Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na yellow colour nd robes bak'i zallah,da yake dama duka suna hannunsu ne mak'ale sai suka yiwa juna murmushi,,kallo d'aya ya wadatar ga mutum yayi saurin gano canjawar da suka yi,duka sunyi fresh da su baya ga y'ar k'ibar da suka k'ara,wacce kallo d'aya zai sa ka tabbatar hutu ne da ya gama zama a jikinsu cikin y'an shekarun yasa su ka samu canjin,,gently suke tafiya suna hira har suka sakko first floor,kai tsaye daga nan ko da suka fito carline suka wuce daga nan suka d'auki hanya,,a yau dukansu jinsu suke daban suna jin duk duniyar babu kamarsu,,fitowa daga school of law tabbas rahama ne kuma sai wanda Allah yayi yana da rabo,tabbas su kam sun san suna cikin wad'annan da Allah yayi masu rabo a gidan duniya,,har suka k'araso cikin school d'in *VILLANOVA SCHOOL OF LAW* dake Pennsylvania fuskokinsu suna bayyanar da tsantsar farin ciki,,bayan an gabatar da bikin yaye sun da basu lambobin girma na zamowarsu lauyoyi aka k'arasa taron da shagali,anyi hotuna na tarihi da k'awaye da y'an uwa,su kam da yake duka daga nan 9ja suka nufo cos suna son yin holidays d'insu a nan shi yasa ya zama daga su sai mazajen su da kuma yaransu,da misalin k'arfe 6pm a agogon New York bayan an tashi a taron yaye sun kai tsaye sai suka nufi airport d'in Philadelphia international airport dake nan Pennsylvania d'in,saboda duka dama ta nan ne suka tsara tashi shi yasa sai suka taho duka buh daga su sai kayan jikinsu ne kasancewar ba sai sun koma New York ba,,around 7pm jirgin sun ya samu damar tasowa daga U.S d'in zuwa 9ja.....





#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••

*56.*
_#Equanimity_

Da misalin k'arfe 2:00pm a agogon Nigeria jirginsu ya samu damar sauka a cikin katafaren filin tashi da saukar jirage na Mal Aminu Kano,lokacin ko da suka iso bayan fitowarsu a nan suka tarar da manyan motocin da Daddy ya tura d'auko su,,duk da a lokacin rana ne a kasar ta Nigeria amma yaran duka gajiya tasa su sunyi bacci,wannan yasa dole sai d'auko su akayi aka fito da su,Sabina dake d'auke da Seeyah a kafad'arta suka jero ita da Hammad da yake shi kuma ya d'auko feeyah ne,suna tafe suna magana k'asa² cike da so da kulawa har suka shiga mota,daga nan aka jera musu convoy security'n Daddy gaba da baya har mayangu road dake cikin Nassarawa G.R.A,,tun kafin isowar su a gida kuwa Mamma tasa sai hidima ake shiryawa duk wani abun ci ko sha da aka san zasu buk'ata an tanadar musu shi,kuma bayan zuwan suma ba'a fasa ba,isowarsu tasa gidan sai ya sake kacamewa,,,sosai suka samu tarba mai kyau daga Mamma,y'an jikokinta duka da yake sun santa sosai fiye da zato ko da yake dai ba a k'asar suke rayuwa ba amma yawan video call da ganinta a pictures yasa ko da suka farka suka ganta duk suka yi gurinta suna murnar ganin Granny,,ranar a nan suka yada zango sai dare bayan sun huta sannan kowa yayi haramar d'aukar iyalansa zuwa gida,a nan kuma ko da Hammad yaso tafiya da iyalinsa fur su Seeyah suka ce baza suje tare da su ba,a gidan Mamma'n za'a barsu gurin kaka,shi kam a gurinsa kusan a iya cewa murna yake dan tamkar idi yaji ranar ta yi masa,sai ya janyeta bayan sunyi sallama suka fashe kowa ya d'auki iyalinsa suka bar gidan,aka bar Mamma da hidimar su Seeyah.
Tun da suka shigo harabar gidan take kallonsa tana murmushi,ganin yadda dai ta sanshi ne a can baya kimanin shekara guda,sai dai da yake yana ganin gyara sosai lokaci² sai ya zama yana nan da kyaunsa kamar babu masu shiga,,kai tsaye bayan shigowarsu kowanne cikinsu bedroom d'insa ya nufa,,a lokacin da Sabina ta shigo nata sashen zuciyarta tana cike fal da farin cikin irin ni'imomin da Allah yayi mata,a gefe guda kuma tsintar kanta da tayi a cikin k'asarta sai tunanin wani sashi na ahalinta ya d'arsu a ziciyarta,baya ga tunanin yadda zata sake inganta rayuwar mahaifanta da take yi a yanzun,,fitowar wasu irin slender tears ne suka asassa sawa tanemi guri ta zauna babu shiri,a cikin tak'aitaccen lokaci damuwa ta kawowa fuskarta ziyara
"Allah sarki k'annena (Samarin baffa) ko kuna cikin wane halin yanzun..!? I knew duk inda kuke yanzun jikina yana bani kuna buk'ata ta a kusa da ku..!"
Tunda tayi furucin sai taji hawayenta sun kasa tsayawa,nan ta sake hawayenta tunawa da Hamudan da Sule,uncontrollable suke sake sauka a saman fuskarta ba tare data hana suba sai da tayi mai isarta a lokacin sannan tayi shiru jin alamun tahowarsa yana shigowa,tun kafin Hammad d'in ya bayyana a bedroom d'in da sauri tayi maza a b'oye tayi whipping tears d'in,dai² yana shigowa ta k'irk'iro murmushi ta kalleshi tana fad'in
"Yallab'ai.! Ai nayi tunanin har kayi wankan.."

