Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana d'aga masa hannu a sakamakon gaisuwar da yake masa da bai samu damar amsawa ba,,tsarin gidan wani irin had'ad'd'en duplex ne wanda tsayawa a fayyace shi zai zama k'auyanci,ta ko ina idan har mutum ya kalla ginin gidan da tsarinsa zai tabbatarwa kansa ya tsaru iya had'uwa,haka nan duk kushen mai kushewa bai isa ya kalli wannan gidan yace bai masa ba,musamman duba da yadda tun daga harabar gidan ya kasance cike da wasu irin shuke² na alfarma,,haka ma daga tsakiyar gidan daya kasance yana d'auke da had'ad'd'en roundabout wanda wasu irin fitilu suke bawa gurin haske nd still suma d'in suna zagaye da kyawawan flowers wanda suka sake k'awata yanayin gurin,hakama ta jikin walls d'in gidan daga duka sides shima ya kasance tun daga ta wajen sa kafinma mutum yayi arba da ainihin cikin gidan,,,direct carport ya nufa da su,bayan ya gama daidaita parking sannan ya fice daga motan ba tare da yayiwa sultan magana ba,shima d'in bai kula shiba ya fito dan yasan abunda shirun sa ke nufi,nan dukansu suka tasamma apartment d'in dake tsakiyar gidan,,Muhammad a gaba yayin da sultan yake biye da shi har suka tsaya bakin k'ofar apartment d'in,ba tare daya tsaya bawa kansa wahala ba ya murd'a handle d'in jikin k'ofar sannan ya tura kansa zuwa cikin k'ayataccen parlor'n yana yin sallama,,sanyayyan k'amshi mai tattare da sanyin ni'ima ne ya buge shi,nan ya d'an lumshe idanunsa a hankali yana jin wani irin farin ciki na ratsa duka veins d'insa a sakamakon tsintar kansa da yayi cikin gidansu.
Sakkowarta kenan daga saman staircase sanye cikin Arabian gown ta yane kanta da vail d'in kayan,y'ar fuskarta nan tasha light make-up daya amsheta,sosai tayi matuk'ar kyau gwanin a saceta a gudu,,karaf sai idanunta suka sauka akansa yana shigowa,ihun murna ta saki cikin k'araji tana fad'in
"Yah *HAMMAD..!"*
Murmushi ya sakar mata yana kallon yadda ta kwaso a guje,ko data zo gabansa bata tsaya wata² ba ta mak'ale shi tana ta murna,sai lokacin Sultan ya saki fuskarsa dake had'e sannan ya d'an matso kusa da su yana fad'in
"Wato shi kad'ai kika gani ko Baby.!?"
Saurin d'agowa tayi daga jikin yayan nata ta waiga inda taji maganarsa,four eyes suka yi da shi yana sakar mata murmushi,amma sai tayi saurin sauke kai k'asa,itanma tana murmusawa nd muryanta k'asa² ta ce
"Kaiii! Yah Sultan,,ai dai kasan ban ganka bane,,kuma ma ai a bayan Yah ka b'uya shi yasa..!"

