Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Amma saboda kafi kowa zuciya shi ne kake k'ok'arin aikata abunda kaga dama,shin zafin zuciyarka shi ne zaisa mu samu amsar da muke buk'ata daga gareta..??"

"Kayi hak'uri Yaya..!"
Tsaki baffan yaja sannan ya maida hankalinsa kanta yana fad'in
*"SHALELE* maza ki fad'a min komai kada kiji tsoron..Shin mene ne ya faru dake..??"
Sai data kalli inda Babanta yake sannan ta fara zayyanawa baffan duk abunda ya faru tun daga fitowarta a gidan har zuwanta bakin rafi da abunda su sarki suka mata,haka nan taimakon da saurayin yayi mata,ba tare data rage ko wasali ba duka ta zayyana masa,,ko data gama fad'a musu abunda ya faru d'in wani mugun kallo baffan ya sakarwa Babanta cike da jin haushinsa yace
"Sai dana fad'a maka ai,amma taurin kai ya hana ka bibiyi inda gaskiya take,,gashi nan ai ka kunyata kanka.. Sai ka saki d'an mutane ai yanzun tunda kaji gaskiyar abunda ya faru ko..!?"
Cike da tsananin jin nauyin abunda ya aikata d'in shima baban nata ya sauke kai k'asa kafin ya saki matashin
"Shi kenan *SHALELE* maza shiga gida kinji,,Allah yayi miki albarka..amma ki daina fita da irin wannan safiyar,sannan ko waye yace zai aikeki in dai mutane basu fara fitowa ba kice masa nace baza kije ba,,kinji ni ko..?"
A hankali ta girgiza kai sannan tace
"To baffa.!"

"Maza wuce kije abunki kinji..!"
Jikinta babu k'wari ta juya ta tafiya zuwa hanyan cikin gidan,har tayi taku biyu sai kuma ta tsaya had'e da waiwayowa,a hankali ta ajiye idanunta akansa had'e da yi masa murmushin ta,,shi kam a gare shi ajiyayyun numfashi ya sauke sannan ya lumshe idanunsa,dai² lokacin baffa ya k'arasa inda suke ya rik'o hannunsa
"Samari muje ko..!?"
Ya janye shi suka nufi hanyar cikin gidan tare,,da sauri Sabina tayi cikin gidan itama dan ganin sun taho,wanda shigowarta yayi dai² da lokacin da sarki ya juya shima zai bar wajen dan duk abunda akayi akan idanunsa ne,yana gurin har lokacin a lab'e yana saurare sai dai sam baiji dad'in yadda reshe ya juye da mujiya ba,,harara Sabina ta aika masa da ita mai d'auke da sak'on tsantsar k'iyayyarsa,cikin jin zafinsa kuma ta girgiza kai,sai dai bata ce masa komai ba ta wuce abunta,tsaki yayi shima zai bar wajen dan yadda yaci buri akanta sai gashi anyi rashin sa'a wani banza yazo ya rusa masa plan,girgiza kai shima yayi cikin kurari ya furta
"Sai na cimma burina akanki Sabina,,sai nayi nasara..!"
Yana fad'in haka ya saki murmushin mugunta sannan ya d'aga k'afarsa a gurin
"Kaii! *LADO* zo nan dan uwa ka..!"
Muryan baffa da shigowarsu kenan shi da matashin ta ambata,k'yam sarki yayi a gurin ya kasa matsawa,yadda hantar cikinsa take kad'awa kuwa da jim yadda baffan ya kira shi ba k'aramin tsoro ne ya sake shigarsa ba,amma kafin ya juyo saboda tantiranci sai ya dake kafin ya juya yana b'ata rai
"Baffa gani..!"
Kallonsa kawai baffan yayi ya girgiza kai,kome baffan ya tuna kuma sai kawai yace jeka zamu had'u anjima,,zan neme ka,saura kuma ka bar gidan kaji.!?"

