Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bai saki ba saima k'ara had'uwa da yake,wanda zuwa lokacin kuwa ba iya hadari kad'ai bane har da wasu irin firgitattun thunderstorms ke tashi,,sam hankulan jama'a tun daga wayewar garin kawo wannan lokacin kusan zamu iya cewa ba'a kwance yake ba,duba da kasancewar a kullum idan har akayi ruwa sai mutane sunyi aikin fito da ruwa daga gidajen su gami da shanyar wasu daga kayayyakin su masu muhimmanci,,a yayin ne kuma a wasu daga cikin sassan garuruwa suke fama da matsalolin hanyoyin da ruwa zai wuce,,wuni guda ana fama a cikin wannan yanayi na k'ila wa k'ala,a haka har aka sallaci sallar maghreb,,tun misalin k'arfe takwas saura y'an mintuna yayyafi ya fara sauka mai k'arfin gaske had'e da wani irin iska dake kad'a ilahirin bishiyu zuwa rufin gidajen da bai samu ingantaccen rufi ba,har zuwa k'arfe 10pm wanda a lokacin ruwa ya sake yin k'arfi sosai fiye da farko,wanda yasa ilahirin gari sai ya sake yin bak'i,ruwa sosai ya kece kamar da bakin k'warya,haka har kusan k'arfe sha biyu na dare ba tare da ruwa yatsagaita ba.

*FLORIDA STATE,,U.S.A..*
Zaune suke su uku cikin *Pura bean coffee company* dake a within arean *Jacksonville* BBC news suka fara watso labarai,ko highlight na news d'in ba'a gama ba,Sultan ya kallesu yana mik'ewa tsaye
"Dude's.. Let us leave,,zaman gurin nan ya fara damuna..Ina buk'atar na kwanta..."
Gaba d'ayansu suka mik'e a tare bayan sun biya chargee's nasu suka fice daga coffee shop d'in suka kama hanyar komawa hostel,,suna tafe suna hira kasancewar tuni Hammad ya gama fushin da yake da sultan aka ci gaba da sabgogin karatu tare..

*NIGERIA..*
A 9ja kuwa yau tunda gari ya waye da wani irin gagarumin tashin hankali aka tashi,musamman ga mazauna yankin garin wudil dake cikin jihar kano,wanda a daren daya gabata cikin k'auyen *KAUSANI* iftila'in ruftawar k'asa ya afku,wanda ata dalilin wannan iftila'i daya faru har ya janyo sama da mutane ashirin sun rasa rayukansu,yayin da wasu kuma da dama suka jikkata (suka samu raunuka),a sakamakon k'asa da tayi laushi sanadin ruwan da ake yawan laftawa a y'an kwanakin har ya janyo faruwar had'arin.....
(To sai muce Allah ya k'ara kiyayewa).