"Yeah..! Dama na san amsar kenan ai,kullum a bayansa nake mak'alewa ba..!?"
Sake sunkuyar da kai tayi tana wasa da ring d'inta nd ba tare data sake yin magana ba sai d'an murmushi da take ta zubawa,,ga Hammad kuwa tab'e baki yayi kafin yaja hannunta suka nufi cikin tsakiyar cuitions while yana fad'in
"Daddy's Kiddo..! Where's the households CEO..!? Naji gidan so quite,,shima wannan sarkin kwallon baya nan ko..!?."
Y'ar dariya tayi wacce ta bayyanar da asalun kyaunta,nd ta kuma bayyanar da tsananin kamarta da Hammad,tana shirin yin magana sai sultan ya rigata
"Kai dai wollahi baka da kirki Mamma d'in ce ta koma Households CEO..!?"
Hararan sa Hammad yayi ba tare daya kula zancen da yake masa ba,sai kasa kunne daya sake yi akan maganar da kid sis d'in nasa ke masa
"Where's she ne daddy's Kiddo..!?"
Ya sake tambaya yana zuba mata ido,a hankali ta masa murmushi kafin tayi nuni da finger d'inta zuwa hanyan staircase,hannun yabi da kallo zuwa inda take nuna masa yana murmusawa,a tsaye ya hangota ta dafe hannunta d'aya a jikin wall tana kallonsu fuskarta cike da fara'a,kallo d'aya ya isa yasa mutum ya gane cewa wannan ita ce mahaifiyarsu shi da Kid sis d'insa d'in saboda yadda suka yi tsananin kama da ita,,cikin sauri ya mik'e a gurin ya nufi inda take while itanma tana tahowa gare shi,rungume ta yayi saurin yi,duk da matar ba wai gajera bace amma duk Hammad ya kere ta a tsayen
"Nayi kewarka yaro na..!"
Hamshak'iyar matar ta furta tana shafa bayansa zuwa kansa nd still suna mak'ale da juna yana zuba mata zance kamar ba shi ne wannan miskilin ba,sai da suka gama murnan ganin juna kafin suka nufo cikin parlor'n tana fad'in
"A'a..! Sultan tare kuke dama..!?"
Murmushi yayi kafin yace
"Ehh! Mamma,, nima abunda yasa banyi magana ba,naga wannan d'an darun naki yana rigima shi yasa nayi shiru..!"
Murmushi tayi tana shafa kan Hammad dake mak'ale da ita kamar k'aramin yaro,while shi kumayana fad'in
"Kaji shi wai d'an daru sai kace wani jariri..!"

"Uhmm! Dafa..!? Kana da maraba ne da infants.."
Hararar wasa Hammad ya jefama sultan d'in sai dai bai ce masa komai ba suka zauna nan cikin parlor,,bayan sun gaisa da Mamma sultan yake cewa zai wuce gida,,nan Mamma tace masa sai dai ya jira anjima sai su fita da Hammad d'in zuwa gidan nasu,,ko mintuna ashirin basu yi da shigowa a cikin gidan ba,tuni har an shirya musu table da kayan abinci na alfarma,,after sun ci sun yi godiya ga Allah (S.W.A) sanna suka mik'e suka yi sama,alwala suka d'aura dukansu kafin suka fito dan a lokacin tuni har har wasu guraren suka fara kiraye²n sallah sannan suka nufi masjeed.