Daga haka baffan bai sake cewa komai ba ya wuce hannunsa rik'e da matashin suka nufi wata bukka dake gefe,wacce ita bata shiga ainihin tsakar gidan ba kamar sauran,,k'unk'uni sarki yayiwa baffan wanda shi baima kula ba dan ya riga ya wuce,sai dai matashin dake bayansa da yake ya juya ya,shi yaga abunda yayi d'in,girgiza kai yayi sannan ya wuce shima,zuciyarsa cike da mamakin halin wannan bawan Allah daya ji an kira da suna biyu a lokaci guda,coz a d'azun yaji ance SARKI yanzun kuma yaji dattijon da suka shigo tare ya ambaci LADO,to shin wanne ne d'aya a cikin biyu..?? Shi ne abunda har yanzun ya kasa ganewa,lokacin da suka shiga cikin bukkar,saman traditional mat dake shimfid'e awajen suka zauna,bayan sun gaisa sai baffa ya kalle shi yana murmusawa kafin ya ce
"Samari shin daga ina ka fito haka..? kuma wane ne kai..?? Mene ne mak'asudin zuwanka nan garin,,sannan yaya ne asalin sunanka..??"

Numfasawa yayi sannan yayi d'an murmushi da cewa
"Ni dai baffa suna na *MUHAMMAD KABEER,* dalilin zuwana garin nan kuma ba komai bane face karatu daya kawo ni..!"
Murmushi baffa yayi sannan ya ce
"Masha Allah samari,shi kaima makarantar jami'a dake nan cikin wudil kazo ba..??"

"Ehh! Baffa..nan ne..!"

"Lallai zuwanka wannan garin alkhairi ne a garemu,,muna godiya sosai da alkhairin ka gare mu,muna kuma yi maka fatan alkhairi,ubangiji yayi maka kyakykyawan jagoranci akan abunda kazo nema,sannan yaci gaba da baka nasara har k'arshen rayuwa.."
Da ameen ya amsa kansa a k'asa,shi kuwa baffa sai bai saurara ba yaci gaba
"Abu na biyu ina mai sake baka hak'uri da abunda ya faru tsakaninka da d'an uwana,wato Aminu..Tabbas a wasu lokutan halinsa sai hak'uri,shi yasa kullum nake yawan yi masa fad'an ya daina saurin yanke hukunci,amma baya ji,saboda zuciyarsa ta banza,yanzun dubi abunsa ya aikata wanda sam bai dace ace yayi hakan ba.."
Murmushi Muhammad yayi sannan ya ce
"Babu komai baffa,,na tabbatar shima saboda bai san ainihin abunda ya faru bane,amma da bazai yi hakan ba,,kuma baffa ko da ni ne a matsayinsa aka zo aka bani labari kwatankwacin yadda aka fad'a muku,tofa zan iya yin abunda yafi nasa,saboda kare martaba da k'imar ahali na..amma babu komai baffa,sam ni banga laifin baba ba,abunda yayi shi ne dai²..!"
Murmushi baffan yayi shima sannan yace
"A'a fa samari,kada kace haka,ai yayi ba dai² ba,kuma nima zan same shi ne,ko dai ya canja wannan muguwar zuciyar tasa ko kuma zamu samu sab'ani a wannan lokacin.."
Dai² nan baban Sabina ya shigo cikin d'akin bukkar da sallama hakama yanayin da fuskarsa ke d'auke da shi yana bayyanar da jin kunya k'arara,,ga baffa kuwa hararar d'an uwana nasa yayi sannan ya ce
"Ai saika samu guri ka zauna ko muyi magana..!"

Murmushi baban Sabina yayi sannan ya zauna k'asa² kuma yana kallon yayan nasa,shi kansa Muhammad da yake gefe abunda dattijon yayi sai daya bashi dariya,sai dai yayi murmushi kawai sannan ya basar,sai dai ko kafin yayi wani yunk'urin nan ya tsinto muryan baban Sabina yana cewa....



