Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kada ta fad'a d'in,suna dai ta addu'ah kan Allah ya tabbatar musu samunsu,a hakan nan suke rayuwarsu mai cike da nutsuwa da walwala,yayin da kwanaki suke sake zuwa suna wucewa zuwa satittika haka nan suma d'in sai suke shud'ewa wani a bayan wani,har cikinta ya shiga wata na tara inda ya gama fallasa asirin girmansa,dan a lokacin sosai cikin yayi wani irin bud'ewar da ita kanta ta sake zama wata k'atuwa,zama kuwa sai da kyar take yinsa haka ma tashi idan zata mik'e sai ta dafa wani abu kafin take iya mik'ewa.

*NIGERIA..*
Tun tafiyarsu a cikin sati biyu na bayan aurensu Badra duka sau biyu suka zo kuma duk ciki babu wanda suka yi sama da sati guda,idan sun zo kuwa a gaggauce suke komawa saboda yanayin aikinsu baya barinsu zuwa su yi kwanaki masu yawa,,sai dai da yake suna yawan yin waya da iyaye da y'an uwa akai²,,a b'angaren Mamma kuwa ko da taga lokaci yana ta sake tafiya shiru babu labarin Hammad zai dawo da Sabina gida yasa ta kira shi don taji ra'ayinsa,amma ko da ta kira d'in sai yace shi ba sai anyi mata wani wankan gida ba fills ma da zasu bata a hospital idan tayi amfani da su sun wadatar,duk yadda Mamma'n taso ta lankwasa shi sai yak'i bisa dole badon taso ba ta hak'ura ta kyale shi,amma k'asan ranta tana nan kan bakanta dan bata hak'urewa abunda ta k'udurce a zuciyarta ba.

*NEW YORK..*
Kwanakin Edd kamar yadda suke zane jikin result d'inta,tunda cikin ya shiga watan haihuwa suke harararta itama tana harararsu,da yake kuma kwanakin sunyi k'arshen wata ne,tunda watan ya shiga sai duk take jinta ba dai² ba,ciwon yau daban na gobe daban,a hakan har sai da ta kusa mamaye kwanakin watan amma shiru kake ji kamar an shuka dusa,,ranar da sati ya zagayo a ranar wata friday lokacin har Edd ya wuce da sati guda,da asubah bayan sunyi sallah suna kwance around 6:00am,cikin daddad'an baccin daya kwasheta kamar wacce aka tasa sai ta bud'e idanunta a hankali,juyawa tayi ta kalleshi tana sauke ajiyar zuciya,haka nan taji jikinta yayi wani iri,nd sai take jinta kamar a cikin danshi irin na mutumin da yayi fitsari,saurin tashi tayi tana duba jikinta da inda take kwance,,a hankaki tana laluba gurin data gani jik'e,ciwon mara ya fara kunnota a hankali² zuwa wani lokaci sai yace bismillah......




#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••

*54.*
_#Exultant_

Ciwo yayi ciwo,gumu tayi gumu,tun tana daurewa ita kad'ai,har ya fara k'ok'arin wuce tunaninta,ko da taga abun ba mai k'arewa bane wahalar kuma na dad'a k'aruwa akan na baya tuni ta fara kiransa cikin murya irin ta mai ciwo,kiran farko tana yi masa ya amsa,kafin ya yunk'uro inda take cikin azabtuwa ta rik'e bayanta tana fad'in
"Laa ilaaha illa anta subhanaka inniiy kuntu minaz'zalumiiyn.. Ya hayyu ya k'ayyum.!"
Saurin sakkowa yayi ya nufo inda take rik'e da baya,while d'ayan hannunta kuma ta tallafe cikinta da shi,tana runtse ido da cije baki ya durk'usa kusa da ita yana d'ago fuskarta dake kife
"Helpmate.! Mene ne..!?"

