Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce masa komai ba,tana sake matse hawaye da sauke ajiyar zuciya a lokaci guda.
Rarrashinta ya fara yi ganin ta sake rikicewa cikin k'ank'anin lokaci,da kyar dai da sid'in goshi har ya samu ta dakatar da kukan,sai ya kwantar da ita ya sake fita,coffee ya had'o mata mai d'an karan zafi sai ya had'a mata da french toast,da yayi cikin sauri²,ya d'ora su saman midi ceramic tray,,kamar yadda ya barta haka ya dawo ya tarar da ita,sai dai izuwa lokacin tuni baccin wahala ya jima da sace ta,ajiyewa yayi ya zauna kusa da ita sai ya zuba mata idanu,wani irin sumammiyar k'aunarta tana sake taso masa,yayin da wuyar k'aunarta taci gaba da ruruwa a zuciyarsa,,ajiyar zuciya yayi sannan ya matsa sosai yana shafa fuskarta,saboda taci wani abu kafin ya bata magani,saboda idan yasan matuk'ar ta samu taci wani abu a cikinta zai k'ara taimaka mata ba zata yi saurin farkawa ba ko da baccin ya sake d'aukar ta,zata samu isashen lokaci.
Tana bud'e idanunta da kuka ta tashi dan dama da shi d'in tayi baccin,hankali a tashe ya rik'o ta yana tambaya
"Helpmate.! Mene ne kuma.!?"
A masife ta d'ago masa kumburarrun idanunta tana fad'in
"Dole mana ka kira ni da helpmate tunda ka gama da ni..!"
Duk iya yadda yake jin tausayinta sai data sashi sakin murmushi mai sauti,sake d'agowa tayi ta kalleshi while tana fashewa da sabon kuka
"Kuma Allah tunda kayi min dariya sai na fad'awa Mamma,tunda dama ta ce kada nayi kuka.."


*(Uhmmm! Lallai za'a kai k'ara fa kam,,,to ku fan's d'in Hammad kunji,sai ku shirya ma Mamma dan hukunci na tane nd ta kafa doka dama tun farkon,,ni dai real smasher babu ruwa na dan bani da party,ko ina ma ina nan,dan haka babu opposition party a guri na).😁*



#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••

*47.*
_#Ardor_

Zaro idanunsa yayi duka yana kallonta rik'e da baki,cikin salon lallashi sai yace
"Please mana,,kiyi hak'uri to na bari,kinji helpmate..!?"

"Ni ka dena cemin wani helpmate."

"Me yasa zan bari..? Bayan kin taya ni taimakon kanmu.!"
Yayi maganar yana mata winking,mugun kallo ta aika masa sai dai bata ce da shi komai ba taci gaba da kuka abunta
"Tashi kinji yar albarkata na baki abinci sai kiyi baccin.!"
Bata tanka masa ba har ya janyo tray d'in sai dai ta gyara zamanta tana yi tana matse ido,,shi ya dunga bata a baki har sai data janye masa hannun gefe sannan ya rabu da ita,bayan ya ajiye kayan ya duba mata painkillers ya bata,tana gama sha ko cikakken mintuna goma bata sake yi ba wani baccin ya sake d'aukarta,ajiyar zuciya yayi sannan ya tattara kayan ya fita da su cikin shauk'inta,,sai daya gyara komai da yayi amfani da su a kitchen d'in kamar ba namiji ba komai ya kammale guri guda sannan ya dawo cikin parlor a dai² lokacin da doorbell yayi ring,duk da yasan ko bai duba ba bazai wuce ace su Sultan bane sai ya tafi kai tsaye da niyyar dubawar,ilai kuwa yana bud'e k'ofa sai ya gansu tsaye cikin shirin fita
"Dude.! Kazo muje..!"
Kansa ya d'age da tambayar
"Ina kenan..!?"
Yayi maganar cike da rainin hankali kamar bai san zasu fitan ba,kallonsa duka suka tsaya yi da mamakinsa yadda ya nuna kamar bai san maganar da suka gama yi ba d'azun kafin su bar gidan,sai Sultan ya danne yace
"Malam kafa san ina ne zamu je,kawai ka taho mu fita.."
Juyawa yayi ciki yana fad'in
"Sai kun dawo,,ni kam bana jin fita yanzun.."
Biyo shi Sultan yayi a baya yana magana k'asa²
"Dan Allah dude ka zo mu tafi.. Mene ne hakan wai kake yi ne..!?"
Bai juyo ba yayi hanyar bedroom yana fad'in
"Nace fa baza ni ba.. Kuyi tafiyar ku kawai ina da aikin yi a gabana.."