#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••

*24.*
_#Separation_

*Hak'ik'a rayuwa da mutuwa duk nufin Allah ne akanmu,shi yake da ikon yanke hukunci game da rayuwar mu duka,tsara labari ba komai bane face nishad'i,ku sani cewa dan wani ya mutu ko wani ya rayu ba abune daya kamata muyi magana akansa ba,tunawa da cewa lallai wata rana muma zamu mutu k'arin imani ne kamar yadda kissar Annabi (S.A.W) da sahabbansa ta zo ku karanta domin na tabbata zaku amfana,,,wata rana Manzon Allah (S.A.W) yana zaune tare da Sahabbansa,sai ya fara tambayar su d'aya bayan d'aya,sai ya fara da Sayyidina Abubakar Assiddik' yace:"Yaa Abubakar! Me kake so a duniya?" Sai Sayyidina Abubakar yace:Abunda na fi so a duniya 1-Zama a gaban ka,2-Kallon ka,3-Ciyar da dukiya ta gare ka,,Sannan Manzon Allah ya koma wajen Sayyidna Umar bin Khaddab,Manzon Allah (S.A.W) yace:"Yaa Umar! Me ka fi so a duniya?" Sai Sayyidna Umar yace:Abunda na fi so 1-Ayi min umurni da kyakkyawan aiki ko da a b'oye ne,2-A min hani da mummunan aiki ko da a bayyane ne,3-Da kuma fad'in gaskiya ko da tana da d'aci.Sannan manzon Allah ya koma wajen Uthman bin Affan yace masa: "Yaa Uthman! Me kafi so a duniya?" Sai Sayyidna Uthman d'an Affan yace:Abunda na fi so a duniya,1-Ciyar da abinci ga mabuk'aci,2- Yad'a sallama,3-Yin sallah cikin dare a lokacin mutane suna bacci.Sannan Manzon Allah (S.A.W) ya koma ta wajen Aliyyu bin Abiy 'Daalib,yace masa: "Yaa Aliyyu! Me ka fi so a duniya?" Sai Sayyidna Aliyyu yace: abunda na fi so a duniya,1-Azumi a lokacin rani,2-Karrama bak'o,3-Yak'ar abokan gaba da takobi.Sannan Manzon Allah (S.A.W) ya koma wajen Abaa zarril Gifaari,ya ce masa: "Yaa Abaa Zarri? Me ka fi so a duniya? Sai Abaa Zarri yace:Abunda na fi so a duniya,1-Yunwa,2-Jinya,3-Mutuwa.Sai manzon Allah (S.A.W) yace:"Saboda me yasa kake son su?" Sai Aba zarri yace:1-Ina son yunwa ne don zuciya ta tayi laushi,2-Ina son jinya don zunubi na yayi sauk'i,3-Ina son mutuwa saboda saduwa da ubangiji na.A wannan lokacin sai ga Mala'ika Jibrili (A.S) ya saukko zuwa majalisar Manzon Allah (domin hirar ta su ta birge shi ),sai yace: ni kuma ina son abubuwa uku a duniyar ku,1-Isar da sako,2-Bayar da amana,3-Son nakasassu.Daga fad'in haka kuma sai ya tashi zuwa sama sannan ya saukko a karo na biyu yace Allah mad'aukakin sarki yana karanta muku sallama,hirar manzon Allah da sahabbai tayi dad'i,harma Allah yana gaishe su sannan Allah yace yana son abubuwa uku a duniyar ku,1-Harshe mai ambatonsa,2-Zuciya mai tsoronsa,3-Jikin da aka jarrabce shi da balaa'i kuma yayi hakuri.Tsarki da godiya sun tabbata ga Allah,, dan haka y'an uwana kada ku manta da Addu'o'i guda uku a cikin sujjadarku..1-"Ya Allah ina rok'on ka kyawawan halaye,2-"Allah ka azurta ni da tuba zuwa gareka tabbatace,3-"Ya Allah mamallakin zuciyata ka tabbatar da ita akan addininka..Majalisar Manzon Allah makarantar mai imani ne.Sannan lada ku manta Ubangiji (S.W.T) ya fad'a a cikin littafinsa mai tsarki cewa:"Shi ne wanda ya halitta mutuwa da rayuwa domin ya jarraba ku,ya nuna waye daga cikinku ya fi kyawun aiki,shi ne mabuwayi,mai gafara."(Suratul Mulki aya ta 2)..Dan haka hak'uri akan komai na rayuwa shi ne mafi alkhairi a garemu,,Allah ya datar damu duniya da lahira..Ameen.👏*
_Tunatarwa ne gare ku masoya..💞_