"Umm Umm!" Yace mata yana ci gaba da nufar inda take zaune,lokacin daya dangane da ita sai ya d'an tsaya kallonta,daga yanayin reactions d'inta ya fahimci ba k'alau ba,amma sai yayi shiru bai ce mata komai ba,sai daya tabbatar ya zauna jikinsu na gugar juna da yasa ta sako wani wahalallen numfashi kafin ya daga lips d'insa without ya kalleta yace
"Mene ne yake damunki ne.!?"
A yadda yayi mata tambayar sai da taji k'irjinta ya buga,but sai ta d'an d'auke kai while shi kuna ya kasa kunne yana expecting yaji amsar da zai gamsheshi da kallon lips d'inta sai dai yaji ta ce
"Babu komai fa..!"

"Really..!?" Yace yana d'age mata gira d'aya,a hankali cike da rashin kuzari sai ta kad'a masa kai duk da tasan inwardly tana da damuwar but fitowa ta fad'a ya gagareta ne,chin d'inta ya rik'o yana kallon idanunta yace
"Kuka ko.!?"
A dame ta d'ago idanunta tana kallonsa,hakan da tayi sosai sai ya bashi damar fahimtar damuwarta,murmushi ya sakar mata yana matseta a jikinsa
"Na fahimci yarinyar nan kin gama raina ni,shi yasa kike k'ok'arin karya min doka ko..??" Girgiza kai tayi tace "A'aahh! Bafa haka bane." Sai daya d'an had'e rai sannan ya ce
"Sau nawa nake miki warnings bana son ganinki kina yawan koke².."
Mood d'in fuskarta ne ya d'an sauya a hankali zuwa damuwa slowly sai tace masa
"Kad'an fa nayi.." Muryarta yana wani irin shivering saboda tsoron fad'an sa,k'ura mata idanunsa yayi yana kallo da mamakinta sosai a fuskarsa yace
"Kad'an kika yi kika ce min.!?"
Sai ta gyad'a masa kai,shima d'in gyad'a mata kan yayi yana cewa
"Good." Sai kuma yayi shiru yana kallonta,kusan mintuna ak'alla uku ya d'auka yana ta kallonta kafin ya sauke ajiyar zuciya yana fad'in
"Amma sau nawane na hana kukan..!?"
Marairaice masa ta kuma yi kamar zata saki sabon kuka tace
"Babu adadi.!"

Yace "Amma shi ne dole dai baza'a jini ba sai anyin ko..!?"