"Shi kenan tunda baza kaba,turo min ita sai muyi maganar da ita.."

"Ita wa kenan..!?"

"Ur helpmate mana..!"

"Bata nan..!"

"Ina ne taje yanzun..? Kai nema zaka barta zuwa wani gurin.?"
Juyowa yayi yana murmushi
"Ni d'in sai aka ce maka bazan iya barinta fita bane..!?"

"A'a kawai dai na fahimci jarabarka ce ba zata tab'a barinta tayi nisa da kai ba.. Please ina take ne wai..?"

"Tana bacci.!"
Yace masa a tak'aice,kallonsa Sultan yayi cike da tuhuma yana maimaita
"Bacci fa kace..!? Har yaushe ta tashima a baccin da zata koma wani..?"
Murmushin dai still ya sake yi da fad'in
"Laifi ne dan mutum yayi bacci.!?"

"A'aahh! Ni bance ba,,amma dai baccin ai yayi yawa,sai kace wanda take fama da sleeping sickness.."

"Uhumm!" Yace kawai,sai ya nemi guri nan a parlor ya zauna ya fasa wucewa cikin kamar yadda yayi niyya da farko,sake kallonsa Sultan yayi cikin nutsuwa sai yayi murmushi kawai sannan yace
"Dan Allah dude tana ina ne..!?"
D'agowa yayi yana kallonsa da idanunsa a shanye
"Baka yarda bane dana fad'a maka tana baccin..!?"
Girgiza kai yayi sannan yace
"A'a.! Kawai dai nayi tunanin wasa kake yi ne."
Bai jira ya kai aya ba yace
"Sai ka dena to,tunda kaji na maimaita maka.."

"Uhumm.!" Shima yace sannan ya juya ya fice yana dariya k'asa²,dan yadda yaga mutumin cikin wannan farin cikin daya kasa boy'ewa yasan tilas akwai abunda ya faru,yana fitowa ko da su Bassam suke tambayarsa ya suka yi da shi,cewa yayi da su kawai suje su d'in ba sai sun je da shi ba,sai suka wuce suka tafi iya su ukun.

Yana ganin fitar Sultan sai ya shige ciki shima yana sakin murmushin,sai daya d'an zauna ya jiran lokacin sallah ya k'arasa,shi kad'ai yayi sallar sa tunda su d'in da suke jam'i basa nan,yana zaune yana addu'o'i har lokacin isha'a ya shiga yayi,da yake har lokacin bai ji alamun su Sultan sun dawo ba sai kawai ya fita ya rufe musu k'ofa,yana shigowa sai ya kalli inda take,har a lokacin itama tana ta bacci abunta hankali kwance,ji yayi bazai iya tashinta ba,dan haka kawai sai ya rabu da ita bai takurata tashi tayi sallah a time d'in ba,,rab'awa yayi gefenta ya kwanta yana sake matsarta,zuciyarsa cike taf da tsantsar k'aunarta dake sake masa multiplying a ko wane dak'ik'a ya shiga lumshe idanunsa cikin tsantsar farin cikin daya tsinci kansa a ciki while yana caressing wasu sassa a jikinta,idanunsa har time d'in a rufe saboda cike suke da baccin gajiya,a hakan yana shashshafata da shak'ar k'amshinta baccin ya d'auke shi ba tare daya shirya masa ba.

Sai around 10pm suka farka a tare sanadiyyar doorbell da yake ta k'ara,shi ya fara mik'ewa ya fita da nufin ya duba,while itan kuma sai ta lallab'a zuwa bathroom,, still dai su Sultan d'in ya gani,da alamun ma dawowarsu kenan a lokacin,kallonsu yayi da mamaki yana fad'in
"Wai tun fitar da kuka yi ne sai yanzun kuka dawo..!?"