••••••••••
A wannan wayewar gari kusan abunda ya afku a daren jiya ba iya garin Wudil kad'ai ya tab'a ba,dan zamu iya cewa garuruwa da dama sun samu afkuwar iftila'i iron wannan,sai dai babu inda akayi rashin da akayi kwatankwacin na garin wudil,saboda nasu lamarin shi ne akan gaba a dalilin munanarsa,daya zama akusan duk hanyar da mutum zai ratsa ta cikin wannan yanki na *KAUSANI* d'ai²kun unguwanni zuwa k'auyuka ne mutum zai shiga ya fito ba tare da yaji labarin anyi mutuwa ko an samu jikkata ba,wani gidanma tun kafin ka shiga zaka jiyo koke²n ahalin gidan a sakamakon rashin da suka yi,,yayin da wasu ke kukan mutuwa wasu kuwa nasu kukan ya ta'allak'a ne dalilin rasa muhallinsu da suka yi,haka nan wasu kuma wa rasa dukiyoyinsu da suka yi ya kawo faruwar hakan.
A cikin k'auyen su *SABINA* ma hakan ce ta kasance,,sai dai su nasu garin tun wayewar gari yake shiru,baka jin sautin komai face k'ugin manyan Van's zuwa caterpillars,haka nan da zarar ka nufo k'auyen tun daga farkon sa zaka fara cin karo da rufin gidaje wanda iska ta d'age daga muhallinsu tayi watsi da su,wani gurinma kana kallo ba sai ka sake ba saboda yadda al'amarinsu ya munana a daliliniftila'in daya faru kusan a nan d'in nema yafi afkuwa.Can daga gefe kuwa motoci ne na y'an jaridu,jami'an tsaro wanda suke da alhakin kare faruwar had'ura,sai kuma wakilan gidan gwamnati,,duka ilahirin jama'ar garin da suke raye an tare su guri guda,majinyantan kuwa tuni har an nufi asibiti da su domin basu taimakon gaggawa,,yayin da har lokacin y'an jaridu suke kan d'aukan rahoton abunda ya faru,har ma da aikin zaro ragowar corpses (gawarwaki) da k'asa ta binne,,,ahalin gidan su Sabina zaune gefe guda sunyi jigum²,fuskokinsu d'auke da damuwa,alhini gami da tashin hankalin da zaisa mutum fahimtar suna d'aya daga cikin ahalin da sukayi rashi a wannan yankin,,idanunsu sunyi wani irin jajir saboda tsabar kuka,damuwa mai girma bayyane k'arara a fuskokinsu,da yasa a wannan lokacin ma ko magana babu mai iya yinta a cikinsu saboda al'amarin ya matuk'ar girgiza su ba kad'an ba.
Yinin ranar sur aka shafe ana aikin ciro gawarwaki amma ba'a gama ba,wanda a k'arshe saboda hak'ar k'asa da akayi ya fara zurfi ya janyo k'asa taci gaba da k'ok'arin fara amsawa,wannan dalilin yasa akan dole aka dakatar da hak'ar k'asar.Daga nan aka tattara matattu da rayayyu a manyan Van's sai sauran y'an kayayyakin su da suka tsintsinta akayi hanyar cikin gari da su.
A ranar bayan an kawo su aka wuce da gawarwakin zuwa asibiti domin sake tantancewa,,ak'alla sai da aka d'auki kwanaki biyu tsakani kafin a bawa ko wane ahali tasu gawar,bayan anyi musu sutura aka sallame su a babban filin gidan sarauta sannan aka kaisu gidanjensu na gaskiya,,cikin wad'anda aka rasa sun had'a har da Baffa,,Baban Sabina kuwa da Baban LADO duka suna kwance a gadon asibiti,sakamakon karaya da suka samu,hakama sauran mutanen gidan da dama sun samu raunuka,,Bayan y'an kwanaki da faruwar wannan *AL'AMARI* duk da gwamnati ta killace al'ummar wannan yanki ta bawa sauran jama'ar da suke raye tallafin muhalli a cikin mabambanta daga unguwannin dake garin kano,,wanda a cikin wad'annan jama'a ya had'a har da ahalin su Sabina,inda suka samu matsuguni a cikin unguwar *Kawo* dake hotoro.Gaba d'aya faruwar *AL'AMARIN* ya zo musu ne a bazata mai tare da wani irin chanjin rayuwa mai tattare da damuwa a sanadiyyar rasa elder da suka yi a wannan zuri'ah..

