Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lallab'a suka dawo suna tafiya a sad'ad'e gudun kada ta kamasu sun d'auka mata phone da yake ta hana su tab'a mata,saura k'iris Seeyah tayi ihu lokacin da taga Feeyah ta d'auko wayar da sauri sai ta rufe baki,har sun juya zasu bar gurin suna b'oye wayar Sabina dake kwance jin motsinsu yasa ta bud'e ido tana kallonsu
"Me kuke yi ne a nan..!? Bance ku sanar da Nanny ta shirya ku kuje gidansu Meenal ba..??"
Tana magana tana sake tsare su da ido
"Asfiiy Mamma,,nahna halla sanazhab fauran.!"

"Yallah! bisir'a..!"
A gurguje suka juya suka bar wajen,suna shiga Seeyah ta kira wayarsa,bayan kiran ya tafi sai tasa wayar a hands free suna ta addu'ar ya d'auka,fuskokinsu d'auke da damuwa lokacin daya d'auka wayan har suna had'e baki wajen cewa
"Appa..!"
Jin maganar yaransu yasa da sauri yace
"Mammana.!? Yaya aka yi ne.!?"
Hankalinsa a d'an tashe cos yasan ba k'aramin abu ke sawa yaji sunyi magana a waya first ba kafin ita
Seeyah tace "Appa dama Mamma ce." Sai suka yi shiru kuma kamar za suyi kuka,a mugun hargitse yake tambayarsu
"Me yake faruwa da Mamman naku..?"
Kuka Feeyah ta saka tace "Appa! We don't even know what's happen..but she's so sad all the time."
A gaggauce yace "Okay.! Kuje maza ku kula da ita,yanzun zan k'araso,kun ji ni ko..? But kada kuce ina dawowa,kunji ko..??"
Suka amsa da "Toh" lokacin da suka ajiye wayar kasa fita suka yi suna kallon juna Seeyah tace "Toh yanzun idan Mamma ta san mun d'auka mata waya yaya zamu yi ne..!?"

Feeyah tace "She won't even care.."

"Noo habibtiiy.! U know Mamma tana mana warnings akan d'auka mata waya fa.."
Kafad'arta Feeyah ta rik'e tace "Kada ki damu 6ter zan mayar yanzun,i promised baza ta sani ba.."
Kad'an Seeyah ta yada kai gefe,suna ta tattaunawa akan yadda za'a mayar da waya suka jiyo doorbell na ring,haka nan feeyah sai tayi tsalle tace
"Yeeeehhh! Ga Appa nan,,muje mu dubamm" a guje sai suka fita ko uniform d'in basu yi detaching ba,,lokacin da suka fito tuni har Nanny d'insu ta zo ta bud'e masa k'ofa,a agujen yadda suka fito har suka isa gare shi suna masa welcome,yana kallon cikin parlor'n yake tambayarsu
"Where's ur mom..!?"
Seeyah tayi masa nuni da hanyar bedroom d'insa cos suma d'in da suka fito basu ganta ba,amma sun san bazai wuce can taje ba,a hankali yace to su je su cire kaya sai suzo su tafi clinic,amsawa suka yi suka barshi nan a parlor'n,yana ganin tafiyarsu ya juya ya wuce master bedroom d'insa,,kwance ya ganta saman bed tayi covering jikinta da spread jikinta yana tsananta shivering,hankalinsa a d'an tashe ya nufe ta yana fad'in
"Subhanallah..! Helpmate wane irin ciwo ne haka in time..??"
A wahalce ta d'ago idanunta da suka koma ja tsabar kukan da tayi bayan shigowarta tana kallonsa,yadda yaga fuskarta ta tasa nan da nan yayi kicin² yana kallonta yace
"Kuka kuma..??"
A hankali ta mayar da idanunta ta kulle tana sakin sabbin hawaye,yadda ya ganta cikin yanayin damuwa sosai hankalinsa ya sake tashi cos ya manta rabonsa da ganin hawayenta,a hargitsen ya haura saman bed d'in ko takalmansa bai tsaya zarewa ba ya d'agota zuwa jikinsa
"Please Rooh.! Na rok'eki ko daina hawayen nan haka tun ba yanzun ba,,shin sai wane lokaci ne zaki daina sawa ina shiga damuwa akan kukanki.?? U know yanzun muna da yara,bamu kad'ai bane fa a gidan,idan har yaran nan suna ganinki a damuwa haka laifina zasu koma gani,cos za suyi tunanin ina takura kine,but a yau zan sake rok'on ki da girman Allah kada ki bari ko da wasa kiyi kuka a gabansu.."
Ajiyar zuciya ta sauke tana bud'e idanunta a lokacin sai ta bud'e baki da kyar tace
"In sha Allah i won't.."

