Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tare da ita,while su duka ukun kuma suna cikin wani aspen black gown mai off shoulder da turban duka a kawunansu mai kalar gold,,lokacin da suka shiga da ita d'akin Baba suka nufa,bayan sun shiga da ita sannan suka basu guri,Baffan Inna,Baban LADO da duk wani makusanci babba a zuri'arta b'angaren Babanta da Inna suna cikin d'akin,tunda ta shiga tana ganin yadda suka had'u kowa yana binta da kallo ta sauke kai k'asa,a hankali hawaye suka fara taho mata,guri ta samu ta rab'a wani irin nutsuwa ya sake shigarta hankalinta a tashe,,baffa ne ya fara yin magana a kaf cikin mutanen gurin saboda ya fi kowa yawan shekaru,bayan yayi mata nasiha sosai mai tsumama zuciya sannan d'aya bayan d'aya kowa dake gurin ya tofa albarkacin bakinsa kafin azo kan Inna da jikinta yayi wani mugun sanyi,d'agowar da Inna tayi ta kalleta bayan tayi murmushi sannan a hankali tace
"Ni kam ba sai nace komai ba,saboda duk abunda ya dace na fad'a mata y'an uwa sun gama fad'ar sa,,abunda kawai zan iya cewa shi ne kiyi hak'uri da duk halin da zaki shiga,rayuwar aure ba kamar irin rayuwar da kika saba yi da mu bane,Allah ya baku zaman lafiya.. Ubangiji ya kad'e fitina,ya tsare hanya..!"
Slowly sautin kukanta ya fara fita yayin da jama'ar gaba d'aya wajen suke bata baki wasu kuma suna fad'in
"Zaki daina ne yarinya,,kowa da haka ya saba.."
Ita dai bata saurari kowa ba taci gaba da hawaye,fita duka sauran mutanen suka yi bayan sun gama mata tsiyar kukan da take aka barsu daga ita sai iyayenta,duk da a lokacin motocin d'aukan amarya sun k'araso amma sai da Babanta ya sake mata nasiha sosai sannan ya kawo sadakinta ya dank'a mata su a hannunta,a nan kukanta ya sake tsananta,sai dai bata karb'a sadakin ba tace ya ajiye a gurinsa,,sannan Inna tayi mata batun tayi hak'uri kada taga basu kaita da komai ba yanzun,sun samu labari ne daga Mamma tace sai an kammala ginin gidansu na nan k'asar da zasu na zama idan sunzo hutu,in sha Allah da zaran an gama d'in za su kai mata kayanta,amma lefenta da komai ankawo d'azun bayan gama d'aurin aure,kuma har anfita dasu,ita dai bata iya cewa komai sai kuka da take,a haka har aka fito da ita da kyar a cikin gidan bata daina kuka ba suka d'auki hanyar state road (gidan surukanta).
Lokacin da suka iso gidan su Hammad sosai aka yi welcoming nasu cikin mutunci da girmamawa,lamarin daya bawa ahalinta matuk'ar mamaki,sai da suka tabbatar sun dank'a amanarta a hannun surukan nata kafin suka yi sallama da su,da kuma itan suka tafi d'auke da sha tara ta arzik'i,ita dai har suka tafi suka barta bata san abunda yake faruwa ba dan har lokacin bata daina kuka ba.

