon typing,yau duka a kwance nake,amma ku k'ara hak'uri please..*



#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••
🎉🎊
💞
*Glory to the Almighty Allah who spared my life up till this moment.I'm very pleased to announce to the world that i'm +1 today.May the good fortune,honor,glory and prosperity descend upon my today...Happy birthday to my humble self.!* ✊
🎊🎉
💞

*50.*
_#Solitude_

Lokacin da Fauzah taga fitarsu daga cikin harabar gidan a sad'ad'e ta iya juyawa ta shiga gidan da fuskar damuwa,,yadda komai ya faru sai yake sake wulgawa mata a ido,har ta nufi masaukinsu da niyyar kwanciya cos a lokacin taji baza ta iya zuwa ko wane guri ba,sai kuma tayi tunanin dole tayi k'ok'arin sanarwa da Mamma halin da ake ciki d'in,,a lokacin har an fito da su Badra ita da Jannat za'a tafi kaisu,sai ta ji ana ta neman inda Sabinar take,kamar dai za ta yi shiru da bakinta sai ta ji baza ta iya rik'e abun a ranta ita d'aya ba,tana kuka ta fad'awa Mamma abunda ya faru tsakaninsu babu jimawa,,duk wanda yake gurin babba babu wanda zatonsa bai kawo kan ciki ne ba,sai duk suka bita da fatan sauka lafiya,,Mamma kuwa rarrashin Fauzah tayi da ta d'ora alhakin faruwar komai akanta,daga nan sai ta bar gurin cike da tsantsar farin ciki ta nufi bedroom d'in Daddy,,shigarta ciki babu jimawa kan wayarta tayi ta soma kiran line Hammad d'in na nan k'asar.

Shi kam a nasa gefen ganin yadda take yi kamar zata amayo y'ay'an cikinta ne ya matuk'ar tada masa hankali,a matuk'ar firgice yake jan motar yana jera mata sannu har suka k'arasa asibitin,tuk'i yake amma duka hankalinsa na kanta da wani irin damuwa mai girma shimfid'e a kan fuskarsa cos shi dai bai da sani akan komai bare yayi zaton faruwar wani abun,nd tunda suka taho d'in yunk'urin kawai take ta kasa tin aman,,tafiyar mintuna uku ya d'auke su suka iso cikin asibitin,basu jima da zuwa ba kuma aka karb'eta aka yi cikin emergency da ita,,bayan lokaci mai d'an dama da shiga da ita Dr yasa ayi masa magana da shi,har lokacin Hammad bai ji nutsuwar sa ta dawo masa ba,buh ana isar masa da sak'on likita yayi saurin bin bayan nurse d'in,a saman gadon da yake office d'in likitan wanda yakw duba marasa lafiya ya hangota kwance tayi lamo da drip a jikinta sai dai zuwa lokacin duk yunk'urin da take ta daina,siririyar ajiyar zuciya yayi yana sake k'ureta da kallo mai cike da ma'anoni daban² had'e da tausayawa
"Have ur sit please.!"
Dr ya fad'a yana sake gyara zaman glasses d'in idanunsa,murmushin k'arfin hali Hammad yayi masa sannan ya zauna saman guest chair,buh hankalinsa duka a kashe yake
"Am Dr JABEER MUHAMMAD.!"
(of my novel,K'addara koh sakaci)
Shima Hammad sai yayi masa murmushin amma ya kasa nutsuwa,sai da Dr JABEER yayi masa y'an tambayoyi dangane da itan da alak'arsu duka ta bashi amsa,sannan yayi masa bayanin komai da take faruwan buh sai dai bai riga ya yanke hukunci akan ciwon ta ba a time d'in,duk da yasan ko ya fad'a d'inma zai yi wuya ace ba hakan bane,buh sai ya k'are da fad'a masa yanzun yasa ayi mata test ne,saboda haka za su jira fitowar

Please Login or Register in order to submit comment