"Ummhhum.!" Yace kafin ya sake cewa "Tashi to muyi magana yanzun.. Ai zaki sanar dani abunda yake faruwa ko..?"
Tana kallonsa bayan ta gyara kwanciyarta a jikinsa ta labarta masa duk yadda suka yi da Inna babu jimawa,,abun mamakin da yayi ne a lokacin ya d'aure mata kai,shi ne murmushin da yake kwance saman fuskarsa,a d'an dame sai ta tsaya kallonsa da mamakinsa kafin tayi k'arfin halin cewa.....





#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••
*In sha Allah few page's suka yi remaining na kai k'arshen labari,,ku k'ara hak'uri tak'i kad'an ya rage min na gama na huta,kuma ku huta da jira.*💞

*57.*
_#Trial_

"Wai mene ne kake wani murmushi..!?"
Yana kallon idanunta yace "To da kuka kike so nayi..?? I thought Inna tace ayi ko..!?"
Ta gyad'a masa kai,sai yace
"An gama magana,tunda har Inna tace,mu d'in su waye da baza muyi mata biyayya ba..?"
Kasak'e tayi tana saurarensa kafin tace
"To kai baka tuna abunda yayi min bane!?"
Yace "Idan na tuna mene ne za'ayi yanzun..? Abunda akayi ya wuce since year's back,ai babu amfanin taso shi ko..?? Nd idan kika duba yadda rayuwarki ta inganta yanzun ko saka shi akayi da kud'i ya rik'e even a side na vail da kika rufa,he won't touch,cos yasan abunda ya faru a baya,wanda zai faru yanzun bazai yi dad'i ba."

"Amma to ai ni ban manta ba.."
Yana kallonta yace "bakya yafiya ne wai..??"

Tace "Mutunci nafa ya so karb'ewa." Yace "ya karb'a d'in ne..!?" Tace "A'aahh" sai ya rik'o fuskarta yace
"To me yasa baza ki manta ba,tunda babu abunda ya faru dake..Ina ganin ya kamata ki yafe masa."

"Ni dai gaskiya A'a,, I won't forgive him..!"
Murmushin takaici yayi yana kallonta yace
"Me yasa sometimes kike da kafiya ne..?? Abu ya wuce da jimawa amma yafewar ne zai gagare ki..?? Kada ki manta he's part of ur family.."

"To dan yana ahalina,ni kuma saina yafe masa da wuri..?? Gaskiya i won't."
Sosai yake kallonta da mugun mamaki yace
"Look my frnd.! Can't u think idan kin yafe masa kema Allah zai duba naki laifukan ya yafe miki..?? Ko kuwa mu saboda son kanmu ne zaisa idan anyi mana laifi muce baza mu yafe ba amma kuma muna so mu a yafe mana.?? Think wisely mana Rooh,abun nan ya faru da jimawa ne,ya kamata ace kin manta da faruwar sa gaba d'aya cos Allah ya tsare ki tun wancan lokacin.. Idan fa har muka ce duk wanda zai mana laifi baza mu yafe masa ba,mu muyi yaya da namu zunuban..?"