Cikin yinin ranar gaba d'aya duk iya son Hammad da yaga Sahibar sa abu gaba d'aya yak'i yiwuwa,saboda tayi masa b'atan daya gagara gano inda ta shige har dare kuma bai samu yaji koda muryarta bama,,ita kuwa a nata gefen suna tare da su Badra yauma kuma tare suka kwana sai dai yau a d'akin Mamma suka zauna saboda na Badra akwai mutane cikinsa.
Hankalin Hammad fa tun safiya har dare gaba d'aya ya kasa kwanciya saboda rashin samun ganinta da bai yi ba yasa hankalinsa ya fara neman tashi,ko a wayar ma daya kira saboda takaici sai company suka masa bak'in cikin jin muryarta ta hanyar sanar masa wai not reachable,tsabar haushin daya ji shima d'in a ranar sai tunaninsa gaba d'aya ya gaza kawo masa kiran Badra ko Jannat yace su had'a shi da ita,,a wannan daren duk da yana cikin damuwar rashin ganinta da bai samu yayi ba daya sashi yayi wani irin lak'was ya koma wani quieten,magana da duk tsokanar su Sultan duk yak'i kulawa,yana jin farin cikinsa over his worried,,yayin da aka ce dare ya fara nisa kuma sai ya zama yayi isolating kansa in front of rabba,strengthening himself wajen nuna tsantsar godiyarsa ga Ubangiji (S.W.T) bisa ni'imar da yayi masa.

*In the morning...*
Tun asubah kafin ma ace gari ya gama yin haske duk wasu kayansu da komai da aka san zasu tafi da shi tuni aka gama settled nasu a motoci,lefenta ne dai da suka zo dasu daga gidan su Mamma tasa a barsu nan idan an d'inka sai a kai mata tunda dai zamansu a can d'in zaifi yawa akan nan,,bayan duk an kammala yi musu shirye² around 6:30am na wayewar litinin d'in suka fito kowa cikin shirin tafiya,(Hammad,Sultan,Sadeeq,Bassam,Jannat,Zeeharis da Badra) duka sun hallara a parlor sai itan kad'ai da ake jiran fitowarta,,sai da suka d'auki ak'alla mintuna kusan ashirin zaune a parlor suna ta hira kafin Mamma ta fito rik'e da hannunta,fuskarta nan tata d'auke da simple make-up da aka mata applying,,yauma dai kamar kwanakin da suka gabata,tana sanye da wani irin long sleeve na arabian gown bak'i sai vail d'in rigar da aka mata rolling d'insa over her head aka mak'ale da pin mai matuk'ar kyau,,tunda suka fito idanunsa ya sauka kanta,kallo d'aya yayi mata amma sai yasa shi yin ajiyar zuciya had'e da lumshe idanunsa,a hankali sanyayyar iskar ni'ima mai tattare da nutsuwa ya fara sauka masa cikin jikinsa,har suka k'araso bai bud'e idanunsa ba,amma yana jin sanyayyen k'amshin turarukanta masu k'arawa zuciya shauk'i a kusa da shi,a hankali yayi k'ok'arin bud'e idanunsa ya sake sauke su akanta,a kusa da shi Mamma ta zaunar da ita sannan ta kamo hannunsa ta had'a da nata tana masa murmushi lokacin daya d'ago ya kalli Mamma da hannunsa wanda take rik'e da shi cikin nata sai yayi murmushin shima amma bai yi magana ba
"Ga amanata nan,na dank'ata a hannunka,,buh ina so ka rik'e a zuciyarka dai² da yini d'aya idan ka bari yarinyata ta zubar da hawaye saboda kai,ka shirya karb'ar hukunci daga gare ni,,zan iya d'aukan komai amma banda ganin b'acin ranta.. Ina fatan ka fahimci kalamai na,kuma zaka na tinawa da su a ko da yaushe..??"
Kai yayi saurin gyad'a mata yana lumshe idanuna
"Shi kenan zaku iya tafiya,,ina yi muku fatan alkhairi,ubangiji yasa albarka a zaman ku,Allah kuma ya sauke ku lafiya."
Mik'ewa yayi cikin hanzari ya rungume Mamma idanunsa suna kawo ruwan hawaye still hannunsa da nata yana a had'e kamar yadda Mamma'n ta had'a su bayan ta zare nata tabarsu rik'e da juna,k'asa² yadda ba kowa zai ji ba sai Mamma'n kawai yace
"Thank u Mah.. Ana ahabbuk-thtiir.."