A can b'angaren Sabina kuwa,lokacin ko data juya bata iya shigewa cikin gidan ba,har sai data ga fitarsa a zauren gidan,sannan da sauri kuma saita sake dawowa cikin soron,tana kallon lokacin daya tsaya suna magana shi da baffa saita lab'e daga gefe tana lek'ensu har sanda taga sun d'auki hanya,wasu irin hawaye ne suka sake zubo mata a lokacin data rasa ko na mene ne,kafin da sauri kuma ta kalli handkey d'insa daya bar mata,sai tasa ta share fuskarta tana kuma ci gaba da kallonsa,kamar kayan tsafi dai² lokacin ta ambaci sunan sa taga ya waiwayo,dan haka da sauri sai ta koma ta sake boy'ewa tana ci gaba da sauke hawaye,ta jima tsaye a cikin soron nasu har zuwa lokacin da taga sun b'ace mata sannan ta juya cikin rashin kuzari da niyyar komawa cikin gidan,,kusan karo suka yi da shi yana niyyar fitowa daga cikin gidan while itan kuma tana shirin shiga,saurin yin baya tayi tana sadda kanta k'asa dan bata son ko kad'an ta bashi fuskar da zai samu lagonta ko ya gaya mata magana,,shima d'in kallonta kawai yayi from head to toe kafin yaja wani wahalallen tsaki,yana tafiya cikin takaici yana fad'in
"Tabb' wannan shi ake kira aikin banza wai harara a duhu,kai dai LADO Allah yaso ka,,baka d'orawa ranka ba bare kasha wahala,,hhhh! Lallai iska tana wahalar da mai kayan kara..Idan ba mutum yaso kai kansa inda Allah bai kai shi ba,ina bak'auye ina d'an binni..!?? Lallai wani ya deb'o ruwan dafa kansa..!!"
A hankali ta d'ago kanta daga k'asa ta bishi da kallo sai dai bata samu damar yi masa magana ba,ta wuce abunta da niyyar shigewa cikin gida tana jan ajiyar zuciya,har ta kai k'ofa zata shige ta sake jiyo shewarsa yana tafe yana fito had'e da dariya,cikin duniyanci irin nasa yake fad'in
"Ayyee! Da rabon muyi kallo nan gaba,,hhhh! Zamu ga yadda k'arshen masu son abun duniya zai k'are,,idan an k'ika ana ganin baka da ko kobo,gobe zata yi aso ka,ko dan rufin asiri idan an kwaso kayan kunya..."
Tsayawa tayi chak a dai² k'ofar tana saurarensa,dai² lokacin daya sake shek'ewa da dariya kafin yasa hannu ya kwab'i bakinsa da yana fad'in
"Sshhh.! Kaji ka..! Kai dai LADON nan da kaud'in baki kake. ,ina ruwanka ne da zaka fad'i abunda zai faru..!?"
Duka yana magana ne da kansa nd still yana ci gaba da tafiya,dariyar muguntar daya saki a lokacin ne tasa Sabina saurin shigewa tana runtse idanu dan yadda maganarsa tayi mata zafi a rai,shi kansa LADON ko da yaga ta shige da gudu² sake tuntsirewa yayi da dariya kafin a fili ya furta
"Kad'an kika gani yarinya.. Daga ke har tsoffinki zaku san kunyi da ni..Mu zuba mu gani..!"
Daga haka shima d'in sai yasa kai ya fice daga soron.

Da gudu² ta wuce duka mutanen dake tsakar gidan zuwa d'aki,tana shiga ta kife akan gadonsu tana sakin kuka mai tsuma zuciya,sai da tayi mai isarta dan yadda take jin abu biyu ya had'e mata a rai a lokacin,matuk'ar idan har ace ba kukan tayi ba tana jin bazata tab'a iya samun sassaucin zafin da take ji a ranta ba,ta jima tana kukan kafin ta rarrashi ranta tayi shiru tana ci gaba da jan zuciya,a hakan nan da take a kife baccin wahala ya d'auke ta ba tare data shiryawa yinsa ba.

Isowarsu baffa k'ofar gidan yayi dai² da lokacin da ake kiran sallah,dan haka daga k'ofar gida ba tare da baffa ya shiga ba sai ya kalli su Hamudan yana fad'in
"Yawwa samarin baffa,maza ku shiga gida kuyi alwala ko,ku taho masallaci.."
Da sauri suka amsa da
"To baffa..!"
Sannan suka yi cikin gidan da gudu suna ihun murna,tun kafin su k'arasa shiga tuni har sun fara bada labarin irin motar da Hammad yazo da ita,ba iya sa'anninsu kad'ai ba hatta da iyayen su mata dake aiki a tsakar gidan sai da suka tsaya sauraren hirarrakin nasu,,inda daga nan sai suka shashantar da batun zuwa masallaci har sai da baffa ya dawo ya tarwatsa su da carbi sannan duka suka fashe.Nan a cikin gidan yasa su duka suka yi alwala a gabansa sannan ya tusasu a gaba har massalaci suka yi sallah,bayan da suka idar duka suka fito daga duka sai suka sake nufo gida inda anan ne kuma suka d'auki ledar da Hammad ya basu su kaiwa Sabina dan su kam nasu tuni baffa yayi dividen nata wa duka yaran gidan,Sule ne ya kalli Hamudan cikin k'asa da murya yadda babu wanda zai ji shi yana fad'in
"Yawwa! Hamudan zo muje mu kaiwa Yaya Sabina nata ko..!? Kaga ma ko nasan zata k'ara mana a nata.."