#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••
_Devoted to my lil 6ters *Real hafsy & Mamah Zee.*_
_Bestowed to *Sis Hubbeey.*_

*Bismillahir-rahmanir-rahiim.*

_My *BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)* hak'ik'a ina godiya sosai da alkhairin ki gare ni,,ke ta daban ce,a cikin masoya ke d'in kin kai mak'ura,wacce samun kamanta sai an sha matuk'ar wahala,,hak'ik'a shi masoyi gaskiya ba'a tab'a gane shi,har sai a lokacin da abubuwa biyu suka samu mutum,,na gode sosai da kulawar ki gareni,ubangiji ya bar zumunci.._

_*My Cweet Sis Nerja'at* wollah ban san ta yadda zan kwatanta miki irin tsantsar farin cikin da kika samu ba,mun gode³ sosai da kyautarki garemu ubangiji ya saka miki da mafificin alkhairinsa,Allah kuma ya bar zumunci._


*4*
_#Worries_

Muryar baban Sabina d'auke da yanayin jin kunyar abunda ya aikata yake cewa
"Yaro dan Allah kayi hak'uri bisa abunda na aikata maka,wollahi ban san haka abun yake ba,dan Allah ka gafarce ni,sharrin zuciya da kuma halin d'aukan magana irin nawa yasa ni yanke hukunci cikin fushi,amma dan Allah kayi hak'uri ka yafe min...!"
Da sauri Muhammad ya kalleshi yana taran numfashinsa
"Dan Allah baba kayi hak'uri wollahi babu komai,,na san ba don komai kayi haka ba sai dan ka kub'utar da iyalinka,kuma na tabbata duk abunda ka aikata kayi shi ne a bisa rashin sanin gaskiyar AL'AMARI,,amma ka d'auka babu abunda ya faru tsakanin mu,nima tamkar d'a nake a gurinka,kana da damar ka hukunta ni idan nayi maka badai²ba,,komai ya riga ya wuce da izinin Allah,baka yi min komai ba.."
Cikin jin dad'i baffa ya kalli baban Sabina kafin ya ce
"Alhamdulillah..! Shin Aminu ko kaga abunda nake yawan sanar da kai..?? A yau abunda ya kamata ace kai a matsayinka na babba kaine kayi,sai gashi ka kasa sai yaro k'arami ne ya gwada maka halin dattako,,shin yanzun kana da bakin magana..?? Me yasa a ko da yaushe baza mu dunga hak'uri da rayuwa ba,,me yasa muke yawan d'aukan al'amura da zafi.?? Wannan dalilin yasa nake yawan fad'a maka ka dunga danne zuciyarka akan abubuwa irin wad'annan,,idan ba haka ba wata rana zuciya zata saka aikata abunda bai kamata ba,,gashi nan ma tun daga yau ka fara ganin abunda nake yawan sanar da kai d'in ai.!"
Girgiza kai baban Sabina yayi cike da jin dad'in nasihar da d'an uwan nasa yake yawan yi masa a lokuta da dama sannan ya ce
"Tabbas Yaya yau kam na ga zahirin abunda kake yawan fad'a min,,kuma in sha Allah daga wannan karon nima ina mai tabbatar maka baza'a sake samun matsala makamanciyar wannan ba,,na gode sosai Yaya da yawan sanyani a hanya da kake,ubangiji ya jik'an magabatanmu kuma ya k'ara girma.."

"Ameen" baffa da Muhammad da suke zaune suka fad'a suna d'an yin murmushi kafin baban Sabina ya sake juyawa ga Muhammad dake kusa da shi yana cewa
"Nafa gode sosai d'an nan..Allah yayi maka albarka,yau gashi a sanadin ka abunda d'an uwana yake yawan nusar dani shekara da shekaru na kasa fahimta,lokaci guda zuwanka yasa na gane,tabbas kai alkhairi ne a tare damu,,zuwanka ya zama wani babban haske a gare mu,,har abada baza mu tab'a mantawa da wannan alkhairin naka gare muba..Allah ya tsare ka,ya shiryar da kai a hanya madaidaiciya.."
Murmusawa ya sake yi yana fad'in "Ameen baba.."
Sun d'an yi shiru na wani lokaci sannan baban yace
"Amma har yanzun bamu san ainihin sunan kaba samari..!"