"Wa'ana kamaan habibiiy.."
Murmushi yayi mai sanyi sannan ya zaro handkey daga aljihunsa ya goge hawayensa ba tare da kowa ya fahimci abunda ya faru da shi ba sannan ya saki Mamma ya d'an ja baya kad'an,,sai da Mamma tayi musu nasiha sosai dukansu har su Sultan,sannan suka sake yin sallama,suna cikin sake yin sallamar da ita ne,sai Badra ta waiga ta kuma waigawa kamar dai tana neman wani abu,Mamma data kula da ita ta kalle ta tana tambaya
"Kiddo.! Mene ne kike nema ne.!?"
D'an murmushin yak'e tayi sannan tace
"Mah.! Ina d'ayar ne wai,naga kowa amma ita ban ganta ba.!"
Gaba d'aya idanunsu komawa kanta suka yi kowa yana son jin wa take neman,Mamma dai da bata fahimci abunda take fad'a ba tace
"Wace ce d'ayar kuma baby.!?"
Satar kallon inda Hammad yake tayi cikin rad'a tace da Mamma
"Mah.! kiyi a hankali kada Yah Hammad yaji."
Murmushi Mamma'n tayi sannan tace
"To uwata.!"
Duka parlor'n sai suka yi dariya amma banda Hammad da ya tafi wata duniyar
"Mah.! Idan ba gulma ba dama waye zaice baya so aji me yake fad'a ne.!?"
Bassam yayi maganar yana mik'ewa tsaye da hararar inda Badra take,Sultan ne yayi caraf ya amshe zancen da fad'in
"Ni kam dai Bassam bansan mene ne Daddy's kiddo tayi maka ba,duk ka takura ta a gidan nan,ko dai².?"

"A'aahh! Ni me zai had'o ni da ita kuwa.!?"

"Fad'i gaskiya dai,ko kana tsoron za mu kwance ma zani ne.!?"

"Idan kun kwance ma baza'a rasa mai d'aure min ba..!"
Dariya suka sa masa,Badra dake kusa da Mamma ta kalleshi tana juya idanu
"Toh dai yanzun so kake kace min munafuka ko me.!?"

"Ohoo! Miki dama idan ba munafircin ba mene ne kike shirin yi.? Kince kada kowa ya ji,ai idan aikin gaskiya ne babu wanda zai k'i aji shi yana aikatawa,,ko ba haka ba..?"
Had'e rai Sultan yayi yana kallon Bassam da wani irin kallo mai kama da harara
"Malam ya isheka haka nan.!"
Dariya Bassam yasa da fad'in
"Haba.! Yah Sultan mene ne to dan na fad'i halinta.!? Ko dai kana goya mata baya ne.!?"

"Amsa kake so na baka.!?"
Gira Bassam ya d'aga masa alamun ehhh,yafito shi Sultan yayi da hannu yana fad'in
"Zo to na fad'a maka ko mene ne kake son sani.!"
Ya k'arashe maganar yana janye hannun long sleeve d'in dake jikinsa
"A'a ni ba sai na zo ba,ka fad'a a haka ma ya wadatar.."

"Tsoro kake ji wai..??"
Kai ya girgiza alamun A'a
"To zo mana,ai nima amsa ne kawai zan baka.."

"A'a ni bazan zo ba fa.."

"Tsoro ko.!?"

"A'aahh.! Tsaro dai.!"

"To kawai kaje mana,ai amsa kake son samu,ko ba haka ba.!?"
Sadeeq da yayi maganar yana kamo kafad'arsa ya tura shi gaban Sultan,saurin gocewa yayi daga inda Sultan yake yana kiran Mamma ta taimake shi,nan ma gaba d'aya suka sake sa dariya,Jannat data k'unshe baki tana dariya bata yi aune ba ta jiyo Bassam yana fad'in
"Ya dai.!? Ke masoyiya kina kallo suke yiwa abun k'aunar ki haka..!?"
A daburce ta saki baki tana kallonsa dan ko kad'an bata tab'a zaton zai fallasa ta a cikin mutane ba har haka
"Aahh.!" Sai kuma tayi shiru tana ci gaba da raba idanu,kamo shi Sultan yayi yana dariya
"Kaji yaro da rinto,wato ma soyayya kake.!? Ai kuwa sai ka jira layi ya zo kanka,,ko mu d'in an fad'a maka ba jiran muka yi ba ne.!?"