*FLORIDA STATE,U.S.A..*
Suna fitowa daga *Pura bean coffee company* direct hanyan komawa skul suka d'auka,suna tafe suna hira yayin da a b'angaren Hammad kuma yayi shiru yana sauraren su kasancewarsa dama ba gwanin da za'a jishi yana magana ba,,tun kafin suyi nisa da inda suke ya fara jin jikinsa yana yi masa babu dad'i,babu wanda ya fad'awa irin yanayin da yake ciki,a haka suka ci gaba da tafiya cikin dauriya har suka shigo cikin skul ba tare da yayi magana ba,a lokacin ne kuma jikinsa ya sake d'aukan wani irin sanyi,kafin a hankali kasala ta fara saukar masa,jikinsa ya sake k'ank'amewa cikin blazer dake jikinsa dan dama yanayin garin akwai sanyi,,yayin da Sadeeq da Sultan suke ta fira abunsu cikin nishad'i ba tare da sun kula da yanayin da yake ciki ba har suka shigo room d'insu,wanda rashin kulawa irin nasu yasa ko da suka ji yayi irin wannan shirun hakan bai sa sun fahimci abunda ke faruwa ba,inda bed d'insa yake ya nufa,da baya ya zame ya kwanta while k'afafunsa na k'asa,ba taare daya iya cire ko da blazer d'in jikinsa ba bare takalmansa ya runtse idanunsa,,ajiyar zuciya ya shiga jerawa irin wacce sai mutum na cikin tsananin damuwa ko yayi kuka,haka nan yake jin jikinsa na sanar masa lallai akwai abunda ke kan faruwa da wani na jikinsa,to amma abunda bai sani ba shi ne,da Daddy'nsa ne,Mamma,Bassam ko kuwa BADRA..?? Ne ke cikin mawuyacin yanayi aka kasa sanar masa,duk ya kasa fahimta,,,cikin k'ank'anin lokaci damuwa ta sake rufe shi,kallonsa Sultan ya juyo yayi yana shirin yi masa magana ya ganshi cikin wannan yanayin da sauri ya nufo inda yake yana fad'in
"Broah.! What's wrong..!?"
Bai iya d'agowa ba bare ya samu damar bashi amsa,shima Sadeeq cikin sauri sai ya matso kusa da su yana kallonsu while yana fad'in
"Dude what's happen..??"
Sultan ne ya waiwayo yana kallonsa da fuskar damuwa
"Nima dai abunda ya bani mamaki kenan,yanzun fa muka shigo dukanmu,yanzun kuma na ganshi kwance,shi ne nima nake tambaya amma yak'i magana.."
Kallon mamaki duka suka tsaya yi masa kafin Sadeeq ya tambayae shi
"Man.! Wai mene ne hakan,mufa kana neman samu a damuwa.! Ya kamata ka fad'a mana abunda ke faruwa."
Da kyar ya mik'e ya zauna har lokacin idanunsa a d'an rufe saboda yanayin da yake jin jikinsa kamar anyi masa mahaukacin duka,,ba tare daya amsa musu ba ya mik'e cike da rashin kuzari ya d'auki waya,Number Daddy ya fara kira,yadda wayan ke sounding a haka shima zuciyarsa ke bugu tsoro fal ransa da taraddadin abunda zai jiyo idan an d'auka,muryar Daddy ya jiyo cike da k'oshin lafiya yana magana ta cikin wayar,sai daya sake sakin ajiyar zuciya kafin yayi masa sallama,bayan ya amsa sannan ya gaida shi cikin sanyin murya,duk da yanayin da yaji Daddy ya amsa masa gaisuwa ya bashi k'warin guiwan fahimtar lafiya k'alau suke,amma bai fasa tambayar lafiyarsu ba,take Daddy ya sake tabbatar masa da lafiyarsu,ajiyar zuciya ya