"Baya nah..!" Sai ta fasa k'ara tana fad'in
"Wayyo Allah zan mutu.. Dan Allah ka taimake ni,bazan iya bafa..! Dama na fad'a maka zan sha wahala ne kace wai likita yace idan ana yi ne baza'a sha wahala ba,,billahillaziiy ko wannan ma kad'ai ya isa a kira shi masifa da bala'i.."
Sai ta sake matse ido tana ta wai³ da hawaye fal idanunta,,tun daya durk'usa d'in rasa abun fad'a yayi ko aikatawa saboda yadda take yi gwanin tausayi,gashi ciwo sai dad'a gaba yake,babu shiri ko da yaga tana ta azabtuwa ne yayi gaggawa ya shiryata,jallabiyya kad'ai ya iya zurawa saman boxers d'in dake jikinsa sai yayi waje da ita,,a gaggaucen ko kafin su wuce su nufi elevator sai da ya yiwa su Sultan alert ta hanyar matsa doorbell a apartment d'insu sannan yayi gaggawar barin cikin ginin da ita,,a hanya ma ko daya nufo clinic d'in da yake kaita awon,gudu kawai yake fesawa bada wasa ba,yana yi yana kallonta da mugun tashin hankali shimfid'e a fuskarsa,cikin k'ank'anin lokaci har suka iso clinic d'in,da yake abu ne na harkar kud'i suna zuwa babu wulak'anci ko jira aka shige da ita labour room,,tun da suka taho daga gida zuwa duk ciwon da tayi kafin zuwansu hospital d'in hankalin Hammad bai gama tashi ba sai da yaga yadda take gumurzu da numfashinta,likita dai da nurses biyun dake kanta kuwa a lokacin masu taimako da bata kwarin guiwar zata iya sai danno cikin suke suna cewa "push,,try,,u can do it" a nan yaji rabin haushinsu,dan kad'an yayi saura bai mari nurse d'in dake cewa tayi nishin ba gwanar dake mammatsa mata cikin,cikin ransa kuwa fad'i yake "ya mutum yana fama da kansa ana danna masa ciki,kuma duk wannan ma bai isa ba sai an wani yiwa mutum k'aryar zai iya,al'halin kuma ga shi ya kasa..?",,shi dai yana ta wajen kanta yana shafa mata kai zuwa fuska amma duk wasu kalmomin da yake tunanin zasu zo na lallami tuni suka gudu suka barshi daga shi sai halinsa a gurin,banda sunayen Allah da addu'o'i babu abunda yake mata,,ak'alla sun kwashe tsayin mintuna talatin ko sama da haka da zuwansu sannan ta fara wani irin yunk'urowa,wani uban dagewar da tayi a lokaci guda had'e da yin k'ak'k'arfan nishi sai ya taimaka mata wajen fitowar kan jaririya ta farko,kuma ya taimakawa Hammad wajen dawowa nutsuwarsa,,likita yana ganin haka da sauri sai ya taimaka wajen fito mata da shi,,hamdala Hammad yayi fuskarsa k'unshe da wani irin fara'a sai ya runtse idanunsa yana jerawa ubangiji kirari da kalmomi masu matuk'ar tsada da nuna jin d'akinsa bisa ga kyautar da yayi masa,still a lokacin da Sabinar take sake maida numfashi cikin azabtuwa da zafin ciwo,cikin tak'aitaccen lokaci kamar tasowar iska gagarumin ciwo ya sake tunkarota,sai da tayi wani dagewar bakinta na ambaton ubangiji ta sake numfasawa cikin k'arfin da bata tab'a tunanin zaizo mata a lokacin ba ta sake sullub'o jaririyarta,wannan karon kam tun kafin ma likitan yayi yunk'urin janyo mata shi tuni ta taho da kanta mabiyiyar na biye mata baya,sai da Dr ya gyara komai ya yanke cibiyar yaran sannan ya umarci nurse d'in ta d'ora mata yaran a saman