"Allah sawak'e,wane jiran zan yi..? Ku dai da kuka ga zaku iya bawa rayuwar tuzanci gudummuwa ai kunga kuna ta fama,,amma mu babu wani jiran da zamu yi.. Ko ba haka bane masoyiya..!?"
Sunkuyar da kai tayi k'asa ta kasa amsawa,a hankali shima Hammad ya matso inda suke yana fad'in
"To wai ku duk mene ne ya janyo wannan batun..!? Mu da muke da tafiya a gabanmu.!?"

"Wollahi Yaya Jerry'n Mamma ce ta taso da shi,wai sai an fad'a mata inda d'ayar take."
Yamutse fuska yayi yana tab'e baki
"Mene ne kuma d'ayar.!?"

"Ohoo! Mata ga dai ta nan tak'i fad'a,shi kuma Yah Sultan yana wani neman bata kariya.."
Murmushi Hammad yayi yana kallon Sultan
"Yane Malam.? Wai son k'anwar nan tawa kake yi ne.!?"
Harararsa Sultan yayi cikin sigar wasa yace
"Meye ruwanka ne a nan kuma..?"

"Ruwa na kake tambaya.!? Saboda ni zan bada ita,shi yasa nake maka magana kana bani amsa a tsaitsaye.! Idan ba zaka fara girmama niba fa sai a fasaah.!"
Ya k'arashe maganar cikin salon jan harufa
"Haba babban Yaya waye ma ya isa yace ba zai girmamaka ba.!? Ai yana fad'ar haka an soke kwangilar kenan..!"
Bassam yayi magana yana wani jinjina kai da yiwa Sultan dariyar mugunta
"Yo ku soke mana,,sauk'in dai nima akwai takardun kwangilar ku da zasu biyo ta ofishina..!"

"Kaii! Dakata mana.! Kana son yi mana alfahari ne!? To idan baka sani ba,wannan kwangilar tuni ta bar k'ark'ashin ikonka,, itanma iko na ce.. Ko kana so na gwada maka ka ganu..!?"

"Ehh! Gwada d'in mu gani idan zai yiwu..!"
Murmushin gefen baki Hammad yayi kafin ya yafito Jannat yana fad'in
"Zo nan k'anwa..!"
Matsowa tayi gabansa tana sunkuyar da kai,shi kuma gogan cikin izza ya kalleta yana fad'in
"Ina so ki bani amsa kowa yaji a nan..!"

Tana girgiza masa kai tace "Toh"

"Kina son Bassam da gaske..!?"
Sai data d'ago ta kalli inda Mamma take sai kuma ta sunkuyar da kai,juyawa yayi inda Mamma take yayi murmushi sannan yace
"Mah.! Ki d'an rufe idanunki ko ki juya baya,,muna wata y'ar magana ce,to kuma ganinki a nan zaisa na rasa amsar da nake son samu.."
Saurin juya baya Mamma tayi tana fad'in
"Idan kuka ce na bar muku wajenma duk zan iya ai.."
Murmushi kawai Hammad yayi yana kallon Jannat
"D'ago ki fad'a min,da gaske kina sonsa.!?"
Kai ta kad'a masa followed by
"Ehhh!"

"Shi kenan an gama magana kuje abunku,ni da kaina zan fad'awa Daddy.!"
Ya fad'a cike da isa,kallonsa Sultan yayi yana tafi
"Da kyau jarumi..!"
D'age shoulders Hammad yayi yana kallonsa
"To ya kaji tsarin..!?"

"Sosai ka burge kam,,amma dai wannan salon kwafarsa kayi ba.!?"
Dariya Hammad yayi data bayyana jerarrun hak'oransa
"Baka yarda zan iya yin hakan bane.!?"