sauke,suka d'an tab'a hira dan dama sun kwana biyu basu yi magana da shi ba,cikin tsautsayi har za suyi sallama a lokacin sai ya sakowa Daddy batun yana son zuwa ya duba su saboda yana jin kewar gida sosai,ko bari Daddy baiyi ya kai k'arshe ba ya tari numfashinsa yana fad'a masa ya bari kawai ba sai ya zo ba,gara yayi zamansa ya maida hankali sosai kan karatunsa,idan dan ta sune a duk lokacin da suka so zasu zo su ziyarce shi,amma shi d'in yayi zamansa sam bai ji dad'in hukuncin da Daddy yayi masa ba,a ganinsa yana tunanin kamar bai dace ace yayi masa haka ba saboda yadda duk abunda Daddy'n yace yayi yana kamanta yi masa biyayya,haka nan yayi ta tunanin dalilin da yasa Daddy'n ya hana shi zuwa. Damuwa fal ransa suka yi sallama da Daddy,bayan ya katse kiran ya kira Mammansa,sun gaisa da ita cike da girmamawa itama ya sanar da ita damuwarsa da duk yadda suka yi da Daddy babu jimawa,,har ga Allah duk da a gabanta suka yi wayar bata so akace Daddyn ga hana shi zuwa ba,saboda ko itama tana jin kewar ganinsa,buh duk da hakan sai tayi ta kwantar masa da hankali akan yayi hak'uri tunda Allah yasa suna yin video call lokaci zuwa lokaci,kada ya sawa kansa damuwa in sha Allah zata yiwa Daddy maganar idan yaso sai suzo su duba shi a skul d'in,godiya yayi mata sannan suka yi sallama ya ajiye wayar,,sake lumshe idanunsa yayi dai² lokacin Sultan ya gama cika da abunda yayi musu,a fusace ya juya ya bar wajen dan ganin rainin hankalin daya shuka musu,shima dai Sadeeq juyawar yayi ba tare daya sake cewa komai ba ya bar wajen.
Bayan barinsu a kusa dashi,ajiyar zuciya yaci gaba da saukewa,lokaci guda kuma tunaninta ya fad'o masa a rai,tabbas yana jin kewarta tun ba yau ba,kuma saboda dalilinta nema ya damu da son zuwa 9ja,badon komai ba sai dan yaga a halin da take ciki yanzun,,sai gashi tun ba'a je ko ina ba daga fad'awa Daddy har ya datse masa hark'alla ta hanyar hana shi zuwa,,duk da ba wannan ne karo na farko daya shirya yin tafiyar ba,amma rashin barinsa sosai yasa shi jin babu dad'i,saboda kusan sau uku kenan yana niyyar zuwa uzurori suna gifta masa wanda ala dole yake hak'ura tunda uzurin ya zame masa wajibi ne idanma baiyi ba babu wanda zai masa,sai gashi a lokacin daya gama sa rai a karo na k'arshe da yake nufin zuwan saboda ganin ya samu dama Daddy ya nuna k'in amincewarsa,,a wannan daren kam dan dai ana cewa bacci b'arawo ne da Hammad kam sai yace bai san da wane lokaci ne ya runtsa ba,bcos gaba d'aya ya rasa nutsuwar sa a dalilin tunani da yayi ta fama da shi.Tun daga wannan rana kuma sai ya zama ko da wasa bai sake shirin zuwa ba dan Daddy yace masa matuk'ar ya taho da saninsa ko babu zai b'ata masa rai,shi yasa ala dole ya yakice batun zuwan bai sake tayar da shiba,haka nan ko da yaga suma d'in basu jeba sai yak'i bin ba'asin dalilin k'in zuwan nasu,,a haka ragowar lokacin da yayi masa saura yaci gaba da tafiya...