k'irjinta,,bayan tsayin lokacin da suka d'auka kwance a jikintan sannan likitan ya sake bata umarnin ta d'auke su ta kimtsa sy,,kukan da Hammad yaji ya karad'e masa kunne fiye da na jariri daya shi yasa shi bud'e lumsassun idanunsa dake d'auke da hawayen tsantsar farin ciki ya sake rik'o hannunta dake cikin nasa sosai yana mata murmushi mai tafe da hawaye,,murmushin k'arfin hali tayi masa itama dai² lokacin da nurses d'in dake kanta suke musun abunda ta haifa ganin musun ya fara neman zame musu kamar fad'a² ne sai d'ayar da ita aka bawa alhakin kula da babies d'in cos ita likitan ya mik'awa su yace ta gyara su tace
"Heeyy! Young lady stop arguing,,see now it's all a baby girl's.."
Sai ta mata nuni da yarinyar dake hannunta wacce take tsaftacewa a lokacin
"Woww.! Cutie's."
Cewar nurse d'in data lek'o kenan a lokacin a dalilin labarin haihuwar tagwayen da yaje musu lokacin bayan fitar likitan tana kallon yaran tana murmushi,rufe baki d'ayar da ake musun da ita tayi cikin tsantsar mamaki tace
"Wow.! She looks like her Dad,,please Deena look at him he's so cute,handsome,hot nd sexy.!"
Yadda ta k'arashe maganar da shauk'i yasa Sabina dake saman gado tayi saurin kallonta,a taken kuma sai ta sake gimtse fuska jin abunda ya fito daga bakin nurse d'in da take satar kallon Hammad continuously tana maganar,nan da nan wani bak'in kishinsa ya taso mata da tsanar baturiyar tuni ta fara jin asibitinma har ya fara neman fice mata arai,bawan Allah shi kam da yake hankalinsa sam baya gurin su duk baima san me suke yi ba,amma a hakan sai data aika masa da sak'on harara coz tana tsammanin yana jinsu ne shi yasa taga yana faman sakin wannan kwantaccen murmushin nasa,sai da taja wani lafiyayyen tsaki a d'an zafafe ta fauce hannunta daga rik'on da yayi mata tana k'ok'arin tashi,cikin harshen nasara nurse d'in dake gyara babies d'insun ta kallo inda take cikin saurin dakatar da ita tace
"Ma'am da kinyi hak'uri kin zauna,idan kika ce zaki tashi yanzun a yanayin da jikinki yake zaki iya haifarwa kanki damuwa ne fa."
Harararta tayi itanma k'asa² sai dai bata ce mata komai ba ta koma d'in ta fasa sauka daga kan bed d'in,sai ta koma ta kwanta had'e da lumshe idanunta,saurin kallonta yayi cikin harshensa na asalin bahaushe yace
"Helpmate.! Mene ne.!? Ko wani guri na miki ciwo ne.!?"
A d'an fusace ta bud'e ido tana kallonsa tace
"Ban sani ba..!"
Sai ta koma ta sake rufe idanunta k'asa² tana mitar abun a ranta,saurin matsowa yayi jikinta yadda babu mai jin abunda zai ce yace
"Pleasee.! Ya kamata kiyi magana idan akwai inda yake damunki kafin su sallame mu sai su duba,kada sai mun tafi kuma wani abu ya taso.."
Harara ta sake banka masa cikin jin haushi ta amsa masa
"Sai dai ka tambayi kurayen can sai su baka amsan tambayarka.."
Yadda tayi yasan a cike take fam da kishi duk da kuma ba wai yaji hirar tasu bane shi duka,sai ya tsinci kansa da sake yin murmushi kafin yace
"Ko zaki iya maimaita min abunda suka ce d'in.!?"
Wani kallo ta bishi da shi tana cije lips d'inta tace
"Na maimaita fa.!?"