"A'a'a! Ko kad'an zaka iya kam,,amma dai ban yarda zaka kai maganar gabansu Daddy ba.."
Gyad'a kai Hammad yayi da fad'in
"Shi kenan kasa ido,,za kayi kallo."
A hankali Mamma data basu baya tana dariya ta juyo da fadin
"Kaii! Ni kam kuzo ku wuce,wannan hiran naku naga alama bazai k'are ba,idan kun shiga jirgi ko kun isa can kwayi shi a can.."

"Laa! Mamma korarmu kike yi.!?"

"A'a na daifi so ku tafi ne,kada ku b'ata lokaci,idan kuka ci gaba da zama har jirgi ya tashi sai kun biya su bata lokacin da kuka sasu yi.."
Ba dan sun so ba haka Mamma ta sako su gaba har bakin mota,y'an uwa da suka zo biki suma wasu ciki suka yo musu rakiya suna masu binsu da addu'o'in fatan sauka lafiya,,sai da taga tafiyarsu sannan ta koma cikin gida tana murmushi had'e da jin kewarsu.

Motoci ak'alla uku ne suka tafi yi musu rakiya bayan nasu guda uku,Hammad da Sabina suna cikin mota d'aya,yayin da Badra,Jannat da Zeeharis suma suke cikin d'aya,sai d'ayar da su Sultan suke ciki shi da Bassam da Sadeeq,duk da Sabina ta so ace tana tare da su Badra amma ina oga ya juye yace bai san wannan batun ba,dole tasa ta hak'ura ta tafi tare da shi d'in,sai dai tun da suka shiga motar tak'i kallonsa bare tayi masa magana har suka k'araso filin jirgi bata yi ko kwakwkwaran motsi ba,,duka da isowarsu da kammala musu komai har shigarsu cikin jirgi ba'a d'auki ko rabin awa ba,,ko a cikin jirgin kansa sai suka kasance suna zaune a b'angarori daban²,sab'anin Hammad da Sabina da suke bigire guda a mafi kusancin gurin zama,kuma har lokacin da jirgi keta k'ok'arin tashi bata yarda magana ta had'a su ba,saboda ita burinta kawai ta zauna tare da k'awayenta,shi kuma fuskantar hakan da take so sai yasa shima ya gimtse yak'i bata fuska bare tace zata kawo masa wasa,a haka har jirginsu ya samu damar tashi babu wanda yayi magana da kowa.
Tafiya tayi tafiya,yayin da suka d'auki tsayin awanni masu yawa a sararin samaniya suna shek'a tafiya cikin giragizai,nan fa jikkunan mazauna cikin jirgin suka fara yin laushi,a lokacin bacci ya fara kawo sumame,,ko ita kanta sarauniyar kuramen dake gefen window bata san lokacin da bacci ya sace taba,,shi kuwa Yallab'ai mai tsuntsuwa da yake idan da sabo hakan ya zama jinin jikinsa ko gyangyad'i ya kasa d'aukar sa bare bacci. Yanayin yadda cikin jirgin ya d'auki shiru shi ne yasa shi waigawa yana d'an kallon yadda mutane suke ta faman bacci kamar a gidajensu,ai kuwa nan yaga fiye da 5/6 na mutanen cikin jirgin duk sun wula zuwa duniyar bacci,wad'anda basu yi bacci ba baifi a lissafa su ba,murmushi yayi sannan ya juya ga abar k'aunarsa yana kallon yadda take wani irin wahalallen bacci saboda wuyanta daya lankwashe,belt d'in jikinsa ya cire sannan a hankali ya matsa kusa da ita sosai yana kallon kyakykyawar fuskarta,murmushi ya sake yi gently sai ya d'ora mata light kiss a saman lips d'inta da suke ta kyalli,lamarin daya haddasa masa jin wasu irin mugun feelings suna taso masa har yayi dana sanin aikata hakan,,a duk lokacin da zai kusanci inda take shi da kansa yasan me yake ji game da ita,sai dai kawai yana daurewa ne,buh a bayan duka Daddy ya kasa fahimtar damuwar,yanzun ma da yake daf ji yake kamar kada ya kyale tunda dai yanzun mallakinsa ce,amma kasancewar yana ganinsu cikin jama'ar da babu tabbas ace wani bazai farka ba shi yasa dole ya sawa zuciyarsa hak'uri har su sauka,kura mata idanu yayi deeply yana ayyanawa a ransa a yau komai zai zama tarihi,sai ya lumshe ido yana sakin bayyanannen murmushi kafin ya bud'e idanunsa akanta,sai daya kalli bayansa da gefe saboda gudun kada wani ya gansu sannan ya juyo ya kalleta,still dai baccin take amma wannan karon a jikinsa ne saboda ya gyara mata kwanciyar shi yasa itama sai taci gaba da juyi a cikin jikinsa ba tare data sani ba,k'asan chin d'inta ya rik'o slowly sai ya d'an d'ago fuskarta dai² yadda zai iya aiwatar da abunda yake so,yana kallonta da murmushi kwance a fuskarsa kamar ance masa idanunta biyu sannan ya kai bakinsa saman nata,passionately sai ya tsotsi lower lip d'inta sannan ya d'ora mata peck a forehead da fad'in
"Sleep tight Helpmate..!"