"A'aahh! Nima fa ban san lokacin da nayi ba,,kuma..!" Sai tayi shiru ta kasa k'arasawa,da wasu irin yanayi a idanunsa yake sake kallonta jin tayi shiru yace
"Nd what.!?"
Shirun ta sake yi ta kasa magana,sai daya riko fuskarta yace
"Kalle ni nan..!"
A hankali ta d'aga kyawawan idanunta tana bin fuskarsa daya d'aure alamun babu wasa da kallo
"Fad'a min mene ne matsalar."
Yadda yayi maganar ta san serious yake buk'atar jin,nd a yadda yake d'in nan komai zai iya yi idan taci gaba da hidden masa abubuwa shi yasa sai ta nemo confidence ta lik'awa kanta,a dake tace
"Kawai fa na tuna da su Hameed ne,shi ne sai naji na kasa daurewa.."
Sai tayi shiru tana kallonsa da sauraren taji me zaice,zunzurutun gaskiyar daya hango a idanunta shi ne yasa bai k'asa a guiwa ba yace
"Da d'in tunda kuka rabu kin tab'a tunanin suna ina.!? I mean yaya suke gudanar da rayuwarsu..!?"
Slowly cikin rashin wadataccen kuzari ta girgiza masa kai,yana sake kallonta ya watso mata wata tambayar
"Umm! Duk bama wannan ba,tambayar a nan shi ne,ina tunanin abunda ban tab'a sani bama kenan tun bayan da kika dawo rayuwata,kuma nima ban bibiya ba,shin suna nan amma bana ganinsu..!? A ina suke ko nace a hannun waye aka barsu..!?"

Ajiyar zuciya tayi sannan tace "Dama shi ai Sulaiman ba yaron wajen baffa bane,k'ani ne a gurin LADO,,Hameed ne d'an gurin baffa sai yayyensa mata guda biyu da suke gidanjensu suna auren yayyen LADO d'in.."
Wani kasak'e yayi yana kallonta da son tuno wane nema LADO d'in da take nufi.!? Ko da ganin zai takura kansa akan nemo sanin abunda ba lallai ya amfane shi ba sai yasa a hankali yana murza hannunta dake cikin nasa yace
"Mene ne yasa amma Baba bai d'auki alhakin kulawa da Hameed ba sai ya barshi wani gurin daban..!?"
Ajiyar zuciya ta sake yi tana kallonsa tace
"Ai shima Baban da farko yaso d'auko su duka har Sulaiman d'in saboda ya san idan ya barsu hannun Innar LADO d'in za'a iya samun matsala,to kuma sai ta hana tace ita a bar mata yaronta.."

"Shi kuma Hameed fa me yasa aka bar mata shi..? Tunda ta hana Sulaiman d'in ai tunani na sai a karb'i shi Hameed cos bata da iko da shi ko..!?"
Idonta ta kyafta tace "Kamar yaya.!?"

Yace "Ehh! I thought tana son gwada ikonta ne akan nata d'an data haifa,,Me zai sa Baba ya bar mata Hameed kuma tunda shi yake da iko da shi ba itaba.!?"

"Ohh!" Tace kafin taci gaba da fad'in "To ai su Hameed d'in ne suka nunawa Baba suna so ya barsu tare,babu yadda Baban bai yi ba akan ya dawo gidanmu da zama amma sai ya nace yace dan Allah baba ya barshi tare da Sulaiman,shi yasa to sai yayi hak'uri kawai ya barshi a can d'in,,amma da farima har ya d'auko shi to damuwar da yayi ta nunawa tasa Baban ya hak'ura ya mayar da shi can.."
Ajiyar zuciya yayi yana jinjina kai yace "Ok na fahimta.. To amma.!" Sai shima yayi shiru yana wani nazarin,kallonsa taci gaba da yi jin zaiyi magana ya fasa tace
"Me fa..!?"

"Nothing..!" Yace yana mik'ewa tsaye,har ya kusa da entrance sai ya waiwayo yace
"Taso muje ki taimaka min..!"
Kallon da me ta bishi,thru his eyes sai ya mata sending amsan,nok'ewa tayi tak'i tasowa a gurin har sai daya dawo ya d'agata,a hakan kuma dan gulma tana nok'ewa suna tafiya ta samu damar rik'e shi gam,kallonta yayi yace
"Madam ya dai..??"