"Ko kuma dai baka sani ba ko..??"
Baffa ya fad'a yana murmusawa,,Fuskarsa d'auke da fara'a shima na jin abunda baffa ya fad'a ya amsawa baba da cewa
"Babah ni suna na *MUHAMMAD KABEER.."*

"Masha Allah..! Cewa za kayi mai babban suna ne,,to ubangiji yasa ka kasance mai yin koyi da abunda mai asalin sunan ya bar mana kuma yayi umarni..!"
Still ya sake yin murmushin kafin suka amsa da "ameen" shi da baffa dake zaune yana kallon su duka,zuciyarsa cike taf da farin ciki,,saurin mik'ewa baba yayi fuskarsa d'auke da fara'a wacce ta gaza boy'ewa ya ce
"Yaya bari naje na dawo,,ba jimawa zanyi ba amma.."

"To Allah ya tsare,,sai ka dawo d'in..!"
Murmushi yayi yana tafiya yace
"Ai Yaya ba wani guri zanje ba,nan cikin gida ne zan shiga na dawo.."
Murmushi duka suka yi,kafin baffa ya sake cewa
"To..amma dai duk da haka ai fita za kayi,kuma kafin ka shiga cikin gida zaka wuce hanya ko..??"
Bai tanka ba saima y'ar dariyar da yayi sannan ya fice,ya bar su baffa suna masa dariyar abunda yayi,,fitowar baban Sabina ke da wuya yana shirin zura takalmansa sai ga LADO yazo giftawa,fuskarsa a had'e ya kalle shi cikin nuna iko yana cewa
"Kai LADO zo nan..!"
Sai da LADO ya d'ago ya kalleshi sannan ya ce
"Ni kake kira baffa..??"
Maganar tayiwa baban Sabina wani iri,dan yadda ya ga kamar LADON yaso raina masa hankali
"Shin idan har ba kai nake kira ba,akwai wani LADON na daban a wajen nan ne..??"

"A'aaa! To baffa ai ni ban san dani kake bane shi yasa na tambaya..kada kaga laifina..shi matambayi ai hausawa sunce baya b'ata..!".
Cikin tsananin mamakinsa baffan wato mahaifin Sabina yake kallonsa
"Kai LADO..Kai..! Yanzun ni kake fad'awa irin wannan maganar..??"
Gunaguni LADO ya sauke kai k'asa yana yi,wanda sune suka sake tunzura baban Sabina, ba tare da LADO ya ankara da tahowarsa ba sai ji yayi kawai baban ya rik'o wuyan rigarsa dama a k'ule yake da shi tunda ya samu labarin abunda yaso aikatawa y'arsa,sannan kuma saboda ya raina musu hankali yazo ya juya labarin,wanda badon Allah ya tak'aice wahala ba da tuni yazo yana fama da kayan nadama da danasani ,,ko daya samu damar damk'an sa bai saurara ba ko tunanin abunda ya kamata yayi ya zabga masa wani shahararren mari wanda yasa LADO gigicewa ya saki ihun azaba,nan take ihun nasa sai ya janyo hankalin al'ummar gidan baki d'aya kwansu da k'wark'wata suka zagaye su duka
"Kamar ni ina matsayin wa ga mahaifinka nayi maka magana sai ka tsaya kana min k'unk'uni,,uwaka kake cewa da kake min gunaguni..?? Dama baka sani ba a ciki nake da kai,duk iskancin da kake a garin nan ana zuwa ana fad'a min,dan ban tab'a yi maka magana ba shi yasa yau da iskancin naka ya motsa ka nemi sauke shi akaina da y'ata..?? Saboda nace bazan baka aurenta ba ko..?? Ai dama sam baku dace da juna ba,kana watsatstse da kai zan d'auki y'ata ne na baka..?? Mutumin da bai san darajar iyaye ba,ta ina ne zai san darajar mace..?? Sam halayen ku basu had'a hanya ba haka ma ayyukan ku,,,abisa abunda ka aikata a yau banda dai Allah ya tak'aita,wollahil aziiym da saina nuna maka kai d'in k'aramin shege ne..amma ka sani ba kai kad'ai ba,dukma wanda yake da mugun nufi akan yarinyar nan,wollahi ya shiga hankalinsa idan ba haka ba matuk'ar wani abu ya sake ya same ta sai inda k'arfina ya k'are tsakanina da koma waye,sai dai daga ranar ace zumunci ya lalace..!"