Tace "Ai Allah zai yafe mana,tunda bamu zalunci kowa ba.."
Kawar da kansa yayi gefe yace "U believed in Allah zai yafe miki naki amma kuma ke baza ki yafewa wani ba,idan har bakya yafewa Allah'n zai kalle kine..?? Kada ki manta Ubangiji da kansa yace yana son bayinsa masu yafiya,,me zai sa ki bari shaid'an ya fara k'ok'arin yin nasara akanki..!? Ya kamata ki canja tsarin zuciyarki,kin fahimci abunda nake nufi ai..?"
Slightly ta tab'e baki cikin k'unk'uni tace "Ni wai yaya akayi ka dawo yanzun..!?"
Bai damu da amsa mata tambayar ba ya mik'e yana niyyar fita ta sake cewa
"Magana fa nake,ka kyale ni..!"
Waiwayowa yayi ya kalleta yana fad'in
"Yaya aka yi ne.!?"

"Na ga ka dawo yanzun ne,so ban san mene ne ya dawo da kai da wuri ba..!"
Tab'e baki ya sake yi yana bud'e k'ofa zai fita yace "Mene ne damuwarka dan na dawo..!?"

"Babu" tace tana mik'ewa daga kwanciyar da tayi,har ya kai k'ofa ta sake cewa
"Ina to zaka jene yanzun..!?"
Bai juyo ba yace "Kina da matsala da fita ta ne.!?"

"Ehhh.!" Tace tana biyo bayansa

"Fad'i ina saurarenki.."

"Ka tsaya to muyi magana.." Tace tana b'ata rai,bai damu daya tsaya ba saboda yasan ta da halin kafiya yanzun kafin ya samu ta dawo hanya sai yayi da gaske,shi yasa tun farkon ya yanke shawaran biyo mata ta nan,cos idan har tak'i karb'a case d'in d'an uwantan da duka yak'inin iyayenta yake kanta,laifinsa za su gani,shi kuma hakan ne baya so shi yasa ya d'auki niyyar sata a hanya
"Please ka tsaya,,ina son magana fa da kai.."
Still bai juyo ba har ya k'araso entrance na d'akin yaransu,itama kuma bata gaji ba taci gaba da binsa a bayan har suka shiga d'akin tare,Nanny suka tarar a lokacin ta gama shirya su suna ta mata hira tana biye musu,suna gaisawa Nanny ta fita ta barsu a d'akin,,twins kuwa ganin iyayensu a tare da gudu duka suka yo gurinsu,Seeyah na kallon Appa'nta tace
"Appa.! Ya jikin Mamma..!?"
Murmushi yayi mata mai sanyi bai ko kalli inda ta tsaya ba yace
"Gata nan ta warware.."
A hankali sai yarinyar tayi murmushi tana kallon Sabina dake kallonsu tace
"Mamma.! How are u feeling.!?"
Sai data lumshe idanunta tace "Am cool habibtiiy.."

Feeyah ma ta matso jikinta a lokacin ta d'aga kai tana kallonta da fad'in
"Mamma.! Are u crying..!?"
Saurin kallon Hammad tayi dake tsaye yayi kicin² da ransa sai ta k'irk'iro murmushin yak'e tace
"Noo! Habibtiiy kaina ne yayi min ciwo shi yasa kika ga kamar nayi kuka.."
Kad'a kai Feeyah tayi tace "Sannu to,kinsha magani..!?" Sabina data tsaya kallonta da mamakin surutunsu ta kad'a mata kai alamun Ehhh,rungume ta yaran suka yi cike da kulawa sai suka ja hannunta zuwa saman bed d'insu while suna fad'in
"Mammah.! Muje ki kwanta to ki huta,sai muyi miki massaging irin yadda kike ma Appa,in sha Allah zai daina duka.."
Murmushi ta sake yi musu,a hankali cikin nutsuwa ta kwanta suka sata tsakiyarsu,calmly suka kai soft nd tiny palms d'insu suna mata massaging kanta da yayi mata wani iri sakamakon kukan da tayi,Hammad kam tsayawa yayi kallonsu cike da k'auna da fatan kusancin su da yaransu ya zama mai girma ta yadda babu wani damuwar da zai hanasu sanar musu komai daya jib'inci rayuwarsu.Bai wani jima sosai ba a tsayen tunda yaga yanzun ta sake da yaran sai ya juya ya fita,,da yake duka excuse ya d'auko a gurin aikin bayan fitarsa master bedroom d'insa ya koma da niyyar yayi wanka ya huta kafin zuwa salatul asr,,lokacin daya bari ya gama duk wani uzurin da zaiyi,yana zaune gefen bed rik'e da phone a hannunsa ya fara k'ok'arin kiran line Inna cos yana son jin kan yadda al'amarin yake,lokacin data amsa kiran after sun gaisa,sosai suka d'auki lokaci suna magana akan waya,kafin suka yi sallama,,shi kad'ai bayan ya gama yake sake nazarin maganar Inna akan case d'in,ya d'an d'auki lokaci zaune shiru da tunani iri daban² kafin ya koma ya kwanta,babu jimawa sarkin b'arayi yayi gaba da shi.