"Me nayi ne..!?" Ta tambaye shi tana tsare shi da idanunta,yace "Babu komai.." Sai ya fuske yana murmushi k'asa² ya nufi side d'insa da ita.

Washe gari sunje *KAWO* gidansu a nan Sabina taga uban gyaran da aka yiwa gidan,shekara d'aya kawai da bata zo k'asar ba amma gidansu yanzun an gyare shi har da su get,abun dai sai wanda ya gani,da suka samu keb'ewa da Inna ma tayi ta fad'a mata irin hidimomin da Hammad da iyayensa suke musu yanzun,tayi matuk'ar mamaki dan ita ko da wasa babu wanda yace mata ga wani abu da yake faruwa a gidan sun,yinin rana duka a nan gidansu suka yi shi suna ta hira da Innarta data rikid'e ta koma Hajiya Inna,hira ce irin ta yaushe gamo suke yi a hakan har Baba ya dawo shima ya tarar da su aka ci gaba da hira da shi,,d'an hutun da suka zo yi Nigeria sosai ya sake kusanta su da wasu dangin da suka jima basu sadu ba,sunyi zumunci sosai kafin suka koma bakin aikinsu,yara kuma suka koma skul,dama su ne musabbabin zuwan,da kwanakin hutu suka tasamma k'arewa kuma suka tattara suka koma.

Barinsu 9ja duka bai wuce da y'an kwanaki ba gagarumin tashin hankali ya danno cikin family'n su,lamarin daya tadawa duk wanda yake da alak'a da family'n Babanta hankali,,a iya rayuwarsu tun kafin su dawo cikin gari su d'in ba mutane ne da ake jin kansu da al'ummah ba,haka bayan sun dawo nan d'in da zama ma basu da abokin fad'a,amma sai ga labarin kama LADO a cikin manyan terrorists ya baza gari,,a hakan kuma duk gidansu Sabina babu wanda yasan wainar da ake toyawa a gidan su LADO d'in adalilin *TANI* data hana Babansu sanarwa Baba,a ganinta abun Allah wadai ne ace d'an data gorantawa su Baban akansa aji wannan al'amarin ya faru da shi,kuma dai abun kunya zai zame mata saboda akansa tayi rashin kunya har Baffa bata kyale ba.
Tunda labarin ya fara walagigi a gari babu wanda ya jiyo sai yau da ana hiran a company'n da Baba yake aiki shima kuma bai fahimci ko su waye al'amarin ya faru da suba,,aiki yake ya duk'ufa labari ya biyo ta kan kama gaggan y'an ta'addan,tunda aka sako hirar bai ce komai ba amma haka nan yake jin wani iri a jikinsa,,a babu² sai da aka kwashe kusan sati guda da batun kamasun amma su Baba basu sani ba,kuma still labarin yana ci gaba da watsuwa a kafafen yad'a labarai,magazine's,zuwa newspaper babu dai inda bai je ba cikin d'an tak'in,kafin kwana goma ya rufa da maganar da ake har gari duka ya d'auka an kama dabar y'an ta'addan da suka damu gari.
Ranar laraba da dare ana kan sake replaying labarin a gidajen TV,Inna da Baba zaune cikin kayataccen parlor'nsu da dare bayan Baban ya dawo daga sallar isha'a suna kallon labarai a NTA sai ga hotunansu an watso,ana ta magana kan irin laifukan da suke aikatawa,nd still kuma a lokacin da aka kamo sun ma an kamasu da miyagun makamai had'e da kwayoyi,zuwa lokacin kam tuni sun daku har kamanninsu ya fara sauyawa,amma ko da manema labarai ke tambayarsu sunayensu da laifin da suka yi aka kamosu,sai Baba ya sake nutsuwa lokacin da aka zo kan LADO sosai hankalin Baba yayi mugun tashi jin muryar LADO da sunansa da inda yake da yayi bayani,sai dai abun d'aure kai a tare da shi,bai wuce yadda yake musanta sa hannunsa a ciki ba,ko gama jin k'arshen labaran basu kai ba saboda tsananin famuwa Baba ya kira line k'anin nasa,bayan ya d'aga sai ya danne damuwa har suka gaisa kafin yace
"Yawwa ni kuwa ina son ka turomin LADO ne dama akwai sak'on da nake son aiko maka da shi.."
Baban LADO cikin damuwa da gudun sanarwa d'an uwan nasa haka ya danne yace da Baba
"Yaya wane irin sak'o ne da bazan zo na karb'a ba ni da kaina..?"