"Uhmmm! Allah sarki,,kaji fa masu y'ay'a,wad'anda uwa ta haifa,ba kamar namu da muka tsinto a juji ba..To Allah na tuba har mene ne abun alfahari a game da y'a macen da kake ta mana wannan balok'ok'on akanta..?? Mu da muka haifi y'ay'a maza ai mu yafi kamata muyi alfahari ba ku da kuke da mace ba..!"
Matar dake matsowa kusa da LADO ta fad'a tana yatsina fuska,ran baban Sabina a matuk'ar b'ace ya kalleta sai dai bai tanka mata ba ya girgiza kai kawai
"Ke Tani shin waye yasa bakin ki a nan gurin..?? Ki kiyaye ni wollahi idan ba so kike na sab'a muku ba..Duk mutum mai hankali taya zai d'auki y'arsa ta cikinsa ya bawa mutun irin LADO..?? Wanda gaba d'ayansa bai kamata ayi alfahari da shi ba,wannan dalilin yasa ko da Aminu yace bazai aura masa ita ba nima nak'i saka bakina a maganar hana shi auren Sabinar,halayen su ba d'aya bane,ta yaya bayan muna jin irin abubuwan da suke aikatawa a gari mu d'auki yarinya kamila kamarta mu had'a ta aure da shi.?? Shin bamu cutar da ita ba idan muka bi son zuciyar mu..?? A yau nima na sake bada goyon baya,idan har Allah yayi mana tsayin rai ko dama ace mun mutu gabanin zuwan lokacin,ban amince a had'a aurensu ba,sannan daga yau kada na ji wani a cikin gidan nan ya sake zuwa min da maganar yana son auren ta,na soke wannan auren had'in aka kowa,dan haka ko wanne yaje ya duba mace a wani ahalin,amma batun auren dangi daga yau na raba shi tunda mun fara samun sab'ani daga wannan gara mu dakatar da abun haka nan,wanda akayi a baya ubangiji ya sanya musu albarka..."
Muryar baffa dake tsaye a bayansu ya ambata,wanda hakan sai yasa su duka juyawa suka bi shi kallo,sai daifa babu wanda ya isa yace wani abu a game da hukuncin daya yanke d'in dan kuwa ya tabbata,saboda kasancewarsa babba a gaba d'aya ahalin gidan shi yasa maganarsa take kasancewa tamkar yankan wuk'a,,,kaf cikin ahalin babu wanda baiyi farin ciki da wannan batun na baffa ba,musamman samarin dake cikin gidan masu tasowa da wasu a cikinsu dama sun jima suna kyamatar auren had'in da ake yi musu,a dalilin ko wacce tayi maka ko bata yi maka ba haka idan har iyayen suka zauna suka yanke hukunci akan lamarin babu yadda zaku yi gaba d'ayan ku dole ku hak'ura ku zauna da juna da dad'i ko babu.Lokacin da baffa ya gama maganar juyawa yayi ba tare daya tsaya sauraron cewar kowa ba zuwa cikin bukkar yana fad'in
"Kai kuma LADO zamu had'u da kai,ba wai na kyaleka bane,zaka ci uwaka tunda dama ita take d'aure maka gindin ka dunga yiwa al'ummah d'iban albarka,zamu had'u ne dukanku zaku sani..!"
Tani cikin k'unk'uni da yake shi baffa bata iya maida masa da magana gaba da gaba sai dai irin hakan ko kuma a bayan idonsa tayi ta harbin iska yasa yanzun ma tace
"Sai dai mu san alkhairi,,kuma shi zamu gani..!"