"Ehh! Idan da hali ba."

"Kuma wai da gaske kake yi ni zan maimaita maka abunda suka fad'a d'in.!?"

"Ehh! Ke mana,to idan banda ke waye yaji ma abunda suka fad'a d'in.!? Ko ni d'in ance miki naji su.!?"
Tab'e baki tayi kad'an tana kallon yaranta dake tsala kuka,a hankali wani sihirtaccen murmushi ya kwace mata wanda har yayi sanadiyyar da yasa ta manta abunda take yi,nan ta lalace ta shagala kallon yadda nurse d'in ke wanke su,a hankali ya juya ya kallo inda hankalinta ya tafi sai yaga yaran take kallo,sai yayi ajiyar zuciya while a fili kuma ya furta
"Lady rigima.."
Tun kafin nurse d'in ta gama tsaftace su tuni har ruwan nono ya fara neman yi mata yawa,k'irjinta ya sake haurawa fiye da lokacin da take da cikinsu,kuma su kansu yaran tun daga zuwansu duniyar da yadda suke kicking legs da koke kad'ai zaisa kayi saurin fahimtar suna buk'atar abincinsu ne,,dawowar likita a lokacin da niyyar sake dubasu ya tarar bata yi wanka ba,take ya fara fad'a wa d'aya nurse d'in,yadda yake yi kamar zai daketa sai yasa ta shiga bashi hak'uri jiki a mugun sanyaye kafin a sad'ad'e sai ta bar gurin tayi hanyar bathroom,ruwa ne mai shegen surutun tasa mata mai d'an zafi a toilet sannan sai tayi mata maganar tayi wankan kafin a kammala shirya yaran dan har time d'in ba'a gama shirya suba,a hankali sai ta mik'e tana harararta tana komai tayi hanyar toilet d'in da taimakonsa,,in few minutes ta gama kimtsa kanta ta fito sai a lokacin duka sai ta fito a matsayinta na maijego,su kuwa yara tuni har an gama shirya su suna hannunsa sai kallonsu yake da wani irin tsantsar farin cikin da bata tab'a ganinsa a ciki ba yana musu murmushi da addu'o'in neman tsari,tana zama nurse d'in data gyara mata yaranta ta sake shigowa tana mata sannu,sai ta ajiye mata wani uban thick tea data had'a mata,ita tsabar mamakin kaurinsa yasa sai ta kalleta,irin kallon da take mata ne yasa ta d'an yi mata murmushi kafin ta lallab'ata ta karb'a tana sha,,yara kamar masu jira suke ta d'auke cup d'in a bakinta sai suka fara tsala kuka,mik'a mata d'aya yayi yaci gaba da jijjiga d'ayar da fad'in
"Ki fara shayar da ita sai ki karb'i sannan d'in.."
D'an kallonsa tayi ta kuma kalli nurse d'in dake niyyar fita duk sai ta wani narke masa fuska tace
"To ai ban san ni yaya ake yi ba,,ko zaka ce ta gwada min.!?"
Yadda tayi maganar da serious yasa shi kallonta yana murmusawa shi kansa sai lokacin yake k'ok'arin tunawa tunda ya san bata da wani k'ani ko k'anwa dole ne kam sai an koya mata dama,babu musu yayiwa nurse d'in magana,kafin ta fitan sai ta dawo har inda suken ta kwatanta mata yadda za tayi sannan ta fita ta barsu,gwanin burgewa a gurinsa lokacin data tallafe yarinyarta tana ta k'ok'arin sa mata nono a baki,haka nan sai yaji sun matuk'ar yi masa kyau,wayarsa ya zaro a hankali daga aljihun jallabiyar ya matso camera,yayi ta d'aukar su pictures kamar bazai daina ba,ita kam abunma dariya yayi ta bata,sai dai zafin da take ji ya hana ta sake sosai,a hakan ta daure tayi feeding d'insu sai uban gumi take kamar ta hau kan mashi,tana gama basu ta zame ta kwanta tana maida numfashi,a ranta kuwa lissafawa take tana tambayar kanta,"yanzun kullum haka zata yi ta jin azaba idan tana shayar da su.!?" Sai tayi shiru ta zubawa guri d'aya idanu tana tunani,a fili kuma cikin rashin sani sai cewa tayi
"Tabbb'! Ai kuwa indai haka ne akwai aiki.!"
Da mamaki ya kallota yana tambaya
"Aikin mene ne.!?"
Saurin kallonsa tayi sai ta d'auke kai bata bari sun sake had'a ido ba ta zame ta kwanta had'e da rufe idanunta kamar mai son yin bacci,murmushi yayi shima ganin bata da niyyar yin magana sai yaci gaba da yiwa yaransa addu'ah,tanda ta kwanta d'in nan ita kam a hankali har bacci ya fara fizgarta ta jiyo shi k'asa² yana fad'in
"Wane suna kike da zab'i a zuciyarki wa yaranmu..!?"
Cikin magagain baccin dake yawo da ita tace
"I don't have anyone.."

"Babu kuma..!?"

"Uhhuumm..! Bani da.."

"Kina nufin baki tab'a zab'ar wani suna ba saboda yaran da zaki haifa..!?"
Tana cikin mayen baccin ta sake cewa
"Ehhh! Na ce maka babu fa,,amma kai ka zab'a musu.."