"A'a.! Shi d'in dai nake so ka turo min idan da hali,idan har nasan zance kazo da kanka me zai hana bazan ce zanzo na kawo maka da kaina ba..?? Ka aikomin shi kawai nace,akwai maganar da nake sonyi da shi ne.."
Babu yadda Baban LADO bai yi da Baba akan yayi hak'uri shi zaizo ya karb'i sak'on amma sai Baba shima ya kafe kan lallai shi LADO yake son ya zo ya karb'a,, k'arshe dai da yaga noway out ne kan batun dole tasa ya sanar da Baba halin da ake ciki,,Baba yana gama saurarensa ya rufe shi da fad'an dalilin da yasa zai b'oye masa,ta inda Baban LADO bai yi tunani ba sai da Baba yayi masa fad'an rashin sanar da shi da baiyi ba,haka yayi ta bashi hak'uri har ya samu da kyar ya katse kiran,,a washe gari kuwa ko gurin aiki bai iya zuwa ba suka tafi Central prison dan su gano halin da LADON yake ciki,sanoda lokacin ajiya ne kawai aka kaisu kafin shari'a ta waiwayensu,, LADO jiki ya lausasa hawaye yayi shi har sun fara neman k'are masa,lokacin da su Baba suka je suka dawo hankalinsu duka a tashe yake dan har irin mutanen da aka ce suna aiki tare sai da suka gani.
Sanda Baba ya dawo ya labartawa Inna ita kanta duk da bata ganshi ba amma hankalinta yayi mugun tashi,a nan d'in nema da suka zauna shawaran yadda za'ayi su nemi lawyer da zai tsaya masa saboda anbasu dama daga lokacin zuwa ranar da za'a fara shari'ar su nemo lawyers,, kai tsaye Baba yana kawo batun Inna tace ai ga y'ar uwarsa nan tunda Allah yasa tana da ikon taimakon a hannunta sai ta tsaya masa,Baba dai jikinsa a sanyaye tunawa da abunda LADON yayiwa Sabinar shekarun da suka gabata kai tsaye yace
"Bana tsammanin uwata zata zo,,kuma duka ma yaushe ne suka koma da za'a ce ta zo batun wani case,,kuma dai kinsan aure take ba zaman kanta ba,saboda haka a bar ma batunta kawai mu nemi lawyer da zai tsaya kan lamarinsa..!"
Inna da take kallon Baba tace "Ai kuwa babu wanda zaiyi wannan sai ita,,idan har ita da take ta gida ba zata tallafaba ina amfanin yin ilimin nata..!?"
Baba yace "Babu,,amma kin san sha'anin yara dole dai mu lallab'a ko da ace mun sanar da ita d'in gudun samun matsala." Inna da ranta ya fara b'aci da batun a lallab'ata² nan ta bud'e wuta tana fad'in
"To ni dai ban san mene ne kake k'ok'arin yi ba,ana batun ayi abu kana a lallab'a ta,,lallab'awar na maganin mene ne..?? D'aure mata ma za kayi kenan kada ta shiga lamarin..!?"
Baba dai ganin irin fad'an da Inna ta fututtuke tana yi sai yace
"Allah ya baki hak'uri,, ni dai na farko ban ce kada uwata tayi ba,amma..!"