"Uhmmm!" Suka ce masa ba tare da sunyi magana ba,sai ya jinjina kai kawai,kayan da ya gani parke a gefensu kamar wad'anda zasu tashi wani k'aramin shop sai ya sake kallonsu da mamakin,da ido yayi musu tambayar kayan na mene ne.?,babu wanda yayi magana cikinsu suka wuce suna shigar da kayan,bayan sun gama kai iya adadin wanda suka ware sai suka juya suka bar wajen suna fad'in
"Sai da safe..!"
Jinjina musu kai kawai ya sake yi sannan yace
"Allah tashe mu lafiya."

Yana ganin tafiyarsu ya maida k'ofar ya rufe sannan ya koma cikin da nufin dubawa ko ta tashin bayan fitowarsa,a saman pray mat ya isketa tana sallah,sai ya wuce shima ya nufi bathroom,alwala ya d'auro bayan ya fito ya shimfid'a wani pray mat d'in ya kabbara sallah,nawafil yayi bayan ya idar a lokacin itama Sabinar ta idar sai yasa ta suyi nafila,bayan sun idar yayi musu addu'o'i sosai,sannan ya kwashe pray mat d'in ya mayar cikin closet,packages d'in da su Sultan suka shigo musu da su ya koma ya d'auko musu da plate sai glass cup daya had'o da shi guda daya kamar rai,yana shigowa ya iske ta har ta sake komawa saman bed ta sake kwanciya,buh wannan karon a rufe duka jikinta yake except fuskarta data fitar waje,ajiye duka kayan yayi ya nufo inda take,har ya zauna bata san ya iso ba sai k'amshin scents d'insa da suka yi alerting nata,a hankali sai ta bud'e idanunta da har lokacin basu gama komawa dai² ba,hannunsa ya kai jikinta yana tab'awa da son gano ko akwai wani ciwon ne a jikinta da bai fahimta ba,d'an d'umi yaji sai dai ba wai irin wanda za'a ce na wani ciwon ba,idanunta ta sake lumshewa a hankali tana sauke ajiyar zuciya.
"Akwai inda yake miki ciwo ne yanzun.!?"
Ya tambaya da tsammanin zata sanar masa,amma sai yaji tayi masa shiru,idanunsa ya zuba mata yana kallonta,sai yayi d'an murmushi ta gefe,ya yanjota jikinsa a hankali,tsabar iya sharri irin nata duk lallab'awar da yake mata sai data sa kuka tana masa shagwab'ar ya famo ta,rarrashin ta yayi bayan ya samu tayi shiru da kyar sai yace ta tashi ya bata abincin,girgiza masa kai tayi ta sake zamewa zata kwanta yayi saurin rik'o ta
"Mene ne.!? Kina jin ciwo ne har yanzun.!?"
Kai ta d'aga masa
"Okay! Sannu toh,,barin canja miki kaya sai ki kwanta ko.!?"
K'asa² ta ce masa "Toh",sauketa yayi sannan ya tashi da sauri ya fita,bedroom d'in daya fara kaita ya koma ya d'auko mata wani arnen custom silk night wear mai azabar kyau kalar purple mai haske,shi ya taimaka mata wajen sawan,sai dai bai had'o mata ko da pant ba,iya rigan kawai ya barta,yana sa mata ya sake shimfid'e ta sannan ya tattara packages da komai daya shigo da su tunda tace masa bata ci ya fice da su,,ajiyar zuciya ta sauke a hankali lokacin daya fita sannan tayi luf tana tuno abunda ya gabata cikin tarayyar su acikin room d'in,sumbatun da yayi ta zuba mata da rikicewarsa akanta komai bai goge ba,ajiyar zuciya ta sake yi data tuno irin kalaman k'aunar da yayi ta zuba mata har da d'an murmushi tayi,,lokacin guda wani mugun kishinsa ya turnuk'eta tunawa da yana da wata matar bayan ta,kuma itama ta san yadda yayi mata hakan zai mata,,yanzun kenan duk wannan k'aunar daya gwada mata itama waccen d'in haka zai mata.? Take taji wasu irin hawayen kishinsa sun gangaro mata sai tasa bayan hannu ta goge su,shigowarsa dai² lokacin ita tasa tayi saurin shigewa cikin spread har kanta ta rufe tana gyara fuskarta,da sauri shima ya nufo inda take ya bud'e mata fuskar yana tambayar ta ko tana lafiya.? Sai ta gyad'a masa kai,shafa kanta yayi zuwa fuskarta sannan yace mata bari ya canja kaya yazo,yana fad'a sai ya koma ta wajen closet,tana ganin ya d'auko pyjamas d'insa yana niyyar canja su a gurin tayi saurin sake shigewa,girgiza kai kawai yayi yana dariya k'asa² sannan ya canja dress d'insa zuwa na bacci yayi following d'inta zuwa saman bed,tunda ta ji yo shi a kusa da ita yana k'ok'arin maida ita jikinsa ta fara tsorata cos a tunaninta wani abu zai sake mata,kan kace me tuni har hawaye ya wanke mata fuska,sheshshek'ar kukanta da ya jiyo da sauri ya tashi ya zauna yana kunna haske,hawaye ya gani sun mata kaca² cikin rikicewa sai ya kamota ya d'orata a jikinsa fuskarsa na bayyanar da damuwa yace
"Helpmate.! What's going wrong.!?"
Bata iya yi masa magana ba saboda kukan da yaci k'arfinta sai tayi shiru dan da kunya ta iya ce nasa tsoronsa take ji,lallab'a ta ya sake yi sannan suka kwanta,a hankali sai ya kai palms d'insa saman spine d'inta yana caressing,sake firgicewa tayi saboda tuna d'azun ma abunda ya faru kenan har ya janyo mata shan azaba a hannunsa,sai ta sake k'ank'ame jikinta da yake wani irin vibration guri guda,fuskantar damuwar da take tare da shi yasa sai ya daina shafatan,a hankali har baccin tsoro ya kwashe ta tana ta sakin ajiyar zuciya.