"Ehh! Kuwan muje mu kai mata..amma kayi shiru to kada kasa su yaroro su ji,,kasan cewa zaiyi shima zashi,kuma bayan ba dasu muka samo ba amma duka baffa ya raba mana kai d'aya da su.."
A sace suka tashi daga cikin sauran y'an uwan nasu suka fice,cikin sauri² suka nufi hanyan d'akin su Sabinar,,tana zaune kamar wacce aka dasa ta had'a kai da guiwa,yayin da ta zubawa guri d'aya ido tana tunani,da sallama suka shigo sai dai saboda nisan da tayi a duniyar tunanin yasa bata jisu ba har sai da Hamudan ya tab'a ta yana fad'in
"Yaya.! Kina jin mu kuwa..!?"
A d'an firgice ta d'ago kanta tana fad'in
"Uhmm! Me kace Hamudan..!?"
Baki ya fara washewa yana kallonta,yayin da yake yiwa Sule alama daya b'oye lesser,shima d'in y'ar dariya ya saki yana mayar da hannunsa baya kafin ya ce
"Yaya..! Kin san me..!?"
Kai ta girgiza musu tana kallonsu duka kafin ta ce
"A'a.. Mene ne..!?"

"A'aahh! Yaya ai sai kin bamu tukuici zamu fad'a miki.."
Siririyar ajiyar zuciya tayi kafin ta kallesu tana girgiza kai
"Shi kenan to naji,,ku fad'a zan baku.."

"Kaii! Yaya kada fa mu fad'a miki kice kin fasa..!"

"Bazan fad'a ba,,ku dai ku fad'a min,kunji y'an k'anne na.."
Ta fad'a a matuk'ar k'agauce
"Aaaa! Yaya sai idan kinyi *ALK'AWARI* zaki bamu sannan zamu fad'a miki.."
Jimm tayi tana kallonsu cikin rabuwarta hankali,idan ta kalli wannan sai ta juya ta kalli wannan duk ta rasa yada za tayi,a hankali kuma cikin rashin wadataccen kuzari ta furta
"Shi kenan nayi *ALK'AWARI* zan baku,,yanzun ku fad'a min mene nw.."
Ledar dake rik'e a hannunsa ya fiddo daga bayansa yana mik'a mata,sai data kalli yaron kafin ta ce
"Na waye wannan d'in..!?"
Yana dariya yake fad'in
"Uhmm! Yaya dama fa shi ne da muka raka shi ya bamu yace mu kawo miki..! Kuma ko Yaya kin san wani abu.!?"
A hankali ta girgiza masa kai while taba amsan ledar,sake rage murya yayi can k'asa kafin ya ce
"Da mota yazo..! wollahi ki Yaya dan baki ga motar ba,,tabb'! Kin san dame motarsa take kama kuwa..!? Cabb' Hamudan d'an bata labarin yadda take..Nifa Allah ko Yaya,tunda nake ma ban tab'a ganin irinta ba.."
Hamudan ne yayi caraf yana cewa
"Ai Yaya idan kika ga motar ko,,aradun Allah sai kin kusa sumewa..Kin ganta kuwa kamar jirgi..Gata k'atuwa ga kyau kamar me..!"
Shiru ta sake yi tana sauraren surutun nasu kafin ta ajiye ledar a gefe kana ta mik'e a gurin,naira goma² ta d'auko ta basu sannan tace suje su kyaleta bata jin dad'i yanzun,ba don sun soba haka nan dai suka fice dan su a son ransu ta bud'e ledar suga ko mene ne a ciki,,bayan fitar su har ta mik'e a kan pray mat d'in sai kuma ta dawo ta d'auki ledar sannan ta sake hayewa saman gadon,,sai data zauna dai² akai kafin ta shiga zazzage abunda yake cikin,kwalayen turaruka ne suka fara fad'owa har guda uku kafin wani kyakykyawan kwalin da yake nad'e da wani irin lesser mai kyalkyali shima ya fad'o,na turarukan ta fara juyawa tana dubawa,turaren good girl idanunta suka fara sauka akai,a hankali ta kai hannu ta d'auka kafin ta zaro shi daga ciki,tsarin kwalban kansa abun kallo ne dan bare kuma abunda ke ciki,yadda aka tsara kwalban da wani irin ado tamkar wani hill shoe,nd idan har bawai mutum ya san yadda abun yake ba koya karanta jikinsa babu lallai yayi saurin gane mene ne a ciki,ita kanta sai data juya shi yafi sau nawa a hannunta kafin ta fahimci abunda ko mene ne nan ta ajiye,sannan ta sake d'aukan d'ayan wanda yake d'auke da sunan *beyonce midnight heat* rad'a-rad'a ajikin kwali,shima kansa turaren ba baya bane,hakama tsarin kwalabansa anyi shi ne ta yadda zai ja hankali,sai kuma d'ayan daya kasance irin 2in1 gift set d'innan,daga sama an rubuta *story of love* da k'ananun rubutu,nd da manya kuma an rubuta *CELEBRATE* sosai sunan yaja hankalinta,har bata san lokacin da wani mugun murmushi yayi escaping daga bakinta ba,a hankali ta rungume kwalin a jikinta tana lumshe idanunta,ta jima a haka kafin ta mik'e ta tattara komai ta mayar cikin adakarta sannan ta dawo ta kwanta akan gado sai sakin murmushi take abunta cike da tunanin abunda ya wakana kafin ya tafi.