"Babu wani amma,kawai kayi shiru kasa ido,in sha Allah komai zai wuce.."
Baba bai sake cewa komai ba sai yayi tsam ya mik'e da fad'in "Allah yasa" daga haka sai ya fice a gidan gudun kada su sake haurawa da ita akan maganar,,,bayan fitar Babah haka Inna tayi ta tunanin mafita daga k'arshe kuma ko data duba lokaci saboda tunanin son tayi magana da Sabina a kan lokaci,taga k'arfe 8pm ne lokacin,sai tayi shiru tana tunanin ko k'arfe nawa ne su a can..?? Duk da ta san akwai tazarar lokaci tsakanin 9ja da can U.S sai tayi shiru tana fad'in
"Na san dai yanzun dare yayi musu nisa,amma ba don haka ba ai da a yanzun zan sanar mata,ayi duk wacce ma za'ayi.."
Haka ta zauna shiru ita d'aya,daren ranar bata iya runtsawar kirki ba lamarin duk ya tsaya mata arai,a hakan a daddafe ta kai wayewar gari,tun da misalin k'arfe 7am ta fara kiran line Sabina na can,sai dai bata d'auka ba har kiran ya katse,tana k'ok'arin sake kiranta kuma sai ga kiranta ya shigo,da sallama ta d'auka bayan sun gaisa ta tambayi jikokinta,shiru ya biyo baya na wani lokaci kafin Inna tace
*"HAFSATU.!"*
Tunda taji Inna ta kira sunanta kai tsayen taji zuciyarta ta tsinke gabanta yana tsananta fad'uwa,but a hakan ta daure ta ce
"Na'am Inna..!"
Ajiyar zuciya Inna tayi seriously tace
"Wace ce ni a gurinki..!?"
Jiki a matuk'ar sanyaye tace "Kece mahaifiyata.."

"Da kyau to da kika san haka..! Shin idan nace kiyi abu za kiyi ko kuwa..?"

Tace "Sure Mah..! Cikin gaggawa ma zanyi gudun kada ranki ya b'aci.."

"Kina tsoron ganin b'acin raina ne..?"
Sabina ta sake cewa "Sosai Inna.."
Ajiyar zuciya Inna tayi sannan tace "Ina son yanzun kisa kunne kiji abunda zan fad'a miki."
Tiryan² Inna ta zayyano mata matsalar da aka samu,wani irin gumi da zafi ne ya fara keto mata duk da weather NEW YORK a lokacin k'ank'ara ke sauka,zuciyarta tana wani bugawa tace
"Inna yanzun mene ne kike so ayi akai..!?"
Kai tsaye Inna tace "Ina so ne kiyi wani abu akan matsalarsa."

"An gama Inna,, in dai hakan zai faranta miki,in sha Allah zanyi.."
Har suka gama waya da Inna gumi ke tsatstsafowa a jikinta,damuwa duk ta rufeta cos ita kam har yanzun tana hango abunda ya kusa faruwa da rayuwarta,sai tayi kwance a parlor zuciya babu dad'i,a hakan har su Seeyah suka dawo daga skul suka isketa kwance,suka mata sannu da hutawa,but suma kansu tun shigowarsu sai suka ga canji cos sun saba idan sun dawo zata rungume su suna murna itana tana yi,amma ranar bata iya ko tsayawa da su ba tace suje gurin Nannay ta shirya su suje apartment d'in su Meenal suce tana gaida Aunty,,yaranta y'an shekara hud'u da watanni tunda tayi maganar ba tare da tayi ko da murmushi ba,yasa duk jikinsu yayi sanyi,but da yake wayon su da kaifin basirarsu har ya zarta shekarunsu,suna wucewa bedroom d'insu Feeyah ta kalli y'ar uwarta tace
"Habibtiiy.! Mu kira Appa ko..?"
Seeyah data nemi guri ta zauna saman bed ta buga tagumi ta kad'a mata kai
"Ummhh.! Mu kirasa mu fad'a masa Mamma bata lafiya.."
Ita kanta Feeyah d'in kad'awa y'ar uwar kai tayi sai kuma tayi saurin fita da yake tafi Seeyah d'in wayo tana cewa
"Lemme snatch Mamma's phone.."

Seeyah tace "Okay.!"
Sai ta biyo Feeyah a baya,parlor'n sula

Please Login or Register in order to submit comment