"Okay.." Yace sai ya ci gaba da abunda yake,can bayan wani lokaci sai ya d'ago yana kallon bayanta yace
"I named Hassana as *SAFIYYA* nd Hussaina as *ASIYA..!* Sunan sunyi miki.?"

"Uhhuumm..! Allah raya su yayi musu albarka.."
Murmushi yayi yace "ameen" sannan ya kwantar da su saman cradles d'insu dake kusa da gadonta,a hankali ya zagayo dai² fuskarta yana shirin mata magana amma sai ya ga idanunta a kulle,murmushi ya sake yi slowly ya furta
"Sleep soundly yah rohii.."
Sai ya sauke fuskarsa dai² cheeks d'inta ya bata light kiss,murmushi yaga tayi masa cikin muryar bacci tace
"Shukhraan'kthiir HABIBIIY.."
Gefen gadon ya d'an zauna daga kusa da k'afafunta sannan ya d'auki wayarsa ya fara k'ok'arin kiran Mamma,,lokacin da Mamma ta d'auka kiran da sallama Mamma ta amsa mishi tana murmushi da tambayarsa ya y'arta take.? Murmushin shima ya fara yi cikin wani irin muryan dake fayyace mood bayan sun gaisa da tambayar juna yadda suke yace
"Mah.! She was delivered.."

"When habibiiy..!?"
Itama Mamma ta amsa masa soundly nd happily
"Ba'a jima ba Mah,, but yanzun duka suna bacci ma.."

"Masha Allah" shi ne abunda yake fitowa a bakin Mamma kafin ta tambaya
"Me muka samu ne habibiiy..!?"
Wata munafukar dariya yayi a kasalance kamar shi ya haihun yace
"Mah am very happy,cos Allah (S.W. blessed us with..!"
Sai yayi shiru cikin salon jan rai
"Yalla habibiiy tell me mana kake jamin rai,ko so kake sai na zo ne yanzun na gani da kaina kayi shiru kak'i fad'a min.!?"
Y'ar dariyar ya sake yi cike da zolaya sannan yace
"No Mah,I will tell u ai,,but tukuicin albishir first.."
Y'ar dariya tayi masa tace
"Ohhh.! Sarkin wayo,,ashe dabara aka shirya min,,zancen kenan dama..!?"

"Ehh! Mana Mah,ki mik'o tukun cos i have a new big³ surprise to u,but shi sai kinzo zaki ji..!"

"Da gaske HABIBIIY.!?"

"Sure Mah.!"
Jimm ta d'anyi kafin tace "Ok tell me now i will share it for u.."
Dariya yayi kamar mai rad'a yace "Mah twin's Allah ya bamu."
Wani farin cikin da ya kwasheta ne yasa soundly ta furta
"Da gaske habibiiy..!?"

"Ehh! Mah, ki duba pictures d'insun na miki sharing yanzun.."

"Awwnnn.! Shukhraan ya k'adiiyr,Shukhraan ³.!"
Murmusawa yayi cikin jin dad'i yace
"Mah yaushe zaku zo ne..!?"
Tace "Goben in sha Allah muna hanya.."

Yace "Allah kawo ku lafiya.." Tace "ameen",sun d'an jima suna hira da ita kafin yayi mata sallama,yana ajiyewa sai ya kira gidansu Sabina itama ya sanar da iyayen ta,bayan nan kuma sai ya kira su Sultan ya fad'a musu ta sauka lafiya,tsabar murnar da suke da samun k'aruwar da suka yi a lokacin gaba d'aya suka d'ungumo suka yo hospital d'in,,lokacin duk da suka iso sai da suka gama rububin d'aukan babies yana kallonsu bai ce musu komai ba,amma suna nufo wurin da take zai ce "A'a kada su tada masa ita,tana buk'atar hutu",duk sun gama dokin nasu suna lik'e da yara kuma wai sai a lokacin da suka gama d'aukin ganin yaran sannan aka fara rigegeniya za'a fad'awa Mamma haihuwar,yana jinsun still yayi musu banza sai murmushin da yake yi,a ransa kuwa fad'i yake "kuyi ku gama ta riga ku sani" Badra ce ta fara reaching line Mamma cikin d'oki ko gaisuwar kirki basu yi ba ta fara fad'awa Mamma,dariya Mamma tayi mata tace
"I think kamar ni da nake nan ma na riga ku sanin anyi haihuwar,ku da kuke nan duk kun shanya baki ya tafi hospital da ita shi kad'ai..!"
Saurin kallon fuskarsa tayi a wayar kuma tace
"Mah.! Wai kin rigamu sani dama.!?"