*ONE YEAR LEAVE...*

*NIGERIA.*
Kimanin shekara guda kenan da faruwar al'amarin,wanda tun a bayan afkuwarsa a lokacin da gwamnati ta shiga lamarin su,sai ya zamanto bata yi watsi da su ba,bayan tallafin muhalli data bawa ko wane ahali,sannan ta samawa da dama daga cikinsu guraren aiki duk da kasancewarsu basu yi karatu ba,ta hanyar yi musu adalci a matsayinsu na y'an k'asa ta tallafawa rayuwarsu,,sannan batun k'ananun yara kuma ta d'auki nauyin karatunsu ta hanyar rarraba su makarantu musamman wad'anda ke cikin karatu kafin afkuwar al'amarin.

Tun bayan dawowarta daga extra lesson saboda gabatowa jarabawar S.S.C.E da take shirin zanawa take zaune cikin d'aki ta tusa litattafanta kamar tana bitar abunda ke ciki,uban tagumin data rafka shi ne kad'ai abunda mutum zai kalla yayi saurin gane hankalinta sam baya tare da abunda idanunta ke kali,,zuwa wannan lokacin tunaninsa ya jima da cika nata zuciya,y'an guntayen hawayen da suka ziraro mata a sakamakon tunawa da tayi babu ta hanyar da zata san ya dawo yasa takai hannu saman fuskarta ta goge hawayen,dai² lokacin Inna ta sawo kai tana shigowa cikin d'akin,akan idanunta duka taga komai daya faru,har tayi kamar zata fita kuma zuciyarta cike da tausayin y'ar tata ta k'araso ta zauna kusa da ita,har ta zauna Sabina bata sani ba sai data dafa kafad'arta sannan ta d'ago idanunta a hankali,girgiza kai Innar tayi cikin nuna alhini da damuwa tana cewa
"Haba Sabina..! Haba..!! Yanzun ace ke kenan ba zaki ji fad'an da nake miki ba,me yasa ne jam kike son komawa haka,sai kace ba musulma ba,ace ko wane lokaci idan kika zauna sai kin zubar da hawaye,,shin me yasa ne kam bakya ji..!? Na sha fad'a mikifa addu'ah itace abunda yafi kamata mu duka muci gaba da yi,in sha Allahu sai kiga ya dawo ya same ki kamar yadda ya tafi,ubangiji shi ya k'addara faruwar komai dan haka idan kin fad'a masa zai ji rok'on ki har ya biya miki buk'atun ki,,muyi ta addu'ah kinji,kada kice kin gaji,da yardar Allah sai kiga komai ya wuce tamkar ba'a yiba.."
Kanta ta sunkuyar k'asa tana sake share hawaye,kan nata Inna ta shafa sannan ta kamo hannunta ta rik'e
"Yanzun dai abunda nake so dake shi ne,kiyi k'ok'arin ragewa kanki damuwa,kina addu'ah nima ina taya ki,da yardar Allah komai zai zama tarihi.."

"In sha Allah Inna zanci gaba da yi.."

"Yawwa to..! Ko kefa ai gara ki saki jikin ki,ubangijin daya raba ku wata rana shi ne zai sake had'a ku da yardar sa.."

K'asa² ta amsa da "Allah yasa."
Sai da Inna tayi mata nasiha sosai kafin ta fita ta barta tana shirin tafiya makarantar islamiyya tunda Allah yasa sun sake samun ci gaba..

A gefen Hammad kuwa,tun kwanaki uku da suka gabata suka dawo k'asar tafe da d'umbin nasarori,sai dai rashin samun lokaci da yasa bai tafi tun a washe gari ba kasancewar saukar dare suka yi,,yau kam daya k'udurcewa ransa komai zai faru sai dai ya faru,yasa cikin shauk'i gami da begen abar k'aunarsa,dan tun daya tashi yake ji a ransa bazai iya jiran rana ta fad'i ba tare da yaje ya gano su ba,tun bama baffa ba daya d'auke shi matsayin d'a,,kyakyatawan murmushi ya saki yana shafo mustache d'insa da hutu ya sa ya sake cika da duhu,a fili ya furta
"Baffa in sha Allah ina hanyar zuwa na ganka.!"
A hanzarce yayi shirin tafiya cikin wani d'anyen baby bazin african getzner mai kalar coffee da aka yiwa aiki da milk d'in thread,ya kawo hula da ake cema tangaran ya murza,banda k'amshin dad'ad'an turarukan sa a lokacin daya fito babu abunda ke ratsa hanya,haka nan fuskarsa cike da annurin zaije ga abunda yake matuk'ar k'auna ya fito,ko da yasa aka shigar masa da kayayyakin da yayi musu tsaraba a sabuwar motar da Daddy ya siya masa k'irar Highlander tokunbo full option,sai yayi ma Mamma sallama kana ya fice a gidan,sai daya biya ya d'auki Sultan a gida kafin su d'auki hanyar garin Wudil,,tafiya suke a motan ba tare da wani hira ba sai cool music dake tashi,tunda suka d'auki hanya haka nan sai yake ganin tafiyar kamar an k'ara mata nisa,ko kuma dai dan ya jima bai zo bane yasa yake ganin hakan,ko kuwa dai dan ya damu ya iso ne shi yasa tafiyar tayi masa nisa oho,agogon hannunsa ya d'ago ya duba lokacin da suka iso mararrabar daya saba tsayawa,parking yayi daga gefe sannan suka fito,sai da suka d'an jira ko zasu samu wanda zasu bawa ajiyar motan,ganin basu samu ba sai yada su d'aukan hanya dan yanayin gurin yayi shiru babu hayaniya bare suga alamun mutane,wannan dalilin yasa kawai sai suka yanke shawaran su tafi,sai daya tabbatar ya rufe ko ina kafin suka tsallaka d'ayan hanunun suka ci gaba da bin hanyar da zata kaisu cikin k'auyen,,tafiya suke yayin da a b'angaren Hammad yake jin fad'uwar da gabansa keyi tun fitowarsu daga gida tana sake tsananta,,tsaf suka gama sharo hanya,sai dai ko da suka iso dai² inda yake tunanin abunda ya rage musu su k'arasa gidan take idanunsa suka fara nuna masa makeken fili babu gini ko kad'an a cikinsa,dan yadda gurin yake ma kamar wanda aka sa tsintsiya aka share ko kuma wanda ba'a tab'a zama a cikinsa ba,duk wani gini da yake ganin ya sani babu shi kwata² a gurin tamkar wanda aka shafe,hajijiya ya fara gani a idanunsa data sashi tsayawa cak yana sake bin filin gurin da kallo cike da tsantsar tashin hankali ya shiga sambatu.....