Bata jira komai ba itama ta janyo hannun LADO tana fad'in
"Muje ciki kaji d'an albarka.."
Harara LADO ya sakarwa Sabina da innarta da suka juya suma suka bar wajen,a ciki² kuma yayi k'wafa da cewa
"Zaku san ni kuka hana aurenta,,aradun Allah dole ma na b'allo muku ruwan da baza ku tab'a iya kare kanku ba,,zan bar muku darasin da sai kunji dama ace kun aura min ita tuntuni,zaku gane KUSKUREN ku,ba dai ni aka tozartar ba,,da kanku zaku fuskanci ba'a tab'a ni a zauna lafiya.."
Su kam su Sabina koda suka shige d'akin su,babu damuwar komai a ransu,suka zauna don cin abincin da Innar ta zuba musu kafin fitar su,wanda sai a lokacin ne Inna ta samu damar kallon SABINA kallo irin na tsanaki kana ta ce
"Uwata.! Wai ni mene ne ya had'a ki da LADO kuma a wannan lokacin..??"
A hankali ta d'ago kyawawan idanunta ta d'an kalli Inna had'e da sakar mata murmushi
"Inna nima ban sani ba,ban san mene ne na tsare masa ba,ban san me yake nufi dani ba,kawai dai ni abunda na sani tun daya cewa Baba yana son ya bashi aurena yak'i amincewa shi kenan kullum yake takurani,kuma ko a yauma abunda ya faru ban san ya akayi yasan na fita ba har ya bini bakin rafin shi da abokansa.."
Shiru Inna tayi tana saurarenta wanda ita kuma Sabinar sai taci gaba da zayyana mata abunda ya wakana a fitar tata har zuwa k'arshe,,dogon numfashi Innar ta sauke kana ta kalli tilon y'ar tata
"Tabbas Sabina akwai wani wanda yasan da fitarki,haka nan ai bazai biki ba duk da kuna da matsala da juna,,amma bama wannan ba,shin mene ne dalilin da yasa ki fita da sassafe irin haka..?? bana ce dake kada ki sake fita a irin wannan lokacin ba..??"
Shiru tayi tana sunkuyar da kai k'asa,muryanta cikin sanyi da rauni ta ce
"Kiyi hak'uri Inna,nima ba'a son raina ne na fitan ba,illah gwaggo Tani data aike ni na samo mata ruwa..!"

"Tani..!? Ta aikeki ki d'ebo mata ruwa..?? Shin bata san Malam ya hana ku fita da wannan lokacin bane..??"
Cikin jimami da damuwa Innar ta fad'a tana kallon y'ar tata
"Ai kuwa tayi kai..daga yau duk kawaicin da nake gwada mata akanki wollahi tunda d'anta yayi k'ok'arin haike miki kuma ta goya masa baya,,zata sani dani take zancen wollahi sai dai daga wannan lokacin mu raba dutse a hannun riga..Wato ma tasan ita ta aikeki amma shi ne zata dunga fad'awa mutane magana son ranta..?? Ai kuwa zata san ta tab'a min ahali,wollahi sai dai a daina zaman lafiyar,ai ba tsoronta ake ji ba,dan taga ana rabuwa da ita,shiru² ai ba hauka bane,,wane ne bai san daraja da k'imar ahalinsa ba..??"