Da dare ma dai kusan labari ne ya so maimaita kansa,lokacin sun gama shirin bacci yake tambayarta ina maganarsu ta kwana.? Tace "ya bari ba yanzun ba,ita gaskiya bacci ma take ji duka" daga haka duk niyyarsa ta son suyi maganar bai yiwu ba,haka ya hak'ura ba don yaso ba ya kyaleta,wasa² tun daga wannan ranar sai da suka shafe kusan sati biyu yana binta da batun tana gocewa,ranar daya gaji ne da lamarin ya sauke mata fushinsa cikin fad'an da bata tab'a zaton zai mata ba,kuma daga ranar gaba d'aya sai ma ya daina tada mata zancen gaba d'aya,a hakan kwanaki suka sake zuwa suka wuce.

*NIGERIA..*
Tun da sanyin safiya gaba d'aya hankalin kowa dake cikin family'n kusan a iya cewa baya jikinsa,,saboda kasancewar ranar yau d'in itace rana ta farko da za'a fara halartar court domin sauraren case d'in su LADO,,gaba d'aya family sun tattara a gidan Baba tin jiya kowa jira yake lokacin shiga court yayi suji yaya lamarin zai tafi,duk da har kawo lokacin basu san a matsayar da al'amarin LADO yake ba,,amma ran Inna zuwa lokacin ya gama b'aci,gashi sai gwada kiran line Sabina take amma sai ake shaida mata a rufe wayar take,gefe guda kuma ga lokaci sai dad'a tafiya yake ba tare da sun san abunda yake going through ba.K'arfe 10:00am shi ne k'a'idar lokacin shigarsu court,,tunda garin Allah ya waye kowa hankalinsa na kan agogo yana hararar lokaci,da misalin k'arfe 9am bayan duk sunyi break a daddafe gidan gaba d'aya suka tattara suka kama hanyar court,kowa dai jikinsa a sanyaye har lokacin saboda rashin sanin tayi.Wasa² har misalin k'arfe 9:56am shiru babu wani labari dangane da zuwanta ko akasin haka,dan haka izuwa lokacin gaba d'aya kowa sai ya fara fidda tsammanin zuwan Sabinar.