Fitowarsu daga masjeed suka nufi gidan,after sun iso tsakiyar parlor'n suka iske Mamma zaune ita da kid sis d'in Hammad,basu wani zauna ba Sultan yayi mata sallama,nd shi kuma Hammad yake fad'a mata zaije gidan su Sultan d'in su gaisa da Mom,,d'agowa yarinyar tayi tana kallon Hammad,yanayin ta cike da son tayi magana amma sai taga bai kalle taba,a hankali ta waiwaya gefen da Sultan yake tsaye kafin tayi magana
"Yah Sultan nima zani..!"
Hammad ne yayi saurin kallonta kafin ya ce
"Ina ne d'in zaki je..!?"
Marairaicewa tayi tana cewa
"Gidan su Yah Sultan d'in zan biku.."
Sai daya harareta kafin ya furta
"Da yake yawo neba zaki je,,ehmm! Bama wannan ba,kina maida hankali a skul ko kuwa.!?"
Shiru tayi tana sauke kai k'asa,siririn tsaki yaja kafin ya tab'a sultan yana fad'in
"Man kaga mu wuce kawai.!"
Kallonsa sultan yayi kamar zaiyi magana da sauri Hammad ya d'aga masa hannu
"Malam..kada kace komai,,wollahi kaji na rantse ko..babu inda zata bimu,,yarinya sai shegen son yawo amma karatu ta tsaya ta maida hankali tak'i,,ai na kusa dawowa ne,zamu gamu..!"
Babu yadda sultan ya iya kan dole yayiwa Mamma sallama sannan yabi Hammad d'in da yadda yake so coz yasan matuk'ar ya fad'i magana baya tab'a canjawa shi yasa ko daya rantse ma yaja bakinsa yayi shiru,nd yaga Mamma bata ce masa komai ba shi yasa dolensa shima yayi musu sallama ya fice,,a carport ya iske shi har ya shige yana jiransa,yana zuwa kuwa suka fice daga gidan,,basu wani yi tafiya mai nisa ba daga gidan nasu,dan duka a k'afa ma idan mutum ya fito daga gidan zai iya hango line d'insu Sultan d'in amma saboda ajebonci dake d'awainiya dasu duka yasa sai da suka d'auki motor,daga nan suka yi cikin Allu avenue zuwa gidan su sultan d'in