Washe gari da safe ko da su Badra suka yi shirin zuwa Pennsylvania Sultan ne yace su bari zuwa wani week d'in,dan haka sai suka hak'ura akan wani week d'in sa koma,,suma kuma ko da suka je office a ranar basu wani jima ba sosai suka dawo dan ma y'an wajen aikin nasu sun tsayar da su suna ta musu sanyawar albarka na auren da Hammad d'in yayi.
Sai da yamma sosai sannan su Badra suka lek'o ta dan Sultan ya shaida musu tun kafin su fita office akan kada su damu da rashin ganinta cos bata jin dad'i,su dai suna jin haka sai suka yi dariya,Zeeharis cikin tsokana tace "Allah sarki princess d'in Yah Hammad Allah bata lafiya",da yamman ma ko da suka shiga apartment d'in nasu,a parlor suka iske ta kwance saman armchair,fuskar nan tayi wani irin fayau kamar ta shekara jinya,bayan sun gaisa da Yah Hammad sai ya fice yana cewa "bari ya lek'a gurin su Bassam" sai ya barsu da ita,yana fita Zeeharis ta dawo kusa da ita ta zauna da fad'in
"Princess sannu.! Ya jikin.!?"
Saurin d'agowa tayi tana kallonta fuska a turnuk'eta kamar koko tace
"Waye yace bani da lafiya.!?"
Dariya suka d'anyi sannan Jannat ta amshe da cewa
"Yah Sultan yace kada mu takura ku,kuma shi yace bakya jin dad'i.!"
Zugum tayi musu tana kallo,cikin zuciyarta da tunanin wato ma zuwa yayi ya fallasata a gurin su Sultan d'in.? Sai kawai tayi y'ar ajiyar zuciya ba ta ce musu komai ba,nan suka zauna mata suna ta hira har kusan isha'a sannan suka mata sallama cike da kewarta suka koma nasu apartment d'in da nufin yin sallah,,cos sun san idan oga yana nan tofa sai dai suyi hak'uri da rashin ganinta,sun san ba ko wane lokaci ne zasu samu damar ganinta ba,,suna fita kuwa babu jimawa shima ya shigo gidan sai ya isketa tana sallah.