Gyaran murya Sultan yayi dake a bayansu suke su kuma su BADRA suna d'ayan hannun a centre d'insu,ba tare daya juya ba yace
"Ya dai Malam..!?"

"A dunga yi dai ana gimtsewa dai.."

"Saboda mene ne..!?"

"Kada a ji kunya a gaban al'ummah.."

"Kunya akan halalin nawa..!?"
Sai yayi murmushi kawai daga haka bai sake cewa wani abu ba ya lumshe idanunsa yana ci gaba da shak'ar k'amshin turarukanta masu dad'i da kwantar da hankali,sake yin gyaran murya Sultan yayi ba tare da Hammad ya juya ba yace
"Fad'i abunda yake bakinka.."
A hankali Sultan ya matso daf da shi ta bayan cikin muryar rad'a yace
"Amma nace ba,,shin zaka bani k'anwar taka..!?"

"A'aahh.! Bazan bayar ba.."

"Haba yallab'ai,kayi hak'uri mana ka tausayawa wannan bawan Allah'n.!"

"Ko kuma tuzuru ba..!?"

"Ehh! Naji ni dai ko me zaka fad'a bazan damu ba,ka amince ka bani k'anwarka shi ne burina.."

"Shi kenan ka bari nayi tunani.."
Harararsa Sultan yayi ba tare da ya sake yin magana ba sai shima yaci gaba da duba magazine d'in dake hannunsa yana murmusawa,while shima Hammad sai yaci gaba da lallab'a abar k'aunarsa,yana fatan su sauka cikin salama.....