Sai misalin k'arfe tara na dare sannan Hammad ya baro gidansu sultan ya nufo gida,bayan irin hiran da suka yi da Mom d'in sultan d'in,,lokacin kam ko daya dawo gidan still suna zaune kamar yadda ya barsu,,sallama kawai yayiwa Mamma da kid sis d'in nasa duk da ta d'auki fushi da shi a dalilin k'in tafiyar da yayi da ita,,daga nan yayi sama abunsa ya shige bedroom d'insa,ko daya shiga shirin bacci ya shiga yi dan yadda yake jin gajiya a jikinsa har lokacin,,almost 30 minutes da shigowarsa ya gama duk abunda zaiyi sannan ya kwanta,a lokacin da yanayin garin ya d'auki shiru shima gare shi hakan ne ya kasance,,yayi shiru abunsa shi kad'ai a d'akin ba tare da jin motsi ko sautin komai ba,yana daga kwancen a hankali tunaninsa ya fara yin nisa zuwa kan abunda ya faru kafin tahowar su gida,yadda komai ya fara dawo masa a kwakwalwa daki² sai ya sashi sake gyara kwanciyansa yana sake holding pillow dake manne a jikinsa,a hankali ya fara lumshe idanunsa while yana licking lip tamkar wanda yaji wani abu mai zak'i akai....



*Tofa.! Fan's gaskiya kam sai kunyi hak'uri dani,dan wollah cikin kwanakin nan Y'an NEPA sun tsiro mana da wulak'anci,, jiya throughout bamu ga wuta ba,nd yau sai after 1,idan komai yayi dai² zaku jini akan lokaci, sai kun k'ara hak'uri..*


#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••
_Devoted to my lil 6ters *Real hafsy & Mamah Zee.*_
_Bestowed to *Sis Hubbeey.*_

*Bismillahir-rahmanir-rahiim.*

*11*
_#Discomfort_

Kyakykyawan murmushi ya ajiye a saman fuskarsa mai tattare da wani irin sukuni nd yana sake holding pillow d'in a jikinsa kamar zai tsaga jikinsa ya sashi ciki,idanunsa ya lumshe take sai ya fara tuna glamorous face d'inta mai cike da tashin hankali nd hawaye,a hankali ya sake sakin ajiyar zuciya dan yadda yake tuna moments d'insa da ita da suka ruga suka wuce,gani yake kamar yanzun ne suke kan faruwa,ya jima cikin wannan yanayin na tunani kafin wani irin bacci mai cike da nutsuwa yayi gaba da shi.

Wasa² yau kwana biyu kenan da dawowar Hammad gida saboda break da suka samu,,sai dai wani abun mamaki a tattare da shi tun daya dawo d'in har kawo wannan kwanakin da aka d'iba ko da wasa bai iya yiwa Mamma maganar kayan da yazo da shi gidan ba,nd bawai kuma dan ya manta bane,sai dan kawai yana tunanin ta yadda Mamma zata fahimci al'amarin da zai fad'a mata d'in,a nasa hangen gani yake idan har dan ace ta itan ne bazai tab'a samun matsala ba,buh yadda daddyn sa zai fahimci lamarin idan har maganar ya kai kunnensa a wannan gab'ar shi ne abun jinsa,dan yadda ya tabbatarwa kansa idan har yaji wani magana sab'anin wanda ya shafi na karatunsa dole ne sai sun kai ruwa rana da shi,shi yasa duka kwanakin sai ya rasa ta yadda zai b'illoma lamarin,,kullum zai fita daga gidan cike da son neman shawaran da zai magance masa matsalar yake tafiya amma kuma idan ya fitan haka nan zai sake dawowa ba tare da ya samu masalaha ba tunda ya kasa sanar ma kowa,shi yasa a kullum ya kasance cike da tsoro yake dan bai san yadda za suyi da Mamma ba idan har taga kayan ya sani dole ne ta tambaye shi.
Yau ma ko daya fita sun had'u da Sultan a race course wajen morning exercise,a nan nema yaso ace sun tattauna matsalar da shi buh sai kuma ya rasa ta yadda zai b'illowa lamarin,shi yasa har suka rabu da juna bai samu daman yi masa zancen ba,nd maganar kullum cinsa yake arai sai dai ya kasa fidda shi ga wani,,cikin wannan k'adamin kwanaki suka ci gaba da wucewa ba tare daya samu damar sanarma da kowa ba ciki kuwa har daita kanta Mamma d'in.