"Ehh! Ko kina mamaki ne..!? Ai shi da kansa ya kira ya fad'amin bayan ta saukan.. Sai yanzun kuka je gurinsu kenan..!?"

Tace "Ehh! Mamma mu ai yanzun muka samu labarin muka taho clinic d'in.."
Murmushi Mamma tayi tace "To Allah ya k'ara musu lafiya.. A gaishe min da kowa.."

"Toh za su ji duka.."
Daga nan suka ajiye wayar,juyowa tayi tana kallon yadda suke mata dariya slowly sai ta juya ta kalli Yayan nata tace
"Haba Yaya shi ne zaka yi saurin fad'awa Mamma.. Duka fa na d'auko niyyar fad'a mata ne shi ne amma zaka riga ni..?"
Murmushi yayi ya kautar da kansa gefe ba tare daya tanka ba,,,tun a ranar basu kai ga kwana a hospital d'inba bayan an tabbatar da lafiyarsu duka aka yi discharge d'insu suka tattara suka kama hanyar gida,tunda suka koma gida kuwa a nan su Badra suka fad'a hidima har dare wajen 10 suna gidan.

*NIGERIA..*
A 9ja kuwa tun a washe garin ranar da aka yi haihuwar kamar yadda Mamma ta fad'a masa zasu taso d'in gaba d'aya sai suka d'auko hanyar U.S d'in,kuma tunda suka samu suka taho d'in babu wanda suka fad'awa,,dama tun bayan da suka yi waya da Hammad d'in ya fad'i batun haihuwar Daddy yasa aka nema musu Visa tun ma a daren ranar bayan ya samu labarin a bakin Mamma,washe garin da asubah suka bi jirgi sai U.S.
A ranar ki da yake basu samu damar isowa da wuri ba dan sai dare suka samu damar isowa sai suka yanke shawarar sauka a hotel kuma still har timw d'in basu yi waya da kowa ba cikin yaran bayan Hammad,,washe gari da safe around 10am sannan suka sake yin waya da shi a lokacin shima sai ya tafi da niyyar d'auko su a hotel d'in da suka saukan,,bayan k'arasowar su a carline yayi parking ya fito,shi ya bud'ewa su Mamma k'ofa suka fito,sai duka suka nufi entrance,ko mintuna biyar basu yi ba suka hauro floor d'in da suke,shi ne a kan gaba suna tafe suna hira da iyayensa yana ta zubawa Mamma shagwab'a tana biye masa,lokacin da suka tsaya bakin entrance na apartment d'in ko kafin ya danna doorbell d'in sai da suka tsaya jim,sannan yayi alerting jama'ar da ke apartment d'in,Zeeharis ce ta zo ta bud'e musu sai faman kyalkyala dariya take,kai da gani kasan hira suke aka taso ta,da mugun mamaki take kallonsu Mamma za tayi magana Hammad yayi mata alamun tayi shiru kada tace komai,juyawa tayi slowly ta kallo inda sauran suke zaune tsakiyar parlor'n suna ta faman dariya dukansu har mazajen nasu tana murmushi,,shi kad'ai ya fara shigowa yana kallon inda suke zaune,sai da ya wani d'age musu kai kafin yace
"Hey dudes.! I have plan a sizeable surprise for u.."
Cikin d'an d'aga murya ya fad'a yadda yasan duka zasu ji shi,waiwayowa suka yi suna kallonsa sai suka yi murmushi,ganin babu wanda yace komai yasa shi lek'a bayansa slowly yace
"Bismillah.."
K'urii suka yiwa entrance d'in duka suna jiran ganin su waye ne zasu shigo d'in,sai ga Mamma ta bayyanar musu,wani ihu suka sa kamar k'ananun yara,kafin suka mik'e da nufin zuwa gurin tan,Daddy ya

Please Login or Register in order to submit comment