"Inna dan Allah kiyi hak'uri ki kyalesu,dama fa abunda suke so kenan ayi ta tashin hankali a gidan nan,Inna idan kika duba duka cikin gidan nan kowa baya kula lamuransu dan haka kawai mu barsu da Allah,tunda dai babu abunda ya far,mu barsu da Allah,duk muguntarsu in sha Allah wata rana zata koma kansu.."
'Dan jimm Inna tayi kafin ta jinjina kai tana cewa
"Shi kenan Sabina nayi hak'uri kamar yadda kika ce,zan kyale sune a wannan lokacin saboda kin bani baki,amma matuk'ar suka sake k'ok'arin tab'a min ke wollahi saina gwada musu fushi na,ki ajiye wannan a ranki ko mai dad'ewar lokacin da za'a d'auka idan har wani abu ya sake ratsowa wollahil aziym bazan lamunce shi ba...!"

"To Inna in sha Allah ma babu abunda zai sake had'a mu da su d'in."
Cikin alamu dake nuna karaya Inna ta furta
"Allah yasa..!"

"Ameen Innata.. Muci abincin to..!"
Sai lokacin Inna ta kalli kwanon dake gabansu da alamun kamar har ta manta ta d'anyi jim idanunta akan abincin har zuwa wucewar wani lokaci kafin tace
"Ke bazan Ciba,ki ci abunki ke kad'ai..!"
Marairaicewa Sabina tayi kamar zata yi kuka
"Haba Innata yanzun duk akan wannan abun ne yasa baza ki ciba..?? Shi kenan to nima na k'oshi.."
Ta mik'e daga gurin tana kumbura fuska,,saurin rik'o hannunta Inna tayi ta dawo da ita gabanta ta zaunar
"Haba SHALELEN Baffa,,ta yaya za'ayi kice baza ki ci abinci ba..??"

"To Inna ba dai ke bace kika ce bakya ci..!"

"Shi kenan mu ci to,,kinyi farin ciki..??"
Murmushi ta saki mai kyau wanda ya bawa fararen hak'oranta damar bayyana kafin ta girgiza kai tana fad'in
"Ehh! Inna..ai dama u always make me feel happier,,ina alfahari dake..!"
Sakin baki Inna tayi sororo tana kallon y'ar tata jin ta mata wani yaren na daban,a hankali kuma ta kamo kumatunta duka biyu tana sakin dariya da cewa
"Ja'ira..! Wato nima sai an gwadamin yaren yahudawa ba..??"
Dariya itama Sabinar tayi,suna cikin wannan yanayin sai ga Babanta ya shigo d'akin da sallama,tsagaitawa suka yi da dariyar da suke yi suka amsa masa,,shima fuskarsa da fara'a na jin dad'in yanayin daya iske su yayi murmushi kafin ya samu guri ya zauna
"To..! Wane albishir kuka samu ne haka kuke ta dariya abunku..??"

"Inafa albishir wannan y'ar taka idan tana nan ai kasan halinta bata tab'a zama bata sa mutum dariya ba.."

"Aaa! Ai hakan yana da kyau,da ace wane ya saka kuka gara ace wane ne ya saka dariya ko ba haka SHALELEN baffanta..??"
Murmushi ta saki tana matsawa kusa da baban
"Ehh! Yawwa Baba na san dama kana bayana ai..!"

"Sosai ma kuwa,mu kullum ai muna tare..Babar nan taki ce dai sai..!"
Da sauri Inna ta tari numfashin sa
"Nayi me ni kuma..??"

"Aaahh! To bari dai mu bar kaza a cikin gashinta..Ko kuwa dai mu fige..??"

"A'a baba a kyaleta.."
Sabina ta fad'a tana dariya,Inna kam cewa take
"Gwara dai a fige idan yaso sai mu ga wanda zaiji kunya..!"
Dariya baban yayi shima ya ce
"Aahhh! To mun fasa gwara a kyaleta kada mu wahalar da baiwar Allah.."

Duka sai suka sake yin dariya,,Baban ne ya d'an tsaigaita cikin alamun na wanda yayi mantuwa ya furta
"Ohh! Ni kam har kun sani zan manta abunda ya

Please Login or Register in order to submit comment