Da sanyin safiya kimanin sati guda da dawowarsu,yana tsakiyar bacci ya jiyo ana knocking,a time d'in shi kam ko tashi ma baiyi ba,sai da yaji ana knocking d'in sannan ya mik'e idanunsa har time d'in cike da bacci ya nufi k'ofan nd yana tambayan waye,daga wajen Mamma ta amsa shi da cewa
"Idan zaka bud'e ne ka bud'e sai kaga ko waye,,if not kuma ka koma kaci gaba da baccin asaran,maimakon ace mutum ya tashi amma tun d'azun abu ya gagara,kusan zuwana uku nan amma still sai da kasa ni dawowa duk da nace bazan sake dawowa tashinka ba,,Allah sa a skul d'in ba wannan shegen baccin kake zuwa kayi ba,shi yasa tun tuni na fad'awa Daddyn ka gara kayi karatu a nesa damu amma ya kafe kan baza kaika karatu waje ba kana yaro,ai ga abunda zama cikin k'asar tamu yake shirin haifarwa nan,,ni dai Allah sa ba wahalar damu kawai kake ba,kana sawa muna b'arnatar da dukiyar mu a banza.."
Murmushi ya saki still idanunsa a rufen dai² lokacin daya bud'e k'ofar nd ya d'an jingina da ita
"Haba Mamma..! Har sau nawa kike son na fad'a miki,,nifa idan ba wai na dawo gida ba,ko baccinma bana komawa idan nayi sallah.."

Hararan sa tayi tana fad'in
"Kai tafi can, waye zaka fad'a mawa wannan zancen naka ya yarda,mutumin da idan ya kwanta tamkar corpse (gawa) shi ne zaka bani wannan labarin k'anzon kuregen naka na yarda.."

"Yeahh! Mamma kawai dai dan baza ki yardan bane,,amma bana iya bacci a skul sosai ki tambaye Sultan tunda shi kina yarda da maganar sa.."
Tab'e baki tayi kafin ta sake kallon shi up to down,cikin yanayin fara fusata ta furta
"Wai Hammad wannan wani sabon iskanci ne ka koyo..?? Ina magana kana tsaye min da idanu a rufe.!?"
A hankali ya fara k'ok'arin bud'e sleeping eyes d'insa da kyar har ya gama ware su,sai dai yana kallonta yana ci gaba da k'ik'k'ifta su alamun baccin bawai ya gama sakinsa ba kenan har lokacin,hararan da Mamma ke sake banka masa ya sashi yi mata murmushin yak'e kafin ya furta
"Mamma what's the problem ne..??"
Siririn tsaki taja kafin ta ce
"Ban sani ba,,da iskanci yasa kazo min da idanu a rufe kenan ko..!? Bama wannan ba,wancan kayan daka bari a booth na waye ne..!?"
Wani mugun fad'uwa gaban Hammad yayi kafin cikin in'ina ya fara fad'in
"Ammm! Ehmm! Mamma.."
Hannu ta d'aga masa alamun ya mata shiru,shirun yayi buh bakinsa sai motsi yake yana son yin magana,duk irin yadda ya taso da bacci a idanunsa duka tuni ya neme shi ya rasa,nd a

Please Login or Register in order to submit comment