Da misalin 10:00am agogo yana bugawa,masinjan court ya lek'o yayiwa jami'an tsaron da suke tare da su LADO magana,aka tusa k'eyarsu zuwa cikin court da tayi wani mahaukacin cika,,bayan shigarsu d'akin yayi remaining silence na wani lokaci,baka jin komai sai motsawar fankokin dake aiki,alk'ali na sama yana kallon yadda aka yi shiru ana sauraren aji cewarsa,sai daya gyara zaman glasses d'in idonsa kafin yace
"Muna sauraren k'ara ta gaba..!"
Magatakardan court ya mik'e,yayi gaisuwa sannan ya fara koro jawabin k'arar da ake,da laifukan da ake tuhumarsu LADO da shi,y'an rubuce² alk'ali yayi saman takardun da Magatakarda ya mik'a masa kafin ya d'ago yana fad'in
"Ina wad'anda ake k'ara..??"
Aka shigo da su LADO duka hannayensu da handcuffs aka sasu cikin bars,alk'ali ya sake juyawa ya kalli taron court ta b'angaren lawyers yace
"Lawyoyin gwamnati da lawyoyin wad'anda ake k'ara idan suna kusa su gabatar da kansu.."
D'aya bayan d'aya lawyoyin gwamnati suke mik'ewa suna gabatar da kansu har su uku,kafin alk'ali ya juya kan su Lado yace
"Ko kuna da wad'anda zasu tsaya muku a cikin wannan shari'a..!?"
Suka ce "Babu." Alk'ali ya jinjina kai kafin ya sake maida kai ga lawyoyin gwamnati yace "bismillah",,ba'a d'auki lokaci mai tsayi ba,tiryan² suke jerowa alk'ali tarin laifukan da ake tuhumar su LADO da shi wanda bayan robbery har da su kidnapping,rapping cases,sannan ga smuggling na miyagun kwayoyi,lokacin da aka gama karanta musu laifukansu alk'ali ya kallesu yace
"Ko wani cikinku yana da tacewa akan laifin da ake tuhumarsa." Saura suka ce "Babu yah mai shari'a" sai daya girgiza kai,yana shirin yin rubutu Lado yayi caraf yace
"Ina da shi Yallab'ai.."
D'agowa alk'ali yayi yana kallonsa kafin yace
"Mene ne maganarka..!?"
Lado yace "Yallab'ai.! Sam duk wasu laifin da aka lissafo ni kam ban san na aikata ba,hasalima duka wad'annan mutanen da aka had'a ni da su bansan ko su d'in su waye ba."
Wani a ciki ne yayi saurin cafewa yace "K'arya yake yallab'ai, yasan komai kuma tare muke yi,idan k'arya nake ga saura nan a tambayesu.." Alk'ali ya tambayesu ko haka ne.? Suka ce "Ehhh.!" Y'an rubuce² alk'ali yayi sannan yace
"Bisa ga k'wararan hujjoji da amsawar masu laifi akan tuhumar da ake musu,ba tare da sun wahalar da shari'a ba,wannan court mai albarka zata yanke musu hukunci bisa ga laifukansu... Hukunci na farko bisa ga tabbatarwa da aka samu akan laifin fyad'e,a dokance hukuncin daya rataya a wuyan duk wanda aka samu da wannan laifin za'a tura shi gidan maza har na tsayin shekaru 25,,sa'annan ga duk wanda aka kama da aikata laifin fashi da makami,hukuncin daya hau kan wanda aka tabbatar yana aikatarwa shi ne d'aurin rai da rai,,sai hukuncin wanda yayi garkuwa da mutune shima a dokance wannan d'aurin rai da rai ne ya hau kansa,shigowa da mugayen kwayoyi daga wata k'asa ta hanyar sab'awa dokar k'asa,idan har aka kama mai wannan laifin za'a d'aure shi a gidan kaso har na tsayin shekaru goma,,,bisa ga tarayya da sukayi wajen aikata laifi da yin gamayyar manyan laifuffuka,,wannan court mai alfarma ta yanke musu hukuncin *KISA TA HANYAR..!"*

"A dakata ya mai shari'a..! Ina da abun cewa.!"
Muryar tayi amsa kuwwa a cikin court,,saurin juyawa mutane sukayi zuwa baya da nufin ganin waye,amma ga family'nta ko da suka hangota tsaye sanye cikin robe da wannan hood d'in na lawyers a saman kanta,wani irin yalwataccen farin ciki suka shiga,Baba ma ba'a barshi a baya ba dan kalmar
"Alhamdulillah.! Alaa kulli halin.." Shi ne abunda yayi ta maimaita fad'a yana sake kallon y'ar tasa da take shigowa tana sake fad'in
"A gafarce ni ya mai shari'a saboda rashin k'arasowa da wuri.."

*SOME HOURS BACK AT NEW YORK CITY...*
_(Mid Manhattan,area:5th avenue,56 street,Trump Tawer).._

Tana kwance tayi d'ai² cikin mayen bacci taji yana tashinta,sannu a hankali ta fara ware idanunta har ta gama bud'e su tar akansa tana binsa da wani irin kallo mai shiga zuciya
"Tashi ki shirya mu tafi..!"
Shi ne abunda yace da wannan husky voice d'in nasa na asalin,cikin murya irinta mutumin dake tsaka da bacci aka katse shi ta ware ido tana kallonsa tace
"Ina zamu je da wannan daren.??"