*Afuwaan fan's.. Kun san na sanar daku idanuna ke ciwo kwana biyu,shi yasa bana iya yi muku posting,,amma kuci gaba da hak'uri in sha Allah komai ya kusa zuwa k'arshe da yardar Allah..*




#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••

*25.*
_#Heartache_

K'ok'arin fad'uwa ya shiga yi a gurin banda sambatu babu abunda yake yi cikin tsananin damuwar da ko iya tantance abunda yake fad'a baya yi,da sauri Sultan yayi k'ok'arin taro shi dan yaga yadda ya taho yana fad'in
"Easy Man..!"
A dak'ile ya d'ago idanunsa da tashin hankali yasa su rinewa lokaci guda ya watsa masa su,duk da yana jikinsa amma bakinsa bai mutu ba
"Me kace..!?"
Ya tambaya cikin b'acin rai kamar Sultan d'in ne ya janyo faruwar lamarin,,yanayin da Sultan ya ganshi ciki shi ya tabbatar masa da lallai akwai damuwa mai girma a tare da shi,dan haka sai ya danne nasa b'acin ran ya sake rik'o shi
"Muje kawai..!"

"Muje ina..!? Gidan wace uwar kake son muje bayan banga abunda nake muradin gani ba tsawon shekara..!?"
Fuskarsa d'auke da wani irin fushi irin wanda tunda Sultan yake tare da shi tsayin tasowarsu bai tab'a ganinsa a cikin kwatankwacin saba,,d'an girgiza kai yayi dan yadda a lokacin yake ganin damuwar da Hammad d'in yake ciki ita tasa shi yi masa irin wannan maganar,rarrashinsa ya fara bayan yayi wearing fuskar damuwa yace
"Ina kace min da zamu je.!?"
Ajiyar zuciya ya shiga saki mai k'arfi yana girgiza kai shima,lokaci guda kuma wasu irin hawayen k'unci suka fara taruwa ta gefen idanunsa
"Me yasa za kiyi min haka..!? Me yasa³..!! Me yasa sai lokacin da kika bari na shak'u dake,na sabarwa da kaina soyayyar ki,,me yasa zaki guje ni a dai² lokacin da kika san nafi buk'atar kasancewa tare dake,,shin baki san a yanzun ne nake marmarin zuwa na ganki ba..? Kin sani nayi miki *ALK'AWARI* akan zan dawo gare ki duk runtsi duk wuya..Me yasa da kika san zaki tafi ki barni baki sanar dani inda zaki je ba..!? Why zaki min haka..!? Why..??"
Kallonsa kawai Sultan ya tsaya yi da matuk'ar mamakin ganin yadda ya dage yana magana shi kad'ai,tab'a shi ya d'an yi cike

Please Login or Register in order to submit comment