#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••

*46.*
_#The Amatory_

Har jirginsu ya sauka a New York Sabina bata farka ba kuma still d'in tana cikin jikinsa,sai dai time to time ta sake gyara kwanciya ko shi ya gyara mata,,izuwa lokacin kam duk wani sauran hak'urin da Hammad yake jin yana da shi da y'ar dauriyar data masa saura tuni ya nemi k'arewa,har ta kai shi ga komawa addu'ar su sauka lafiya haka nan,cos shi dai ya sani ba zai iya ci gaba da jurewa ba,kuma har ga Allah yana ji idan aka ce zasu k'ara sama da wasu y'an awanni tabbas zai iya yin abunda ba shi kenan ba.
Da misalin k'arfe 9:00pm a gogon na Nigeria wanda yayi dai² da 3:00pm a agogon k'asar ta U.S,wanda idan muka lissafa tazarar dake tsakaninmu da su zai bamu adadin rata na awanni shida,jirginsu ya sauka a katafaren filin tashi da saukar jirage na *LaGuardia airport* dake nan cikin New york City d'in,,sannu a hankali jama'ar dake cikin jirgin wad'anda suka farka daga nauyayyen baccin daya d'auke su har zuwa wad'anda suke ido biyu a lokacin sai kowa ya hau kimtsa jikinsa saboda jirgi ya riga ya sauka k'asa har an bud'e k'ofar fita,,sai a lokacin da jirgin ya samu damar isowar sannan ita da kanta ta tashi ba tare daya tada ita ba,,jinta kwance a jikin abu yasa sai ta d'an bud'e idanunta da sauri,kwance ta ganta sadidan a saman k'irjinsa,,tunanin lokacin data shige masa ta fara,sai dai iya son ta binciko lamarin ya gagari tunawarta,d'an motsawa tayi a hankali sannan ta d'ago kanta ta kalleshi,hakan da tayi sai ya tabbatar masa ta farka nd tana so ta tashi,hannunsa daya zagayeta da su ya zare ba tare da yayi magana ba,a hankali itanma sai ta mik'e duk a rikice saboda irin kallon da su Jannat suke binta da shi,zumbur kuma ta wuce ta nufi hanyar toilet d'in cikin jirgin,,a hankali mutane suka fara fita cikin nutsuwa,,Hammad kam tunda ta tashi bai samu damar motsawa ba,sai da yaga fitowarta sannan ya tashi suka kamo hanyar fitowa a taren,a wajen suka iske su duka suna jiran fitowar su,bayan an gama musu duk wani checking sai suka tattara da su da kayansu suka bi cab's da zasu kaisu gida.
A cikin mintuna k'alilan suka iso mid Manhattan dake a fifth avenue nan cikin birnin na new York,,tunda suka shigo cikin arean 56th street yanayi yadda tsarin unguwar da gine²nsu suka kasance masu dogayen benaye gwanin burgewa duk sai suka ji suna matuk'ar son tsarin gurin,daga *SABINA* har su kansu duka sauran y'an matan sai suka ji gurin yayi musu sosai,musamman kuma daya zama quite place ne babu ruwan wani da wani kowa harkar gabansa yake,kallon tsarin gurin ta sake yi a hankali sai ta lumshe idanu tana shak'ar sanyayyar iskar dake busawa mai tattare da ni'imomi tana murmushi,lokacin da cab d'insu ta samu damar tsayawa a carline dake gefen k'aton ginin na *TRUMP TAWER* sannan ta samu damar bud'e idanunta suka fita,tana fitowa sai ta sake d'aga kanta tana kallon ginine²n,ita dai tunda take ko da da yake basu cika yin nisa daga cikin skul d'insu ba a iya zuwanta sai take ganin kamar bata tab'a ganin gini irin wannan ba,har bayan an sallami masu cab da suka kawo su bata sani ba,tana can kallon ikon ubangiji da kallon ginin da suke tsaye a gabansa da yake da hawa² masu matuk'ar yawa,nd ya kasance anyi shi ne da wani irin concrete construction na dark glass curtain wall,daga can d'an nesa kad'an ta saman entrance na ginin harda wani design da aka masa ya bada wasu stepped facade,su kansu kuma stepped corners d'in dake jikin ginin sai aka yi filling d'insu da wasu irin shuke² masu kyau,sake d'aga kai tayi a hankali ta kallo can k'ololuwar samansa,tsabar nisan da taga yayi mata sai ta juya ta kalli sauran dake gefe da gefe da basu kai shi ba,kanta taji ya fara neman juyawa a hankali sai ta sauke idanunta k'asa dan kallon gine²n yasa ta fara ganin kamar zasu ruguzo mata a kai,a ranta kuwa tambayar kanta take ko ginin zai kai hawa nawa.? Cos ita dai a iya d'aga kanta da tayi bata iya gane ko hawa nawa ne da shi ba,,security ne a ko ina barbaje suke tsaron gurin suma saboda yawan su har ba'a cewa komai,da yake a cikin ginin akwai gidan shugaban k'asa Donald Trump a mafi k'ololuwar nisa

Please Login or Register in order to submit comment