Ranar Saturday da safe da yake dukansu suna gida babu mai fita,kuma zuwa lokacin Sabinar ta samu sauk'i sai ya shirya musu fita tare da su Badra gaba d'ayansu cos yasan zata ji dad'i,,lokacin da suka ji batun fitar sosai suka yi murna cos a gurinsu da yake wannan shi ne rana ta farko da za su fara fita tun bayan zuwansu shi yasa suke ta murna zasu ga garin sosai,,around 10am suka fito duka cikin shiri,kada kuso ganin k'auyenci a gurinsu saboda yadda wannan fitowar ya zame musu wani abu na musamman,,nima dai sai lokacin na fahimci ashe wancan zuwan ma dan dai suna gajiye ne shi yasa basu maida hankali kan kalle² ba *TRUMP GRILL* suka fara biyawa suka d'anyi ciye² sannan suka yi guzuri da yake ranar yau duka ya tsara musu yinta ne ba a gida ba,daga nan ko da suka fito sai suka shiga *TRUMP ICE CREAM PARLOR* kowa ya d'auki dangin abunda ransa yake so,gaba d'aya kuma daga nan sai suka bar cikin ginin Tawer d'in suka nufi *CENTRAL PARK ZOO* da yake shima a cikin Fifth avenue d'in yake,,sun yi yawo sosai a cikin zoo d'in sun sha iska,picture's d'in tarihi kuwa duk inda suka je sai sunyi su,,a gefen yallab'ai Hammad shi dai ko ina aka je yana mak'ale da abarsa baya bari tayi masa nisa,wani lokaci ma da yake har tsokanar sa su Sadeeq suke yi akan ya barta ta sha iska,sai dai ya kalle su ko yace "ba ku da hankali ai,da kun san darajar mata da baku shirya yi min maganar na barta ta huta ba,,daga hutu ina sakinta nayi sake wani d'an baturen ya ganemin ita shi kenan sai dai ku mayar ma dasu Daddy corpse d'ina 9ja" suma kansu suna jin ya ce haka sai suyi dariya kawai suna cewa "Allah dai ya kaimu namu lokacin,maji mene ne kake ji",,ranar dukanta a wajen yawace² suka k'arar da ita,tun fitar su sai yamma sosai sannan suka dawo gida,shima d'in kuma ko kafin su wuce sai da suka shiga *GUCCI STORE* da yake shima a nan Trump tawer d'in yake amma yana daga b'angaren northeast ta wajen entrance na ginin,sun yi siyayya sosai kama daga kan jakankuna da takalma masu kyau da tsada,sannan suka shige ciki saboda k'uratowar lokacin sallah,shi yasa ma sai basu samu damar shiga Gallery d'in Robert Miller da suka yi niyyar yi ba,sun barshi kan sai wani ranar idan sun sake yin irin wannan fitowar.
Tunda suka shigo gida da yake apartment d'in su Barda suka baje kowa sai ya hau ihun gajiya duk da sun ji dad'in fitar ba kad'an ba,suna shigowa shi dai Hammad ya wuce yayo alwala a d'aya room d'in da yake duka a room d'aya suke had'uwa su kwana,,itama wucewa tayi da nufin d'auro alwalar,sai duka y'an matan suka biyo ta,cak ta tsaya lokacin data fito daga bathroom ta tarar da Jannat tana bud'e luggage's tana fitar da kaya,sai ta bita da kallo,bayan ta gama k'are mata kallo sannan tace
"Wai ku nan kayanku suke har yanzun.!?"
Da mamaki Jannat ta d'ago ta kalleta sai tace
"Ehh! Mene ne.!?"

"Babu ma'adanin kaya ne a nan d'in.!?"
Ta tambaya tana kallon walls d'in d'akin
"Ina kuwa yake.!? Mu dai tunda muka zo bamu gani ba.!"
Y'ar dariya tayi musu sannan ta nufi wall d'in yamma da d'akin,ba tare da sun san me hakan yake nufi ba suka ga k'ofa tana bud'ewa da kanta,sakato suka mata suna kallo lokacin da had'ad'd'en reach-in closet dake d'akin ya bayyana,sai suka fasa ihu suna fad'in
"Allah bar mana ke princess,, aradu kin k'aro yaji.."
Ihunsu ne yasa Bassam tambayar lafiya.? Sai suka ce babu komai sannan suka nutsu suka ci gaba da hira k'asa²,kafin wani lokaci duka suka shirya kayansu a ciki har luggage's d'in ma suka yi musu guri daga can k'asa,,bayan sun yo alwalar suka fita parlor,jam'i suka yi bayan sun idar sai suka shige kitchen da nufin nema musu d'an abun motsa baki duk da a k'oshe suke,,sun jima sosai a cikin gidan suna ta hira y'an matan da samarin,,around 9pm sai suka yi sallama duka kowa ya kama hanyar tafiya domin ya samu ya kwantar da hak'ark'arinsa.