"Tashi ki shirya,ni bance ki tambayeni inda zamu ba.. All I want from u shi ne ki bini duk inda nace.."
Tsayawa tayi kallonsa har ya gama maganar kafin ta sauka daga saman bed d'in tayi hanyar bathroom,saurin kallonta yayi yace
"Kiyi sauri fa,kinsan bana son jira."

"Uhhuumm.!" Tace ta wuce ciki,fuskarta ta wanke da bakinta ta d'auro alwala,bayan ta fito,ta tarar har ya ajiye mata Arabian gown a gefen gado,ita dai mamaki take da lamarinsa musamman a cikin kwanakin,to amma tana so ne ya dawo dai² shi yasa ko a yanzun ta kasa yi masa musu a gaggauce har tasa rigar tabi bayansa,a parlor ta iske shi zaune saman armchair yana jiranta,tana fitowa ya mik'e da sauri ya wuce gaba tabi bayansa jikinta a sanyaye,har suka sakko carline babu wanda ya yiwa wani magana sai da taga yana k'ok'arin tada mota sannan ta juya ta kalle shi tana fad'in
"Hayat..! Baka min bayanin inda zamu bafa da wannan daren.."
Bai tsaya kallonta ba yace
"Idanunki zasu gane miki koma inane zamu je.."
Sai yayi shiru bai sake cewa komai ba itama haka,hanyar LaGuardia airport da taga sun d'auka da sauri ta sake kallonsa tace
"Amma fa dear bai kamata mu taho mu bar yara ba.."
Bai damu daya kalleta ba yace
"Mene ne zai same su..? Suna tare da Nanny,nd su Badra too,sai mene ne dan mun taho babu su..?? Skul d'in nasu zamu katse ne muce sai mun taho da su..?? Idan batun kariya kike yi kuma ubangijin daya haliccemu ya fiki sanin su d'in yara ne,so kiyi min shiru kawai bana son yawan magana.."
Shiru tayi bata sake tankawa ba saboda ganin temper d'insa ta fara haurawa,shima sai yayi shirun har suka iso airport aka musu abunda ya dace suka wuce,,within few minutes da isowarsu jirgi ya d'aga dasu zuwa 9ja cikin wannan daren ba tare da sun sanar da su Sultan ba haka suka d'auko hanya,,ko cikin jirgin ma da suka shiga babu wanda ya samu damar yin magana,a hakan suna zaune kusa da juna,ita dai data samu gefen window tana gyara zamanta ko da taga tafiyar kurame za suyi nan wani daddad'an bacci ya sake kwasheta,kallonta kawai ya tsaya yi lokacin daya tabbatar tayi nisa a bacci sannan ya gyara mata Vail d'inta da yake k'ok'arin zamewa,,tsayin awannin da suka shafe a cikin giragizai suna shawagi gaba d'aya bai samu dama ya iya runtsawa ba har jirginsu ya sauka a Kano,daga airport lokacin da suka d'auko cab sai suka gidansu,a gaggauce bayan sun iso suka samu suka yi wanka tare,suna fitowa shi da kansa ya shiryata cikin kayan lawyoyinta itama ta taimaka masa ya shirya cikin k'ananun kaya da suka ainihin karb'arsa,,tunda suka gama abunda suke ko breakfast basu yi tunanin yi ba saboda a lokacin abunda ya rage a 10am baifi mintuna ashirin ba kuma sun san dole zasu gamu da matsalar traffic a hanya,shi yasa suka yanke shawaran sai sun dawo d'in,suna tafe yana tuk'i a hanyar su na tafiya ba tare daya juyo ya kalleta ba yace
"Kin san abunda ya kawo mu ai ba..??"

Tana kallonsa ta had'iye wasu terrified saliva's a hankali ta kad'a masa kai,d'an waiwayowa yayi ya kalleta slowly kafin yace


Please Login or Register in order to submit comment