Cikin wad'annan kwanakin da suka gabata a cikin ko wane wayewar gari,suna yinta ne cikin tsantsar so,yarda da juna gami da shak'uwa mai k'arfi da take sake ninkuwa tsakaninsu,da yake tun daga ranar daya ragargaje sadakinsa wani abu bai sake shiga tsaninsu ba,ita kam hakan sai yayi mata dad'i sosai,dan dama ta k'udurce ita da shi in dai a wannan fannin ne sai ta Allah,shima d'in kuma ko da ya fahimci yadda take baya² da shi tun daga lokacin sai yaja baya da nuna mata kwad'ayinsa a filin,k'ark'arinsa da ita wasanni,idan ba su ba kuma tofa sai dai ya rungume pillow,cos da zaran taga zai zarta ta dira masa rikici kenan,har sai ya rabu da ita sannan zai samu nutsuwa ranar ko jikinsa bata yarda ta kwanta,tun da ya fahimci hakan sai ya rabu da ita,amma deeply abun yana ci masa jiki,tun yana dauriya da hakur'in zuba mata idanu har abu ya fara neman fin k'arfinsa,,,da daren ranar bayan sun dawo suna shigowa gidan a lokacin sun baro apartment d'in su Badra kenan,sai ya wuce bedroom d'insa ya barta nan a parlor da nufin watsawa jikinsa ruwa ko zai samu rangwamen abunda yake ji cos fitarsu a yau d'in da kusancin da suka samu yasa damuwa ta rufe shi,,shi yasa ma ko da ya shigo d'in bayan yayi wanka ya shirya cikin pyjamas,sai ya fito ya nemi lime juice duk dan kada matsalar yayi masa nisa,a parlor ya zauna yana kallon kwallo abunsa,while ita kuma ta shige a lokacin,sai da ya d'auki mintuna ak'alla biyar da zama sannan ta fito daga bedroom d'in itama sanye da wasu irin women's sexy pyjamas,d'ago ido yayi ya bita da kallo lokacin data wuce shi zuwa kitchen tukun ya dawo da hankalinsa kan abunda yake yi,,goran juice d'in daya tsiyaya ta tarar a saman storage closet ya manta bai mayar da shi inda yake ba ya fita,itama ko data gani sai ta manta da abunda ya kawo ta,d'auka tayi tana dubawa zuwa wani lokaci sannan ta bud'e goran had'e da tsiyayawa cikin cup ta dasa shi a bakinta,mugun tsanin da yayi mata a baki shi ne yasa da sauri ta juya gefen basin ta zubar sannan ta wanke bakinta,sai data d'auki lokaci a cikin kitchen d'in tana yamutse fuska saboda tsamin da juice d'in yake da har ya kashe mata baki da saurin sai ta ta fito,cikin parlor'n ta ratso still yana zaunen yana ci gaba da sipping juice d'in yana yi yana matse fuska saboda rashin dad'insa,inda yake ta nufo da zuwa ta amshe cup d'in a hannunsa,saurin d'agowa yayi yana kallonta,a hankali har ta kai cup d'in bakinta ta d'and'ani ruwan da harshenta,yamutse fuska tayi cikin salon rashin jin dad'i ta bar gurin da cup d'in a tunaninta zai yi magana amma sai taga yayi shiru bai ce mata komai ba,har ta kai bakin kitchen sai ta waiwayo tana kallonsa ko da taga hankalinsa duka a kan TV sai ta dawo,a kusa da shi sosai ta zauna jikinsu na gogayya,bayan ta ajiye cup d'in a gefe sai tace
"Me kake yi da shi ne.!?"
Yi yayi kamar bai jita ba,ita kuma hakan da yayi sai yasa ta d'an ji damuwa saboda rashin kulawarsa,sake tambayarsa tayi buh still ko juyowa ya kalleta yak'i yi bare tasa ran zai tanka mata,hannunta ta kai saman beard d'insa tana shafawa sannan ta rik'o chin d'insa tana marairaicewa
"Please.! Kana fa jina amma

Please Login or Register in order to submit comment